Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai shi malam dayasan yanayin d'ansa tuni ya hango farin ciki tattare dashi.

&&&&&

A ranar da yamma kayan gadon Jiddah suka iso, kayane masu k'yau da tsari dakuma tsada gwargwadon k'arfin Uncle yahya, kowa yagani saiya yaba, saidai idan mak'iyi kuwa.
Ganinfa abin da gaskene sai jikin Jiddah yakuma sanyi, ga Yaruwaiya tadage sosai take kuma gyarata da tsumata a k'amshi.
Sheikh Aliyu yana kiran Jiddah su gaisa, yakuma bata hak'uri akan bazai samu sake shigowaba, dan yayi busy da yawa, ga shirin tarewarta ga walimar musabik'ar dataje Saudia wadda malam yace za'a had'a data aurensu.
Ita hakanma sai yay Mata dad'i, dan dama batason yazo yaga taji ciwonan Na hannunta, sannanma dai tafison su zauna nesa-nesan, shiyyasa jitake inama su Umma zasu yarda a kuma d'aga tariyar. Daka ganta kasan tana tare da damuwa, datasamu ke6ewa ita kad'ai sai kuka, ita kanta Umma dauriya kawai takeyi, su Zarah kam duk sunyi wani sukuku dasu suma, kewar Y'ar uwarsu Na matsuk'ar damunsu.

Washe gari aunty zulai dasu Aunty Saudah, hannatu suka iso, dan haka aka rankaya gidan Aliyu yoma Jiddah Jere.
Tarba ta mutunci suka samu dagasu aunty Ruk'ayya da Maimunatu, dan bazama kata6a cewa itace kishiryar Jiddanba, yanda taketa hidima dasu abun gwanin birgewa.
Dukda gidan Alhaji garba yafi Na Aliyu komai hakan bai hana gidan Aliyu k'ayatar dasuba, dan ba arzik'in bane abin birgewa kawai, zaman kafiya da kwanciyar hankali shine abun buk'ata ga kowacce d'iya mace.
Tsarin gidan babu ruwan kowa da kowa, dan kowacce kamar 6angarenta daban zamuce, sai dai bawani k'atun k'atunbafa, dan bawani katafaren gida baneba, yanada dai girmansa gwargwadon hali, kuma tsarin yayi, iri d'ayane da sashen Maimuna, babu wani banbanci saina kayan d'aki, komai Na Jiddah pink and White ne, iya gwargwadon iko dolene a yabama Uncle yahya, kayan gadonta d'aki biyun duk aka zuba, kicinma kam Alhamdllh, saidai mak'iyi. Dayake sunada yawa dandanan suka gama, dan zuwa magriba sun dawo gida, sunata zuzuta tsarin gidan, sun nunama Umma video recording d'in da sukayo, itama sosai ta yaba, dad'i kuma ya kamata, dan yanzune hankalinta ya kwanta da auren d'iyarta.
Koda suka nunama Jiddah k'in kalla tayi, saima ta fashe musu da kuka.
Aiko dariya suka sanya Mata, ganin da gaske takeyi duk sai jikinsu kuma yay saniyi suka shiga rarrashinta.

Washe garifa dangi suka Fara sauka, zuwa yamma gida yayi taf, dangin Umma danasu Abba, kamar taron farko wannan karonma sai rabuwa sukayi saboda gidan Umma yamusu kad'an.
A ranar da yamma kuma aka kawo lefen Juddatulkhair daga angonta Sheikh Aliyu maina, suma ammusu tarba ta girma da mutuntawa, kuma kowa ya yaba da lefen Masha ALLAH, dan saidai mak'iyi kam, abin tamkar bana bazawara ba.
Jiddah dai ko tarinta bakaji a gidan, koda su aunty siyama suka buk'aci ganinta k'in yarda tayi, dole suka hak'ura suna fad'in ai dai gobe iyanzu takusa shiga gidansu.


('('('('('('('('('('('

A yayinda ake shagalin tarewar Jiddah kuma shima Alhaji garba yanacan yana shagalin tarewa da sabuwar amaryarsa da aka d'aura aure yau hajia deluwa bata saniba, sai wajen tashin hantsi taga anzo ana kwashe kayan 6angaren Jiddah, dariya tayi sosai tana fad'in Badole ka kwasheba, da kabarsu su shekara dan itadai tatafi kenan har Abadan.
A wajen kwasar kaya masu kwasar sukaci Karo da abinda Hajia deluwa ta sakama Jiddah. Basuyi k'asa a gwiwa ba suka Kira Alhaji garba suka shaida masa..
Mamakine ya kamashi, babu jimawa yadawo gida bayan an d'aura aure, kai kawai yake iya jinjinawa saboda takaici, ko tantama bayayi wannan aikin deluwa ne, wato wannan shine yasaka Jiddah haukacewa idan tagansa, shine kuma yasatake masa wari?. Sakasu yayi suka k'ona, itakuma bai Mata maganaba dan yanzu bashida lokacinta, ta amaryarsa yakeyi wadda takasance gogaggiyar Y'ar bariki, dan hajia bariki ma ake kiranta, tafi hajia deluwa komai, idanma kud'ine itama ta Tara, tadad'e tana nunama Alhaji garba so amma yana shareta, hajia deluwa kuwa sosai ta tashi hankalinta lokacin dataji hajia Rahina bariki Na sonsa, dan shige-shigen malamai taitayi dan kar hajia rahina tashiga zuciyar Alhaji garba.
To a yanzu kuma gashi tashigo batareda ta saniba, ko wane irin zama za'ayi=9 kuma=F



('('('('('('('('('('('

Jiddah datasha kuka zazza6i ya rufeta ta kwanta, duk hayaniyar ganin lefe da y'an biki sukeyi sama-sama takejinsu saboda barci dake fusgarta, zuwa wani lokaci barcin yay awon gaba da ita gaba d'aya.
Cikin barci tafara mafarki mai ban tsoro, kafin daga bisani tasamu k'arfi akan Wanda suketa dambe a mafarkin, a fili kuwa tajik'e sharkaf da zufa, ga mazari da jikinta kemata.
Fannah data shigo domain gwargwad'a Mata lefe da kayan arzik'in da ya sheikh ya zuba ta isketa a wannan hali, jijjiga Jiddah tafarayi tana kiran sunanta, ihunta shine yajawo hankalin mutane sukayo d'akin.
Da k'yar aka samu Jiddah ta farka, amma saita Fara wani fisge-fisge da gurnani cikin wahaltuwa, numfashima dak'yar take fisgarsa, daga k'arshema saita sank'ame alamar ta suma.
Ummace ALLAH yabama k'arfin zuciyar d'akko magungunan Jiddah da sheikh Aliyu ke bata har yanzu ta zuba turare a rushi, yayinda Maman Sadiq keta shafama Jiddah ruwan addu'oin a fuska.
K'ara ta k'walla kafin tafara rawar jiki da zufar dake cigaba da kwararo Mata, bayan kamar mintuna uku saita koma tayi lakwas tamkar ba itaba, saikuma hawaye dake kwarara Mata a fuska. Daga baya kuma barci ya sake kwasheta.
Uncle yahya da aka Kira a waya ya k'araso, Koda sukai masa bayani sai sukaga ya d'aga hannu sama yana fad'in Alhamdullahi, ALLAH mungode maka dakabama yarinyarnan lafiya, ALLAH yasa iyakar wahalar kenan.
Tambayarsa suka shigayi, nanfa yaymusu bayanin insha ALLAH Jiddah tasamu lafiya daga lalurarta.
Kowa murna yashigayi, saidai Umma Na mamakin ya akayi haka cikin sauk'i? Kodai Uncle yahya ya d'auki wani matakine basu saniba?. Ganin babu mai bata amsa yasa ta hak'ura, tasan idan komai ya lafa zai Mata bayani.
Da wannan aka cigaba da shagali.


('('('('('('('('('('('


Dukda Busy da Aliyu yayi haka yasamu ya nemi Jiddah a waya saboda duk yau basu gaisaba, amma saima yaji wayar switch up, dole ya hak'ura dan yasan gobe iwar haka insha ALLAHU tana gefensa.

Baiwar ALLAH Maimunatu, duk yanda kaso gano halin datake a ciki baka isaba, dan ta danne zuciyarta sosai, yayinda kulawa da tattalin da mijinta ke bata ya danne kaso mai yawan gaske Na damuwarta.
Harkokinta taketayi, danma laulayi yana takura Mata sosai, batajin dad'in jikinta, dauriya kawai takeyi.
Yauma gaba d'aya da daddare bayan yadawo nasiha yayta Mata da lallashinta cikin kalamai masu sanyi da saka zuciya nutsuwa. Hakanne yasakata itama bashi dukkan farin ciki batareda ta d'auki fushi Na tunanin gobe iyanzu yana tare da amaryarsa ba.


('('('('('('('('('('('.

Washe gari Jiddah ta tashi garau da ita, wannan Yakuma tabbatarma dasu Umma lallai an dace kam. Yau tunda aka tashi da gyaran jikin Jiddah aka fara, dan sunayin sallar asubahi aka Fara zuba Mata kunshi da kitson Bare-bari d'an asalai (barbarawa=9>-&
@&), tayi k'yau harta gaji.
Sai dai daka ganta kasan batada sukuni, magana kad'an za'ai Mata ta6are baki tana kuka.
Y'an uwama saisuka koma tsokanarta, musamman abokan wasa, saisu Aunty Sauda ne ke kareta.

('('('('('('('('('('('

Abba dai duk wannan hidimar da akeyi baya gari, dan tun Randa aka fiddo kalifa daga station suna dawowa yahad'a kaya zuwa Abuja wajen wani Alhaji Sammani Moddibo, abokinsane amma yanzu ya haye dan d'an majalisane a Adamawa, Da Abba yabuga tunaninsa yagama yaga babu wajen mafaka, danya Kira Mijin y'arsa Sauda danya ranta masa kud'i ALLAH ya tak'aita wahala Sauda ta d'aga sannan wayar na agunta, saida yagama fad'ar buk'atarsa sannan tace masa To Abba ai nice, Ashe dama y'a mace nada amfani da Rana? Ai nazata bazakama ta6a tunamu a cikin y'ay'ankaba balle kabiyo mazajenmu da buk'ata. Batajira cewarsaba ta yanke wayar taredayin blocking d'insama gaba d'aya, shinefa takira Uncle Yahya da Umma ta sanar musu.
Wannan Abu da Sauda taimasa ba k'aramin Sosa masa zuciya yayiba, dan haka yashiga tsinarta yana had'a kaya, aranar yawuce Abuja.
Harkuma yau da Jiddah zata tare bai dawoba, ya iske Alhaji Sammani bayanan, amma saiya zauna jiransa saiya dawo, dan ance tafiayar kwana biyar zaiyi, to aganinsa dayayi wahala biyu bai dawoba ai gara ya zauna ya jirasa kawai, yama huta da bala'oin daya baro a cikin kano.
Auren Jiddah kuwa yana komawa yabiya Alhaji garba kud'insa saiya tsinkashi, danyayi alk'awarin tunda Yaruwaiya taci zarafinsa gaban y'ay'ansa saiya huce akan Umma, sannan saiya shukama Uncle yahya rashin mutuncin da ko'a hanya bazai sake nunashi a matsayin d'an uwansaba.


>&<
@&Anna ha[s| aa|[ aahsfh|?.


('('('('('('('('('('('


*_11:00pm_*

Harabar makarantar su Jiddah tagama cika taf, bakajin komai sai k'ira'ar alkur'ani mai girma, tarone daya tara manyan bak'i daga yankunan arewaci da kudanci.
Dan taron an shiryashine da manufa biyu, Na murnar nasara da Nageria tayi a gasar diniya, dakuma murnar taya hazik'in malami Sheikh Aliyu da Amaryarsa Jiddah tauraruwa a daular musulinci.
Jiddah na sanye cikin k'yak'yk'yawar sutura, ko ina Nata a rufe ruf, ko tafin hannunta da k'afa baka gani, fuskarta kam tamkar kullum tana lullu6e da nik'ab, sai sirrin k'amshi mai sanyi take fitarwa.
Madina ce a kusa da ita sai sauran d'aliban ajinsu.
Ahakanma hawaye taketayi, dukda ayau tanajinta wani sakayau tamkar an sauke Mata kaya, ko kad'an batajin komai game da maza.........
Sassanyar muryarsa data farajan k'ira'ar alkur'ani cikin suratul Bak'ara ce ta katse tunaninta, cikin fad'uwar gaba da bugawar zuciyarta sauri-sauri ta d'ago ta kalli saitin inda muryar ke fitowa.
Zaune yake a cikin kujera 1Seat, hannunsa rik'eda microphone, yana cikin shadda wagambari kalar sararin samaniya (skyblue) harda babbar riga, hularsa da takalmansa ma duk kalar shaddar saidai su masu duhune, babu abinda ke fita tattare dashi sai wani annuri Na kwanciyar hankali, yayi wani fresh dashi alamun komai yana tafiya masa dai-dai. Yau shine Rana tafarko data samu zarafin masa kallon tsaf, Masha ALLAH gwargwado Sheikh Aliyu maina yanada k'yansa, Abu mafi k'awata taswurar kamilalliyar fuskarta shine tambarin salla dan6arere dake a goshinsa, sai sajensa zuwa gemu daya kuma fidda sirrin nagartarsa da cikar kamala musamman dayasha gyaran fuska da aski a yau. Harya gama karatun yafara Addu'a Jiddah batasan anayiba, saida aka kirayi sunanta sannan Madina ta zungureta ganin batai ko motsiba.
Babu shiri tadawo hayyacinta kafin tamik'e bisa taimakon Madina. Itace taimata rakkiya har inda ake buk'atar ganinta.
Tunda aka Fara shelanta sunanta yake baza Ido yaga ta ina zata 6ullo ne? Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke daya ganta tamkar yanda yay fata, danshi mutumne shi mai kishi sosai, dan taronnan da farko k'ok'arin hanata zuwa wajen yayi, kasancewarsa komansa yakan nema shawarar malam kafin ya aiwatar saiyaje ya sanar masa. Malamne ya lallashesa akan yabarta taje yaudai d'aya, kodan manyan mutane dazasu halarci taron, dan kowa zaiso ganin wannan gwana data samo mana nasara. Da wannan malam yaci k'arfin sheikh Aliy.........
Bai ankaraba yajiyo zazzak'ar muryarta na jawo ayoyi cikin kwarewar larabci da takatsantsan. Lumshe idanunsa yayi bugun zuciyarsa Na k'aruwa. Wajen yayi tsitt bakajin komai sai ajiyar zuciyar jama'a.
Tuni muryar Jiddah ta karye alamun kuka takeyi, wad'anda sukasan hali su malam Abdul'ra'uff dama sunsan za'a rina, tuni ta karya zuciyar jama'ar wajen, wasu sai sharce yawaye sukeyi.
Saida takai har k'arshen suratul Al-Anbiyaa kafin a dakatar da ita. Wajen zamanta takoma itada madina, dad'i yasaka Umma share hawayen da suka wanke fuskarta, itakam kullu yaumin tana alfahari da haihuwar y'ay'a Mata, babu abinda zatacema Ubangiji saidai godiya.
An fara gudanar da abinda ya tara mutane, Wanda dukkan manya sun yabama Jiddah dajan Addu'ar fatan alkairi dazaman lafiya nahar abada itada gwarzon mijinta tauraron duniyar musulunci, duk kuma k'yautar data samu shike zuwa ya kar6a Mata. Mutane sai k'usk'us suke akan hakan, yayinda y'ammata irinsu Tawan (Miss Xoxo==) suketa k'yasawa, jisuke inama sune sukeda wannan Hafizin masani a gidauniyar addinin islama.
Sak'on jawabi daya kamata Jiddah tayi Na godiya shine yakar6a microphone yayi a maimakonta. Dan yayi alk'awarin babu mai sake jimasa muryar mata gaskiya, karatunma datayi jiyay tamkar yaje ya hanata, da k'yar ya iya tausar zuciyarsa harta gama, shiyyasa yaturama malam mustafa massage akan karsu sake kiran Jiddar, duk abinda ake buk'atar tayi akirashi a maimaikonta.
Murmushi malam mustafa yayi, dan yasan wanene Aliyu akan kishi. Dan haka yabi dokarsa, komai za'a buk'aci ganin Jiddah saiya Kira Aliyun.
Bayan andawo salar zuhur malamai suka fara gudanar da lecture mai taken *_GIDAN AURENMU_*, wadda dai anyitane ta musamman domin ango da amarya.
Jiddah dai Tasha kuka acikin Nik'ab harma kanta namata ciwo.

Gab da la'asar aka tashi, bayan Jiddah tayi gaisuwa da mutane da hotuna tasamu ta sulale batareda sunko gaisa da Aliyu ba.


&&&&&&&

Koda suka dawo gidama ba zama sukayiba, dan shirye-shirye aka faraima Jiddah Na mik'ata gidan miji.
'Dakin Umma taje ta k'unshe a k'arshen gado saboda azabar ciwo da kanta kemata, duk hayaniyar y'an yinin biki ta addabeta.
Anayin Sallar magriba kuma Fandau ta tasota aka fara tsumata dawasu sirrikan k'amshi Na musamman.

*_08:00pm_*

Angamawa Jiddah dukkan abinda ya dace da ita, sai iyaye dasuka baibayeta ana Mata nasiha, Umma ma a wannan Karon kasa cewa komai tayi, saima hawaye dake bin kumatunta, dan haka takasa magana. Said da k'yar tace, ALLAH ya bada sa'a, yabaku zaman lafiya, adaiyi hakuri, ayi hak'uri, ayi hakuri dakomaima za'aci karo dashi. Daganan Umma tayi shiru bata sake maganaba.
Sosai su Zarah ma ke kuka, dan Walida ma hardasu amai, hakan saiya saka mutane dayawa kuka, dukmai d'iya mace yanacin Karo da Abu biyune a irin wannan ranar, farinciki dakuma d'acin rabuwa da y'arsa.
Haka aka fita da Jiddah gidan Uncle yahya, acanma fad'an Tasha sosai da nasiha, Uncle yahya ya kamo hannunta har wajen motar y'an d'aukar amarya, dagashi sai Jiddah suka shiga d'aya, sauran jama'a suka shiga.
Sun Isa gidan Aliyu inda aka had'a wani taron walima da d'alibansa suka shirya masa, sun samu k'yak'yk'yawar tarba daga dangin Sheikh Aliy gadanga k'usar yak'i, yayinda Uncle yahya yatsaya da Jiddah har k'ofar Maimunatu, saida tafito ta durk'usa har k'asa ta gaisheshi sannan ya dank'a Mata hannun Jiddah yana jaddada musu Kalmar hak'uri da tsoron ALLAH wajen kwatanta nagartaccen zama da ALLAH bazai k'onasu akansaba wajen cutar da juna takowace siga.
Maimunatu ta amsa da insha ALLAH Abba tana hawaye itama, dan ita duk zatonta Uncle Yahya mahaifin Jiddah ne.

Maimunatu itace taima Jiddah rakkiya har cikin d'aya daga d'akunan barcinta, saida ta zaunar da ita a bakin gado sannan tace, *_Amincin ALLAH ya tabbata a gareki k'anwata kuma Y'ar uwata, ina miki marhaban da shigowa wannan gida, ina rok'on Ubangiji ya kad'e dukkan wata fitina dazata shiga tsakaninmu, ALLAH yabamu zaman lafiya ya dasa mana k'aunar juna mai tsafta a zukata, yabamu ikon yima mijinmu biyayya da k'yautata zaman takewa a tsakanimu har ranar da mai rabawa mutuwa zata raba._*
Kasa magana Jiddah tayi, sai hannun Maimuna data kuma matsewa a Nata tana kuma sakin kuka, rungumeta Maimunatu tayi itama tana Nata hawayen.
Wannan lamari ya burge jama'a, wasuma sunaji inama sune da wad'annan k'yawawan zukatan masu sauk'i da d'aukar rayuwa ba komaiba.
Munafukai masu burin kunna wuta kam sai jikinsu yay sanyi k'alau, a fili kuma sukaita ta6e bakuna.
Dangin Jiddah sunyi farin ciki da sauyin alkairi da d'iyarsu ta samu, dan haka suka juya cikeda farin ciki. Dan Uncle yahya yace babu mai kwana.

Tunda kowa yafita sai Jiddah tazame a gadon ta kwanta, dan kanta wani irin ciwo yake mata, har wani jiri-niri take gani. Zuwa 12:30 gidan yay tsit alamar kowa yatafi, har lokacin Jiddah Na kwance takasa barci, saima hawaye datake zirarwa har yanzu...............
'<



*_Harda sauran Na jiya Na had'a muku=D, kai gaskiya harma dana gobe, irin wannan dogon page haka=(=F<=9_*&
@&








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=-=O<_*
[12/18/2019, 2:29 PM] =؞Noorunnisa=؞: *_Typing=_*



*_=ءHASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=اMUTUM DA DUNIYARSA....!!=ا_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce><_*

*_[41'42]_*


..............Aliyu bai samu shigowa gidaba sai wajen sha biyu, gidan yayi tsit bakajin komai sai k'arar Gen... Da aka kunna, sashen Maimunatu ya nufa, nanma dai tsit yake, komai kuma a kashe, bedroom d'inta ya wuce.
Tana kwance tayi luf tamkar mai barci, amma idanunta biyu tana kuka Mara sauti, jin an bud'e kofar yasata saurin share hawayenta cikin dabara kafin ya kunna wutar d'akin.
Cikin sanyinsa yake takowa gaban gadon yana fad'in Habibty kalb badai barciba?.
Maimuna najinsa amma tayi shiru, ya zauna a bakin gadon yana lek'a fuskarta, kasa daurewa tayi tasaki murmushi saboda hannunsa daya tura a rigarta. Hannunsa ta janye tana tashi zaune cikin kumbura fuskar shagwa6a. Haba dai Yaya barcifa nake amma ka tadani.
O ALLAH yaushe wannan malamar tafara koyan k'arya?. yak'are maganar dajan hancinta.
Dariya tayi, tace, Ya gajiyar taro?.
Uhm wannan Ku za'a tambaya ai Habibty, yanzu dai ya za'ayi dani?.
Idanunta tad'an waro waje, Yaya a wajenmi?.
Komaima madam.
To yanzu dai tashi kaje kayi wanka ka baza turare kaje wajen k'anwata tana jiranka, nikam sai jango wlhy barci sosai nakeji ga gajiya.
Matsawa yay jikinta yana murmushi, Haba hajiyata kod'an wankanma baza'a tausaya amunba yau?.
Maimuna ta marairaice fuska tana fad'in ALLAH yaya bakaji jikinaba, ko ina ciwo yakeyi, danma nasamu zazza6in ya saukane fa.
Cikin tausayawa yakuma rungume ta yana k'ara jinjina mata da k'aunarta mai girma dake kuma k'arfi a ransa, tunda yashigo ya fahimci kuka take, amma kasancewar Matar kwarai saita had'iye ta taresa da farin ciki, shikam yama za'ayi ya wulak'anta wannan baiwar? Ai ta wuce hakan a garesa.
Yanda ya matseta sosai yasata sakin k'aramar k'ara, da sauri ya sassauta Mata rik'on tareda kallon fuskarta, yanda ta tura bakin gaba yabashi damar d'ora nasa akai. Tunma tana zame-zamen bataso harta nutsu tabashi had'inkai.>-
Bai bartaba saida ya tabbatar jikinta yay sanyi da zuciyarta sannan ya kwantar da ita yana shafa matashin cikinta daya fara d'agowa.
Addu'ar barci yafara karanto Mata, itadai tanata kallonshi da k'arajin k'aunarsa musamman da kishinsa, tanaji tana gani yau zasu raba shinfid'a, tunda tazo gidan hakan bai ta6a faruwaba sai dai idan tafiya yayi, amma yazatayi? Idan har takasance mai tsannatawa saidai ta saka kanta a musabar damuwa da rashin kwanciyar hankali, dan bata isa yin jayayya da hukuncin ubangiji ba.
Bayan ya shafa Mata addu'ar ya kwanto jikinta, zatayi magana ya d'ora hannunsa saman bakinta alamar tayi shiru. Shirun kuwa tayi tana sauke ajiyar zuciya.
Iska yafara hura Mata a kunne, ahankali tafara lumshe idanunta, saida yaga barci yafara cin galaba akanta kafin Yakoma Mata tausa, dand'in hakan yasaka nannauyan barci kwasheta, dama gashi gajiya tamata ligif. Saida ya tabbatar barcinta yayi nauyi sannan ya kuma tofeta da addu'oi ya gyara Mata kwanciya ya kashe fitilar ya fice yana murmushin dashi kad'ai yasan ma'anar kayansa.
Nasa sashen yanufa, Wanda ya kasance a tsakkiyar nasu Jiddah, amma shifa falone kawai da bedroom, shima kuma yaune zai Fara amfani dashi, danda a d'ayan bedroom d'in sashen Maimunatu yake, bayan d'aura aurensa da Jiddah kuma ya gyara nasa, dukda bai ta6a kwanaba saikuma yau.
Komai an saka, bakajin komai sai k'amshin sabon kaya Dana turaren da Maimuna ta saka. Baiwani 6ata lokaciba yashiga wanka ya fito, jallabiya Fara k'al mai gajeren hannu ya saka, yad'an saka turare ya fito, Gen... Yaje ya kashe, saima yaga an maido wuta wadda yake k'yautata zaton yanzu suka kawota, canjawa yay sanan ya doshi sashen jiddah.
Garin yakumayin tsitt dan d'aya takusa, sosai ya yaba da k'ok'arin iyayenta, sai fad'ar Masha ALLAH yakeyi, komai yagama dacewa da sashen.
Saida ya lek'a bedroom d'in farko yaga babu kowa, sai dai nanma komai tsaf yake, ga k'amshi mai dad'i yana tashi. 'Dayan ya nufa, inda ya hango Jiddah kwance a kan gadon, tawani takure waje d'aya.
Bata dad'e dayin barci ba, dan fuskartama jik'e take da d'anyun hawaye daya kuma tabbatar masa hakan, sassanyar ajiyar zuciya ya sauke yana zama kusa da ita, yakai hannu ya d'auke gyalen dayad'an rufe mata fuska kad'an, babu wata kwalliya mai yawa a fuskarta, saima ruwan hawaye dake jik'e da fuskar, murmushi yayi aransa yana jinjina k'aunarta da kuka, akance yacika saurin kuka, amma yalura jiddah senior d'insace.
Yanda jijiyoyin kanta suka tashi saiya fahimci batada isashshiyar lafiya, yakai hannunsa saman goshinta, hakanne yasaka Jiddah farkawa ta bud'e Idonta, da sauri ta tashi zaune jikinta yana 6arin tsorata. Saurin rik'o hannunta yayi dan ya lura tsorata tayi.
Relax Hajiyar tsoro.
Dukda ta fahimci shine hakan baisakata nutsuwaba, dan bata Saba kusanci da wani namiji

1 Comments On MUTUM DA DUNIYARSA
avatar
rukayya-yahuza

1 year ago

Reply

Kai book dinnan ya hadu iya haduwa

Please Login or Register in order to submit comment