Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gida ”,



“To zo muje waje tunda kinki yarda kar driver yazo muna nan ”,



Ta dauki Jakarta
ta zasu futa Arifa ta shigo ajin ganin halin da Amrah take ta rude tace “lafiya Amrah? Meya same ki? haka tayi ta tambayar ta.......




*MORE* *COMMENT*
*MORE* *TYPING.......🖊️*



*Addeejerh❤️*

*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI/RUBUTAWA*


*BY* *KHADIJA* *ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


29~30


Nasreen tace “Wallahi Arifa ciwon ciki takeyi tun dazu nayi - nayi taxo muje clinic taki wai tunda an tashi wai ita gwara taje gida da fatan Malam Isah yazo ?”



“Eh yazo mu karasa naga ta jigata ” futa sukai suka karasa motar da sauri Malam Isah ya futo subhanallahi mai sunan baba ta ba lafiya?



Shiga sukai yaja su da sauri Nasreen ta karasa motarsu,



Tunda suka tafi Zee take ta Jan tsaki ba Wanda ya tanka mata.


_______


“Subhanallahi Amrah ya naga kin kwanta akasa cikin ne ?"daga mata kaina ta yi,


“Toh bari inje in Kira Mama” ta fuce.


Dakin Mama tashiga ta same ta tana waya tana ganin ta ta katse wayar,“ke!!Arifa me zaki wani fadon daki ba nace kuna knocking ba!"me ya faru?


Mama kiyi hakuri Amrah ce tun dazu cikin ta ke ciwo be dena ba...




Tsawa ta daka mata “idoit fuce ki bani guri a kan wannan banzar yarinyar zaki tayar da hankalin ki",



Sum sum ta fice a ranta tana mamakin halin Mamansu hijabin ta tasa ta fice Makotansu ta shiga,



Wata Matace zaune a falo tana kallo Arifa tayi sallama amsawa tayi fuskarta dauke da murmushi “su Arifa manya yau kece a gidan nan? Ina Amrah? Zoki zauna na cika ki da surutu " zauna wa tayi suka gaisa tace“ wallahi Aunty Makaranta ce ta boye mu yanzu ma Amrah ce ba lafiya dan Allah ko zamuje ki ganta tana ciwon ciki",



“Subhanallahi tashi maza muje" futa sukayi direct dakin Amrah Suka nufa yadda ta tafi ta barta haka suka same ta ,



Aunty ta daga ta se sannu suke mata ,



Amrah tace “zanyi fitsari Aunty hafsa ta taimaka mata tashiga toilet din ,



Tana shiga ta fara Kiran Aunty tana kuka ,



Da sauri ta karaso kofar toilet din lafiya Amrah? Aunty naji ciwo jini tuni Aunty ta dago me ke faruwa ,



Taimaka mata tayi ta mata bayani kunya taringa ji ta sunkuyar da Kai,


Sallama ta masu tayi ta tafi harta tafi Mama batasan ma tashigo ba........✍🏻✍🏻




*MORE* *COMMENT*
*MORE* *TYPING* ...✍🏻🖊️



*_Addeejerh❤️_*
*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI /RUBUTAWA*


*BY* *KHADIJA* *ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________

Na sadaukar da page din gareki my granny late hajiya Fatima ❤️Allah maki rahama and Granny hajiya Hadiza ibrahim shamaki💓 Allah kara nisan kwana
Amin.


31~32


*_Two days_*


Amrah ce ta futo daga dakinta akwana biyu duk ta sake ramewa Amma duk da haka jikinta dum dum da ita ba wanda zece yar shekara 16 bace hips dinta masha Allah,



Agogon falon ta kalla karfe 7:30 na safe bawanda ya tashi a lokacin kitchen tashiga ta fara kiciniyar hada breakfast tun kafin mama ta taso,



Da sauri-sauri ta gama hada break din ,



Ta wanke kayan da ta bata ,ta jere kayan a dining bayan ta dibi Wanda zataci zama tayi ta karya ,


Falo ta futa ta gyara tana cikin gyarawa Arifa ta futo tace “Sannu Ya Amrah dame zan taimaka maki?”, ”Ai Arifa nama gama se turaren wuta da zaki taimaka kisa mun",


Toh bari insa .


Se karfe 10am Mama ta sauko cike da kasaita daga gani futa zatai se kwas kwas takalmin ta keyi,



Alhaji jibrin da iyalan sa suna karyawa a dining zama tayi ta Sha tea ,“Daddy yaushe zaka chanja mun waya?" Daddy ya kalleta“Zee Dududu yaushe aka baki wayar ma da har za'a chanza? ”.



Mama tace “haba Alhaji ko ba zaka chanja mata bane ”, “ranki ya dade ba cewa nayi bazan chanza mata ba”


Kallonta yayi “Ke Zee yanzu wacce kikeso a chanza maki?” “iPhone 11 pro nakeso” yace “sha kurumin ki ai kamar a chanja maki",



Tana murna tace “yeahhh" kissing dinshi tana fadin Allah barmun kai Daddy na .



“Amin” ya mike “toh madam zan futa akwai wani abun”


Ita ma mikewa tayi “bakomi Alhaji se zaka sauke ni a gidan Mariya kawata ”,



“Haba Hajiya office fah zani driver ya kaiki”,



“Kagaa Alhaji in bazaka sauke ni ba shikenan !!!”

“ Aaa Hajiya muje ”



Arifa ta masu adawo lafiya ta haura sama,



Sunzo futa suka hadu da Amrah gaishe su tayi Alhaji ne kawai ya amsa ya wuce gun mota Mama tace “ke kuma daga ina?” tana in ina tace da..ma ..naje ...na..gyara..wa ya umar daki ne ,


Ok wuce kuma ki tabbata kin gyaran daki na dana Alhaji ,


Amrah tace “toh adawo lafiya”


Shiga tayi ta fara gyara dining da suka karya tana tunanin sigarin da ta ganin a dakin Ya Umar tana mamakin yana shekara 18 yana Shan sigari kaico!!!,



Haka ta cigaba da aikin ta tana cikin aikin taji horn window ta leka motar Ya Umar tagani dim kirjinta ya buga ,



Juyawa tayi ganin ya nufo falon ,



Shigowa yayi yace “ke" taki amsa wa tayi “ke ina maki magana zaki mun banza ni sa'an ki ne ”,



“To naga ba suna na bane" ta murguda masa
baki ,



“Ni kike wa magana haka?” nufo ta yayi tayi har takai jikin bango tass ya kifa mata mari har seda jin ta da ganinta ya gushe na sakanni,



Arifa da sauko warta kenan tace “haba Yaya me ta ma zaka mareta haka.. tasss itama ya bata rabonta ..........✍🏻🖊️




*MORE COMMENT*
*MORE TYPING✍🏻🖊️*




*_Addeejerh❤️_*


*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI/RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*HAPPY MAULUD*
🌙
Ina yiwa Allum'mar musulmi masoya Annabi Muhammad (S.A.W) murnar zagayowar ranar haihuwar sa.




33~34


Dukansu ya keyi da kyar suka gudu dakin Amrah suka sa key ,



Zuciyar shi na tafarfasa ya futa ciro cigarette yayi ya kunna ya nufi side dinsa,


___________


*_Da_* *_Daddare_*

Karfe 6:30pm ta futo tasha English wears anyi make-up,



Mama tace “Zee Ina zuwa haka ?ansha kwalliya ne", “kar dai Mama kin manta zanje birthday din khairiya”,



“Ohh yar nan haka ne jeki bangaren Umar ki kira mun shi yazo ya kaiki",



Futa tayi ta shiga bangaren sa dake da dan tazara da side insu ,



Knocking tayi taji shiru kofar ta bude falon taga wayam dakinsa ta nufa nan ma baya nan se taji zubar ruwa a toilet da alamu wanka yakeyi zama tayi akan couch tana charting sedai tayi wajen 15 minutes a zaune sannan ya futo,tsawa ya daka mata “Me kike a daki na?" ”Yaya dama Mama ke kiran ka" ”toh jeki kice ina zuwa bari na shirya" futa tayi.



Tana zaune ta gaji da jira se turo baki take,



Shigowa yayi yace “Mama gani ance kina kira na" ,“Ehh na Kira kane zaka kai zee birthday kawarta"



“Haba mama taje driver ya kaita mana yarinyar Dan ta rainani ni zan kaita",




Kamoshi mama tayi jikinta “Haba baba na kayi hakuri ka kaita",



Mikewa yayi “to tayi maza ta same ni a garage" ya kalli agogon da ke daure a tsintsiyar hannunsa nanda 10 minutes “In ke kuma baki futo ba zan fasa kaiki”,


Fucewa yayi tana jin haka da sauri sauri ta bishi dama ta gama shiryawa suka tafi suna hawa kan titi ya kunna waka yana shatata gudu Zee se danna waya takeyi ,



”Ke ina ne gida?" Kwatance ta masa gani yayi ya ma San layin,


Yana sauketa ya fara bunkawa cikin sa hayaki wayar shi ya dauka wani number yayi dialing ana dagawa tace “J-boy ganinan fah a hanyar gidan ku kwana biyu bamu hadu ba"



Shekewa yayi da dariya yace “ kace old man yana gida”


Karasawa yayi kofar gidan yace gashi ya karaso“ ka futo kar ka batan lokacin” ya kashe wayar,


Futowa yayi yana waiwaye motar ya shiga suka tafa yace “J-boy kwana biyu nasan ba ku hadu ba gashi kadan kora ko kaji relief" dariya yayi yace “ wallahi kamar kasani ai da old mana yadowa shikenan yanzu ma ya kwacen key din mota”Kyalkyalewa Umar yayi da dariyaa....✍🏻🖊️




*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* .......✍🏻🖊️




*_Addeejerh❤️_*



*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI/ RUBATAWA*


*BY KHADIJA ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
Na sadaukar da page dinnan gareku Fans din 👩‍❤️‍👨FANSAN RAN MAHAIFANA👩‍❤️‍👨Group 1&2

35


Se wajen 11pm Umar ya koma gida yana shiga yaga Mama kadai ce a zaune tana kallo,



Kallonshi tayi tace "Haba Umar ba sallama kawai ka fadon ka wani tsoratani",


Shafa kansa yayi yace “Sorry Mama nafa yi sallama sedai in bakiji ba”,

“ okay"


“Mama Zee ta dawo?"kallonsa tayi tace “A'a bata dawo ba kawarta takira ta rokeni in barta ta kwana da safe zasu kawota ”,



“Toh Ina yarinyar nanne? zanje inyi wanka ta kawo mun coffee side dina",



“Ok Son seda safe" fucewa yayi bayan ya mata peak.


Amrah ta kwala mata Kira da sauri ta futo,


Tace “gani coffee Zaki hadawa Umar ki Kai masa side dinsa",





Tace “to" kitchen ta wuce a cikin 7 minutes ta gama hadawa ta nufi side dinsa,



Tana tafe gabanta na faduwa knocking tayi taji shiru tafi minti biyar a tsaye gashi tana jin tsoro taga 11:15 tayi,



Tana cikin tunani taji ance “come in ” tace shi Kuma wannan lafiyar sa kalau muryar shi a shake tabe baki tayi tace “ko Ina ruwa" na shiga tayi tana shiga warin sigari ya doki hancin ta kallon shi tayi tace ”Innalilllahi",



Yana zaune yana busa sigarin sa,


“Ke!!!dallla malama kin wani kura mun idonki kamar mayya",


Jikin na rawa ta ajiye akan table ta juya da sauri-sauri ta shiga side dinsu ta tarar Mama har ta hau sama addua tayi ta rufe kofar ta wuce daki....


__________


*_Washegari_*


Amrah ce a zaune a parlour tare da Arifa suna kallo Zee na sama tana bacci tunda ta dawo ,



Suna cikin kallo sukaji Sallama,


Amrah ce ta kalli kofa a guje ta mike tana murna “Oyoyo Nasreen" suka rungume juna,



Ta rike hannun ta suka karasa falon gaisawa sukai Arifa ta mike ta shiga kitchen,



Hannun ta rike da tray ta dawo dire shi tayi a gaban Nasreen,



Nasreen tace “Nagode" Arifa zama tayi aka cigaba da hirar da ita “kefa Amrah gidan Yaya Hayatuddeen zanje kinsan tunda akayi auren sau biyu naje Aunty Suwaiba tana cewa inje kema tace kuna kusa baki zuwa",


Arifa tayi murmushi tace “Dama wallahi mungaji da zaman gida Amrah tunda Mama bata nan kawai muje da la'asar ma dawo",


Amrah ce ta kama baki “ke Arifa la'asar kika ce fa in Mama ta dawo fa",


Dariya su Arifa sukai suka hada baki gurin cewa “Allah Amrah kin fiye tsoro",



“Naji toh ku tashi mu tafi",



Futa sukai suka zaga bayan layi..........✍🏻🖊️



*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* .......✍🏻✍🏻

_Assalamualaikum ya kuke da fatan kuna lafiya,yadda naga comment dinku yasa ni nishadi shiyasa nace bari in faranta maku rai_ 👏🏻

_Farin cikin ku shine nawa_ 😇🥰


Bissalam👏🏻


*_Addeejerh❤️_*


*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨




*LABARI/RUBUTAWA*




*BY KHADIJA ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*


Na sadaukar da page dinna gareki Mama hajiya Amina Abdu Ahmad ❤️much love🤍


36~37


Suna k'arasawa k'ofar gida Nasreen ta samo dutse tayi knocking kusan 4 minutes ba a bud'e ba,



Sai gashi wani Dattijo ya bude kofar, washe baki yayi yace ”Hajiya Karama ke ce dama ki min Afuwa na d'an kewaya ne", tace “bakomai Baba Habibu" ta kalli garage din tace “Baba Yaya bai fita bane?"

“ Ehh wallahi "



“Okay"suka karasa ciki,



Da Sallama suka shigo tana zaune a falo,

Amsa sallamar tayi tana murmushi, karasowa suka yi suma da fara'a d'auke a fuskar su gaisawa sukayi ,



Tace “Yau gidana yayi Albarka tunda naga Hajiya Amrah a gidan, muna kusa Amma bata shigowa da cewa ma nayi bazan kulaki ba ai",



Murmushi tayi tace “Aunty suwaiba kaina bisa wuyana" ta fad'a tana had'e hannunta alamun ban hakuri , ta d'ora da fad'in, “Aunty kinsan abubuwa sun mun yawa gashi sam ba'a barinmu muna fita",



“Nasani" Murna ta ringa yi ta rasa inama zata sa su ta cike masu gaba da kayan ciye-ciye sai nan nan take dasu,



__________



*_Some minutes later_*



Nasreen ce ta hade rai tace “Yaya kanajin mu sai yanzu ka fito",



“Haba Autar Ummi sorry wanka nayi"


“Okay Yaya, gaishe shi sukayi",


Kallon Amrah yayi yana tafa hannun yace “Yau kece a gidan mu ba'a ganin ki sai da Aminiyar ki dama ita Arifa sai da ke ita ma ake ganinta",



Murmushi kawai tayi,


“Autar Ummi yaushe zaki tafi" kallon shi tayi tace “Au Yaya kora ta ma kake"



“A'a fa ba haka nake nufi kawai inason mu tafi tare zanje gaishe da ummi ne"


“Okay",


Aunty Suwaiba tayi murmushi tace “rabu da shi kanwa ta in ma kwana zakiyi Ina ruwansa ",



Zama yayi aka cigaba da hira dashi,



Chan Amrah tace “ke Arifa kinga an fara kiran sallah, ki taso mutafi",



“Yaya Amrah bafa abunda Mama zatayi mana",


“ A'a ni dai gara mutafi"


Yaya Hayatuddeen ya shafa kansa yace “gaskiyar Amrah bari nayi sallah sai mu tafi tare ya Mike ya tafi masallaci ",



Su kuma sukayi tasu a gida yana dawowa suka Mike zasu tafi Suwaiba ta shagwabe, yace “meye kuma my subee?",


Wasa ta fara da zoben hannun ta tace ,“dama ina so in bika ne in gaishe da Ummi",



Kyalkyalewa yayi da dariya su Nasreen ma sai da suka dara yace “Akan hakane zaki mun kuka dauko himar dinki"



Ai da gudu ta shiga daki da karfi Nasreen “tace kar dai a mana asara" tana murmushi, Yaya ya kai mata duka yana fadin “Autar Ummi baki da kunya",



Har kofar gidan suka sauke su Allah ya taimake su Mama bata dawo ba,


Suna shiga daki sukaji ana knocking dum! gaban Amrah yayi,



A rude Amrah ta fito, bude kofar tayi , tana zaro ido,



Tace “Sannu da zuwa Mama"


“Ciwo nake da zaki min sannun?" “Zee ai tace min kun fice yau sai kin fada min gidan uban wa kukaje............✍🏻✍🏻





*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* .....✍🏻🖊️




*_Addeejerh* ❤️_


*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI /RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*



Na sadaukar da page dinnan gareki my inlaw Aunty fatima😂🥰( khalifatti)❤️

38~39

Zane ta tayi sosai tace “Ina ita ma wannan yarinyar take Arifa!! Arifa!! Arifa!!" tana kwala mata kira,

Na'am ta amsa ta futo duk ta firgice tace “Gani Mama ",

“Ina kiranki kin mun banza ko ? Uban me kike a dakin?" tana tsare ta da ido,

Cikin in Ina ta ce “Da..ma.."bata k'arasa ba ma ta rufe ta da duka tana fadin “Kedai yarinyar nan Sam baki da hankali da tunani nidai badan wani abu ba se ince chanja mun ke akayi",

Cikin kuka Arifa tace “Dan Allah kiyi hakuri" ko saurarar ta batayi ba ta cigaba da dukan su gajiya tayi dan kanta ta rabu dasu

Kuka suke yi ba mai rarrashin juna,
____________

*1* *YEAR LATER*


“Assalamu Alaikum" haka tayi ta sallama ba Wanda ya amsa,

Shigo akayi mama ta maida kallonta kofa a gadare tace “Ke Yana kin takura mun da zuwa gida",

“Ke kinga Sa'a ba neman fitina nake ba se kace ba Musulma ba ana sallama ki ki a'msawa ".

Amrah taji muryar Aunty Yana tayi maza ta futo Sannu da zuwa tayi mata suka gaisawa zasu shiga dakinta har sun Kai kofa,

Mama tace “Hmmm za'ayi abunda aka saba" Yana ta bude baki kenan zata bata amsa Amrah ta bata hakuri,

“Da ki barta mana ta fadi abunda zata fada ",

Amrah ta kama hannun Auntyn ta suka shige daki,

Suna zama Amrah tace “Ina uncle? na zata tare zakuzo?" Yana tace “Wallahi ya so zuwa kinsan yanayin aikansa"

Amrah tace “Hakane Allah bashi sa'a",

“Amin rabin raina",

“Sannan zan ma fada maki da tuni na manta na tafi",

“An tura Uncle dinki Jigawa zai je yayi wani aiki ina tunanin tare zamu tafi ma Amma ba dadewa zamuyi ba in ban tafi ba nanda wani satin amma in kin ji ni shiru mun tafi da mun dawo zanzo",

“Toh aunty Allah taimaka",

Yana tace “Amin".

Kare mata kallo Aunty Yana tayi tace “Rabin Raina lafiya kuwa duk naga kin rame ga damuwa fal a fuskarki",

Amrah tace “Aunty bakomai fa",

Aunty Yana ta hade rai “Ba zaki fada mun ba?" sassauta muryar ta tayi tace “ko bayan ni kina da Wanda ya fini da zaki fadawa matsalarki?"tayi saurin girgiza kanta ,

Aunty Yana tace “Yauwa fada mun mene",

Tace “Dama Aunty ya Umar ne ya ke mun wasu abubuwa da bangane ba kuma wai yanaso na nace ni banson shi wai wallahi sai na so shi kuma ze fadawa Mama da Daddy..... bata karasa ba Aunty Yana ta kundumo ashar tace “Bari inje in fara ja wa Uwar shi kunne kaga Dan iskan Yaro" ta dauki jakar ta tana banbami ta futa falo tana futowa ta ga Maman na saukowa

Tana karasowa cike da masifa Aunty Yana tace “kija wa yaron ki kunne ya futa harkar Yarinya ta" ko saurarar mai zatace ba ta fuce fuuuuuuuuu

Amrah na rakube jikin bango se zare ido take daki ta koma da sauri tasa key ta Mama sai muzurai take.........✍🏻🖊️


*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* ✍🏻🖊️




*Addeejerh❤️*


*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI/RUBUTAWA*


*BY KHADIJA ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


40~41

*_Bayan kwana biyu_*

“Umar wai kai an fada ma amrah ce kadai mace a duniya da zaka nace se ita iyee?"



Daga masa hannu yayi yace “Kaga Daddy kai ma fa sanda za kayi aure haka aka ma dan nace
Ina sonta se a hanani"



Alhaji jibrin ya Mike ya isa gabansa tass ya wanke sa da mari yana fadin “Ni zaka kalla ka fada mun maganar banza",



Umar yace “Na fada din".


Alhaji Jibrin ya daga hannu kenan ze sake Marin sa Mama ta rike hannun tana fadin “Haba Wai sai kayi ta Marin sa akan wata banzar Yarinya Dan kawai yace yana sonta shima ko me abun sonta ya takura kansa akanta",



Alhaji jibrin ya koma ya zauna be ce mata kala ba,

Umar ya fuce ya barsu a parlourn.

___________

*2 hrs later*


Amrah ce take gyara a dakin Alhaji jibrin ta bude bedside drawer din kenan se wasu zoben gold suka fado da sauri ta dauka tana tunanin Ina ta taba gani zobu nan karami da babba da wani tag a jiki a daure tana dubawa taga sunan ta da na abbiey dinta,



Mamaki take ina aka same su ,



Bata karasa mamaki ba seda taga wasu takardun filaye na Abbiey,


Dumi taji a kuncinta shafawa tayi taga Ashe kuka take maidawa tayi ta cigaba da gyaran ta tana sake sake a zuciyarta,


Tana gamawa ta fuce ,


Direct kitchen ta nufa ta dora girki,



Arifa ta shigo kitchen bakin ta dauke da sallama Amrah ta amsa ,


Arifa tace “Sannun yaya Amrah tace Yauwa arifa” Kama mata tayi suka karasa,


_____________


Ke!! ke!! ke!! Amrah na jin haka ta futo da sauri tace “Na'am gani Mama" ta zauna a kasa kusa da kafar maman ,



Mama ta kamo kunne ta kara tayi tana oshhh Mama tace “kinaji ina fada maki Umar yace yana sonki ki ka wani ce wai baki sonshi dama kin samu yana sonki shegiya
Yarinya",



Amrah ta tashi rike da kugu tace “Ba mai mun dole nace din bana son shi din kuma bazan soshi ba ehee!!" ta murguda baki,


Mikewa Mama tayi ta shako ta tana “Fadin ni kikewa fadawa?haka Mara kunya" ta tsinka mata mari ta hankada ta hannunta ya bige da center table tasa kuka,



Barin ta Mama tayi ko damuwa ba tayi da halin da take ba
Ta haura sama,



Amrah ta lallaba tashiga ta dauko himar dinta a lokacin Arifa na bacci a dakinta



Da sauri ta fuce tana kuka mai gadi na mata magana ta masa banza ,



Titi ta karasa ta tari Adaidaita ya kaita kundila a kofar wani madaidaicin gida ta sauka bashi Dan kudin da take tarawa tayi,



Mai gadi ne ya taso ganin tana kuka yace “lafiya yar nan ?",



Ba tace masa komai ba yace to gashi kuma Hajiyan basa nan dazu da sassafe su kayi tafiya,



“Nima kuma yanzu tafiya zanyi”



Ya shige ya kulle k'ofar gidan ya juyo ya kalleta yace “Amratu ya baki tafi ba?" tace “Malam ayuba hutawa nake zantafi",


Girgiza kanshi yayi yace nidai na tafi Allah bamu Alhari ya kama hanyarsa,


Tana nan a zaune taji anyi horn taki dagowa aka sake yi ,


Assalamu Alaikum" nan ma shiru da wata zazzakar muryarsa yace “Baiwar Allah lafiya kina zaune anan har naje na dawo kina zaune ko wasu kike jira?" Jim yace “ke ko kurma ce?",



Amrah ta dago da jajayen idanuwanta bude baki tayi da shakakkiyar muryar ta tace “Gidan Aunty na nazo bata nan sunyi tafiya ne,



Kare mata kallo yayi yace “To taso in maida ki gida",


Ta girgiza masa kai,


Ganin a tsorace take tace “Karki ji tsoro ni ba abunda zanyi maki gida kawai zan kaiki"
Tashi muje ,


Tace “A'a ni bazani ba nidai in naje kashe ni za tayi Allah",



Mamaki yake wace zata kashe ta ,


Be tsaurara bincike ba yace “To shikenan taso muje gidanmu se in maida ki gida ba abunda zata maki",


Zo muje mikewa tayi ,



Kallonta yayi yaga ta na yamutsa fuska tana makale hannu,



Yace “lafiya meya samu hannunki ?"


A hankali tace “Faduwa nayi",



Girgiza kansa yayi yace “Muje asibiti to",


Suka shiga mota suka tafi.........✍🏻🖊️



*MORE COMMENT*
*MORE TYPING.......* ✍🏻✍🏻



*Addeejerh* ❤️


*FANSAR* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI /RUBUTAWA*



*BY KHADIJA ADAM IDRIS*


*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


42~43

Suna shiga asibiti yayi dialing wata number ana dagawa yayi sallama gaisawa suka yi yace “Doctor Mutallab ga ninan a asibitin ku nakawo wata patient”
Ko me yace ohoo yace Ok bari muje office mu jira ka".


Kallonta yayi ta cusa kanta a cinyarta shidai yarinyar na bashi tausayi yace “Tashi mu shiga ciki" dago kanta tayi idanuwanta jajir dasu tunda suka taho take kuka,


Ciki suka shiga a saman 'kofar Ansa Dr Mutallab Muhammad,



Shiga sukayi 10 minutes da shigar su ya shigo suka gaggaisa,



Dr

1 Comments On FANSAN RAN MAHAIFANA
avatar
khadija-1-2-5

9 months ago

Reply

Tnx

Please Login or Register in order to submit comment