Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Jiddah ta kwanta mata arai, nanma sunWan jima dan saida sukai sallar isha'i, suka koma sashen Hajia bah-bah saboda kiransu da Na'ima tayi suzo suci tuwo.

Lokacin da Aliyu ya shigo gidan ya iskesu sunacin tuwo a falon hajia bah-bah. Bayan sun gaisa da bah-bah Na'ima ma ta gaisheshi, bisa kuskure Jiddah ta Wago kai suka haWa ido, gira yaWan Waga mata yana nuna mata tuwon da ido.
Murmushi ta masa haWe da ™aramin gwalo, ya murmusa shima yana mi™ewa domin zuwa gaida sauran matan gidan.
 Aliyu ka zauna a kawo maka tuwo .
 A'a Bah-bah, Alhmdllh, kinsan ni ba cin abincin darenma nakeba kwata-kwata .
Cikin hangame baki tace,  Wai wanan halin naka har yanzu baka barshiba Ali? Randa baka yini agidaba shikenan bazakaci abincin iyalinka ba? .
 Bah-bah ai inacin na safe, rashin cin abinci dare abune mai ™yau, yana ™ara lafiya inhar mutum zai iya jurewa .
 A'a wlhy badaniba kam, yoni idan banci tuwo da darebama jinake tamkar banida lafiya a gidan nan .
Dariya su Jiddah saukayi kaWan, kujifa hajia bah-bah da wani batu, saikace wadda batayi salla ba.
Shidai Aliyu fita yay yana mata dariya. Bai daWe sosai ba ya dawo yana faWin,  Kumuje ku gaida malam akwai inda zamuje insha ALLAH .
Maimuna da Jiddah suka mi™e, dan dama sungama cin abincin, harma sun wanko hannunsu da baki. Sallama sukaima Hajia bah-bah, suka koma Wakunan su gwaggo suma sukai musu sallama, harda ´ar tsarabarsu ta kuka da Wanyen kuSewa da daddawa suka samo.
Saida sukai sallama a ™ofar falo aka basu izinin shiga sanan suka shiga, sun iske malam da Aliyu zaune suna magana, idan ka gansu dolene su baka sha'awa, harsun tsuguna daga farkon falon malam yace,  A'a ´a´ana ku shigo mana ciki .
Duk a kunyace suka koma gabansu sosai, kansu a ™asa suka gaidashi, ya amsa musu cikin fara'a tareda tambayarsu gidan da rayuwar yau da kullum, sanan ya Wora da nasiha a garesu su duka ukun mai ratsa jiki, yakuma sanya musu albarka tareda fatan alkairi a zamansu.
Suko kansu na ™asa sunata amsawa da amin, yayinda ™aunar tsohon da girmansa na ™ara yalwatuwa a ransu.
Baija zancen yayi tsawoba yace,  Aliy tashi kuje dare nayi, dan ALLAH ka gaidamin shi, ga wanan kabashi kafin nazo .
Tashi Maimuna da Jiddah sukayi suka fita, dukda basu fahimci zancenba sunga yadace su basu waje ko akwai abinda zasu tattauna.
Bayan fitarsu Aliyu yace,  Zaiji insha ALLAH baba, amma kabar kuWinka zan bashi injika insha ALLAH .
 A'a karSi wanan ai tsakanina dashine, kuma nima ina bu™atar ladan sarkin wayo ya™are maganar da tsokana.
Murmushi Aliyu yayi ya karSi kuWin, sanan sukai sallama da malam ya fito. Ya iske harsu Maimuna sun shiga mota, sai Na'ima dake tsaye ajikin motar suna magana.
Cikin samarin dake gefe Waya yazo ya buWe masa motar da addu'ar sauka lafiya, dama sunzo suka gaida su Jiddah cikin mutuntawa.
Koda suka tafi a hanya bai musu bayanin inda zasujeba.
Ita kuma Jiddah gaba Waya hankalinta ma bakan hanya yakeba, game kawai take a waya tana sauraren hirarsu jefi-jefi suma, saida har suka shigo cikin anguwar sosai ne Jiddah ta Wago kanta donson ganin inama suka dosane?.
TaWan waro idanu da faWin  Ai nan anguwarmune .
Dariya Maimuna tayi ta juyo tana kallonta,  Wai da gaske dan ALLAH? .
 Wlhy kuwa aunty .
Aliyu na jinsu amma ya™i tanka musu, a ™ofar gidansu Jiddah yay fakin sannan ya juyo yana kallon Jiddah.
 Ku shiga, zan shigo daga baya nima .
Jikin Jiddah kuma sai yayi sanyi, cikin langaSar da kai tace,  Basai gobe idan ALLAH ya kaimu kaceminba? .
Ganin Maimuna ta fita saiya shafa kumatun Jiddah, shima cikin kwantar da murya yace,  Haka naje, insha ALLAHU zan kawoki gobenma kinji .
HaWiye ™wallan daya cika idonta tayi, ta sauke ajiyar zuciya sanan ta fita. Har suka shiga gidan idonsa na kansu, saida suka Sacema ganinsa ne ya sauke ajiyar zuciya da Waukar waya domin kiran Uncle yahya.

('('('('('('.

Su Umma duk suna tsakar gida zagaye da Abba da Uncle yahya ke bama Abinci.
Hakanne yasaka Jiddah yin turus tana binsu da kallo, dama ´an uwanta basu tafiba? Idonta ta sauke akan Abba dake kwance WaWWaure da karan Wori, sai Hajia Hindu dake gefe zaune ´a´anta zagaye da ita itama.
 Lah yaya Jiddah kece?  Cewar walida data fito daga Wakin Abba Wauke da kwanon magani .
Sauranma duk sai suka maido kallonsu ga ™ofar, Zarah tazo ta rungume Jiddah suka saki kuka tare, dan Jiddah ta fahimci gidansu babu lafiya.
Aunty Hanantu data hangi Maimuna ce ta mi™e tana faWin  Ashe tare kuke? Shigo mana Maimunatu .
Gwiwar Maimuna a sanyaye itama ta shiga ciki, dan alamu dai sun nuna babu lafiya kam.
Uncle yahya yayma Jiddah da Zarah magana sanan suka saki juna, Jiddah tazo gaban Abba ta dur™usa tana hawaye,  Abbanmu miya sameka? .
Dukda haushinta da yakeji dan shi duk akanta yadora laifin, data zauna gidan Alhaji garba wanan bala'in da duk bai afka masaba, amma ya daure yace,  Wannan kukan ya isa haka ko? .
Kasa tsayar da kukan Jiddah tayi, Maimunatu tazo gabansa itama ta durkusa ta gaidashi, da masa ya jiki?.
Amsawa yay cikin alamun yanajin jiki matu™a, itama Jiddah ta gaidashi, ana cikin haka Uncle yahya daya fita suka shigo da Aliyu, dama su Umma duk sun kimtsa, gashi a kwai wutar nepa.
Tabarmar dake shinfiWe a farkon shigowa wadda Jiddah taje ta zauna kusa da Abba Uncle yahya ya nunama Aliyu, kansa a ™asa bai kalli kowaba ya zauna, Jiddah da gaba Waya hankalinta baya wajen saijinsa tayi kusa da ita, mi™ewa tai tabar wajen, takoma inda Umma take tana sharar hawayenta.
Aliyu ya gaida Abba yana faWin,
 D'N (N#R3N 7NGOH1L %PFR 4N'!N 'DDGO .
La ba'asa tahoorun in sha'al-lah. (Ba komai, tsarkaka ce in ALLAH ya yarda).
#N3R#NDO 'DDGN 'DR9N8PJEO  1N(NQ 'DR9N1R4P 'DR9N8PJEP #NFR JN4RAPJCN .(3(9 E1'*)
Asalul-lahal-'azeem rabbal-'arshil-'azeem an yashfeek (7). (ina rokon ALLAH mai girma, Ubangijin Al'arshi mai girma, ya warkar da kai. (sau bakwa).
*_(MANZON ALLAH, tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya ce;  Babu wani bawa Musulmi da zai ziyarci mara lafiya wanda ajalinsa bai riga ya zo ba, sannan ya fadi wannan (addu'a) sau bakwai face ya sami lafiya )_*.
_Falalar Da Ke cikin Ziyarar Mara Lafiya._
*_(ANNABI, tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi, yace; "Idan mutum ya ziyarci dan uwansa Musulmi (da ba shi da lafiya) to yana tafiya ne cikin lambunan aljanna yana tsinkar 'ya'yan itaciyarsu, idan ya zauna sai rahama ta lullube shi. Idan da safe ne Mala'iku dubu saba'in za su yi ta yi masa salati har ya shiga maraice. Idan kuma da maraice ne mala'iku dubu saba'in za su yi ta yi masa salati har ya wayi gari)_*.
Aliyu yaja doguwar addu'a ga Abba yana share kwallar da shima suka cika mada ido na tusayin Abban
Su Aunty Sauda na amsawa da amin.
Duk sun gaidashi da masa godiya, itama Umma ya gaidata tareda jajanta lamarin, Jiddah na jikinta tana hawaye, yayinda Umma keta shafa kan Jiddah alamar lallashi.
Aliyu ya janye idonsa daga jiddah ya maida akalar gaisuwar ga Hajia Hindu data cika tai fam da haushi, itama yay mata addu'ar samun afuwa.
Ta amsane kawai dan yayi mata mugun kwarjini, yanda takema mazajen su Aunty Nafisa yatsine-yatsine shi saita gaza masa, harshenta har sar™ewa yake wajen saurin amsa gaisuwarsa.
Basu baro gidanba sai goma da rabi, shima saida Uncle yahya yace yakamata su tafi dare yayi, ´an dubiya daketa shigowa ma sinWan rage saboda dare ya farayi.
˜iri-™iri Jiddah ta sanya kuka ita anan zata kwana, tun kowa na Waukar abin wasa har suka lura da gaske take, shikuma Aliyu baice uffanba yay musu sallama ya fice abinsa bayan ya ajiye kuWin da malam yace aba Abba da wanda shima ya bashin, sai kayan marmari dasuka tsaya a hanya suka saya.
Uncle yahya ne yayma Jiddah jan ido sanan ta mi™e su Zarah suka rakota inda Maimuna da Aliyu ke jiranta.
Babu wanda ta kalla ta buWe bayan motar tashiga tana cigaba da kukanta, Uncle yahya yabama Aliyu hannu sukayi musabaha da godiya shikuma Aliyu nama Abba addu'ar samun lafiya.
Saida suka bar ™ofar gidan su Zarah da Uncle yahya suka koma cikin gida.
A hanyama Jiddah kukanta takeyi, sai dai bamai sautiba, amma su Aliyu na jinta, Maimunatu ce kawai keta lallashinta da bata baki, amma sam Aliyu ya™i tankawa, ita kuma shirunsa saiya kuma tunzurata takasa yin shiru kodan lallashin da Maimuna ke mata.
Suna isa gida itace farkon fita tabarsu a mota, da kallo kawai Aliyu ya bita, Maimuna zatabi bayanta Aliyu ya dakatar da ita,  Kinga Maimoon barta kinji .
Cikin langaSe kai tace,  Haba yaya yazakace a barta, kukafa takeyi? .
Fitowa yay daga motar shima,  Tunda nace kibarta kawai ki barta, kukan nata harda na hanata kwanane, indai banda rashin son gaskiya taya za'a ™ara musu nauyi bayan wanda suke ciki, idan tayi ha™uri da safe zata koma insha ALLAH .
Shiru kawai Maimuna tayi, amma ita harga ALLAH bataga laifin Jiddah ba, ko itace sai taso kwana Win, to amma ita kanta shaidace akan wannan halin nasa, zata iya rantsewa tunda akai aurensu bai taSa barinta taje gida ta kwana ba, yini ma yata Sata rai kenan. Dan haka sai bataja maganarba ta wuce sashenta.
Shima nasa ya nufa batare da yabi ko wannensu ba.

Tunda Jiddah ta shigo ko hijjab bata cireba ta kwanta a gado tana cigaba da kukanta, tausayin Abbansu da ba™incikin an hanata kwana cikin ´an uwanta yake kuma tunzura kukan nata, ga haushin Aliyu, dan da ace yaso ta kwana ai zaice ta zauna, kuma babu wanda zai hana, rashin amincewar tasane ya saka Uncle yahya korota.
Tana nan kwance harya shigo, dukda taji ™amshinsa ko motsi batayiba.
Kansa kawai ya Wan girgiza, ya ajiye kofin shayinsa da Maimuna ta haWo masa sannan ya zauna kusa da ita.
 Hauwa'u! .  Ya kirayi cikakken sunanta abinda bai cika yiba, saboda sunan mahaifiyarsa kenan .
Tsoro ya kama Jiddah, saboda jin yanda ya kirata a dake, tamkar ba shiba, hawayenta ta goge sanan ta amsa cikin rawar murya.
 Tashi zaune ki cire wanan hijjabin .
Bata musa masaba ta tashin, takuma cire hijjabinta amma ta™i kallonsa.
Shima bai kalletan ba yace,  Tashi kiyi shirin barci .
Tamkar munafuka haka ta tashi sum-sum zuwa bayi. Shikuma ya Wau shayinsa yafara sha yanamai jin tausayinta da ahalinta, sosai lalurar Abba ta tsaya masa a zuciya, ita kuma tana neman ™ara masa zafi da ™uruciyarta.
Yana shan shayin ta fito, kayan barcinta ta Wiba ta dawo ta bayansa ta saka, nanma baice mata ™ala ba, amma da lafiya-lafiya ne cazai shi zai saka mata.
Tana gama shiryawa ta Waura zani tazo ta kabbara shafa'i da wutiri. Shidai Aliyu na zaune yana kallonta harta idar.
Sai kumbura fuska takeyi tana cigaba da share hawayen dake zubo mata, hannu ya mi™a mata alamar tazo, da tayi nufin no™ewa, amma sai taga rashin dacewar hakan, tadai turo baki sanan ta matsa kusa da gadon.
Hannunta ya kamo ya jawota zuwa jikinsa a hankali. Tana jinta kwance a ™irjinsa saita kuma fashewa da sabon kuka.
 Oh ALLAH, ya isa haka mana Jiddah, ko sokike nima namiki kukan ne? .
Kanta ta girgiza masa alamar A'a.
 To kiyi ha™uri kinji, insha ALLAH zai samu lafiya, Addu'a ya kamata muyi masa ai ko .
 Amma shine ka™i yin magana danace zan kwana? .
Murmushi yayi yana shafa kanta, cikin kuma sanyaya murya yace,  To nayi laifi amin afuwa, amma kema kinsan hakan bai ™yautuba, kwananki ai ™arin wani nauyine, idan ALLAH ya kaimu saikije ki yini kinji .
Da sauri ta kallesa,  Da gaske dan ALLAH? .
Yanda tai maganar saita so bashi dariya, amma sai ya gimtse ya sumbaci goshinta yana faWin  Insha ALLAH Qurratul ain, ALLAH dai ya basu lafiya, yakuma tsare gaba .
 Amin ya rabbi, ammafa ni babu wanda ya faWamin abinda ya faru .
 Ni dai Uncle yace min ´an fashine suka shiga, amma nasan za'a faWa miki insha ALLAH, sai kinje gobe idan ALLAH ya kaimu .
Shiru kawai Jiddah tayi, tausayin Abba nakuma ratsata.


('('('('('('('('('('('

Washe gari da wuri ta tashi ta haWa breakfast, kunun gyaWa sai soyayyan dankalin hausa data yankashi dogaye, saita soya miyar attarugu zalla da albasa, harta gama Aliyu bai shigoba daga massalaci dayaje. Tana gyaran bedroom ya le™o.
Durkusawa tayi ta gaidashi, bai shigoba ya amsa daga inda yake tsaye a ™ofa,  Mizan tayaki dashine? .
Kanta ta girgiza masa tana faWin  A'a ka barshi, shara kawai zanyi .
Kansa ya jinjina mata ya juya ya fita, ta bishi da kallo saida ya fice sannan ta mi™e taci gaba da aikinta. Ko morping yau ™inyi tayi, tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga ta atanfa, kayan karin kumallon ta Wiba zuwa sashensa. Shima har yayi wankan yana shiryawa ta shigo.
Idanu ta zaro tana Wan dafe ™irji, sanan ta marairaice fuska tana faWin,  Dan ALLAH kayi ha™uri, banzo na haWa maka ruwan wankaba .
 Tab ai bazan ha™uraba yarinya ..
Dur™usawa tayi agabansa,  Dan ALLAH fa nace .
 To saikin faWi sunana .
Babu shiri ta Wago ta kallesa, yako yi kicin-kicin da fuska tamkar gaske,  Idan har baki faWaba gwammajan ma bazaki jeba ko .
Tuni ta fara hawaye,  ALLAH ni bazan iya faWar sunanka ba .
 To saikin faWi abinda zaki ringa kirana dashi, danni nagaji da maidani surukinki da kikeyi .
Wai shi dama haka wanan mutumin yake?
Jiddah ta ambata a zuciyarta dan takaici, harga ALLAH da burin zuwa gidansu ta kwana, hardasu mafarki, dan haka gara tafaWa tasamu taje, kuma kasa tayi da kanta sanan tace, *_ Zauji ghaliy _*.
KafaWunta ya kamo ya Wagota zuwa jikinsa yana faWin  Masha ALLAH Aglannissa, daga yau karna sakejin an Soyemin suna ana kwana-kwana .
Kanta ta Waga amasa alamar amsawa.
Sakinta yayi ta taimaka masa ya ™arasa shiryawa, sanan taje kiran Maimuna dansuyi kari..........
'<Øûß


_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._

*ŠAURIN OYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ˜ADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ŠAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RA˜UMI..!* (Bilyn Abdull)

=ØGÜ<Øûßkarku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*>ØÝ<Øýß>ØÝ<Øýß>ØÝ<Øýß



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*=ØOÞ<Øûß=Ø-Þ
[12/31/2019, 3:25 PM] =ØžÜNoorunnisa=ØžÜ: *_Typing=ØòÜ_*



*_=Ø¡ÜHASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=اÜMUTUM DA DUNIYARSA....!!=اÜ_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>ØÝ<Øûß_*

*_[61–'62]_*


............Koda su Ashir suka amso kuWi a kotu ™iri da muzu suka hana Alhaji Garba, hasalima shi baisan wainar da suke toyawa ba, dan yakoma sashen amaryarsa ya tare, kwata-kwata baya barin rana ta gansa, musamman ma da yanzu yasan yanada laifi a wajen ´a´ansa akan abinda yayma mahaifiyarsu, toshi babban ma abinda yakeji a ransa gameda ita shine tsananin tsanarta, ko kaWan baya sha'awar koda tunata ma.
A yau yay nufin kiran Abba ya tuna masa zancen kuWinsa, amma sai wayar ta™i shiga, hakanne yasakashi maida akalar kiran ga yaransa na kasuwa akan su bincika masa Alhaji Zakari a shagonsa.
Mamaki ya kama Labaran, yace,  Alhaji wane kuma Alhaji Zakari za'a gani a kasuwa bayan shagon nasama yadawo naka? .
Zaune sosai Alhaji garba ya tashi, dama kwance yake amarya namasa tausa,  Labaran ban fahimci zancen nakaba ai nima, bani a warware .
Labaran dai baiyi jayayya ba ya Wakko labari tundaga tushe ya zayyanema Alhaji Garba, babu shiri kuwa ya rikito a gado, amarya na tambayarsa mike faruwa bai kulataba.
Sashen Hajia Deluwa ya nufa, wadda zuwa yanzu ka ganta dole tabaka matu™ar tausayi, dukta kuma ficewa hayyacinta, ´an kuWin da su Ashir suka amso miliyan goma suka bata, sukuma suka rabe sauran harda ™anwarsu dake karatu. Shagon kuma yazama na yayansu saboda shine ya saya. Amma sai sam kuWin basu gusar mata da damuwarta ba, itadai tafi bu™atar mijinta a gareta, babban tashin hankalinta na gaba kuma warin da takeyi, wanda hatta ´a´anta saisun toshe hanci suke iya zuwa inda take, jiya wata ´ar uwarta tazo gidan, amma sam kasa zama tayi tanata faman toshe hanci, ita kuma ko kaWan batajin warin saima ™amshinta na gayu datake zubawa a kullum........
Banko ™ofar da Alhaji garba yayine da ™arfi yay matu™ar firgitata ta mi™e zumbur tana kallonsa,
 Alhaji lafiya kuwa? .
Hannunsa toshe da hanci yace,  Ban kuWina .
Cikin sanyaya murya tace,  wane kuWi Alhaji? .
 O bama ki saniba ko? To wanda ´a´anki sukaje suka amsa a kotu .
Baki ta taSe cikin ™arfin hali,  Yanzu dan ´a´anka sunci waWannan ´an kuWin daga cikin abinda yake ha™insu shine zakazo kanamin haya™i, idan ka mutu sukeda gadon su ai .
Galala yay yana kallonta tamkar wani soko, yace,  Aiyyyy dama maganar danakeji a gari gaskiyane? Bakida buri saina mutu kuci gado keda ´a´anki, to aiko yau Winnan basai gobeba zaki kama gabanki, saidai kisa a biyo dare yau a kasheni, kosu su Ashirun suzo su karni gobe a raba muku gado, bankuma yadda keWin jahila baceba sai yau wlhy, dama da ALLAH yayma namiji arzi™i to kullum burin mace ya mutu suci gado itada ´a´anta, shiyyasa kikaita korar min mata kina musu asiri ko?, to ai dama tuni bokan naki yazo ya sanarminin kafin ya mutu, dan har kasuwa yazo ya sameni ya faWan duk tsiyatakun da kuka aikata, harda haukata yarinyar Alhaji zakari, wanan ne yasani burin barmasa kuWin, dama ina masa barazana ya banine domin hakan yazama izinina a garesa ya kiyayi halayyar cin bashi, shine ku ™wararru kukaje kuka amshi kuWin, kisani wanan karon bazakuci a banzaba kamar yanda kuka sabaci, insha ALLAHU kuma saikin rigani mutuwa, kije na sakeki saki Uku, kuma a yau nakeson ki barmin gidana .
Wani gigitaccen ihu hajia deluwa ta kwala ta yanke jiki ta faWi a wajen babu rai.
Alhaji garba baibi takantaba yay fitowarsa.

A wanan mummunan yanayin autarta data dawo daga makaranta yau cikin Wokin ganinta ta isketa, bata sanarma kowa zatazoba saboda ta basu mamaki, sai ita ta tarar da abin mamakin.
Itace takira baban yayansu a waya.
Ankai hajia deluwa asibiti a san™ame, bakuma a samu farfaWowarta ba sai washe gari, wanda har zuwa lokacin babu alhaji garba babu dalilinsa, ama ranar suka cane dubai yawon amarci shida amaryarsa.
Hajia deluwa dai sai yamma lis ta farfaWo, saidai kuma tasamu mummunan ciwon Sarin jiki, Sarinta na dama baya aiki gaba Waya har ido Waya, saida Waya take gani shima bishi-bishi, baki kuwa ya karkace yana zirar da yawu.
³a´anta sun shiga tashin hankali matu™a, sunyi kuka sosai dan suna ™aunar uwar tasu, sai dai basuda yanda zasuyi.
Haka suka cigaba da jiyyarta, tun sunayin abun da marmari har suka koma biyan likitoci su kula da ita, suko suka koma kan harkokinsu, sai dai suzo su dubata. A kwana a tashi kuma sai dubiyarma ta fara gagararsu zuwa, dan saisu haWa kwanaki biyu basu le™ata a asibitiba.
Likitoci suma suka fara ™osawa da ™azantarta, aiko suka kira su Ashir suzo su kwashi abarsu.
Wannan ne silar dawowarta gidan jiyya, har kuma sanan Alhaji garba bai dawoba, dan sunacan suna hutawarsu da amarya dake fama da ™aton ciki, haihuwa yau ko gobe.
Tunda aka maido hajia deluwa gida fa babu mai mata kallon arzi™i, dan bilki mai aikima tuni ta gudu abinta, haka hajia deluwa zatayi kashinta da fitdari babu mai gyarawa, ga tsoro da ake bata kullum, taita ganin halittu masu ban tsoro, haka zataita kuka babu damar ihu, wanima lokacin dariya za'aita SaSSakawa, amma tarasa a inane, kokuma aita kuka, ko kukan dabbobi kala-kala, gaba Waya ta susuce, itaba mahaukaciyaba ita ba gawaba. Mai kula da itanma saita gadama take bata abinci tana toshe hanci, data zirara mata take baro sashen.
autarta kuwa ™iri-™iri tabar zaman sashen, takoma sashen babanta, saitayi satima bata kalli sashen hajia deluwaba.
Ruwa a jallo hajia deluwa ke fatan ganin koda Waya daga cikinsu Jiddah ne

1 Comments On MUTUM DA DUNIYARSA
avatar
rukayya-yahuza

1 year ago

Reply

Kai book dinnan ya hadu iya haduwa

Please Login or Register in order to submit comment