Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ALLAH yay mana arzik'in sauro kam tamkar d'angwate da kud'i”.
Dariya sukayi su duka har Jiddah, ta rufe tukunyar tuwon data gama tuk'awa tana d'an yarfama rutsin wutar ruwa danya rage zafi kar tuwon ya k'one. “Y'ammatan Umma ya kuka baro Aunty tamu dasu Affan?”.
“Lafiya lumi wlhy Yaya Jiddah, tamace ace miki ta gode da cika alk'awari”.
Murmushi kawai Jiddah tayi, dan tasan laifinta.
”Wai ina Umma?”. ‘Cewar Zarah dake k'ok'arin shiga bayi’.
Jiddah tace, “Taje gidan Uncle yahaya, Maman Sadiq ce k'irjinta ke ciwo, shine taje dubata”.
Walida da Zarah suka had'a baki wajen fad'in “Ayya ALLAH ya k'ara lafiya to”.
“Amin”, Jiddah ta amsa.

Ledojin walida ta d'auka takai cikin d'aki tana fad'in “Yaya Jiddah mi zamu tayaki dashine? Naga yau aikin yamuku dare”.
“Wlhy kuwa auta, amma nama gama, dan miya na farayi sannan, sai dai idan tsakar gidannan zaki share a kunna maganin sauro musami wajen zaman hira”.
Walida ta amsa da to tana nufar inda tsintsiyarsu take.
Zarah ma koda tafito sai tace bara ta kwashe tuwon ita kuma. Haka suka k'arasa dukkan ayyukan suna hirarsu a nutse, dolene su burgeka, dankuwa akwai shak'uwa da k'aunar juna mai yawa tattare dasu, hirar tasuma duk akan Auntynsu ce Nafisa.

Ana kiraye-kirayen Sallar magriba Umma ta shigo, a lokacin su Jiddah sun gama komai, sai k'ok'arin d'aura alwala da sukeyi, amma banda Zarah dake fashin salla.
Atare suka amsa sallamar Ummansu, yayinda suke mata sannu da zuwa da tambayarta mai jiki.
“Da sauk'i Alhmdllh, y'an yini sai yanzu muke ganinku?”.
“Wlhy kuwa Umma, aunty dasu Affan Na gaisheki, yanata kukama saiya biyomu gashi gobe akwai makaranta”.
Y'ar dariya Umma tayi tana cewa, “Ja'iri yau kuma? Amma ranar dayake yaga babansa ai babu yanda banyi ya zaunaba yak'i. Yaya kuka baromin yarinya ta?”.
“Lafiya lau take Umma, ammafa ni sai naga aunty Nafisa kamar laulayin ciki take?”.
Harara Jiddah ta zubama Zarah mai maganar,
“O ke Zarah, wlhy bakida kunya, yaushe kikai girman gane mai ciki?”.
“Tab lallai, kaji Yaya Jiddah da wani batu dan ALLAH, cikin saikace wani abu........”
Hijjab Umma ta cillamà Zarah tana fad'in “Zarah k'aniyanki kinji, Anya kuwa ba aure zansa ayi mikiba?”.
“Wlhy dama yafi Umma, dan Idonta kullum k'ara fetsarewa yakeyi yarinyar nan”.
Waleeda dake alwala ta kwashe da dariya, yayinda Zarah ta kwad'a Mata harara.
“A'a nikam Yaya Zarah karki huce kaina, bani nakar zomanba”.

Haka kullum suke cikin tsokanar juna da wasa da dariya, hakan kuma baisa raini yashiga tsakaninsu ba, Ummansu ta maidasu tamk'ar k'awayenta, sune abokan hirarta sune shawararta, shiyyasa suma basuda wasu aminai a waje sai ita, saikuma a tsakaninsu su biyar.
Sune abokan juna, sune aminan juna, sune y'an uwan juna.


*_Dare_*

Da daddare suna zaune a tsakar gida sunacin tuwo, yayinda Zarah kema Umma bayani akan kayan da sukazo dasu.

“Umma tsarabar Dadyn Affan ce Aunty tace mu kawo, takuma bamu kud'in makaranta tace gobe muje mu biya mukoma makaranta”.
Umma tace, “ALLAH sarki Nafisa baiwar ALLAH, ALLAH ya saka Mata da alkairi, yamata albarka itada zuri'ar ta daku baki d'aya, ALLAH ya cigaba da had'amin kanku kunji”.
“Amin Umman mu”.suka had'a baki wajen amsawa. Kayan aka shiga bud'ewa, sabulan wanka da wanki, sai man shafawa da omo, kayan shayi da maltina rabin katon, da biredi manya guda uku da kud'in makarantar su Zarah sai kaji biyu gasassu.
Addu'a sukaita zubama yayar tasu, Umma ta kirata tai mata godiya da addu'a, tace aima dadyn Affan godiya shima.
Sund'an ta6a hira zuwa tara na dare suka mik'e domin kwanciya, saboda sauro daya damesu gashi kuma su Zarah zasu makaranta gobe.


('('('('('('('('

Da wuri su Walida sukai shirin makaranta, sannan sukai Karin kumallo da d'umamen tuwon jiya da Jiddah ta tashi da wuri ta d'umama musu.
Bayan wucewarsu makaranta tagyara gidan duka da taimakon Umma, dukdama gidan bawani babba baneba. Saida tagama komai itama zuwa tara da rabi tai shirin tafiya Islamiyya.
Tsaf tai shirinta cikin Uniform d'inta kalar ruwan toka, (ash color) yad'au guga sai d'aukar ido yake, turarenta da Aunty Nafisa ke k'ok'arin saya musu ta fesa kad'an, sannan ta d'aura Nikab, saidai bata sakeshiba tafito rataye da jakarta mai d'an tsawo kamar suwaga. 'Dakin Umma tashiga da sallama, tana zaune da alama sallar walha ta idar.
“Umma naga bakiyi Addu'a ba, gashi nakusa makara, nawuce saina dawo”.
Kai Umma ta d'aga Mata batare da tayi magana ba, dan batason katse addu'arta.
Jiddah Na fitowa soro ta Saki nik'ab d'inta tare da gyara hijjab d'inta tai addu'ar fita daga gida sannan tafito. Tafiya take a nutse kuma a sanyaye, kanta a k'asa dukda ta sakaye fuskar tata da nik'af. Kullum haka take cikin suturta jikinta, dayawan y'an anguwar a haka suka Santa, saika Tara mutum goma basu iya siffanta maka kamannin fuskartaba, saidai a tafiya kokuma kwatancen ta da suna mai saka hijjab har k'asa da nik'ab, amma mafi yawancinsu sun manta da kamanninta, dan tunda tafara mallakar hankalinta takoma suturta fuskarta..............
'<Øûß


*_Yanda kuka kar6i labarin yasakani farinciki matuk'a, ina godiya=ØÞ>ØÝ<Øûß, dan haka kumuje Zuwa my guysù&
@& ù&
@&_*





*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*=Ø-Þ=ØOÞ<Øûß
[11/16/2019, 6:33 PM] =ØžÜNoorunnisa=ØžÜ: *_Typing=ØòÜ_*



*_=Ø¡ÜHASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=اÜMUTUM DA DUNIYARSA....!!=اÜ_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>ØÝ<Øûß_*


*_[3......]_*


..............Malam Abdul-ra'uff Maina babban malami ne da akeji dashi cikin Najeriya da wasu k'asashen k'etare makwaftan k'asar, ALLAH ya azurtashi da tarin ilimi, ga tsage gaskiya komai d'acinta a wa'azinsa, yanada manyan makarantun addini sosai a cikin Najeriya da k'etare, dukda bashine kad'ai ya ginasuba, akwai taimakon attajirai da jama'ar gari masu buk'atar d'aukaka kalmar ALLAH.
Matan malam Abdul-ra'uff hud'u cif, duk da dai a yanzu uku suka rage, ALLAH yayma matarsa ta biyu rasuwa shekaru kusan 15, ALLAH ya azurtashi da y'ay'an da adadinsu zai iya kaiwa 17 a duniya kuma maza da Mata.
Huwaila itace uwargidansa, yaran gidan suna kiranta da suna Hajia bah-bah, yaranta shidda, maza uku mata uku, Muhammad, Zainab, Abubakar, Adawiyya, Ni'ima, Mahmud.
sai ta biyu da ALLAH yay mata rasuwa, Sunanta Hauwa'u, suna kiranta da Annau, yaranta uku, Ruk'ayya, Aliyu, Siyama.
Ta Uku Habiba, suna kiranta iya habi, yaranta hud'u, Umar, Bilal, Aminatu, Abdul-aziz.
Sai Amarya Mariya, suna kiranta gwaggo, yaranta hud'u itama, Binta, Usman, Asiya, Na'imah.

Agidan malam bazamu ce ba'a kishiba, anayinsa kam sosai, saida ba kishi Na haukaba, kishi akeyi Na matan da sukeda ilimi.
Mafi yawa daga cikin y'ay'an malam ALLAH yabasu ilimi sosai, amma Wanda zai iya bugar k'irji yakira magajinsa Kai tsaye shine *ALIYU*.
*Aliyu* mutumne nutsatstse, ma'abocin zirfafa ilimin addini da yad'ashi, yanada sauk'in Kai sosai, bashida fad'a ko yawan hayaniya, komai nasa zaka gansa a sanyaye akuma nutse, badan bashida k'arfi baneba, a'a sanyi tamkar halittarsace, dan ko maganarsa haka take cikin sanyi da nutsuwa. Tunda ALLAH yayma mahaifiyarsu rasuwa sai suka koma kamar an waresu, bakomai Na gidan zakaga an sakosuba sai dai idan mahaifinsu Na kusa, hakan yasaka Aliyu bai damu da sabgogin gidanba inhar bana y'an uwansa biyu ba Mata, gashi yanzu duk sunyi aure sun barshi.
Zurfin iliminsa da yawan maida hankali wajen bama addini gudunmawa yasaka mahaifinsu malam Abdul-ra'uff yawan jawosa a jiki, ga tausayin maraicin da suke ciki. Aliyu ya ziyarci wurare daban-daban domin Neman ilimin addini, kullum cikin ziyartar zaurukan malamai yake, ba a Neman ilimin addini ya tsayaba, yana ta6a kasuwanci dai-dai k'arfinsa, dan yanada shago Na saida kowane irin nau'in littafi na Addini da magungunan musulinci, ko kad'an bai yarda yajira daga waniba, koda kuwa mahaifinsane.
Wannan k'ok'arin nasa da ho66asa yasaka wasu daga cikin y'an uwansa jin haushinsa, dan aganinsu kullum Malam yafison Aliyu fiye da kowa a gidan. Bawai su kad'aiba, hatta da iyayensu suna a kan wannan tunanin.
Saidai kuma bahaka bane ga malam, dukda dama ko cikin y'ay'anka akwai Wanda zakaji yafi soyuwa a gareka shi duk yanason yaransa, dan mutumne Maison y'ay'a sosai, kawai abinda basu ganeba (zuciya na k'aunar mai k'yautata Mata a koda yaushe) wannan shine kawai sirrin da Aliyu yabi wajen samun matsayi ga mahaifinsu dama wasu jama'ar dake zagaye da mahaifin nasu.

Yanada shekaru 27 a duniya ALLAH ya had'a jininsa da wata yarinya y'ar makwaftansu, sannan kuma d'aliba a makarantar mahaifinsu inda shima yake koyarwa idan yana gida.
Tunda malam ya fahimci k'aunar dake tsakanin Aliyu da Asma'u saiya nema masa aurenta, dayawan jama'ar gidansu hakan ya 6ata ransu, dan akwai yayunsa da basuyi aure ba kusan su uku. Dayake babu mai damar magana sai basuce komaiba akasha biki cikin tsari Na addinin islama.
Bayan aure da kamar wata uku matsaloli sukai yawa a gidan Aliyu, dan kuwa tunda akakai Asma'u gidansa yakasa kusantarta, badan bashida sha'awar hakanba, a'a lamarinne kawai ya gagara bisa alamun bashida cikakkiyar lafiya.
A matsayinsa na mai ilimi zaunar da Asma'u ya farayi ya fahimtar da ita akan tayi hak'uri ya fahimci baida lafiya, baikuma ta6a fahimtar hakanba saida yay aure, dan kafinma yay aure yakanji sha'awa, sai dai a jarabawa ta Ubangiji yakasa biya Mata buk'ata, yana neman alfarmar fara neman magani.
A wannan zama tayi masa uziri da fahimtarsa, amma yayinda tafiya tafara nisa sai hak'urinta ya nemi gazawa, dukda k'ok'arin neman magani da Aliyu yakeyi ba'a daceba har kusan watanninsu bakwai da aure.
Yakanyi wasanni da Asma'u, amma idan anzo batun biyan buk'ata sai Abu ya gagara, ita kuma hakan yana tada hankalinta daga k'arshe kuma babu biyan buk'ata.
Tabi ta saka kanta a matsananciyar damuwa, dukda k'ok'arin kwantar mata da hankali da Aliyu keyi. Ahankali sai y'an gidansu suka fara fahimtar akwai Marsala, mahaifiyarta ta turketa da tambaya itada yayarta, amarya dake murjewa danjin dad'i ita sai bushewa take a tsaye.
Bata wani tsaya Jan maganaba ta sanar dasu komai.
Tun daga lokacin komai ya harmutse, sukace sai Aliyu ya sakar musu yarinya. Yanason matarsa, dan haka yayta basu hak'uri da k'arin neman alfarma akan magani dayake nema, amma Sam sai sukak'i saurarensa.
Ganin abun zai tasarma tozarci dan harsun fara yawo da magana a anguwa sai malam yayma Aliyu nasiha da nuna masa muhimmancin hak'k'in Asma'u, tunda ta nuna bazata jureba ya sawwak'e mata kawai, kar nan gaba wata 6arnar ta biyo baya.
Cike da damuwa da tashin hankali yabama Asma'u saki d'aya, har hawaye saida yayi, dan yana masifar son Asma'un.
A ranar dai kam sai a asibiti ya kwana, kwanansa uku ya murmure yadawo gida, lokacin dayaje gidansa saiya iske sun kwashe komai, sai iya kayansa kawai aka bar masa, shima abinda keda muhimmanci ya d'iba ya kulle gidan ya fito zuwa gidansu.
Ganin yana tare da damuwa malam ya shawarcesa kozai koma karatune?.
Babu musu ya amsa. Dandanan aka shiga cuku-cukun nema masa gurbin karatu a k'asar Saudia. Cikin sati biyu komai ya kammala, ya cane cikeda kewar ahalinsa da y'an uwansa Mata biyu, Ruk'ayya da Siyama.

Tafiyar Aliyu Saudia saita zame masa alkairi abin alfahari, dan ya ture komai gefe ya maida hankalinsa ga karatu da addu'oin ALLAH ya bashi lafiya, tunda yakuma jin dad'in zak'in karatu saiya manta da wani batun aure. Ya maida hankalinsa tuk'uru. akan Neman ilimi da zurfafa bincike wajen malamai. Cikar kamala da girman mazantaka irinna nutsatstsun samari ta bayyana a gareshi, yazama cikakken mutum ma'abocin yawan ilimi, dukda shekarunsa kad'an suka haura talatin hakan bai hana masana duniyar ilimi girmamashiba, idan yana zuba maka tafsir da yaren Nasara (English) zaka d'auka baisan komai a yaren Africa ba, hakama idan ya juye Larabci abin ba'a magana, saika d'auka wani cikakken balarabene d'an asalin k'asar Saudia, hakama 6angaren yarensa Na Hausa yana nan daram a harshensa bai manta komaiba, dukda baya cikin Nageriya tafsiransa suncika ko'ina Na k'asar cikin harshe daban-daban, wa'azinsa yana saka zukatan bayin ALLAH nutsuwa ta musamman da k'arajin tsoron ALLAH, idan kaji tafsir nasa dolene ka nutsu wajen saurare da k'arajin tsoron UBANGIJI matuk'ar k'urewa, tsage gaskiya yake komai d'acinta.
Tunda yabar Najeria bai sake waiwayenta ba, saidai idan mahaifinsa yaje Umara ko wani Abu ya kaishi ya ziyarcesa, amma koda yaushe suna tare a Video call da mahaifinsa da y'an uwansa su Siyama dama sauran jama'ar gidansu.
Ganin shekaru sunja malam ya shawarcesa akan ya dawo k'asarsa hakanan, kodan ya cigaba da kula dawasu al'amura nasa, saboda shi girma yafara kamashi, sauran yaransa kuma ba kowa keda makamancin halayya ta Aliyu ba, hasalima yafisu indai a fannin ilimine.
Bisa ga bin Umarnin mahaifinsa ya tattaro ya dawo, kusan shekararsa d'aya kenan, tunda ya dawo malam ke zuba ido yaji kozaiyi batun aure, amma shiru kukeji babu wani motsi, sai harkokinsa Na k'ok'arin yad'a ilimin addinin islama yakeyi ta hanyoyi da dama. Dan ALLAH ya d'aga darajar *_Sheirk Aliyu Abdul-ra'uff Maina_* fiye da zaton mai hasashe a ciki da bai Na Najeria da k'asashe masu mak'waftaka, harma sunansa nason fin Na mahaifinsa dan masu iya magana kance kowa da zamaninsa.


Wannan kenan=ØLÜ<Øûß=ضÞ<Øûß
@&.



('('('('('('('('('('('

K'arfe d'aya dai-dai su Jiddah suka tashi daga islamiyya, kamar yanda ta saba saida tai salla a masallacin makarantar gudun kafin taje gida lokacin salla ya shige, gashi a k'asa zata tafi.
Bayan sun idar da sallar da d'alibai irinta masu tsayawa ta tako a nutse zuwa wajen makarantar, da d'an sauri-sauri take tafiya akan k'ok'arinta na isa gida da wuri ta taimaki Umma da aiki, tasan tana can tana fama da gawayi danyin girkin rana. A hankali ta furta “Anya Abba kana tsoron gamuwarka da mahaliccinka kuwa? Kana gudun tashi cikin masu shanyayyen jiki a jerin raunana wajen gina adalci akan iyalai? Ya rabbi ka shiryi Abbanmu, ka ganar dashi gaskiya kafin ka kar6i ruhinsa”. hawaye masu d'umi suka gangaro a kumatunta, bata damu da son sharewa ba dan tasan babu mai ganinta, da wannan ta k'arasa gida.
Kamar yanda ta saba tai addu'ar shiga gida sannan ta shiga da sallama bayan ta tsaya a soro ta goge hawayenta.
A k'ofar kicin ta iske Umma nata faman fifita wutar gawayin.
Umma ta amsa Mata tana fad'in “Lale da malama Jiddah, har an dawo?”.
Jiddah ta yaye nik'ab d'inta tana murmushi saboda jin tsokanar Umman tasu, “kai Umma inafa malama, kodai d'aliba, sannu da gida”.
Umma dake dariyar amsar Jiddan tace, “yauwa, ai kuke da sannu”.
Bokitin fenti Jiddah ta jawo ta zauna tareda k'ok'arin kar6ar maficin hannun Umman. Umma ta hanata tana fad'in “A'a baiwar ALLAH daga dawowa, kid'an huta mana ko Uniform ki samu ki cire, nasan dai kinyi salla a can?”.
“Umma karki damu, wlhy banajin wata gajiya, dama saurin danaketa yi kenan, dan jiya gawayinnan Na fahinci jik'ak'k'ene, yau da safema da k'yar ya kama”.
“Aifa naga alama wlhy, sauk'inma nagama miya, dan nasamu sund'an kawo wuta shine nayi akan abincan da Nafisa ta sayo mana, ina k'ok'arin d'ora shinkafar suka d'auke wutar”.
“Ai y'an wutarnan basuda alk'awari, sannu da k'ok'ari Umma, amma ina kika samu kud'in kayan miya harda gatantamu?”.
Murmushi Umma tayi, sannan ta mik'e zuwa cikin kicin d'in tana bama Jiddah Amsa,
“Kud'in adashin nanne hajia Lantana ta kawo, ni harma Na fidda ran samunsu, to naga ga kajin da Nafisa ta bamu sai kawai naba Dauda ya yomin cefane”.
“ALLAH sarki Ummanmu abin alfaharinmu, mai share kukanmu, ALLAH ya saka da alkairi, kingani kuma darajar hak'urin da mukai ga kud'in wajen hajia lantanar sun fito, bayan kowa ya fidda ransa ga samunsu, Umma sai ki koma sana'arki karmu cinye kud'in a ciki mu koma tsugunne-tsugunne”.
“Nayi wannan tunanin wlhy nima Jiddah, shiyyasa tun d'azun Na Kira Nafisa muka kuma shawartawa kafin kuma ku dawo kuji yanda mukai”.
“To shikenan Umma, aimu duk abinda kuka yanke dai-daine a garemu, ALLAH yayi mana jagora”.
“Amin” Umma ta amsa.

Bayan gawayin ya Kama sosai Jiddah ta d'ora ruwan shinkafa, cikin amincin ALLAH dandanan ta gama, tana cikin kwashewa a kula su Zarah suka shigo da sallama, kowa a galabaice yake saboda rana. Sannu Jiddah tai musu, hakama Umma. Walida ta wuce gaban randarsu da suke zuba ruwan sha saboda k'arancin rashin wutar lantarki ta k'asar tamu Tasha.
“Ke kuwa walida ki taimaki kanki da wannan ruwan hakanan kafin ya k'ulle miki ciki”,
Kofin ta ajiye tana had'iye Na bakinta cikin hura hanci, “Umma wlhy k'ishirwa Na kwaso, yau Na manta banje da ruwaba saboda saurin karmu makara, nikuma bana iya shan Na bohol d'innan Na makaranta wlhy”.
“to miye matsalarsa?”. Cewar Jiddah dake shiga falo da kular abinci..
Caraf Zarah tace, “Yo iyayi irin nata dai Yaya Jiddah.......”
“Kai Yaya Zarah kiji tsoron ALLAH, kemafa kinsan baida dad'i wlhy”. ‘ta k'are maganar da turo baki gaba’.
Umma dai tana jinsu bata sake tankawaba, saida tagama kashe wutar da Jiddah ta sauke abinci sannan tace, “Da wannan gardamar mara amfani dama tashi kukai kuka cire Uniform kuka watsa ruwa, dan sai k'aurin rana kuke”.
Duk sai suka kumbura baki, wai danmu Umma zatace suna k'aurin Rana.
Fahimtar hakan ya saka Jiddah da Umma kwashewa da dariya, Umma ta toshe hanci tana ra6awa ta gefensu ta shige d'akinta. Jiddah ma saita shige d'aki tana dariya.
Zarah da Walida suka kalli juna suna jinjina kai irin zamu rama d'innan. Walida tace, “y'ar uwa barsu sunci bashi indai munai, daga Umma har yaya Jiddah kowa munsan lagonsa. Dariya suka kwashe da ita suna tafawa, sannan duk suka mik'e zuwa d'akinsu inda Jiddah ta shiga.

Duk d'insu saida kowa ya samu ya watsa ruwa, Walida tayi salla sanna suka hallara a falo domin cin abinci. A babban faranti Jiddah ta zuba musu suka saka miya da namansu a sama, suduka har Umma suka saka hannu bayan walida ta d'ebo musu ruwan tulu mai sanyi. Dama can haka suke cin abinci su Biyar, bayan auren Aunty Nafisa ne suka koma su hud'u, tunda suka taso a wannan tarbiyar suka tsinci Kansu, harma sun Saba, kowa baya iya sakin jiki yaci abinci shi kad'ai saida y'an uwansa. (Iyaye mu kula wlhy, cin abincin yaranmu a waje d'aya yana k'ara musu k'aunar juna a zukata, dan kowa nacin yawun d'an uwansa, shak'uwa da soyayya na sake shiga tsakaninsu, wannan k'yak'yk'yawar d'abi'ar da muka bari tana taka rawar gani wajen raba kayin y'ay'anmu tundaga tushe. ALLAH yasa mugane=ØOÞ<Øûß).

Babu mai magana har suka gama tsaf, suka koma kan nama, kowa yanaci a nutse babu had'ama balle nuna zalama. Bayan sunyi nak walida ta kwashe kwanikan ta gyara wajen, daganan suka baje a falon suna cigaba da hirarsu mai cike da k'arama juna sani ba surutai marasa amfaniba............
'<Øûß



Wannan kenan=ØLÜ<Øûß=ضÞ<Øûß
@&.




*_Assalamu alaikum, dan ALLAH Zan d'anyi wani tsokaci a fahimceni. Gameda masu turamin massages ta PC wasu suna ganin tamkar wulak'ancine idan sun tura ban amsasuba a lokacin, Ku gane wani Abu, inada aurefa, sannan inada uzirirrika tamkar kowacce mace, sannan duk lokacin da ka gama typing ko sha'awar ta6a waya bakayi wlhy, ji kake kanka ya d'auki zafi, sannan fa bake kad'ai bace, mutum yakan samu sak'onni sama da 200 a rana d'aya, banda Na groups, tayaya kuke ganin Zan iya amsasu a lokaci d'aya=ØÞ?, shiyyasa nake barin kamar sak'o Na yau Na amsashi da safe kafin Na Fara typing, dana gama nai posting saisu wuce gaba d'aya, to dan ALLAH kuringa mana uziri=ØOÞ<Øûß. Kuma masu Comments a groups wlhy ina kula da kowa, kuma inajin dad'i matuk'a, amma kunyi yawan da bazan iya binku d'aya bayan d'aya Na amsaba wlhy, dan groups ne sama da 30, dan ALLAH kuma kuyi mini afuwa, amma kuna raina kuma ina kula da motsin kowa wlhy, ngd ALLAH yabar zuminci, inajin dad'in addu'oinku gareni da mahaifina=Ø-Þ=ØOÞ<Øûß>ØpÝ>ØpÝ>ØpÝ=ØLÜ<Øûß_*


_Naga an bud'e groups d'in MUTUM DA DUNIYARSA kusan 8 kuyi hak'uri sunyi yawa wlhy, dan haka Zan fita a wasu, kafin Ku had'ama wayata zafi=ØÞ, inba hakaba nakoma la6e a WhatsApp aradu=Ø+Þ>Ø#Ýù&
@&ù&
@&._









*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=Ø-Þ=ØOÞ<Øûß
[11/17/2019, 10:09 PM] =ØžÜNoorunnisa=ØžÜ: *_Typing=ØòÜ_*



*_=Ø¡ÜHASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=اÜMUTUM DA DUNIYARSA....!!=اÜ_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>ØÝ<Øûß_*

*_[4......]_*


..............Kamar yanda suka saba a kowanne dare bayan sallar isha'i akwai karatun manya magidanta a masallacin k'ofar gidan malam. A da shikeyi, amma dawowar Aliyu sai abun ya rabu biyu, malam Na koyar da dattijai, shikuma Aliyu matasa. Kowacce rana akwai littafin da suke karantawa, yauma kamar kullum Qur'an ne a gabansu, yayinda Sheirk Aliyu Maina ke karanto ayoyi daga suratul An-nisa cikin zak'in muryarsa da sanyin irinna masu nutsuwa. da

1 Comments On MUTUM DA DUNIYARSA
avatar
rukayya-yahuza

1 year ago

Reply

Kai book dinnan ya hadu iya haduwa

Please Login or Register in order to submit comment