Join Our WhatsApp Group

FANSAN RAN MAHAIFANA Complete Hausa Novel Document by FANSAN RAN MAHAIFANA


FANSAN RAN MAHAIFANA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 39198



FANSAN RAN MAHAIFANA

Reading Time: 3 Hours

Added On: 06, Oct 2023

Author: Nana Khadijatu ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : ????AINUWA ????RITER'S

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 235.62 kb

File Type: txt

Views: 486+

Download: 288+

Last download: 12 hours ago

Description/Story: 👩‍❤️‍👨 *FANSAR RAN MAHAIFAINA* 👩‍❤️‍👨


BY KHADIJA

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


I dedicated this page to my lovely mommah❤️❤️long life is my wish insha Allah



01-02
Babban compound ne me dauke da bishiyu da shuke -shuke da ka ga gidan naira ta jiku, gidan yana da bangare biyu babba da karami da kaga babban shine main house din karamin BQ ne bangaren masu aikin gidan

Wani tangamemen parlour ne da yayi masifaffen tsaruwa kana shiga wani shihirtacen kamshi ne ze ziyarce ka, Misalin 10:55pm wata mata ce ke saukowa daga stairs tasha buban leshi ga kunnen ta yasha dan kunnen gwal, muryar ta naji me dadin sauraro da saura kiris alkalami na ya fadi tana fadin amrah bazaki tashi kije ki kwanta ba kallon ya isa haka salon da safe a tashe ki kiki tashi alhalin kinsan kina da school ke kullum bakya gama shiryawa se a hanya tun yanzu gwara ki gyara kafin ki rasa me maki fadan nan.



Yarinyar da aka kira amrah ce ta dago ammi dan Allah kiyi hakuri sponge Bob nakeson karasa kalla saura 4 minutes a gama ana gamawa zan kwanta pls kuma ammi kidena zance mutuwa,


Ammi ta harare ta tare dayin kwafa tace karma ki tashi ki barin in hadawa abiey coffee in futo baki tashi yarinyar na karewa kallo baza ta Gaza 10 yrs ba


Ay ana gamawa amrah ta tashi a guje tayi upstairs dakuna uku ne a saman nata na ammi se na abiey wani daki ta nufa tare da sallama amsawa akayi daga ciki wani magidanci ne da akalla yayi 45 yrs da laptop a gabansa kome yake oho taje ta Rungumeshi tana abiey naam uwata( saboda sunan babarshi gareta Maryam) me kike baki kwanta ba kallo nake tana wasa da sajen fuskarshi shi to maza a je a kwanta


“Nace oh ni yasu yarinyar da aka ce ta kwanta ce tazo nan”


Knocking akayi “yes come in” bakin ta dauke da sallama ta shigo hannun ta rike da karamin tray da mug akai turus tayi tana kallon amrah tsawa ta mata da ta gigitata malama tashi kije ki kwanta,


Abiey ya dago yana fadin Haba falmata ki dena mata tsawa haka sai ki firgitata se tana tsoron ki, dama Alh kai ke goyon bayanta take abun da taso


Tashi tayi sum sum tace masu good night Ammi tace karki manta da addua abiey ko ya ce sweet dreams uwata fita tayi dakinta ta nufa wanda komai pink and purple ne gadon ze dauki mutum uku anjere teddy's akai



Bayan fitar ta ammi ya rufe laptop din ya kalleta tace Haba Alh kayi aiki a office a gida ma aiki ya kamata ka ringa hutawa sipping coffee dinsa yayi tare da fadin angama madam na dena yana kashe mata ido



Murmushi kawai tayi bari nayi wanka dama shi yayi
Kasa ya sauka kayan kallo da futulu yayi tare da tabbatar da kofar a rufe take saman ya koma direct dakin amrah ya nufa ya tarar harta chanja kaya tayi bacci murmushi yayi ya ja mata duvet ya rufe ta saboda ana sanyi-sanyi, addua yayi mata ya bata peak a goshi ya kashe fitila kofar yaja mata


Dakin sa ya nufa ya tarar Ammi ta kwanta shima kashe futula yayi ya bar dim light kwanciya yayi ya rufesu nan naja masu kofa nace asuba ta gari Mr and Mrs Abdulmunaf.........


***********

Da safe misalin karfe 6:30 Ammi ce a dakin amrah suna ta tataburza akan ta tashi tayi shirin school


Amrah ta turo bakin ta ciki shagwaba da magagin bacci tace dan Allah ki karan 10 minutes

Anki din bazan kara ba ace ki kwanta da wuri kitsaya kallon yayan aljanu oya tashi ki kuma tabbata kafin ki futo Kinyi sallah da gyaran gado if not hmm ni da ke ne Kinji ko



Tana bubbuga kafa tace toh tare da fadawa toilet


Ammi binta tai da kallo tana fadin Allah dai shiryamin ke ta fice


Kitchen ta nufa ta tarar da saude me kula da harkar kitchen harta shigo durkusawa tayi hajiya ina kwana lpy kalau kin gama hadawa amrah lunch box din



Aa nadai kusa , OK In kin gama seki maku anun kari keda Adama bata shigo bane..... Sallama akai ammi ta amsa Adama kin shigo ehh hajiya ina kwana lpy kalau Dan Allah ki maza ki share parlour kafin alhaji ya sauko sannan kisa turaren gurin yana ay kin ganeshi ehh yauwa kayan sharar ta dauke ta futa


Ammi kiciniyar hadawa abiey abun kari dan ita Sam bata yarda masu aiki su yi ma mijinta girki



Tana gamawa takai dinning ta jere


Hawa upstairs tayi dakin amrah ta shiga ta tarar da ita a akwance a bakin gado daga ita se towel alamun tayi wanka,



Ammi a harzuke ta kama kunnenta ta murde kuka tasa mata

Ke wai amrah mesa kullum kike son sani magana


Ayy bata bar dakin ba seda ta shirya school bag ta dauka sauka tayi ita kuma ammi ta wuce daki domin yin wanka


Tana futowa ta shafa lotion da humrori a jikin ta shiryawa tai cikin riga da zani na atamfa me adon ganye tare da daura daurin zahra buhari fes ta futo yar chubby da ita kamar ka sureta


Futa tayi ta nufi dakin alhaji har ya shirya yana sa links turare ta fesa masa tare da daukar briefcase nasa suka sauka parlour.


A guje amrah ta rungumesu tana gaishe su Kinyi breakfast “yes"Ammi ta rike kumatun ta good girl to kije malam idi ya sauke ki


Peak tabasu ta fice suka tafi


Su kam dinning suka nufa Bayan sun gama karyawa alhaji ya wuce office



Wata katafariyar school aka sauketa direct class ta nufa primary 3b na gefen staff room Bayan shigar ta se ga wata saar ta tashigo Rungume juna su kai


Yarinyar duban amrah tai tana fadin yau bestie kin riga ni zuwa

Ay nasreen in fada maki ammi ce kwana biyu.... Bata karasa maganar ba sukaji ringing bell na assembly suka fice



*********
Da yake yau Thursday ne sports zasuyi dan haka kowa field ya nufa Bayan assembly banda amrah da nasreen aminan juna


Seda suka ga an tafi field suka shiga aji wani seats naga sun nufa


Hmmmm nasreen kinsan wannan yar rainin HanKali dan taga ita kadai tayi maths assignment shine take wani daga Kaii bata hadu damu bane ai


Bag din yarinyar suka bude suka ciro maths da English exercise book dinta suka yayyaga tare da sawa a dustbin



Tafawa sukai amrah na fadin gwara da muka hada har English din yar iskar yarinya

Futa sukai tare da nufar field din............ ✍🏽✍🏽✍🏽

👩‍❤️‍👨 *FANSAR* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨





BY KHADIJA

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


I dedicated this page to my aminiya ta masoyiya ta mummyn maheer💃( my zakara) ina sonki Lodi lodi


03 -04

_____________

Maiduguri
"Wai Yana ba ki gama hada mun ruwan wankan ba ne?" Wata mata ce zata kai kimanin shekara hamsin da biyar ce ke maganar.

"Na gama yanzu zan fito." In ji wacce aka kira da Yana, matashiyar budurwa ce ita, ba ta da tsayi kuma siririya chocolate colour ce, akalla dai za ta yi shekara ashirin da huɗu.

Masha Allah suna da rufin asirinsu

Shigar Umma ɗaki ke da wuya aka ji ihu wanda ya firgita mutane sosai, da sauri Yana ta leka toilet ɗin, yanayin da taga umma sai da ya sanya ta kuka. Tana kwance kasa ba ta ko motsi, a guje Yana ta nufi titi nemo adaidaita, mai gadi magana yake yi mata amma ta yi masa banza saboda ba ta da lokacin da za ta yi masa bayanin halin da ake ciki.
Ganin yanayinta da sauri mai gadi ya shiga maƙota ya sanar da matar gidan halin da ya ga Yana a ciki, ai da sauri ta nufi gidan. A lokacin har Yana ta nemo mai adaidaita sahu, da taimakon maƙociyarsu aka kai umma asibiti.

**kano**
Hajja Falmata ce zaune a falo tana kallo, Amrah ta shigo tana ihu ko sallama babu ta ringa cillar da kayanta.
Ammi ta tsaya kallonta


"Baiwar ubanki ce za ta kwashe kayan da kika watsar Amrah ki kiyaye ni fa kin shigo wa mutane ba ko sallama kamar gidan kafurai."

Ba ta san Ammi na falon ba zaro ido ta yi waje, haɗe da saurin cewa
"Ammi don Allah ki yi hakuri ."

"Kar ma ki daina in kin ga dama ki ci gaba, matsa daga kaina, ki yi wanka da sallah ga abinci a dinning." Ammi tana gama maganar ta hau stairs.
"To" kawai Amrah ta ce haɗe da bin umarnin Ammi.



___________

Maiduguri

Asibitin kusa suka kai Umma *mamman shuwa hospital* da take cikin GRA, kai tsye Emergency aka shiga da ita doctors suka dukufa a kanta oxygen aka sa mata da kyar numfashinta ya dawo daidai.

Yana sai zagaye take tana kuka , sai bayan kamar minti 30 sai ga doctor ya fito yana sharce gumi da sauri ta tare shi tana cewa
"Doctor ta farfado? Me ya same ta? Ta jera masa tambaya biyu a lokaci daya.

"Ku biyo ni office." Iya abin da ya ce kenan, ba su musu ba suka bi bayansa har office ɗin, bayan sun zauna ya fara magana kamar haka
"A iya binciken mu ta kamu da ciwon shanyewar bari jiki sakamakon hawan jininta da ya hau."

Zumbur Yana tayi tana “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" luu tayi zata fadi Aunty Aisha tayi saurin taro ta,



“amma za mu iya ganin ta ko? " glass dinshi ya zare


“eh zaku iya amma kar amata hayaniya dan ta samu bacci senan da 3hrs muke sa ran farfadowar ta Allah bata lpy",


“Amin mungode" suka fice.


______________
Hajja falmata ce a kitchen tana girki wajen 3:30 Alh ya kusa dawowa saude na taimaka mata wayarta tai ringing saude ta miko mata
Da sauri ta daga danganin kanwarta ce yana banji me a kace ba ammi ta ce “subhanallah ya kike kuka Yana Innaalillahi garin ya hakan ta faru? ",

“Kiyi shiru insha Allah baza mu rasata ba kamar yadda muka rasa abbah kidena kuka bari Alhaji yadawo gobe insha Allah zamuzo ".

____________
Maiduguri
Aunty Aysha ce ke fadin “Yana bari naje gida na baro su Nafisa dukda nasan yayan su ya dawo sai in taho da abincin ".


Yana ce ta dago tace “to Aunty sekin dawo dan Allah ki tahon da hijabi ”

“Toh sena dawo ”


Fita tayi bakin titi Dakyar ta samu adaidaita sahu s uka nufi *damboa* *road*.


Kofar gate din aka sauke ta gida ne na masu kudi me babban compound da garage da ze dauki motoci wajen Shida,


Kwankwasa main door din tayi aka bude wata budurwa ce yar kimanin 17 tana sanye da riga da wando kanta ta yane gyale jelar gashinta ya zubo fara ce siririya asalin fulani ce

“Sannu da zuwa mommy”


“ Yauwa nafisa yayan ku yadawo naga motarsa”

“ ehh yana daki kansa na ciwo”


tohh yasha magani amma

“ ehh "

Ta shige, “ Yauwa kin gama girkin kinsa a basket”

" ehh "Nafisa ta amsa

“Yauwa yar albarka Bari nayi wanka ”

Dakinta ta ta nufa tayi wanka ta shirya fess mata a gurin Alhaji Saifudden Aliyu wanda aiki ne ya kai su maiduguri saboda shi custom ne yayansu uku hijab din ta dauka ta futa.

Ta futo ta nufi dakin babban danta Ammar tayi knocking “come in " shiga tayi yana zaune yana chatting tashi yayi “mommy kindawo naji ance ummah ba lpy “ehh "ya kan naka “ai yayi sauki",

“ok zoka sauke ni a asibitin" saurayi ne da yayi 20.



Futowa sukai ya dau basket ta ce ma Nafisa ta rufe gidan in sun futa su kadai a gida.



“Nafisa in auta tashi ki bata abinci "



Futa sukai suka nufi asibitin......... ✍🏽✍🏽

👩‍❤️‍👨FANSAR RAN MAHAIFA NA👩‍❤️‍👨





*BY* *KHADIJA*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

I dedicated this page to sis Fatima eyman and sis zahratty for your support and caring 💞❤️✨

05-06
____________
Bayan awa uku Wanda yayi daidai da magariba aunty Aysha na sallah Yana tashiga toilet futowar ta yayi daidai da farkawar Umma motsa baki take maganar taki futowa Yana ta nufe ta tare da fashewa da kuka.


Aunty Aysha na idarwa ko addua batai ba ta karasa gunta “umma zaki sha ruwa ne ?"


Kamota tayi tana motsa baki ruwan ta bata da taimakon Yana,

“ Yana ki kira mana doctor din kice ta farka " toh " aunty aysha ta ce.


Da sauri suka shigo tare da likitan duba ta yayi “Alhamdulillah jikin da sauki za a iya bata liquid food"

“Bari to a bata akwai kunu se abata"yana ta amsa


“yauwa a bata " fice wa yayi,

Kunun aka bata ta dan sha.

Magana take kadan kadan yana dake kusa da ita lura da hakan ta kai kunnen ta kusa da bakin ta,

“Yana ciwon nan nasan ba tashi zanyi ba dan haka ki fadawa Alhaji...


Read / Download FANSAN RAN MAHAIFANA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On FANSAN RAN MAHAIFANA
avatar
khadija-1-2-5

1 month ago

Reply

Tnx

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album