Join Our WhatsApp Group

NI DA YAYA SADEEQ Complete Hausa Novel Document by NI DA YAYA SADEEQ


NI DA YAYA SADEEQ

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 64470



NI DA YAYA SADEEQ

Reading Time: 5 Hours

Added On: 03, Oct 2023

Author: Siddiqahtulkhaireey Yahya (Sbeauty) ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +966591512794

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 337.59 kb

File Type: txt

Views: 1579+

Download: 726+

Last download: 1 day ago

Description/Story:     NI DA YAYA SADEEQ
               

Love story 2021 typing free book

      

                Na
Siddiqahtulkhaireey Yahya (Sbeauty)

             EWF📚💪

  
         TSOKACI

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, ban ƙirƙiri littafin NI DA YAYA SADEEQ saboda wani ko wata ba, nayi ne saboda nishadantar da Al'umma gami da faɗakar da su, kuma wannan shine littafina na farko fatan zakuyi hakuri da kura kuran da zaku ci karo da su.

     SADAUKARWA

Wannan littafin sukutum ɗin sa, sadaukarwa ne ga mahaifiya ta. Hajiya Rukayya Muhammad (kamfani)
             
                
_________________________________ 
                  
Shafi na farko

بسم الله الرحمن الرحيم

_______A zaune nike a kan tabarma cikin baranda, isaka na kaɗa bishiyar mangwaron da ke tsakiyar gidan mu, ganyen ta na faɗowa ƙasa gunin burgewa, dambu ne a gabana cikin wata y'ar samira inaci ina suɗe yatsun hannu na, saboda dambun yayi min daɗi kamar kar ya ƙare.

Ƙawata Ladiyo ce ta shigo gidan mu hannunun ta rike da goshin ta yana zubar da jini, koda na ɗaga kaina na kalle ta bance mata uffan ba, illah maida kaina ƙasa da nai  na cigaba da cin dambu na, sai da na cinye dambun tas sannan na kora da ruwa, kana na buɗe baki na iya ƙarfi na nayi wata ƙatuwar gyatsa, wacce da gani kasan tarashin mutunci ce, irin wacce idan yaya Sadeeƙ yana guri nayi yake buge min baki.

Kallan Ladiyo nayi na taɓe baki na ce "Ladiyo wai lafiya kika zo ki ka tsaya min a kai? Ko aiko akayi?".

Ladiyo da dama jira take in tambaye ta, saboda tasan in bani na tambayeta ba tana iya faɗa min na gwasale ta, tana kuka take faɗan  abinda ya faru cewa "ina yaron da jiya muka barar mai da markaɗe?".

"Eh na tuna shi me yafaru?".

"Yanzu haka daga aken da Ummata tai min gidan su Zulai anso mata kuɗin zubin a dashi nike, bayan na anso kuɗin, kan hanya ta ta dawowa na haɗu da yaron, wai ashe nan ne layin su, shine yai tamin ruwan duwatsu tako ina, har wasu abokan sa da suka gani suka taya sa, Allah ya taimake ni baban
Ramma yazo wucewa, shine da yaga abinda ke faruwa, ya tsawatar musu, shine suka ƙyale ni, amma wallahi inaga da sai dai a ɗauko gawa ta saboda jifan da suka min bana wasa bane, ko gida banje ba nayo nan saboda ya bani saƙo gunki cewa, idon ki idon shi sai ya fasa miki goshi".

"Kan uban nan, yanzu dama acikin ƙauyen nan a kwai wanda zaija dani, har ma yace zai fasa min goshi, to ƙaryarsa taci ƙarya, wallahi kaf ƙauyen Dande banga mai tara ta gaba da gaba ba, kin san dai ko ta baya sai an shirya, to amma tunda yace haka muzuba ni dashi, shege ka fasa, ɗan halak sai yanka, kafin ya fasa min ni zan fara zuwa gidan su in fasa na Babar sa inya so kinga yaji daɗin fasa min nawa da hujja".

Inna da fitowar ta daga ban ɗaki kenan da buta a hannun ta, bayan ta aje butar ta ce "wai ke da wa siddeeƙah? Kike mulmulo irin wannan ashar ɗin, kamar bakya zuwa islamiya"? .

Cikin sakalci na ce "yo Inna bakiga Ladiyo bane?".

Sai alokacin Inna ta lura da Ladiyo da ke a tsaye gindin rijiya hannun ta ɗore bisa goshin ta.

"Na ganta sai akai yaya"?.

Cikin ƙosawa da tambayar da take min na ce "yo wai ke Inna bakiga goshin ta bane a fashe jini yana zuba?".

"Na gani man, ai tunda taƙi rabuwa dake, tana tare da wahala, gashi ta zama lusara bata iya taɓuka komai, amma tsokana fal cikin ta, tsokana kuwa tamai ƙarfi ce".

Na ce "yo Inna wanda yafasa mata goshin ne nima yace ace min ido na idon shi sai ya fasa min, shine abin yabani dariya da takaici har kika ji nayi wannan ashar ɗin, kuma wallahi idan duka ƙauyen nan gatan shi ne wallahi sai naci ubansa, duk abinda zai faru ya daɗe bai faru ba, be san wace ce Siddeeƙar  Inna bane shiyasa, amma ko yaran goye aka amaba ta masa suna na, nan take jikin sa yake fara rawa saboda karo dani babu daɗi".

Banyi aune ba naji anbige min baki, a  masifance na ɗago da kaina dan naga wani mai tsaurin idon ne, da har ina magana zai bigen baki.

Diriricewa nai, ganin shi a gaba na nasan ko ba a faɗa ba shine ya bigen baki,   ɗan ƙaramin baki na na zumɓuro.  Yayin da muka haɗa ido ya wani kashe min idon sa ɗaya. Yana cewa "shegiya mai zubin aljanu, bari na fara cin naki uban, kamin shi yaci nasa, shashasha kawai, naga ƙafar ki a waje kiga yadda zanyi da ke, sakarya daƙiƙiya kawai, ba arabi ba boko, sai yawan gaɗa a dandali, ke fa ko a cikin matan ƙauyen kin fita zakka, saboda kinfi su wauta da tumasanci, saboda kin ga Inna na ɗaure miki gindi kina yin abinda kika ga dama, kina ganin kamar gata take miki, to ki sani Inna ta riga da ta gama cin kasuwar ta, ke kuma yanzu kike fara tasowa. Saboda baki san komai game da rayuwa ba, kwata-kwata ma nawa kike? ko 14 years old baki kaiba amma kin addabi mutanan gari, kullum ana cikin kawo ƙarar ki muna bada haƙuri".

Ladiyo dake tsaye har yanzu kamar wacce aka dasa ya kalla, irin kallon nan na gargaɗi kana ya ce "ke yama kike da suna?".

Ladiyo dake a tsaye hannun ta akan goshinta, cikin rawar baki da rikicewa ta ce "Ladiyo".

"Oho koma dai maye sunan naki maza ki bi nan". yai mata nuni da hanyar fita gidan."

Ya kuma cewa "ko a ƙofar gidan nan idan kika bari na kuma ganin ki, to ko na lahira sai yafiki jin daɗi, bare kuma in ga wa'innan y'an ƙafafuwan naki a cikin gidan nan, Allah sai na ɓaɓɓallaki".

A kausashe ya ce "Ina fatan kinji abinda nace miki? idan kunne yaji gangar jiki ta tsira. "Oya maza ɓace min da gani, kamin nayi ball da ke".

Ladiyo jiki na 'bari ta bar gidan mu, a ɗari da hamsin.

Kallo na yayi muka haɗa ido ya wurgo min harara, ramawa nima nayi, gami da haɗawa da ƙunƙuni ciki-ciki na ce "nima fa idon nan ba fina akai ba, da har ake wani min barazana da su, kuma mu zuba ni da kai, zaka san ka bige min baki".

"ke! Me kike cewa?".

Sai alokacin Inna tai magana, saboda tasan ɗazun ko tayi ba mai sauraron ta, ta ce "haba Garba,
waini me yarinyar nan taimaka ne daka tsaneta? ba nason haka fa, tun ba yau ba nasha faɗa maka, amma dake ka rainani bakajin magana ta, ko kaɗan saboda kaga ni kaka ce, to alhaji ƙaramin zai zo ai, tunda watan ya kusan ƙarewa, idan kai ban isa da kai ba shi na isa dashi. Kuma shine mahaifin ka, idan yafaɗa maka wataƙil kaji nasa tunda ni kaƙi jin nawa".

Ya san halin Inna sarai da mita, dan haka sai ya kawo wasa a maganar ya ce "haba hajjaju makkatun mu karrama, ranki shidaɗe, ki daɗe kiyi ƙarko, kiyi shekarun bishiyar dabino, wane ni ai ban isa in raina ki ba, duk da cewa nike aurenki amma ke ke bada umarnin, Kuma yadda Kiki ce hakan ake yi, ina mai tabbatar miki bani kuma shiga shirgin ta daga yau".

washe baki Inna tai, cikin jin daɗin furucin shi ta ce " ko kaifa Garba shikenan ya wuce amma da kasa ka y'ar mutane gaba sai ramewa take, shiga ciki yanxu zansa ta kawo maka abincin naka.

💋💋💋💋💋💋
_Kar ku manta kuyi_

Comment
Shear
Vote

_I love you all_

💋💋💋💋💋💋

*S BEAUTY CE ✍️*

   NI DA YAYA SADEEQ
        

Love story

              Na

Siddiqatulkhaireey Yahya
            (S beauty ✍️)

             
                 *EWF*📚✍️
_________________________________
               
Page 02

بسم الله الرحمن الرحيم

           
_________Inna tace, "daure ki tashi ki kaiwa yayan ki abincin sa, kinga daga aiki ya dawo ya gaji ga yunwa".

Ɗaure fuska ta nayi ina turo baki nace, "ni dai Inna bazan kai mishi ba, duka na zaiyi, baki ga yadda yake bina da kallo kamar wani tsohon  maye ba, kwana biyu  bai samu ya dakeni ba, kinsan halin muguntar sa ba sai nayi masa laifi ba, yana iya ina shiga ya rufo ƙofa, ya jibge ni, kin san
shi kullum cikin jin haushi na yake".

"A haba, yau dai Garba ko kunnan ƙashi ne dashi bazai dake ki ba, kina kallon yadda na tsawatar mishi a gaban ki, idan ko har ya kuskura ya taɓa ki saina haɗashi da Alhaji Ƙarami, tashi maza kije ki kai mai yar albarka".

"Yo ina  abincin nasa yake?".

"Yana kitchen mana, inda kika ɗauko naki".

koda na ɗauko abincin a saman kaina na ɗorashi ina ɗigir-gire.

  "A a fa kada tsautsayi yasa ki zubar mai, kinga yana cikin fushi, babu abinda bazai iya miki ba". A cewar Inna

"Haba Inna bazai  zube ba sai dai idan kece kike so ki zubar dashi, amma ai ba yau nikeyi ba, kuma bai taɓa zubewa ba".

"To Allah ya bada sa'a" ta faɗa tana mai shigewa ɗaki abinta.

Ni ko na cafke da "Amin hajiya Inna".

Ina tafe ina 'yan waƙe na, ina tafa hannu, hanyar ɗakin yaya Sadeeq na nufa saboda yana daga hanyar waje ne. Koda nazo bakin ɗakin ban tsaya yin sallama ba, kuma ban buga kofar ba, duk da yasha yimin gargaɗi a kan indaina shiga masa  ɗaki, ba tare da nayi sallama ya bani izinin shiga ba, ko kuma na buga masa kofar. Amma tsabar taurin kai irin nawa sai naki yin ko ɗaya acikin umarnin shi, kawai bankaɗa ƙofar nai, Ina tura ƙofar na bankaɗa labule  nakutsa kaina ciki. Yanayin da naga yaya Sadeeƙ ne  yasa nasaki wata uwar ƙara, har saida kular abincin kaina ya faɗi, murfin kular ya buɗe dambun ciki ya watse.

A fusace yah Sadeeƙ ya nufo ni, kamar mayunwacin zaki, kamin in ankara ya wanka min kyawawan maruka, haske nagani wal-wal a idanu na, har saida ji  na ya d'auke na wasu 'yan daƙiku, ba wani abu ne ya firgita ni ba, illah ganin sa da nai babu riga, kirjin sa ɗauke da yalwataccen gashi baki siɗik dashi, kwance luf-luf bantaɓa ganin ɗa namiji haka ba tunda nike  a rayuwa ta, ja da baya na fara yi, ina rawar baki, yayin da shi kuma yake nufo ni, haƙiƙa na furgita dashi matuƙa. Saboda haka na fara ihu iya ƙarfina, yadda Inna zata iya jiyo ni, tazo ta cece ni.

Takaici na ne ya kuma kama shi,   cikin zafin nama ya cafko ni, belt ɗin jikin wandan sa ya zaro, sai alokacin nai yunƙurin guduwa daga ɗakin. Amma ina aikin gama ya riga ya gama, saboda riƙe yake gam da hannu na, maida ƙofar yai ya rufe harda samata kye da sakata, kana ya soma duka na, kamar Allah ya aiko shi, kota ina zabga min belt ɗin yake yi. Ihu nikeyi da duka murya ta, saboda naga so yake ya kashe ni, tun kamin lokaci na yayi.

Inna dake cikin ɗaki tajiyo ihuna da gudu ta fito tazo bakin ƙofar ɗakin sa, buga ƙofar tafara, tana kiran suna na da ƙarfin ta, ganin ba kiran sunan nawa ne mafita ba yasa tafara kiran sunan yah Sadeeƙ, Garba Garba kada ka kashe 'yar mutane na shiga uku, dan Allah ka yaƙuri ka ƙyaleta haka nan, komai tai maka ai tadaku, bazata ƙara ba daga yau insha Allah".

Tun ina iya jiyo muryar Inna tana magiya har nadena jiyo ta, nasan tagaji ne saboda bata jure yawan magana yanzu sai hawan jinin ta ya tashi.

Sadeeq kuwa kunnen uwar shegu yayi kamar bashi Inna kema magiya ba, tuni Inna hawaye sun fara zarya a kan kuncin ta, saboda tasan yah sadeeƙ, ba ƙaramin aiki ya ɓallo ba.

Ni kuwa har muryata ta dashe ko sautin ihun nawa ya daina fita, hawaye ne kawai suke zubar min, kuma har yanzu bai dena duka na ba, saida yaiwa jikina ruɗu-ruɗu, ya tabbatar da ya min lis, sannan  ya tsaya yana haki, kamar wanda yai dambe da ƙartai, "shiiiiiiii"  ya faɗa yana wani irin huci.

Gefe ya koma gami da harɗe hannayen shi guri ɗaya, kana ya saki murmushin muguntar daya saba.

Ni kuwa duk da dakuwar da nai, baki ba bai mutu ba, saboda cikin raina cewa nike, "mugu, baƙin azzulumi, burin ka yacika kaci zalina, kuma Allah sai yasaka min" .

Wata doguwar ajiyar zuciya naja kamin na fara sauke numfashi da sauri da sauri". Cikin isa da taƙama ya ce "idan naƙara jin kinja ajiyar zuciyar nan wallahi saina sako farkon dukan nan, koma nayi miki mafiyin wanda nai yanzu".

Ya cigaba da cewa "so nake kiyi shiru kamar bakya gurin nan, ke ko numfashin ki kar naji saukar shi, hakan ne kawai idan kikayi zaki temaki kan ki, ki fita da ƙafun ki, batare da anzo an ɗauke ki ba".

Nasan halin yah sadeeq sarai, ba ƙaramin mugu bane, saboda haka nayi Kamar yadda yace kan kace me? numfashina ya fara neman ɗauke wa, ina ta ƙoƙarin dawo dashi ba tare da yah Sadee'k ya gane ba.  ji nike kamar ana so a zare min raina saboda azabar dukan dana sha, gaba ɗaya jikina raɗaɗi yake, ga kaina da nike jinsa kamar zai bar gangar jikina ya faɗi kasa.

Lura da yanayin yadda nike ciki ne yasa yaya Sadeeƙ  cewa " kaɗan ma nai miki wallahi, saboda batun yauba nasha faɗa miki ki dena shigo min ɗaki kamar ɗakin arna, ke bama ɗakina kawai ba, duk inda zaki shiga ki shiga da sallama a matsayin ki na musulma, Amma dayike kunnen ki na ƙashi ne, ina gama faɗa  kike watsar da maganar anan, to wannan shine na ƙarshe wallahi idan aka ƙara ai koki baki sallama ba kika shigo zakiga abinda zan miki".

"Shashasha, Tashi kiban guri, na gaji da ganin wannan mummunar fuskar taki, gashi kin tsura min ido kamar sa'anki ne yake  magana".

Tashi tsaye nayi Ina layi ina bin bango har na iso bakin ƙofar na buɗe. Ina fitowa naci karo da  inna dake faman sintiri. Kamar wacce tayi ƙarya. Cikin sauri Inna takomo ni. zubewa nai a jikin ta babu numfashi, ihu inna tafara tana kiran ya Sadeeƙ da karfin ta, Garba inalillahi wa'innah ilaihi rajiun, shikenan ka kashe ta. Garba...


Read / Download NI DA YAYA SADEEQ

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On NI DA YAYA SADEEQ
avatar
zainab-2-9-9

7 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album