Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saya mataba, kinga kodai Sana'a tayi da kayanta ai, amu talakawa ajiye firij ai badan gayu muke ajiyewa ba, ina ganin mizai hana acire a sadakin Jiddah sai a saya ko Wanda bai wuce dubu arba'in baneba zuwa hamsin haka”.
A take kowa ya aminta da maganarta, Yaruwaiya tace, “Kumafa gaskiyane wlhy, inaga hakanma shi kawai za'ayi, amma afara sanarma kawunku yahya sanan, saimuji shi mizaice, mace babu sana'a ai akwai matsala, randa miji yatashi baidashi sai kowa yay zuru-zuru, irin wannan ke kawo yawan husuma kuma wlhy, shi yana wuya saboda talauci kaima kana mak'ogwaro, abu kad'an zai hasala kowa ya fusata saikiga anyi sama”.
Umma ce ta d'auki waya ta Kira Uncle yahya, cayay mata gashinan a hanyar gidan ma. Tana ajiye wayar babu jimawa saigashi yazo. Bayan an gaggaisa Yaruwaiya tamasa bayani, 100% ya yarda da shawarar, danshima aljihun nasane yayi k'asa, amma harga ALLAH yayi niyyar siyama Jiddah duk abinda yadace mace ta bud'e ido tagani a d'akinta, musamman abinda za's iya Mora har a sana'a.
Bayan sun gama tattaunawane yasamo musu motar dazata kwashi sauran kayan Jiddah da akwatinanta da kayan gara dadai sauran tarkace.
Umma kawai aka bari a gidan sai wasu tsoffi uku danginsu Jiddah 6angaren su Abba, su Balu, aunty Zulai, aunty hannatu, Walida, suka wuce gidan Jiddah. Maman Sadiq, Yaruwaiya, aunty Saudah, Aunty Nafisa, sai Zarah suka wuce kasuwa k'arasa sayo abinda ya rage Na Jiddah.


('('('('('('('('('('('

Ikon ALLAH ne kawai yakawo Abba kano, ammafa wujiga-wujiga ya Iso saboda 6acin ran da yake a ciki.
Su Hajia Hindu na zaune a Dani itada yara suna dinner ya shigo ko sallama babu, Maneer yatashi da gudu yaje yana masa oyoyo. Rik'e hanunsa yayi kawai amma yakasa magana, saima wata uwar harara daya zubama su hajia Hindu itada yaran, “yanacan yana wahala su sunanan hankalinsu kwance”, dan duk sunwani zubo masa idanune amma babu Wanda yace masa koda sannu.
Tsaki yaja yana sakin hannun Muneer yashige abinsa. Hajia Hindu ta ta6e baki tana d'auke kanta. Shima Hussain bakin yad'an ta6e kafin yace, “Wai Mom mi akaima Dady ne daga dawowarsa?”.
“Ina Zan sani Hussain, ai tare muke daku anan ya shigo”.
Dariya Kalifa yayi yana fad'in, “ku nifa kwana biyunan gani nake kamar Dady a rikice yake, kokuma rud'un tsufane oho”.
Dariya suka sanya gaba d'aya, Hajia Hindu ta mik'e tana, “Kai yaranan ALLAH ya shiryeku, kodai tsohonne ma ai ubankune dai, bara naje naji mike faruwa”.

Kwance ta iske Abba hannunsa dafe da kansa, zama tayi gefen gadon kusa dashi, “Abban kalifa lafiya kuwa?”.
Banza yay mata tamkar baimajiba, saida ta maimaita sau uku kafin ya janye hannunsa ya kalleta da idanunsa dake jajur, sai dai yagaza cemata uffan.
Hakanne yad'an tada hankalinta, takuma maimaita masa tambayar.
Mik'ewa yay zaune yanajan guntun tsaki, “Yanzu nan Hindu na d'auki tsawon kwana shiddah bana gidannan, amma nadawo kuna kallona tamkar wani kashi, wane iron rainine wannan?”.
cikin kwantar da murya ta kallesa, dan zatonta koya samo kud'inne, shiyyasa ta aro sabon ladabi, “Ohni Hindu, yanzunan Abban kalifa wace irin maganace wannan dan ALLAH? To kayi hak'uri, wlhy mamakin yanda kashigone yasanyamu yin hakan, yaya Abuja? Ina fatan dai andace da samun kud'ad'en?”.
Jin yanda ta kwantar da murya sai Abba ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta “Bansan yanda zanyiba Hindu, ina cikin tsaka mai wuya, kud'in danaje nema ban samoba, dolene a darenan naje na turke Y'ar iskar yarinyarcan yaronan ya saketa, nasan inhar Alhaji garba yaga zata dawo gareshi zai hak'ura ya barni”.
“Hummm Alhaji kenan, to ai daga baya kenan wannan, komafa miye ya faru laifinkane, Kaine ka 6ata komai a randa Alhaji garba ya kiraka, sannan nabaka shawarar musanya masa da Zarah, amma sai kak'i saurarena, to ai yanzu bakada hurumin rabama Jiddah aure kuwa balle bashi ita, dan ta tare tunma shekaran jiy.....”
A zabure ya mik'e, “k ban fahimcekiba? Ni da raina za'akai y'ata gidan miji ban saniba?”.
Baki hajia Hindu ta ta6e tana masa wani kallon rainin wayo, balle taji babu kud'in, “Oh kajimin Abban kalifa fa, yo yaune karan farko da aka Fara Kai y'ay'an naka gidan aure bada saninka ba? Naga ko hannatu sai dama tayi wajen wata biyu da aure ka sani, Zulai kuwama saida takusan haihuwa .
Hannu yakai tamkar zai maketa saikuma ya fasa, ya bangajeta ya wuce zuwa bayi. Bayansa ta raka da harara tana k'ya6e baki, saima ta fice abinta kawai tabar masa d'akin.


('('('('('('('('('('('

Kamar da wasa k'aramar magana saita zama babba, dan tsawon kwana uku Alhaji garba ya gagari hajia deluwa sakawa a ido, tunda ya shige sashen amarya a randa aka kawota bai sake ko lek'o wajeba, sallama agida yakeyi, abinci kuwa bashida Matsala, dan amarya ke musu daddad'en girki, cikin k'awayenta takira tabada umarnin ayo musu cefane mai yawa, wannan yasa suka kuma yima hajia deluwa nisa, sai dai tajiyo sautin kid'a Na tashi, knocking kuwa tayi har hannunta ya gajiya, tayi wujiga-wijiga da ita, nutsuwa ta gagareta, takira malam Na marwa yafi sau dubu amma wayar yak'i shiga, komai saiya kuma harmutse Mata. Su Kansu su Ashir sunma kasa gane kanta kwata-kwata, gefe kuma su hajia Hindu k'awayenta na kuma tunzurata a waya.

Aiki ya samu mata>Ø#Ý

('('('('('('('('('('('

Sai wajen sha d'aya Jiddah ta farka, ta tashi kuma bata samu Sheikh Aliy a d'akinba, hakanne ya sata d'anjin dad'i, yunk'urawa tayi zaune da k'yar, dan jikinta duk ciwo yake Mata, ji kawai tayi hawaye suna zirara Mata, yanzu nan wannan abunne har kesa mace yin zina?, miye abin dad'i anan banda bak'ar wahala? Wai a hakanma shi bawani gama shigarta yay gaba d'aya ba kamar yanda yafad'a, tayi kusan zaman minti talatin tana hawayenta, Wanda dalilinsu yafi k'arfi a kewarsu Ummanta, sakkowa tayi a gadon zuwa bayi, tasamu takumayin tsarki da ruwan zafi tayi wanka, lokacin walha ya wuce, hakan Yakuma sakata takaici.
Saida ta shirya sannan ta gyara d'akin tasaka turaren wuta, takardar data gani saman mirror ta d'auka ta karanta.

_Ina fatan tashinki cikin aminci da farinciki Aglan Nisaa (Mafi tsadar mace) amin afuwa na fita saboda wani uziri, ga abinci nan a falo auntynki ta kawo miki, Ku yini cikin aminci da kariyar ubangiji matana._

Guntun murmushi tayi tana had'iye hawayen da suka cika idonta, ta linke takardar ta ajiye sannan tafito. A falo ta iske abincin karin kumallonta daya ce, bata cutama kantaba ta zauna taci dai-dai iyawa tasha maganin daya ajiye Mata. Tanason zuwa ta duba Maimuna amma tanajin kunyar tafiyarta, haka ta zauna shiru harma takai da kwanciya cikin kujera ta fad'a duniyar tunani.
A wannan yanayin su Walida suka iso suka sameta, wani farin ciki Na musamman ya kamata, ta tashi cikin hanzari domin tararsu, sai dai taku biyu tayi tatsaya cak saboda kallon dataga sun tsaya sunama k'afafunta.
Aunty Hannatu dayake tanada hankali saita basar dasu ta hanyar zuwa ta rungume Jiddah.
Jiddah tad'an sauke ajiyar zuciya dan a ganinta k'ila basu fahimci abinda take zarginba.
Kayan hannunsu suka ajiye suma sauran sukazo suka rungumeta, kafin su saketa su kuma fita kwaso sauran kayan.

Maimuna dataji hayaniya ta fito, dan dama tun d'azun take d'an zagayo Jiddah taga kota tashi, Aliyu yace Mata kanta ke ciwo, dukda zuciyarta ta sosu da tunanin wani Abu daban hakan bai hanata lek'owa taga kota tashiba.
Da fara'arta takemusu sannu dazuwa. Suma suna amsawa fuskarsu d'auke da Fara'a, koda tace zata tayasu d'aukar kayan sai Balu ta hanata, dukda haka saida ta amshi agogon dake wajen Aunty Zulai suka k'arasa falon Jiddah.
Jiddah Na ganinta tai k'asa da kanta tana wasa da yatsun hannunta, dan ita gani take kamar Maimunatun tasan abinda sukayi a daren jiya.
“Ashe kin tashi K'anwata, tun d'azun nake zagayenki amma saina iske kina barci”.
Batare da Jiddah ta kalletaba tace, “eh wlhy aunty, maganin murar Dana Shane yasani barci”.
“Dama yace kanki ke ciwo, yanzu dai ya daina ko?”.
“Eh ya daina Alhmdllh”.
“To ALLAH ya k'ara afuwa, sannu”.
“Yauwa aunty, kema yanaki jikin?”.
“Alhmdllh”.
Su Balu ma duk sukaima Maimuna ya jiki bayan ta zauna sun kuma gaisawa cikin mutunta juna, mik'ewa tayi ta fita itada Walida data kira.
Suna fita aunty Hannatu tace, “Wlhy Jiddah kin more da abokiyar zama ba irin namuba da kullum fitina bata k'arewa, dan ALLAH kema ki kwantar da hankalinki Ku zauna lafiya, nasan kishi abune mai zafi, amma inka had'a da hak'uri sai ALLAH ya sauk'ak'a maka, ita kanta nasan tanajin zafi, amma take dannewa saboda tasan mutuncin kanta”.
Kan Jiddah a k'asa tace, “Insha ALLAHU aunty zan kiyaye, kumani wlhy bana wanijin haushinta, dan tanada kirki”.
Dariya sukayi, Aunty Zulai tace, “Zakijine Jiddah, har yanzu akwai saurankine, bakigama tantance abinda akema kishinbane ba, babu macen da zatace bata kishin mijinta ai”.
Balu zatayi magana su Maimuna sukayi sallama, hakanne ya sakasu barin maganar, ruwane ta kawo musu sai zo6o data dafa d'azun da safe da Aliyu yace yanaso, saita had'a musu shi yanzu takawo musu, akan shid'in saita data masa wani kafin ya dawo.
Sallamar su Yaruwaiya ce ta karad'e gidan, Maimuna talek'a tana amsawa, suma cikin fara'a take musu sannu da zuwa, suma suna amsawa cikin mutuntawa da sakin fuska.
Sun shigo da tarkacen da aka k'arasa sayama Jiddah dakuma freight d'inta madaidaici ruwan toka.
Sannu sukayiyyi musu sannan sukai gaisuwa da Maimuna tafita domin nema musu d'an abinci mai sauk'i.
Zarah da bakinta baya iya shiru ta kalli Jiddah tana fad'in “yaya Jiddah mi akayi miki? Dan dagani kuka kikayi amma? Idonki duksun kumbura fa”.
Rasa amsar da Jiddah zata bata tayi, kafin kuma wani ya bata amsa cikin manyan takuma d'auki kwalin maganin da Jiddah tasha na rage rad'ad'i da ciwon jiki tana dubawa, tad'ago zata kuma jeho wata tambayar Aunty Saudah ta dakatar da ita, “K akku ya isa haka da ALLAH, batajin dad'ine ko dole saikinji mike damun Nata?”.
“Yi hak'uri aunty Saudah, nifa kawai dana ganta wani irine, sainake ganin ko wani abu wani yamata, kinsan mai kishiya, gakuma hardasu maganin ciwon jiki, yaya Jiddahr ce tacika sanyi, naga kuma kishiyar nan tata akwai shegen way...”
Kulli Yaruwaiya tayimata a baya, “Zarah ki iya bakinki, banason maganar banza fa, irinkune dangin dake had'a fitina a gidajan y'an uwanku idan sunada abokiyar zama, wlhy koda wasa karna sakejin wannan banzar maganar akan abokiyar zamanta”.
Kai Zarah ta d'aga tana tura baki da shafa inda Yaruwaiya ta doketa, su aunty Saudah ma duk fad'a sukai Mata akan hakan da nuna Mata rashin k'yautawa.
Walida tace, “Wlhy matarnan tanama da kirki, wace macece za'aima kishiya a wannan zamanin ta iya dannewa ta kwar6i kishiyar da danginta kamar haka?”.
“Wlhy gaskiyarki Walida, aike kinfi Zarah hankali”.
“To maganar ta isa hakanan, a canja da wata kuma”.

Daga nan suka saki maganar suka koma wata daban, sunayi suna bud'e kayan, wasu na gyagygyarasu inda ya dace. Hakanne yasaka Jiddah d'an sakin jikinta, amma tak'i yarda ta tashi ko nan da can.
Kusan awa d'aya saiga Maimuna da kular abinci babba da zata iya d'aukar abincin dazai wadatar dasu, duk sukai Mata sannu da godiya.
Murmushi kawai tayi, dan hankalinta yakwanta dasu, yanda suke girmamata, dukda yawanci duk san girmeta, Zarah ce kawai takula kamar bata sakin jiki da ita sosai, amma hakan bai dametaba dan k'aramar yarinya take kallonta, kuma baizama dole dama kowa ace kamasaba.
Bayan fitarta sukayi haramar sallah, yayinda akabar wasu a kicin suna k'arasa gyarawa.
Aunty Saudah ta kalli Jiddah tana fad'in “Wane d'aki kuke kwana Jiddah?”..
Da hannu ta nuna mata kamar zata nutse dan kunya.
“A to bara muyi amfani da wannan mu kenan, wancan yazama Na k'aninmu ai”. ‘cewar Aunty Nafisa’.
Dariya sukayi irinta shak'iyanci suka shige. Jiddah k'in tashi tayi saida taga sun shige, su Zarah kuma hankalinsu na a kicin sannan ta lalla6a d'ayan d'akin domin yin salla.

Bayan an idar da sallah Aliyu ya shigo gidan, saida yafara shiga sashen Maimunatu sannan, itace take sanar masa zuwan y'an uwan jiddahr.
Hakanne yasashi zuwa dansu gaisa, amma saiya iske falon shiru, sai maganganunsu da yake jiyowa a kicin da d'ayan d'akin, kamar zai koma da baya saikuma ya nufi d'ayan d'akin da Jiddah take, a nufinsa saiya kirata a waya dan zatonsa tana kicin ko d'ayan d'akin da yakejin firarsu.
Jiddah dake canja kaya duk zatonta Zarah ce ko walida, batareda ta juyoba tace,  Zarah zoki jamin zip d'inan sama .
Murmushi Aliyu dake tsaye yana kallonta yayi, yatako a hankali zuwa gareta................
'<Øûß



_Naga kuna Neman shiga rud'ani akan buk d'in da kuka gani jiya, wancan sunansa *WUTSIYAR RAK'UMI...* Na kud'ine da zamuyi Na k'ungiya, so dukmai buk'ata zai sayane, guda biyarne muka fitar, pages na jiya kuma d'and'anone=Ø Þ, ciwon Kai ya hanani yimuku typing jiya>Ø&Ý<Øûß
@&_.



*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*>ØÝ<Øýß>ØÝ<Øýß>ØÝ<Øýß



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*=Ø-Þ=ØOÞ<Øûß
[12/25/2019, 1:59 PM] =ØžÜNoorunnisa=ØžÜ: *_Typing=ØòÜ_*



*_=Ø¡ÜHASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=اÜMUTUM DA DUNIYARSA....!!=اÜ_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>ØÝ<Øûß_*

*_[51–'52]_*


............Duk yanda yaso daurewa karta fahimci shine yakasa, maimakon ya zuge mata zip Win tamkar yanda ta bu™ata saiya Sige da tura hannayensa cikin rigar ya zagayo dasu saman cikinta.
Ba™aramar firgita Jiddah tayiba, tanemi juyowa a razane yay azamar Wora kansa saman kafaWarta yana faWin,  Afuwa hajjaju nine ba Zarah ba .
Kasa motsin kirki Jiddah tayi, sai jikintane ke mazarin tsumar tsoro, muryarta na rawa tace,  Sannu da dawowa .
 Yauwa amarsun Aliy, yaya jikin dai? .
Shiru tai ta kasa amsawa, gaba Waya tagama takura, gefen zuciyarta kam addu'a take ALLAH yasa kar cikinsu Walida wani ya shigo, ita abindama bata fayimtaba inasu Aunty Nafisa suke? Harya shigo nan....... Firgita tayi tana Saurin dafe hannunsa dake neman canja salon yawo a rigarta, cikin sar™ewar murya da matu™ar in ina tace,
 Su..su..s..u aunty Sau..dah sun.. zo fa .
Dariyar dake nemen kufce masa ya danne da ™yar, dama yayi mata hakane dan tayi magana. Fuskarsa Wauke da shinfiWaWWen murmushi ya cire hannunsa yana juyo da ita. Kasa kallonsa tayi, hannunsa yasaka ya Wago haSarta yana faWin,  Tun randa na fara ganin wannan fuskar na fahimci matsoraciya ce ke kam .
Murmushin da bata shirya yibane ya kufce mata, tasaka hannayenta ta rufe fuskarta. Yanzun kam saida ya dara, ya jawota jikinsa yasaka mata zip Win.
Komawa yay ya zauna a bakin gadon yana kallonta tana ta wani sinne kai, aransa kam dariyar yanda taketa kare ™irjinta yakeyi da faWin mata kenan, hakafa Maimunatu taita masa, amma kwanaki naja tana kuma sakin jikinta dashi, yasan itama Jiddahn zata koma dai-dai ne, duk macen kirki dolene asameta da wannan kunyar, danshi baiga birgewaba ga ´ammatan yanzun da idanunsu ke a soye, watama Wan kukannan idan za'a kaita gidan miji batayi, ™agarama take atafi, suna Waukar hakan wayewane basusan zubar da kimarsu suke ta Wiya maceba, koshi mijin sai dai ya™i faWa maki amma saiyaji baki birgeshiba kwata-kwata, duk son wayayyar mace da wasu mazan keyi sunason koyaya taWan ringa kunyarnan a gabansu, domin kunya ita kanta jan ajine ga Wiya mata, kuma alamune na kin kwankwaWi tarbiyyane a gidanku, danshi abinda yake kallon mace mara kunya *BALLAGAZACE* kawai mara isashshiyar tarbiyya. Numfashi yaWan sauke yana kallon jiddah dake tattare kayan data cire, amma koda wasa ta™i duban sashen da yake.  Juddatulkhair muje na gaida su auntyn namu naje naWan kwanta na huta kafin lokacin sallah ko .
Kanta ta jinjina masa tana ajiye kayan hannunta, cikin sanyinta tace,  To .
Harta kama hanyar fita yace,  Zonan na tambayekima .
Dawowa tayi da baya, zata dur™usa ™asa ya kamo hannunta yana faWin,  Zauna anan . Ya nuna mata bakin gado kusa dashi.
Bata musaba ta zauna, kanta a ™asa tana wasa da yatsun hannunta.
 Kinsan mizan tambayeki? .
 A'a .
Murmushi yayi mai sauti yana kuma maida hankalinsa gareta,  Wai kinsan sunanama kuwa? .
A mugun bazata tambayar tasa tazo mata, dan haka ta Wago kai tana kallonsa cikin waro idanu.
Babu shiri shima dariya ta kufce masa, mi™ewa yay tsaye yana cewa,  Dama sonake naga idonki kuma nagani, tashi muje ki rakani .
Jitai tamkar zata nutse dan kunya, wlhy rayuwar bawan ALLAHn nan tana matu™ar burgeta, tarigada ta taso Abbansu banda jaraba babu abinda ya iyayima Umma, idan sunga fira tsakanin mata da miji cikin aminci to sai dai idan gidan Uncle yahya sukaje, amma a gidansu dai a'a, itafa zatama iya lissafa dariyar Abba data gani a rayuwarta, wannan yasaka duk abinda Aliyu yay mata sai take ganinshi tamkar wani mijin novels ko film=ØÞ.

Fita tafarayi falon ta barsa a Wakin, su aunty Hannatu na zaune sunacin abinci, yayinda su Balu ke Waki suna salla sukuma.
Yanda taketa wani nu™u-nu™u da sissinkuyar dakai ne yasakasu zuba mata idanu.
 Lafiya kuwa Jiddodo?  Aunty Zulai tai maganar .
Kuma ™asa tayi da kanta kafin tace,  Aunty wai dama shine zaku gaisa .
Harsun fara dariya saikuma kowacce ta rufe bakinta da hannu saboda harar da Aunty Saudah ta zuba musu dukda itama danne tata dariyar take, yanda Jiddah tayi maganarne dole tabaka dariya.
 Wlhy Jiddah yanda kikasan ´ar da haka kike, bakisan sunansa baneba? .
Murmushi tayi kanta a ™asa,  toni aunty bansan yanda zance muku ku ganeba .
Cikin tsokana Aunty Nafisa tace,  Sai kice auntys Hubbiy zaizo ku gaisa .
Ido jiddah ta zaro saikuma ta narke fuska,  kai Aunty Nafi wlhy nidai babu ruwana .
Yanzukam kasa daurewa sukayi, saida sukaWan dara kaWan.
Yaruwaiya tace,  To Wan nawa yana ina? .
Da hannu jiddah ta nuna Wakin data fito.
 K jiddah wai kina nufin yana ciki? .
Kai ta Wagama aunty hannatu mai maganar.
Hannu sukasa suna dafe bakuna, Aunty Sauda tace,  Wai kina nufin dama tun Wazun yana nan? .
Cikin son tsokanarsu Jiddah tace,  eh mana .
Babu wanda bai rikiceba dukansu, Maman Sadiq ta zubama Jiddah da™™uwa tana faWin,  Jiddah kinci gidanku, shine dan iya shege kika barmu muketa zuba da sakin magana .
Dariya jiddah keyi, saikuma tarufe bakinta da hannu tace,  Wasafa nakeyi, wlhy yanzu yashigo kuna Waki kuna sallah, su Zarah kuma suna kicin .
Babu wanda bai sauke ajiyar zuciyaba a cikinsu, yayinda aunty Nafisa ke faWin,  ALLAH kafin nabar gidanan saikinci gidanku jiddah .
Nanma dariyar Jiddah tayi tanama aunty Nafisa gwalo.

Shiekh Aliyu dake Waki duk yana jiyosu, murmushi yay yana mamakin dama tana magana haka, da sai yaga kamar tafishi shiru-shiru, amma yaukam dayaji bakinta saiya kuma tabbatar da kunyace kawai da rashin sabo dasu.
Šakin ta shigo da sallama, ya Wago idanu yana kallonta da amsa mata.
 Na faWa musu zakaje ku gaisa .
 Wakikace musu zaizo? .
 Kai mana .
 Niwa? .
Shiru tayi dan an ™ureta kuma.
 Shiyyasa nace bakisan sunanaba ai madam, muje kirakani to .
Kafinma yakai ™arshen maganar harta kai ™ofa, dan batason yazo yacim mata.

Tunkan su fito dama sun kimtsa, Aliyu ya zauna saman kujerar farko idan kafito daga bedroom Winsu, fuskarsa shimfiWe da murmushi yana musu sannu da zuwa.
Duk suka amsa masa cikeda girmamawa, yau gasu ga babban malamin da sukeji a redio da tv a gabansu, matsayin mijin ´ar uwarsu.
Sun gaisa cikin mutunta juna, sunata kuma mamakin sau™in kai irinna Aliyu, har yana tsokanar yaron Aunty Hannatu wanda dashi kaWai akazo dan ™aramine sosai.
Suma su Zarah sun fito suka gaisa dashi, yace,  Walida kece ´ar zaman Waki ko? .
Dariya tayi tana faWin  A'a malam, ai Umma bazata yardaba .
 Aini sainaje na ro™eta tabamu ke auta. Idan kuma auta batason nesa da Umma sai

1 Comments On MUTUM DA DUNIYARSA
avatar
rukayya-yahuza

1 year ago

Reply

Kai book dinnan ya hadu iya haduwa

Please Login or Register in order to submit comment