Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

👩‍❤️‍👨 *FANSAR RAN MAHAIFAINA* 👩‍❤️‍👨


BY KHADIJA

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


I dedicated this page to my lovely mommah❤️❤️long life is my wish insha Allah



01-02
Babban compound ne me dauke da bishiyu da shuke -shuke da ka ga gidan naira ta jiku, gidan yana da bangare biyu babba da karami da kaga babban shine main house din karamin BQ ne bangaren masu aikin gidan

Wani tangamemen parlour ne da yayi masifaffen tsaruwa kana shiga wani shihirtacen kamshi ne ze ziyarce ka, Misalin 10:55pm wata mata ce ke saukowa daga stairs tasha buban leshi ga kunnen ta yasha dan kunnen gwal, muryar ta naji me dadin sauraro da saura kiris alkalami na ya fadi tana fadin amrah bazaki tashi kije ki kwanta ba kallon ya isa haka salon da safe a tashe ki kiki tashi alhalin kinsan kina da school ke kullum bakya gama shiryawa se a hanya tun yanzu gwara ki gyara kafin ki rasa me maki fadan nan.



Yarinyar da aka kira amrah ce ta dago ammi dan Allah kiyi hakuri sponge Bob nakeson karasa kalla saura 4 minutes a gama ana gamawa zan kwanta pls kuma ammi kidena zance mutuwa,


Ammi ta harare ta tare dayin kwafa tace karma ki tashi ki barin in hadawa abiey coffee in futo baki tashi yarinyar na karewa kallo baza ta Gaza 10 yrs ba


Ay ana gamawa amrah ta tashi a guje tayi upstairs dakuna uku ne a saman nata na ammi se na abiey wani daki ta nufa tare da sallama amsawa akayi daga ciki wani magidanci ne da akalla yayi 45 yrs da laptop a gabansa kome yake oho taje ta Rungumeshi tana abiey naam uwata( saboda sunan babarshi gareta Maryam) me kike baki kwanta ba kallo nake tana wasa da sajen fuskarshi shi to maza a je a kwanta


“Nace oh ni yasu yarinyar da aka ce ta kwanta ce tazo nan”


Knocking akayi “yes come in” bakin ta dauke da sallama ta shigo hannun ta rike da karamin tray da mug akai turus tayi tana kallon amrah tsawa ta mata da ta gigitata malama tashi kije ki kwanta,


Abiey ya dago yana fadin Haba falmata ki dena mata tsawa haka sai ki firgitata se tana tsoron ki, dama Alh kai ke goyon bayanta take abun da taso


Tashi tayi sum sum tace masu good night Ammi tace karki manta da addua abiey ko ya ce sweet dreams uwata fita tayi dakinta ta nufa wanda komai pink and purple ne gadon ze dauki mutum uku anjere teddy's akai



Bayan fitar ta ammi ya rufe laptop din ya kalleta tace Haba Alh kayi aiki a office a gida ma aiki ya kamata ka ringa hutawa sipping coffee dinsa yayi tare da fadin angama madam na dena yana kashe mata ido



Murmushi kawai tayi bari nayi wanka dama shi yayi
Kasa ya sauka kayan kallo da futulu yayi tare da tabbatar da kofar a rufe take saman ya koma direct dakin amrah ya nufa ya tarar harta chanja kaya tayi bacci murmushi yayi ya ja mata duvet ya rufe ta saboda ana sanyi-sanyi, addua yayi mata ya bata peak a goshi ya kashe fitila kofar yaja mata


Dakin sa ya nufa ya tarar Ammi ta kwanta shima kashe futula yayi ya bar dim light kwanciya yayi ya rufesu nan naja masu kofa nace asuba ta gari Mr and Mrs Abdulmunaf.........


***********

Da safe misalin karfe 6:30 Ammi ce a dakin amrah suna ta tataburza akan ta tashi tayi shirin school


Amrah ta turo bakin ta ciki shagwaba da magagin bacci tace dan Allah ki karan 10 minutes

Anki din bazan kara ba ace ki kwanta da wuri kitsaya kallon yayan aljanu oya tashi ki kuma tabbata kafin ki futo Kinyi sallah da gyaran gado if not hmm ni da ke ne Kinji ko



Tana bubbuga kafa tace toh tare da fadawa toilet


Ammi binta tai da kallo tana fadin Allah dai shiryamin ke ta fice


Kitchen ta nufa ta tarar da saude me kula da harkar kitchen harta shigo durkusawa tayi hajiya ina kwana lpy kalau kin gama hadawa amrah lunch box din



Aa nadai kusa , OK In kin gama seki maku anun kari keda Adama bata shigo bane..... Sallama akai ammi ta amsa Adama kin shigo ehh hajiya ina kwana lpy kalau Dan Allah ki maza ki share parlour kafin alhaji ya sauko sannan kisa turaren gurin yana ay kin ganeshi ehh yauwa kayan sharar ta dauke ta futa


Ammi kiciniyar hadawa abiey abun kari dan ita Sam bata yarda masu aiki su yi ma mijinta girki



Tana gamawa takai dinning ta jere


Hawa upstairs tayi dakin amrah ta shiga ta tarar da ita a akwance a bakin gado daga ita se towel alamun tayi wanka,



Ammi a harzuke ta kama kunnenta ta murde kuka tasa mata

Ke wai amrah mesa kullum kike son sani magana


Ayy bata bar dakin ba seda ta shirya school bag ta dauka sauka tayi ita kuma ammi ta wuce daki domin yin wanka


Tana futowa ta shafa lotion da humrori a jikin ta shiryawa tai cikin riga da zani na atamfa me adon ganye tare da daura daurin zahra buhari fes ta futo yar chubby da ita kamar ka sureta


Futa tayi ta nufi dakin alhaji har ya shirya yana sa links turare ta fesa masa tare da daukar briefcase nasa suka sauka parlour.


A guje amrah ta rungumesu tana gaishe su Kinyi breakfast “yes"Ammi ta rike kumatun ta good girl to kije malam idi ya sauke ki


Peak tabasu ta fice suka tafi


Su kam dinning suka nufa Bayan sun gama karyawa alhaji ya wuce office



Wata katafariyar school aka sauketa direct class ta nufa primary 3b na gefen staff room Bayan shigar ta se ga wata saar ta tashigo Rungume juna su kai


Yarinyar duban amrah tai tana fadin yau bestie kin riga ni zuwa

Ay nasreen in fada maki ammi ce kwana biyu.... Bata karasa maganar ba sukaji ringing bell na assembly suka fice



*********
Da yake yau Thursday ne sports zasuyi dan haka kowa field ya nufa Bayan assembly banda amrah da nasreen aminan juna


Seda suka ga an tafi field suka shiga aji wani seats naga sun nufa


Hmmmm nasreen kinsan wannan yar rainin HanKali dan taga ita kadai tayi maths assignment shine take wani daga Kaii bata hadu damu bane ai


Bag din yarinyar suka bude suka ciro maths da English exercise book dinta suka yayyaga tare da sawa a dustbin



Tafawa sukai amrah na fadin gwara da muka hada har English din yar iskar yarinya

Futa sukai tare da nufar field din............ ✍🏽✍🏽✍🏽

👩‍❤️‍👨 *FANSAR* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨





BY KHADIJA

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


I dedicated this page to my aminiya ta masoyiya ta mummyn maheer💃( my zakara) ina sonki Lodi lodi


03 -04

_____________

Maiduguri
"Wai Yana ba ki gama hada mun ruwan wankan ba ne?" Wata mata ce zata kai kimanin shekara hamsin da biyar ce ke maganar.

"Na gama yanzu zan fito." In ji wacce aka kira da Yana, matashiyar budurwa ce ita, ba ta da tsayi kuma siririya chocolate colour ce, akalla dai za ta yi shekara ashirin da huɗu.

Masha Allah suna da rufin asirinsu

Shigar Umma ɗaki ke da wuya aka ji ihu wanda ya firgita mutane sosai, da sauri Yana ta leka toilet ɗin, yanayin da taga umma sai da ya sanya ta kuka. Tana kwance kasa ba ta ko motsi, a guje Yana ta nufi titi nemo adaidaita, mai gadi magana yake yi mata amma ta yi masa banza saboda ba ta da lokacin da za ta yi masa bayanin halin da ake ciki.
Ganin yanayinta da sauri mai gadi ya shiga maƙota ya sanar da matar gidan halin da ya ga Yana a ciki, ai da sauri ta nufi gidan. A lokacin har Yana ta nemo mai adaidaita sahu, da taimakon maƙociyarsu aka kai umma asibiti.

**kano**
Hajja Falmata ce zaune a falo tana kallo, Amrah ta shigo tana ihu ko sallama babu ta ringa cillar da kayanta.
Ammi ta tsaya kallonta


"Baiwar ubanki ce za ta kwashe kayan da kika watsar Amrah ki kiyaye ni fa kin shigo wa mutane ba ko sallama kamar gidan kafurai."

Ba ta san Ammi na falon ba zaro ido ta yi waje, haɗe da saurin cewa
"Ammi don Allah ki yi hakuri ."

"Kar ma ki daina in kin ga dama ki ci gaba, matsa daga kaina, ki yi wanka da sallah ga abinci a dinning." Ammi tana gama maganar ta hau stairs.
"To" kawai Amrah ta ce haɗe da bin umarnin Ammi.



___________

Maiduguri

Asibitin kusa suka kai Umma *mamman shuwa hospital* da take cikin GRA, kai tsye Emergency aka shiga da ita doctors suka dukufa a kanta oxygen aka sa mata da kyar numfashinta ya dawo daidai.

Yana sai zagaye take tana kuka , sai bayan kamar minti 30 sai ga doctor ya fito yana sharce gumi da sauri ta tare shi tana cewa
"Doctor ta farfado? Me ya same ta? Ta jera masa tambaya biyu a lokaci daya.

"Ku biyo ni office." Iya abin da ya ce kenan, ba su musu ba suka bi bayansa har office ɗin, bayan sun zauna ya fara magana kamar haka
"A iya binciken mu ta kamu da ciwon shanyewar bari jiki sakamakon hawan jininta da ya hau."

Zumbur Yana tayi tana “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" luu tayi zata fadi Aunty Aisha tayi saurin taro ta,



“amma za mu iya ganin ta ko? " glass dinshi ya zare


“eh zaku iya amma kar amata hayaniya dan ta samu bacci senan da 3hrs muke sa ran farfadowar ta Allah bata lpy",


“Amin mungode" suka fice.


______________
Hajja falmata ce a kitchen tana girki wajen 3:30 Alh ya kusa dawowa saude na taimaka mata wayarta tai ringing saude ta miko mata
Da sauri ta daga danganin kanwarta ce yana banji me a kace ba ammi ta ce “subhanallah ya kike kuka Yana Innaalillahi garin ya hakan ta faru? ",

“Kiyi shiru insha Allah baza mu rasata ba kamar yadda muka rasa abbah kidena kuka bari Alhaji yadawo gobe insha Allah zamuzo ".

____________
Maiduguri
Aunty Aysha ce ke fadin “Yana bari naje gida na baro su Nafisa dukda nasan yayan su ya dawo sai in taho da abincin ".


Yana ce ta dago tace “to Aunty sekin dawo dan Allah ki tahon da hijabi ”

“Toh sena dawo ”


Fita tayi bakin titi Dakyar ta samu adaidaita sahu s uka nufi *damboa* *road*.


Kofar gate din aka sauke ta gida ne na masu kudi me babban compound da garage da ze dauki motoci wajen Shida,


Kwankwasa main door din tayi aka bude wata budurwa ce yar kimanin 17 tana sanye da riga da wando kanta ta yane gyale jelar gashinta ya zubo fara ce siririya asalin fulani ce

“Sannu da zuwa mommy”


“ Yauwa nafisa yayan ku yadawo naga motarsa”

“ ehh yana daki kansa na ciwo”


tohh yasha magani amma

“ ehh "

Ta shige, “ Yauwa kin gama girkin kinsa a basket”

" ehh "Nafisa ta amsa

“Yauwa yar albarka Bari nayi wanka ”

Dakinta ta ta nufa tayi wanka ta shirya fess mata a gurin Alhaji Saifudden Aliyu wanda aiki ne ya kai su maiduguri saboda shi custom ne yayansu uku hijab din ta dauka ta futa.

Ta futo ta nufi dakin babban danta Ammar tayi knocking “come in " shiga tayi yana zaune yana chatting tashi yayi “mommy kindawo naji ance ummah ba lpy “ehh "ya kan naka “ai yayi sauki",

“ok zoka sauke ni a asibitin" saurayi ne da yayi 20.



Futowa sukai ya dau basket ta ce ma Nafisa ta rufe gidan in sun futa su kadai a gida.



“Nafisa in auta tashi ki bata abinci "



Futa sukai suka nufi asibitin......... ✍🏽✍🏽

👩‍❤️‍👨FANSAR RAN MAHAIFA NA👩‍❤️‍👨





*BY* *KHADIJA*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

I dedicated this page to sis Fatima eyman and sis zahratty for your support and caring 💞❤️✨

05-06
____________
Bayan awa uku Wanda yayi daidai da magariba aunty Aysha na sallah Yana tashiga toilet futowar ta yayi daidai da farkawar Umma motsa baki take maganar taki futowa Yana ta nufe ta tare da fashewa da kuka.


Aunty Aysha na idarwa ko addua batai ba ta karasa gunta “umma zaki sha ruwa ne ?"


Kamota tayi tana motsa baki ruwan ta bata da taimakon Yana,

“ Yana ki kira mana doctor din kice ta farka " toh " aunty aysha ta ce.


Da sauri suka shigo tare da likitan duba ta yayi “Alhamdulillah jikin da sauki za a iya bata liquid food"

“Bari to a bata akwai kunu se abata"yana ta amsa


“yauwa a bata " fice wa yayi,

Kunun aka bata ta dan sha.

Magana take kadan kadan yana dake kusa da ita lura da hakan ta kai kunnen ta kusa da bakin ta,

“Yana ciwon nan nasan ba tashi zanyi ba dan haka ki fadawa Alhaji ali,ya nukura da falmata na yafe ma su zan bi abban Ku Allah raya munku Naso ganin auren ki amma hakan baze ba Allah Baku zaman lpy da mijin ki ”
Aunty aysha tace “Amin”


Yana ta ringa kuka


Alhaji Ali ne ya shigo da iyalansa se wajen 11:30 suka tafi ko wanne sedai yayi kwalla.




__________
*Kano*

Su abiey ne a falo suna kallo bayan amrah ta gama assignment nata,


Ammi kallo take amma hankalin ta baya kan kallon.

Abiey kallonta tayi ganin fuskarta da damuwa “falmata ”

Dagowa tayi yace “ki kwantar da hankalin ki anyi waya jikin ta sauki"

Tace “Alhaji tun dazu gaba na ke faduwa "

Insha Allah ba abunda ze faru muje mu kwanta .


**********

2:45 na dare rurin wayar Ammi ya tashe su da sauri ta dauko wayar gaban ta na faduwa se da wayar ta kusa tsinkewa ta daga kirji ta dafe tana fadin “innalillahi wa inna ilaihir rajiun ” Ta saki wayar abiey na tambayar ta ammi tayi suman zaune chan seta fara fadin“ shikenan umma ta tafi ta barmu ”fashewa tayi da kuka daren ba wanda ya runtsa a cikin su.



____________
Maiduguri
A asibiti umma Allah ya mata cikin dare,
Yana tunda umma ta mutu ta Suma har seda aka kara mata ruwa aunty aysha ce ta kira su ta sanar masu a daren seda safe za suzo saboda duk a nesa suke banda Alhaji ali dake garin..........


____________
*Kano*
“hmm Alhaji kasan hajja falmata haushi take ban bata neman mutane ko dan mijinta nada kudi” Wata mata ce yar kimanin shekara 32 .


Rabu dasu sa'a, akalla Mutumin ze kai shekara 42.

( Saa mata ce a gurin Alhaji jibrin kani ga Alhaji Abdulmunaf ya'yan su uku)

********
Da asuba Ammi jikin ta duk a mace ta hada masu kayan ta da na Alhaji, Alhaji ya hada na amrah duk da ita gidan kaninsa ze kaita dake sharada saboda school.


Ammi tashin amrah tayi tai wanka ganin yanayin ammi amrah tace “idonki ammi yayi ja abiey ne ya maki abu ko dukan ki yayi ”

Kallonta ammi tayi kamar tayi dariya amma ba damar yi,

“Amrah ki shiga wanka umma Allah ya mata rasuwa ”
Amrah tace “Allah ji kanta "

Ammi ta amsa Amin, saboda school dinki Zaa akai ki gidan uncle jibrin.


Tana murna tace “zanga zee"

Yaro kenan Ammi ta fada tare da futa.

Karfe bakwai suka nufi maiduguri bayan sun sauke amrah ya bar kula da companyn sa a gun kaninsa.


____________
Maiduguri
Ammi seda suka dau ki awa 8 a hanya saboda tsaye tsaye basu Karaso da wuri ba suka nufi *damboa* *road* tun daga titi motoci suna shiga layin su Ammi ta fara matsar kwalla,

Ammi ta shiga gidan abiey ya tsaya a waje karbar gaisuwa lokacin an dade da kaita.

Tana shiga Yana taxo ta Rungume ta kuka suke ba me rarrashin juna,

Cikin shessheka da shakewar murya yana tace “shikenan mun rasa umma kamar yadda muka rasa Abba” kuka suke sosai.


Aunty aysha ce tayi karfin halin cewa “falmata ba kukan ku take bukata ba addua zakuyi mata "


Ammi ruko hannun yana tayi ta zauna aka gaisa.


_____________

Amrah ce zaune a falo tana kallo da yake weekend ne aka chanja channel,

Ta dago dan ganin wane“ya umar ya zaka chanjan channel ina kallo”


Hararar ta yayi an chanja din me zakiyi,


Amrah ce tace "bansani ba" tana murguda masa baki make bakin yayi tare da daga hannu ya falla mata Mari ta saki ihu .

Ta daga hannun kenan taji an rike hannu......... ✍🏽✍🏽✍🏽

*FANSAN RAN MAHAIFANA 👩‍❤️‍👨*





BY KHADIJA

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*





This page is dedicated to sweet en sweet 💖and yusrah Abdullahi Aliyu❤️✨💫


07-08

Juyowa ta yi don ganin wa ya rike mata hannu. Hajiya Sa'a da suke Kira mama da fitowarta kenan.


A fusace Hajiya Sa'a ta fara magana
“Ke don baki da kunya Umar din za ki mara? Ya ba ki shekara biyu fa! Ko kwana ya ba ki ai ya fi ki”

Amrah ta ce “Mama mari na fa ya yi ”

”Miye to dan ya mare ki? Dalla ban guri"


A guje ta tafi tana
“Allah Ya isa na " ta yi saurin shigewa dakin yan'matan, su biyu ne yan'mata ɗaya za ta yi 8 ɗayar kuma 10.

Yar shekara 10 ce ta kalli Amrah shekeke a wulakance ta cigaba da game dinta a tab. Zee kenan

Yar shekara 8 din ta tambayi Amrah me ya faru fada mata ta yi

“Ayyah ki yi hakuri kin ji yaya Amrah" kafin Amrah ta yi magana Zee ta ce "ke wai Arifa me yasa kin fiye shisshigi? sai me don an mare ta yarinyar fa ba ta da kunya"

Haka ta yi ta banbaminta ita kaɗai ba wanda ya tanka mata.


Arifa ta ci gaba da assignment dinta Amrah na taimaka mata dan ta fita class.

Zee daman ita ba ta damu da yin assignment ba. Ko school din ba ta

1 Comments On FANSAN RAN MAHAIFANA
avatar
khadija-1-2-5

9 months ago

Reply

Tnx

Please Login or Register in order to submit comment