Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya dudduba hannu ya kalleshi yace “Karka damu targade ta dan samu yanzu zan bata wani Pain reliever da wani cream,



“Ok Doctor yanzu ni ban futo da kudi ba" ya shafa sumar sa yace “ka hada kawai cikin bills in Abba ya dawo ya baka".



Dr yayi murmushi “kaji ka da wani zance ni base an biya komai ba ai an riga an zama daya,



Yace “Toh Dr mungode Allah sa afi haka"Dr ya amsa da “Amin" musabaha su kayi suka fuce ita dai Amrah kanta na kasa saboda tunda Dr ya shigo ya kura mata ido ta sunkuyar da kanta.



Futowa sukayi daga Asibitin tunda suka hau titi ya ke ta janta da hira Sai dai ta amsa masa E'h ko A'a.



A k'ofar wani tsanfatsetsen gida yayi horn Maigadi ya bude masa ya masa Sannu da zuwa.


Ya zura hannunshi a aljihu kudi ya zaro ya Mika masa yana “Fadin Baba ga wanna ba yawa ayi cefane",


Ya ke hakoransa yayi duk sun dafe da goro hannu biyu ya karba yace “Mai yawan kenan dan nan Allah yi albarka , Allah baka mata ta gari".


Ya amsa “Amin Amin Baba"ya wuce parking space parking yayi murmushi yayi yace “To futo mun karaso sai na cewa Mommah kina tsoron kar danta ya fille maki kai" dariya tayi yace “Ko kefa Amma da kinyi zugum ba annuri”,


“Futo mushiga ciki”.


Falo suka Karasa yayi knocking daga ciki aka ce “Come in".


Yayi gaba tabishi a baya bakinsa dauke da sallama ya shiga wata mata ta amsa fuskar ta dauke da murmushi tace “Oyoyo Babana" zuwa yayi ya zauna akusa da ita a kasa ya dora kanshi a cinyar ta yace “First love na same ku lafiya",


Mommah tace “Lafiya kalau” tana shafa kansa.


Ta kalli Amrah tace “Yammata karaso rabu da wannan shagwababen yaron" ta k'arasa maganar tana dariya ya
hade rai.



Murmushi tayi ta zauna a kasa tace “Ina wuni”,


Ta amsa “lafiya kalau Yan Mata ya sunanki?"


A hankali tace “Amrah!",


Mommah tayi murmushi “Suna Mai dadi Masha Allah!",

Mommah ta kalle shi yasan Karin bayani take nema ,


Bayani ya Mata .


Cike da tausayi ta rungumo ta jikin ta tace “Allah sarki bari nakira Nafisa ta kaita dakin su tayi wanka taci abinci nan da kwana biyu sai aje a dubo in Auntyn nata ta dawo",



Nafisa!!Nafisa!! da sauri ta Amsa kiran daga daki da sauri ta futo tace “Gani mommah"


Mommah tace “Ga Yar uwa nan Sunan ta Amrah kikai ta tayi wanka ki kula da ita",


Nafisa tace “To Mommah" da murmushin ta tace “Sannu sister Amrah ta mayar mata itama da murmushi tace “Yauwa" Kama hannun ta tayi suka nufi daki.


Seda yaga sun kusa barin falon yace “Nafisa ko ki lura da ni ko?"


Juyowa tayi da sauri tace “Sorry big bro ban kula ba"

Ya dan harareta yace ”Dama ina zaki kulani kinyi kawa" Yana murmushi Wanda ya zame masa jiki,


Dariya tayi suka shige daki......✍🏻✍🏻✍🏻




*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* .....✍🏻🖊️




*_Addeejerh❤️_*


*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI/RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*



Na sadaukar da page dinnan gareka My favorite brother Yaya Halifa🤍❤️

________


44~45

Suna zaune a dining da daddare Mommah tace “Auta je ki Kira mun wadan chan yaran a daki suzo suci abinci Kuma Nafisa tasan banson aci abinci a kwata".


Auta ta Mike tace “Toh" da gudu ta shiga dakinsu.



Baram ta fada tsawar da Nafisa ta daka mata ta dawo nutsuwar ta tace “Wai ke Auta kullum kina girma kina cin kasa kin wani fadowa mutane ko sallama?" Amrah ta fada duniyar tunani (haka itama fa tayi rayuwa kenan),


Kama kunnenta tayi tace “Kiyi hakuri Yaya Nafisa",


Nafisa tace “Shikenan meya faru?”


”Dama Mommah ce tace kuzo kuyi dinner".


“Ok gamunan zuwa"

Ta futa su ka mara mata baya.


Suna zama Amrah tace “Barka da dare Mommah",


“Yauwa Amrah"


Shiru sukayi Wanda Al'adar gidan ne basa magana in ana cin abinci.


Suna gamawa Mommah tace “Ammar gobe ina ga ka sake zuwa inda ka same ta ko Auntyn ta sun dawo",


Murmushi yayi yace “To Allah kaimu".


Mommah ta Mike tace “Amrah zo muje daki na zamuyi magana",


Cike da ladabi tace “To ta mara mata baya"


Suna shiga Mommah ta zauna a bakin gado,



Zata zauna a kasa Mommah tace “A'a Amrah hau sama",


Amrah ta girgiza kanta tace “Mommah ki barshi".


Mommah ta hade rai ganin haka ta hau ta zauna,


Mommah tayi murmushi tace ya
“Yauwa ko ke fa tayi shiru Sannan tace “Amrah"


Amrah ta dago ta kalleta Mommah tace “Ina ta so dama in tambaye ki nake ganin karna takura maki",



Amrah ta sunkuyar da kanta tace “Bakomai wallahi mommah",


Mommah tace “Yauwa inaso inji labarin me sanadiyar barin ki gida ?".


Amrah tayi kwalkwal da ido Mommah tace “Ba kuka fa nace ki mun ba",



Labari Amrah ta fara bata tun asali ,


tana gama bata labarin ta fashe da kuka.


Mommah ta rungumo ta tana rarrashi a ranta ta mamakin da ma ana samun mutane irin haka kuwa,



Rarrashin ta tayi tace “ki hakuri nan gaba ze zama labari......."


_________


Su uku zaune a falo Mama ta gyara zama ta dubi Alhaji tace “Alhaji kaga yarinyar nan har yanzu Bata dawo ba",


Alhaji cike da mamaki yace “Amma ta yaya akayi haka ta faru?"


Kafin Mama tayi magana Umar yayi karaf ransa a bace yace “Bawani kawai kedai kin koreta ne daga nace ina sonta to nidai ina sonta sai na Aureta!!!"


A fusace Alhaji ya mike tsaye ya daka masa tsawa tana fadin “Baka da kunya Mahaifiyar ka kake fadawa haka?".


Tsaki Umar yaja ya fuce batare da yace komai ba........✍🏻✍🏻



*Zakuji ni kwan biyu shiru bisa rashin chaji da bani dashi* 👏🏻👏🏻



*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* .....✍🏻🖊️




*_Addeejerh_* ❤️


*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI/RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


46~47


Amrah na futowa daga kitchen zata shiga dakin Mommah taji tayi karo mutum tana dagowa taga wane Ya Ammar ne da sauri ta dukar da Kai tana fadin “Y hakuri Yaya".


Yayi murmushi yace “Bakomai Amma kina kula in kina tafiya”.


Amrah tace “Toh".


“Yauwa in kun gama girkin ku mun magana zan dan futa", ta Amsa “to"da sallama ta shiga dakin Mommah.


__________

Tafe take tana karatun Qur'ani cikin zazzakar muryarta ta k'arasa gurin Mai gadi ta Mika flask din da ke hannunta tana fadin “Malam Hamza ga abinci ka".


Yayi murmushi yace “Nagode Allah maki Albarka".


Amrah ta masa Murmushi tace “Amin Nogode" ta juya ta tafi.


Tana zuwa kofar dakin su sukayi kicibis da Nafisa.


Nafisa tayi( baby face) Kamar zatayi kuka hakan da tayi ya bawa Amrah dariya Nafisa tayi Murmushi tana Kai mata duka da sauri Amrah ta kauce .


Nafisa ta kalleta tace “Wai ina kikaje ne banganki ba?"


Amrah tace “Wallahi na kaiwa Malam Hamza Abinci ne".


Nafisa tace “Bari na Kira Big bro yazo an gama Abinci".


Amrah tace “Ok bari nayi wa Mommah magana".


Gaba daya kowa ya hallara Mommah ta zauna chan ta fara cin abinci ta kalli Nafisa tace “Wai ina Auta ne?"



Nafisa ta dago tace “Mommah kinsan dai k'asar yar ki tana chan tana baccin da ta Saba na mutawa!" ta na kunshe dariyar da tazo mata.



Mommah tace “Nafisa kinci kaniyar ki Autar ce kasa kuma ayy bacci ma lafiya"


Nafisa ba tace komai ba ta cigaba da cin abinci ko ina tsit sai karar TV dake ta aiki.


Bayan sun gama cin abinci suka dunguma zuwa falo.


Ammar ya dora kansa akan cinyar Mommah Nafisa ta hade rai tayi kicin da fuska tace “Mommah ki kalle shi babba dashi ta kwanta a cinyar".


Mommah ta dan harareta tana fadin “Ina ruwanvki ya kwanta din".


Nafisa ta fara bubbuga kafa cike da shagwaba tace “Dama ai Mommah kinfi sonsa komai baban ki"


Amrah ta kyalkyale da dariya ita dai familyn na burgeta Amar ya harare to irin(if I catch you)Ta sake shekewa da dariya .


Mommah ta kalleta tayi Murmushi harga Allah ita dai yarinyar ta shiga ranta.


Ammar yace “Yauwa Mommah kinga wajen sati kenan Ina zuwa gidan Aunty nata Amma basu dawo ba".


Mommah tace “To!! ikon Allah" ta kalli Amrah da tayi kwalkwal da ido tace zo nan yata tashi tayi Ta zauna kusa da Mommah, rungume taMommah tayi tana shafa bayan .


Ammar yana bala'in tausayin ta tunda yaji labarinta.


Mommah tace “Yanzu gashi ke baki da Number ta ?".


A hankali Amrah tace “E'h".


_________


Zee tace “Mama wa ya sani ma yarinyar ko yawan ta zubar ta tafi wajen sati fa kenan aikin banza,shegiya ta tafi ta bar mutane da aiki ga kayan wanki na sun taru"ta karasa tana tura baki.



Mama ta kalleta tace “Wallahi ba abun mamaki bane ko yawan karuwanci ta tafi........✍🏻🖊️



*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* .......✍🏻✍🏻



*_Addeejerh_* ❤️


*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI/RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


48~49
______________


Amrah ce a kitchen tana yankan Alaiyahu tana cikin yankawane ta yanke Dan yatsanta ,Da sauri ta saki wukar hannunta tana yarfe hannun ta kwalla Kara.



Tundaga bakin kofar shigowa Ya Ammar da shigowarsa kenan ya jiyo karar Amrah da sauri ya karasa cikin kitchen din dan ganin me yake faruwa.


Ohh shit abinda ya Ammar ya fada ganin meya faru tsugunnawa yayi a gabanta.



Cikin yanayin damuwa ya kalli fuskar Amrah wacce hawaye ke ambaliya a fuskar ta yace “wukar tayi kaifi sosai koh?".


Cije lebe kawai Amrah take dan baza ta iya magana ba dan zafin har cikin kwanyarta takeji.



Ganin yadda jinin ke zuba yayi maza ya lumshe lulu(eyes) idanuwansa kamar mejin bacci tsikar jikinsa na tashi.


Mommah ta nufe su tana fadin “Ihun me naji ne haka?"turus tayi ganin meya faru .


Ya Ammar yace “Wallahi yankewa tayi bari muje ayi treatment" futa sukayi daga kitchen suka nufi dakin Mommah.



Yana sa mata spirit ta fara kuka tana shiii shiii Nafisa da shigowar ta kenan ta kyalkyale da dariya tana tafa hannu tace “Waya ga su Amrah in anzo haihuwa” ta sake shekewa da dariya, dada tunzura Amrah tayi.


Mommah ta harare Nafisa tace “Ba gwara ita ba in kece sekin cikawa mutane gida".


Ya Ammar yace “Mommah rabu da ita"


Mommah ta kalli Ammar tace “Inaso zaka Kai su shopping anjima in ba abun da zakayi Nafisa ta ishe ni kayan shafe shafen ta sun kare ".



Murmushi yayi yace “Mommah na (your command is My wish) se muje din".



Mommah ta shafa kansa tace “Babana Allah baka Mata ta gari Allah baka masu ma biyayya yadda kake mana".



Sun kuyar da kansa yayi ya Amsa da “Amin".



Ze futa yace “Ku shirya nanda 30 minutes".



Juyi Nafisa tayi tana Murna tace “Karka damu Yaya yanzu kuwa".


Murmushi yayi ya fuce.


Mommah ta kallesu tace “Kuje ku shirya kinsan shi baya son jira".


Da sauri Nafisa ta kamo Amrah tana fadin “Taso muyi sauri"suka fuce Mommah tayi Murmushi.


Suna Sallar la'asar suka tafi a kofar Jifatu suka yi parking Nafisa an fente fuska Amrah ko powder da lipstick.



Ammar ya kalle su yace “Ku fara shiga ganinan zuwa".


Nafisa jikin ta na rawa ta dauki basket ta nufi wajen cosmetic komai ta ringa diba tana gamawa ta nufi gurin kayan zaki inda tafi karfi Amrah dai ba tayi wani tsince tsince ba.



Ammar ya k'arasa gurinsu yana fadin “kun sani sai zagaye nakeyi".



Basket din Nafisa ya kalla cikin fada yace “Ke wai Nafisa kunnen kashi gareki ne da ke an hana ki shan zaki sai kace baki san il'larsa ba ne".


Nafisa tace “Sorry Yaya"


Ammar ya hade rai yace “Gerrout Malama yi maza ki rage tun kafin na sassaba maki" .


Jikin Nafisa na bari ta fara ragewa tana chuno baki.


Cike da kulawa ya kalli Amrah yana nuna basket din yace “Haba Amrah wanna me kika diba oyahh dibi abinda kike so ", janta yayi gurin dogayen riguna ya ringa dibar mata Kamar ba gobe Nafisa se kumbure kumbure take yi.



Bestie Bestie!!!! Muryar da Amrah taji ne ya sata juyo wa da murnarta tace “Nasreeeen!!!!!!!.........✍🏻🖊️



_*Kuyi manage pls 👏🏻👏🏻tun safe kaina ke ciwo shiyasa kuka jini shiru luv u all*_❤️🤍




*MORE COMMENT*
*MORE TYPING......* ✍🏻✍🏻




*_Addeejerh_* ❤️


*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨



*LABARI/RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


50

Nasreen ta taho a guje ta rungume Amrah tare da fashewa da kuka ta ce "Amrah Ina kika shiga ne naje Gidan Uncle Mama ta dinga masifa tana faɗin a jiyarki na bata, kina can kin tafi yawon karuwancinki da kika saba, ta min korar kare raina a ɓace na bar gidan".
Cikin kuka Amrah ta ce; "uhm ke dai bari labarin na da tsaho ba zai yiwu a nan ba sai an zauna ".



su dai su Nafisa suna tsaye suna kallon Ikon Allah ba ƙaramin tausaya masu su kayi ba.



A bangare Ammar ya rasa meyasa kullum in Amrah na kuka hankalinsa yake tashi domin jin kukan nata yake tamkar ana sa masa rushen wuta a zuciyarsa .



Suka saki juna suna kallon juna Nasreen tana Murmushi ta ce; "Amrah kin ganki kuwa kinyi kyau kin murmure abinki gwanin sha'awa".



Amrah ta ce; "haba dai zolayata dai kike?".



Nasreen ta Kama baki tana fadin "Hala bakya kallon kanki a mudubi ? Allah ba wani zolaya gaskiya nake faɗa maki"



Murmushi Amrah tayi kawai bata ce da ita komai ba.



Nasreen ta ce “Bestie har yanzu kina miskilanci nan naki?",kafin Amrah ta bata Amsa Ammar ya kallesu yana murmushi yace; "kun gama kukan kun dasa hira kun shanya mu ko oho kun ma manta da mu yana ware hannayensa".




Sai a lokacin Nasreen ma ta lura dasu tayi murmushi ta ce; "Kayi haƙuri haka muke in mun haɗu ina wuninku?" ta karasa maganar tare da yin hugging din Nafisa "ƴar uwa yi haƙuri murnar ganin Amrah ne yasa sam ban kula da ku ba",



"Haba karki damu ba komai Ammar ya kalle Amrah yana murmushi har sai da dimples din sa suka lotsa ya shafa sumar kansa kafin daga bisani ya ce; "Ya kamata kuyi sauri ku gama muje na sauke ku a gida dan a kwai inda zanje".



Nasreen tayi kwakwal da ido kamar za tayi kuka ta ce; "haba dan Allah daga zuwanku?"



Dukansu suka sa mata dariya idan ka cire Amrah da Murmushi kawai tayi Ammar ya kalli Nasreen yace; “bafa gida mukazo ba ko kin manta ne?".




Nasreen ta kalli Amrah ta ce "Bestie na manta na fada maki nayi waya Yaya Hayatuddeen ya siya mun", Amrah ta ce; "kai gaskiya nayi farin ciki sosai wallahi na tayaki murna".



Amrah ta kai dubanta wajan Nafisa ta ce; "Dan Allah Nafisa ara min wayar ki in karbi number ta".



Nafisa ta ciro wayar daga cikin jaka ta mika mata sukayi exchanging contact.



Nasreen ta ce; "Bestie kema ya kamata kiyi waya fah".



Amrah tayi murmushi kafin daga bisani ta ce; "Insha Allah zanyi komai lokaci ne".



Zuwa sukayi suka biya kudin inda Ammar ya biyawa Nasreen godiya ta masa.



Suka fuce a boot aka sa kayan .


Amrah da Nasreen kamar karsu rabu.



Tunda suka hau titi Nafisa ta ishe su da surutu Ammar ya juyo ya dalla mata harara ya ce "Kedai bakin ki baya taba shiru", Nafisa tayi tsit kuwa da bakin ta.



A kofar wani shago yayi parking ya ce; " ku jirani na fito".




Bayan yan Mintuna ya dawo hannun shi rike da leda ya mikawa Amrah yace; "karbi".



ta zuba masa idanu ba tare da ta karba ba har sai da ya sake magana "ki karba ki gani Mana".


Hannu biyu tasa ta karba .


Tana bude ledar Abun da ta gani ne ya sata saurin dagowa kallonshi tayi .



Murmushi kawai yayi Amrah sai zuba masa godiya take har sai da yace ya isa hakan.



Nafisa ta karbe ledar tana fadin "Mene ne a cikin ledar in gani naji sai zuba godiya kike",



tana budewa kwalin waya ta gani ta kwalla Kara su Amrah sukayi saurin toshe kunnen su tace "Ohhh My God! iPhone 11 pro..........✍🏻🖊️



*Nagode sosai naga Adduoinku Naji sauki Nagode da kulawarku Allah bar kauna Amin* 👏🏻❤️🥰




*MORE COMMENT*
*MORE TYPING.......* ✍🏻✍🏻







*_Addeejerh_* ❤️

*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI /RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


51~52

Ammar yayi saurin yin parking ya juyo ya kalli Nafisa yace; “baki da hankali ne zaki fasa wa mutane dodon kunne?".



Ta marairaice fuska tace; “Sorry Yaya duk murna ne yasa hakan".



Mtsww ya ja tsaki ya fara tuki ita dai Amrah Murmushi tayi tana Mamakin yadda in suna tare basa shiri Sam.



A kofar gate yiyi horn lokacin a na Kiran Sallar Magariba da sauri Mai gadi ya bude masu.



Yana parking ya bude ma su boot ya kalli Nafisa ya ce; “In kun kwashe kayan ku tabbata kun rufe motar zanje Masallaci inyi sallah", ya Mika Mata mukullin Motar.



Su ka kwashe kayan suna shiga falo ba kowa Auta ta tafi hutu da tunda daga waje za'a ji hayaniyar ta tana kallo



Direct daki suka wuce daki domin yin sallah kar su makara.



Amrah ce ta fara shiga tana futowa ta shimfida sallaya tasa himar din ta ,ta tada sallah tana idarwa ta daga hannunta sama tana Adduoi bata San lokacin da hawaye ya fara ambaliya daga idonta ba se dataji dumi a kumatun ta, ta shafa Adduar ta mike.



Ta kalli Nafisa Wanda tun da Amrah ta fara addua take kallon ta.



Da sauri Amrah ta goge hawayen da ya zubo mata ta yi saurin wayancewa tana murmushi ta mikawa Nafisa himar din ta ce; “maza tashi kiyi sallah muje gurin Mommah".



Bayan ta idar suka nufi dakin Mommah ta zaune akan sallaya tana lazimi suka jira ta gama .



Kallon su tayi tana Murmushi ta ce; “Yan mata na kundawo?".



Murmushi su ma sukayi tare suka ce “Eh".



Ta ce; “To Ina yayan naku kun tafi kun barni ni kadai ga Auta ma bata nan me deben kewa".



Nafisa tayi dariya ta ce; “Mommah kodai tsoro kike ji ne ......"



Da sauri Mommah ta Kai mata duka tana fadin “Kaniyar ki Nafisa naga Aamun kin maida ni kakarki".



Amrah tayi dariya ta mike,ta ce; “Ina zuwa".



Dakin su ta nufa ta kwaso kayan da suka shigo dasu.


Tana gamawa ta ce; “Mommah ga kayan da Yaya ya sai Mana,ya sai mun waya ma ta mika mata kwallin karba Mommah tayi tace toh Allah saka mungode Allah Kara budi,
Ina fatan kin masa godiya?"Amrah ta daga kanta tace “E'h".



Mommah ta ce; Yauwa se asa chaji ........ knocking akayi Mommah ta ce; “Yes come in shigowa yayi bakinsa dauke da sallama Mommah ta sakar masa murmushi zuwa yayi ya zauna a kasa kusa da Mommah ta shafa kansa ta ce; “Sannu da dawowa Babana naga abubawan Alheri da Kayi Allah ma Albarka Allah Kara budi.



Ya Amsa da Amin Amin first luv.



Ta kalli Amrah ta ce; “Yata je ki kawo masa Abinci ".


Amrah tace to ta mike ta fuce.


Harta futa yana kallonta Mommah tana kule da shi tayi Murmushin su irin na manya.



Mommah tace Babana dawowa yayi nutsuwar sa ya shafa kansa Yana kallon ta ya ce; “Na'am" Mommah ta ce; “yau favorite din ka nayi".


Rungume ta yayi ya ce; “that's why I love u Allah bar mun ke Allah Kara nisan kwana ".



“Amin Babana" Mommah ta amsa ta bashi peak a kumatu Murmushi yayi .


Se a lokacin ya kula da Nafisa da ta turo baki gaba ya ce; “Mommah ita kuma wannan fa ?"



Mommah tayi murmushi ta ce; “kishi take da Kai".



Yayi dariya ya ce; “Aikam tana ruwa".


Dariyar da yayi ya dada tunzura Nafisa aguje ta bar dakin.......


______
*_Washegari_*

Arifa ce ta futo duk ta zuge ta rame ta shiga dakin Mommah da sallama.



Mommah na ganinta ta ce; “Ina zuwa anjima zan kira" kit ta kashe call din



Ta kalli Arifa tayi tsaki ta ce; “Aikin banza kin wani
tada hankalin ki akan wanchar karuwar".



Da sauri Arifa ta ce; “Auzubillahi minar shaidanun rajim".


Tassss Mama ta dauke ta da mari tana fadin “Nice shedaniyar dan na taba kanwar uwar ki ko?", da sauri Arifa ta girgiza kanta tana kuka.


Tsawa Mama ta daka wadda ta rudar da Arifa ta ce; futa ki bani guri sum sum ta fuce....


___________

Mommah da Amrah se Ammar da be Dade da dawowa ba zaune a falo , Amrah tayi shiru mommah ta kalleta ta ce; “Amrah kodai kina tunanin gida ne ?".


Girgiza kai Amrah tayi kana ta ce; “Mommah wlh ina tunanin zuwana gidannan , kinga mama zata iya had'amin wata gwaramar a gurin uncle ".
Ammar dake gefe yanajin zuciyar shi babu dad'i ,yadubi Amrah da tayi kalar tausayi alamun tana Cikin damuwa ya ce; “Meyasa kikeson tafiya ki barmu?".


Amrah ce tafashe da wani matsanancin kuka ta ce; “ba haka bane narasa ya zanyi da rayuwata,babu su Ammi " cikin she'shek'ar kuka take maganar Mommah ba karamin tausaya mata tayi ba,Ammar kuwa seda ya share hawayen da bai san lokacin da suka fito daga idanunshi ba suka gangaro kumatunshi ba.


Mommah ce tadubi Amrah kana ta ce; “Lokaci d'aya iyayen 'naki suka rasu ?".



Amrah da kejin mutuwar tadawo mata sabuwa yanzu ta ce; “Motar suce tayi hatsari kwanaki ma Ina gyaran dakin uncle naga wasu zobuna guda biyu nawa da na Abiey acikin wata maajiyar Abiey din".



Ammar ne ya nisa kana ya ce; "wanan maganar ta Amrah abin dubawa ce".



Mommah da takasa magana tanajin son Amrah har cikin zuciyar ta ta ce; yanzu dai gobe se a maida ki gidan uncle din naki da yamma".



Amrah tayi saurin girgiza kanta kana ta ce; “A'a Mommah nidai bazan koma ba " ta karashe maganar cikin kuka.


Mommah ta rungumo ta ta ce; “karki damu ba abunda zai faru zamu na zuwa kinji",haka Mommah ta ringa lallashin ta.............✍🏻🖊️




_Nagode da adduar ku👏🏻👏🏻 masoyana na fara jin sauki see abunda baa_ _rasa ba_ .




*MORE COMMENT*
*MORE TYPING......* ✍🏻✍🏻




*_Addeejerh_* ❤️



*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨



*LABARI/RUBUTAWA*



*BY KHADIJA ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


53~54


Washegari da safe wajen karfe bakwai Amrah da Nafisa ne a kitchen suna hada breakfast Nafisa ta shagwabe fuska tace; “Yanzu Amrah tafiya za kiyi ki barmu ?".



Amrah tayi fuskar tausayi tace; “To ya za muyi kar ki damu zamu na yin waya ai ko?" Tayi maganar tana murmushi Nafisa ta rungumeta tana shafa bayanta ta ce; "hakane" Amrah tayi mata wani murmurshi wanda yafi kuka ciwo.



Suna jera breakfast din a Dining Mommah ta futo karasawa gurin su tayi tana faɗin "Har kun gama hada break din?", Amrah ta kalli Mommah son Matar na kara ruruwa a cikin zuciyarta cike da damuwa Kamar zatayi kuka ta ce; "Mommah yanzu tafiya zanyi?"
ta karasa maganar cikin muryar kuka,



Mommah ta rungumota jikinta tana bubbaga bayanta alamar lallashi "karki damu yata bana ce

1 Comments On FANSAN RAN MAHAIFANA
avatar
khadija-1-2-5

9 months ago

Reply

Tnx

Please Login or Register in order to submit comment