Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tofeta sanan yashiga mata tausa a hankali.
Luf tayi tamkar tayi barci, hakanne yasaka Aliyu barinta, ya kashe mata fitila sanan ya fita tareda ja mata ofar.
Yana fita hawayen da batasan dalilinsuba suka ziraro mata, itadai tasan tayi murna dazaije can ya kwana, dan itadai takura takeyi da kwanciyarsu a gado Waya, amma batasan dalilin dayasa wani sashen zuciyarta yakejin Waciba, komi hakan yake nufi oho?.
Ta daWe batayi barciba tanata juye-juye, sai can tsakkiyar dare barci Sarawo yay awon gaba da ita.

&&&&&&&

Da asuba lokacin daya leo tashinta salla harta tashi, tana zaune a bakin gado tana addu'ar tashi daga barci ya shigo. Kallo Waya taimasa tai asa da idonta tana gyara wuyan rigarta take a buWe sosai.
baice da ita komaiba ya juya ya fita, ta Wanbi bayansa da kallo harya Sacema ganinta. Ajiyar zuciya ta sauke tamie zuwa bayi Wauro alwala............
'<



_Masoyan Abba zakari Amin afuwa fa, babu ruwana Alaline=J&
@&&
@&&
@&>#_.


_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._

*AURIN OYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI AYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAUMI..!* (Bilyn Abdull)

=G
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*><><><



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*=O<=-
[12/29/2019, 1:44 PM] =؞Noorunnisa=؞: *_Typing=_*



*_=ءHASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=اMUTUM DA DUNIYARSA....!!=ا_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce><_*

*_[57'58]_*


.............Ciwon dake afarta ba shine matsalarta ba, hankalinta naga kuWin hannun aninta, gashi bataga alamun wayarta na tare da itabama........
Umma ta katse mata tunani da faWin,  Maman Hussain ki daure kici abincin nan, ciwo bayason zama da yuwafa .
Hajia hindu ta Wan sauke numfashi, ta asan ido ta harari Umma kafin ta yatsine fuska,  Zanci Maman Nafisa, abincinne gaba Waya bayamin daWima ni wlhy .
Umma taWan murmusa, saboda tasan baa hajia hindu ta faWa mata. Abba ma na jinsu, sai dai babu bakin magana, a zuciyarsa kam babu abinda yake jinjinawa sai yayyawar zuciyar Umma, wai ita wace irin mutumce mai maida sharri da alkairi?. Bashida mai bashi wannan amsar, sai hawayen da suka gangaro masa ta gefen ido wanda su Umma basu gsniba. Shi kansa baisan dalilin zubarsuba, zafin ciwone? tausayin kansane? Kokuwa nadamace?, shidai yasan har yanzu baiji a ransa ya aikata badaidaiba gasu Umma, yanzu da ace aansane maza sukazo a manya da asar waje za'a kaisama jiyyarnan.........

Shigowar Uncle yahya ce ta katse tunanin Abba, tare yake da mijin Aunty Nafisa, saisu Aunty Zulai dake a bayansa suduka harsu kalifa.
Da gudu su Hassan suka nufi uwarsu, Maneer ne kawai yaje wajen Abba yana faWin  Abbanmu bakada lafiya? Miya sameka? .
Ummace ta janye Muneer ganin zai fara kuka, Abba ya janye idonsa daga Muneer da Umma ya maida kansu Kalifa da ko sau Waya basu kalli inda yakeba, sun zagaye uwarsu suna faWa mata arya da gaskiya da akai musu a gidan Umma. Tuni ita kuwa launin fuskarta yagama canjawa...
Tsawa Uncle yahya ya dakamusu, kafin ya zubamusu dauwa da faWin,  Kunci gidanku, toku su wanene da idan kukai laifi baza'a hukuntakuba?, waWannan ba yayyenku baneba?, ko Walida ce ta tsawatar muku ba dole kujiba balle Zulaiha da Nafisa, duk wanda na arajin bakinsa saina zanesa a asibitinnan, gida kam ai dole kuzauna tunda bakuda kamarsa yanzu. Kekuma maman kalifa kin zauna saurarensu bazaki ko tsawatar musuba .
Cikin Kumbura fusaka tace,  Yo yahya minene abin tsawatarwa anan?, daba a cuta musuba zasu faWane .
Tsit gurin yay duk suna kallonta, Abba ne kawai yaji daWin abinda tayi a ransa, danshima yaji haushin an dokar masa an lelensa, saidai babu bakin magana.
Daganan babu wanda yakuma tofa baki acikin lamarin su kalifa, anan suka yini a asibitin har yamma liis sanan Uncle yahya yace su koma gida.
Hajia hindu naji na gani Uncle yahya ya kora su kalifa daketa ununai su bazasu komaba, wai tuwo da koko da shinkafa kawai akeci a gidan, sukuma basu iya ciba (hhhhh aan turawa=9).
Ko kallonsu Uncle yahya baiyiba, danshi dariyama suke bashi wlhy.
Su Aunty Saudah suka tuntuSi Uncle yahya akan batun faWama Jiddah, murmushi yayi,  Karku damu zata sani, amma sonike sai zuwa kamar jibi haka, duka yaushe taje gidan mijin da za'a sakata fitowa?, sonake sai zuwa jibi ta cika sati biyu insha ALLAH, suma zuwa sanan sun fara samun saui, kunsan Jiddah da ruWiya, kuma zuwanta bashine zai basu lafiyaba ai .
Sun amsa da to, tareda gamsuwa da maganarsa.

('('('('('('('('('('('

*_Bayan kwana biyu_*

Har zuwa yau Jiddah batasan mike faruwaba, kuma tana waya da Umma da Uncle yahya, hakama aunty Nafisa, babu kuma wanda ya faWa mata.
Yauma dai haka ta yini ita kaWai a sashenta, saboda zuwan da Amina da Hassana sukayi gidan, sanda sukazo tana sashen Maimuna suna kallon wani tafseer Win Sheikh Aliy, amma tundaga shigowarsu jikinta yay sanyi, dan wani kallon banza sukaita binta dashi, koda ta gaidasu babu wanda ya amsa saida Maimuna tace Auntys jiddah nafa gaisheku. Duk a yatsine sukace  oh ALLAH sarki, bamuji bane .
Jiddah bata gazaba takuma maimaita musu gaisuwa, lokacin ita Maimunatu taje kicin kawo musu ruwa, tsaki sukayi mata basu amsaba, hakanne ya sakata miewa tabaro sashen ta dawo nata jikinta sanyi alau da tunanin sukuma su wanene? Tagadai Waya na bala'in kama da Maimunatu (Hassana). Koda ta dawo sashenta sai abin yakuma untata zuciyarta, tana cikin tunani a falo saigasu sun shigo Maimuna ta rakosu wai zasuga Waki, dan ita maimuna batasan abinda suka kuma yima Jiddah ba.
Jiddah ta saki fuska takuma tarbarsu da mutuntawa a nan ma, babu inda basu shigaba, amma sai wani yatsine fuska suke, komai suka gani sai Amina tace,  Aunty Hassana nikam ba wanan abun bane ranar muka taya a wajen an gwangwan Wincan dubu uku? .
 Shinefa ar uwa, kinma manta dubu biyu suka barmana daga baya .
 Hakanefa wlhy, nama manta .
Gadajen Jiddah ma da kujerunta haka sukaita musu iskanci, wai Hassana taje kasuwa akace za'ai mata a dubu arba'in, amma tace basuyi mataba tawuce nan.
Ran Maimunatu ya Saci sosai, dan haka taja hannun aunty hassana suka fice, amma saita fisge tana mata masifa.
Acan kuma Amina nata gaggasama Jiddah magana ta rashin mutunci, itadai jiddah batace mata komaiba, saima kanta data duar a asa tana wasa da yatsun hannunta, har Amina tayi tagama ta fice sanan ta Wago tana kallon ofa hawaye na ziraro mata, ta daWe a falon tana kuka kafin ta koma bedroom ta kwanta, ganin zata untata kanta da yawa ta kunna karatun Al-Qur'ani tana saurara, a haka barci ya kwasheta.
Sai da Maimuna tazo kawo mata Wanwake da tamusu na ranane ta tadata dan har anyi salla ma.
Sannu tamata da godiya, Maimuna tafita saboda su Amina basu tafiba, da zama ta kawo mata abincinan da hanawa sukayi sunata mata masifa, sai da tace wlhy zata kira Malam ta sanar masa kafin shima Aliyu ya dawo ta faWa masa, sannan ne suka bata hanya suna zaginta wai baiwar kishiya. Itadai batabi takansuba ta fito kawoma Jiddah abincin.

Har yamma lis su Hassana suna gidan, sai bayan la'asar ne suka tafi, jiddah najin tafiyarsu saboda dariyar da sukeyi suna sakin magana a kanta, amma sai tai fita, dan duk zuciya nason mai yautata mata.
Maimuna sashenta ta koma, duk zuciyarta babu daWi itama, dolene tasaka a takama su Aunty Amina birki akan zuwa gidan, dan itadai baza'azo a haWa mata fitina a gidan aurenta ba, suna zaune lafiya a Sata musu zama, badan Jiddar tanada hankaliba da biyema su Aunty Hassana zatayi sosai, dan ba kowa zai yarda da wannan cin kashinba, jitai Jiddah takuma birgeta, sai dai yanzu tsoronta karta faWama Aliyu abinda ya faru ne.


('('('('('('('('('('('

Alhmdllh jikin Abba yaWanyi saui, dan kuwa kumburin fuskarsa ya sauka, sai daifa yanashan azamar afa da ugu, wanima tashin hankali shine Worin karayar ugunsa bata Woruba, likitoci sukace sai an sake, ankumayi yau da safe yaci azaba iya iyawa amma ba'a daceba, shine Uncle yahya ya yanke shawarar kiran wani na gargajiya, dan haka yaroi likitan akan su sallami Abba za'a canja masa asibiti, sunyi hakanne dan sunsan idan sukace na gargajiya za'a likitocin bazasu yardaba, shikuma tsoro yake kar goma ta lalace biyar bata gyaruba.
Sosai hajia hindu tayi murna da wanan sallama, dan itafa ba damuwarta Abba ba, hankalinta nakan kuWin data saka aninta yazo yay musu fashi. Kamar yanda Umma da Uncle yahya suka yanke shawara haka akayi, kai tsaye gidansu Umma aka wuce dasu Abba, Wakin dake soro Uncle yahya yasaka aka hudo ofa ta cikin gida tun jiya, ita kuma hajia hindu aka kwashe kayansu Zarah daga Wakinsu aka gyara mata.
Su aunty sauda duk basuso hakaba, dan yanzu dai ba gidan Abba baneba na Jiddah ne, saida Umma taita tausarsu sannan suka bar zancen.
Sosai hankalin hajia hindu ya tashi, wai ana nufin wanan gidan data bari tsawon shekara sha shida dawasu watannine za'ace ta dawo da zama?, wanan ai ci bayane, dolene ta nemo aninta a yau yakawo kuWin nan tanemi aramin gida tasai musu itada aanta, shiko Abba yazauna nan yayi jiyya, idan ya warke ya nemesu.
Abba kam yana cikin azabar ciwo, bayama tantance a ina yake balle asan sirrin ransa
Gidan dai yamusu kaWan sosai, amma haka sukai maleji, da daddare wasu sukaje gidan Uncle yahya suka kwana.
Su kalifa kam abufa ya damesu, sai kuka sukema hajia hindu basa son wanan gidan, sudai akoma gidansu. Hajia hindu saita sake rikicewa, dan ita kaWai yaran suke addaba, basayi gaban su Uncle yahya.
Washe gari da safe mai gyara yazo, sabon Wori ya sakema Abba a ugu, suma kam Abba yayita babu adadi, su Zarah kuka kawai sukeyi, hakama Umma takasa daurewa, sosai takejin tausayin Uban aan nata dukda tsiyatakun daya shuka mata.
An gama gyaran Abba ya samu barci na wahala, a lokacinne hindu tasamu zarafin tambayar Uncle yahya wayarta wai zata sanarma danginta.
 Wayoyinku suna cikin wata jakarki na zuba, tana nan inaga an taho da ita, amma ina Zulaiha itace kamar nabama jakar dazamu taho? .
aunty Zulai dake sharo Wakin Umma tace,  Eh Uncle tana nan Wakinta a jar jaka .
 yauwa to kinji tana nan, sauran kayanku suna gidan malam Alfah na roi alfarma aka kai can, saboda mu gidajen namu babu inda za'a iya lode waWan nan kayan, kayan gado dai dasu kujeru duk an saidasu harma katufun, guda ukunan dakika gani kaWai muka bari, acikin kuWinne ma akabama mai gyaranan kuWinsa, dan wlhy nidai kuWin dake wajena sun are, a jiyama saida na taSa kuWin sadakin jiddah dubu ashirin aka Wako sauran kayanku, amma an maida mata yanzu haka, wanan daliline yasa muka matsa aka sallamoku daga asibiti, tunda bamuda kuWin cigaba da biyan kuWin gado da sauransu, yarannan kuma su Hannatu iya oari sunyi dagasu har mazajensu, koma nace suna cikinyi .
A Wage hajia hindu ta amsa da  Uhhum . Dan taji haushin saida musu kayan gado kuwa, amma babu komai aiga kuWinan.
Babu wanda yasakebi ta kanta, saboda amsar da tabama Uncle yahya ta Uhum kowa tabashi takaici.

Shidai Uncle yahya yay musu sallama yatafi gida danya Wan huta kafin Abba ya farka.

***********

Da rana akayi faten doya da wake da alayahu, iri-iri su Hussain sukace bazasu ciba, babu wanda ya tanka musu sai Umma daketa musu nasiha da lallashinsu, amma iri da muzu sukai saurarenta, saima rashin kunya da suka nemi yimata, aiko Aunty Hannatu dukda haurinta tai azamar taka musu birki.
Hakan saiya harzua hajia hindu tafara sakin magana, gashi tana yaSe waje Waya tana fama da kanta.
Aunty Zulai zatai magana Umma ta hana, takumace kar wanda ya sake tankawa, daga yanzuma komi su Halifa zasuyi a gidan babu ruwansu, abinci dai idan andafa a basu, suci ko karsuci wanan yarage nasu ai.
Hajia hindu dai tanata neman ananun magana babu wanda ya kulata, ga takaicin neman kaninta da take a waya amma tai shiga, tamasa kira yafi hamsin sai dai ace mata Busy, tun tana Waukar abin wasa har nutsuwa ta fara gagararta.


Hummm hajia Hindatu yaya dai&
@&=9?.


('('('('('('('('('('('

Jiddah na zaune a falo bayan tayi sallar la'asar tana duba littafin *Ahdhari* Aliyu ya shigo da sallama, Wago idonta da sukai alamun tayi kuka tayi ta kallesa tana amsawa, ya tsaya a ofa tareda buWe mata hannayensa alamar tazo gareshi.
Murmushi tayi tamie jiki a sanyaye, dan yariga ya shaida mata hakan dokane acikin tsarinsa, kuma koba komai tana buatar jin Wuminsa a halin yanzun da zuciyarta ta wuni a untacennan.
Shigewa tayi ajikinsa tana sauke tagwayen ajiyar zuciya.
shima numfashi ya sauke, yace,  Nayi kewarki Jiddah na .
Ahankali ta furta  Nayi kewarka sosai nima .
Babu shiri yay azamar Wago kanta, dan maganarta tabashi matuar mamaki, baiyi zaton hakan agareta ba nan kusa. Lumshe idanunta tayi tana murmushi, dan batason su haWa ido.
 Jiddatulkhair da gaske koda wasa? .
Fuska taWan shagwaSe tana tura masa baki,  Da gaske mana . Ta kare maganar da maida kanta a kirjinsa.
 Masha ALLAH, Alhmdllh Adaratul ainy (Turaren zuciyata) ya kuma rungumeta yanajin sonta nakuma tasiri a ransa .
Bayan sun zauna taje ta kawo masa ruwa. Yana sha idonsa a kanta, dan ya kula tana tare da damuwa kamar yanda maimuna ta sanar masa, saboda sashenta yafara zuwa, itama ya isketa cikin damuwa, ya tsareta da tambaya shine ta sanar masa abinda su Hassana sukazo sukayi, ransa ya Saci sosai. Amma sanin halin Maimuna bazata taSa sakasu suma Jiddah hakanba sai itama ya lallasheta akan karta damu, shi yasan bazata sakasu suyiba hakanba ga jiddah, sunyine kawai dan raWin kansu, amma zai taka musu birki insha ALLAH.
hakan sai ya saka zuciyar Maimuna Wan samun nutsuwa, amma damuwarta kuma halin da jiddah take a ciki.
Aliyu ya Wauki aniyar gwada Jiddah yagani kozata masa maganar abinda su Aminar sukazo sukayi.
 ammatana mike faruwa? Na ganki wani sukuku, ga idonkifa kamar kinyi kuka ......
Murmushi jiddah tayi tana danne abinda ya tokare ranta,  Babu komai, kumani ba kuka nayiba, kawai kewar Ummana nakeyi .
Idanu ya tsura mata zuciyarsa na tunanin ita takeson sanarma kenan? To amma dataso hakan ai da tayi tunda ga waya a hannunta, saurin kauda wanan tunanin yayima daga ransa, ya ajiye kofin da yasha ruwan yakamo hannunta cikin nasa idonsa akan fuskarta,  Haba tawan, anya kuwa kewar su Ummace kawai? Kodai Auntynki ce? .
 lah A'a wlhy, ni aunty tsakanina da ita sai sambarka, kawai dai kewar su Ummance .
 Shikenan, insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu zan kaiki, yanzuma tashi ki shirya danayi wanka zamuje mu gaida su malam, kinga baki taSa zuwa gidanba tunda kikazo.
DaWine sosai ya kama jiddah, harga ALLAH tana aunar dattakon tsohon, tuni taji nauyin da zuciyarta yayi kaso mafi yawa ya ragu.
tace,  To abincifa?
 Naci abinci a office din mustafa, shiyyasa na kira auntynki nace karkuyi dani .
Murmushi tayi, dukda batasan anyi hakanba, kuma girkin Maimuna ne har rana, sai yanzu da yammarnan ita zata karbesa, batareda tace komaiba ta mike, harta nufi ofar fita Aliyu ya kirata, juyowa tayi ta kallesa, yace,
 Ina zakije kuma? .
 Zan haWa maka ruwan wankane .
 Karki damu zoki haWamin a bayinki kawai .
Kanta ta jinjina masa ta dawo da baya zuwa bedroom nata. Binta yayi da kallo harta shige, ya Wan sauke numfashi yana jingina kansa da kujera, a zuciyarsa yana tunanin miyasa tai faWa masa abinda akai matan? Zai sake gwadata dai ya gani, harga ALLAH yana mamakin yanda wasu lokutan halayyar Jiddah da Maimuna suke kamanceceniya da juna, kodan dukansu sunada ilimin addinine da tarbiyya, kuma Alhmdllh suna aiki da sanin da ALLAH yay musu, sarai yasan salon kishin kowacce amma hakan bai hanasu yautata zamantakewar dake tsakaninsuba..........
Jiddah ta katse masa tinani, idanunsa ya buWe, ya kama hannunta yana faWin  Zomuje ki tayani wankan to .
Sosai ta zaro idanu da faWin  Wankafa? .
Tabashi dariya data zaro idon, ya ranwafo kanta yana jan hancinta,  Malama bayason koyi da sunnar MANZON ALLAH ne? ANNABI yana wanka da Matansa har hannayensu na gogayya a cikin ruwa, bayason samun wanan atotuwar ladar tawajena .
Hannu ta saka ta rufe fuskarta tana aramar dariya, shima yay dariyar yana jan hannunta sukai ciki....

('('('('('('('

Gabda magriba suka fito da nufin barin gidan, dan Aliyu soyake yay sallah a masallacin ofar gidansu, Kasancewar Jiddah ce da girki maimuna tace ya shiga gaba, amma sai tai tace,  A'a wlhy Aunty ke zaki shiga, ba girki zaki dubaba, kimarki ta matsayin babba a gareni .
Daga Maimunatu har Aliyu binta sukai da kallo harta shige baya, sanan suka kalli juna sukai murmushi, kowannensu yanajin aunarta da kimarta a ransa, yayinda itama hakanne daga gareta.
Sun isa anata hada-hadar shiga sallar magriba, Jiddah da Maimuna suka shige cikin gidan, shikuma Aliyu yashiga masallaci..........
'<


_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._

*AURIN OYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI AYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAUMI..!* (Bilyn Abdull)

=G
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*><><><



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*=O<=-
[12/30/2019, 1:58 PM] =؞Noorunnisa=؞: *_Typing=_*



*_=ءHASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=اMUTUM DA DUNIYARSA....!!=ا_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce><_*

*_[59'60]_*


............Duk da agidan Maimunatu ta girma, kuma akwai mariiyarta Iya Habi, hakan baisakata kaisu canba itada Jiddah, saita nufi Wakin hajia bah-bah uwargidan Malam.
Sosai Hajia bah-bah taimusu tarbar mutunci, hakama Na'ima tafito fuskarta ajie da alamar alwala tayo tana musu oyoyo.
Harara Maimuna ta zuba mata tana faWin  Ani a amsa Win, aini yarinya mun Sata .
 Haba-haba Uwar ukunmu, yi hauri, nasan nayi laifi amma wlhy tafiya nayi tun bayan bikin yaya Ali, kuma tambaya bah-bah kiji. Aunty Amarya sannu dazuwa kinji .
Murmushi Jiddah tayi tana amsawa.
Hajia bah-bah ta katse musu jancen da faWin,  Da wannam surutun da kika tsaresu dashi da alwala kika kaisu sukayi ga Aliyu can zai tada salla .
 To bah-bah. Kunga kumuje to .
akin Na'ima suka koma, domin yin sallar acan.

Bayan an idar da sallah Aliyu na gaisuwa da mutane wayarsa tayi ring, cirota yay daga aljihu ya duba, ganin Uncle yahya saiya faWaWa murmushinsa, bai Wagaba saida ta tsinke sannan shi ya kirashi da kansa.
Daga can shima Uncle yahya murmushin yayi ya Waga, cikin girmama juna suka gaisa, Uncle yahya yama Aliyu bayanin halin da Abba ke ciki kusan kwana uku.
Sosai hankalin Aliyu ya tashi, yace,  Uncle aida an sanar mana, babu wata damuwa, ko yau aka kaita washe gari hakan ta faru ai dolene tafito, kuma koni aida nazo dubashi. Insha ALLAH gamunan zuwa bayan isha'i .
 ALLAH ya kawoku, nagode a gaida min malam .
 Zaiji insha ALLAH .
Sosai lamarin ya zauna a zuciyar Aliyu, duk zuciyarsa taimasa babu daWi, tausayin Abba sosai ya Warsu a ransa. Matsawa yay kusada malam dake zaune yana duba alur'ani ya sanar masa da abinda ke faruwa.
 Ya Salam, ALLAH yabashi lafiya, yasa kaffarane a gareshi, insha ALLAH zanje na dubashi nima .
 Amin baba, to ALLAH ya bada iko, suma tare muke dasu sunzo gaisheku, daga nan zamu wuce mu dubashi insha ALLAH .
 To masha ALLAH, hakanma yayi .
Bayan an idar da salla malam yasaka Abba a cikin doguwar addu'a, wadda ta saka Aliyu jin daWi sosai.

A cikin gida kuwa su Jiddah suna idar da salla sukazo suka gaida hajia bah-bah, cikin fara'a ta amsa musu tareda sanya musu albarka. Sanan tace suje su gaida su Gwaggo.
Sun fara zuwa sashen gwaggo amarya, itama ta tarbesu da fara'a, basu baro sashenba saida za'a kabbara sallar isha'i, sashen iya habi suka shiga, itama ta tarbesu da barkwancinta, tareda jin daWin ganin Maimunatu ta bata cikin damuwa, saitaji

1 Comments On MUTUM DA DUNIYARSA
avatar
rukayya-yahuza

1 year ago

Reply

Kai book dinnan ya hadu iya haduwa

Please Login or Register in order to submit comment