Join Our WhatsApp Group

SAINA AURI MATAR NOVEL Complete Hausa Novel Document by SAINA AURI MATAR NOVEL


SAINA AURI MATAR NOVEL

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 21191



SAINA AURI MATAR NOVEL

Reading Time: 1 Hours

Added On: 29, Sep 2023

Author: Hajara Bala ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : ANNURI WRITER'S ASSOCIATION.

Author Phone : 08130561988

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 114.93 kb

File Type: txt

Views: 624+

Download: 137+

Last download: 3 days ago

Description/Story: [11/16, 18:20] Ablaaa: *🦋SAINA AURI MATAR NOVEL*🦋


*BY*
*Haajara abla*

*MARUBUCIYAR👇🏻*

*GATA MUGUN ABU(rashin sama mugun abu.*

*ZAN RAYU DASHI.*

*RAYHAN.*

*BURIN ZUCIYA.*

*RUMANA.*


*💫💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION.*💫
(Annuri is the best.)


https://facebook.com/groups/743377583724957/



*Page 1_2*


Sakamakon wata gagarumar isakar dake kad'awa mai mugun k'arfi yayi sanadiyyar fad'uwar wata y'ar k'aramar rumfa ta langa² dake sakar gidan,da sauri MALIYA ya mik'e tare da Jan wani tsaki na takaici da b'akin cikin kalar wanan rayuwa. Wani d'an k'aramin d'akin k'asa ya shiga mai d'auke da shimfid'ar tabarma,daga gefe d'aya kuma wata gana must go ce,wacce da alama dai kayan sa ne a ciki,sai wad'ansu tarkacen sa da suke cikin d'akin...
Zaman sa keda wuya saman tabarmar aka fara ruwan sama mai k'arfin gaske,wanda yasa yayi tsam ya mik'e tsaye dan kuwa d'akin nasa ma zuba yake,haka ya cigaba da tsayuwa har aka kammala ruwan nan,gashi abin da yake k'ara bashi takaici ba rana bace dare ne sosai dan kuwa da rana ce bama zai zauna a cikin gidan ba balle yaga takaici...


Bayan an kammala ruwa yaja wani tsaki sanan ya gyara wajan gyarawa ya d'akko tabarmar da shimfid'ar ya shimfid'a a gefe sanan ya kwanta,aikuwa babu jima wa bacci mai nauyi ya d'auke sa...



"My MALIYA ka tashi kayi breakfast kana ganin lokacin fitar ka office yayi ka tashi muje ga ruwa can nayi maka wanka nawan." Tana fad'ar haka tana masa wani cakulkuli,yana motsi yana murmushi haka nan ya bud'e idanuwan sa ya kalle ta mace iya mace wanan itace ake kira first lady babu inda bazaka shiga da ita ba,babu wacce zata nuna mata wani abu wow ga kud'i ga kyu ga ilimi ga soyayya kamar dai matar novel haka take....
Cike da murmushi yace"ohhhh darling yanzu har safiya tayi?"

"Lol my MALIYA kada dai kace min safiyar tayi maka saurin yi."
"Eh wallahi darling haka nan nake so nace."
Cike da murmushin jin dad'i ta kawo bakin ta saitin nashi zata masa kiss kenan yaji kamar a mafarki kakar sa tana kwad'a mata muciyar dake hannunta wacce yanzu ta gama dama koko da ita." Yanzu ace kai saboda tsabar rashin hankali,ace ka girma amma baka san ka girma ba haba TUKUR maine yake damunka wai,anya kuwa baka da matsalar junnu,abin haushin ma kai ba k'aramin yaro ba balle ace k'uruciya ce ke damunka yanzu a k'alla ba a k'asaru ba zakayi shekara talatin dabiyar amma Sam har yanzu hankali bai zo maka....." Kafin ta k'arasa rufe baki cike da takaici da bak'in ciki MALIYA yace"gaskiya gaskiya abinda kike min sam bakya kyuta min,yaza'ayi ina cikin baccina mai cike da mafarki mai dad'i na AURI MATAR NOVEL kinzo kin wargaza min kin wani tashe ni,kaiiiiiii gaskiya nidai nidai,wallahi sa'ar ki d'aya ma kece amma wallahi da wata tayi min abin nan Allah dasai ta gane kuskurenta."
Kaka ta saki baki tana jinsa tare da tallafe hab'a tana mai k'ara cewa" iyeeeee TUKUR lallai wuyan ka yayi kauri har ya isa yanka ni kake fad'awa wanan bak'ak'en maganganun lallai TUKUR to dakai da matar da kake cewa ta mobal ce(novel) ko to sai na had'a gaba d'aya naci muku uwa,kuma bani kake fad'awa wanan magan ganun ba Musa ubanka shi kake fad'awa,ina fatan kana jina dakyu."

Dafe kai MALIYA yayi sanan ya'kara dubanta a wani ya mutse yace" ohhhhh my god wai maiyasa kike shigar min hanci da k'udundune ne,wai tsaya yanzu da kike tashina mai zakiyi min.?


"Uwaka zanyi maka nace uwaka zanyi maka TUKUR wallahi ka kiyaye ni,tun asuba bakayi sallah ba gashi har rana ta fito amma kace mai zan maka nake tashin ka."

"Haba kaka nifa kada muzo nan dake,na fad'a miki tun bayo ba ki daina cemin TUKUR ki daina ni d'inan sunana MALIYA kuma mijin matar novel ko kunaso ko bakwaso....

Izuwa wanan lokacin tuni sauran mutanen da suke b'angaren su MALIYA kowa ya lek'o suna ganin wanan dramer da kullum tak'i ci tak'i cinye wa,abinka da gidan k'oye ko wacce ta fito daga d'akin k'asanta tana bawa idonta abinci,inda SABO kowa ya saba da wanan girman kan da rashin kunyar TUKUR kullum bashi da aiki sai mafarkin matar novel,haka Babar sa saidai tayi tagumi takaici tayi kukan takaici yaya zatayi da wanan jarabawar kaddarar samun d'a irin TUKUR dole sai ha'kuri.....

Zaune yake akan wani benci na majalisar sa,wanda shine ogo danshi ya kafata haka zakaga anzo ana ta gaisheshi ana sai MALIYA sha kindum,SAIKA YI,SAIKA AURI MATAR NOVEL A DUK INDA TAKE, haka zaita amsawa yana washe baki yana wa mutanen k'oyen alk'awarurrka kala² da yake duk k'oyen mahaifin sa yafi kowa arzik'i shiysa ma yake k'ara ji da kansa...


K'oye idan akace maka k'oye ma da sauk'i to shi MALIYA yana cikin k'oyen k'ayayo,amma sai Allah ya taimake sa Baban sa yasa shi a makarantar Allo bayan ya gama karatun ne aka kaishi boka anan kusa da garin su,inda su wanan k'oye ne dan baza'a ce masa k'auyen k'ayayau ba,suna da wutar nefa sanan Alhmdlh suna da service na waya,to shikuma inda MALIYA yake Sam babu service sai yayi tafiyayyi sanan zaman da yayi yayi karatun har zuwa matakin nayin candy shine ya k'ara bashi wayewa,dan kuwa baima fiye zama a k'auyen suba yafi tafiya can d'ayan garin dan yana da wata waya daya dage ya siya to yana hauwa kafar sada zumunta na Facebook wani lokacin....



Kamar dai wasu lokutan yauma TUKUR yayi wanka yazo wanan garin,daman d'an acab'a ne yake kawo shi naira d'ari zuwa d'ari komawa,haka duk kusan sati yake zuwa dan yayi caji sanan yad'an lek'a yana gizo gizo...


Zaune yake bisa tabarma yana ta had'e² number daya saba had'awa,saboda yaji ance y'an burni suna yawan irin amfani da waya haka to yasan tabbasa watarana acikin had'a numbobin nan da yake to tabbas watarana zai had'u da MATAR NOVEL...







REALHAAJARAABLA CE.✍🏻sainaji sharhin ku,da yarda kuka amshi wanan tafiya tamu.😅
[11/16, 18:20] Ablaaa: *🦋SAINA AURI MATAR NOVEL*🦋


*BY*
*Haajara abla*



*💫💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION.*💫
(Annuri is the best.)


https://facebook.com/groups/743377583724957/



*Page 3_4*


Daining wata number yayi cikin sa'a kuwa number ta shiga,amma saida ta kusa katsewa sanan aka d'aga. Cike da zumund'i MALIYA ya gyara zama yana washe baki yace "hello." Yafad'a cikin wata kwantaciyar murya cike da sa ran wata rantsatsiyar budurwa zata amsa masa,kwasam ba zato ba tsammani yaji wata k'atuwar muyar tace"hello wake magana." Da sauri da kuma inda inda yace"sorry oga (da yake yana san idan yana magana ya ringa sa d'angutun turancin sa tunda yayi secondary) ina mai wayar." Daga d'ayan b'angaren kuma mutumin yace"wane mai wayar idan banda ni,Malam nine mai wayar,saidai ko wrong number. "
"To shikkenan daman Nana nake nema ashe kuma number badaidai nasa.... Kafin ma ya 'karasa wacen mutumin ya datsen kiran... Tsaki yayi sana ya jefar da wayar ba tare da yayi niyya ba....


Wata Zuciyar ce ta k'ara bashi kwarin gwiwa yadad'a furata" bazan karaya ba,kuma bagudu babu ja da baya har sai na nemoki na aure ki matar novel aduk inda kike..


Janyo wayar yayi ya bud'e y'ar datar sa yahau Facebook. Wani Baban tsaki yaja aikin banza duk wata mace da yagani ya bita yayi mata magana ko karb'arsa batayi a matsayin aboki balle kuma yasa ran har zata masa magana... Ba tare da nasara ba haka ya rufe datar tashi,ya tashi yahau mashine ya koma gida cike da takaicin rashin nasara....




Bayan kwana biyu,haka rayuwa taci gaba da tafiya kullum shekaru suna k'ara ja,amma shi Sam TUKUR baya ganin wanan shidai kawai burin sa bazai AURI koyawa ba sai matar novel...


Zaune yake saman benci a majalisar sa,yana zaune yana ta faman tunane² da ya saba kawai yaji mutum tsaye agabansa.. D'agowa yayi ya kalleta sai a lokacin tayi sallama cikin sassayanr muryarta sana tace masa"ina shini MALIYA daman gyad'a nakawo maka idan zaka saya." Murmushi yayi kaf cikin y'an k'auyen nan adama tana da hankali dan haka ma tasu tazo d'aya da ita.

Da murmushi a saman fsukar sa yace" sauke ki zuba min ina buk'atar gwangwani d'ya." Da murmushi a saman fuskarta ta sauke ta fara zuba masa,yana ta dariya yanaci yana bata labari... Kamar daga sama suka jiyo muryar kandala tana surba bala'eh.


"Waiii waiii wani ke gani kamar adama,to wallashi biki isaba,kowa yasani kaf nan k'oyen bani da wanda nake so sai MALIYA shine zaki biyo ta bayan fagge to biki isaba." Haka tazo sai ta cakumo adama,cike da takaici dabbacin irin na kandala yace" idan biki sake taba wallahi saina wanwanka miki mari,mara mutunci mara tarbiyya,ke ko a tafin silifas d'ina aka aura min ke bana warware ba,ai wallahi gwanda ma na mutu banyi aure ba....


Haka dai kadala ta sake tada wani bal'in yana fad'a tana fad'a,akan wallahi ko yak'i Allah babu wadda ya isa ya AURA sai ita...


Saboda tsabar takaicima da bak'in ciki ko gyad'ar baiciba ya bawa adama kud'inta ya wuce gida yana mai k'ara yiwa kansa addu'ar Allah ya tsaresa ai ko gawarsa bazai bari a aurawa kadala ita ba.....


Ya kira number bi ayau sunkai goma amma babu wacce ya had'a daidai,har bazai 'kara kiraba sai wata zuciyar tace ya k'ara kira ko Allah yasa a dace,aikuwa yayi daining wata number da ya had'a,aikuwa ta shiga yayi sa'a amma yayi rashin sa'a dan kuwa har takase ba'a d'auka ba,sake kira yayi nan ma tagaji da k'ara da ruri amma ba'a d'aga ba,har saida ya kira sau uku,ganin haka sai zuciyar sa ta raya masa koma dai wacece wanan mai wayar to tabbas tana ji da kanta kamar dai irin matar novel d'inan,bari kawai ya adana number,wata zuciyar tace to wane suna yadace kasa yanda zaka gane sai kawai zuciyar sa tabashi yasa MATAR NOVEL haka nan yayi saving number da wanan suna batare da yasan number ma ta macece kokuwa ta namijj ce,ta d'an garuwace kokuwa mai abincice a atasha.(shidai ya Sani.)


Haka ya kamo hanya ya dawo gidan zuciyar sa fall farin ciki dan haka kawai ya tsinci kansa cikin wanan farin cikin...


TUKUR shine asalin sunan sa ya taso a cikin k'oyene sosai shida iyayen sa a wani gari da ake kira dama gari, anan akwai wani k'oye to a wanan k'oyen suke,TUKUR yayi boka shiyasa yabawa kansa suna MALIYA dan kuwa yanaso ko baiyi kud'iba to babban burinsa a duniya kafin ya mutu shine ya auri matar novel, TUKUR tunda ya shiga secondary school yafara karance² novel,sai yaji a duniya babu wacce yake burin aure sama da ita dan kuwa matar novel komai ta iya k'arshe ce a komai,shiyasa yaji duk duniya idan bai AURI MATAR NOVEL ba to kuwa har duniya ta nad'e babu shi babu aure(kunji fa readers nidai abla naga ikon Allah a wajan MALIYA.)yayen sa sunyi sunyi har sun hak'ura dan kuwa y'an k'auyen duk sun samu abin fad'a,har 'kannensa duk sunyi aure harda ma yara amma ina shiga yace idan ba matar novel ba baiga matatar aure ba,dan kuwa sauran mata duk rako matan novel sukayi duniya matar novel gata da komai ga wayewa( ke kaji kamar shid'in wayis ne.) Haka dai har iyayensa suka gaji suka zubawa sarautar Allah ido, daman k'auye kowa yasanshi sai ya auri matar novel ma ake ce masa,haka dai ake rayuwa inda kandala tayi fatali da ra'ayinsa da komai tace ita bata San wanan ba kawai ita burin ta shine ta AURI MALIYA...





Kamar duk wasu satuttuka da zasu zo su shud'e haka nan MALIYA bai gaji da fita zuwa wanan mak'otan k'auyen nasu ba dan neman matar novel...


Yana wajan mai shayi yana shan shayi a mak'otan k'auyen nasu da yaje, anan yaji yanda ake had'uwa da mutane y'an gayu a birni.
"Ai nake fad'a muku duk wata mai kyu da ji da gayu ga aji ga wanka ga kud'i to mutum ya tahi birini,aradun Allah birni yayi sosai fa nake baku labari,da natafi birni kamar kar na dawo garin nan,saboda birni aljannar duniya." Cike da tsaguwa MALIYA yace masa"bawan Allah dagaske kaje burni?"
"Hhhhhhhh ai bani yi maku k'arya,ai abin da nagani hmm hmm hmmm abin ba'acewa komai."
"To bawan Allah zaka koma ne ko kuwa shikkenan bazaka koma ba."
"Kaaaaiiii daina fad'i ya za'ayi nak'i komawa,yanzu ma zuwa nayi na had'o wasu kud'ad'en gonar mu ta gado nake cen na kama sana'a ko kayan masarufi irin su kayan miya nake saidawa a birni a radun Allah na haye."

MALIYA bashi da burin yin wata sana'a ko yaya take amma kuma gashi dama tazo to tabbas zaibi wanan bawan Allah burni shima zai kama sana'a sanan kuma sai ya nemo matar novel a birni a duk inda take dan kuwa shi dan itama zaije birinin..


"Aikuwa nima ina son zuwa yaya kenan za'ayi."
Wanan saurayin mai bada labari ne ya juyo ya kalle shi sukayi face to face sanan yace masa,kana da kud'i?"
Gyara zama yayi sanan yace "gaskiya bani da kud'i.. Kafin ma ya rufe bakinsa saurayin yace" to baka da zuwa birni. "
"A'a ai baza muyi haka dakai ba,dole na nemu kud'i duk inda suke ai ko gonar Baba ne sai na saida,yanzu kai yaushe zaka tafi."

"Ni zuwa sati guda zan koma."
"To shikkenan kafin nan zanje duk yanda akayi zanyi abinda ya dace zan sayar da gonar Baba sanan zan tawo nan dan mu tafi brini."


"To shikkenan Allah ta kaimu lokacin."

"Ameen. Yafad'a yana mai sakin wata k'ara wacce duk tasa mutanen firgita sanan suka had'a baki wajen fad'ar lafiya kuwa MALIYA.( da yake ya fad'a masu sunan sa.)
Wata dariya ya sake saki sanan yace" lafiyar kenan kawai murna nake saboda zanje birni,kuma zanje birni badan komai ba sai dan ganin na had'u da MATAR NOVEL.. "

"Matar nobal kuma wacece matar nobal?" Duka y'an wajan suka tambaya dan basu san wacece haka ba.....





Haajara abla ce.✍🏻
[11/16, 18:21] Ablaaa: *🦋SAINA AURI MATAR NOVEL*🦋


*BY*
*Haajara abla*



*💫💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION.*💫
(Annuri is the best.)


https://facebook.com/groups/743377583724957/


*Page 5_6*

Murmushi yayi sosai wanda ya fito daga k'asan zuciyar sa,sanna yayi gyaran murya yace" ba matar nobal nace ba,matar novel nace,kuma insha Allah nidai ita zan aura dan indai akaga nayi aure to na rantse da Allah matar novel na aura..." Cike da haushi wasu kuma da matsuwa suji wai mai yake nufi ne suka ce dashi" haba MALIYA muna so to kafad'a mana wace matar novil d'in sanan kuma a ina take."
"Hhhhhhhh ai matan novel samun su sai sa'a nake fad'a muku mata ne dasuka San kansu wajen komai da komai,kai sai inci kalar matan Aljannar nan ne su hurul ini.."

"Hhhhhhh to MALIYA idan haka ne kenan kowa ma zaiso ao yadace da kalar wad'an nan matan a duniya." MALIYA ne yaja dogon numfashi yace" ai baku Sani ba,ba'anan matsalar take ba,dole sai namiji ya tara wasu mak'udan kud'i kuma irin kyakkyawan nan ne ajin farko shine fa suke auren sa."
Dariya kowa yasa hatta dame shayi saida ya dara sanan sukace" to kai yanzu MALIYA baka da d'aya daga cikin biyun dakake wanan zumud'in to taya kake ganin abubuwa zasu kasance a haka taya kake ganin tafiya zata yiyu a haka kaiba kyu ba saanan kaba kud'in ba dad'in dad'awa ma kaid'in d'an k'auye ne..." Wani daga cikin mutanen wajen mai shayin ya fad'a yana dariya....



MALIYA mutum be...


Read / Download SAINA AURI MATAR NOVEL

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album