Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

╨╧рб▒с>■  └┬■   ░▒▓│┤╡╢╖╕╣║╗╝╜╛┐                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                    ье┴g Ё┐0,╡bjbj┌к┌к *╕└ob╕└ob6т       ╖**жжжжж    ║║║║ ╞|║╥74BBBBBё$є$є$є$є$є$є$$9╢╝;P%uж%жжBB█М7╜$╜$╜$ЎжBжBё$╜$ё$╜$╜$╜$B    а╠d$щ┘    $p╜$▌$в70╥7╜$ <Г$: <╜$ <ж╜$ ╜$%%╜$╥7                                                                     <*B l:  An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels
[11/14/2019, 4:19 PM] =╪Ю▄Noorunnisa=╪Ю▄: *_Typing=╪Є▄_*



*_=╪б▄HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=╪з▄MUTUM DA DUNIYARSA....!!=╪з▄_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>╪▌<╪√▀_*


*_й2019_*


*(P3REP qDDQNGP qD1QN-RENpFP qD1QN-PJEP*

_In the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful._



*[1......]*


............Tafe take tana zirar da hawaye masu d'umi da saka k'unar zuciya. Kasantuwar Nikab d'in dake sakaye da fuskarta ya hana bayyanuwar kukan nata ga mutane, dukda dai hakan bai hana wasu kallonta ba, musamman wad'anda sukeda tabbacin itace.
Cikin Nutsuwa da sanyi take tafiya, kanta a k'asa dukda kuwa tana sanye da dogon hijjab da nik'ab. Isowarta inda zata yasa ta tura murfin k'ofar gidan kalar madara ta shiga da sallama.
Dattijuwar da bazata gaza shekara hamsinba ta d'ago daga d'ibar ruwan da take a rijiya ta amsa Mata.
УWa'alaikissalam, yanaga kin dawo dandanan? Kobaki iskeshi a gidan bane?Ф
Nik'af d'inta ta yaye, kamilalliyar fuskarta ta bayyana, ta d'an sakin guntun murmushi tace, УEh Umman mu, na tarar har ya tafi kasuwaФ.
Batareda ta jira amsar Umman tasuba ta wuce gaba. Binta da kallo Umma tayi, ko kad'an bata yardaba, tasan ta 6oye mata ainahin abinda yafarune acan kamar yanda ta saba gudun kar ranta ya 6aci. Ta d'an sauke ajiyar zuciya tana girgiza Kai, sannan ta ajiye gugan hannunta ta d'auraye hannun da ruwan data jawo ta nufi d'akin da yarinyar ta shiga.
Zaune ta isketa ta zabga uban tagumi tana cigaba da kukan, amma jin sallamar Ummansu sai tai saurin share hawayenta ta maye gurbinsu da murmushi. Da kallo kawai Umma ta bita tana mamakin zurfin ciki irinna y'ar tata, ita har tausayinta take gameda zaman gidan aure, idan bata sami miji na gariba sai dai aita cutarta........
Maganar budurwar ya saka tunaninta katsewa.
УUmma wai su Zarah basu dawoba har yanzu?".
Zama tayi kusa da ita tana fad'in УBasu dawoba Nafisar ma ta kirani tace sai zuwa yamma zasu dawo, zasuyi Mata wani d'an aikiФ.
УHumm ni dad'ina da Aunty Nafisa kenan, baka isa kaje gidanta kafito bata nanuk'a maka aikiba, son jikinta yayi yawa wlhy ita da Zarah UmmaФ.
Murmushi Umma tayi kawai, amma batace komaiba. Sai da taga budurwar zata mik'ene tace, *УJIDDAH!,* dawo ki zauna muyi maganaФ.
Babu musu ta dawo inda ta tashi ta kuma zama, УTo Umma gani, wacce magana ce?Ф
Numfashi Umma ta sauke, kafin ta tsare Jiddah da idanu, УJiddah ya kukayi da Abbanku?Ф.
УLah Umma aina cemiki ban iskeshiba, yatafi kasuwa sanda najeФ.
УBan yardaba Jiddah, nifa mahaifiyarku ce, duk d'inku nasan halin kowanne, ki daina k'ok'arin 6oyemin abinda ba sabo bane a gareni da rayuwataФ.
УUmma kiyi hak'uri, aganina yawan maimaita magana bashida amfani, hak'uri da mantawa da abinda yawuce shine dai-daiФ.
УDuk nasan da hakan Jiddah, kedai fad'aminФ.
УShikenan Umma tunda kin matsa. Na iske Abba a gida yanama Karin kumallo, bayan mun gaisa dashi da aunty Amarya, saina sanar masa nazone ya taimakemu da kud'i su zarah sun koma hutu, gashi kuma basu biya kud'in makaranta ba belle su kuma, gashi su waleeda Jsce zasu zana a wannan shekaran. Wlhy Umma bakiga yanda Abba da Aunty Amarya suka hayayyak'o minba, har Abba yana fad'i bazai gaji da takaicin *HAIHUWAR y'ay'a mata* ba harya koma ga ALLAH, wai mune muka dabaibaye DUNIYARSA shiyyasa yakasa gaba ya kasa baya, shi baiga amfaninmu ba inama laifin ciyar damu abinci da yakeyi, yariga ya rantse sisin kwabonsa bazai ta6a kashewa akan muyi karatu ba, gara ya sayama su kalifa ice-cream yasan duk tsiya nan gaba zai amfana dasu...........Ф kuka ya sark'eta takasa k'arasa maganar, saima fad'awa datai jikin Umman.
Shiru Umma tayi takasa cewa komai, sai k'ok'arin Had'iye wani Abu daya tsaya Mata a mak'oshi takeyi, yayinda hannunta ked'an bubbuga bayan Jiddah.......
Jiddah takuma katse Mata tunani da fad'in УUmma wlhy Duniyarnan tama fitarmin akai, wataran nakanji tamkar zancen Abba gaskiyane mu Mata bamuda wani amfani acikin wannan al'ummar, kowa gani yake amfaninmu daga a haifemu sai muyi aure mu haihu, babu wata gudunmawa da zamu iya kawowa a duniyarmu, mune muke d'aukar ciki, muyi goyonsa, mu haihu, muyi raino, muyi tarbiyya mutum yakai wani matsayi, amma MACE itace zai fara k'ask'antarwa, MACE itace zai fara d'auka mara muhimmanci, itace zai Fara kira mai k'aramar k'wak'walwa, itace zai Fara kira mai k'aramin tunani, itace wadda yake Fara kallo takalminsa abar takawa ako yaushe, mune jagororin AL-UMMA amma mu ake maidawa MAK'ASK'ANTA, Umma Abbanmu namana haka to yaya Miji zaimana muji haushi? Anya kuwa Umma Abbanmu y..........Ф
Da sauri Umma ta rufe bakin Jidda tana fad'in УKul jiddah karna sakeji, koma dai minene shi mahaifinku ne, bai cancanci kowanne irin furiciba, addu'a itace kawai makaminmu da hak'uri kinjiФ.
Kai Jiddah ta d'aga Mata tana share hawaye.
Umma tace, УInaga kawai Zan samu Na saida Kujerunnan su koma makarantar, dan duk suna a ga6ar dabai kamata ayi wasa da itaba, kodai karatun secondary d'in suka samu ALLAH ya amfana, mutum dai yasamu abin fidda kai aduk inda ya tsinci kansa, kema da bakiyiba keda y'ar uwarki ALLAH ya baki miji nagari dazai kula dake kamar yanda y'ar uwarki ta daceФ.
УAmeen Umma, amma baikamata a saida kujerunnan ba, mudai jira muga kozai biya d'in kokuma Uncle zai dawo da wuri, dan nasan shima hankalinsa Na nanФ.
УHumm Jiddah kenan. Kema dai kinsan hali basai nafad'aba indai Abbanku ne, mudai jira yahayan kawaiФ.
Shiru Jiddah tayi tana had'iye wani Abu mai d'aci daya tokare mak'oshinta, ji take da zata samu wata dama akan MAZA masu irin halin Abba, to lallai shine Wanda zata Fara hukuntawa domin na bayansa su Shiga hankalinsu da koyar yanda zasu *MARTABA Y'AY'A MATA*.


('('('('('('('('('('('


*ASALIN LABARIN*

*Alhaji Zakari yaro* d'an asalin jihar Adamawa ne, amma mazaunin kano, dan acikin kano ya bud'i ido yagansa tun a zamanin k'uruciya, ALLAH yayima Mahaifinsa rasuwa tuni, amma sai mahaifiyarsa taci gaba da zama bata koma Adamawa ba, ita tacigaba da kula da al'amuransa harya kai munzalin aure. Da kanta tabashi damar nemo matar aure, anan kano kokuwa cikin y'ay'an dangi dake Adamawa.
Cikin ikon ALLAH ya za6o matarsa cikin dangi, dankuwa acan Adamawa tushensa ya d'akkota, hasalima auren zumincine a tsakaninsu. Sosai mahaifiyarsa tayi murna da za6insa tai ta sanya masa albarka. Babu 6ata lokaci aka shiga shagalin biki Na y'an gata, domin kuwa su biyu iyayensu suka Haifa, dagashi sai k'aninsa yahaya. Ansha biki amarya Aminatu ta tare anan cikin birnin kano. Zamane akeyi mai cike da nagarta da k'aunar juna, dan kuwa suna son junansu, sai da Aminatu ta shekara uku a gidan miji sannan ALLAH yabata ciki, zokaga murna wajen Zakari da mahaifiyarsa da k'aninsa yahaya, a kullum fatan Zakari Aminatu ta Haifa masa d'a Namijine, wataran har takanji haushi a yanda yake nuna k'iri-k'iri yafison a Haifa masa y'ay'a maza, to idan ta haifi mace kenan bayaso? Idan wannan tambayar tazo mata a rai hankalinta yakan tashi, domin tarasa yanda zuciyarta zata iya kar6ar amsar.
ALLAH da ikonsa ciki ya isa haihuwa, a wani daren lahadi Amina ta tashi da nak'uda, gabannin asuba da taimakon ALLAH dana surukarta ta haifo y'arta mace. Tunda mahaifiyar zakari ta sanar masa abinda aka Haifa saiya canja fuska, murnar da yaketayi takoma ciki, batare da yako d'auki y'ar ba ya buga takalminsa ya fice, bai dawoba sai da daddare, wasa-wasa dai Zakari yak'i d'aukar yarinya, hud'uba ma sai wani makwafcinsu yahaya yakira bisa umarnin mahaifiyarsu akaima yarinya. A kayan shagalin suna da ya saya saiya raba uku yabada kashi d'aya, mahaifiyarsa batasan abinda ke faruwa ba, dan a gabanta 6oyewa yakeyi, sai a daren sunan da taga kayan daya kawo takaici ya kamata, kiransa tai ta nema ba'asi, nanfa yashiga kame-kame, itako ta balbaleshi da fad'a, ta inda take shiga ba tanan take fitaba, yayinda shikuma yaketa bada hak'uri da neman afuwa. A daren yakawo sauran kayan, washe gari akasha shagalin sunan baby dataci suna SAUDA.
Bayan haihuwar Sauda zaman Amina da Zakari ya canja alk'ibla, ya janye mata sosai, dukda ta damu amma saita danne zuciyarta darajar mahaifiyarsa dake k'yautata mata, da gudin tsinka igiyar zuminci. Shekarar Sauda biyu takuma samun wani cikin, nanma dai Zakari yakuma k'wallafa rai ga haihuwar d'a Namiji, yakoma ririta Aminatu. Itadai mamakinsa take ainun, amma bata ta6a cewa dashi uffanba har cikinta yakai haihuwa.
Tab an da6a kenan, inji masu iya magana, dan kuwa wannan karonma Aminatu Mace ta sake haihuwa k'yak'yk'yawa San kowa k'in Wanda bai samuba, itadai murna tai tayi da kuma godema ALLAH da wannan k'yauta. Amma ga zakari ba haka bane, dankuwa jiyay yakuma tsanar Amina, wai danmi zataita cika masa gida da y'ay'a Mata. A wannan Karon koda ya takalota da fitina bata d'aga masa k'afaba, tai masa tatas, wannan shine silar guntulewar aurensu, sai a gidansu aka rad'ama jaririya suna Hannatu, dan kuwa Zakari yace yabar mata bayaso. Ran mahaifiyarsa yakai k'ololuwar 6aci, ta tattara kayanta takoma Adamawa ita da yahaya.
Shekarar su d'aya da rabuwa da Aminatu yasake aure, Wanda da k'yar mahaifiyarsa ta amince, saida ma Baban Aminatu ya saka baki.
Saidai wannan karonma auren Zakari da Ai'sha baiyi k'arko ba, dankuwa tun a haihuwar farko suka raba jaha, sakamakon haihuwar d'iya mace mai suna Zulaiha. Itama yace bayaso ya barmata. Ananma sosai mahaifiyarsa ta fusata, amma bisa hak'urin da dangi sukaita batane yasata hak'ura. Zakari yakuma auren Rammah. A haihuwar farko Rammah ta haifi mace itama, tashin hankali kenan, dankuwa Zakari yakai k'arshen fusata da haihuwar Mata da ake masa, a cewarsa haihuwarsu batada wani amfani sai d'orama mutum nauyi (=╪A▐humm).
Itama dai batakai labariba ya 6alleta tareda bar mata y'arsa mai Suna Nafisa tace bazata rik'eba. Dole ruk'on Nafisa yakoma hannun mahaifiyarsa dake Adamawa.
Bayan Aurensa da rammah saida ya shekara hud'u bai k'ara zancen aureba. Sai kuma rana tsaka ALLAH ya had'ashi da Y'ar Shuwa wato Yagana, Zakari ya had'u da Yagana ne a Adamawa, lokacin yazo gaida mahaifiyarsa, yayinda Yagana kuma sunzo biki makwaftansu mahaifiyar Zakarin. Dandanan soyayya ta k'ullu a tsakanin yagana da Zakari, dukda sukarsa Na auri saki da k'in haihuwar y'ay'a Mata da akaita kawo Mata. Ba awani ja lokaciba manya suka shiga magana, akaje har Maiduguri aka d'auro auren Yagana. Saida tayi sati biyu a Adamawa sannan suka taho kano, bisa ga dogon gargad'i da mahaifiyarsa tai masa, takumace inhar ya Saki Yagana ALLAH ya isa bata yafeba koda a bayan rantane...........
'<╪√▀



(Turkashi=╪F▐<╪√▀).






*_ya RABBI ka gafartama iyayenmu=╪-▐=╪O▐<╪√▀_*
[11/14/2019, 9:49 PM] =╪Ю▄Noorunnisa=╪Ю▄: *_Typing=╪Є▄_*



*_=╪б▄HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=╪з▄MUTUM DA DUNIYARSA....!!=╪з▄_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>╪▌<╪√▀_*


*_Ya rabbi kabani ikon fad'ar abinda zai amfanar da al'ummarka, ka tsare harshena daga fad'ar abinda zai cutar daku da ni baki d'aya._*=╪-▐=╪O▐<╪√▀


_Ya ALLAH ka gafartama mahaifina abin alfaharina da dukkan y'an uwa musulmai da suka rigamu kwanta dama=╪O▐<╪√▀=╪-▐_


*_Wannan littafi tukuycine a gareku my sweet sisters, ina gidiya da karamcinku gareni, alkairin ALLAH yakai gareku a duk inda kuke._*>╪p▌>╪p▌>╪▌<╪√▀

_Billy s Fari_
_Ummu Basheer_
_Fareeda Musa sweery_
_Ai'sha Manshat_
_Hafsat writer d'in Hafiz_


__________________________________


*_[2.....]_*


................ Zakari dai yataho da Yagana kano cikeda farin ciki, sunkumazo sun zauna lafiya har ALLAH yabata ciki itama, a lokacinne kuma yahaya shima yadawo kano suka cigaba da kasuwancin atanfofi da shaddoji shida d'an uwansa Zakari.
To a wannan Karon dai Yagana ta Haifa masa Namiji, wayyo zokaga murna da tsalle da shirin suna Na bajinta, ragoma biyu aka yanka kuma manya-manya. Ansha shagalin suna yaro yaci suna Nuhu. Sai dai kash bayan suna da kwanaki uku yarasu, wannan Abu yasaka Zakari takaici, harda kukansa rurus, kaikace wani babban mutumne yarasu.
Babu dad'ewa Yagana takuma samun wani ciki, Zakari ya shiga tattalin ta kamar zai maidata a ciki, dan a ganinsa Namijin za a kuma Haifa masa. Sai dai kuma shi Ubangiji babu mai masa shishshigi a lamarinsa. Koda Yagana ta haihu saiga d'iya mace. Babu kunya Zakari ya nuna tsantsar takaicinsa da haihuwar jaririya, gashi babu damar sakin Yagana. Yarinya taci suna *HAUWA'U (Jiddah)*, ko kad'an Zakari bai damu da Hauwa'u ba, koda ciwo takeyi babu ruwansa balle ya damu, ahaka takai yaye aka yayeta, Yagana takuma samun wani cikin. Nanma Zakari ya saka idon ganin namiji, amma saiga mace, itama kiri-kiri ya nuna bayaso, taci suna Fatima (Zarah), bayan an yayeta saiga wani ciki, a wannan Karo zakari baiwani damuba, hasalima ya maida hankalinsa ga kasuwancinsa ne daketa ha6aka gaba d'aya, ga shirin auren Yahaya da sukeyi kuma.
Ansha bikin yahaya da matarsa Zulaiha, itama ta tare anan cikin anguwar, amma haya ya kama kafin ALLAH yakawo kud'in gina d'an filinsa daya siya. Bayan auren yahaya da kwana ashirin da uku ALLAH yayma mahaifiyarsu rasuwa, takuma jaddada wasiyarta ga Zakari inhar ya saki Yagana bata yafeba. Sunsha kuka da alhini rasuwarta, kwananta tsara a k'asa Yagana tafara nak'uda, amma sai Zakari ya nuna halin ko inkula akanta, acewarsa bazai wahal da kansa da dukiyarsa ba ahaifa masa wadda bazata iya taimakonsa da komaiba idan ta girma. Haka Yagana tasha matuk'ar wahala kafin ta haihu dak'yar, wahalar da tasha yasaka jinjirin jigata yazo babu rai. Hankalin Zakari yatashi matuk'a, yakumaji haushin kansa ainun, dan aganinsa sakacinsa yasaka su6ucewar Abu mafi daraja da soyuwa a gareshi, ya rungume gawar yaron yayta hawaye da ALLAH wadai ga abinda yayi, daya kai Yagana asibiti da yanzu d'ansa Na nan a raye.
Baki kawai Yagana ta ta6e ta d'auke kanta, takaici Na kuma cimata a zuciya.
Saida takusa shekara sannan ALLAH ya kuma bata wani cikin, zakari yadage tuk'uru wajen bata kulawa da addu'ar samun Namiji a wannan karonma.
Zan iya cewa Yagana ta haihu kusan lokaci d'aya da Zulaiha Matar yahaya, zulaiha ta santalo d'anta Namiji, itako Yagana mace. Takaicifa kamar zai kar mutumin naku. (=╪▐=╪▐).
Babu wani abun arzik'i dayayi a taron sunan tamkar sauran y'ay'ansa Na baya, ranar suna yarinya taci suna Hadiza (waleeda) saboda sunan mahaifiyar su zakari aka sanya Mata, d'an yahaya kuma Abubakar.
Bayan haihuwar Waleeda Ruk'on Nafisa yadawo hannun yagana, tunda yanzu babu mahaifiyar su zakari. Tsakani da ALLAH yagana ke ruk'on Nafisa, inma ba fad'a tayiba bazaka ta6a sanin ba d'iyarta baceba. Yanda take bama y'ay'anta tarbiyya haka take bama Nafisa, duk abinda ta siya musu itama zata saya Mata.

Zakari kam babu ruwansa da maganar yaransa, tsakaninsa dasu sai hantara da duka, yak'i sakasu boko balle Arabic, daga waleeda ma sai haihuwar ta tsayama Yagana baki d'aya, ita murnama tayi sosai, y'an uwantama suka tayata. Da taimakon yayan Yagana aka saka su Jiddah firamari da islamiyya harma Nafisa, yahaya ma yana bada gudunmawa, dukda a tsorace yakeyi saboda a k'ark'ashin Zakari yake har yanzu.
Matar yahaya kuwa tanata haihuwarta, cikin ikon ALLAH kuma maza taketa haihuwa, shikuma yana masifar son a Haifa masa mace, sai yayta sha'awar su jiddah.
Shekarar waleeda takwas a duniya Zakari yaje makka, a wajen aikin hajji yahad'u da matar aure mai suna Hajia Hindatu. Hindatu irin gogaggun matan nanne masu Ido a tsakar goshi, ta ta6a aure amma haihuwarta d'aya ta fito, bata dad'e da fitowa ba suka had'u da zakari. Tun a Saudia soyayya ta k'ullu a tsakaninsu, suna dawowa Najeriya babu 6ata lokaci akasha biki.
Ko kad'an auren bai d'aga hankalin yagana ba, dan damuwarta itace a gabanta, takuma San wanene Zakari, idan baisamu cikar burinsa ba (haihuwar namiji) to itama hindatun ba k'afa zai d'aga mataba.
A gida d'aya aka had'asu da farko, dukda Zakari yafara ginin wani gida mai k'yau dayafi Wanda suke ciki d'an k'arami mai d'aki uku da kicin d'aya da bayi d'aya a waje.

Sosai Hindatu kema Yagana Ummansu Jiddah iskanci kala-kala, su Jiddah kuwa basu isa su wala a gidansuba zata makesu. A lokacin kuma Nafisa nada shekara 19 dan tama isa aure, Jiddah kuma 14, Zarah 12, Waleeda 10.
Tuni Nafisa tabar zuwa boko dan daga firamari itada Jiddah basu cigaba ba, yayan yagana dake taimaka musu ALLAH yayi masa rasuwa, ganin nauyi zaiyima yagana yawa dukda d'an kasuwanci da takeyi saitace Jiddah da Nafisa suyi hak'uri, k'annensu su Zarah suyi su sai suci gaba da islamiyya kawai. Basu musaba suka amince, Zarah da Walida suka cigaba dayin boko da islamiyya, Nafisa da Jiddah kuma islamiyya kawai.
Zuwan Hindatu saiya kuma harmutsa komai Na gidan, domain kuwa shekararta d'aya ta haihu d'a Namiji, murna da shagalin da Alhaji Zakari yayi 6ata lokacine, bayan shekara biyu takuma tagwaye duk maza. Nanfa likafa taci gaba, dan gidan da Alhaji Zakari ya gina dukda girmansa sai yace Hindatu ce kawai zata koma ciki. Dukda abin ya6ata ran Yagana saita danne, tai masa ALLAH ya sanya alkairi.
Acanma akayi sunan tagwayen hindatu. Bayan suna babu dad'ewa Nafisa tasamu miji, babu bincike babu komai Alhaji Zakari yace yabashi, takaici Yakama mahaifiyar Nafisa da Yagana (dayake mahaifiyar Nafisan suna mutunci da yagana sosai saboda ruk'on gaskiya da taima y'arta, itama tayi aure tuni ta hayayyafa ma).
Haka dai akasha biki, Alhaji Zakari baima Nafisa wani abun arzik'iba, a cewarsa baya zuba jari inda bazai kwashi ribaba. Komai sai mahaifiyarta da yagana sukayi iya k'ok'arinsu, saikuma dangi.
Sosai Alhaji Zakari ke nuna banbanci tsakanin y'ay'ansa maza Na wajen Hindu (wadda suke kira Aunty Amarya) dasu Jiddah.
Hindu takuma saka haihuwar d'a Namiji, yanzu yaranta hud'u duk maza, kalifa, Hassan, hussen, Najib.
Alhaji ya sakasu makaranta mai tsada, komai suke buk'ata an tanadar musu, sun taso y'ay'an Hutu, Ana shagwa6asu ainun.
Yayinda gasu Jiddah ba haka bane, ko Alhaji zakari zai musu Abu saiyayi musu tozarci, bakuma zaiyi yanda ya kamata ba, saiya had'a wata baizo wajen Ummansu Jiddah da sunan sauk'e mata hak'k'i Na aureba, kayan abinci ma saiya gadama, saidai yahaya yakawo, wataran kuma ya hanashi ma.
Jiddah iyakarta firamare itada Nafisa, yanzu haka shekararta 20 dai-dai, tana makarantar islamiyya, hafizace ta alkur'ani mai girma, tayi zurfi matuk'a a fannin ilimin addini, ta halarci musabak'an alkur'ani kashi-kashi, kuma tayo nasara, amma a boko saidai abinda ba'a rasaba da Wanda k'annenta su Zarah ke koya Mata.
Da taimakon Uncle yahaya dana Umma, Zarah da walida ke karatu, dukda makarantar gwamnati sukeyi saida ji6in goshi ake iya kare musu buk'atun yau da kullum, dukda ALLAH yayima mahaifinsu arzik'i gwargwadon hali babu ruwansa da su.
Zarah Na shekara 18, tana aji biyar a makaranta, tasamu Matsala ne a wata shekara aka maidata baya, amma da yanzu tagama secondary, itama babu laifi tana ta6a karatun addini. Walida kuwa tana 16 itako ajinta uku a makaranta, sune zasuyi jsce yanzu. To ankoma Hutu amma gashi uncle yahaya bayanan, yayi tafiya, shine Umma tace Jiddah taje wajen Abbansu kozai taimaka ya bada, amma saita dawo da 6acin ran cin mutuncinsa dana matarsa hindu (aunty amarya).


('('('('('('('('('('('


*_MUN DAWO LABARI_*


Sai yamma lik'is Zarah da Walida suka dawo nik'i-nik'i da ledoji, Jiddah dake tsakar gida tana tuk'in tuwo akan gawayi tai sagade tana kallaonsu, dukda tasan hakan daga aunty Nafisa ne, kullum cikin k'ok'arin k'yautata musu takeyi da abinda ALLAH ya hore Mata.........
Maganar Zarah ce ta katse ta.
УKai Yaya Jiddah, irin wannan sakin baki haka? ALLAH sai sauro ya antaya cikiФ.
Walida dake dariya tace, Уgashinan kuwa yana yawo k'umu-k'umu wlhy, aimu gidannan
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On MUTUM DA DUNIYARSA
avatar
rukayya-yahuza

6 months ago

Reply

Kai book dinnan ya hadu iya haduwa

Please Login or Register in order to submit comment