Join Our WhatsApp Group

BAKAR WASIKA Complete Hausa Novel Document by BAKAR WASIKA


BAKAR WASIKA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 137261



BAKAR WASIKA

Reading Time: 11 Hours

Added On: 10, Apr 2023

Author: Khadeeja Candy ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08036126660

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 721.49 kb

File Type: txt

Views: 6482+

Download: 4156+

Last download: 8 hours ago

Description/Story: *💔-BAKAR WASIKA-💔*
_Mai Farin rubutu_

From the writer of

RAI BIYU
HAFSATU MANGA
ZAGON KASA
ZABIN RAI
KHADIJATU
GOBENA
ZAKI
FULANI

©®Hakkin mallaka nawa ne ni Khadeeja Candy, ban yarda a sarrafamin labari ta kowace siga ba balle har a dorashi a YouTube ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba domin zai iya janyowa mutum matsala saboda haka a kiyaye ⚠

SADAUKARWA.
Na Sadaukar da littafin nan ga Hajiya Habiba da iyalanta.

GAISUWA
Ga Mutanen Kirki, Rahma Kabir, da Mrs J Moon.

GABATARWA.

BAƘAR WASIƘA...
Mai farin rubutu

Idan aka ce Bakar Wasika Mai Farin Rubutu. Ana nufin wani dunkulelen sako mai wuyar fassara, kamar mutum mai nagarta sai wani mummunnan kaddara ta fada masa.

Ban ce tafiyar mai sauki ba ce.
Ban muku alkawarin zallar soyayya ba.
Ban ce babu farincikin ba.
Kunci, bakinciki da damuwa, sune abubuwan da suka taru suka tare farincikin AMINATU, kalubalen rayuwa bayan wata rayuwar, tabbas akwai kuka akwai damuwa da bakinciki.

Labarin Tafida, Rafi'a, Laila, Madina, Ramlee, Faruk, Amal, Kabir da kuma Aminatu.
Labarin BAKAR WASIKA. Labari ne da zai tabo wani bangare na rayuwar mace, kuma wani bangare na rayuwar al'ummarta da iyayenta...
Ina fatar zaku karbe shi kamar sauran, duk kuwa da na san ba lallai ne yai muku dadi ba domin ba soyayya ce zalla ba, kalubalen rayuwa ne da fadi tashin yar gudun hijira!
A ina zata kwana? Wa zai bata masauki? Taya za a fahimce ta har a nade mata damuwarta? Wa zata kaiwa kukanta iyeyenta ko al'ummarta? Ta ina mafarkinta ke tabbatuwa? Ashe bayan wuya akwai wata wuyar, bayan dadi ma akwai wata wuyar, bayan wuya kuma akwai dadi.
Tabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai tsoro a mafarkin da ka gagara farkawa! Ta ina lamarin ya fara? Ina tsakiyarsa da karshe? Yaushe damuwar zata wuce? yaushe bakincikin zai gushe? Sai yaushe hawayen zasu tsaya? Zuwa yaushe ne kuncin zai yanke?
Ashe a cikin rayuwa akwai wata rayuwa? A cikin rayuwar ma akwai mutuwa?

Labarin BAKAR WASIKA kirkiraren labari ne kamar sauran labaraina, kun san dai ban saba baku kunya ba ko?😉 Wannan ma zai zo muku fiye da yadda kuke tsammaninsa inshallahu. Sai dai ba free ba ne na kudi ne, but ina da free pages daga 1-10 ga masu son jin dandanon labarin kamin biya.
Kamar yadda kuka sani bana editing labari so ku yi hakuri da duk abun da zaku gani.

P. O. V
Na nufin Point Of View.


                      بِسْمِ ٱللَّٰهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ


Page -1⃣

Matashiyar yarinya ce yar shekara goma sha-bakwai dauke da farantin giɗa tana tsaye jikin window makaranta tana leken daliban da ake yi wa darasi.
Yadda ta maida hankali tana sauraren darasin da ake wa dabiban sai ka rantse da Allah har da ita a cikin daliban. Ilmin zamani na daya daga cikin abubuwan da suke matukar burge Aminatu kuma shi ne kadai abun da ta rasa a yanzu, wanda ta riga ta maye gurbinsa da talla a halin yanzu, a izuwa yanzu ta tabbatar bata da muhalli a ilmin zamani, sai dai shi ilmin yana da muhallin a zuciyarta.

"Ba ni gidar goma"

Wata dalibar ta fada da kamar rada gudun kar malamin da yake musu darasin ya ji ta, a munafunci ta jefowa Aminatu wata tsohuwar naira goma, sannan ta maida hankalinta gurin Malamin.
Aminatu ta duka kasa ta sauke farantin dake hannunta sannan ta dauki naira goma din ta daga hijabinta ta saka naira goma din cikin hular dake kanta ta gyara hijabinta sannan ta dauki giɗar ta mika mata, yarinyar ta karba da sauri ta boye.
A lokacin ne malamin ya hango Aminatu tana kallon allon da yake koya musu darasin, kusan wannan shi ne karo na barkatai da yake arba da yara na shigowa makarantar talla, wani lokacin har cikin ajijuwa suke zagayawa idan sun ga babu malamai a ciki.
Sai dai tsayawa a nasu ana daukar darasin karatu babu kamar Aminatu domin ko daliban makaranta basa nuna mata natsuwa da maida hankali sai dai su nuna mata iya rubutu da kuma fahimtar darasin yadda ya kamata domin su a kullum suna aji ne, ita kuma sai idan talla ta biyo da ita.

"Mtcheesss idan ba makarantun kauye ba ina ake wannan abun? Ace makaranta a bude har masu talla suna shigowa, ko wane aji babu ganbu (Kaure) balle har ma ace an zagaye mana makarantar"

Malamin ya fada cike da jin zafin yadda aka wofintar da abun da ya shafi ilmin boko a yanki.
Aminatu na jin haka sai ta duke kasa gabanta na faduwa, daman can yarinya ce mai gujewa fitina da tsoron bacin ran mutane. Dukuduku tai ta fice daga gurin cikin sanda ta koma can bakin kofar makarantar inda suke zama ita da sauran masu talla suna jiran a tashi yan makaranta fito siye siye.
Rayuwar Aminatu rayuwa ce da ta ginu da ilimin addinin da kuma talla, domin bayan noma da mahaifinta yake yi wanda shi ne mafi akasarin mutanen garin galadi suke yi, babu wani abu da aka doraga da shi a gidansu kamar tallar da take, da rana zata kai giɗa makarantar boko, dare kuma ayi mata tuwo, da safe kuma ta fita tallar koko, hakan yasa rabin rayuwarta ta kare a talla. Sai dai ko kadan bata da matsalar rayuwa ta ko'ina domin ita kadai ce mace da mahaifiyarta ta haifa bayan zaratan maza bakwai. Rayuwarta kusan haka rabin rayuwar yan matan garin take ba kowa ya ke damuwa da karatun boko kamar yadda suke damuwa da talla ba, domin talla tana ba su komai cikin har da kayan dakin da ake yi ma yan mata.
Garin Galadi wani yanki ne dake cikin karamar hukumar mulki ta shimkafi, gari ne mai cike da albarka manoma, kusan idan ka ambashi shimkafi kowa ya san gari ne na manoma garin mai cike da albarka da kuma mutanen kwarai. Karamar hukumar Shinkafi tana cikin jihar Zamfara, shiyyar arewa maso yammacin Najeriya. Hedikwatar karamar hukumar tana cikin garin Shinkafi kuma karamar hukumar na da iyaka da karamar hukumar Zurmi Maradun da wasu sassan jihar Sokoto da jamhuriyar Nijar.

Garuruwa da kauyukan da suka kunshi karamar hukumar Shinkafi sun hada da Miyasa, Shinkafi, Bwane, Tunga, Fidani, Tubali, da Faru. An kiyasta yawan al’ummar karamar hukumar Shinkafi ya kai 177,811 mazauna yankin da ‘yan kabilar Hausa da Fulani suka mamaye. Yaren Hausa dai ana magana ne da shi a karamar hukumar, addini Musulunci shi ne addininsu.
Karamar hukumar Shinkafi tana da fadin kasa kilomita murabba'i 674 kuma tana da matsakaicin zafin na digiri 34. Karamar hukumar tana da kogin Tafin Kaiwa da ke ratsa cikin yankinta yayin da matsakaicin saurin iska a yankin ya kai kilomita 11/h. Noma wani babban aiki ne na tattalin arziki da al’ummar karamar hukumar Shinkafi ke aiwatarwa.
Sauran muhimman ayyukan tattalin arziki da al'ummar karamar hukumar Shinkafi suka gudanar sun hada da farauta, kasuwanci, kiwon dabbobi, da ayyukan fata.


*** *** ***

Tana zaune a gurin har aka tashi yan makarantar masu siyen gid'ar suka siya, wanda tai saura sai ta dauki farantin ta dora akai ta nufi gida tare da kawar tafiyarta Rumaisa, suna tafe tana kirga kudin gidarta har suka kawo mararabar hanya (Hanyar da ta kasu hudu) a nan sukai sallama kowa ce ta nufi gidansu. Da sallama ta shiga gidan kamar yadda ta saba.

"Wa'alaikissalam yar Inna yar Albarka"

Inna ta fada tana juyowa ta kalleta fuskarta dauke da murmushi. Sanusi ya wara ido ya zubar da ruwan daya wanke tufafinsa.

"Mu da ba yan Inna ba a nuna mana bolar mu"

Aminatu ta kyalkyale da dariya kamar ba ita ba, tai saurin aje farantin dake kanta ta mikawa Inna kudin hannunta sannan ta karbi dawon (Fura) da Inna take da inna take kirbi (Daka) ta cigaba da yi tana fada mata ko nawa aka samu yau.

"Aminatu Auta, himma dai yar Audu"

Sanusi ya sake fada da fuskar zolaya, daman can indai yana gida ya fi kowa zolayarta kamar wata abokiyar wasarshi.

"Na ji dai ai ina aiki dai ni ba kamar sauran auta ba ne, kai da baka iya noma fa sai sana'ar tireda"

Ta masa gwalo. Sai Inna ta saka dariya.

"Fada masa dai yar auta gogar aiki, shi baya iya aikin karfi irin na maza sai sana'ar zama"

Aminatu ta wani yi warrr da ido tana jin kirarin da Inna tai mata har cikin ranta, ganin hakan yasa Sanusi sake tsokanarta.

"Eyee su igeee anji dadi, Igengen..."

Take ta turo baki gaba.

"Inna kin ga yana ce min Ige ko?"

"To maza nawa aka haifa kamin a haife ki? Kin zama Ige ai"

Aminatu ta kalli Inna da kwababbiyar fuskarta kamar zata fashe da kuka.

"Inna kina jinsa ko?"

"Dan Allah Sanusi ka gama ka fita ka bar mana gidanmu, ya zaka takurawa Auta"

Inna ta fada. Sai Aminatu ta gyada kai

"Atooo"

Dariya yai ya debi ruwa a babbar buta ya zagaya bandakin da ya kasance na kasa kuma iya tsawon habar mutum, (shoulder) domin idan ka mike tsaye gaba daya, za a iya hangoka.
Kamin ya gama wanka Aminatu ta gama kirba dawon har ta kwashe ta zuba wani, Auta ce amman ba kamar sauran ba, domin bata da ƙwiyar aiki, ita dai bar ta da shagwaba da yawan kuka idan an taba ba.

"Baka ma wanku ba tsami kake yi"

Ta fada tana yatsina fuska kamar gaske. Dariya yai ya shiga karamin dakin dake kusa da na Inna ya shirya cikin wata karamar shadda ta marasa karfi da ta gama shan jiki ya saka hullarsa taɓani ka ji Hadisi, sannan ya fito yana ta kwanbo da talkaminsa na roba.

"Wallahi ba kai kyau ba"

Cewar Aminatu tana dariya, sai Inna ta taya ta.

"Lallai kam kyau ai sai Auta hanci har baka (Baki) sai dai a gwada mata haske shi ma kadan"

"Inna Wallahi ki daina biyewa wannan yarinyar, idan ma ta samu miji irina ta more..."

Har Aminatu ta bude baki tai magana sai kuma tai shiru ta maida dubanta gurin yayanta Amadu, wanda take tsoro kamar mutuwarta domin idan yana a cikin gidan bata da sukuni ko wani motsin kirki bata yi. Na tsantsiyar yarinya ce, sai dai shigowar Amadu ya saka ta kara natsuwa ta yi tsit a gurin kamar babu ita. Amadu irin mazan nan ne da basa wasa da yara balle kuma ita da take kanwarsa ta biyar.
Wani tsohon babur dinsa Honda ya turo ya karaso inda suke, Inna na nashe dawon a tukunya, Aminatu kuma na zaune gaban turmin idonta kasa.

Inna ta daga kai ta kalleshi yana kokarin jingine babur din ta ce.

“Ka dawo?”

“Eh ya gidan?”

“Lafiya Kalau, ya kasuwa”

Ya dan yi jimm cike da damuwa sannan ya sauke ajiyar zuciya.

“Kasuwa da godiya Inna, amman abubuwan kasar nan sai hamdala, komai kara masa kudi ake, idan baka da wani babban jari yanzu sai kasuwancin ma ya gagareka”

“To ya za'ayi kasar ce ta zama abun da ta zama, Allah ya ba mu azzaluman shugaban ni, ba su da tausayi kansu kawai suka sani”

Cewar Sanisu yana nufo inda suke, Sai Amadu ya amsa masa.

“Wallahi ga rayuwar mutane an maida ta kamar ta dabba, kai har kara ma dabba a yanzu, kuma sun kasa daukar mataki basa ma son ana ji, Nigeria kam ban san yaushe zata gyaru ba”

“Allah ya kyauta, ni dai na wuce shago”

Sanusi ya sake fada, sai Inna ta bishi da addu'a.

“To Allah ya tsare ya bada sa'a”

Har ya fice Aminatu bata dago kanta ba, ko da wasa bata son ta hada ido da Amadu, ba ganinsa kadai ba ko muryarsa ta ji sai ta ji gabanta ya fadi.

“Inna Ina Lami kike neshen dawo da kanki? (Saka fura a tukunya)”

Amadu ya tambaya.

“Kai ma ai kasan bata nan, da tana nan ai ba zata bar ni nai wannan aikin ba, ta je ganin dan Kuidu (Kaciya)”

Ya shaf kansa.

“Na manta ta fada min, abubuwan ne sun yi yawa Wallahi”

Ya fada yana nufar bangaren da Iyalinsa suke. Domin irin katon gidan nan ne na kauye mai fili wanda yaya suke dibar bangare suna kafa na su iyalin, bayan shi da yake da mata daya, Musa mai mata biyu ma a gidan yake zaune, sai dai shi ya fitar da kofar gidansa ta can baya sai an zagaya za a iya shiga, Iro da Sanusi ma da ke shirin aure a cikin gidan suka gina gurin da za su aje matansu.



TALBA POV.

Yana zaune a dining din har Momy da Baaba suka gama hada abun karyawa. A hankali ya dago yana kallon yadda Baaba take jera kulolin, hannunsa suke da wayarsa. A hankali ya lumshe idonsa ya bude, cike da kasaita ya motsa bakinsa, yana maida dubansa gurin Momy wanda taja kujera ta zauna.

“Baaba a fadawa yaran nan su fito su karya”

Matar da aka kira da Baaba ta dan risinawa Momy cike da ladabi.

“To ranki ya dade”

Ya nufi upstairs da sauri, da ido Talba ta bita kamin ya maida dubansa gurin KB da ya fito a daya daga cikin kokafin da suke can dayan bangaren falon.

“Momy ina kwana”

KB ya fada yana kokarin jan dayar kujera ya zauna, sai Momy ta amsa masa ba yabo ba fallasa, sannan ya mikawa Talba hannu suka gaisa, ya shiga hadawa kansa tea. A tare Amal da Leila suka sauko downstairs din, kai tsaye suka nufu dinning area, Amal da far'arta kamar kullum, Leila kam sai wani sham kamshi take musamman da ta hango Talba a zaune a dinning din.
Amal ce ta riga isa ta zauna tana fadin.

“Ya Talba Morning”

Ya kai dubansa gareta yana sakar mata murmushi as respond, irin murmushin nan da be saba zama a fuskarsa ba. Bayan ta gaishe shi ta gaishe da KB.

“Ya KB Morning”

“Morning Amal”

Ya amsa yana kai plantain a bakinsa. Leila na zaunawa Talba ya mike tsaye cike da izza, sai duk suka kalleshi.

“Ah ah ba karyawa za kai ba?”

Momy ta tambaya.

“Zan yi breakfast a waje”

Ya amsa kamar an amsa dole, already yayi nisa da dinning din. Sai da ya fice daga falon gaba daya sannan Momy ta kalli Leila.

“Kun sake yin fada ne?”

Leila ta kalleta cike da damuwa.

“Momy miyasa kullum ni ce mai laifi?”

Momy ta zare mata ido.

“Yes tun da ya dawo sallah asuba yake zaune a nan, idan har babu komai to babu abun da zai saka ya zauna tun 6:30 har 9:30 dan kawai kin zauna kuma ya tashi ya ce ya zai karya a waje, zan kaiwa Daddynku abinci yanzu, ki same ni daki anjima”

Momy na fadar hakan ta mike tsaye ta dauki wasu tsadaddun kuloli ta nufi kofar da zata sadata da bangaren Daddy.

“Ni ma ba zan karya ba”

Amal ta fada tana turo baki alamar ranta ya...


Read / Download BAKAR WASIKA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On BAKAR WASIKA
avatar
aisha-7-1

5 months ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album