Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba sai nayi shawara tukun".



Dariya yaɗan yi kaɗan yace "To shikenan bazan matsa miki ba kinji Sweetheart? Kiyi shawara dakyau amma kar ya wuce gobe coz Kar ki saka zuciyata ta tarwatse".



Murmushi ita dai tayi bata ce komai ba.



"Byee Sweetheart ki kula da kanki".


Daga nan ya kashe kiran


Murmushi ya ziyarci fuskarta ........🖊️✍🏻






*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* ......✍🏻✍🏻





*Addeejerh* ❤️


👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI/RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM IDRIS*
( *shalelen kainuwa* ❤️)
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*


66~67

Arifa cike da tsokana ta kalli Amrah da keta Murmushi ta ce “Wai Yaya Amrah ya naga tun dazu sai wani murmushi kike yi ko kinsamo mana uncle har yayi nasarar sace zuciyarki ne?".




Amrah ta kaimata duka tayi maza ta kauce har tana wantsulawa ƙasa daga saman gado tana Murmushi.




Amrah ta ce “Ni bani da wani Saurayi mara kunya kawai .



Arifa ta kyalkyale da dariya ta ce “Gashinan alamu ma baki da gaskiya in tayi tsami dai maji" ta fice daga dakin da gudu tana dariya.




*Da daddare*



Amrah na kwance wajen 12:10pm sai juyi take tana saka maganganun Ammar a ranta.




Mikewa tayi ta ciro Wayarta a chaji kunna data tayi rabonta da hawa whatsApp tun Asuba da ta hau .



Rudu rudu messages suna ta shigowa anan taga Yaya Ammar ya mata magana nashi ta fara dubawa Ya ce Sweetheart na kasa bacci ina jiran Amsar ki.




Rasa mai zata ce mashi tayi ta dubo numbern Nafisa Aiko taga tana online ta ce ”Hello feenah!" Nafisa ta ce ”Hi ya kike sister Ya Arifa ki gaishe ta" Amrah ta mata reply ta ce “Wallahi dukan mu lafiya kalau yasu Mommah da Auta ki gaishesu" Nafisa ta ce "zasuji" Amrah tace “Ai nayi fushi dake".




Emojin murmushi Nafisa ta turo mata tace “Yi hakuri Yar uwa ranar Friday in Yaya ya dawo daga Masallaci zai kawo mu nida Auta" Amrah ta ce “To Allah kaimu" Nafisa tace “Amin goodnight zan kwanta" Amrah ta ce “Okay bye".



Zata kashe data kenan taga Ashe Ammar ya mata magana ta duba sai ta ga ya ce ”Sweetheart kina online kin mun shiru".




Ta tura mashi I am sorry Yaya immediately ya turo mata reply ya ce “Okay no wahala sweetheart na jiki shiru"?




Amrah ta ce ”Yaya na Amince" tayi sauri ta kashe datar tana murmushi ta tura wayar karkashin filo ringing wayar ta fara tana dubawa taga Ya Ammar ne taki dagawa ta kashe wayar ma gaba daya.


_________


*Washegari*


Washe gari bayan Daddy yayi ma Mama sallama akan zai je wani waje bazai daɗe ba, yana fita ta taɓe baki a fili take faɗin ”Shashasha nima ba ƙara ganina zaka yi ba".




Miƙe wa tayi tashiga wanka ta shirya cikin kayan ta riga da zani na atamfa kalan ja, ta cakare da ɗaurin ɗankwalin ta na ture kaga tsiya, sai tavyafa mayafi ta ɗauko jakan ta ta zuba takardun filayen nan sannan ta fito.




A falo ta tarar da Arifa zaune tana kallo, can kan dinning kuma Zee ce zaune tana karyawa ta dan ji karfin jikinta.




Kallon su tayi gaba ɗaya kamar yanda suka zuba mata idanu.



Mama ta ce “Ni zan fita anguwa ba kuma lallai in dawo yanzu ba, sai zuwa dare, kuma bana son ko wacce ta neme Ni acikin ku har sai kunga dawowa na".



Zee tayi tsagal ta ce "Ina Mama zaki je?"




Ɗan ya mutsa fuska Mama tayi ta ce "ke dai ki kula da kanki har ki ƙarasa warke wa, sai na dawo".




Har tafice Arifa bata yi magana ba illa kallon Maman da take yi, haka kawai taji gaban ta na faɗuwa kuma ta rasa meyasa.




Sai kuma daga baya ta miƙe cikin sauri ta nufi ƙofar ta buɗe ta fita.




A lokacin har motan Mama ta fice daga gidan, sai ta juya jiki a sanyaye ta koma ciki, bata zauna a parlour'n ba ta nufi ɗakinsu.




Tana shiga da sallama Amrah dake zaune riƙe da waya ta'amsa mata tana bin ta da kallo kafin ta ce
"Lafiya dai sis menene?"



Zama Arifa tayi gefen ta cike da sanyin murya ta ce
"babu komi Yaya Amrah, kawai bana jin dadin yanayin ne".



"Allah Sarki Allah yayi miki maganin abinda ke damunki".



"Ameeen ƴar uwa".



"Yauwa kinga yanzu muka gama waya da Ya Ammar yake ce min zai zo anjima, yanzu ya zan yi gashi Mama tana nan?"




Arifa murmushi tayi tana dafa kafaɗanta ta ce "kar ki damu Mama bata nan ai, yanzu ta fita".




Waro ido tayi da mamaki ta ce "Ina Mama zata je da safe, ko dai anyi wani abun ne?"




Arifa ta ce “Bakomai amma ta ce kar mu neme ta sai dare ma zata dawo".



Amrah ta ce “Toh Allah dawo da ita lafiya".



A hankali Arifa ta ce “Amin".



Amrah ta lura tana cikin damuwa saita fara bata labarai.



Mama ce tayi parking a kofar gidan Mariya tayi knocking taji shiru sai ta ciro wayarta ta Kira bata daga ba sai a na uku ta daga a fusace Mama ta ce “Haba Mariya meye haka Ina ta Kira kinki dagawa".




Cikin muryar bacci Mariya ta ce “Meya faru ne ni Kinga ke kika tashe ni daga bacci".




Mama ta ce “To nidai gani a kofar gidan ki kizo ki buden kofa".




Mariya ta ce “Toh ganinan zuwa".




Tazo ta bude mata aiko Mama ta baje a falo Mariya ta kalleta ta ce “Hajiyata ke kuma daga ina haka?".



Mama ta ce “Daga gida wallahi".



Mariya ta ce “Ina Alhaji kuwa"?.



Wani shu'umin Murmushi tayi ta ce “Yana chan ya saki baki na yashe dan iska sai dai yaji a salansa".



Mariya ta kyalkyale da dariya suka tafa....


________



*Da yamma*


Amrah ce ta shirya cikin wata red Abaya ta mata kyau sosai abunka da farar mace.



Arifa ce ta kalleta ta ce ”Sai kiyi kwalliya"



Hade rai Amrah tayi ta ce ”Bawani kwalliya da zanyi fa".



Arifa ta marairaice ta ce ”Nidai kiyi dan Allah "



Amrah ta ce “Dole sai nayi kwalliya ne bari dai na shafa hoda da lipstick".




Arifa ta kalleta ta ce “Gashi harkin futo kinyi kyau ".




Murmushi Amrah tayi ta feffesa turare suka fuce falo su kadai a gidan tunda Mama ta fuce Zee ita ma ta futa.




Kallo suka kunna wayar Amrah ce ta fara ringing da sauri ta dauka ganin Yaya Ammar ne tana dagawa ya ce “Ganinan nazo fah" ta ce ”Haba Yaya sai kace bako ka shigo" cikin fushi ya ce “In ba zaki futo ba shikenan sai na koma".



Da sauri Amrah ta ce ”Yi hakuri ganinan zuwa" ta mike ta fice.



Saida Arifa ta daidaici Amrah ta futa gate tayi sauri boyewa jikin fulawa
dan hangosu da tayi.




Suna tafe suna hira abunsu gwanin shaaawa Ammar ta kalleta ya ce “Sweetheart kinyi kyau fah" Murmushi tayi Wanda ba karamin kyau ya mata ba shima yana Murmushi sai ji sukayi ”karas" karar flash .




Suna dagowa suka ga Arifa hannunta rike da waya tana dariya .




Dukansu suka sa dariya falon suka karasa suka cika masa gaba da kayan ciye-ciye da sauri ya kallesu ya ce “Wannan fah?.




Da sauri Arifa tayi dariya ta ce “So nake gaba daya ka cinye kafin kiftawa da Bismillah".




Waro ido yayi ya shafa cikin shi lafaffe kamar Wanda ba acin Abinci ya ce “A wane cikin ?".



Dariya Arifa tayi ta ce “A cikin ka mana".



Yayi murmushi ya ce “So dai kike yau nayi bindiga na fashe dukansu suka sa dariya.




Hirarsu suke banda Amrah da Murmushi take masu Ammar sai janta yakeyi cikin hirar.



Chan Arifa ta mike ta ce “Ba na shiga ciki'.



Hira su Amrah sukayi sosai irin ta masoya ba laifi Amrah ta dan sake
Ya dan ci snacks kadan da lemo ya mike zai tafi ya kalli Amrah ya ce “Je ki ciron recorders din" .




Sama ta haura ta ciro na dakin Mama duk dakin a hargitse ta ciro na dakin Daddy ta Kai mashi ya ce ta kira Arifa suyi sallama.



Har kofar gida suka rakashi ya bawa Amrah kudi taki karba sai Arifa ce ta karba ya masu sallama ya tafi ..........✍🏻🖊️




*MORE COMMENT*
*MORE TYPING........* ✍🏻✍🏻




*Addeejerh* ❤️


👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI/RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM IDRIS*
( *shalelen kainuwa* ❤️)
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*


68~69


Ammar yana komawa gida ɗakinsa ya zarce sai da ya yi wanka ya shirya cikin ƙananan kaya kafin ya zauna akan sofa ya kunna recorder ɗin ya soma ji, sai da ya gama tas ya tabbatar da duk hujjan da suke nema akwai shi wanda zai tabbatar musu da zargin da suke ma Daddy sannan ya kashe ya adana ya miƙe.




Dole sai ya fara zuwa wajen Mommah sun yi shawara kafin ya maka su a court.





Don haka ɗakin Mommah ɗin ya wuce kai tsaye.




*****


Daddy da ya dawo ya tambayi su Zee ina Mamansu suka ce ta fita, don haka ya ɗau waya ya fara kiranta amma wayan A kashe, sai ya nufi ɗakinsa kawai.




Yau dai yana son duba takardun da ya ajiye, don haka kai tsaye ya duba amma babu su babu alamun su, zufa ne ya fara karyo masa ya sake dubawa yana tunanin ya chanza masu guri amma bai gani ba, sai kawai ya cire hulan sa yana fifita da hular, A taƙaice sai da yayi ɗai-ɗai da ɗakin bai samu abin da yake amma bai gansu ba.




Fitowa yayi ya shiga ɗakin Mama nan ma duk a hargitse, sai ya fara duba wa duk da yasan ba'a nan ya'ajiye ba, amma yana duba sip ɗin kayanta yaga wayam babu kaya.




Salati ya ringa yi ya rikice.



Tunanin da ya kawo masa cafka akan kar dai Mama ta yashe shi ne? ya fita ɗakin A sukwane yana ƙwalawa Arifa kira.




Daga Arifa har Amrah sai da suka fito a guje su na kallon sa




Kallon Arifan ya yi baki na rawa ya ce "ke..ke waye acikin ku ya shiga ɗakina ya gyara min sanda zan dawo?".




Arifa ta ce "Daddy ai Mama ne ta shiga ta gyara ita da kanta".




Numfashi yasoma fitar wa da ƙarfi yana zazzare idanu, ya sake cewa "to to bata baki wasu takardu ki 'ajiye min ba?"




Girgiza kanta Arifa tayi ta ce "A'a Daddy".




Amrah kuwa dake tsaye jin maganar takardu sai jikin ta ya fara tsuma, tsoro ne Ya kamata kar Daddy ya gane ita ta ɗauka kuma hakan da yayi aranta tace kar dai da sa hannun Daddy a kisan iyayenta tuni idanuwanta suka kada.




Sai da yabar wajen kafin hankalin ta yaɗan kwanta ta nufi ɗaki da sauri, taɗau waya zata kira Ammar, sai dai bai ɗaga ba, sai da tayi masa missed calls uku kafin ta haƙura.




****



Al'amarin Daddy fa ya rikice sosai musamman da ya duba ɗayan wayan sa wanda ya manta sa yau agida yaga an turo masa texts rututu duk an kwashe kuɗin account ɗin, sai kawai ya zube ƙasa tamkar sumamme, nan kuwa a ransa ɗimuwa ce yayi masa yawa.




Sai da yayi kusan mintuna 20 kafin yadawo hayyacin sa, ya tashi tsaye yana sababi




“Kai wlh ba zai yiwu ba, babu wanda zai min haka sai ke Sa'a, Ni zaki yaudara? Wlh ƙarya ne baki isa ba duk inda kike sai na nemo ki zaki san kin yaudare ni".





Surutu yake yi kamar sabon kamu, haka ya dauki mukullin mota ya fice daga gidan.




Duk inda yasan zai samu Mama sai da yaje amma bai same ta ba, ya Kira wayan ta yafi cikin kwando amsan ɗaya ne akashe, sai wajen goman dare ya dawo gidan.




Sai da yatashi yaran ya tambaye su ko ta dawo? suka ce bata dawo ba.




Dama a lokacin Arifa sai kuka take yi ta kasa barci Amrah na faman rarrashin ta.




A ranan haka Daddy ya kwana ido biyu barci ya ƙwaurace masa, da sassafe kuma ko wanka bai yi ba ya sake bazama neman mama .




Wasa wasa kwana biyu kenan da tafiyan Mama babu labarin ta, al'amarin da yaƙara firgitar da Daddy kenan, duk ya fita hayyacin sa.




Ba ma shi kaɗai ba har ta Arifa duk ta sauya ta rame , a tunanin ta ko wani abun ne ya samu Maman nasu.




Ita kuwa Zee ko a jikin ta, domin tun a ranan saurayin ta ya kira ta akan zasu haɗu, washe gari ta fita bata sake dawowa ba suna can sun tare a Hotel .




A kuma cikin kwana biyun ne Ammar ya gama duk shirye-shiryen sa ya kai Daddy ƙara Police station, Daddy na zaune a gida aka zo akayi ram dashi.




Duk da Arifa bata san mai yayi ba sai kuka take yi tana faɗin kar a tafin mata da Daddyn ta.




Amrah kanta sai da ta share hawaye, ba don komai ba sai don tausayin Arifa, yanzu bata san ya zatayi ba idan har ta gane Yaya Ammar ne yakai ƙaran sa sannan kuma duk saboda ita ne .



******


Dukan Daddy yan sandan suka dinga yi duk ya jigata wani acikin su yace “Zaka fadi ina ka boye matar ko kuwa?".




A galabaice Daddy yace ”Bansan inda take ba nima' dan sanda yace “Badai zaka fada ba ko? yace masu continue bea......kafin ya karasa DPO ya karaso gurin su yace ”Kuu rabu da shi" tare suke da Ammar .




Ammar ya kalli Daddy duk ya futa hayyacin shi da sauri ya kau da kanshi.




Ammar ya kalli DPO yace “Wannan da yake ta ambata Matarshi ce amma ta gudu yanzu nemanta zamu ba zama yi dole sai an kamota ita ma".





DPO yace “Haka ne Barrister"




Ammar ya shafa kanshi yace “To zan tafi ni zan dai kiraka waya muyi magana".




DPO yadan take mashi baya......🖊️✍🏻






*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* .....✍🏻✍🏻




*Addeejerh* ❤️


👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨




*LABARI/RUBUTAWA*




*BY KHADIJA ADAM IDRIS*
( *shalelen kainuwa* ❤️)
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

70


Ai kuwa Aunty Yana ba ta dade ba ta zo ta dauke su suka rufe gidan.




A binciken ƴan sanda sun gano inda Mama take zaune, don haka suka je har gidan suka cafko ta, ita ma a cell aka sata sai zunduma ihu take yi kamar wacce ta ta'bu, anyi-anyi ta yi magana ta ƙi, don haka suka kulle ta suka bar ta nan tunda babu yanda za su yi, jiya da dare dady ya faɗi a sume aka kai shi asibiti, nan Likitoci suke cewa ya samu shanyewar ɓarin jiki ne sakomakon jininshi da ya yi masifar hawa.





Ƴan sanda da suka yi ta fama da Mama tayi magana amma taƙi daga ƙarshe sukai ta gana mata azaba, sai da ta wahalu kafin ta sanar musu da komai akan ita ta kwashe kuɗaɗen da takardun ta gudu.






Lokacin da Ammar ya zo DPO ya sanar masa, shi Ammar ɗin yace kawai a tura su Court saboda a amsar ma yarinyar haƙƙinta, domin yana zargin ba mutuwar Allah da Annabi iyayenta sukai ba.





Don haka a cikin kwana biyu komai ya kammala an tura case ɗin court, sai dai har a lokacin Daddy bai farfaɗo ba.






Ko da akai zaman farko sai aka ɗaga Shari'an har sai Daddy ya farfaɗo sannan za'a kawo sa court ɗin.



*********



*BAYAN SATI UKU*



Abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da farfaɗowar Daddy, duk da ba ya iya taɓuka komai amma haka aka sanya shi a Wheel chair ranan da za'a koma court aka kai shi.






A ranan ma har da su Amrah dasu Mommah duk sai da suka hallari zaman court ɗin.





Bayan kowa ya hallara har da Alƙali sai Ammar ya tashi yana gyara rigarshi ta lauyoyi ya fara da faɗin.





"Ni sunana Brr Ammar Abdullahi Lauya mai kare wacce ta kawo ƙara".





Sannan ya zauna.




Alƙali ya ce "idan da Lauyan waɗanda ake zargi ya miƙe".





Maga-takarda ne ya miƙe ya ce "ya me girma mai Shari'a basu da Lauyan dake kare su kamar wancan lokacin".




Jinjina kansa yayi sannan yayi rubutu kafin ya ɗago kansa yana kallon Mama ya ce "ko kina da Lauyan da zai kare ku?".




Matse hawaye Mama tayi duk ta sauya kamanni ta gama galabaita a cell ɗin da aka ajiye ta, girgiza masa kai tayi.





"Magana zaki yi yanda kowa zai ji ki Sa'a Ibrahim" cewar Alƙali yana kallon ta.





“Babu ya mai Shari'a" Sa'a Ibrahim ta faɗa a hankali.





Arifa dake zaune kusa da Amrah ta rufe idanunta tana ta fidda hawaye, ko kaɗan baza ta iya kallon iyayen nata a wannan halin ba.





Gyaran zaman gilashin idonshi Alkali yayi ya kalli Ammar ya ce “To Brr zaka iya ci gaba".





Tashi Ammar yayi ya ce "Nagode ya mai Shari'a"





Sannan ya tako zuwa gaban court ɗin ya ce "......🖊️✍🏻




Kuyi manage pls😩😩






*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* .........✍🏻✍🏻






*Addeejerh* ❤️


👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨




*LABARI/RUBUTAWA*




*BY KHADIJA ADAM IDRIS*
( *shalelen kainuwa* ❤️)
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*



71

Ammar ya tako gaban court din ya ce "Nagode ya mai sharia, ina son a gabatar min da Alhaji Jibrin Usman don amsa wasu tambayoyi da zan mashi."





Maga-takarda ya miƙe yace "idan Alhaji Jibrin Usman na nan ya fito".




Wani ɗan sanda dake bayan Daddy shi ya gunguro keken sa suka fito.




Ammar ya tako zuwa gaban shi ya ce "zan so ka sanar da kotu Menene alaƙar ka da Alhaji Abdulmunaf Usman da kuma sanadin da suka rasu shi da matar sa?"





Yawu Daddy ya haɗiye daƙyar, cikin maganar sa wanda baya fita sosai sabida karkacewar bakinsa ya ce "Yayana ne shi, kuma sun yi hatsari ne lokacin da suka mutu".




Jinjina kai Ammar yayi ya ce "bayan ya rasu sai ka sauya duk wani kadaransa da sunan ka, har ta Companyn sa ka mallake alhanin akwai ɗiyar sa, meya saka kayi hakan?"




Hawaye Daddy ya fara yi jikinsa na rawa ya kasa yin magana.




"Muna sauraron ka kotu zata so ta san menene dalilin ka na yin hakan".





Buɗe baki yayi baki na rawa ya ce "Matata ce ta sanya ni yin hakan sabida wasu dalilai namu".





Murmusawa Ammar yayi ya ce "ko zaka iya faɗa mana dalilin?"




Shiru yayi be ce komi ba



Ammar ya ce “Kotu fa tana sauraron ka".




Da kyar Daddy"Saboda mu mallaki ƙadaran sa".




Numfashi Ammar yaja kafin yace "shine ku kayi sanadin da suka bar duniya don ku mallaki dukiyar sa ko?"




Tari Daddy yasoma yi yana zazzare idanu.





Daga can Mama ta ɓarke da kuka tace "wlh babu ruwana shine ya kawo shawaran mu kashe su don mu mallaki dukiyar sa"



"Odar.. odar..".



Alƙali ya buga gudumansa sabida jin hayaniyar Mama ya cika wajen.




Hawaye Daddy yake fitar wa cike da takaicin Mama, dama sosai yake ciki da ita akan yaudaran da tayi masa, yanzu kuma tana shirin ɗaura masa laifi kacokan, Allah yasa yana da bakin sa bai gama mutuwa ba da bai san ya zai yi...




Maganar Ammar ne ya katse masa tunanin da yake.




Ammar ya kalli Daddy yace “Muna sauraron ka Alhaji Jibrin, ka dai ji abinda Matar ka ta faɗa, shin zaka faɗa mana gaskiyar zance ne ko kuwa kana son in kawo shaidun da zai tabbatar da cewar ku ne kuka aikata musu hakan?"



"Zan faɗa". Cewar Daddy yana sharce zufan fuskarsa da hannun sa ɗaya mai lafiya kana ya ce


"Tun farko Matata ta bani shawaran kashe Yayana don mu mallaki kuɗin sa, tun ban yarda da dan Yayana bai rage ni da komai ba shawara bani ta ingiza ni har nabi dokin zuciya muka shirya yanda zamu yi subar duniyar gaba ɗaya.."




Shiru yayi sabida kukan da yaci ƙarfin sa saida yasha kuka sosai cikin rawar baki ya fara da labarin ya ce ranar 17 ga watan October 2020 da daddare misalin karfe 9 na dare naje gidan wana Alhaji Abdulmunaf Usman muka gaisa sai yake cemun kanshi ke ciwo ya bani kudi na kaiwa Mai gadi ya karbo mashi magani na futa har bakin gate na bawa Mai gadin ina ganin futarshi na nufi motar Yaya da yake futa office da ita na Ciro karafuna irinsu plier sannan na cire burki",cikin kuka ya karasa zancen.






Amrah ma fashewa tayi da kuka tana tuno rayuwarta da iyayenta.




Gaba ɗaya Kotun sai suka ɗau hayaniya suna tirr da Daddy da irin wannan zalunci nashi.




Ammar murmushi yayi don bai yi tunanin za suyi saurin amsa laifin su ba, amma gashi Allah da ikon sa bai kawo shaidun sa ba amma gaskiya ta fito.




Juyawa yayi zuwa gaban table ɗin su sannan ya ɗauko wasu files da recorders ya miƙa ma maga-takarda ya ce


"Wannan shine hujjan da nake dashi na cewar Alhaji Jibrin da matar sa Sa'a Ibrahim suna da hannu dumu-dumu akan kisan Alhaji Albdulmunaf da Matarshi Hajiya Fatima Abbagana, sannan record ɗin maganganun su ne da suke yawan yi akan shirin nasu, da wannan na ke roƙon kotu nan mai Adalci da ta yanke musu hukunci dai-dai da laifin su, Nagode".


Sannan ya koma ya zauna.




Saka record ɗin aka yi nan aka soma jiyo muryan Mama da duk shirin da take yi akan yaudaran Daddy ta gudu da kuɗin, sannan kuma da inda suke maganar su biyu da Daddy ɗin ta yanda komai zai zama nasu, duk dai wani shiri nasu sai da ya fallasa.




Kuka sosai Mama da Daddy suke tayi cike da nadama, basu taɓa tunanin asirin su zai tonu haka ba.




Bayan an gama jin duk wasu shaidu, sai hayaniya ta ɓarke cikin kotun, sai da alƙali ya buga guduma kafin a nutsu ayi shiru.




Glass ɗin sa ya gyara kafin ya fara rubutu, bayan ya gama sai ya ɗago kai ya fara magana kamar haka,




"A bisa tarin hujjoji da aka gabatar sannan kuma da yadda masu laifi suka amsa laifin su ba tare da sun ba kotu wahala ba".




Shiru yayi kafin yabuɗe shafin littafin gabanshi kana yaci gaba,




"Kotu ta yanke ma Alhaji Jibril ɗaurin rai da rai a gidan kaso sakamakon shine mutumin da yaje ya cire musu burki har suka rasa ransu, don haka shi zai ɗau alhakin mutuwar su, zai zauna na tsawon shekaru goma tare da horo mai tsanani sannan kuma daga bisani a zartar masa da kisa ta hanyar rataya a bisa dokokin Musulunci, ita kuma Sa'a Ibrahim kotu ta yanke mata zaman kaso na shekara goma da horo me tsanani, sannan zata biya tara na dubu ɗari biyar, idan wannan hukuncin bai muku ba kuna da damar da zaku ɗaukaka ƙara a nan gaba".




Sai ya buga gudumarsa sannan ya miƙe tsaye, haka su ma mutane suka tashi suna mai faɗin,





"Kotuuuuuuuuuuuuu".




Kuka sosai Arifa ta ɓarke dashi tana faɗa wa jikin Amrah Wanda itama kukan ta ke yi........🖊️✍🏻







*MORE COMMENT*
*MORE TYPING*......✍🏻✍🏻







*Addeejerh*❤️

👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI/RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM IDRIS*
( *shalelen kainuwa* ❤️)
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*


72


*BAYAN WATA BAKWAI*


_NOT EDITED_ 🥺


Abubuwa da yawa sun faru a wannan watannin ciki kuwa harda sa ranar auren Amrah da Ammar wata biyu masu zuwa.





Amrah ce zaune akan kujera rike da wata kyakkyawar jinjira da gani sabuwar haihuwa ce.





Amrah kuwa sai danne-dannen waya take

1 Comments On FANSAN RAN MAHAIFANA
avatar
khadija-1-2-5

9 months ago

Reply

Tnx

Please Login or Register in order to submit comment