Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gate sukai horn mai gadi ya bude masu suka shiga,


Aunty Sumayya tace ta shiga da kafar dama tare dayin addua.



Har dakinta aka kaita ta zauna a bakin gado fuskar ta lullube da lafaya.


Masha Allah gidan ya tsaru kowa se san barka yakeyi haka mutane aka tafi Ana santin gidan.



Bayan 15 minutes kowa ya watse se Amarya da kawayenta suna shirin tafiya dinner Amarya an shiryata cikin red gown da silver head tasha kwalliya masha Allah kamar ka sureta.


Motocin tafiya dinner ne sukazo dan tafiya da amarya da kawayenta



Seda kawayen suka kaita har motar sannan suka nufi tasu babbar kawarta fatima tashiga gaba *fabs* *event* *centre* suka nufa an tsara komai Kawar amarya fatima ta bada tarihin Amarya abokin ango Abdallah ya bada tarihin ango an ci an sha bawanda ze ce beci abinci ba kowa ya gwangwaje da aka tashi duk Wanda ze tafi seda aka bashi savouniers Amarya da ango suka nufi gidansu asuba ta gari.

________
*Bayan* *sati* *daya*


Abbiey ne yake kwalawa Ammi Kira yana fadin Wai falmata baku gama shiryawa ba kinsan inason zuwa police station se in wuce office.


Tana saukowa tace Gamunan futa suka futa ta rufe gidan.


Abbiey ya kira malam idi yace kaduba motar Dana ce ma jiya daddare bawani matsala,


Cikin girmamawa yace ehhh na duba komai lafiya.


Abbiey yace masha Allah suka shiga motor suka tafi.


Suna hawa titi Ammi ta kalleshi tace muje kawai mu sauke Amrah danni ba zama zanyi ba se malam idi yazo ya dauke ta nikuma se mu wuce office din tana marairace murya,


Abbiey yana dariya yace falmata baki da dama yarki ayy na motar dai ko kin manta ,


Kallo Amrah tayi da hankalinta nakan game dinta.


Haka suka ringa hirar su cike da so da kauna har suka karasa gidan Yana sosai tayi farinciki da zuwansu bare da Amrah zata wuni amma bata jidadi ba da yayarta baza ta zauna ba tacika masu gabansu da kayan ciye ciye ba lefi sun danci suka ce zasu tafi.


Amrah seda tabi su ta rungemusu ta dade rungume jikin Ammi tayi kissing nata tace karfa ayiwa Aunty fitina.

Tace toh suka futa har mota suka rakasu Ammi ta dade tana kallon Yana tace Yana ga Amrah nan koda na rasu dan Allah ki rike mun ita sannan in suruki na yadawo ina gaisheshi.



Yana tayi murmushi me hade da kwalla tace insha Allah se kinga auren Amrah harma da jikoki ,


Murmushi ammi tayi tace Allah sa sannan tace saduwar alheri har suka futa suna dagawa juna hannu ita da Amrah.


Suna futa titin stearing ya kwace Abbiey yayi ta kokari rikewa ina ji kake
tim motar ta kifa tayi gefen titi mutane aka yo gunsu ana “innalillahi wa inna ilaihir rajiun" motar ka na gani dakyar mutanen ciki zasuyi rai mutane akayi kokari aka ciro su duk jikinsu gilasai aka karasa dasu asibiti.

Wani ne yasamu Waya acikin jakar Ammi ya duba last call dinta Yana ya gani,

Dialing yayi Ana dagawa ya labarta mata innalillahi kawai ta ringa maimaitawa ta tambaye shi asibitin yace “mata aminu kano teaching hospital ",

Cikin Yan mintina suka karaso asibitin ita da mijinta suna zuwa har Allah ya masu cikawa ba rabon su gana tayi kuka sosai kamar ranta ze futa tana ta surutai tana rungume da Amrah hatta shikansa auwal din yayi kwalla kowa a gun ya tausaya mata......... ✍🏽✍🏽✍🏽


Yanzu wasan ya fara🔥🔥


*Shin* *ko* *kunsan* *Alhaji* *jibrin* *ze* *kai* Yana *kara* , *ko* *me* dalili?


Kubiyo ni kuji


*MORE* *COMMENT*
*MORE* *TYPING* ........ 🖋️✍🏽


*Addejerh* 🥰

*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI* / *RUBUTAWA*


*BY* *KHADIJA* *ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

Na sadaukar da page din ga mahaifina Alhaji Adamu idris much luv❤️my hero Allah ja da ranka Allah kara ma nisa Kwana da daukaka
Amin ya rabbi👏

17~18
Haka suka dauke su aka tafi dasu gidan Yan aikin gidan hankalinsu ba karamin tashi yayi ba ganin iyayen dakinsu sun rasu musamman malam idi se fadi yake kafin su tafi yace na tabbata motar ba matsala se kuka.




Haka aka kaisu falo Auwal ne yaringa sanarwa da yan uwa Yana kwata -kwata ba ta hayyacin ta se kuka takeyi Amrah ma da taga tana kuka se itama taringa yi.



Suna zaune sai ga Alhaji Jibrin da matarsa idonsa yayi jajawur ya nufi yayan nasa ya fashe da kuka yayi tayi kamar karamin yaro.



Amrah ce taje ta kusa da Auwal tace “uncle su Ammi bacci suke anan suje daki mana?" girgiza kansa yayi sannan yace “bacci suke nan yafi masu dadi ”,



Tayi shiru rungume ta yayi .



___________
*Bayan* *awanni*

Yan Maiduguri sun karaso .


Haka yan uwan su Abbiey da yake Allah yayi wa iyayensu rasuwa ba bata lokacin aka masu
Sutura kowa yana ta zubda kwalla.





Yan uwan Abbiey kowa se fadan kyawawan halin su Ammi sukeyi dukkansu sun samu shaidun kwarai makota kowa seda ya zubda hawaye sunyi babban rashi.




Futowa akai dasu falo za a kaisu gidan su na gaskiya Amrah ce ta rike Alhaji Ali tana fadin“ ina zaku kaimun su Abbiey ?karku tafin mun dasu suna bacci ",



Ya nukura ce takamata ta na sharar kwalla ta rungumeta chan seta fara sambatu tana fadin “Wayyo ko su Ammi sun mutu Nasreen ta ba cewa da yayanta aka daukeshi ta tambaya aka ce mutuwa yayi ”kallon ya nukura tayi tace “Aunty su Ammi ma hakane seta fashe da kuka ”Ya nukura ta girgiza mata kai kowa gurin ya tausaya mata su Aunty summaya ne akan Yana da ta Suma taki fardowa .




A waje aka sallace su sosai suka Samu jamaa tun daga layinsu har titi cike yake da mutane kowa ze budi bakin su kyawawan halinsu yake fada .



Har aka dawo daga kaisu Yana bata farfado ba da kyar aka samu ta farfado haka taringa sambatu tasa mutane da yawa zubda da kwalla .


________
*Bayan* *kwana* *uku*

Yau sadakar uku Anyi addua .


Da yamma lokacin kowa ya watse Alhaji Jibrin yace wa Alhaji Ali yana da magana .

Yace“ toh” sama suka hau harda su Ya nukura ,

Alhaji Jibrin yace “dama naga anyi uku ne inason tafiya da Amrah ”.


Kafin kowa yayi magana Yana tace “wallahi baze yiwu ba ni zan rike Amrah Yaya ta barmun wasiyar in rike mata Amrah ”,



Cikin tsawa “yace naga Yar wana ce ni zan riketa abun da yafi an bar maki wasiya to gwara ma kiji ni zan riketa kome zaayi ”.


Magana ta kaure kamar fada,


Cikin tsawa Alhaji Ali yace“ ke Yana yi mana shiru wannan ba maganar ki bace manya na magana kina sa baki kar in kara jin kinyi magana”.


Sai ya kalli Alhaji Jibrin cikin kwantar da murya yace “kaga dan Allah kayi hakuri Yau akai uku ka bari sai ranar bakwai koda yamma ka tafi da ita ”,



Yace “toh Allah ya kaimu ya dibi iyalansa suka tafi ”.



Suna tafiya Yana taringa masifa ita bazata bayar da Amrah ita zata riketa.


________


*Bayan* *yan* *kwanaki*


Yau akayi sadakar bakwai din sun Abbiey da yamma lokacin mutane da dama sun tafi .



Alhaji jibrin ne yashigo lokacin su kadai ne a falon aka gaisa suna gama gaisawa yace “dama nazo tafiya da Amrah ne "


Ya nukura tace“ to ai sun tafi gidan Yana”.


Cikin masifa yace “baze yiwu ba aii ta
na sane ta dauke yarinyar dan haka yanzu ko a dawo da ita wallahi ko in kai kara ai yar Yayana ce ni zan riketa ”


Alhaji Ali na masa magana an ma kwata-kwata be saurare shi ba ya fice



*MORE* *COMMENT*
*MORE* *TYPING* .....🖋️✍🏻

*_Addeejerh_🥰*
*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI* / *RUBUTAWA*


*BY* *KHADIJA* *ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

Na sadaukar da page din ga daukacin masoyana ko Ina kuke💗✨✨

19~20
Bayan kwana biyu su Ya nukura suna zaune a falo duk ba zu tafi ba akayi knocking ,



Alhaji Ali ne ya tashi ya bude ,



Wani matashi yake tsaye musabaha sukayi “bawan Allah shigo ka zauna duk da bangane ka ba”



Yace “Dama baza ka gane ni ba turo ni akayi ”Ya mika masa wata envelope,



Karba yayi yana masa kallon tuhuma yace “wannan kuma fah ”


Matashin yace “in ka bude zaka ga kome ya masa sallama ya tafi ”.



Alhaji ya koma falo suka fara tambayar shi
Ko lafiya labarta masu yayi ,



Ya nukura tace “bude muji me envelope din ya kunsa”,


Budewa yayi yasa glass dinshi ya fara karantawa cike da fargaba ya mike yana fadin “ni Alhaji jibrin ze wulakanta ya kaimu Kara akan an hanashi yarinyar nan",



Yana tace “Kara kuma? to wallahi bazan bashi ita ba "

Kallonta yayi yace “aa Yana da ya wulakanta mu gwara a bashi yarinyar nan mu ma ringa zuwa ganin ta Bari in kirashi yazo Kawai ya dauketa",


Kuka ta fashe dashi tana kallon Amrah dake cin abinci a dining hankalinta baya gurinsu tana tausaya mata sosai.


_________
*_Bayan_* *_minti_* *_25_*


Se ga Alhaji jibrin ya shigo aka gaisa .



Yana ce ta sauko da kayan Amrah tana jan akwatin idonta se ziryar hawaye yake,



Amrah na biye da ita malam idi aka Kira ya dauki kayan ya kai mota



Amrah tace “Aunty Yana tafiya zamuyi ne”



Rungume ta tayi tace “aa Amrah gidan uncle Jibrin zaki je kinkoma chan zan na zuwa kinji Yar lele na "


Amrah ta kafe ita bazataje gidan ba uncle jibrin ne ya janyo ta jiki ya lallabata ze kai ta shan ice cream ,



Da siyasa aka lallabata haka suka tafi kowa na alhinin tafiyar ta Yana tasha kuka .


___________

Alhaji sannu da zuwa da annashuwar ta tareshi tana ganin Amrah ta chanja fuska ,



Shiga sukayi Arifa naganin Amrah ta ringa tsalle tana murna suka rungume juna .




Arifa tace kindawo gidanmu? Tare zamu na zuwa school? muna zuwa islamiya ko? haka tayi ta jero mata tambayoyi ita dai daga mata kai tayi ,




Mai gadi ne ya shigo da akwatin ta, Arifa uwar rawar kaii ta Kama akwatin zasu ja ita da Amrah,




Mama ce ta harari Arifa tana dungure mata kai “ke dai kinfiye shisshigi banza ”Kawai ta wuce daki ta barsu .




Suna shiga daki zee ta harare su tana fadin a haka zaki kare ,




Basu kulata ba suka je kan gadon suka zauna.



*MORE* *COMMENT*
*MORE* *TYPING* .....✍🏻🖊️


*_Addeejerh🥰_*

*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨



*LABARI* / *RUBUTAWA*


*BY* *KHADIJA* *ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

Na sadaukar da page dinnan ga members din kainuwa💃❤️writers


21~22

*Washegari*

Yau su Ya nukura suka tafi gidajen su Bayan sun sallami yan aikin gidan suka rufe.

________
“Ke Amrah dan ubanki ince kiyi wanke- wanke dan kin raina ni baza kiyi ba ko? tana tsare ta da ido,



Girgiza kai tayi tana kallonta ba tare da tace komai ba,


Kwade tayi tana“ fadin kina kallona da wadan nan idanuwan naki kamar zaki cinyeni”



Amrah taki kulata tashiga kitchen din.


Haka taringa bambamin ta ita kadai.


Tsayawa tayi tana kallon kayan wanke -wanken ta rasa ta Ina zata fara ta bulbula omo kwanukan duk manja haka ta ringa wankewa,

Tana cikin wanke- wanken Arifa tashigo se
Waiwaye take yi tace “Tun dazu naji mama na maki fada naki futowa se yanzu na leko naga ta tashi ”,



Cikin fuskar tausayi Amrah tace “ni bana wanke -wanke”,



Arifa tace“ to ai ko Yaya zee bata aiki yar aiki keyi yanzu mama ta koreta”.



Haka ta Kama mata suka karasa wanke- wanken.


_________
*Da* *yamma*


Su Amrah ne suka futo cikin shirin tafiya islamiya suka tafi.



Ana sauke su zee tayi gaba ta barsu ta shige aji Amrah ta bita Arifa ta wuce ajinsu,



Suna shiga Amrah ta gaishe da malamin da ke ajin ita ko zee ko ajikinta ta wuce buguzun- buguzun,

Malam Yusuf ya daka mata tsawa “ke dan baki da tarbiya ki ganni bazaki gaishe ni ba ki wani je ki zauna zo nan”,



Taso wa tayi tana harare duka ya kaimata “bazaki gaishe ni ba? ”



“Ina wuni ”


“Haka ake gaishe da mutum a tsaye”,




Seda ta haresa durkusawa tayi ta sake gaishesa,



“Tashi koma ki zauna"



Nasreen ce takewa Amrah magana a hankali “nifa Zee dinnan haushi take bani se shegen girman kai ina fatan dai bakya kyaleta in ta maki "



Amrah tace “Ina ma nake kulata balle tamun wani rashin mutunci ai bata samun ido ita take haukan ta” tana dago kanta taga Malam Yusuf ya na harararta.




Dena hirar sukayi aka fara karatu ya karbi hadda.



Zee da kyar ta iya bayar wa har Seda malamin ya Zane ta.



Da aka tashi zasu tafi gida sunzo futa zee ta bangaje ai ko ta shako hijabin ta ...... ✍🏻✍🏻✍🏻


*MORE* *COMMENT*
*MORE* *TYPING* ...... 🖊️✍🏻

*In* *naga* *ruwan* *comment* *Kullum* *zan* *ringa* *posting*, *in*ko* *banga* *comment* *ba* *hakan* *yana* *nunamun littafin* *bai* *maku* *ba* 🙅🏻‍♀️💁‍♀️

*Addeejerh* 🥰
*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI* / *RUBUTAWA*


*BY KHADIJA* *ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

Na sadaukar da page dinnan gareki first love❤️

23~24

Amrah ce zaune a ɗaki ita kadai ta fada duniyar tunani kawai taji an watso mata kaya a fuska,



Cikin fusata ta tashi danganin wane haka zee ta gani ,



“Ke!!! Wai zee wane irin iskanci ne haka, Ina zaune zaki wani watso mun kaya a fuska ?"

Cike da gadara tace“na watso din ki maza ki wanke mun kayan bacci nane”.



Amrah tana nuna ta da yasa tace “wallahi zee ki kiyaye ni bazan wanke din ba gwara ki maza kima kwashe tun kafin in kara fasa maki baki ”




“Au haka kikace to bari inje in fadawa mama ita ai kyaji maganarta ”


Futa tayi,Arifa dake bandaki ce ta futo duk ta saurari abun da ya faru ta zauna gefen Amrah tana fadin “wallahi karki yadda ki wanke ......."


Mama dasu ku shigo tare da zee ta kalli Arifa tace “to munafuka me kike kulla mata?ki kiyaye nifa !yarinyar Sam baki da kishin abunda aka ma yar uwar ki banza”



Ta juya kan Amrah “ke kuma dan baki da mutunci tace ki wanke mata kaya kice bazaki ba”.




Amrah na bude baki zatayi magana ji kake fauuu mama ta mareta kuka tasa ,



Cikin bala'i mama tace “ko zakiyi kukan jini sekin yi wankin nan maza kwashe kayan nan .”



Jekin ta na rawa ta debi kayan ta na kaiwa bakin toilet tace Allah ya isa na ! tayi maza ta fada toilet din tare da sa key,

Mama se bala'i take tana bubbuga kofar amma taki budewa ,



“Zaki futo ne ja'ira ni kikayi wa Allah ya isa”



A fusace ta bar dakin .


__________

*_Bayan_* *_wata_* *_biyu_*

Hajiya Sa'a ce suke zaune gaba dayansu a falo ta kalli Alhaji “ wai Alhaji yaushe zamu koma gidan chan ne? na fara gajiya da wannan gidan "



”Haba saa ta ai munkusa komawa karki damu nan da kwana biyar mun koma ni Ina ja'irar yarinyar nan ne ?",



“Tana kitchen dafawa umar indomie take ",



Futowa tayi ta Mika wa hakimin yana zaune indomie din karba yayi yana kallonta irin ( you don't have sense) yace “ke a garin ku haka ake dafa indomie kin tsuga mata ruwa banza baki iya komai ba",




“To ai tun farko seda nace
Ban iya dafawa ba akace sena dafa tana murguda masa baki".



Alhaji yace “ kaji ja'irar yarinya wuce ki sake dafa mashi wata kuma ki sake yin irin ta yanzu ki gani",



“Alhaji rabu da ita ne tama yi”



Sum sum takoma kitchen din.

________
*_Bayan_* *_kwana_* *_biyar_*


Zee ce ta fada kan gujera tana fadin “Kai kuga wannan gidan da muna wanchan gida ga Wanda ya fishi ”




Hajiya saa se zagaye take tana guda ta je gurin Alhaji tana “fadin nima yanzu zan ci kudi in ture Ina dagawa",


“In koma hajiya sama hajiya kasa ”ta kyalkyala ɗariya



Alhaji jibrin yace kwarai kuwa..........✍🏻✍🏻✍🏻




*MORE* *COMMENT*
*MORE* *TYPING.....✍🏻🖊️*



*_Afwan_* *_pls_🙏🏻* *_za_* *_kuji_* *_ni_* *_shiru_* *_banyi_* *_posting_* *_da_* *_wuri_* *_ba_* *_jiya_* *_mun_* *_wuni_* _a_ *asibiti* *mama* *ba* *_lpy_* *_har_* *_ruwa_* *_aka_* *_kara_* *_mata_* *yau* *_kuma_* *_bansamu_* *_tym_* *din* *yin* *_typing_* *_ba👏🏻_*




*_Addeejerh❤️

*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI /* *RUBUTAWA*


*BY* *KHADIJA* *ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*_Special_* *_thanks_* *_to_*

Ummu afaf
Ummu Muhammad
Princess👸
My zakara
Sweet
Ummu manal
Beauty
Khadija sulaiman garba@

Da ma sauran Wanda ban samu fada ba👏🏻❤️



25~26


Amrah ce adaki se sauri ta ke ta shirya ta kusa yin letti dalilin wanke-wanken da tayi ,



Futowa tayi daga dakin ta dake k'asa daya zama nata sabanin nada da yake sama,




Tana futowa ta tarar har sun gama breakfast tanajin yunwa haka ta hakura saboda Mama tace indai ta tsaya cin abinci tafiya zasuyi subar ta kuma sedai ta hakura da zuwa,



Ta ga gwara ta je makarantar tafi jin dadi.


__________



“Ke Amrah baki ga yadda kika rame bane duk idanuwan ki sun fad'a ”




“Ba dole in ringa ramewa ba Nasreen kinsan kullum Mama cikin kuntata mun take"



“Yau ma kinga badan yanzu naci abincin ki da haka zan zauna ko breakfast banyi ba ,kinga tun da ta fuskanci banson indomie inta sandare shine ta hadoni da ita "



Nasreen ta kama baki “wallahi Amrah kina bani tausayi Sam Mama bata da imani.....bata karasa ba zee tashigo tana fadin ”ana halin munafukai ,kuma ke Nasreen tana nuna ta da yatsa uwar ta wa kike cewa bata da imani?"




“Ke Zee ko wa kike karki kuskura ki nuna ni da yatsa in ba haka in balle yatsar in ga Wanda ze tsaya maki”



“An nuna din ki yi abunda zakiyi"



“Nasreen har taje kamar zata zauna ta tsinto Zee nacewa"



“Banza kinji tsoro
In ba........dumm Nasreen ta kwada ta ak'asa suka rufe ta da duka wata yar ajin su ta shigo taga me ke faruwa gashi tana tsoron su Amrah ballantana ta rabasu,



Da gudu ta futa takira wani Malami dakyar aka raba su ,



Wuce wa yayi dasu Office din principal Zee se kuka take kawarta na rarrashinta tana zugata karta yarda,



Zane su akayi,



Suna futowa Amrah tace ”wallahi basu isa sun dake ni a banza ba kawo kunnen ki kiji ....kyalkyalewa tayi da dariya suna tafawa,



Nasreen tace “bestie akwai ki da tunani haka za'ayi”

__________


“Kefa yarinyar nan mutum ya saki aiki kik'i yi Dan kin raina mutane”



“Mama fah na wanke"



“Dan uwarki a hakane kin wanke kodai kin sheka ruwa kinyi buja -buja da kika saba",



Kasa kasa tace “ badai tawa ba"


Kwade bakin ta tayi ni kikewa 'kunkuni maza jeki sharewa umar daki saura kiyi mara kyau gashinan kinyi...........




*MORE* *COMMENT*
*MORE* *TYPING........✍🏻🖊️*



_Kuyi_ _manage_ _pls👏🏻👏🏻_ _inason_ _Kara_ _yawan_ _page_ _din_ _Amma_ _naga_ _baze_ _yiwu_ _ba_ _sedai_ _zan_ _ringa_ _posting_ _biyu_ a _rana_ in _naga_ _ruwan_ _comment_ _inko_ _bangani_ _ba_ _sau_ _daya_ _zannayi_ .




*_Addeejerh* ❤️_
*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI* / *RUBUTAWA*


*BY* *KHADIJA* *ADAM* *IDRIS*


*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

Na sadaukar da page dinnan gareku yan uwa na Khadija Adam idris da rukayya Adam idris ❤️ni cikon triplets din ku na miko gaisuwa ta 👏🏻

27-28


Suna dawowa suka tarar da su mama a falo da sauri ta tashi tana fadin ke Zee me yafaru naga idanuwan ki sunyi ja? Fuskarki ta kumbura? Cike ta shagwaba tace “ba Amrah bace daga na masu magana kuma maganarki naji suna yi shine ita da kawarta Nasreen suka mun duka, “shine suka maki haka zasu illata mun ke"shako Amrah tayi ta ringa dukanta da wayar charger ta na kuka tana Allah ya isa na bakinta ya ki mutuwa,



“Shegiyar yarinyar ku sake taba mun yarinya ku gani ,kuma wuce ki dauko tsintsiya ki je yau ke zaki share compound dinnan ko zaki mutu”



Murguda mata baki tayi “se ki jira in cire uniform inyi sallah ko ? “Ko me zakice se kinyi abun da na saki mara kunya



Arifa ta kama hannun ta taho muje daki , Mama tace “ kedai yarinyar nan Sam baki da hankali anayi wa uwarki rashin kunya sunyi wa yayar ki duka baki damu ba”,


Arifa a hankali tace“ yi hakuri mama".


Wucewa sukai suka barta .


Hannun zee taja suka hau sama ta gasa mata jiki.

___________


Amrah! Amrah ! Amrah firgigit ta tashi dafe goshinta tayi tana fadin Kai mama ta fiye masifa dan ba Wanda ze kirani haka se ita ji tayi an cigaba da kiranta tashi tayi ta futo mama ta gani a tsaye rike da kugu ,“ina kiranki dan kin raina mutane baza ki amsa ba? Amrah tace “bacci fah nakeyi"!,


Inyeeh “kenan ga yar hutu ko to wuce ki je kiyi wanke -wanke ”


Amrah tace“ wlh nina gaji nayi sharan compound bazan iya ba ...... bata karasa ba mama ta dauketa da mari tass......



Assalamu alaikum akayi sallama haba Sa'a “me wannan yarinyar ta maki zaki mareta marainiyar Allah kina cin zalin ta" muryar da Amrah taji ne yasa taje ta rungumeta tana kuka tace Aunty Yana kwana biyu nayi missing naki ..... Anci zalin nata ta mun rashin kunya ,



danta maki rashin kunya seki mare ta baki san yaro bane,



Kallon Amrah tayi tace “Rabin raina me yasa kika mata rashin kunya?"


“ Allah aunty ban mata rashin kunya ba cewa tayi inyi wanke-wanke gashi ta sani sharar compound dazu shine fah nace na gaji seta mare ni "ta Kara fashewa da kuka,



Yana ta gigiza Kai kawai tayi ta ja hannunta suka shige daki ,


Zama tayi a falon ta dora kafa daya kan daya tana raunar cingum kass kass.




*5* *YEARS* *LATER*



“Amrah dan Allah ki tashi muje clinic ki karbi magani cikin na ciwo amma kinki zuwa",



Dagowa tayi a 'jikace tace “Nasreen bazan iya zuwa ba ko tashi bazan iyayi ba gashi an tashi kawai zan tafi

1 Comments On FANSAN RAN MAHAIFANA
avatar
khadija-1-2-5

9 months ago

Reply

Tnx

Please Login or Register in order to submit comment