Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai ji tayi an fizge wayar da sauri ta dago.





Ammar ne tsaye yana sakar mata wani kayataccen murmushi mai narka zuciyar wanda akai wa.





Mayar mashi da martani tayi ta ce “Sannu da zuwa Nurul qalb zuwa ba sanarwa?".





Zama yayi a kusa da ita ya ce “Kinsan bazan iya dadewa banganki ba".




Murmushi tayi ya kalleta ya ce “Miko mun Ammita (sunan Ammin Amrah aka sa mata Fatima) mu gaisa.




Babyn ta mika mashi cike da so da kauna yake kallon ta ya ce “Masha Allah samha tayi wayo sosai naji ma ta kara nauyi.





Aunty Yana da futowarta kenan ta ce “Ba dole tayi nauyi ba ni kuma na rame tana zuke ni yarinya sai cin balai" ta karaso ta zauna kusa da Ammar gaisawa su kayi.





Murmushi Ammar yayi ya ce “Gaskiya Auntyn mu Ammin mu bata da wani ci".






Hararar shi Aunty Yana tace “Dama kace haka mana aini tana wata shida zan ma yaye ta ".




Ammar ya ce ”kin ma isa....




Amrah ce ta dire mashi tray a gabanshi cike da kayan motsa baki.





Murmushi ya mata ya ce “Sannu Sweetheart dina".





Da sauri Amrah ta zauna tana sunne kanta cike da kunya.





Aunty Yana ta dauki muhucin gefenta ta kwada mashi tana dariya ta ce “Wallahi sam baka jin kunya ta".





Ammar ya ce “Toh inji kunyarki a wa?" yana murmushi.




Yana ta ce “a suru.....Bata karasa maganar ba samha chanyara kuka.





Da sauri Aunty Yana ta hade rai ta ce ”Kun ganta ko na fada maku ita acici ce ko minti talatin fah ba tayi ba dayin bacci ".






Ammar da Amrah suka sa dariya bakaramin kyau ya masu ba sun dace sosai.





Ammar yana kunshe dariya ya ce “Sorry Auntyn mu ataimaka mata".





Ta chuno baki ta karbe ta ta ce “Dama so kake na tashi na barku ku soye ko?" tana kanne masa ido .





Murmushi kawai yayi ita kuma ta shige daki.





Juyawa yayi ya fuskanci Amrah ya ce “Dear muma haka zaki bamu babies ko ?".





Murmushi Amrah tayi tana rufe idonta da gefen dan kwalinta.






Dariya Ammar yayi ya ce “Naga ranar da Zaki dena wannan kunyar ne.....hira sukayi sosai.



*******



*Bayan kwana biyu*


“Assalamu Alaikum"Aunty Yana tayi sallama.





Mommah ta ce ”Wa'alaikumus Salam" fuskarta dauke da murmushi ta ce ”Sannun ku da zuwa da ni da naga yamma yayi nace ko kun fasa ne" .





Zama tayi suka gaisawa ta kare masu kallo ta kalli Aunty Yana ta ce “Ina Samha da Yata ne naga daga ke sai Arifa?".





Aunty Yana ta ce ”Ai Aunty Aisha suna chan suna soyewar su" ta karashe zancen cikin dariya.





Mommah tayi Murmushi ta ce ”Hmmm ai ni har mamaki suke bani basa jin kunyar kowa kuma baba nane mara kunyar cikin ".





Aunty Yana tayi murmushi ta ce “Aunty Aysha mun k'afa hira ko tambayar mai jiki banyi ba na sha'afa".





Mommah ta ce ”Wallahi kuwa ".




Aunty Yana ta ce “Ya jikin Abban kuwa?".





Mommah ta ce “Da sauki ulcer dince yanzu gidan kowa a kwaita ".





Aunty Yana ta ce “Wallahi kuwa Allah dai kara mana lafiya".




Mommah ta ce “Amin" kana tace “kuzo mushiga ku ga jikin nashi".





Mikewa su kayi yana kishingide a falon Shi yana ganinsu ya ce “Ahh su Yana kune a gidan namu yana kokarin mikewa".





Da sauri Aunty Yana tana murmushi ta ce “Sannu Abban ba sai ka tashi ba murmushi ya mata suka gaisa tare da mashi ya jiki suna dan taba hira chan yace wa Mommah “Aisha dan mikon ruwa".





Arifa ta mike ta ɗauko ruwan cikin ladabi ta bashi .




Mikewa su Yana sukai Abban ya kallesu ya ce “Har zaku tafi ?".




Aunty Yana tayi murmushi ta ce ai sai dare ai zamu tafi chan side in Aunty Aysha zamuje mu barka ka huta.





Murmushi yayi ya ce “Naji Yata shiru ma basu shigo ba".




Mommah ta ce ”Ina zata shigo babana ya rike ta suna chan ai yaran naka ne sai a hankali"





Dariya Abba yayi ya ce “Aisha kin sawa yaran nan ido da yawa fa".




Murmushi Mommah kawai tayi.




Su Aunty Yana sukai mashi Allah kara sauki.




Suna futa su kayi kicibis da su Amrah Samha a kafadarta tana ta baccin.




Aunty Yana ta harare su ta ce “Maras kunya kunga damar shigowa kenan ko?".




Ammar ya ce “Eh ya ranki fari ko baki?".



Cikin murguda baki Aunty Yana ta ce ”Fari tass".





Amrah dai ba tace masu komai ba .




Karasawa sukayi gurin Abban suna shiga .




Abban cike da farin ciki ya ce “Masha Allah Ya'yana ".




Sunkuyar da kai Amrah tayi ta zauna a ƙasa cikin kunya ta gaishe shi tare da yi mashi ya jiki.





Sosai ya ringa janta a jiki ita ko ta ƙasa sakewa dashi tana jin kunya.





Chan suka mike sakamakon Kiran Sallar Magariba da akayi.





Abban ya shafa kan Amrah ya ce “Allah ya maku albarka ya nuna mana Auren ku.




Amrah ƙasa Amsawa Ammar kuwa yana murmushi ya ce “Amin Amin".




A guje Amrah ta futa daga falon Murmushi Abba yayi...........🖊️✍🏻







*MORE COMMENT*
*MORE TYPING*........✍🏻✍🏻






*Addeejerh* ❤️


👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI/RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM IDRIS*
( *shalelen kainuwa* ❤️)
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*


73

*Bayan wani lokaci*


Wasa wasa lokaci yaja saura sati biyu auren Amrah da Ammar ko wane bangare sai shirye-shirye suke ba kama hannun yaro.





Arifa Nafisa ne da Amrah ne a daki suna hira da Nasreen da tazo yanzu hararar Amrah Nasreen tayi ta ce “Aikin banza kinki kiyi sauri ki shanye wannan abun da baifi ki shanye a minti biyu ba kuma kinsan kasuwa zamu ga rana nayi".





Amrah ta turo baki ta ce “Ni zaku dagawa mutane hankali abinda saura sati biyu,kuma dan baki san dacin wannan tsumin bane.






Dukansu suka kyalkyale da dariya Nafisa tana dariya ta ce “Nidai gwara ki tsaya kiwa Yayana gyara sosai".





A fusace Amrah ta dauki filon gefen ta ta cilla mata tana dariya ta ce “Wallahi Nafisa kin fitsare da yawa ai sai na fadawa Mommah gwara suyi maki aure tun kafin ki ja mana magana........"




********



"ke yi sauri ki shirya mana kina wani nawa". Cewar Nafisa tana kallon Amrah".




Ba tace mata komai ba taci gaba da shiryawan ta, sai da ta gama suka fito Parlour inda su Arifa ke jiran su, sallama sukai ma Aunty Yana suka fito driver ya kai su kasuwa.






Siyayya su ka yi na costumes da kayan da zasu saka a matsayin su na ƙawayen amarya da na ita kanta amaryar, kaya masu kyau suka zaɓa.





Sun ɗau wajen awanni uku kafin su gama suka dawo, lokacin da suka dawo gida duk a gajiye su ke.






Aunty Yana na zaune da Samha a jikin ta tana breast feeding dinta suka zo suka zube a ƙasa ko wacce tana sakin hamma da numfashi kamar Wanda su kayi gudu.






“Kai amma ku kam ragwaye ne, yanzu fitan nan naku shine har kun gaji?" Cewar anty yana tana kallon su.






Amrah ta ce "Aunty baza ki gane bane, wlh mun sha baƙar wahala, daga mu je nan shagon sai muje can saboda babu abinda muke so anan".





Nasreen ta ce "Ai ni wlh cikina ya ƙwaƙwule gaba ɗaya yunwa nake ji".





Itama Arifa ta ce "Ashe muna ɗaya wlh, nima yunwa nake ji har wani amai amai nake ji".






"Ai ni har da barci nakeji ". Nafisa ta faɗa tana sake sakin hamma






Dariya Aunty Yana tayi ta ce "ku dai kuka sani, ku je dining ga abinci can sai ku ɗiba, amma yanzu ku ware min na Amrah don yanzu zan kira waya a ɗaukar mata lokaci na ƙure wa muna buƙatar ɗinkin dan kar ayi mana buja-buja".





Arifa ta ce "to muma a haɗa da namu mana".





"A'a ai na wajen amarya daban yake, ku naku ku bari akwai inda na ta nada muku, shima anjima za'a zo a ɗauka"cewar Aunty Yana tana sa Samha a kafada.





Dining su ka nufa su ka zauna suna cin abincin suna hira kamar ba su ne su ka ce a gajiye suke ba, har da su tafawa ana shewa, duk maganar bikin suke yi inda suke shirya abinda zasu yi.





Amrah kuwa hankalin ta Sam baya kansu Nasreen ta sheke da dariya ta kalli Amrah ta ce “Besty tunani Nurul qalb din ake ne?".





Da sauri ta juya taga ko Aunty nanan taga tama riga da ta tashi ta maida kallonta kan Nasreen din ta ce “Ina ruwanki kin fiye sa ido"tana hararar ta.





Suka kyalkyale da dariya Nasreen ta ce ”Ohhh kedai burin kunya kike...........".




*Some days later*



Yau saura kwana uku bikin yan uwa har sun fara zuwa Ya Nukura ma ta karaso da na ta iyalan Matar kawu Ali tazo ita ma da nata tawagar ita ma gidan ya dada kacamewa sai hayaniyar yara anata shirye-shirye.





Amrah ce zaune akan filo Aunty Sumayya matar kawu Ali tana yarfa mata kananun kitso irin nasu na Maiduguri wayarta ce ta fara ringing tana dubawa taga Nurul qalb ke yawo akan screen din taki dagawa har wayar ta tsinke.





Sake kira a kayi again taki dagawa Aunty na lure da ita .





Ana uku ne Aunty Summaya ta ce ”ki dauka mana"





Cikin kunya Amrah ta dau wayar tana ficewa Aunty Summaya tayi murmushi ita ma taje suka cigaba da hira da su Ya nukura.






Waje Amrah ta futa ta daga wayar tare dayin sallama cikin zazzakar muryarta daga chan Ammar ya amsa tare da fadin “ya ke kyakkyawa cikin kyawawa da fatan kina cikin koshi lafiya?" ta ce “Lafiya kalau Nurul qalb da fatan Kai ma haka?" da sauri ya ce ”Niidai ba lafiya ba".




A rude Amrah ta ce “Mai ya faru?" shagwabe murya yayi ya ce ”Bani da lafiya saboda rashin ganin ki wallahi sweetheart nayi kokari wajen kwana 10 ban ganki ba".




Murmushi Amrah tayi tana sauke ajiyar zuciya ta ce “Allah har ka tsorata ni".




Ammar ya ce ”Baki missing nawa ba ko?", da sauri ta ce “A'a wallahi ba haka bane".





Yace ”To indai kinyi missing nawa toh anjima da daddare in nazo ki fito kinsan anyi b'aki bazan iya shigowa ba".





A shagwabe ta ce “Kasan su Aunty baza su barni ba na fito".




A fusace ya ce ”Toh shikenan" ya kashe wayar bai ko saurari mai zata ce ba .





Duk sai taji zuciyarta ba dadi haka tayi ta kira yaki dagawa a karshe sai message ta mashi akan cewa zata san yadda za tayi ta futo yayi hakuri jikin ta a mace ta koma aka karasa mata kitson........🖊️✍🏻






*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* .......✍🏻✍🏻




*Fans sai mun hadu ranar* *bikin* 💃💃💃💃





*Addeejerh* ❤️


👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI/RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM IDRIS*
( *shalelen kainuwa* ❤️)
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*



74~75

Da daddare Amrah ta fakaici idon su Aunty Yana ta futa da Ammar yazo ta lallaba su Nasreen suce tana bandaki.





Gaisawa kawai su kayi su ka dan taba hira ta koma ciki bayan sunyi sallama cike da ƙaunar juna.





Tana zama a daki Aunty Yana ta shigo ta kalli Amrah din dake haki kamar wanda kare ya biyo ta .





“Biyo ni muje daki ayi gyaran jikin nan saura kwana biyu akai ki dole mutashi tsaye sosai" cewar Aunty Yana.





Amrah ta shagwabe fuska Kamar za tayi kuka ta ce “A bari dan Allah sai anjima".





Duk su Nasreen suka sheke da dariya har da yan matan Ya nukura su biyu Basma da Nihal sai y'ar Kawu Ali shukra.





D'akuwa Aunty Yana tayi wa Amrah tana fadin “Anki a bari din oyo tashi muje".





Zumburo baki Amrah tayi kamar shantu tabi bayan Aunty Yana.





Su kuwa su Arifa hirarsu suka cigaba.




_Washegari_




Ranar laraba ana gobe fara biki .




Amrah ce ake yar'yadawa lalle ja da baki sannan aka yiwa su Nasreen ma wanda dama tun saura kwana uku bikin su ka tare a gidan.




Sai ya bawa ake da lallen Amrah wanda yake daukar ido abinka da farar mace.





Da daddare Ya nukura tasa Amrah ta cinye kazar Amaryar tass ta na ci ta na kuka sannan tayi wanka anda aka sa wa ruwan turarurruka.




********



Ranar Alhamis da safe su Nasreen suka dai bi kayan da za su da yamma na kamu suka nufi chan gidan su Amrah da yake yafi girma dan a gida za ayi kamun .





Driver ne ya sauke su a gidan lokacin Aunty Yana na compound din tana nunawa masu decorations din yadda zasu yi Samha dake bayanta sai chanyara kuka take.





Su Amrah na karasowa daf da ita dukansu sukayi mata sannu ta kallesu ta ce ”Sannun ku kuma ku shiga ciki".






Amrah ta ce ”To Aunty kawo Samha mu shiga da ita".





Aunty Yana ta ce “Anya baza ta ishe ku da kuka ba".




Amrah tayi murmushi ta ce “Za dai ta baki kunya ne kawo ta ki ga".




Aunty Yana ta ce “Toh" tare da sauko da ita, ta mikawa Amrah aiko Amrah na karbar ta tayi shiru tsitt Kamar ........





Kama baki Aunty Yana tayi ta ce ”ikon Allah ka ganni da yarinya tayi shiru".




Dariya su ka sa dukkan su su ka karasa ciki.





Direct dakin Amrah na d'a su ka wuce tun nata sanda su Ammi na da rai.





Karfe 4 na yamma a ka fara kamun ba karamin kyau Amarya Amrah tayi ba Kamar ka su re ta.





Ansha rawa sosai su Arifa kamar kugunsu zai balle .





Sai wajen 8 na dare kowa ya watse.




A gajiye su Amrah su ka koma daki duk su ka baje akan gado kowa na sauke ajiyar zuciya.





Bayan sun huta su ka tashi su ka fara layin wanka
su na shirin kwanciya Aunty Summaya ce ta shigo
yar aiki na biye da ita dauke da katon tray a hannunta ajiyewa tayi ta fice.





Aunty Summaya ta kallesu ta ce ”Ga Abinci nan kuma ku tabbata Amrah taci!! ta kalli Amrah tace inji baki ci ba sai na sassaba maki wallahi" Amrah ta ce ”Toh mungode" Aunty summaya tayi murmushi ta fita.





Bararrajewa su kayi su na lodawa cikinsu Abinci kamar sa ci babu har Amrah din banda Nafisa dake lallatsa waya .





Arifa ta jefa wa Nafisa filo tana fadin ”ba zaki sauko kici Abinci ba ko kina faman latsa waya?".





Da sauri Basma ta ce “kika sani koda saurayin ta take charting".




Nafisa ta ce “Rabu dasu sis ko ina ruwan su dani", ita kuwa Nafisan dama Yaya Ammar take turawa hotunan Amrah da tayi mata dazu saida ta gama ta je taci abincin.





Ranar raba dare su kayi basu yi bacci ba ana ta hira ita kuwa Amrah waya su ke tayi da Nurul qalb dinta.





_Washegari_




Ranar Juma'a da daddare yan matan Amarya sai shiryawa su ke zasu tafi gurin dinner.





Ita kuwa Amarya Amrah sai tsantsara mata kwalliya ake .






Mai kwalliya Aunty Yana ta sa aka dauko mata takanas.





Ba karamin kyau Amarya tayi ba karas kawai kake ji ko ina flash ke haskawa.





Ita kanta mai kwalliyar sai da ta yaba irin kyan da tayi.




Su Nasreen su ma akayi masu ta su kwalliyar.





Ammar ne ya kira Nafisa yace ga sunan sun karaso su na jiran su ta ce “Toh Yaya gamunan futowa ya ce “To" tare da katse wayar.





Ana gama ma su su ka fuffuto gidan tsit kowa ya wuce gurin dinner sai su kadai.





Wata bakar BMW su Amrah su ka nufa,Amrah ta shiga baya Nasreen ta shiga gaba gurin mai zaman banza.





Su kuma su Arifa su ka shiga sauran motocin comboy suka masu suka sa su a tsakiya *MARHABA EVENT* *CENTER* suka nufa .






A fakaice Amrah ta kalli Ammar ta cikin mayafin da ta rufe kanta ta kare mashi kallo yana sanye cikin shigar shi ta Alfarma yasha sky blue shadda an mata aiki da blue-black zare kalar kayan da ta sa duk kamshi ta ya cika motar.





Suna karasawa hall din su ka jeru Amarya da Ango a tsakiya su na shiga aka sakar masu wani irin kida.






Mutane aka ringa mikewa ma su daukar hoto nayi ma su video nayi.





Amarya su kaje su ka zauna a gurin da aka tanadar ma su bayan zamansu aka fara dinner din ka'in da na'in.






MC ya ce ”Idan babbar Kawar amarya na nan tazo ta ba mu tarihin Gimibiyar nan".






Cike da kasaita Nasreen ta futo tana taku dai-dai tarihin Amrah ta fara bayarwa cikin harshen turanci ta na gamawa ji ka ke raf raf raf ana ta mata tafi ba karamin burge mutane tayi ba ta koma ta zauna.






Sannan aka kira babban abokin Ango Salman ya bada tarihin Ango shima aka ringa tafa mashi ya koma ya zauna nan aka fara hotuna da Amarya da Ango.






Serving abinci aka fara ba wanda zai ce bai sa mu ba chan na hango click din yan FANSAN RAN MAHAIFANA fans sunsha ankon su da yawan su sun zo irin su Princess,Sweet en sweet,su mummcyn khadija,su ummu rufaida ,Khadija Sulaiman Garba,Zarah,firdausi sani da dai sauransu.






Sweet da Princess sai zuba loma su ke lol.





Ansha bikin angwangwaje su Nasreen sun sha rawa Aunty Yana ta yi rawa kowa ya gwangwaje.






Sai 12 ma dare aka tashi kowa zai tafi saida aka bashi savouniers ...




********




A yau ne rana bata karya sai da uwar diya taji kunya misalin 10:30na safe dubban mutane suka shaida daurin auren *MARYAM ABDULMUNAF* *USMAN* da *MUHAMMAD AMMAR* *ABDULLAHI* bisa sadaki dubu dari .


Kowa ka ganshi ya na cikin farin ciki ba re ma mai gayyar Ango Ammar sai gaisawa ya ke da yan uwa da abokan arziki.




A cikin gida wata marokiya ta sanar an daura auren Amrah na jin haka ta sa kuka tuno iyayenta su Nasreen su ka ringa mata dariya chan su ka ga kuka yaki ci yaki cinyewa suna ta lallashin ta amma taki yin shiru.





Aunty Yana Arifa ta fita ta kira dan tazo ta ga mai ke faruwa a rude ta biyo Arifa.





Tana shiga ta nufi Amrah ta rungumo ta jikin tana shafa bayan ta tace ”Kukan name rabin raina?".




Cikin muryar kuka tace Ammina da Abie.....ta kara fashewa da matsancin kuka ita ma Aunty Yana sai tasa kuka





Su ma su Arifa saida su ka yi kwalla dan sun tausayawa masu.





Ya nukura ce ta shigo tana fadin ”Ina Amaren ne ga Angwayen sunzo ba ku fito......maganar ce ta tsaya a bakin ta ta ka sa karasawa ganin mai ke faruwa.





Cikin masifa Ya nukura ta ce “Wannan wa ne irin shashanci ne kuma Yana zaki sa yarinya a gaba ku na kuka,maza kafin in bude idona ku gyara fuskokin ku futo" .





Gyarawa Amrah kwalliya akayi su ka sauko ana tayi mata Allah sanya alkhairi da fatan zaman lafiya compound din gidan suka fita gurin angwayen ana ta hotuna.





Kama hannun ta Ammar yayi yaji wani irin laushi ita kuwa tsigar jikin ta ce ta tashi a hankali ya ce mata “kuka kika yi ko ?" girgiza kanta tayi ya ce ”Gashinan idonki ya nu na ko zama ne bakyason yi dani ?" a hankali ta ce “A'a" ya ce “toh karki sake kinji kar zazzabi ya kama ki ta ce “To"...





********



Sai yamma likis wajen karfe 5:30 na yamma motocin daukar Amarya su ka karaso .





A ka futo da Amarya cikin shigarta na Alfarma ta sha lafaya kalar ja da baki sai kuka take bayan tarin nasihohin da aka yi mata tana rungume da Aunty Yana da kyar aka banbare ta daga jikinta a ka sa ta a mota.





Gidansu Ammar su ka fara zuwa su Mommah su ka yi mata nasiha.





Wuce aka yi da ita gidan ta da ke Rijiyar zaki wanda Abba ya gina ma shi.




Su na karasawa Aunty Summaya ta umarce ta da ta shiga da kafar dama tayi addua a gefen gadon dake dakin ta aka ta zauna.





Kowa ya ga gidan sai dai ya ce Masha Allah an zuba kaya sosai ko iyayenta na raye sai haka.



******


Sai karfe 10 na dare angwayen suka karaso.........🖊️✍🏻





Aradu nagaji😂😂🏃🏻‍♀️sai mun hadu a next page domin jin yadda zata Kaya😁


Gidan biki zanje ne💃





*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* .......✍🏻✍🏻





*Addeejerh* ❤️


👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI/RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM IDRIS*
( *shalelen kainuwa* ❤️)
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*


76~77

Hayaniyan Abokan Ango ne a falo shi ya fito da su Nafisa su ma.





Tunda suka fito Salman abokin Ammar ya ƙura wa Arifa idanu, tunda ya ganta ɗazu yaji ta burge sa sosai sabida nutsuwar ta.




Su na zama aka fara gaisawa ana hira, ɗaya daga cikin abokan ne yace,


"To ku kira mana amarya mana, don har da ƴar nasihan mu muka ƙunso".





Hararan sa Ammar yayi yace "babu inda zata fito, kabar ta ta huta wani lokacin kwa hadu".





Yanda yayi maganar cike da kishi ya saka su kwashe wa da dariya, sai da suka taɓa hira kaɗan sannan suka yi abinda ya tara su, inda ƙawayen amarya suka ce sai sun bada kuɗin siyan baki, su Nasreen da Nafisa ne kan gaba wajen tambayan kuɗin .





Wani daga cikin abokan yace "ke Nafisa wai ba a cikin tawagar ango kike ba mai ya sako ki cikin ƙawayen amarya?"





Dariya tayi tace "ka tambayi Yayana mana ai ƙawata ce ita dole kuwa in zaƙalƙale, mu dai kuɗin da kuka bamu be mana ba ya kamata ku ƙara dan amaryar tamu tsada gare ta".





Hararan ta Ammar yayi yace "duk ke ce ki ke jan zance, don Allah kuyi ku gama kun bar min Amaryata ita kaɗai mu huta".





Ai kuwa nan suka saka dariya Abokan sa suna tsokanar sa akan ya ƙosa, ya kwantar da hankalin sa yanzu zasu bar masu gida.





Nan dai aka gama siyan baki cike da wasa da dariya ana nishadi.





Su Arifa sai da suka koma ciki don yin ma Amrah sallama, ashe tana nan laɓe a bakin ƙofa tana duba su taga in tafiya zasu yi, tana ganin sun shigo ta ƙanƙame Arifa da Nasreen dake sahun gaba ta fara yi musu kuka.




Mai zasu yi sauran in ba dariya ba, sai tsokanar ta suke yi.





Nafisa har da mata waƙar "ke kika ce kina so da baki ce kina so ba da ba'a baki shi ba"ta dariya tana dada tunzura ta.





Haka dai su kai ta tsokanar ta daƙyar tabar su suka tafi, sai da Shukra da Basma sukai ta rarrashin ta, inda tuni su Nasreen sun fice ma don basu son su ma su yi kukan domin sosai taba su tausayi, ji suke yi kamar kar su tafi.





Suna fita suka haɗu da abokan ango da suke haraban gidan tare da Angon ya rako su, su suka ɗauke su don mayar dasu gida, Salman jiki na rawa yace ma Arifa tashigo cikin motan sa, babu musu kuwa ta shiga don bata kawo komai a ranta ba.





Ammar sai da yaga tafiyar su kafin ya koma cikin gidan, bedroom ya shiga inda ya tarar da Amrah na kwance saman gado tana ta kukan ta, wajen ta ya ƙarasa ya zauna ya saka hannu ya ɗago ta.




Kanta a ƙasa bata kalle shi ba, haɗa jikin sa da nata yayi ya rungume ta sosai har yana sakin numfashi, ai nan Amrah tayi tsit da kukan da take yi ta fara rawan jiki cike da tsoro.






Ganin haka yaɗago ta daga jikin nasa yana murmushi yace "Sarkin tsoro babu abunda zan miki,

1 Comments On FANSAN RAN MAHAIFANA
avatar
khadija-1-2-5

9 months ago

Reply

Tnx

Please Login or Register in order to submit comment