Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fiye zuwa ba saboda samun goyan bayan iyayenta.


_______________


Maiduguri

Ranar sadakar uku da daddare mutane duk an tattafi se na jiki.

Hajja Falmata ce da yan'uwanta a ɗakin Umma suna tattaunawa.


Alhaji Ali ya ce“Ni dai a gani na tunda bai fi saura wata biyu auren Yana ba, se Kawai ta zo ta zauna a gidana tunda a Maiduguri za a yi biki nake ga se ya fi, amma ku me raayinku? "


Ammi ta ce “Amma yaya wani hanzari ba gudu ka ga a halin yanzu Yana tana cikin damuwa ta bini Kano za ta fi samun kwanciyar hankali da nutsuwa ba kamar a nan ba"

Duk sunyi na'am da shawararta.

Alhaji Ali ya Kara da “kun ga yanzu gidan nan a shawara ta meze hana a sanya haya tunda ba mai zama, sai ina kula da shi tunda ina kusa ya kuka gani ?"

Ya Nukura ta ce “ Ni ma dai haka na gani tunda in an bar gidan ba kowa shedanu za samu gurin zama ba asan kuma me zai faru ba"

Duk sun amince.

__________
Kano

Amrah ce a class an fita break suke hira da Nasreen


Amrah tace “Allah Nasreen gidan uncle jibrin ba dadi kwata- kwata har na matsu Abiey su dawo kina kallo kullum mama indomie take samun a lunch box tunda ta fuskanci bana so ko na fada ma uncle ba ya mata magana shi kanshi ba ya kulani sosai Arifa ce kadai muke shiri"

Nasreen ta ce “tab "

“Nasreen kinga zee ran nan zata mun hauka mu kai fada na fasa mata hanci hakoranta biyu sai da suka cire ”,

Tafawa sukai Nasreen ta fashe da dariya tana cewa
"Amma besty kin birgeni dadi na dake ba ki son hauka."

Wata yarinya ce ta shigo tana “Yeeee ka ga manyan yara duk wanda ya taɓo ku, ya tabo wa kansa, ku wuta ne a taɓa ku a ji zafi." Haka ta cigaba da yi masu kirari.

Amrah“ tace Fatima kin shigo"


"Ehh wallahi na shigo." zama ta yi suka cigaba da hira..........



_____________
Maiduguri
Washegarin sadakar bakwai ranar kowa zai tafi. Karfe 10:05 na safe Abiey shi da Alhaji Ali don a gidansa ya sauka


Yau za su tafi gida flight za su bi saboda malam idi tafiya ya yi saboda kai Amrah school.


Sallama sukai suka nufi airport Alhaji Ali ya sauke su har sai da jirginsu ya tashi ya koma gida tunda suka tafi Yana ke ta kuka......... ✍🏽✍🏽✍🏽

*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨



Story
And
Writing


BY

*KHADIJA* *ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*



Na sadaukar ga Wannan page din gareku masoyana a duk inda kuke Ina alfahari daku❤️❤️Ina godiya


09-10

____________
Kano
Bayan su Ammi sun dawo aka dauko Amrah tayi murnar dawowar su bare ma da taga an taho da Aunty Yana.




Washe gari

Da safe bayan Alhaji ya gama karyawa, office ya je domin ya ga me ke wakana, yana zuwa ya tarar komai ya taɓarɓare, wasu kuɗin sun ma ɓata.



********

Su Ammi ne dukkan su a kan dinning da daddare, Ammi ta ce “Wai yau Alhaji naga ka daɗe a office ko lafiya? Nasan dai ba wani aiki tunda jibrin na nan”.

Ajiye spoon dake hannun sa ya yi ya ce “To ai Falmata da zaman jibrin da babu duk ɗaya ne".

"Meyasa ka faɗi haka Alhaji?".

Ajiyar zuciya Alhaji ya yi sannan ya nun fasa ya ce "Ya za ai bazan faɗi haka ba Falmata, bayan da jibrin din a wajan har naje na naimi wasu kudade narasa".

Cikin kulawa Ammi ta ce "Alhaji ka da duba da kyau kuwa?".

"Wallahi na duba, nayi iya bincike na amma ban gansu ba, naira dubu ɗari da hamsin bangani ba.”

“Innalillahi Wa inna ilaihir rajiun!" Abunda Ammi ta iya faɗi kafin ta ɗaura da faɗin “Yanzu jibrin a wajan aka yi wannan taɓargazar".

"Ga zahiri kina gani".

Taɓe baki Ammi ta yi cike da mamaki, ta buɗi ba ki, za ta yi magana.
Sai kira ya shigo wayar Abiey ɗaukar wayar ya yi tare da tashi ya kara a kunnen sa ya hau stairs yana amsa wayar.


__________
Alhaji jibrin ne
Zaune a falo wanda ya tsaru da kayan ado na zamani, Daga duk kan alamu zaka tabbatar da yana cikin farinciki, baki washe ya ce “Sa'a ke kam ina ba ki labari Yaya Abdulmunaf ya na nan yana binciken ta ya aka sace wannan kuɗin ".


Sa'a murmusawa ta yi wanda ya bawa damar hakwaranta fitowa waje ta ce "Haha Alhaji ai kuɗi kam har sun tafi inda ake bukatar su, na tura wasu Inna sai dai ya yi hakuri" ta ƙare maganar tana shekewa da dariya.



___________
*Bayan* *kwana* *uku*


Alhaji Abdulmunaf ya yi iya binciken yadda akayi kudin suka bata an rasa ganewa haka ya hakura ya fauwalawa Allah.


__________
Ammi ce dake zaune a falo, ta shiga kwallawa Amrah kira.


Daga sama Amrah jiyo kiran, amsawa ta yi da iya karfinta tare da fitowa daga ɗakinta ta sakko ƙasa.

Ammi tsare ta da ido ta yi kafin ta ce “kina ji ina ta kwala maki kira, dan raini hankali baza ki amsa ba".

Saukar da kai ƙasa ta yi murya a sanyaye ta ce "Ammi kiyi hakuri, wallahi na amsa".

"Ok, Ina fatan Kin gama assignment ɗin ki? "


Cikin sanyi murya Amrah tace "Ehh nagama".

Ammi ta ce “Yauwa Amrah dan Allah ki ringa jin magana kinji ni". Gyaɗa kai Amrah ta yi nan Ammi ta ɗaura da faɗin "Ki shirya zamu futa daga can zamu biya mu yi shopping "

Cike da farin ciki Amrah ta ce "To" Ɗan rawa ta yi ta juya sannan ta ce "Yeeeh sai Ammi na". Tana faɗan haka ta haura sama cikin farin ciki domin fara shiryawa.

Ammin bin ta da kallo ta yi tana murmushi, tana jin son Yar ta na karuwa cikin zuciyarta.


__________
*After* *some* *hours*


Su Ammi sun dawo ba lefi sunyi zagaye sosai ,



A yan kwanaki har Yana ta dan sake dan ba lefi hajja Falmata na zagayawa da ita kuma bata yarda Sam ta zauna ita kadai ba aguri saboda tunani... ✍🏽✍🏽✍🏽





MORE COMMENT
MORE TYPING.......... 📝🖋️



Kuyi manage👏👏 pls da Wannan banjin dadi ne

👩‍❤️‍👨FANSAN RAN MAHAIFANA👩‍❤️‍👨



Story
And
Writing

By

*KHADIJA* *ADAM* *IDRIS*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/
group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*



Na sadaukar da page dinnan ga Hauwa hadi Kawata and Halima hadi Kawata much love sisters❤️✨wannan page naku ne kuyi yadda kuka ga Dama dashi💃


11~12
*Washegari*
Amrah ce a dakinta tana ta bacci da yake weekend ne ba school.



Ammi ce take saukowa ta kalli Yana da ta kunna kallo amma hankalin ta Bayan gurin kallon ma, harta karaso gunta batasani ba taba ta tayi firgigit ta kalleta ta wayance tana fadin“ yaya har kinsauko? ”



“Na sauko mana taya zaki sani kina nan kina sawa kanki tunani so kike ki sawa kanki ciwo ne hakuri zamuyi adduar mu Umma take bukata a halin yanzu Allah daya bamu ita shiya karbeta" tuni idanuwan ta kwalla ta taru,



Yana ta fashe da kuka Ammi ta rungumeta tana shafa bayanta Yana ta fara magana tana cewa yaya falmata na rasa yadda zanyi ne na saba da Umma komai tare muke mu kwana tare har unguwa tare muke zuwa” kara fashewa tayi kuka sosai ta karyawa Ammi zuciya tasa kuka aka rasa me rarrashin juna.



Alhaji ne yashigo ya tarar dasu “haba falmata ya zaki sa Yana a gaba kuna kuka keda zaki rarrasheta a halin yanzu adduar mu Umma take bukata ”



Ammi ta share hawayen ta masa sannu da zuwa Yana ma ta masa ya amsa da yauwa,



Ammi tace “Alhaji ya na ga kadawo gida yanzu ko lpy? "


Kansa ya shafa yace ”wlh falmata mantuwa nayi wani file na manta gashi an kusa shiga meeting karfe 1:00 pm”agogon ta ke daure a tsintsiyar hannunshi ya kalla yace “gashi har 12:23 pm dan Allah ki sauri ki daukon
yana bedside drower nakusa da reading table Dina a kasan wata jarida "


Amsawa tayi da toh ta nufi sama dan cika umarnin sa shikuma ya zauna yana yi wa Yana nasiha.



Ammi ce ta sauko cikin ladabi ta mika masa ya amsa tashi yayi ze futa rakashi tayi suna futa ta tambaye shi anjima zata gidan jibrin ya shiga motar yana cewa “toh sekun dawo ki dau kudi a gefen kayana ki sai wa yaran tsaraba”.


Ammi tace “toh mungode Allah kara budi Allah kiyaye hanya ”


Amin.
Lokacin har an bude masa gate har seda ya fice ta koma cikin gida.


_________
*3hrs* *30* *min *later*

Amrah ce ta sauko cikin shirin ta na islamiya kalar din uniform din milk.



Ammi ta kalleta cikin so da kauna tace “inyeeh Amran Ammi ta fara girma har kin shirya ".



“Eh Ammi na shirya ".


Ammi tace“ da kyau ai Yau kinsha bacci Se aje aci abinci ",



Toh ta wuce dining taci abincin ta tafi islamiya Bayan su Ammi sun mata Allah bada saa.


Ammi ta kalli Yana tana fadin “in an yi laasar zamuje gidan sa'a naga ita bata da alamun zuwa ni inje kinga Amrah taje bamuje ba dauko ta akayi ”




Hade rai Yana tayi tace “haba yaya ita batazo ta maki gaisuwa ba Se ke zakije,ga matar tayi ta wa mutane kallon banza ni na tsani matar kuma Se me dan sun rike amrah na kwanaki
Ai ita dolensu ce su riketa ko ba ku ”


Ammi tace “ kome tayi ta je dan kanta nidai zanje ”

“Amma wlh Yaya hakurin ki yayi yawa ni bazan iya ba wallahi tana fadin haka ta haura sama”,

Girgiza kai Ammi tayi ta bita da kallo.

_________
*Bayan* *la'asar*


Su ammi sunje gidan jibrin suna knocking aka bude masu Arifa ce ta bude tana ganin Ammi ce ta rungumeta tana murna tace “Ina Amrah? ".

Ammi na murmushi “tace tana islamiya ku meya hana ku zuwa "?.


Arifa tace “kaina ke ciwo yaya zee tace baza taje ba ” zama sukai Ammi tana kallan zee da ko albarkacin gaisuwa basu samu ba.


Arifa tashiga dakin mama ta fada mata su Ammi sunzo.


Zee seda taja tsaki sannan ta gaishesu Ammi ce Kawai ta amsa ta kallonta cike da mamaki tashi tayi tashige daki.



Sunan azaune har minti kusan talatin hajiya saa bata futo ba.


Yana tace“ ki taso mu tafi dan aikin banza se ta wani shanya mutane,


Kafin Ammi tayi magana mama futowa da isa ta zo ta zauna a dakile suka gaisa se cin magani take,


Chan tace“ falmata ya hakuri "

Ammi tace “da godiya "

Ba wanda ya sake magana acikn su.

Chan Ammi ta tashi zasu tafi tare da ajiye ledar hannunta tace a bawa su Arifa ko kallon ledar batayi ba tashige daki.


har garage Arifa ta rakasu anan suka hadu da umar shekeke ya gaishesu ya wuce.


Arifa tace “a gaishe da Amrah ",

Da toh Ammi ta amsa suka tafi.



Tun hanya Yana take ta mita har suka karasa gida......... ✍🏽✍🏽✍🏽



MORE COMMENT
MORE TYPING............ 🖋️✍🏽


Daga alkalamin khadija💫

*FANSAN* *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨


*LABARI* / *RUBUTAWA*



*BY* *KHADIJA* *ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


Na sadaukar da wannan page din ga dokacin yan kainuwa writers💃

13~14

Yau su Ammi suka nufi Maiduguri sakamakon gobe ne sadakar 40 din Umma wannan karan harda Amrah aka tafi an masu hutun makaranta.


____________
Maiduguri

Su ammi basu Dade ba suka isa Maiduguri saboda flight suka biyo,


Sanda suka je gidan Umma suka Tarar da matar Alhaji Ali Aunty safiyya tare da masu aiki suna gyara sannu da aiki su kai masu .


Aunty safiyya ta tare su ba lefi ta basu abinci lafiyayye .


Bayan sun Huta sunci abinci suka zauna a falo,Aunty safiyya ta kalli Yana tana tsokanar ta tana fadin kaga amaryar wani satin .

Yana cikin kunya tasa mayafin jikinta ta rufe fuska tana murmushi ,dukansu dariya suka sa mata .


A guje ta tashi ta bar masu falon ta nufi dakin Umma tana shiga ta fashe da kuka tunowa da Umma Haka tasha kuka har barci ya kwasheta.


________
Amrah an samu yara Ana ta wasa se murna take ta ma manta da Ammin ta.

Horn akayi me gadi ya bude Ya nukura ce da nata tawagar suka iso ai nan gida ya kara kacamewa ba abunda da ake ji se hayaniyar yara.

Sanadin hayaniyar yaran ya tashi Yana futowa tayi falo zama tayi kusa da Ya nukura suka gaisa kallonta Ya nukura tayi tana kare mata kallo tace “Yana kinga kuwa yadda kikai kyau kuwa kinyi kiba cikin dariya tace da alama su falmata sun iya kiwo" kallon Ammi tayi tace “falmata kin fara mata gyara ko?, gashinan na taho da wasu kayan gyaran jikin wata Yar Sudan ta hada mun.


Ammi tace“ yauwa Yaya wallahi gwara a gyara yarinyar nan kwata - kwata bata son gyaran shiyasa nace in munzo kila in kinsa ta a gaba ta tsaya ".


Aunty safiyya tace“ nima nasa an hada mun kaya anan Maiduguri dasu humra ”


Yana ce ta tabe baki kamar zatai kuka tace “ni ai gyaran se yayi yawa dan Allah ku kyale ni haka"


Hararar ta Ya nukura tayi tana fadin“kaniyar ki nace Yana na kula Sam bakisan ciwon kanki ba Ina gyara yake yawa shasha Kawai ki tsaya Yan matan kano su kwace maki miji, badai saura sati daya ba bikin tare ai zamu tafi se Bayan biki".


Yana ce ta chuno baki tana kunkuni,

Ammi tace“ banza da bata san ciwon kanta ba ”.


Shiru tayi tana danna wayarta bata sake magana ba.


Haka sukaci gaba da hirar har su Alhaji ali da Abbiey suka shigo aka cigaba da hirar,


Abbiey ne yace “tunda munje munga gida dakuna uku ne falo biyu da kitchen ni na dauki nauyin yin kayan dakuna biyu da falo ahalin yanzu ma na bada Oder kayan ”

Godiya sukai masa har seda yace godiyar ta isa.

Alhaji ali yace to ai Alhaji yayi yawa da karage mu ma munyi aikin ladan.



Hade rai abiey yayi yace “ai nima Yana kanwa ce aguna Kome na mata banfadi ba ”

Alhaji Ali yace“ hakane to nima na dauki nauyin daki dayan da falon ”



Ya nukura tace “ni kuma na dauki nauyin yin kayan kitchen”.

Aunty safiya tace“nima ba za a barni a baya ba Nima na dauki nauyin dinner da za'ayi ”,


Yana ce tasa kuka ganin tana da gata bata rasa komai ba.


Ba Wanda yayi kokarin rarrashinta dan sunsan kukan farinciki takeyi.

________
*Bayan* *kwana *2*
Anyi 40 lafiya Yau kowa ze koma masaukinsa su Ammi ma Yau zasu koma bikin Yana ya karato tare zasu tafi tare da Ya nukura da iyalanta domin da niyar biki ta taho flight suka bi.


*_Kano_*
Karfe 4 na yamma su Ammi suka iso .

________
Da daddare Ya Nukura tasa Yana agaba se ta shanye wani magani.


Tana yamutsa fuska ta fara sha seda ta shanye ta ajiye roba tace“Yaya in da wani ki karan yana da zaki Wanda yaya falmata ke bani ba dadi wallahi”.




Hararar ta tayi“ baza a Kara ba uwar shan zaki Yana Ina kwabar ki da shan zaki yana da illa sosai ”


Tashi ki shiga toilet na hada maki ruwan wanka toilet ta daura tana shiga toilet din wani sihirtaccen kamshi ya ziyarce ta tafi rabin awa acikin ruwan daga bisani ta futo.



Futowar ta kenan Wayarta ta fara ruri da sauri ta daga Wayar ganin sweetheart ke yawo akan screen din,


Dagawa tayi tana fadin “Assalamu Alaikum sweetie na ya kake ko me aka ce a dayan bangaren ta kyal-kyale da dariya tace haba sweetheart me kake ci ne na baka na zuba nanda kwana biyar zan zama taka har ka gaji da ganina hira sukai sosai sannan sukayi sallama cike da so da kauna.


*_Washegari_*
Alhaji ne a office dinshi duk ya Tara ma'aikatansa sakamakon rasa wasu kudade da akai akalla kudin yayi 2.5 million........... ✍🏽✍🏽✍🏽


MORE COMMENT
MORE TYPING...... 🖋️✍🏽

*Assalamu* *alaikum* *ya* *kuke* , *ya* *gida*, *ya* *yara* *da* *fatan* *duk* *kuna* *lafiya* 😇 *Allah* *sa* *hakan* *kwana* *biyu* *zakuji* *ni* *shiru* *banjin* *dadi* *se* *kuma* *wayata* *ta* *dan* *samu* *matsala* *yanzu* *ma* *manage* *nayi* *na* *maku* *Wannan* *wallahi* *I* *hope* *Zaku* *karbi* *uzuri* *na* *bissalam* 👏



*_Addeejerh_* 🥰

*FANSAN *RAN* *MAHAIFA* *NA* 👩‍❤️‍👨




LABARI/RUBUTAWA



*BY* *KHADIJA* *ADAM* *IDRIS*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
Wannan page naka ne babban yaya Harisu Adam idris much love ❤️💖💫

15~16
Abbiey yayi iyaka bincike an rasa yadda akayi aka rasa kudin an duba har CTV cameras ba abun da ake gani.



Da ya koma gida ya sanar da Yan gidan kowa ya taya shi jimami.

*Bayan* *kwana* *uku*
Yau biki saura kwana biyu Yan uwa daya sunzo Yau su Aunty Aysha da Aunty sumayya tunda suka zo basu zauna ba Ana ta zurga -zurga.


Da daddare a dakin Ammi Ana ta hirar yaushe gamo,


Ammi tace “wallahi yau dinnan tun azahar zuciya ta take bugawa bansan me ze faru ba”,


Yana tace “Yaya nasan akan rasa kudinnan duk kika tashi hankalin ki insha Allah zaa gane koma waye ni nafi ma zaton kaninsa ne jibrin”.



Ya nukura ce cikin dan daga murya tace “kul Yana kidena zargi sanin gaibu se Allah karki sake ta dora da fadin falmata ki yadda da kaddara mai kyau ko akasin ta insha Allah gaskiya zata bayyana”.

Cikin sanyin murya tace toh insha Allah, haka suka cigaba da hirarsu har dare ya tsala.

________
Rana bata karya sedai uwar diya taji kunya,

A yau ne ranar asabar karfe 10:30 aka daura auren *Auwal* *Umar* *Malumfashi* da *Yana* *Abbagana* *Usman* akan sadaki dubu dari Wanda dubban mutane suka shaida ko wa ka gani alokacin yana cikin farinciki mara misaltuwa bare me gayyar ango bakinshi ya ki rufuwa se gaisawa yake da mutane Abbiey ma haka sosai manyan mutane suka halarci daurin auren.

Acikin gida Yana tanajin an daura auren take ta kuka ummanta ce ta fado mata arai addua ta mata Allah mata rahama.



Tana cikin kukan wayarta ta fara ruri dagawa tayi tare dayin sallama daga can akace godiya da tabbata ga Allah da ya cika mana burin mu na zama maaurata har namasu yau ingan ki a gidana murnushi tayi tace “kafiye azzazabi wlh sweetheart ci gaba yayi da tsokanarta da ta gaji ta kashe Wayar, kawayenta suka fara tsokanarta da ta zama ta zama dauko riga ta zama dauko riga ta zama dama furar nan.......


Me kwalliya ta gyara mata fuskar ta falo ta fito aka ringa gaigaisawa da Yan Uwa da abokan arziki kowa na mata fatan alkhairi.



Angwaye ne sukazo aka ringa daukar hotuna.

Wajen biyar da rabi motocin daukar amarya sukazo.



Bayan Amarya ta gama shiryawa aunty sumayya ta Kama hannunta ta kaita dakin Abbiey duk suna zaune.


Sosai sukai mata nasiha me ratsa jiki kuka ta ringa yi, Ya nukura tace “Yana duk abunda ya dace mu fada maki tun rannan mun fada maki sedai na kara tunatar dake yi nayi bari na bari aure dan hakuri ne Allah gidan zamankine na har abada” .



Aka amsa da Amin.

Ammi dake kusa da ita ta rungume tana kuka shafa bayanta Ammi taringa yi sannan tace “Yana ki zauna da mijinki lafiya duk abun da yace kiyi kiyi indai be sabawa addini ba in yana magana karkisa masa baki har sai yakai karshe Allah baki zaman lafiya da zuria dayyiba yasa gidan zamankine ".

Amin. Kowa ya mata nasiha tare da fatan Alkairi .


Da kyar aka banbareta a jikin Ammi aka sata a mota su hudu ne a baya Ammi, Ya nukura da kanwar ummansu da ita kadai ta rage se amarya gaba kuma babbar Kawar amarya ce.

Sauran Yan Kai amarya suka shishiga motoci.

Amrah tana tare dasu Aunty sumayya.


Unguwar kundila suka nufa a kofar wani

1 Comments On FANSAN RAN MAHAIFANA
avatar
khadija-1-2-5

9 months ago

Reply

Tnx

Please Login or Register in order to submit comment