Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

MUQADDARI NE Complete Hausa Novel Document by MUQADDARI NE


MUQADDARI NE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 177952



MUQADDARI NE

Reading Time: 14 Hours

Added On: 14, Jun 2024

Author: Rahmatullah Muhammad ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08064400100

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 976.01 kb

File Type: txt

Views: 381+

Download: 1161+

Last download: 8 hours ago

Description/Story: ο»Ώ[7/31, 2:00 PM] Reine Ghana: πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€πŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€MUQADDARIπŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€2018πŸ™†πŸ½β€β™€
πŸ™†πŸ½β€β™€


1⃣


RAHMATULLAH (Hajia)



Har soron qarshe na cikin gidan suka shiga kana ta sauke qaton bukitin pentin dake kanta wanda ke cike da ruwa, ta kalli qaninta mai kimanin shekaru 11 tace "Nura dauki ka shiga dashi, ai xaka iya ko?" ya fara kicin kicin daukan bokitin yana cewa "eh ya SAKEENA, ai qarasawa ne kawai" ta labe a bayan kyaure shi kuma ya shiga cikin gidan da ruwan kamar shi ya debo.


Haka suka dunga debowa tana kawo masa har cikin soro yana qarasawa dashi saboda fin qarfinsa da bokitin yayi. Sai da suka cika duk abunda ke gidan sannan matar gidan ta dakko kwanansa ta xuba masa dafaffiyar taliya da manja da yaji, yayi mata sallama inda tai masa umarnin ya dawo da yamma.



Ya fito soro inda sakeena ke rabe ya nuna mata taliyar yana washe baki da cewa "ya Sakeena yau taliya akai, kamar tasan ina san taliya, taho muje gida muci" taja hannunsa suna tafiya itama da murmushin daya xame mata dabi a indai tana tare da Nura, ita kan ta rasa irin son da takewa qaninta Nura tanajin kamar itace uwarsa da ubansa.


A tsakar gida suka tadda matar babansu mai suna Inna, da harara ta bisu har suka ci burki a gefen tsakar gidan inda nan aka ware musu gurin xaman a tsakar gidan wanda Inna bata gajiya da fada musu cewar ko raban gado aka tashi baxasu samu inda ya wuce nan ba.



Idon Inna akan kwanan hannun Nura, tai kwafa da cewa "sannunku barbadaddu daga makarantar sai kuka tafi yawon barbada ko? Memakon ku dawo ku cire uniform yanda kowane dan arxiqi yake cirewa" Nura da bai cika raga mata ba ya harareta yace "ba yawo mukaje ba neman abinci mukaje, ba a bamu ba ai dole mu fita mu nema" sakeena tai saurin toshe mai baki tana juya musu taliyar. Inna kuwa kamar mai jira tahau sababi "eh baxan baku ba, ubanku meya mutu yabarmun banda wannan kejin gidan? Ita kuwa ba a xancen matsiyaciyar uwarku domin haka taxo garinnan da sunan aure daga ita sai kayan jikinta, wlh bantaba ganin abun kunyar dana gani akan uwarku ba wai kaxo gidan aure ko cokali babu balle tabarma shiyasa baxan daina xargin a bariki ya samota ba."


Duk da maganganunta na yiwa sakeena ciwo bata nuna hakan ba, sun duqufa lomar taliya kuma dama andade ba a hadu ba πŸ˜„. Ana haka qaramin dan Inna ya shigo me suna umar shekarunsa 6, idonsa na kaiwa kan taliyar ya nufesu yana cewa "lah taliya? Xanci," suka matsa masa ya xauna zaisa hannu kenan Inna taxo ta janyeshi yana tirjewa tana cewa "wlh baxakaci taliyar nan ba, inkaci kaci hantar ubanka, babu abunda ya hadaka da wadannan tanbadaddun" sakeena ta dago idonta taf kwallah, bata jurar duk sanda inna ta rabasu da yayanta saitayi kuka itadai tanason yan uwanta yan uba duk da inna bata bari ko doguwar magana ta hadasu. Muryarta na rawa tace "Inna dan Allah ki bari yaci, umar dan uwanmu ne Allah ya hadamu dasu bamu da wadanda suka fisu ku... " ta tari numfashinta "yimun shiru uwar tsara xance anyo gadan dadin baki irin na yan bariki a gurin gyatuma, karki kuskura ki kuma hada yayana masu usuli da ku, domin su in aka fara xayyano nasabarsu sai an dangana har kan sarkin musulmi. Ku kuma in banda qedarar uwarku mai kama da bulalar dukan mahaukata da idanu kamar na mayu da aka kawo mana ko kare ba a kuma nunawa da sunan dangin uwarku ba. Ai wannan qedara ta cuceni ta batamun zuria ta haifamun wake cikin shinkafa" ta qarasa tana share hawaye.



Sakeena ma hawayen take, inda sabo yaci ace ta saba da wannan gorin na inna amma xuciyarta bata jura duk sanda inna ta kira uwarsu da qedara kuma karuwa sai tayi kuka. Ta cire hannunta a taliya duk kuwa da yunwar da takeji ta barwa Nura yanaci dake shi bai gama sanin abunda duniya take ciki ba.



Tana yawan tunanin mahaifiyarta, sassanya doguwa fara me dararan idanuwa, duk bata gama wayo ba uwar ta mutu ta barsu cikin wata irin bahaguwar rayuwa wacce tayi tsananin qazanta bayan mutuwar ubansu. SAKEENA ABBAKAR LIMAN kenan.

**** **** **** **** **** **


Tun matar gidan da Nura ke aikatau bata lura da cewar aikin da Nura keyi na debo ruwa yafi qarfinshi harta gane, saboda kama sakeena da tayi a soro a tsaye taje xubar da shara ta tuhumeta me takeyi anan ko taxo yimata sata ne? Tsoron ambatar sata da tayi yasa sakeena fada mata gaskiya qanin take tayawa debo ruwa abasu abinci. Matar ta yamutsa fuska tana tambayar sakeena "wai ku baku da iyayene?" a dan diririce sakeena ta bata amsa "a e ai sun mutune" jikinta yayi sanyi jin hakan ta gyara tsaiwa tace "to aikema sai kixo indunga baki wani aikin kinayi, sai inbaku abincin da zai isheku." sakeena ta sunkuya har qasa tana mata godia.



Tundaga wannan rana suka xama bayi a gidan wannan mata. Da asuba tayi suke tashi suyi sallah sutafi makatar allo wacce sukeyi anatashi zasu tafi gidan aikinsu wanda da farko aikin sakeena a gidan shara da wanke wanke kafin daga baya matar gidan ta fuskanci sakeena qaqqarfar yarinyace ta hada mata da wankinta da kuma na yaranta wani lokacin harda na mijinta dan tsabar zalunci. Suna gama aikin safe zata basu dumamen abincin dare wani sa in da ruwan koko ko shayi suci su tafi. Sukan koma gida sako uniform din makaranta wanda daganan komi makarar da sakayi se sunyiwa inna nata aikin ba tare data basu koda ruwan gidan ba sannan su tafi makarantar boko wacce suna tasowa gidan aikinsu xasu dura suyini cur suna mata bauta har laasar lokacin shiga makatar yamma sannan su tafi in sun dawo ma nan suke komawa sudanyi abunda yarage kafin magrib su tafi gida da kwanon abincinsu na ladan bautar da suka yini sunayi. Suna sa qafa a gidan gorin Inna zaice salama alaikum tasasu agaba da zagi da gori da ambato uwarsu dake qarqashin qasa, hakan kuma baya hana acinye abincin da nata yayan duk kuwa da qoqarin hanasu da take.



Yakasance aikin yabi jikinsu harma da qarin wankau da sakeena keyi dan samar musu sabulun wanka dana wanki dan su huta gorin Warin dauka da kyamar zama kusa dasu da akeyi. Ada idan matar gidan tasata wankin yayanta takan faki ido tasa kayansu a kumfar ta wanke, cikin akasi ta kamata tai mata tas harda barazar korarsu daga aiki tayi, acewarta ya xata hada kayansu me baqar qazanta dana yayanta? Tun daga ranar sakeena ta samarwa kanta mafitar yin aikin wankau dan samar musu abun wanki.



Cikin qanqanin lokaci ya zamana sakeena da Nura yayan margayi Mal Habu Liman kanyi kowane irin aikin qarfi domin abasu abinci. me nema na tare da samu, sun sami saukin rayuwa ta fannin samun abin kaiwa bakin salati amma suna bautuwa bautar data wuce abunda ake basu.

***** **** ***** ***** ****

ASALINSU


Mal Abbakar Liman su biyu ne suka taso a gurin mariqinsu shi da yayarsa Hafsatu. Iyayensu sun mutu tun suna yara, riqonsu ya dawo hannun qanin ubansu. Hafsatu tayi aure da wani malamin makarantar secondary a qauyen wanda daga qarshe ya samu canjin gurin aiki daga qauyen zuwa cikin garin kano.





Yayin da Abbakar yakai munzalin aure kawunsa ya dade da rasuwa, kasancewar basu samu illimin zamani ba yasa yake sanaar jan mota xuwa garuruwa. Dafarko da karan mota ya fara kafin daga baya ya koma driver. Acan qauyensu (BAGGADANO) cikin qaramar hukumar Dawakin tofa a jihar kano ya hadu da Lauratu wacce ta kasance matarsa ta fari auren saurayi da budurwa. Sun haifi yaya 4 da Lauratu wacce yayanta ke kira da Inna kafin ya auri mayafiyar su sakeena.




Ya hadu da itane a wani xuwa da sukai da motar Lakoja (kogi state) ita kuma takasance tana tallan kifi. Xuwansa na farko suka hadu a tasha suka fara soyayya suka rabu bayan lokacin tafiyarsa yayi hankalin ta ya tashi amma yayi mata alqawarin xai dawo.


Mahaifiyar su sakeena ta kasance yaren Igala kuma mabiyar addinin Christa, duk da tasan akwai hatsari sosai kasancewar Abbakar bahaushe kuma musulmi amma ita soyayya bata shawara balle ta fada...


Read / Download MUQADDARI NE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album