Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

CLASS MATE Complete Hausa Novel Document by CLASS MATE


CLASS MATE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 2803



CLASS MATE

Reading Time: 0 Hours

Added On: 30, Oct 2023

Author: Zainuddeen Jibril ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08034840276

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 15.15 kb

File Type: txt

Views: 896+

Download: 262+

Last download: 24 hours ago

Description/Story: “CLASS MATE”
( ungulu da kan zabo )


















ZAINUDDEEN JIBRIL
Tel: 08034840276
Email: deenysalaf08@gmail.com

GODIYA


Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, wanda iyawarsa ta zarce tunaanin kowa da komai, shi ne masanin sirri da ma abin da ke sarari, ikonsa ya wuce hasashen mutum bare dabbobi, shi ne kadai ke tafiyaar da lamura ba tareda karkata ba.


Salati ba adadi na yo gun Annabi Muhammadu (SAW) dan gata kuma sha lelen ubangiji, wanda binsa ya zamo wajibi kuma tilas akan duk mai kaunar ya sami dacewa da gidan tsira a gobe kiyama.


Na hada da iyalan gidansa da sahabbansa, tareda duk wadanda suka bi tafarkinsu ya zuwa ranar tonon asiri.


Ina mika godiyata zuwa ga mahaifiyata, da Allah ya sadata da gidan aljanna ya kuma kara daukakata ya yafe mata zunubanta ya lullubeta da rahama da jinkansa. Inason mamata sosai.


Masoyana, ina jinjina gare ku, da kokarin karatun kwamacala da nake gwaba muku, a hakan dai kuke daurewa kuke karantawa, Allah ya bar mu tare, ina yin ku irin sosai dinnan.



TSOKACI


Wannan labarin gajere ne kuma kirkirarre ne, na rubuta shi ne lura da wata barna da ke faruwa a cikin jama’a; in da za ka ga tsakanin mace da namiji kamar wasu mata da miji ko muharramai a yadda mu’amula ke gudana tsakaninsu, duk da sunan “class mate” wato abokin karatu a aji.


Labari ne na Sumayya tareda mai gidanta Ahidu, wadanda suke zaune lafiya da junaansu, suke gudanar da komai a gidan aurensu yadda ya dace, kafin tsautsayin “class mate” ya hau kan Sumayya, wanda ya yi sanadiyyar rusa duk wani farin ciki da suke ciki har ta yi danasanin kasancewa daya daga cikin wadanda suka yi boko.


Kamaar yadda na fada a sama, cewa labarin kirkirarre ne, sunaye da wurare da na yi amfani da su suma kirkira na yi, duk wanda ya ga sunansa ko halayyarsa ta dace da labrin ko jigon labarin, dace ne kawai.


Na yi wa dan gajeren labarin suna da “class mate”. Ina rokon ubangiji da ya datar da mu da alkhairi ya kuma sa abinda za mu rubuta ya fadakar ya kuma sa ya zama sanadiyyar tsirarmu a gobe kiyama.



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




Kamar kullum yau ma tun safe na ci kwalliya bayan da muka kammala break fast ni daHuubyna, tun ina cikin shower nake tuannin yadda yake kallona cikin shauki da nuna soyayya, hakan ta sa sai rero wakoki nake na Hausa hip-hop na Zainuddeen Zain ina cike da murna da bege hade da shaukin kauna, har nake ji, ba macen da ta kai ni dacen miji. Mijina ba ta yadda safiya za ta waye ba tareda ya gayamin zantuka masu ratsa zuciya ba, haka ko a cikin mutane ba ya gazawa wurin nunamani kauna, hakan ta sa nake bugun gaba da shi.

A jikina English wears ne, dan guntun skirt wanda ba zai wuce rabin cinyata ba, baki ne, wanda ya baiwa farar cinyata damar bayyana sosai, sai pink riga da ta matse ni sosai kamar dai yadda skirt din ya matse ni, sai rolling na gashin kaina da na yi kasancewar ba kitso a kaina, sosai ni kainaa ina jiyo kamshin gashin kaina wanda ya yi tsawo kuma ya ciko, duk ba wannan nake alfahari da shi ba, sai yadda Ahidu ke hadiyar yawu a duk lokacin da ya dora idanuwansa a surar jikina, ni kuwa sai tashi nake da gangan da sunan dauko wani abu a fridge ko daki, kawai domin na yi rangwada ta gabansa yadda zai ji dadi.

Sai fira muke yi kasancewar duk ranar weekend haka muke yi, ba ya zuwa ko’ina sai da maraice mu fita yawon zagayawa a kafa. Soyayya dai tsakanina da mijina har ta wuce kwatance.

Wata rana da ba zan taba mantawa da ita ba, mun tafi shopping mall domin mu yi sayayya, daga isarmu, na hango Sufy. Sufy class mate dina ne da muka yi kratu a jami’a ta JASU (Jarwo State University). Daga nesa muka fara jefawa juna zagi, “ke shegiya, ashe kina nan?” “shege mugun kwaro ina kuma aka shige?” daga isowarsa ya miko min hannu, ni kuwa abinka da sabo na mika masa muka tafa, ya rike hannuna cikin nashi, sai fira muke ta tuna baya, hannuna a cikin nashi yana wasa da shi, cen ya kalleni ya ce, “wallahi Sumy kinanan da kyawunki kalli fa yadda sai wani fresh kike karawa ga jiki duk ya ciko..” sai a lokacin na tuna fa tare muke da mijina Ahidu, kuma a kusa yake da ni, waigowa da zan yi, na ganshi sai mamakinmu yake, fuskarsa cike da alamar tambaya, gaba daya idanuwansa suka rikide suka koma ja, Ahidu da yake da haske sosai Fulani ne ga gemu mai tsawo da kasumba, amma haka fuskarsa ta dawo jawur, ya hadiye fuska kamar wanda aka turowa da sakon mutuwa. Na kalle shi, cikin rashin nadama na sake mayar da kallona zuwa ga Sufy, sai na ce “ga mijina” shi kuwa cikin rashin nadamar abinda ya aikata, kuma ya ki ya saki hannun nawu ya kalle shi ya ce “Ah! Yallabai kai ne ka kwashe muna most beautiful yarinya on campus?” ba tareda ya kalle fuskarsa ba, kawai ya dubi hannunsa da ke rike da nawu hannun, ya fara tafiya zuwa mota. Ganin haka nasan akwai matsala, cikin sauri na fizge hannuna cikin nasa, yana cewa “lafiya” na kasa ko na amsa masa, na fara sauri domin na tarar da mijina da ke kokarin bude kofar mota.

Sufy kuwa sai ya rike baki yana mamakin wannan abin, cen ya gyada kai ya wuce.

Ina masa magana, amma sam ya ki ya kulani nayi magiya na yi shagwaba na roke shi amma sam ya ki ya ko kalleni, tuki kuwa sai takar mota yake yi kamar wanda zai tashi sama, saura kiris mu buge wata mai tuyar awara kan titi.

Da misalin shida da sha bakwai na maraice muka karaso gida, ya fita ya bude gate din gida ya shiga ya yi parking, har yanzu dai ya ki ya ko kalle ni, ‘yan kayayyaki da muka siyo daga Shopping Mall dole ni na dauko su na saka cikin gida.

Shigowata ta yi daidai da shima zai fita, har yanzu fuskarsa a murtuke, har ma murtukewar yanzu ta dara ta farko. Na rike hannunsa, na ce “Hubby me ke faruwa ne?” ya janye hannunsa ba tareda ya kalleni ba ya fice abinsa cikin sauri.

Bayan na ajiye kaya, na shiga zullumi da tunanin me na yi wa wannan bawan Allah, iya sanina muna zaman lafiya, yau shekararmu daya da wata uku da aure, duk da ban haihu ba, ko kadan bai taba nunamin wani abu da rayuwata za ta iya baci a kansa ba, yana nunamin kulawa da soyayya, har ta kai ga ya shwagwaba ni, yau kuma ga shi yana kokarin jefa ni cikin yanayi da ban taba tsintar kaina a ciki ba. Nan wasu zafafan hawaye suka fara rigangayar sauka a lallausan kumatuna, tuni sautin kukan ya ci karfina har da shessheka, naci kuka har aka tada sallar magariba, na je na yi sallah, na dawo na dauko abincin da na girka muna kafin mu fita, na jera kan dining table, na shiga kamar yadda na saba na tsala wankana, da daukar kwalliya mai jan hankali, na dire kan TV ina kallon tashar Equity TV, ina jiran shigowar Hubbyna, amma shiru har aka fara sallahr isha, abinda ya bani mamaki sosai kenan, domin tsawon zamana da shi, duk inda yake, to bayan magariba yana gida, domin a lokacin muke cin abinci, idan muka kammala isha kuma, sai mu shiga fira har ila ma sha Allahu.

Daga ida sallah na dauko wayata coolpad, na danna lambarsa, amma har ta katse ba a dauka ba, a raina nace inaga aiki yake yi, na sake dawowa na dirshe a bakin TV naa ci gaba da kallo. Ban Ankara ba agogo ya buga kusan sha dayan dare, a lokacin har barci ya daukeni na farka, na sake janyo waya, na kira, kawai sai naji karar wayar a parlour, fitowa da zan yi, sai na ga Ahidu kwance kan three seater, waya cen kan teburi, sai kallon sealing yake yana karatun wasikar jaki. Nazo cikin rangwada na hau kujerar na dafa jikinsa da niyyar na sumbace shi, sai ya tashi zaune, fuska a murtuke.

Ganin haka na gurfana na saki kuka na ce “ka dubi girman Allah ka sanar da ni, laifin da na maka.” Ganin na shiga damuwa ya ce da...


Read / Download CLASS MATE

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album