Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dama rarrashin ki zan yi tunda kinyi shiru to sauko muje falo kici abinci".





Bata ce komai ba illa saukowa da tayi tunda ya riƙe mata hannu babu yanda zata yi, suna fitowa falon ya zaunar da ita saman tattausan karpet ɗin dake tsakiyar parlour'n, kana ya nufi kichen ya ɗauko Plates da Spoon tare da wuƙa ya fito, shi yazuba abincin cikin Plate sannan ya yanka kazan ta yanda zai musu daɗin ci, duk ya ciro drinks ɗin cikin ledan ya jera mata a gaban ta sannan ya zauna.





"Yauwa bismillah kici iya cin ki bana son in ga komi anan".





Ɗago kan ta tayi ta kalli kayan da ya jera mata a gaban ta, sai ta ƙara noƙewa alamun baza ta ci ba.






Lallaɓa ta ya fara yi ya na jan ta da suratu a haka har ta ɗan yaga kaɗan taci tace ta ƙoshi, abincin ma kasa ci tayi duk da kuwa tana fama da yunwa dan tun safe , youghot ne ka ɗai tasha sosai saboda yayi mata daɗi.





Shima ba wani cin yayi ba sabida hankalin sa gaba ɗaya baya kan abincin, zumuɗi ya hana sa ci, tattare kayan yayi ya kai kitchen sannan ya zo ya miƙar da ita suka nufi ɗaki, wanka ya umarce ta ta shiga tayi, sai ta shige toilet ɗin ba tare da ta cire kayan ta ba.




Shi dai sai dariya yake yi a ransa yana faɗin "uhmmm duk wayon amarya...".





Sai da ta fito sannan shima ya shiga, lokacin da ya fito ta haye kan gado ta ƙudundune, duk da ba wai kayan barci ta saka ba amma doguwar riga mara nauyi tasa wanda tasan bazai fito da tsiraicin ta ba, wai duk wai kar yace ta burge shi.





Ya kalleta yace mata sauko muyi sallah.




Sau kowa tayi ta ɗau Himar tana ƙoƙarin sakawa.





"Au daman kinyi alwala ne?"ya tambaye ta.




Gyaɗa masa kai ta yi ta na saka Himar ɗin ta





Dariya ne yaso kufce ma sa, sai dai ya danne don kar ya fito ta mashi rigima.





"Uhm daman kinsan zamu yi sallar ashe kika haye gado"ya faɗa aransa yana shige wa gaba akan sallayan da ya shimfiɗa.





Bayan sun idar yay musu addu'a mai tsawo kafin ya shafa ita ma ta shafa.





Ta na gamawa ta haye kan gadon da sauri ta shige can ƙarshen gadon.




Murmushi yayi ya cire kayan shi ya shiga wanka ya fito ya zauna a kan stool ya shafa wanchan ya shafa wannan kamar wani mace.




ya na gamawa ya hau kan gadon bayan ya kashe fitilar ya bar dim light.





Chan kusa da ita ya kwanta tana jin saukar numfashin sa a bayan ta jikin ta ya fara rawa kamar mazari da ma batai bacci ba ji tayi ya fara yawo da hannunsa a ilahirin jikin ta...........Asuba ta gari na fece .






Shesshekar kukan ta kawai ke tashi a dakin rungumo ta yayi jikin sa tana kokarin kwacewa ya matse ta yana shafa bayan ta cikin sanyi murya kamar zai yi kuka ya ce “Dan Allah kiyi hakuri mana Kinga jikin ki har ya fara zafi".




Da sauri ta kwace daga jikinshi tana tana hararashi dariya ce ta kusan kwace mashi ta tashi zata shiga toilet taji ba zata iya ba sai ta tsugana ta fashe da kuka.





Zuwa yayi ya dauke ta har cikin bandakin ya kai ta ta ce ya futa ya na dariya ya fice.





Ta dade sosai dan saida ta Kara gasa kanta futowa ta yi tana ware kafa kamar yar kaciya lol,da sauri ya tashi dauke ta ya zaunar da ita akan couch ya sa mata hijabi ta tada sallah shi kuma ya futa kitchen ya na hada mata tea ya ji an yi knocking .





Zuwa yayi ya bude Drivern Mommah ne dauke da basket ya gaishe da Ammar kana ya ce “Gashi inji Hajiya kuma tace wai basai tayi girki ba har na tsawon kwana bakwai ita zata na turo da Abincin".





Godiya Ammar yayi mashi ya koma ya na budewa ya ga Chips ne da farfesun kayan ciki murmushi yayi ya ce “Allah sarki Mommah ta ina sonki" diba ya yi a plate ya dauki tea din ya nufi dakin shi .





Tunda ta idar ta nannade a gurin harta fara bacci ya tashe ta ya ringa lallaba ta yana lallashi ba laifi ta dan ci ya ballo magani ya bata.


*********



*ZEE*



Zee abun nata har yayi yawa tun daga ranar da Mama ta gudu ita ma ta je gurin saurayin ta hotel suna badala waiyazubillah.





Har ya sa mo masu gida ya mai da ita matar shi duk sanda ya so ya zo mata .




Har dai ya mata alkawarin aure karshe ya gudu ya barta ,ma su gidan ku ma su ka zo su Kai mata korar kare ba ta biya kudin haya ba.




Haka ta koma yawan clubs clubs anan ta hadu da wa ni dan siyasa har ya sa mata HIV




*UMAR*


Umar abun shi ma ba'a ce wa komai tunda kudaden shi suka kare.



Shi da abokanan sa su ka fara fashi su na samun kudi suna shayeyen su da bata yayan mutane .




A halin yanzu ma an kama su ........🖊️✍🏻











*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* ......✍🏻✍🏻





*Addeejerh* ❤️


👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI/RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM IDRIS*
( *shalelen kainuwa* ❤️)
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*



78~79

Ranar da Amrah da ta cika sati daya ta fara girki .




Da yamma Ammar ya dawo tun daga bakin kofa ya fara jiyo kamshin girki direct kitchen din ya nufa tana tsaye tana yanka carrots sai jin motsi ta yi wanda ta tsorata dama tunda ya fita wani tsoro ya mamaye ta da karfi ta kurma ihu yayi maza ya toshe mata baki.




Ta na jin kamshin turaren shi ta gane shine.





Kwalkwal tayi ido za tayi kuka ya kyalkyale da dariya ya ce “Ashe matar tawa matsoraciya ce".




Hade rai tayi ta juya ta cigaba da aikin ta rungumo ta yayi ya ce “Sorry wifeey ban san zaki tsorata ba"





Ta chuno baki ta ce “Bawani ka na sa ne" dan bakin nata daya tsone mashi ido yayi kissing .






Ya Kama kunnen shi alamun ba da hakuri ya na shagwabe fuska ya ce “Yi hakuri bazan sake ba kinji in na sake kimun bulala".





Dariya ta kyalkyale dashi ganin yadda ya yi side hug ya mata yana murmushi ya ce “toh zo mu je daki ki taya ni wanka nagaji da yawa"Ya na kanne ido daya.




Da sauri ta noke kaii ita bazata ba.




*TWO MONTHS* *LATER*



Ammar na shiga dakin Amrah ya jiyo kakarin amai daga toilet da sauri ya ƙarasa toilet din.





Ya tarar da ita durkushe rike da cikin ta tana sheka amai sosai ta baci da aman rike ta yayi har ta gama ya wanke mata baki sai sannu yake mata.





Ya cire mata doguwar rigar jikinta ta ya daura mata towel .




Ya zaunar da ita a bakin gado ya juya kenan zai dauko mata wasu kayan ta fara kakarin amai yana juyowa kenan ta sheka mashi aman a jiki har sai da ta gama .




Cincibarta ya yi su ka koma toilet din ya gyara mata jiki ya ciro kaya sannan ya kwantar da ita.






Ya futa ya hado ma ta tea da kyar ta yi kurba uku shima sai da ta dawo dashi.






Ba karamin rikicewa yayi ba yasa mata himar ya dauketa kamar jinjira ya sa ta a mota ya zagaya side dinshi ya ta da motar da sauri mai gadin ya bude ma su gate.





Asibiti suka nufa direct office din Dr Mutallab suka nufa tests ya sa aka yi mata.







Bayan yan mintuna sai nurse ta shigo cikin rusunawa ta mikawa Dr Mutallab ta mika Mai envelope karba ya yi ita kuma ta fice glass ya sa ya fara Karantawa yana murmushi.






A hasalce Ammar ya ce “Haba Dr ya naga kana murmushi mata ta ba lafiya ?".






Zaunar dashi Dr Mutallab yayi ya na wani irin murmushi ya ce “Calm down Ammar ka bi komai a hankali,ka saurare ni".




Ita dai Amrah ta lumshe Idanuwanta.




Dr Mutallab ya mikawa Ammar hannu ya na murmushi shima Ammar ya yi murmushin yake da bai Kai zuciya ba






Dr yace “Congratulations Ammar I am so happy for you matar ka na da ciki wata 2 da kwanaki".






Wani irin tsalle Ammar yayi kamar karamin yaro bai sanda ya sun gumi Amrah yana juyi da ita ita kam mamaki duk ya cika ta kenan yi daya ta samu ciki Dr Mutallab sai dariya ya ke mashi.







Sai da ya gaji dan kanshi ya ajiyeta ita kuma duk kunya ya Kama ta ya yi hugging Dr yana fadin ”Wanna albishir din da ka fada mun zan baka tukuici mai tsoka".






Mumushi Dr ya yi ya ce “Toh godiya na ke Allah sauke ta lafiya" Amin Ammar ya amsa ya rubuta ma su maganin da zata sha.






Su ka tafi tunda su ka tafi yake lallabata ko motsi ta yi zaice lafiya sweetheart mai ya faru.





Parking yayi a gefen hanya ya kalleta cike da kulawa ya rike hannunta ya ce “Yanxu mai kike son ci wifeey sai muje restaurant?".





Cikin halin ciwo ta ce ”Nidai dan sululub nake sha'awa"




Da sauri yana ya mutsa fuska ya ce “Mai ne Dan sululub kuma?"





Murmushi tayi ta ce ”Au ba ka san shi ba ".




Ya marairaice fuska ya ce “Ban san shi ba dan Allah wifeey ki nemi wani abun mai sauki".





Aiko tace ita in bashi ba ba abunda zata iya ci.





Ko mai ya tuna ya kira Mommah ya sanar da ita su na gama wayar ya na murmushi ya kalle ta ya ce “ta kwana gidan sauki Mommah tace za ta sa Nafisa tayi maki" a hankali tace “Toh" ya ja motar su ka nufi gidansu Mommah.






Su na karasawa ya yi maza ya zaga side din ta ya dauke ta aiko ta sa mashi rigima sai ya sauke ta.





Suna zuwa dai-dai kofar falon tasa mashi kuka dan dole ya sauke ta.






Su na shiga bakowa a falon sai auta tana kallo su ka yi sallama a guje tazo ta rungume Amrah tana murna tsawa ya daka ma ta wanda ya gigita ta ya ce “ke mai haka sai kin kayar da ita".




Auta ta marairaice fuska ta ce “Sorry".





Mommah ce ta karaso falon tana fadin “Babana lafiya ka shigo kana fada?" ta kalli auta ta ga ta yi kwalkwal da ido.






Sosa keya ya yi ya karasa gurin ta su ka gaisa Amrah ma ta gaishe ta sai sunkuyar da kai ta ke Mommah ta yi mata ya jiki.







Nafisa ce ta fito hannunta rike da plate tazo ta ajiye a gaban Amrah ta na gaishe da Ya Ammar sannan su ka gaisa da Amrah ma .





Da sauri Amrah ta fara cin dan sululub din hannu baka hannu kwarya wanda ya sha tumatir da Albasa ga manja da yaji da ma tun sanda Nafisa ta kawo ta ke hadiyar yawu.





Tuni Mommah ta dago jirginsu daki ta koma.





Ammar ne ya kalleta ya ce “Haba sweetheart kici a hankula karki kware ke fa kadai kike ci dariya Nafisa ta sheke da.............




*BAYAN WATA* *BAKWAI*



Amrah ce zaune akan carpet ta Mimmike kafafuwan ta da suka kumbura Ammar na mammatsa mata ,ta tasa kankana a gaba tana tasha wanda kullum sai ta sha safe, rana, dare.



*Da daddare*


Wajen ƙarfe 03:30pm na dare Amrah ta fara jin ciwo a jikin ta, ciwon ne ma ya tashe ta sabida yanda ta ke jin bayan ta ya riƙe sosai ga marar ta dake mata ciwo, da farko taso ta daure sai sintiri ta ke yi a tsakar ɗakin tana yarfe hannaye, da taji azaban sai ƙaruwa ya ke yi gashi ta haɗa zufa kashirɓan ai ba shiri ta fara kuka jin ciwo yaki ci yaki cinyewa.






Ta na duƙe ne a ƙasa sai murkususu ta ke yi tana faman kiran sunan Ammar.






Ammar kuwa bai ji ba yana ta bacci, sai da ta buɗe murya tana kuka da karfi sosai kafin ya jiyo kukan na ta cikin bacci kamar a mafarki, ya na buɗe idanun sa ya hange ta a ƙasa durƙushe, da ya ke ta kunna fitila lokacin da ta tashi.







Da sauri ya sauko a rikice ya nufe ta ya na kiran sunan ta, amma ina bata jin sa iyakan dai hannun sa da ta damƙo tana faɗin,






"Kataimaka min zan mutu wayyo Allah na bayana wayyo Kwankwaso na,wayyo mara ta na na shiga uku, wayyyoo.."





Hankalin Ammar ya yi matuƙar tashi sai yi mata sannu ya ke yi ya ma rasa mai ma zai yi, sai daga baya dabara ta faɗo mashi ya miƙe da sauri yaɗau waya ya kira Momma.





Ya na sanar mata ta fara mashi faɗa akan mai ya ke jira bazai ɗauke ta su tafi asibiti ba?,shi sam ya rikice ya manta da wani asibiti.





Hakan ne yasa yayi saurin saka wayan shi a aljihun gajeren wandon sa ya saka jallabiya itama ma ya sa mata hijab din ta take sallah ya sungume ta daƙyar sabida girman cikin ta, fita su ka yi ya saka ta a mota yaja motar a sukwane yabar gidan bayan mai gadi ya buɗe masa Gate.





Su na isa asibitin aka amshe ta aka yi labour room da ita Ammar zai bisu suka dakatar da shi.





Zagaye Ammar ya ke ta yi a reception ɗin ya kasa zama ya kasa tsaye ya rasa ina zai sa kanshi, har sanda su Mommah da Nafisa su ka zo yana nan tsaye ya na ta kai komo, lokacin da suka zo suka ganshi a haka ai sai su ma hankalin su ya ƙara tashi sosai Nafisa har da kukan ta Mommah ko Addua take yi.






Ana haka ita ma Aunty Yana ta zo tunda Momma ta faɗa ma ta ta rude, haka suka zauna suna jiran fitowan likitocin amma shiru ka ke ji har safiya ta yi tangararas






Momma ce ta ce ma Ammar ya je ya yi sallah tunda ko sallan asuba bau yi ba yana nan yana sintiri.




******


Ko da ya je yayi sallan bai fito ba sai da yayi ta mata addu'an Allah ya sauke ta lafiya, lokacin da ya dawo har Daddyn su ya karaso .





Haka su ka yi cirko-cirko suna jiran fitowar likitocin har a lokacin kuwa babu labarin haihuwar Amrah tana can tana shan wahala ta kasa haihuwa, sai faman kiran mijin ta take yi.......🖊️✍🏻








*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* ........✍🏻✍🏻








*Addeejerh❤️*


👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI/RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM IDRIS*
( *shalelen kainuwa* ❤️)
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*


80~81

Wasa-wasa har rana ta take tana shirin faɗuwa Amrah bata haihu ba.



A lokacin Ammar har ya fita hayyacin sa sai kuka ya ke yi kamar yaro, Momma ke ba shi haƙuri amma ina ya kasa kwantar da hankalinsa gani yake kamar Amrah zata mutu.



A cikin su babu wanda ya tafi sai Daddy da Nafisa ne suka koma gida, ita Nafisan ta koma don dafo musu abinci, har ta dawo su ka ci abinci su ka yi Sallah amma shiru babu labari.



Sai alokacin ne ɗaya daga cikin Likitocin da su ke duba Amrah ya fito, anan sukai kansa suna tambayan sa halin da ake ciki.




Ce musu yayi su biyo sa Office, bayan sun shiga sun zazzauna yake faɗa musu halin da ake ciki.



“Amrah ta kasa haihuwa da kanta kuma gaskiya suna buƙatar jini sai an saka mata ko ƙarfin ta zai dawo jikin ta, idan kuma aka ƙara wasu awanni bata haihu ba zasu yi mata CS dan zata iya samun jijjiga"cewar likitan.




Nan fa hankalin su ya sake tashi sosai Aunty Yana da Nafisa suma kuka su ke yi sosai wannan karon domin sun bi sahun Ammar.



Jinin Ammar ɗin aka gwada aka ɗiba yayi dai dai da nata sannan aka ƙara mata.



Awanni biyu sun shuɗe babu haihuwar Amrah don haka dole aka shirya don yi mata theater, ana cikin shiryawan ne za a shiga da ita ta fara naƙuda gadan-gadan sai ga yaro ya fito, bata fi minti biyar ba ta sake sulluɓo ɗiya mace.



Nurses su ka yanke masu cibiya suka gyaggyara su.



Wata nurse na futowa su Ammar suka yi kanta suna ta jero mata tambayoyi ta haihu.



Nurse din tayi murmushi ta ce congratulations ta haihu an samu twins mace da namiji .



Sujjada Ammar yayi yana godewa Allah kowa sai murna.



Bayan an kintsa su sannan ne aka basu damar shiga, shima ba wai zasu jima bane don ba'a son hayaniya kasancewar Amrah na bacci.



Ko da suka shiga yaran suka ɗauka masu tsananin kyau da burge wa, an shirya su cikin kayan sanyi su sai bacj su ke yi.



Ko wannen su sai washe baki ya ke yi da wannan kyauta da Allah yaba su, barin ma Ammar har da ƙwallan sai da yayi ido biyu da yaran nasu sosai suke kama da shi kamar yayi kaki.



Allah mai iko wai waɗannan yaran yanzu mallakin sa ne? Abinda yayi ta sakawa a ransa kenan bakin sa yaƙi rufuwa.



Wajen gadon da Amrah ke kwance ya nufa bayan ya miƙa wa Aunty yana macen dake hannun sa, zama ya yi bakin gadon yana riƙe da hannun ta cike da tsananin ƙaunar ta a ransa, ta sanadiyar ta yau ya samu kyauta mafi girma wanda ba kowa ne ke samun irin su ba.




Haka dai suka kasance cikin farin ciki, masu zuwa ganin jarirai da uwar su sai zuwa suke yi, sosai asibitin yayi makil mutane sai zuwa ganin su ake yi, sai wajen 09:30pm na dare ta farka.



Washe gari kuma aka sallame su suka koma gida, har a lokacin taƙi ba ma yaran nono.




Mommah ce ta shigo dakin da Amrah take hannun ta dauke da tray ta ajiye shi a kan center table ta kalli su Arifa da suke daukar twins a hoto tace masu “in Amrah ta futo daga wanka kuce nace ta tabbata ta cinye tuwan nan ".



Arifa ce ta amsa da toh.



Ita kuma mommah ta fice tana futa Amrah ta fito tana chuno baki gaba.



Wata yar dattijuwa na biye da ita tana mata fada tana fadin “banzayen yara wankan zaku na gudu duk ku ragwargwabe tun kafin ku tsufe ".



Banza Amrah ta mata tana kunkuni su Nasreen su ka kyalkyale da dariya da sauri ta balla masu harara su ka sake kyalkyalewa da dariya.



A harzuke ta tashi ta fara shiryawa ita kuma dattijuwa inna mairo ta karbi macen ta fara mata wanka.



Aunty Yana ce tashigo hannunta rike da Samha tana bacci ta gaishe da inna mairo tana kwantar da samha su Amrah suka gaishe ta ta fara cin tuwon ta da yaji man shanu da yajin daddawa.



Tana gamawa cikin fada fada Aunty Yana ta kalli Amrah tace “Oya tunda cikin ki ya dauka sai ki bawa yaran su ma susha dan shashanci tun da aka haifesu baki basu nono ba ko laifin uban mai sukai maki , kafin in bude ido na inga kin basu.......kafin ta karasa Ammar ya yi sallama
Aunty Yana ce ta amsa gaishe su yayi.



Ya kalli Amrah ta chuno baki yace “lafiya mai ya faru sweetheart? wa ya taba mun ke?"



“Wa ko zai taba ta in banda ita da zata cutar da yara taki basu nono kwata kwata" cewar Aunty Yana ta mikewa ta fuce duk su Arifa suka mara masu baya.



Suna futa ya rungumo ta a jiki shi ya na fadin “Yi hakuri kinji kidan basu kadan zasu sha "



Ya dauko macen ya dora mata a cinya ya zuge mata zip din rigarta ya ciro nonon ya sa ma babyn a baki tana kamawa Amrah tasa ihu tana cire nonon .



Tayi kwal kwal da ido tana kallonshi tace “kaga zata tsigen ko?".



Dariya ce taso kwace mashi amma ya danne ya rumgumo ta a haka ya sawa yarinyar a baki da sauri ta runtse ido tana cije baki a haka ta gama sha tayi gyatsa sannan ta bawa namijin shima yayi gyatsa.


____________


*Ranar Suna*


Yau take suna an radawa twins suna baby girl din *FATIMA* za'a na kiranta _Basma_ shi kuma baby boy din *ABDULMUNAF* za'a na kiranshi _Bassam_ ba karamin murna Amrah tayi ba da karar da Ammar ya mata an yanka raguna hudu da sa guda da Abban su Ammar ya bayar gudunmawar shi.



Da safen su Amrah su kayi anko shadda ita da Nurul qalb din ta ansha hotuna sosai.




Ansha suna sosai su Nasreen har anko suka yi a wani event center a kayi sunan an raba savourniers a jaka masu dauke da hotunan Basma da Bassam.



Ammar tunda akayi suna ya dawo gidan Mommah ya tare ya takura a bashi matarshi.




Mommah ta rantse tace sai sunyi arbain.




Haka ya dawo gidan ya tare har sai da sukayi arbain da kwanaki yaje ya kai Mommah kara gurin Abba ta ki bashi matashi Abba yasa Mommah ta bashi matarshi.




Bayan watanni yan biyu sunyi wayo sosai.




*NINE YEARS AGO*



"Sweetheart Wai har yanzu baki gama shiryawa bane?"



"Na gama Nurul qalb gani nan fitowa". Amrah da ke cikin ɗaki ta faɗa.



Ba ta jima ba ta fito cikin shirin ta na Swiss less mai ruwan madara da ratsin ja, sai gyale da ta yafa daga saman kanta bayan tasha ɗaurin ɗankwali mai kyau wanda ya zauna ɗass gwanin sha'awa.



Ammar na zaune saman kujera, sai ƴan uku da su ka haifa kyawawan yaran su, yanzu shekarun su huɗu sun yi wayau sosai, Bassam da Basma kuma suna gidan Mommah tun shekaran jiya sun je mu su weekend, shine su ma yau zasu je daga nan sai su taho da su.



Tana isowa cikin parlour'n ya miƙe ya na kallon ta.



"Wow my sweetheart kinyi kyau".



Murmushi tayi mai ban sha'awa kana ta ce "kai ma haka Nurul qalb ".



"Ok muyi sauri lokaci na ƙure wa gashi har rana tayi, ku tashi muje .....".



Gaba ɗaya tashi suka yi yaran, Ammar ya riƙe musu hannu, itama Amra ta riƙe ma ɗayan hannu suka fice.



Mota suka hau suka bar gidan, a cikin mota sai hira su ke yi su na dariya yayin da ƴan uku suke taya su da shirmen su.



"Nurul qalb tsaya don Allah in raba ma mabaratan can sadaƙa".



Tsayawa yayi kamar yanda ta buƙata, har ta buɗe ƙofa zata fita ya ciro kuɗi cikin aljihun sa masu yawa ya mika mata ya ce "gashi ki ƙara da wannan ko nima zan samu ladan".




Murmushi tayi ta'amsa ta fice ba tare da ta kula da ƴan uku( Rayyan , Ra'is sai Nidal) dake faman ce mata zasu bi ta ba.



Ajiyan zuciya Ammar ya saki idanun sa kan Amrah da har ta kusa ƙarasawa wajen mabaratan, sosai yake ƙaunar matar nasa sabida tausayi da take dashi, gashi bata da rowa ko kaɗan duk abinda ta samu to na mutane ne masu bukata , yanzu haka duk kuɗaɗenta da ta gada ta bada an gina masallatai, rijiyoyi da sauran abubuwan da Ya kamata mai imani ya kasance yana aiwatar wa don samun lada kuma ta kafa kungiyar mata .



Amrah na Isa wajen ta fara raba musu kuɗin, dai dai tazo kan wata mata wacce tafi kowa yanƙwane wa da lalace wa, duk tayi furu-furu kayan ta duk a yage, ta miƙa kudin zata bata kenan matar da ɗago suka haɗa idanu da Amrah.



Ko barci ta tashi babu ta yanda za'a yi baza ta gane Mama ba sabida muguntan da tayi mata a rayuwanta, da sauri ta janye hannun ta tana

1 Comments On FANSAN RAN MAHAIFANA
avatar
khadija-1-2-5

9 months ago

Reply

Tnx

Please Login or Register in order to submit comment