Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanyi kozatasha tirelar maganin gyaran Kanta to wlhy tamkar a banzane, dan bazai Mata amfanin komaiba, dan haka idanma zaki maida hankalinki ki maida, yanzu hakama hajiya ladidi mai adashe tace zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zata kawo miki wani”.
Kan Jiddah a k'asa tace, “To Umma nagode .


('('('('('('('('('('('

Aliyu kam ya ajiye wayar yay yana maida hankalinsa ga Maimuna, dan kimarta tawuce ya amsa wayar wata mace a gabanta, a ganinsa hakan tamkarma cin fuskane da had'a k'iyayya a tsakanin matan nasa.
 Hiya-huwa kinyi k'yau ainun Masha ALLAH”.
Wani dad'ine ya ratsata jin sunan daya kirata dashi, ta kama hannunsa ta sumbaci tsakkiya, cikin narke masa tace, “Hilmy yanzu kaima zakayi fiyema dani”.
“haba-haba, ai idan ana dara fidda uwa ake gimbiyata, samun k'yak'yk'yawa irinki acikin Mata sai an tona, kina kallon kaniki a madubi kuwa?”.
“Kai yayana kadaina fasamin Kai hakanan fa, kaidai zauna Na shiryaka muje ka karya, dan sak'onin daka sakani Na amsa wad'anda Zan iya jiya naci Karo dawani mai muhimmanci”.
Kallonta yayi sosai, “Mi sak'on yace?”.
”A'a kabari saika karya”.
“Karki damu fad'amin kinji”.
Mai tafara shafa masa, _“Cayay ka taimakeshi da shawara akan lafiyarsa, yanada Mata harda yara a tsakaninsu, iya gwargwadon iko suna gamsar da juna a shimfid'a, dukda dai ya fuskanci shi mutumne mai rauni dan baya iya jan lokaci wajen tarayya da ita amma sai bata ta6a nuna damuwartaba akan hakan, Sai kuma dukda wannan matsalar daya sani saiya k'ara aure, to a yanzu halin dayake ciki shine baya iya gamsar dasu su biyun, amaryar tashi kuma tafara nuna itafa bazata iyaba, itama Uwargidan haka, hakan kuma yafara kawo musu matsalar yawan hayaniya da matan nasa musamman Amaryar, shikuma yarasa yanda zaiyi, ya gwada magunguna da ake saidawa Na gargajiya sai dai tasirinsu kuma bawani mai tsayi baneba agaresa ake komawa Y'ar gidan jiya, shikuma duk yanason matansa yanason cigaba da rayuwa dasu.”_
Ajiyar Zuciya Aliyu ya sauke, ya taimakama Maimuna dake k'ok'arin saka masa kaya, saida suka kammala tasa masa turare sannan suka fito yana fad'in “Wannan matsalar abar dubawace, kuma insha ALLAH zanyi magana akanta yau a masallaci, dan munada majalisi, matsalace babba wannan Maimoon data dabaibaye Mazajenmu Na arewaci, ammafa tamafi illa a kudancinmu, kawai sudai sun fimu himmar gyara kansune, matsalarmu mu mazan arewa shine mun d'auka mace ita kad'ai yadace ta gyara mana kanta, mukuma abinda muka iya kawai munemo kud'i muyita aure Ana kiranmu jarumai a waje, a cikin gida kuwa bama iya hasalama iyalinmu komai, Mata da yawa suna cutuwa ta wannan sigar, saidai basa iya magana saboda kunya, soyayyar mutumin arewa a iya wajene kawai saikuma amarcin watanni uku, ita kuma mace kota tsufa tana buk'atar tattali da soyayya ga mijinta, koda bakada wadatar dukiya soyayyar dazaka nuna Mata kad'ai wlhy zakiga ta gamsar da ita da jagorantar zamanku har k'arshen rayuwa”.
“Wlhy Yaya maganarka gaskiyace kuma”. Maimuna dake zuba masa a bincin tafad'a cikin damuwa.
Ajiyar zuciya shima ya sauke, dan abi yana Sosa masa rai, amma insha ALLAH a wannan Karon zai amayar dashi ya huta, dan ba Neman ilimi da tafseer kawai al'umma suke buk'ataba, akwai wasu manyan abubuwa Na rayuwa da muhimmancinsu yakai adinga tunatar da mutane shi kodan samun sauk'in da duniyar aurarrakinmu ke fuskanta a halin yanzu.


('('('('('('('('('('('

Jiddah da Umma na a tsakar gida suna shirin girkin rana da hira wadda rabinta duk ilimin zaman aure Umma ke k'arama Jiddah haske akai cikin hikima.
Tamkar an jefo Abba ya banko k'ofa jikake garam!!!, duk zabura sukayi suna kallonsa, Kai tsaye kan Jiddah dake tsaye a bakin rijiya yayi tamkar wani bajimin zaki...........
'<Øûß




=Ø(ÞAbba zakari mi zakai mata kaikuwa?.=ØFÞ<Øûß


_Barbarawa ayimin afuwa (Au bare-bari=ØFÞ<Øûß>Ø-Ý). wata tace ba sunansu hakaba, Barbarawa kamar bunsuru wai=ØÞ, bani Na fad'aba Y'ar uwarkuce tace, karku dafani yau su tawan (miss Xoxo)ù&
@&ù&
@&ù&
@&._



*_Albishirinku fa, CIKI DA GASKIYA mafa ya sauka a gareku adai YouTube channel tv na Abban Dausayi, saiku garzaya kar ayi babuku gayis_*.ù&
@&ù&
@&ù&
@&









*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*=ØOÞ<Øûß=Ø-Þ
[12/16/2019, 9:06 PM] =ØžÜNoorunnisa=ØžÜ: *_Typing=ØòÜ_*



*_=Ø¡ÜHASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=اÜMUTUM DA DUNIYARSA....!!=اÜ_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>ØÝ<Øûß_*

*_[37–'38]_*


..............Da sauri Umma ta sha gaban Abba dake nufar Jiddah tamkar wani bajimi, ture Ummar yayi yasaka k'afa ya tad'e Jiddah dake Neman guduwa.
Fad'uwa tayi k'asa akan hannunta, dan haka ta fashe dakuka saboda zafin daya ratsata.
Waya ya jefa Mata, “'Dauki wayar nan kikira Wanda aka d'aura miki aure dashi yanzunan kice ya sakeki”.
Kuka Jiddah takuma fashewa dashi, ta d'auki wayar ta rik'e, da sauri Umma ta kwace tana fad'in “Bazata kirashinba, Kai mizai hanaka kiranshi kace ya saketan?”.
“Yagana! Yagana!! Kina shigarmin hanci da yawafa”.
“To mizai hana ka fyatoni ka huta, wlhy wannan karon duk abinda zakayi sai dai kayi amma bazan d'auki wannan masifar ba.......”
A fusace ya d'aga hannu zai Mari Umma
“Wlhy karka sake ka ta6ata!!”. ‘Yaruwaiya dasuka shigo yanzu babu dad'ewa tafad'a a matuk'ar tsawace, dan sunji mafi yawan abinda ke faruwa’.
Cak Abba ya dakata, bai marentanba baikuma sauke hannunsa ba.
Zarah da Balu sukazo suka d'aga Jiddah dake kuka zaune, hannunta harya fara kumbura alamar taji ciwo. Itama Yaruwaiya zuwa tai ta janye hannun Umma suka bar Abba a wajen, yakasa motsi balle dogon tari.
Hayawaye kawai Umma taji sun gangaro Mata, duk k'ok'arinta Na 6oye mugayen halayyar Abba ga danginta yau sai da ya tonama kansa asiri, shekaru ashirin suna tare bata ta6a Kai k'ararsa wajen iyayentaba idan yamata Abu, aganinta hakuri shine maganin komai, sannan yawan Kai k'arar miji gidanku ko gidansu tamkar zubarwa da kanku darajane, dan iyayenka zasu rage ganin darajarsa, idan kuma iyayensane suma zasu rage ganin darajarka.
Zarah da Jiddah ma hawaye suketayi, ga hannunta dake Mata azabar zogi, shiru babu Wanda ya iya cewa uffan a cikinsu, kowa da abinda zuciyarsa take sak'awa.
A tsakar gida kam kwafa Abba yayi yafita yanamai jin haushin Yaruwaiya, amma ko giyar wake yasha bai isa cigaba da abinda yay niyyaba, dan Yaruwaiya ba kanwar lasa baceba, kad'an daga aikints ta ketashi gaban y'ay'ansa.


('('('('('('('('('('('

Tuni zufa ta jik'e hajia Hindu saboda azabar da k'afarta kemata, k'arar data kwallane yasaka kalifa zuwa d'akin.
“Momy miya sameki?”.
“Kalifa Abbanku ne ya karyamin k'afa”. Tafad'a cikin jin azaba. Gabanta yazo ya zube yana Kama k'afar dahar tafara kumbura, “Momy mikikai masa yay miki haka?”.
“Babu abinda nai masa kalifa, dan kawai Na fad'a masa gaskiyane”.
“Kiyi hak'uri Umma ALLAH ya saka miki, bara Na Kira direba mukaiki asibiti.

Da k'yar Kalifa ya iya taimakama Hindu tafito suka shiga mota, Wanda aka aiko daga makarantar su kalifa danyaje da Abba ganin yanda jama'ar gidan suke kamar a tashin hankali saiya sulale ya koma makaranta Kai rahoto.
A asibiti kam anduba hajia Hindu data samu targad'e a k'afa, nanda akaimata gyaran datasha azaba. Magunguna aka bata suka dawo gida.
Saidaifa a k'asan zuciyarta tanajin bazata bar abinda Abba yay mata yatafi a banzaba, dolene saita rama wlhy. Tana zaune afalo tana cika da batsewa Abba ya shigo, harara tashiga watsa masa, amma ko kallon inda take baiyiba yay shigewarsa d'akinsa zuciyarsa nacigaba da tafasa, shi yanzu a ina zai samo wad'annan kud'ad'en yabama Alhaji garba? Kodai shawarar Hajia Hindu zaibi yabashi Zarah? To amma kuma shi Alhaji garban zai amince ne?, kansa yadafe cikin matsananciyar damuwa, gaba d'aya yama rasa miya dace yayine?. Yana cikin wannan halin wayarsa tashiga ruri, sharewa yayi tamkar bazai d'aukaba, saikuma yaja tsaki yana fisgo wayar saikace itace tai masa laifin.
Daga makarantar su kalifa ne, a fusace ya d'aga, ko sauraren sallamar da akai masa baiyiba yace, “Minene?”.
“Babu komai Alhaji, akan maganar yaronkane da muka turo da d'an rakiya, yadawo mana babu Kai babu yaron kuma”.
“Kaga da ALLAH karku dameni, harma nawa kalifa yake dazai zauna fad'a dawani akan mace, nifa banason sharri, suje can sunema Wanda ya fasama d'ansu kai, Mtsoww aikin banza kawai”. K'itt ya yanke wayar.
Yin haka dakamar mintuna talatin saiga mai gadi yashigo wai ga y'an sanda sunason ganin Alhaji.
Da mamaki Hajia Hindu dake tule a zaune tace, “Y'an sanda kuma? To miya faru to?”.
“Wlhy hajia bansaniba”.
Kalifa ta kwalama Kira, yafito yana kumbura baki da k'unk'unin antasoshi yana hutawa, “Kaje kakira Abbanku yayi bak'i kazonan kana cunomin baki”.
Tafiya yay d'akin Abba yana mangara Kai dacigaba da k'unk'uninsa. Babu jimasa suka fito tare, yanzuma Abba baiko kalli hajia Hindu ba yafice kalifa Na biye dashi.
Koda suka fito kalifa yaga y'an sanda da Baban yaron dasukayi fad'a saiya juya zai gudu cikin gida, amma d'an sanda d'aya yay ram dashi.
Haukace musu Abba yayi da masifa, ko kad'an basu saurareshiba suka tafi da Kalifa dake kuka. Hajia Hindu ma data rarrafo danjin masifar Abba da kukan kalifa kukan ta sanya tana rok'onsu su dawo Mata da yaronta, amma kobi takantama basuyiba.


Abifa yayma Abba yawa=ØFÞ<Øûß=ØÞ.


('('('('('('('('('('('

Yau Aliyu a masallacin k'ofar gidansu yay sallar magriba saboda akwai majalisi da sukan shirya Na k'arshen kowane wata da akan gabatar bisa tsarin malam.
Masallacin yacika taf da magidanta, samari, harma da tsofaffi, Ana idar da sallar isha'i Sheikh Aliyu yafara gudanar da wa'azi mai taken *DAMI MUKA SHIRYA TAFIYA LAHIRA?* , masallacin yayi tsait, daga muryar malam mustafa dake jan bak'i saikuma Sheikh Aliyu dake fassara cikin tsantsar ilimi da kuma fad'ad'a kowace aya domin a fahimta, lokaci-lokaci mutane kanyi kabbara, jikinsu dukyayi sanyi saboda tsoro, har zuwa k'arfe goma da rabi aka fara karanto tambayoyi.
Kafin yabada amsar tambayar farko yacire gilas d'in idonsa yana gogewa da handky d'in hannunsa, cikin sanyin nan nasa yace, “Amin afuwa Zan amsa tambaya uku ne kacal acikin wad'annan tambayoyin, dan akwai tambayar danake da burin amsata anan wadda wani bawan ALLAH ya turomin, to Alhmdllh yace shi ma'abocin zuwa wannan masallacinne, sannan kuma wannan zaman baya wucesa aduk wata, to tambayarsa tanada muhimmancin data shafemu muduka, shiyyasa naza6i amsata anan domin mu farka daga sakacinmu, sauran tambayoyi kuma insha ALLAH zamu tsara yanda za a amsasu koda daga bayane”.
Take kowa ya aminta da batunsa, dan haka malam mustafa ya karanto tambayoyi uku kacal Aliyu yabada amsarsu daganan Yakoma kan Sak'on da Maimunatu ta sanarmasa d'azun da safe.
Saida ya maida siririn farin gilas d'insa sannan yace, “Mai sak'on yana magana ne akan matsala dayake fuskanta gameda rayuwar aure tsakaninsa da iyalansa irinta rauni wajen biyamusu buk'ata a shimfid'a, amma dukda yasan da hakan yaje Yakuma k'ara aure batareda yatashi yafara Neman maganiba. Lallai wannan sakacine mai girma, sannan akwai cutarwa ga iyalanka, tayaya baka iya gamsar da mace d'ayaba sannan kakuma tarkato ta biyu? Sannan babu wani mataki Daka d'auka akan hakan kafin ka k'aro d'in?, tayaya muke tunanin Matsaloli bazasu k'aruba?, ayanzu dukanku nan dazance wanene *Jarumin Namiji?* saikucemin Wanda ya iya rik'e gidansa daci da sha dadai buk'atu nayau da kullum ko?”.
Atake suka bashi amsa da eh.
Aliyu yay murmushi yana gyara zamansa, batareda ya kallesuba yace, “To lallai wannan bazamu kirashi cikakken jarumi ba gaba d'aya, sai dai dolene mu yaba masa wajen sauke nauyin dake kansa na wani 6angaren hak'k'ok'in aure. Jarumin namiji shine mai k'ok'arin tsare dukkan wani hak'i na iyalansa, ci, sha, sutura, wajen zama, ya kula da addinin iyalinsa, yakula da zamantakewarta da makwafta da zumincinta ta 6angaren danginta da danginsa, ya nuna mata soyayyar dazata saka zuciyarta kwanciya waje d'aya batareda y'an wasan kwaikwayo da jaruman littafi na birgetaba, a wajen shimfid'a yazama Oga kwata-kwata yanda za'a ringa kiransa maigida cikeda tsantsar girmamawa, ba yana magana ana kauda Kai da murgud'a bakiba”.
Dariya suka Sanya, yayinda shima Aliyu yake darawa da kare fuskarsa da hannu.
“ALLAH kuwa karkiji wasa, duk k'ok'arin mace wajen iya girki, tsafta da kwalliya daduk wata kisisina inhar batada nagartar kar6ar mijinta a shinfid'a zakaga Mijin baya kallonta da daraja, kuma duk yawan son da yake mata saiya gudu kaga babu komai, saigaka tarasa kansa, takuma rasa ina matsalar takene?. To haka shima namiji duk k'ok'arinsa na karema mace hak'k'ok'inta inhar bashida jarumtar biya mata buk'ata to wlhy zata daina ganin darajarsa da shakkar fad'a masa duk maganar datazo bakinta, da yawan rainin da matayenmu ke mana tushensa shine ragwantakarmu a shinfid'a, kabari basir da sanyi sun gama cinyeka amma kullum idonka nakan y'ay'an mutane, da yarinya tawuce kashiga lasar la66a da had'iye yawu kana mata kallon da addini ya haramta maka, amma matarka dake gidama baka iya biya mata 6uk'ata yanda ya kamata. Akulum matayenmu sunada k'ok'arin gyaran Kansu a kanmu, dan a hasashe babu wanda yakai matanmu k'ok'arin shaye-shayen magungunan nan na k'arin Ni'ima, dukda suma matan ina k'alubalantarsu dan basabin matakan daya dace wajen shan maganin. A mashayinka namai gida daga lokacin da kukai shekaru biyu da aure da matarka yadace kafara neman gyara kanka, danfa kafara komawa cus malam. Kai kanka kazauna ka k'iyasta da watannin farko na amarcinku irin nanuk'ema amarya da kakeyimana, kai abindama yakamata namiji yayi daga shekarar dayasan zaiyi aure yadace yafara dagewa da amfani da maganin sanyi dana basir, dan sune manyan abinda kemana lahani, bakuma komai ke kawosuba sai abincin da mukeci, mutum a yini saiyaci maka abinci Kala kusan goma sha dukshi kad'ai, kuma zaka samesu duk maik'one, tayaya basir bazaiyi ram damuba?, kafara gyara kanka malam tunkan amarya tashigo daga ciki, yanda idan tashigo tajika zam, kanayin magana zatace hakane Alhaji koda bakada ko sisi kuwa”.
Nanma dariya mutane keyi, samari damasu kunya nata sunkuy dakai, shima kansa malam Aliyun kansa a k'asa yake baya kallon kowa, dama malam bayanan yamayi tafiya.
“Ina muku wannan maganarnefa akan gaskiya y'an uwana, domin wlhy sakacin gyara kayinmu yana bada gudunmawa wajen saka matayenmu a masifu Na mad'igo da zinace-zinace ko amfani dakansu wajen samun biyan buk'ata, wata badan kud'i take aikata wad'annan fasik'ancinba, saboda kawai mijinta baya iya gamsar da itane, mace tadage tasayi kayan gyaran kanta tasha babu ko sisisnka Alhaji, kuma dan kawai ta burgeka, buk'atar mijinta ta taso Mata amma dayazo bazai iya gamsar da ita yanda ya kamataba saiyaja gefe, tayaya muke tunanin bazata nemawa kanta mafitaba?, ga masifu da kafafen social network d'innan sukazo mana dasu iri-iri, matarka taje tashiga taganoma kanta masifar dazata dameta kai baka kusa da ita, koma kana kusa bazaka iya biya Mata buk'atartaba Yaya kake ganin za'a k'are? Wlhy inda zaka zama jarumi wajen bata kulawa da kare mata duk wani hak'k'inta a shimfid'a ko soyayyar da suke gani a finafinan banzarnan bazaiyi tasiri agaresuba, dan mace kota gani saitaga ai shirmece, wadda mijinta ke Mata tawuce wannan, tayaya ta film da hikayoyin marubuta zata birgeta balle har tadinga kokwanton anya akwai irin wannan soyayyar kuwa a duniya?. To tasaba Nata Mijin daga mazurai sai matsalar Neman kud'i yasani, wanima saiyakai k'arfe sha biyu a majalissar da ba'a komai saisurutan banza da wofi da nad'oma kai zunubi, lokacin dazai shigo gidan tajima dayin barci, saidai cikin barci taji yana Neman tausheta. Mufa mazan hausawa ko d'an soyayyarnan kafin biyan buk'atama ba iyawa mukaiba, kana zaune mace bazata ra6u da jikinkaba saikunzo kwanciya, data zauna kusa dakai kace batada kunya, wanima ko a wajen kwanciyar dayasamu biyan buk'atarsa to matar tana gabashin gado shikuma yana yammaci, burinka kawai ka kashe gobarar gabanka kakoma gefe. Haba tayaya mace zata yarda akwai soyayya a duniya inba ta film da littafiba? Addininmu babu abinda bai koya manaba, babu Wanda yakai MANZON ALLAH iya soyayya ga iyalansa, miyasa bazamuyi koyi dashiba domin samun farin ciki a gidajenmu, mudaina d'aukar matanmu bayinmu komasu kula mana da gida da yara kawai, ba haihuwa da raino da bautar cikin gida bane kawai aikin mace, baka bata ci dasha da sutura kawai bane yadace dakai, ka nuna Mata soyayya da kulawar dazata ringajin itad'in macece wadda ta isa hamshak'iya, babu birgewa a garemu ace da zarar mun aure mace tayi hauhuwa d'aya shikenan saimuce soyayya ta k'are, waya gaya maka soyayya takare malam? To komin tsufanku soyayya bata tsufa, soyayyar gaskiyama ana girmane tana Kara girma, tomu matsalarmu yawancinmu shawa'a ke kaimu ga aure ba soyayyaba, shiyyasa kwanaki naja matsalolin gidajen aurenmu Na k'ara girma da bunk'asa, amma kullum idanunmu nakan matan waje, kakasa gyara wadda ka ajiye tayaya wadda take a waje bazata birgekaba?. Dan ALLAH yakamata mu gyara, akwai abubuwa da yawa dasuke gyara namiji shima, ba Mata bane kawai keda wad'annan magungunan, akwai wad'anda idan kasha kaikanka zasu motsama jarumtarka ta yadda zaka gamsar da iyalinka, amma maganar gaskiya mu maida hankalinmu wajen Neman maganin basir dana sanyi a farko, insha ALLAHU namuku alk'awarin Baku wasu sirrika a zama nagaba dazai taimakeka wajen gamsar da iyalinka, abinda muka fad'a dai-dai ALLAH kabamu lada, Wanda mukayi kuskure ALLAH ka hafe mana baki d'aya...................
'<Øûß



*_Dadai nace bazanyi posting ba, amma ganin nagama typing da wuri nace bara nayi muku kawai_*.





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=Ø-Þ=ØOÞ<Øûß
[12/17/2019, 8:52 AM] =ØžÜNoorunnisa=ØžÜ: *_Typing=ØòÜ_*



*_=Ø¡ÜHASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=اÜMUTUM DA DUNIYARSA....!!=اÜ_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>ØÝ<Øûß_*

*_[39–'40]_*


..............Zuwa yamma lik'is Zazza6i mai zafi yarufe Jiddah saboda ciwon da taji, hannun harya kumbura, Ummace talura danhaka taje inda Jiddah ke a kwance takamo hannun.
Y'ar k'ara Jiddah tayi tana rik'e hannun Umma da fad'in “Wayyo Umma akwai zafi”.
“Yanzu nan ciwo kikaji a hannun Jiddah amma kikayi shiru da bakinki? Yanzu daban kulaba haka zakiyita zama dashi? Ga jikinkinan har zazza6i ya sauka”.
Hawaye kawai Jiddah keyi takasa magana, tsaki Umma tayi tana mik'ewa, yayinda can k'asan ranta ke k'ara zafafa da lamarin Abba, yau gaba d'aya a cikin 6acin ransa ta yini, kai dukama gidan harsu Balu.
Waya Umma ta d'auka takira Uncle yahya, yace yaje Jigawa amma gashinan a hanyar dawowa.

Sai bayan Sallar magriba Uncle yahya yazo damai gyara, sosai Jiddah ta jigata da kukan azaba, ga lalurarta, danma yanzu ALLAH ya sauk'ak'a abun sosai bakamar daba.
Ana gamawa aka bata maganin zazza6i Tasha ta kwanta sai barcin wahala.

Umma suka zauna da Uncle yahya bayan mai gyara ya tafi, bayani taimasa akan abinda Abba yazo yayi yau, sosai ran Uncle yahya ya6aci, ananma yake shaida Mata shima yaje nemansa a kasuwa akace yaje jigawa shine yayo nan gidan ya zubar musu da tujarar su.
Umma tarik'e ha6a tana fad'in “Anya kuwa Alhaji yanada isashshiyar lafiya Uncle d'insu?”.
“Wlhy lafiyarsa lau Maman Nafisa, abinda ya shukane kawai yafara girba, dan hak'in yarannan kawai ya ishesa ishara, yanzu haka d'azun Saudah takirani take shaidamin wai yakira mijinta yabashi bashin miliyan ashirin, dan ALLAH Maman Nafisa kijifa zubarwa kai mutunci”.
Ran Umma a matuk'ar 6ace tace, “Takirani nima wlhy, rasama mizance Mata nayi, dan ni lamarin mahaifinsu yafara fitamin a kai gaba d'aya, jira nake kawai naga yarananan sunsami matsugunni wlhy nak'ara gaba”.
“Kiyi hak'uri Maman Nafisa, dan ALLAH kibar wannan tunani, ke kamar uwace agaremu, idan babuke wazamu kalla muji sanyi, dagani sai d'an uwana iyayenmu suka Haifa suka Bari, amma kece kika mayemin gurbinsa, idan kin goce ni dawa kuma Zan zauna?”.
“Uncle d'insu abunne da ciwo, yaufa soyay yamareni gaban Jiddah, badan ALLAH yakawo su Yaruwaiya ba yakake tunanin za'a k'are? Dan wlhy nak'udiri aniyar ramawa daya mareni .
Kasama magana Uncle yahya yayi, in banda tafasa babu abinda zuciyarsa kemasa.


('('('('('('('('('('('

A police station dai rufe kalifa akayi yanata kuka, kusan a tare suka Isa da Abba, yayi-yayi iya iyawa abashi belin kalifa a sasanta magana amma uban d'an ya rantse sai kalifa yayi kwanan kanta, wasa-wasa har dare Abba yanacan yana fama, sai kusan sha d'aya yabaro station d'in yadawo gida, hankali tashe Hajia Hindu ta tareshi da zancen kalifa, bayani yaymata yay shigewarsa d'aki yabarta tana kuka harda kururuwa.
Suma sauran yaran duk sunyi jigum-jigum.
Washe gari dai dole Abba yaje makarantar su kalifa, amma Sam principal d'in saiyak'i saurarensa, acewarsa yanzu magana tana hannun hukuma, miyasa lokacin da suka buk'aci ganinsa yak'i zuwa?.
Duk yanda Abba yaso nuna musu kud'i abin ya gagara, ga hajia Hindu Nata musu kuka, dan kasa hak'uri tayi saida ta biyosu.
Kwasa sukayi zuwa station d'inma, canma Sam ba'a sauraresuba, saida Abba yakashe kud'i sosai kafin aka sasanta magana akan Abba zai biya kud'in asibitin yaron daduk wasu abinda zai buk'ata harya warke, aka kuma yiwa kalifa tsakani da yaron.
Sunje asibitin suka duba yaron, Ashe sosai kalifa yaji masa ciwo kuwa, sun masa sannu suka taho abinsu.
Aiko wujiga-wujiga suka dawo gida, hajia Hindu ta rungume kalifa tana kuka, hakama su Hassan duk sun rungumeshi da murnar dawowarsa.
Kan Abba yai zafi sosai, sannan dagashi har hajia Hindu babu Wanda yayma kalifa fad'a akan lamarin.


('('('('('('('('('('('


A washe gari Uncle yahya yaje wajen malam Abdul-ra'uff suka tattauna maganar tariyar Jiddah, sosai malam yay farin ciki da matso da maganar, dan sun yanke nanda kwanaki uku kacal.
Ananma Sheikh Aliyu yazo ya samesu, shima sosai yagamsu dahakan, amma kunya ta hanashi Nuna farincikinsa a gabansu malam. Sai

1 Comments On MUTUM DA DUNIYARSA
avatar
rukayya-yahuza

1 year ago

Reply

Kai book dinnan ya hadu iya haduwa

Please Login or Register in order to submit comment