Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zamu na zuwa ganin ki ba"

Amrah ta daga mata kaiii Mommah tayi Murmushi ta ce; "yawwa good girl" tana share mata hawayen da ya zubomata.




*_Bayan wasu awanni_*



Mommah ce ta kwalawa Amrah Kira.



Daga daki Amrah ta amsa "Na'am gani Nan zuwa Mommah"

Da sauri ta futo Mommah ta kalleta tace; "kun gama hada kayan kuwa?".



"E'h" ta bata amsa a takaice kanta a kasa tana wasa da zoben hannunta.



Tausayin ta duk ya Kama Mommah cikin damuwa ta ce; "To kuyi sauri ku fito mu tafi" ta kalli Agogon dake daure a tsintsiyar hannun ta tace; "Ga shi yanzu har biyar tayi".



Amrah ta ce; "toh ta shige daki".


Fitowa sukai Nafisa na Jan Akwatin Amrah
Suna ta kukan rabuwa da juna.



Mommah ta kallesu tana faɗa "Nifa kukan nan ya ishe ni sai kace cewa akayi kun rabu kenan, kun hana kanku sukuni haba! ku wuce mu tafi dan Allah!".


Suka fito compond Ammar na zaune yana saurarar kira'ar sudais .

Da sauri ya fito zai budewa Mommah kofa Mommah tayi Murmushi ta ce; "Allah dai ya ma Albarka kullum bazan fasa maka Addu'a ba".



Yayi Murmushi sa mai kyau ya ce; “Amin Mommah" ya rufe kofar bayan tashiga ta zauna, ya koma Mazauninsa ya tada motar suka fuce daga gidan.


___________


Suna shiga unguwar Sharada suka nufi gidan su Zee horn Ammar yayi Mai gadi ne ya leko sai da yaga motar su Amrah ce sannan ya koma ya bude masu.



Ammr ya cusa hancin motarsa gidan yayi parking ftowa sukayi gaba dayan su .



Suka dunguma gaba daya cikin gidan Mommah tayi knocking bude mata Akayi Hajiya Sa'a na ganinta ta hau washe haƙura ta basu hanya tana faɗin "Sannunku da zuwa Hajiya"





Amrah dai na makale a bayan Nafisa Ammar ne karshen shigowa.



Suka zazzauna aka gaisa Mama da bata kula da Amrah ba sai lokacin ta kalleta tayi saurin mikewa ciki da masifa da tsawa ta ce; "au Har kin gama yawan ta zubar din naki kin dawo, to ai kuwa zanci ubanki ne wallahi!!".



Ta mayar da dubanta gurin da Mommah take zaune ta ce; "Hajiya ina kika samo wannan shegiyar Yarinyar me mugun hali irin na uwarta".




Mommah tayi maza ta kalli Mama tana faɗin "Subanallah! Hajiya ya kike zaginta me yayi zafi haka?".




Cikin masifa ta ce; "oh Dama ke kike daure mata gindi kenan take iskancin da taga dama tana zama da dadiru ita da wannan Dan naki me idon mage? ko da yake ai ke kanki kinyi kama da magajiya bai sha nono abanza ba".




Ammar ya miki da sauri idanunsa sunyi jajir jijiyoyin kansa sun Mimmike ya dakawa Mama tsawa “Maganganun ki fa sun fara mun tsauri karki kuskura kice Zaki fadawa Uwata maganar banza..............🖊️✍🏻





*MORE COMMENT*
*MORE TYPING......* ✍🏻 ✍🏻




*_Addeejerh❤️_*


*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI/RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM* *IDRIS*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*



55~56


Mama ta kalleshi ta ce “An fada din me zakayi mara kunyar banza shege kawai!".



Mommah ta mike tana nuna Mama da yatsa ta ce ”A hirrrr dinki karki kuskura ki Kara sheganta mun d'a”a fusace ta dauki jakarta , ta kalli Nafisa dake zazzare ido tace “taso mutafi".



Mikewa Nafisa tayi suka fuce da gudu Amrah ta bisu .



Mama ta ce “Gwara a tafin ke Kuma ki dawo se naci ubanki yau agidan nan".



Bata ko saurare ta ba ta
Rukunkume Mommah ta na fashewa da kuka Mommah hawaye tafara tana tausayin Marainiyar Allah sun dade rungume da juna kafin su rabu.



Mommah ta sa hannu a Jakarta ta zaro kudi ko kirgawa batayi ba ta mikawa Amrah tana Fadin “gashi ki rike ko kina bukatar wani abu kana ta ce “Ki Kara hakuri Amrah Allah baki ikon cin wannan jarabawar taki Amin".



Cikin gunjin kuka ta ce “Toh Mommah Nagode", Nafisa ta rungume Amrah tana kuka.



Ammar da ya kasa jure jin kukan Amrah ya banbare Nafisa daga jikin ta.




Mota ya shiga gurin Mai zaman banza ya bude dashbox ya debo kudi Yan dubu dubu.



Ya karasa gaban Amrah ya damka mata kudin ya kalleta Ya ga idanuwanta sunyi jajir dasu da sauri ya kau da kanshi ya ce ”ga wannan ki Kara zan Kira ki ".



Amrah ta ce “Nagode ya daga mata hannu"



Hugging din su Mommah da Nafisa tayi sukayi Sallama har seda suka fuce ta koma ciki.



Tana tura kofar falon ta kwallara Kara sakamakon wayar charger da Mama ta zuga mata .



Arifa da ta dawo daga makota tana shigowa taji kara sauri ta fara taga saurin baze ba tasa gudu.



Tana shiga falo tayi turus tana zazzare ido ganin me ke faruwa ta kwallara Kara tana fadin “Mama karki kasheta Mana"



Mama ta shako Arifa tana fadin “In kashe ta din mana dan ubanki" ta wurga ta kan kujera.



Seda ta take Amrah dake kwance rikis a kasa tana rusgar kuka, Mama ta debe kudin ta haura sama.



Arifa ta Kama Amrah ta kaita daki ta dauki akwatin ta ma
tazo zata ajiye Akwatin ta lura da Amrah dake rawar 'dari a rude ta ce “Lafiya Yaya Amrah?"


__________


Ammar suna zuwa gida direct dakin shi ya wuce ya fada kan couch ya lumshe Idanuwan sa da su kayi jajawur yana tunanin irin cin mutuncin da Mama ta mashi tana fada mashi bakaken maganganu suka fara dawo mashi cikin kwanya “Ohh dama ke kike daure mata gindi kenan ta ke iskanci tana zaman dadiro da d'an naki me idon mage ,ko da yake ai ke kanki kinyi Kama da haka gada yayi be sha nono a banza ba!!!!!!!!!!!" Da karfi ya naushi bango Yana kama kanshi.




Mikewa yayi ya nufi bathroom ya sakarwa kanshi ruwa zuciyar shi na tafarfasa.


_________


Arifa ta yaye bargon da Amrah ta lulluba dashi tana fadin “Tashi ga maganin na karbo maki".




Lallabawa Amrah tayi ta mike zaune Arifa ta ballo mata maganin ta karba ta sha .



Tana sha ta kwanta kwanciyar ta kenan Wayarta ta fara ruri ta kalli Arifa ta ce “Dan Allah mikon wayar ".



Arifa ta mika mata ta zauna kusa da ita tana karba taga Bestie ke yawo a akan screen din dagawa tayi ta Kara a kunne.


Nasreen:Salamu alaikum


Amrah :waalaikumus Salam


Nasreen: Bestie kin koma gidan kuwa?


Amrah : E'h


Nasreen: Bestie lafiya naji muryar ki haka baki da lafiya ne?meya faru?.



Amrah : karki damu zazzabi ne fa kawai.



Nasreen: Zazzabin ne zaki cewa kawai ne kuna tare da Arifa Amma ko? Allah baki lafiya Bestie.


Amrah : Amin E'h muna tare


Nasreen: Ok gobe in nazo gidan Yaya Hayatuddeen zan shigo Aunty suwaiba ba ta da lafiya wallahi


Amrah: Allah kaimu


Nasreen: Amin ki gaida Arifa


Sallama sukayi


Amrah ta ce “Arifa bestie na gaishe ki", Arifa ta ce “Ina A'msawa amma nake ganin kina boye wayar nan kar Mama ta gani”.



Amrah ta ce “Toh ta koma ta kwanta taji Zazzabin ya fara sauka".


__________


*Da daddare*


Amrah ce ta lallaba ta futo zata sha ruwa Arifa tayi bacci ta shiga kitchen ta kunna bulb din.



Ta debi ruwan kenan taji motsi ta juya kenan taga Ya Umar tana rawar baki tace Lafiya me ka keso cikin muryar bugaggu ya fara fadin shin....kika.....gudu ....ko ta fara ja da baya yana binta har takai jikin bango.




Cikin sarkewar murya tace meye.... haka.... Ya.... Umar...rumfa ya mata Bata zata ba taji hannun sa na yawo a jikinta .




Ta fakaici idonsa ta dauki tabaryar turmin karfe da ke kusa da ita ta buga mashi a goshi har sau biyu...........🖊️✍🏻





*Ku cigaba da bin Alkalamin 🖊️ Addeejerh* ❤️ *Yanzu aka fara buga* *wasan*





*MORE COMMENT*
*MORE TYPING........* ✍🏻✍🏻




*_Addeejerh❤️_*



👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI/RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM IDRIS*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*


KYAWAWAN HALAYE SU AKA FI BUKATA BA TARIN ILMI BA.

Shak Muhammad Basheer Al-ibrahimy Allah ya masa rahama yana cewa dalibansa "Kada karancin rabonku cikin ilmi ya dame ku matukar kun samu rabo mai yawa na kyawawan halaye. Domin Al'ummarku tafi tsananin bukatar kyawawan halaye sama da yadda take bukatar ilmi, saboda wannan kaskanci da wannan Al'umma take cikinsa a yanzu ta same shi ne saboda karancin kyawawan halaye ba wai dan karancin ilmi ba".



57~58

Dafe goshin yayi tana ganin haka ta gudu daki dan firgitar da tayi ko ruwan ma bata sha din ba.



Tana shiga tasa key ta jingina a jikin kofar dafe da kirji sai Ajiyar zuciya takeyi.



Umar Yana layi ya koma side dinsa.



Amrah bata iya bacci ba sai wajen karfe biyu na dare Shima bacci barawo ne ya saceta.



*Da safe*


Amrah da tayi sallah da Asuba ta samu ta dan koma bacci ta na cikin bacci taji an watsa mata ruwa firgigit ta farka.



Ta mutsutsuka idonta ta bude mama tagani rike da karamin bokiti a hannun ta tana mazurai,



Cike da masifa Mama tace "shegiyar yarinya ke har kina tunanin kina da damar komawa barci to dan ubanki tashi zakiyi kije kiyi aiki wuce kitchen kiwa mutane breakfast ta jefa mata bokitin ta fuce tana kumfar baki".



Jiki a mace Amrah ta chanja kayan jikinta ta fito daki ta nufi kitchen girki ta dora ta koma falo ta share tasa freshner ta jera Abincin a dining.



Komawa kitchen tayi zata wanke kayan da ta bata tana cikin wanke-wanken taji kanta na juyawa luuuu tayi ta fadi .



Dai dai lokacin Arifa ta shigo da karfi tace "Inallillahi wa inna ilaihir rajiun Amrah!


da gudu ta karasa wajan Amrah ta durƙusa a gabanta ta tallafota jikinta tana kuka ta ce;


Amrah lafiya me ya sameki? Mama! Mama!! Mama!!!"

da gudu Mama ta shigo kichen ɗin tana faɗin "Arifa Lafiya?"

"Mama Amrah ce ta faɗi"

"Mtsww! shine za ki wani kwala min kira kisa min faduwar gaba a banza!"


"Haba Mama kalli kiga yanda take fa"


"Na gani sai mai ta mutu mana!" ta fita daga kichen ɗin tana masifa. Arifa ta bita da kallo fuskarta na nuna damuwa Mama na ficewa ta dawo da dubanta ga Amrah cikin tausayawa ta ce;


"sannu Amrah" Amrah ta lumshi idanunta ta amsa sannun da Arifa take mata cikin azabar ciwo.


Arifa ta ce; "za ki iya tashi muje daki?"
"Uhm! eh" ta bata amsa cikin karfin hali tana kokarin miƙewa tsaye, Arifa ta taimaka mata ta mike tana rike da ita har zuwa daki ta kwantar da ita tana mata sannu.

__________

*Bayan Awa uku*

Nasreen tana zaune kusa da Amrah ta ce; "Amrah ki tashi ki shirya tunda kince kunyi waya da Ya Ammar zai zo ya kaiki Asibiti, kar ya tarar baki shirya ba".



"Toh" Amrah ta ce, Nasreen ce ta taimaka mata ta shirya ko zama ba suyi ba ya Kira ya karaso.



Da Arifa suka tafi dan gidan ba kowa Mama ta ficewarta unguwa ba tare da ta sake zuwa ta duba halin da Amrah take ciki ba.



Suna zuwa Asibitin direct Office din Dr Mutallab Muhammad suka nufa .



Suka gaggaisa cikin gaggawa yayi treating nata batare da bata lokaci ba dama Family Doctorn sune, basu wani jima ba suka tafi gida, a hanya ya tsaya ya saya masu kaza da yoghurt ya sauke su a gida bayan su Nasreen sun fita Ammar ya tsayar da Amrah,


ya zuba mata ido shafa sumar kanshi yayi ya kira sunanta "Amrah"


Ta dago kanta ta dan kalleshi cike da jin nauyinsa ta amsa da "na'am Ya Ammar"
Yace "ina so zamuyi wata magana anjima".



Fuskarta dauke da Murmushi ta ce: "to Ya Ammar Allah ya kaimu Nagode sosai ka gaishe dasu Nafisa da Mommah"



Yayi dariya wanda har sai da siririyar wushiyar shi ya bayyana ya ce; "za suji Insha Allah, sai anjima ki kula da kanki kinji Allah ya ƙara lafiya"


Amin Nagode" tayi maganar tana mai fitowa dagq cikin motar, yaja motar shi ya tafi ,ta shiga cikin gidan fuskarta cike da murmushi wanda ita kanta ta rasa na miye.



Zama sukayi suka rakarkashe da kazar da Ammar ya sai masu kasancewar har zuwa lokacin Mama bata dawo ba,
Amrah dai ba sosai taci ba.



Nasreen ta kalli Agogo tace "3:55pm bari nayi sauri na koma gidan nasan Yaya ya kusan futa"



Ta mike tsaye tana ɗaukar jakarta ta karasa wajan Amrah dake kishingide ta bata peak suka rungume juna Nasreen tana faɗin "Zan tafi bestie gobe zan shigo in na gama aikin da zanyi Allah baki lafiya".


"Amin Nagode kiyi wa Aunty Suwaiba sannu".



Nasreen ta amsa da “to" tayi hugging Arifa suka yi sallama.


________

"Assalamu Alaikum"

"Wa'alaikumus Salam"


Mommah ce ta mike cike da Murna tace "Yana anya ba batan hanya ki kayi ba".


Yana tayi Murmushi ta zauna kusa da Mommah tana dariya ta ce; "Aunty Aysha ina wuni ya gida yasu Nafisa".



Mommah tace "lafiya kalau duk suna lafiya, Nafisa ta tafi gidan Auntyn su zata dauko Auta ke kam ai bakya neman mutane ko a waya"



Yana ta sunkuyar da kanta tana wasa da bakin mayafinta ta ce" "Aunty Aysha Kai na bisa wuya wallahi kwanaki naso zuwa sai akayi wa Auwal chanjin gurin aiki da ba ma tare zamu tafi ba sai kuma yace na shirya mu tafi tare, shiyasa kika jini shiru kwana biyu wallahi, amma kiyi hakuri wuni ma zanyi sai dare"



Mommah tayi Murmushi ta ce; "Ai bakomai Amma na taya shi murna Allah taya shi riko "


"Amin"


Mommah ta karewa Yana kallo kafin daga bisani ta ce; "Yana ya naga kin rame Lafiya dai ko?".


Idon Yana ne ya kada a rikice Mommah ta ce; "Lafiya me ya ke faruwa fada kukayi da shi Auwal din ne?".



Da sauri Yana ta girgiza kanta Mommah tace " to Mene ne fada mun"


Yana ta fada jikin Mommah cikin rawar murya ta ce; "ƴar gidan Yaya Falmata na nema na rasa tunda nadawo hankalina ba a kwance ya ke ba wallahi”.



Mommah tace "Kamar ya an rasa ta? kamar wata dabba, ina kanin uban nata da har za'a neme ta a rasa?".



Yana ta dubi Mommah tace "Aunty mutanen da ba sonta su ke ba miye damuwar su da ita,
da naje matar gidan ta ringa fadan bakaken maganganu har da cewa ta tafi yawon karuwanci, tunda rayuwar da ta zaɓawa kanta kenan za su hanata ne? zantuka dai marar daɗi sukai ta faɗa min" ta karashe maganar cikin kuka.



Mommah ba karamin tausaya ma Yana tayi ba ta ce; "kai duniya tazo karshe wai dama ana samun mutane irin haka Allah kyauta!

haka fa wata yarinya kwanaki da Ammar ya kawota sak haka ita ma walllahi ga ta Yarinyar me hankali jiya muka maida ta gida, sam zumunci yanzu yayi karanci a wannan zamanin da muke ciki kowa nasa ya sani".



cikin ajiyar zuciya Yana ta ce; "Allah sarki! ya sunan ta kuwa?".


Mommah ta ce; "Amrah"


Zumbur Yana ta mike tana fadin "Amrah walllahi walllahi itace itace Aunty yar gidan Yaya Falmata".



Mommah ta kamata ta zaunar da ita suna fuskantar juna Mommah ta ce; "wai kina nufin Amrah ce ƴar Falmata?"



"Ko shakka banayi Aunty ita ce, idan kikayi duba labarin da na baki kince iri daya da na wacce kuka mayar jiya ne, kuma kinga sunan ma iri daya ne"



Mommah ta ringa tafa hannu tana fadin "lallai biri yayi kama da mutum shiyasa tun dana ga Yarinyar naga kamar nasan me Kama da ita".


Yana tayi Ajiyar zuciya fuskarta cike da Annuri ta rungume Mommah tana fadin "Allah Nagode ma da Amrah ta fada hannu nagari" Mommah tana mumushi ita ma.



Yana ta saki Mommah ta marairaice fuska tace "Amma da Baki maidata ba"



___________


Amrah na gyara gadonta taga wayar ta na haske.


Da sauri ta Karasa dan ganin mai kiran Ya Ammar tagani da sauri ta daga.


Cikin zazzakar muryarsa mai ruda Yan mata yace “Asssalamu Alaikum"


Da sauri ta cire daga kunnenta ta kalli screen din sanna tace “Wa'alaikumus Salam ya Ammar.

“Da fatan kaje gida lafiya nafa gode"

Mumushi yayi Wanda har sai da taji sautin shi ya ce; "Lafiya kalau ya jikin naki?"

"Alhmdllillah da sauki sosai"
"Madallla Allah hakan ake so, Allah ya Kara sauki"
"Amin Ya Ammar Nagode".


Dukansu sukayi shiru kowa da irin tunanin da ya ke zuciyarsa, Ammar ne ya katse shirun dake tsakaninsu

"Hello Amrah kina jina?"
tana murmushi ta amsa masa da "eh Ina jinka Ya Ammar"


"Yauwa tun dazu naso yi maki magana sai na ga bakya jin dadi shiyasa na ce bari na bari zuwa jimawa jikin ya kara sauki sai na maki maganar, Hello

"Ina jinka"

"am dama na zauna nayi tunani akan maganar da kikayi ranar ne akan takardun filayen Abban ki inaso ki kula kiyi takatsantsan da movement din kowa na gidan".



Amrah ta danyi jm kafin daga bisani ta ce" "zanyi yadda kace Insha Allah"

"Yawwa Good girl sai anjima ki gaida Arifa".


___________

"Zee ya fa kamata muje Asibitin Aman nan da kike yayi yawa"


Zee ta kalle Mama da idanunta da suka mata nauyi cikin Muryar mai ciwo ta ce; “Toh".


Mama taimaka mata tayi ta shirya suka tafi asibiti.



A kofar wani karamin Asibiti Mama tayi parking
a saman Asibitin ansa *AURORA SPECIALIST HOSPITAL*.



Kasancewar private ne basu wani jima ba suka ga likita ya danyi rubuce rubuce a takarda ya Kira wata Nurse ba a jima ba Nusre din tashigo ya kalli Nurse din yace "ki Kai su lab ayi mata test din fitsari da na jini" ya mika mata takardar.



Rusunawa Nurse din tayi ta karba tace "Okay sir".


Ta kalle su Mama "sannu Hajiya muje ko?"


Mama ta miki tsaye tana rike da Zee ta ce; "toh" suka bi bayanta.



*After 15 minutes*



Doctor ne ya karbi result din yana sa glass dinsa ya fara duba takardar yana Murmushi.



Mama cike da mamaki tace "Doctor yana ga kana Murmushi?".



Doctor yace "Abun farin ciki ne ai"


ya gyara zaman glass din idonsa yana kallon Zee Yana murmushi, ita kuma Zee duk tayi tsuru-tsuru fuskarta cike da fargaba.



Cike da neman karin bayani Mama tace "bangane ba fa doctor?".



"Congratulations Hajiya yarki na da juna biyu kin kusa yin jika".



Da sauri Mama ta Mike da tsananin firgici ta ke faɗin “Ciki fa kace! Ina karya ne doctor ni yata bata da wani ciki!!!!!!!!!!...............🖊️✍🏻




_Comments dinku sun sani farin ciki sosai shiyasa nima nace banasa ku farin ciki_ _yadda kuka sani shiyasa nayi dogon typing_ .





*MORE COMMENT*
*MORE TYPING.....* ✍🏻✍🏻





*Addeejerh* ❤️



👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI/RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM* *IDRIS*
( *Shalelen* *kainuwa❤️)*


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*


59~60

Doctor ne ya kalleta yace “to mudai abun da bincike ya nuna mana kenan in Baki yardaba sai kije wani Asibitin".



Mama cikin masifa tace “Gwara mu chanja asibitin yarinya na Zazzabin zaka ce wani ciki ....



Da sauri doctor ya dakatar da ita cikin tsawa yace “gerrout from my office Zaki samun headache dauki yarki ku fuce patients na jira na".



A fusace ta fizgi hannun Zee suka futa baram ta bugo kofar.



Wani Murmushi doctorn yayi yana shafa sajen fuskarshi yace “Allah ya kyauta ya shirya",ya cigaba da duba patient dinshi .


__________

Su Mama sun zazzaga asibitoci da yawa Amma amsar daya ce.


Mama ta daki sitiyarin tana fadin “matsala banson cikin nan ya nuna ki zubar mun da mutunci kowa kace a cire sai su wani ce su masu imani basa cire ciki"ta karasa maganar cikin kumfar baki.



Mama tace “ohh na manta bari na nemi Mariya ta bamu wata mafutar ".



Ciro wayar ta tayi a jaka tayi dialing number Mariya ba a daga ba ta sake Kira........


__________


Mariya tace “ga wani maganin tasha bayan Awa biyu cikin ze bi rariya ".



Dariya Mama tayi tace “Shiyasa nake son ki Mariya kina ja da yawa".


Mariya ta sheke da dariya suka tafa


*Bayan Awa biyu*


Zee ce kwance a dakin Mama wani irin murdawa taji marar ta tayi ihu ta saki Da sauri Mama ta juyo ta kalleta tana fadin “Lafiya Zee"? dai girgiza mata Kai take Mama duk ta firgirta ta kamata suka sauka kasa.



Asibiti Mama ta kai Zee ganin halinda da Zee din take Nurses din suka fara bata taimakon gaggawa duk yadda suka so cikin kar ya zube sai da zube.



Wani doctor ne ya futo yana sharfe gumi da hanki din hannun sa.



Da sauri Mama ta taso a rikice tace “ya akai doctor da fatan ba abun da ya same ta?"

Ta ringa jero mashi tambayoyi .



Shafa kanshi doctor din yayi ya kalleta yace “Hajiya sai dai kiyi hakuri mun yi iya yinmu dan cikin kar ya zube Amma Ina ".



Mama Bata ko nuna damuwa ba tace “Doctor zan iya ganin ta amma?".



Doctor yace “E'h Zaki iya ganinta ruwan da aka Kara mata inya kare zamu sallame ta".



Mama ta kalleshi tace “toh nagode".


Doctorn bai ce komai ba ya tafi office din shi Yana mamakin Mama yadda bata damu da zubewar ya fara tunanin ko cikin bashi da uba da sauri ya kawar da zargi a ranshi ya cigaba da harkokin gaban shi


____________


Amrah na cikin gyaran dakin Umar bata san ya dawo ba se ji tayi an kinkimeta se cilla kafafuwa take tace “Dan Allah ya Umar ka sauke ni ".


Ko saurarar ta bai yi ba ya jefa ta kan gado tana kokarin tashi ya danne ta yana fizge hijabin jikin ta.



Dagewa Amrah tayi ta gantsara mashi cizo a damtsen hannun shi..........🖊️✍🏻


*Gashi kuyi manage pls zanje asibiti ne nayi wannan dan kar kuji ni shiru Amma insha Allah next page dogo zan zanyi*

*Allah bar kauna* ❤️




*MORE COMMENT* *MORE TYPING* .......✍🏻✍🏻






*Addeejerh* ❤️


👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI/RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM IDRIS*

( *Shalelen kainuwa* ❤️)


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*.

No burdened soul can carry the burden of another,Even if one weighted down calls for help with its burden, nothing can be lifted from it, even if they were related. You are to warn those who fear their Lord inwardly, and perform the prayer. He who purifies himself purifies himself for his own good,To Allah is the ultimate return.
Suratul Fadir V:18




1 Comments On FANSAN RAN MAHAIFANA
avatar
khadija-1-2-5

9 months ago

Reply

Tnx

Please Login or Register in order to submit comment