Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

61~62

*Bayan kwana uku*


Mama ta kalli Mariya tayi wani shu'umin Murmushi ta ce “Ai shi kanshin Alhaji Jibrin din target na ke dana mashi bai sani ba aikin banza".



Mariya ta ce ”Allah Hajiyata shaka mun mana" tana kyalkyalewa da dariya.



Kasa kasa Mama ta ce ”Ai nake fada maki saida nayi yadda zanyi nasan password din account din shi ,shiyasa ai na kada shi can kasar wajen zai ci ubansa ne Sai dai kawai yaga ana zuke mashi kudade".



Mariya ce ta shake shakiyiyar dariya suka tafa ta ce “Muma fa kar a manta damu abamu mudan lasa ".



Mama ta ce “Haba Mariya ba sai kin fada ba kedai kawai sai dai kiji Alert".



Mariya ta ce “Haka nake son ji Hajiyata, Shiyasa nake kara son ki".



Mama ta ce “Sai wannan yarinyar da na ke so ayi maganin ta naga ta fara tasawa banso inga tana kula samari wanchan yaron da nake fada maki da suka dawo da ita naga santa a idonshi gashi masu kudi ne kawai so nake ya fara son Zee".



Gyara zama Mariya tayi ta kalli Mama ta ce “Haba Hajiyata akan wannan kike wani tayar da hankalinki? mu da muke da mafuta".



Mama ta ce “Dagaske Mariya ?"



Mariya ta ce “E'h mana ga boka Gagarabadau aikin shi kamar yankan wuka ne”.



Mama na yake hakwara ta rungumo Mariya ta ce ”Kai kawata shiyasa nake sonki wallahi yanzu yaushe zamuje gurin bokan kafin dai Alhaji ya dawo zamuje ko?".



Mariya ta ce “Toh tunda haka ne yaushe zai dawo?".



Mama ta ce “Ina tunanin ko nan da kwana biyu"



Mariya ta kalleta ta ce “Kinga gobe sai muje da safe Amma fah ki tanadi ma'kudan kudade dan shi baya aiki sai da kudi".



Mama ta ce “Mariya karki damu da wani kudi nidai indai burina zai cika ko nawa ne zan bayar".



Mariya ta ce “Shikenan su ka cigaba da hirarsu ".

_________

Amrah ce ta futo parlour ta zauna gidan ba kowa Arifa ta tafi islamiya dan Amrah tayi sauka Zee kuwa tunda Mama ta fuce ita ma ta tafi gidansu kawarta.



Kunna kallo Amrah tayi kallo take amma hankalinta baya gurin wani tunani ne ya fado ranta ta tuno maganar Ammar ya dawo mata .



Kamar an tsikareta ta hau sama ta murda handle din dakin Alhaji taga ya bude a ranta ta ce ikon Allah yau Mama bata rufe dakin ba ,ba tayi dogon tunani ba tashiga dakin ta fara binciko takardun filayen Abbiey dinta.



A kasan bedside drawer taga takardun filayen dauke wa tayi ta gyara ko Ina da ta hargitsa.



Da sauri ta sauka kasa ta shiga dakinta Wayarta ta dauka tayi dialing number Ya Ammar sai da ta kusan katsewa ya dauki wayar.



Tabce “Assalamu Alaikum" ya Ammar ya amsa “Waalaikumus Salam ".



Amrah ta ce “Ya Ammar Ina wuni ya aiki". Ammar yace “Lafiya kalau aiki Alhamdulillah da fatan kina lafiya?" Amrah ta ce “Lafiya kalau" ya ce “meya faru"?.ta ce “Yaya akan takardun filayen nan ne ni kadai ce a gida gashi na dauko su".


Ammar yayi Murmushi da ta jiyo sautin shi ya ce “Kinsan mai zai faru?" ta ce “A'a".



Ammar ya ce “ki rike takardun dama ina kusa da gidan ku zanzo in karba sai naje ayi fake copy dinsu in nazo zan kiraki ki kawon Amma ki tabbata kin boye a himar dinki”, Amrah ta ce “Haka za'ayi sai ka karaso".



*Bayan yan Mintuna*



Ammar ne ya kira Amrah yace gashi yazo da sauri Amrah tasa himar dinta ta kwashi takardun.



Tunda ta futo Amrah yake kallonta ba kifta ido tasha purple himar abun ka da farar mace Masha Allah yace har ta karaso bai sani ba sai da tayi knocking ya dawo hankalinshi ya bude kofar .



Idanuwansu ne suka sarke cikin na juna Ammar ya mata wani kallo wanda bata gane mashi ba da sauri ta ce “Yaya ga takardun ".



Karbar takardun Ammar yayi ya ce “Okay bari naje nayi photo copy din zan rike original din a guri na".



Amrah ta ce “toh Yaya sai kadawo" ta koma ciki yaja motarshi ya tafi.


___________


Ammar ne yashigo ya tarar da Amrah A falo ya kalleta ya ce “Gashi ki maza ki mayar kafin su dawo " yana mika mata takardun.



Da sauri ta karba ta haura sama taje daidai kofar dakin Alhajin taji anyi horn tuni hantar cikin ta ta kada.



Da sauri tashiga ta maida su mazaunan su


tana saukowa tana kokarin dai dai ta nutsuwar ta kenan Mama tashigo ta karewa Ammar kallo dake latsa wayarshi ta maida kallonta ga Amrah.



Ta Kama baki ta ce “Ohh ni Sa'a kai kam kaji kunya ka gama iskanci ka da yarinya a gidan ku har sai kazo gida na ko?".



Sai lokacin ma ya kalleta cikin kumfar baki ya ce “Ki kiyaye ni fa da tsauraran maganganun ki dan ruwa ba sa'an kwando bane ehee!!!!".



Mama ta ce “In naki fah?"
Amrah dai na raku'be a gefe daya.



Ko saurarar Mama Ammar din beyi ba ya futa a fusace.


*Washegari*

Mama ce daga sama ta fara kwalawa Amrah Kira Amrah dake kitchen da sauri ta Amsa ”Na'am" da iya karfinta Mama ta ce “kizo ki sharen daki".



Amrah ta ce “toh" taje ta dauko kayan sharar ta hau saman taje dai dai dakin Mama tafara jiyo Maganganu kus kus.



Tana shiga Mama ta katse wayar da take ta dallawa Amrah harara cikin bala'i ta ce “Ke yarinyar nan algunguma ce ba nace kina neman excuse in Zaki shigo mun daki ba?"tana tsare Amrah da ido



Amrah ta ce “Kiyi hakuri Mama zan gyara".



Mama ta ce “Kada Allah yasa ki gyara din ma" tana kwafa,ita dai Amrah kanta na kasa .



Mama ta yafa wani sharasharan mayafi ta dauki jaka ta jefa cingum a bakin ta ta fara taunawa kass kass takalmin da tasa yana bada wani sauti.



Amrah ta ce “Mama sai kin dawo",ko kala mama bata ce mata ba ta futa".



Aikin ta Amrah ta fara a ranta tace ko wace waya Mama take yi da ta ganni sai ta katse a ranta tace akwai ayar tambaya akai gaskiya.


Haka ta gama gyaran ta karya lokacin Arifa ko tashi batayi daga bacci ba .



Tana gama karyawa ta Kira Ya Ammar yana dagawa tayi sallama ya Amsa tayi Murmushi ta ce “Kardai Yaya ni na tashe ka da Kira?" Ammar ya ce “Aa wallahi dama na tashi sai ki ka Kira ta ce “Okay" sai ya ce “An samu wani abun ne? Mai ya faru?".



Sai da ta nisa sannan ta ce “Wallahi ya Ammar kwana biyu sai naga Mama tana waya da ta gannin sai ta katse ".



Sai da Ammar yayi dogon nazari sannan ya ce “Kinaji na".



Amrah ta ce “Ina sauraren ka Yaya" Ammar ya ce “Yauwa karki wani damu zan kawo maki Abun daukar murya kisa a dakin Maman da Uncle dinki ki tabbata inda baza a gani ba dan nasan innace kina recording a waya baze yi wu ba sanna zaki na sa abun daukar muryar a rigarki da fatan kin gane ?".


Amrah ta ce “Nagane Yaya sai kazo ka gaishe da Nafisa".

Ya ce “Toh zataji" su kayi sallama.



Mama ce tayi parking a kofar gidan Mariya dialing number dinta tayi tana picking Mama ta ce “Mariya gani na karaso ki futo muyi sauri", Mariya ta ce “Toh
ganinan".



Mariya ce tafuto tasha wasu shegun kaya tana karasowa ta bude gefen Mai zaman banza gaisawa sukayi.



Wani mugun gurin sukaje da ba abunda akeji sai kukan tsuntsaye Mariya ta ce “Hajiyata yi parking anan gurin bokan ba gurin parking", Mama ta ce “Okay".


Wani surkukun guri suka shiga wata karamar bukka suka nufa cikin karaji suka ji ance “Ku cire takalmanku ku shigo da baya".



Cika umarnin Bokan suka yi sunzo zasu shiga Mama ta ce ”Assalamu alai........kafin ta karasa a ka daka mata wata iri yar tsawa da sai da hanjin cikinta suka kada a tsorace ta kalli Mariya.



Wani mutum suka gani fuskarshi bakikirin ba kyan gani Idanuwan sa jajawur dasu .



Zama sukayi Mariya ta ce “Boka dama ....



Cikin shakakkiyar murya ya ce “Dakata nasan Mai ke tafe da ku an riga da an fada mun".



Da sauri Mama ta kalli Mariya , Mariya ta girgiza mata.



Bokan ya kalli Mama da jajayen idonsa ya ce “Baso kike a raba ta da wannan yaron ba Ammar ya koma gurin yarki Zainab ko?".



Da sauri Mama ta daga Kai ta ce “Hakane boka ".



Bokan ya ce “Ina fatan Mariya ta maki bayanin komai ko ?"


Mariya ta ce ”Na mata bayani karkaji komai akwai kudi sosai".



Boka ya ce ”Yauwa ya fara wasu surutai sai ga wata kwarya ta fado gabanshi da wani karamin kwalba a ciki.



Ya mikawa Mama kwalbar hannunta na rawa ta karba cikin shakarkiyar muryashi ya ce “Ki tabbata yarinyar ta shafa wannan turare indai sun hadu da Ammar din zaiji tana warin ja‘ba zai tsaneta
hankalinsa zai koma Kan
yarki".


Mama ta ce “Toh"


Boka Gagarabadau ya ce “Yauwa ki sa kudin acikin kwaryar nan Aljanu zasu zo su dauka".


Da sauri Mama ta Ciro bandir din yan dari biyar-biyar daga jakarta.



Boka ya ce masu “Ku tafi da baya-baya......... ✍🏻🖊️





*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* .......✍🏻✍🏻



*Addeejerh* ❤️

👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI/RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM IDRIS*

*(Shalelen kainuwa* ❤️)



*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*


*HAPPY ONE YEAR ANNIVERSARY* 🎂🎂❤️

💦 *AREWA WRITERS* *ASSOCIATION* 💦
Allah Kara daukaka


63


A kan hanyarsu Mama na komawa gida Mariya ta kalli Mama dake tuki ta ce “ki fa tabbata Yarinyar nan ta shafa turaren fah".



Wani irin Murmushi Mama tayi Bata ce komai.


__________


Arifa ce tayi knocking dakin Zee taji shiru tura kofar tayi da sauri ta karasa gurin Zee ta dago ta tana fadin “Sannu Yaya Zee" cikin karfin hali Zee tace “Yauwa Arifa”.



Ba karamin tausayawa Yayarta Arifa tayi daukar cup din da ta shigo da shi tayi tace ”Yaya Zee ga tea Dan Allah ki daure kisha".



Karbar tea din Zee tayi ta fara kurba tasha ya Kai rabi ta mikawa Arifa karba tayi ta Ajiye ta bata magungunan ta tasha ta koma ta kwanta.



Arifa ta rufe ta fuce.

________

Amrah tana gama waya da Ammar Arifa ta shigo kallon Amrah tayi sannan tace Yaya Amrah Ina Zaki je haka naga kinasa himar ?".



Amrah tace “Ya Ammar ne yazo Wallahi zanje mu gaisa".



Cikin zumudi Arifa tace ”Muje mu gaisa dashi".



Amrah tayi Murmushi tace “Muje to"tana yin gaba.



Suna futa kofar gate Yana jingine jikin mota ya rufe idanuwansa.



Arifa ta cewa Amrah “Bari kiga abun da zan mashi".



Suna zuwa dab dashi Arifa tayi Muryar maza tace “kuyi sauri ku samun Shi a mota" tana danne dariyar da tazo mata.


Da sauri Ammar ya bude idanuwansu yana kallon su Amrah yana dariya yace “ke dai wallahi Arifa baki da dama,dama nasan sai ke Allah shirye ki in Banda abun taya za'a dauke ni" ya karasa zancen cikin dariya su Amrah ma saida suka dara gaisawa sukayi hira suka ringa yi da Arifa ita dai Amrah bata sa masu baki ba.



Chan Arifa ta kalli Ammar tana murmushi tace “Yaya bana koma ciki Yaya zee Bata da lafiya ita kadai ce a ciki ".



Shima Murmushi yayi yace “Ayyah Allah bata lafiya" ya Mika mata kudi yace “Ga shi a siyi kayan kwalliya ".



Arifa ta kalleshi ta ce “A'a Yaya baza'ayi haka ba kabarshi Ina da kayan kwalliya basu kare ba"



Hade rai Ammar yayi yace ”kawai ke dai bazaki karba bane ?"



Da sauri Arifa ta ce ”A'a Yaya ba haka bane".



Ammar yace “To ki karba rusunawa Arifa tayi tasa hannu biyu ta karba tana fadin “Yaya nagode".



Murmushi Ammar yayi yace ”Ko kefa" ita ma Murmushi tayi tace “Sai anjima ka gaishe da Nafisa" yace “zataji" ita kuma ta shiga gida



Arifa na shiga ya maida kallonshi gurin Amrah yace yana xuwa cikin mota ya koma ya dauko abun daukar muryar ya mikawa wa Amrah karba tayi ya shafa sumar kanshi yace “Ga shi ki maza kisa a dakunan su Uncle din kafin Maman ta dawo ".



Amrah tace “Okay" sukayi sallama ta koma ciki ya tafi.



Amrah na shiga ciki ba ta tsaya yin komai ba ta nufi dakin Mama Arifa na dakin Zee.



Amrah ta karewa dakin kallo tana tunanin ta Ina zata sa recorder din chan ta dane gefen abun mudubi dake kusa da drawer a chan karshen drawer din ta makala recoder din wani irin Ajiyar zuciya ta saki lallabawa tayi ta fice .



Harta nufi stairs zata sauka sai ta tuno maybe dakin Uncle a bude yake aikuwa tana murda handle din taga kofar a bude tana shiga idon ta ya sauka kan lamb aiko da sauri taje ta makala recoder din a jiki ta sauka .



Mama ce ta sauke Mariya a kofar gidanta Mariya tace “To sai munyi waya", Mama tace “Okay nafa gode".

_________

Arifa na zuwa dai dai dakin Mama taji ana maganganu da sauri ta kara kunnenta taji Mama na fadin “Ai Mariya karki damu yanzu ai jan Yarinyar zanyi a jiki sai nasan yadda za'ayi ta shafa turaren nan" tana shekewa da dariya tace “Ai har shopping na mata Kinga tana kwalliya Amma a gurin shi Ammar din warin jaba take Kinga dole ya hakura da ita".



Da sauri Arifa ta dafe kirji tace “Subhanallahi! kardai gurin boka Mama taje “Innalillahi wa'ina ilaihir raji'un!



Tana jin motsi tayi maza ta gyara .


Cikin rashin gaskiya Mama ta ce “Mai kike yi anan?".



A hargitse Arifa ta ce “Dakin Yaya Zee zanje".



Mama ta kalleta tace “To shiga ki dauko wata leda a dakina muje kasa gurin Amrah".



Cike da mamaki Arifa ta dauko ledar.



Amrah na zaune a gefen gado su Mama suka shigo da sauri Amrah ta mike ta ce “sannu da zuwa Mama" Murmushi Mama tayi ta ce “Ai nadawo Ashe kina daki kina hutuwa”, mamaki Amrah ta fara anya kuwa Mama ce kuwa ?.



Kamar Mama tasan tunani take ta ce “To gashi na maki siyayya Yan matana asha kwalliya ga wannan turaren ana shafawa ana kamshi” tana mika mata kwalbar turare tana wani irin Murmushi.



Murmushin yak'e Amrah tayi ta karbi turaren tana fadin “Na gode sosai"!.



Ba tare da Mama ta ce komai ba ta fice tana futa ta kyalkyale da dariya tana fadin “Yaro Yaro ne.......✍🏻🖊️





*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* .....✍🏻✍🏻





*Addeejerh❤️*


👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨



*LABARI/RUBUTAWA*



*BY KHADIJA ADAM IDRIS*
( *Shalelen kainuwa* ❤️)

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

Na sadaukar da page dinnan gareki ummu Dahirah kiyi yadda kike so dashi💃❤️💃 godiya Allah saka da Alkhairi inna tsaya gode maki sai mu kwana mu hantse🤣💃


64~65



Fitan ta Amrah ta faɗa duniyar tunani, sosai take mamakin sauyawan Mama har ta soma dasa zargi a ranta.



Arifa kuwa tana zaune itama tana tunanin hanyan da zata yi ta hana Amrah saka turaren nan batare da ta tona ma Mamanta asiri ba, can daga baya ta saki ajiyan zuciya tuna dabaran da yafaɗo mata.




Kallon Amrah tayi da har yanzu tana tunani aranta, sai ta miƙe ta dawo kusa da ita tana murmushi ta ce;


"Wow sis yanzu kin koma ƴar gatan Mama ne kuma? Wai shin ma yaushe kuka soma ɗasa wa ne da ita?"




Murmushin yaƙe Amra ta saki ta ma kasa faɗin komai.



Arifa tace"Kawo muga abinda ta siyo miki ko nima zan ɗau nawa tunda ta manta damu".




Bata jira cewar Amrah ɗin ba taja ledan ta soma fito da kayan ciki tana gani, fuskarta duk annuri sai yaba kyan kayan take yi, taɗago turaren tana gani tace,


"Sister wallahi ina son turaren nan daga gani zai yi ƙamshi sosai, bari in ji".




Buɗe wa tayi tana shirin zuba wa a hannu sai kuma tayi saurin miƙe wa tana wancakalar da turaren nan kuwa ya zube a ƙasa gaba ɗaya
Baki Arifa din ta bude tana waro idanuwa.



Itama dai Amra kallon yanda turaren ya zube take yi.




"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!!.. Don Allah kiyi haƙuri na zubar, wallahi shaf na ma manta Mama ta saka Ni dafa ma Yaya Zee Indomie kuma na zauna".




Dariya Amrah ta saki tana kallon ta tace "lah wallahi babu komi kamar kinyi wani babban laifi? Dama ai kin rigada kin ce kina so ko baki zubar ba zan baki".




Langwaɓe kai Arifa tayi tana cewa "To don Allah kar ki faɗa ma Mama idan ta tambaye ki?"



Gyaɗa mata kai tayi kafin tace "Bazan faɗa ba, je ki kar taji shiru ki ja ma kanki".




Dariya Arifa tayi ta nufi hanyan ƙofa tana faɗin "Bari in zo sai in zaɓa abinda nake so, Kar fa ki mayar".



"To sai kin dawo".



Arifa tana cikin kichen tana dafa indomie din Mama ta shigo tana kallon ta.




"Ayyo ai na aza kina can ɗakin ne baki fito ba, ko uwar ma me kika zauna yi Oho?"




Ita dai Arifa tunda ta kalle ta tasad da kanta ƙasa bata ce komai ba.




"Kiyi sauri ki gama ta gaji da jiran ki". Mama ta faɗa tana juyawa ta fice.




A Parlour ta zauna ta zuba ma tv Ido tana kallon shirin kwana casa'in a Arewa 24.



Babu jimawa da zaman ta Umar yafaɗo parlour'n a hargitse.




"Kai kuma fa lafiyanka kuwa? Daga ina?" Cewar Mama tana bin sa da kallon ƙurilla.




Fuska babu walwala ya sami wuri ya zauna batare da yace uffan ba.



Tsaki Mama taja tana sababi.



Fitowar Arifa daga kichen da Plate a hannu duk parlour'n yaƙara gume wa da ƙamshi.



Kallon ta Umar yayi yana huro hanci yace "ke meye cikin Plate ɗin nan?".


"Yaya Indomie ne".



"Kawo nan wallahi dama yunwa nake ji".



Da sauri Mama tace "kai asuwa? To Zee aka girka ma wa bata jin daɗi zata ci, kai kuma kabari ta girka maka wani".




Ɓata fuska yayi yace "Haba Mama sai in ta zama har sai ta girka wani, wallahi bazan iya ba".




Sai ya miƙe yanufi Arifa da har ta nufi ɗakin Zee ɗin.



Yana zuwa ya'amsa yadawo parlour'n ya zauna.




"Wallahi Umar kar ka soma cin abincin nan". Mama tafaɗa a harzuƙe, sai kuma taƙara da cewa,



"Kai ka tafi yawon ka sai sanda kaga daman dawowa zaka dawo saboda ba'a isa da kai ba ko? Sai yanzu ma nake ganin gaskiyar Mahaifinka wallahi ka fara gagaran mu".




Tsaki Umar yaja yana faɗin "sabida wannan dai banzan abincin ne kike gaya min magana ko?"




Sai ya kifa Plate ɗin a ƙasa ya miƙe a fusace yabar falon.



Mama kuwa sai zuba salati take yi tana tafa hannu. "Na shiga ukuna yau naga abun da yafi ƙarfi na".



Arifa da har yanzu tana tsaye tana ganin ikon Allah sai ta juya da zummar tafiya.



Mama tace "ina zaki ke kuma? Zo ki ƙara dafa mata wani tunda ya zubar da wannan".




Ƙwalla ne suka cika mata idanu tace "Mama wallahi bazan.."



Mama ta ce; "Rufe min baki ki wuce kije ki girka mata, dama ba ke ce kike tausayin Amrah ba duk abinda na saka ta sai kin nuna rashin jin daɗin ki? To yau sai ki fanshe ta, kiyi sauri da Allah kina ɓata min lokaci".




Jiki babu ƙwari Arifa takoma cikin kitchen ɗin ta sake ɗaurawa.




A ɗaki kuma Amrah da taji ta shiru bata dawo ba, sai takwanta abunta tana tunanin Ammar a ranta.




“Assalamu Alaikum" da sauri Mama ta tashi fuskarta ba yabo ba fallasa tace "Sannu da zuwa Alhaji saukar dare".



Alhaji ya zauna akan kujerar yana wash yace “Wallahi nagaji sosai kawo mun Abinci.....kafin ya karasa da gudu Arifa tazo ta rungume shi ta na oyoyo Daddy “Sannu da zuwa ina tsarabar mu?"



Daddy ne yana murmushi yace “Nidai dagani karki karya ni tsaraba kuwa sai na huta".




Arifa tace “To Daddy" sai Daddy yace “Niko Ina Zee ne ?".



Mama tace “Batajin dadi ne zazzabi take".




“Subhanallahi!!" Daddy yace “Banaje na duba ta ki taho mun da Abinci".




Mama ta kalle shi tace “Nafa cema ba Abinci sai biredi in bazaka ci ba shikenan!"




Alhaji yace ”To kikawon" iya abunda yace kenan ya nufi sama Arifa ta kinkimi Akwatin shi .



Mama ta bishi da harara .



Bayan su Mama sun kwanta Alhaji yace “Hajiya naga ana ta cirar kudi Alhalin baki fadan ba".




A harzuke Mama tace ,“Saboda ka maidani barauniya chan ka nemi wanda ya cire ma kudin aikin banza!!" taja tsaki ta juya tana kallon bango shiru ya mata baice komai ba.



*Washegari*



Amrah na zaune a daki tana karatun Qur'ani taga wayarta na haske da sauri ta karasa gurin wayar number tagani da Kamar baza ta daga ba sai kawai ta daga.




Murya da taji ne yasa ta fadin ”Aunty Yana kece Ina wuni" Aunty Yana tace “Lafiya kalau Rabin raina dama nasan bazaki sannan number din ba yanzu dai ya kike da fatan komai Lafiya kalau?".




Cike da farinciki Amrah tace “Lafiya kalau" sai kuma ta shagwabe murya tace “Amma kwana biyu nayi missing naki baki zo ba ".




Aunty Yana tace ”Yi hakuri Rabin raina wallahi bani da lafiya laulayi ne ya sani gaba jiya da daddare aka sallamoni ga uncle dinki bayanan sai makota ne ma suka kaini asibitin ga an rufe mun sim ,karki damu Ina Kara jin saukin jikina zanzo in ganki".




Cikin Murna Mara misaltuwa Amrah tace ”Dagaske Aunty ciki ne dake?" Aunty Yana tayi dariya tace “E'h Mana ".




Amrah tace “Amma babyn namu ya wahalar mun dake"Kamar zatai kuka dariya Aunty Yana tayi suka cigaba da hirarsu.........



__________


Amrah na kwance tana tunani taji wayarta dake gefenta tayi bip alamun message ya shigo.



Da sauri ta duba taga Ya Ammar ne ya turo fara karanta sako kamar haka...“Assalamu Alaikum ina fatan a yanzu kina cikin ƙoshin lafiya?



Amrah dama ina so in sanar dake wani abu dake cina arai ne, duk da naso in barshi har nan da ɗan wani lokaci da naɗiba ma kaina but hakan ba me yiwuwa bane agare ni, na kasa jure abinda nake ji akan ki shiyasa nayi tunanin sanar dake kar lokaci yaƙure min kwado yamu kafa



Amrah Ina ƙaunar ki tun ranan farko da na ganki, wlh soyayyar ki tayi min mugun kamu da bana iya runtsawa kullum cikin tunanin ki nake, don Allah idan har babu kowa cikin ranki ki amince dani Ina son ki da yawa ki taimaka mun



Bazan yi barci ba sai naji amsar ki yau, ina fatam zaki dawo min da reply? sai na jiki".



Shiru Amrah tayi tana sake kafe idanun ta kan rubutun, ta jima tana wasi-wasin anya abinda ta gani ba gizau bane? sai da ta sake maimaita saƙon aƙalla sau uku kafin ta yarda tabbas Ya Ammar ne yatura mata kuma ba gizau bane gaske ne.



Bata san sanda ta saki murmushi ba takoma takwanta tana rufe idanun ta, yau ranan tazo mata a wani irin bazata da bata taɓa tsammani ba, shiru tayi kawai tana sauraron bugun zuciyar ta har alokacin murmushi be bar fuskarta ba.



Wajen mintuna goma sai wayan tasoma ringing alamun kira, dasauri ta tashi zaune tana waro idanu sakamakon ganin sunan Yaya Ammar, nan gabanta ya soma faɗuwa tunawa da cewa ya buƙaci ta bashi amsa,



Jiki a sanyaye dai ta amsa call ɗin takara a kunne.



Shiru ne ya biyo baya kafin daga bisani taji Muryan Ammar ɗin cikin sanyin murya ya kira ta,


"Amrah".


"Uhm". Ta faɗa ahankali.



"Ban ji kin dawo min da amsa bane? Ko kuma.."



Shiru yayi be ƙarasa ba sabida baya son abunda ke ransa ya zamo gaskiya.



"Amra Ina son ki sosai wlh, Plz ki bani amsa ta a yau ko zuciyata zata samu sukuni kinji?"



Cikin jin kunya Amrah tace "Yaya Ni dai yanzu kabari ba yanzu zan baka amsa

1 Comments On FANSAN RAN MAHAIFANA
avatar
khadija-1-2-5

1 year ago

Reply

Tnx

Please Login or Register in order to submit comment