Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

ZUMA SAI DA WUTA Complete Hausa Novel Document by ZUMA SAI DA WUTA


ZUMA SAI DA WUTA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 56092



ZUMA SAI DA WUTA

Reading Time: 4 Hours

Added On: 22, Jul 2023

Author: Xarah Bukar ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Nagarтa Wrιтerѕ Aѕѕocιaтιon

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 309.41 kb

File Type: txt

Views: 1391+

Download: 667+

Last download: 3 days ago

Description/Story: [9/7, 12:35 AM] Xarah Bukar: *Zυмa*
ѕaι da wυтa

na
©хaraн вυĸar

®Nagarтa Wrιтerѕ Aѕѕocιaтιon {NWA)

ѕpecιal тнanĸѕ тo ѕa'eed вeвejι

ѕpecιal greeтιngѕ тo мy вeloved ѕιѕтo Samrah (ĸιna raιna ĸυllυм, ιlyѕм❤)

ғanѕ ĸυyι нaĸυrι da gajerυn pageѕ da zagυ ganι.

(01)

Su hud'u ne zaune cikin had'add'an office dinsa. Ko wanne sanye da kayan yan sanda, saishi na biyar dinsu dake sanye cikin Charcoal Gray and navy blue suit, kakkyawa ne mai cikar zati, kalan fatar sa wankan tarwad'a, ak'alla zai kai kimanin shekaru talatin da bakwai a shekaru. Tattauna issues suke game da ta'addanci da satan mutane dake addaban kasar gabadaya.
Sun jima suna tattaunawa, daga bisani mik'ewa sukai had'e damai sallama suka bar office din. Guntun Tsaki yaja hade da kallon wayarsa dake ruri kusan awanni da suka shud'e, hannu yakai kan desk din yadau wayar hade da dubawa, miss call biyar yagani na Aunty B da na Hajiyar su. Dafe kai yayi cike da tsananin takaicin sanin dalilin kiran. Tsaki ya saki had'e da janyo side drawer na desk din ya fiddo file mai rubuce da sunan Ummi ajiki da stamp din missing daga sama, bud'e file din yayi yanai dubawa yaji an turo kofar office d'in, bai dago ba yacigaba da zabgarsa.
Kyakyawan saurayine mai kimanin shekaru talatin da uku ya shigo, bai karasa ciki ba ya tsaye bakin k'ofar, fuskar sa ba walwala.
"Morning sir"
Ya furta atakaice.
Ba tare daya dago ba.
"Salim Abbas right ?
"Yes sir"
Salim ya amsa cike da haushin yadda ya ambaci sunanshi cikin salon rainin wayo.
Saida ya jima sannan ya Dago ya kallesa, wani mugun kallo ya aikawa mai.
"hope you're clean, kasan i dislike working with drunkard"
Kasa magana Salim yayi zuciyar sa na tafasa, ya mugun tsanan Ogan shi ba kad'an ba, banda 3 weeks suspension daya bashi ya dawo kuma yana neman wulakantashi.
Bai hankalta ba yaji ya cigaba da magana. "kana iya komawa position dinka, amma kasani next time it won't be 3 weeks but a whole life time".
Juyawa Salim yayi ya fice daga office d'in batare dayace kanzil ba banda tafarfasa da zuciyar sa yake.
Shi kam gogan cigaba yayi da duba file din, hotunan Ummi dake ciki yad'au yanai dubawa, kallon k'urilla yakema hoton da tunanin ina zai nemota, asalima she is 10 years a hoton. Acewar hajiya kuma zatakai 19 by now. Saidai babban takaicin sa bai wuce ta ina xan fara binciko taba, a iya sanin sa a Gombe ta b'ata ba Abuja inda yake aiki ba. Rufe file din yayi hade da maida ta cikin drawan sannan ya mike ya fice daga office din. Inda maajiyar motarsa kirar formatic 350 ya nufa ya shiga sannan yama Aunty B text msg na gayanan zuwa. Jan motar yayi bai zarce ko ina ba sai gidan su dake Asokoro na cikin garin Abuja.
***
Shingid'e dattijuwa Hajiya Laurat take bisa lausassiyar doguwar kujeran palon, hannuta rike da waya tana sauraran kiran d'anta da tun daxu take danna mai kira baya picking. Babbar diyarta Aunty Bilkisu ta fito daga kitchen hannunta rike da mug tanai kurban shayin dake ciki, karasa shiga palon tayi tanai kara duban agogon hannuta hade da takaicin rashin karasowa Mujahid, gashi kuma tana da patience dake jiranta a asibiti.
Zama tayi kusa da Hajiya hade da kwantar da murya tace,
"Hajiya a hakura kawai, wanan wahala ce kawai zaki d'aurawa Mujahid, yarinyar nan fah dakanta tabar gidan Ubanta, babu wanda ya koreta, gaskia nidai banga amfanin nemo taba.."
Mugun kallo da Hajiya ta watsa mata yasa tayi azaman tsuke kalamanta.
"Bilkisu ki kiyayeni, na dauka kece babban mai hankali ashe baki da hankali, shiyasa duk cikin ku Jafar yafi yemin, shine kadai ke fahimta ta"
Shuru Aunty B tayi ba tare da tace kanzil ba, saima tsumu tsumu da tayi kamar wace aka tsamo cikin ruwa. tasan halin tsohuwar su yanzu saita dau zancen da zafi ta inda take shiga ba tanan zata fita ba.
Daidai bakin k'ofar palon ya tsaya chak sakamakon kalaman Hajiya na karshe daya tsinkawo a kunnuwansa, sallamar daya ke kokarin yi kasawa yayi jin tanai magana cikin daga murya da fusata.
"Muddin bai nemo Ummi ba saina mugun b'ata masa rai, tun yaushe mukai zancen dashi amma har yau babu feedback kuma lokaci na tafiya burina kawai ta bayyana na hadashi aure da ita"
Tashin hankali da firgici ne suka bayyana a fuskarsa, ji yayi gabadaya jikin ya sank'ame kamar jini bai zagayawa cikin jijiyoyin jikinsa. Dakyar samu karfin motsawa,
ahankali ya fara taku baya sannan ya juya da azama ya koma inda yayi parking motarsa ya tsaya hade da dafe kanshi.
Ruwane ya cinye Aunty B da mamakin kalaman Hajiya, Ummi data baiwa iskanci baya shine Hajiya take kokarin kakkab'awa kaninta, duban hajiya tayi, ganin lailai ba wasa take ba yasata fara kirkiro murmushin dole.

Dafe yake da kanshi kaman xaiyi kuka, gabad'aya Hajiya ta daura mai zafi, bai taba yadda Hajiya batason shi ba sai yau dayaji abunda take shirin aikatawa. Sai dai yayi alwashin hakan bazai faru dashi ba, harga Allah yana da niyya nemo Ummi saidai kudirin Hajiya yasanya bazai nemo taba saidai ma yayi fatan duk inda take a dosar kasar kar ta bayyana. Hannayan sa biyu ya hada had'e dakaiwa glass din motar noushi cikin fusata yanai huci. Horn din mota dayaji yasanya shi waigawa kallon motar data danno kai cikin gidan.
"Ya salam, from one Problem to another" ya fadi aranshi hade da saurin kawar dakai gefe tamkar bai ganta ba, cikin ranshi addu'a yake Allah yasa karta iso garesa.
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: *Zuma*
ѕaι da wυтa

na
©хaraн вυĸar


{02}


Murmushin jin dad'i ta saki sakamakon ganin shi da tayi, taso su hadu da safe kafin ta tafi skull saidai tuni ya rigata sammako.
Gefen motarsa tayi parking motar ta kirar corolla xL sanna ta fito, jikin ta sanye da uniform din Premiere acedemy, short gray skirt da white long sleeve mai hade da maroon necktie.
Da murmushi ta doso shi, ganin ba fuska ya sanya ta shan jinin jikinta, gabanta na dukan uku uku.
"Ina kwana ya Mjay
Mugun kallo ya aikamata tare da kara shan magani.
"Da ban kwana ba zaki ganni anan"
Tsura mata idanu yayi jiran amsarta.
Kai ta girgiza.
"Naga kaman ranka abace.." Tayi shuru idonta ya ciko da kwallah
Gyara tsayuwar sa yayi hade da kokarin bude kofar motar yana fadin.
"bana hanaki shiga hurumi naba, waiku matan nan miye matsalan kune".
Guntun saki yaja cike da takaici yadda mata ke bada kansu, balle yar karamar yarinyar dake tsaye gaban sa, shiyasa har ilah baiga perfect woman data dace dashi ba.
Marairace murya tayi tace "yaya kayi hakuri, am not happy da yadda na ganka ne.
Tsaki yaja, tsayawa mata magana bata lokaci ne, shigewa yayi motar hade da janta yabar ta nan tsaye jiran tsammani.
Sakin baki tayi tanai kallon motar harta fice daga gidan, Kaman zatayi kuka ta wuce Jiki sanyaye ta fara takawa cikin gida. Duk a gaban ido Jafar, daga windon saman dakinsa ya hango draman su, tabe baki yayi, aranshi yanai fadin duk shishigi da takemai bashi zai hana ya gwasaleta taba, cusa kai ba kwarjini. Daukar wayar sa yayi ya fito daga dakin hannusa rike da briefcase da suit jacket, cikin sauri ya sauko daga stair din, inda Hajiya take ya nufa hade da mata sallama daman tuni tasan da tafiyar sa kaduna akan wani case dinsu can na kare hakkin mutane, addu'ar saukar lafiya da fatan alkhairi tahau zuba mai, Aunty B kuwa shuru tayi gudu kartace wani abun tasha fada.
"Aunty kina nan ashe baki wuce ba" Jafar ya fadi.
"Yayanka ya shanyamu, nima tashi xan na wuce" Mikewai tayi tana ci gaba da fadin "hajiya nikam na wuce aiki, sai wani zuwan"
"A sauka kalau, ina gaida yaran" acewar hajiya cikin kota kula da yanayinta.
Daidai Bakin kofar sukayi kicibis da ita zata shigo, ganin aunty B yasata sakin fara'a hade da gaidata.
Cike da faraa ta amsa mata hade dacewa "Junaina harkun tashi so early"
"Aunty yau bamu da exam, chilling da friends ya kaini skull, gajiya nayi na dawo, mun kusa ma gama Waec din"
Aunty B tace "Allah ya baku saa.." Cikin saurin tayi maganar sakamakon wayarta data shiga ruri, hannu ta daga mata hade da ficewa tanai kokar daukan call din, Sai sannan ta lura da Jafar dake tsaye yanai kallonta, da alamun bashi da shirin yi mata magana.
"ya Jafs sai ina haka rike da briefcase" ta fadi hade da karasawa ciki, zama tayi kusa da hajiya cikin salon yauki da shagwabe fuska..
Yace "idan kinason...


Read / Download ZUMA SAI DA WUTA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album