Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rawa bai saketaba, saima bakinsa daya d'ora saman goshinta ya sumbata kafin yace, “wannan lalurar taki batamin adalciba, dolene kafin ki tare da izinin ALLAH na nemo mafita”. Yana gama fad'a ya sumbaci la66anta sannan ya saketa.
Dukda halin datake ciki Na gushewar nutsuwar wucin gadi hakan bai hanata yomasa rakkiyaba kamar yanda Gajiram ta gargad'eta.
Tun a bakin k'ofa ya Danna key d'insa motarsa takawo haske day'ar tsuwwa, bud'ewa yay yashiga yana d'ebo ledojin gefensa ya mik'o Mata.
K'in kar6a tayi tana shirin juyawa. Da hanzari ya damk'o hannunta yana fad'in “Hajiyata tunadai miji nake ba saurayiba”.
Dariya maganarsa ta bata, ledojin ya zura mata a hannu yana sumbatar hannun, “Kiyi mafarkina daga farkon dare har k'arshe”.
Kanta a duk'e tace, “Nagode ALLAH ya k'ara bud'i na alkairi, yakaika gida lafiya”.
“Amin *Qurratul ain*, maza shiga gidan dan bak'aramin k'ok'ari naiba barinki fitowa nan da wannan gyalen, danma kawai Darene kuma mota ta kare”.
Murmushi tayi tana d'an risinawa da fad'in “saida safe”.
Harta shige idonsa k'yam akan bayanta, ajiyar zuciya mai k'arfi ya sauke tareda jingina da kujera yana lumshe idanunsa, yakai hannu yana shafa gemunsa Na sunnah kafin ya maida hannun ga cikinsa, a hankali ya furta  Kunun aya yafara aiki kenan .
Bud'e idonsa yayi yatada motar a kasalance yabar anguwar tamkar bayason tuk'in.


('('('('('('.

Duk a falo Jiddah ta iskesu har Uncle yahya dasu Sadiq da basuyi barciba, gaba d'aya suka zubo Mata idanu, hakanne yasakata yin kasa da kanta tana sakin ledojin hannunta a k'asa, gani take kamar duk sunsan miya faru tsakaninta da Sheikh Aliyu.
“A'a Jiddodo yada sakin ledoji haka?”.
Uncle yahya yafad'a fuskarsa a washe da murmushi.
“Babu komai Uncle”.
“To Alhamsullhi, ya tafi ne?”.
“Eh”.
“To ALLAH ya tsare, basaikin zaunaba kumuje Na rakaku gida dare yayi”.
Ledojin Jiddah ta d'iba takaima Maman Sadiq.
“A'a Walida d'aukar Mata, wannan nakine ai”.
“A'a mama bafa nawa baneba”.
Uncle yahya ya katse zancen da fad'in “Kinga walida d'auka Mata kumuje”.
Babu Wanda yay masa musu sukabi Umarninsa.
Jiddah ta d'auki hijjabinta ta saka suka fita sunama Maman Sadiq dasu Mageed saida safe.
Har k'ofar gida ya rakasu, saida yaga sun Shiga sannan ya juya batareda yashigaba shi.

Su Umma duk suna zaune basuyi barciba suna jiransu.
Balu ce ke fad'in “A lallai wannan d'an nawa ya iya zuwa, amarya mikika samo mana?”.
Fita Jiddah tayi takoma d'akinsu takasa bata amsa, nanfa suka shiga yimata dariya da tsokanarta, tana jinsu amma tak'iyin ko tari, sai abinda ya faru tsakaninta da Aliyu keta dawo Mata kamar wata almara ko shirin film.
A can kuwa Gajiram ta bud'e ledojin dasukazo dasu. Kayan marmarine sai ice-cream da kaji guda biyu, sai kuma kwalin waya harda Sim card.
Nanfa suka shiga godiya ga Aliyu da fatan alkairi dana zaman lafiya garesu.
Gajiram tace walida ta d'auka takaima Jiddah, amma sai Umma ta dakatar da ita. “Ba haka ya kamata ba, ki raba kowama ya samu, wannan shine dai-dai”.
Gajiram tasan halin Y'ar uwarsu da k'yak'yk'yawan tsari akan yaranta, dan haka tabi umarninta, kaza d'a aka ajiyema gidansu Uncle yahya, kayan marmarinma aka d'iba musu, ice-cream aka ajiye roba d'aya, ta raba komai nasu tabama su Jiddah rabi suma su uku suka d'auki rabi.
'Dauka su Zarah sukai da wayar Jiddah suka nufo d'akinsu zuciyarsu wasai dakumajin lallai yanzune Y'ar uwarsu tayi aure.
A tsanake sukaci komai sukai gidiya ga ubangiji, kafin su dasa fira da k'ok'arin had'a wayar Jiddah dukda babuma wuta.
Suma su Umma dai hirar tasu duk akan tariyar jiddahrne, sunayi sunacin abin arzik'in da ya sheikh Aliy ya kawo.


('('('('('('('('('('('.

A haka ya lalla6a hanyar gida bayan ya tsaya yasayama Maimunatu abin motsa baki itama.
Dukda dare yafarayi hakan bai hana ya iske tsirarun mutane a bakin masallacin k'ofar gidansaba, dayake akwai wuta a anguwar tasu su, dukda yabaro anguwarsu Jiddah babu kuwa.
Wani saurayine dasuke a bakin masallacin ya tashi ya bud'e masa gate, bayan yashiga ya rufe, saida ya tsaya Aliyu yafito a mota ya gaidashi sannan yafito yana masa saida safe.
Aliyu kuma ya kulle gidan danya shigo kuma kenan, tsarabar Maimunatu ya d'iba yanufi cikin gidan duk a matuk'ar kasalance, Wanda kallo d'aya zaka masa ka tabbatar da bashida kuzari ko kad'an, dukda shi mutumne mai sanyi dama amma saiya kuma narkewa yanzu.
A yanda Maimunatu dake zaune a falo taji sallamarsa kawai saida ta d'ago da sauri ta kallesa da k'yau.............
'<Øûß









*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*=ØOÞ<Øûß=Ø-Þ

[12/15/2019, 3:10 PM] =ØžÜNoorunnisa=ØžÜ: *_Typing=ØòÜ_*



*_=Ø¡ÜHASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=اÜMUTUM DA DUNIYARSA....!!=اÜ_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>ØÝ<Øûß_*

*_[35–'36]_*


..............Kallo d'aya taimasa ta d'auke kanta tana murmushin k'arfin hali, jikinta duk sai ya kuma sanyi, itadai tasan Aliyu ba mutum bane mai yawan fitina, hasalima sunkan jera kwana hud'u batareda ya nemeta ba, sannan baya d'aukar dogon lokaci tare da ita, wannan dalilin yasakashi dagewa wajen gyara kansa, dan a ganinsa ba mace kawai yakamata taima miji gyaraba, suma mazan yadace suna gyarawa........
“Ko ba'ayi murna da dawowataba Na koma Gimbiya”. Maganarsa ta katsema Maimunatu tunaninta, mik'ewa tayi ta nufosa, sai da ta rungumesa da sumbatar kumatunsa kafin ta sakesa ta amshi kayan hannunsa tana danne kwallar data cika idonta, dan sosai taji k'amshin turaren daba nashiba a jikinsa, tasan kuma bai wuce Na amarya ba, a yandama yadawo mata kad'ai ya isheta amsa.
Bin bayanta yay ya zauna yana sauke numfashi, kallonsa tad'anyi batareda tace komaiba tawuce kicin, babu dad'ewa tadawo d'auke da tire.
Gabansa ta dire, ya d'ago kansa daya jingina a kujera yana kallonta, itama shi take kallo, cikin danne zuciyarta tasaki murmushi tana fad'in “Wai miya sakaka laushi haka Annur?”.
Zamansa ya gyara sosai tareda kamo hannunta ta zauna a gefensa. Muryarsa a matuk'ar sanyaye yace, “Babu komaifa madam, naga kin damu”.
“To ba doleba Yaya, kafita muna farin ciki kadawomin a sanyaye, kaga sainaga ko wani abune yafaru da jiddan ko wani a gidansu ai?”.
“To kwantar da hankalinki, babu abinda yafaru tanama gaisheki. Bani ruwa nasha kedai”.
“ALLAH Sarki, ina amsawa nima, kuma Alhmdllh tunda babu wata damuwa”. Jug dake kan tire ta d'auka tafara tsiyaya abin ciki a k'aramin kofi.
“Minene wannan zaki bani?”.
Da mamaki ta kallesa sannan ta kalli jug d'in, “Yaya had'in kwakwar dakace namakane d'azun ai, to wlhy nama manta, sai bayan fitarnan taka dasuka kawo wuta Na tuna shiyyasa nayi, kajiko harma yayi sanyi”.
Amsar jug d'in da kofin yayi ya ajiye k'asa, “Barshi dan ALLAH Maimoon inba kasheni zakuyiba”.
Cikin waro ido Maimuna tace, “Yaya kashewa kuma?”.
“Eh mana, ba dole nace kashewa ba, ita tabani kunun aya, kekuma zaki bani had'in kwakwa?”.
Babu shiri Maimuna ta kwashe da dariya, haba no wonder tagansa a sanyaye.
Harara ya zuba Mata yana wani shagwa6e fuska da fad'in “Abindama zakimin kenan ko? Maimakon kiji tausayina”.
Baki Maimuna ta toshe da hannu tana had'iye dariyarta da k'yar, “ALLAH Yaya kaid'inne kaban dariya, ni duk kasakani a tsorone da farko”.
“Humm bazaki ganeba wlhy, tsautsayi kawai ya sakani shan kunun ayarnan da yawafa, gashi kuma yasha had'i kamar yanda kikemin, Nidai Ahmad ai yagama dani daya bani wannan sirrin”.
“Haba dai Yaya godiya yakamata Kai masa ai”.
Hannu yasa ya jawota jikinsa, murya k'asa-k'asa yace, “Wayace ban gode masaba, badan iyakancewar Mahaliccina da taimakon Ahmad ba da yanzu ban mallaki koda mace d'aya ba balle Mata biyu ma ai Sarauniyata, amma wad'annan had'in ba k'aramar harmutsani sukeba”.
Hanu Maimuna tasaka ta rufe fuskarta tana Y'ar dariya. Shima saiyay murmushi yana kuma sakata a jikinsa.
Tarigada tasan muhimmmanci duk irin wad'annan abubuwan ga mijinta, hakanne yasakata kar6arsa d'ari bisa d'ari tun a falo aka fara canja hanya.


=ØFÞ<Øûßù&
@&.



('('('('('('('('('('('

Jiddah dai gaba d'aya tama rasa yanda zata fassara abinda sheikh Aliy yay Mata, wani iri duk takeji a jikinta, duk hirar dasu Zarah keyi hankalinta baya tare dasu, har aka maido wuta suka saka cajin wayar.
“Wai Yaya Jiddah mike matsalarkine? Tunda muka dawo kinyi sukuku”.
Kallon Zarah tayi mai maganar, kamar bazata tankaba saikuma ta sauke numfashi tana cewa, “Babu komai, kaina ked'anmin ciwo kawai”.
Sannu suka shiga jero Mata cikin tausayawa, Walida harda zuwa ta samo Mata magani. Bata musaba ta kar6a tasha sannan tayi shirin barci suka kwanta.
Barcinma k'in d'aukarta yayi, sai tunane-tunane takeyi, tunda take bata ta6a soyayyaba, hasalima baifi sau uku zuwa hud'uba ta ta6a tsayawa da saurayi, dan dawahala tana tafiya samari su tareta a hanya ko yimata magana (Muhimmancin nagartacciyar sutura ga d'iya mace, yakan saka mutanen banza shakkar zuwa gareka, abinda y'anmatan yanzu dama matan auren muka gaza fahimta kenan), wannan yasaka komai Na Aliyu take masa kallon *Sabon al'amari* a gareta, ganin barcin yama gagareta saita mik'e tafito domin d'aura alwala.
Nafilfili taita gabatarwa, kafin tayi zaman karatun littafi mai tsarki, a wannan time d'inne suma su Zarah suka farka, sai suma sukayo alwala.

Koda Jiddah tasamu ta kwanta sai barcinta yazama mafarkin Aliyu kusan gaba d'aya, da asuba abin ya tsaya mata a rai, tasara miyasa ya mannema zuciyarta har irin haka?.


Fans zasu baki amsa jiddodo>Ø)Ýù&
@&.


('('('('('('('('('('('

Gaba d'aya Abba zakari a takure yake, yasaba harkokinsa Na kasuwanci a kullu yaumin, amma anzo nan an ajiyeshi wai dan ya huta, anyama kuwa wannan ba tsarin Yahya baneba? Zumbur yamik'e saboda amsar da zuciyarsa ta basa, lallai wannan haka yake, akwai munafinci a wannan lamarin, tunda dai ai shine ya kawo likitan, to waima miyasa yagaza tariyo yanda suka k'are a Station ne?, shiru yay nawani lokaci, kafin babu shiri ya lailayo wani ashar ya dire a k'asan tayis, a lallai yahya yagama ganin gadon barcinsa, yanzu kuwa zaije ayita tak'are wlhy.
Batareda jiran likitaba ya had'a inasa-inasa ya nufo gidansa da Hajia Hindu ke a ciki.


('('('('('('('('('('('.

Hajia deluwa hakimce a falonta Na alfarma tana waya da hajia Hindu akan auren Jiddah, sai dariya take kwasa tasamun nasara, dan yanzu sakayau takejinta tamkar an sauke Mata kaya a Kai, Alhaji Garba datun farkon fara wayar yashigo yay tsaye tamkar gunki yana saurarenta, dawowarsa kenan daga tafiyar da yayi, cikin zumud'i yanufo sashenta saboda shigar bazata yay mata batasan da dawowarsaba yau, amma saiyaci Karo da abinda ke Neman fasa masa zuciya.
Jiddah tayi aure bashiba, mahaifinta ya yaudaresa, matarsa itace ta ruguza masa dukkan shiri ta k'ark'ashin k'asa.
A fusace ya fisge wayar ya ratsata da k'asa akan tayis, nan take tayi kwatsa-kwatsa.
Hajia deluwa data mik'e a fusace tuni mamaki da tsoro ya baibaiyeta, dan batasan da shigowarba ko kad'an, amma dayake manyan matane sunsan takan duniya saita dake tana kallonsa hankali a kwance.
“Alhaji lafiya kuwa? Ya daga dawowa sai fushi haka? Mi wayata Tamaka?”.
“Ban saniba Yahanasu, yanzunan kece da kanki zaki aikata shed'anci Na ruguza auren sunna? Dama son aurena da Jiddah dakiketa nunawa da farko munafuncine Ashe? Lallai yau nakuma yarda makircin mace yafi Na shaid'an girma, anyama kuwa bakece kika kori Jiddah daga gidannanba?”.
“Yo Alhaji kaga laifinane? idanma ni d'ince”.
“No ya za'ayi inga laifinki, ban ganiba wlhy” yay wata dariya ta basawa, kafin ya nunata yana cigaba da fad'in “Kijira sakamakon aikinki Na ruguzamin auren Jiddah da kashe mana aure”.
Yana gama fad'a yay ficewarsa, mamakine ya kama hajia Deluwa, tafara safa da marwa Na tunanin to mizai Mata? Miya shirya? Kodai sakinta zaiyi?. Gabantane yay wata mummunar fad'uwa, jikinta Na rawa tabi bayansa.
Amma saita tarar ya gark'ame k'ofarsa, duk Nokin d'in datai masa bai kulataba. Kuma yana jinta sarai, dan yanama zaune a falonsa yana k'ok'arin kiran Abba Zakari a wayane.

Abba datunda yabaro gidan doctor yadawo gidan hajia deluwa ta tareda da farin cikin samun lafiyarsa, dukda tagansa awani tsume alamun zuciyarsa a kusa take hakan bai hanata tarairayarsa yay wanka yaci abinci ba, harzai fita gun Uncle yahya ta dakatar dashi da maganar kalifa daya shigo gidan yanzu babu jimawa sannan Abba yana wanka.
“Kin dakatar Dani, bakice komaiba kin zubamin idanu”.
“A'a Abban kalifa, bafani nakar zomonba, dama kalifane aka koro daga makaranta sunyi fad'a dawani yaro akan budurwa ya fasa masa Kai, yanzuma haka abinda ake ciki iyayen yaron sunce bazasu yardaba, shiyyasa aka koro kalifa yazo yaje da mahaifinsa yana d'akinsu, Wanda aka turosu tare kuma yana a bakin gate yana jiranka”.
Zugudi yayi yana kallonta, bakinsama yamasa nauyin daya gaza furta komai, harma yaushe Kalifan yagama balaga dazai fasa kan wani akan mace?, ina wannan sharrine kawai za'aima yaronsa, dan haka babu inda zayi yanada matsalar data girmi wannan shirmen........
K'arar wayarsa daya kunna babu dad'ewa ta katse masa tunani. Wata mummunar fad'uwa gabansa yayi saboda ganin mai kiran, yanda ya gwalalo idanune yasaka hajia Hindu lek'a wayar, itama saida ta fiddo ido kafin tace, “Abban kalifa ka d'aga mana”.
Kallonta yayi awani yanayin data kasa fassarawa, wayar Na tsinkewa aka sake bugowa, amma Abba yakasa d'auka.
Hakanne Yakuma fusata Alhaji Garba daga can, a matuk'ar harzik'e yakuma dannoma Abba Kira.
“Alhaji ka d'auka mana” hajia Hindu tafad'a tana nuna masa wayar, ganin bashida niyyar amsawa ita saita amsa tana saka masa a kunne.
Yanda Alhaji garba yay magana dagacan a harzuk'ene yasaka Abba kwarewa da yawu yahau tari.
“A lallai Alhaji zakari, ni zakaima d'ibar albarka, k'in amsa wayata da kayi kawai ya isa bani shaidar kana kan sani ka aurar da y'arka, to ni bazan zauna 6ata lokacina akan hayaniya dakaiba, saidaifa ina mai tuna maka maganar kud'ina miliyan hamsin cif nanda wata d'aya kacal wlhy, dan wannan shinema adalcin dazan maka, sannan kuma namik'a komai a hannun d'ana Ashir dashi zakuyi nabarka lafiya”.
Wani haushine ya turnik'e Abba, Dama ga zuciyarsa a kusa take, jira yake a ta6osa ya fidda fushinsa, cikin tsantsar bala'i shima ya dakatar da Alhaji garba dake shirin katse kiran. “To naji d'in saime, ank'i a baka auren Nata, waishin kasheni zakuyi da haukankune?, shin da wanne zanji? Kama tambayeni yanda akayi mana amma saika hau kaina saboda wata banzar miliyan hamsin, Kai da mutuncinafa babu Wanda ya isa ya takani”.
Tsaki Alhaji garba yayi ya yanke wayarsa.
“Amma Abban kalifa da bakai masa hakaba ai, gara ka lalla6ashi ko Zarah saika bashi madadin Jiddar ko?”.
Wata uwar harara ya zuba Mata, kafin yasaka hannu ya hankad'ata baya, tareda tad'e k'afarta dake hanyar dazai wuce, a take k'ashin k'afar yay k'arar samun rauni.
dukda k'arar wahala data saki baibi takantaba ya tsallaketa yafuce a fusace.



Turk'ashi=ØFÞ<Øûß=Ø(Þ.


('('('('('('('('('('('

Gaba d'aya yau Sheikh Aliyu bai fita ko inaba tunda yadawo sallar asuba, dukda kuma yau litinin amma sai yay lafewarsa gida, ga Maimuna ma dai bawani isashen lafiyane da itaba, amma dayake tanada dauriya sai bata cika langa6ewa ba, da taimakonshi suka gyara gidan, kicinma shine ya tayata had'a musu Karin kumallo sannan suka gyara komai tsaf. Wanka yatafi yi yabarta tana shirya abincin a falo.
Yad'an jima a bayi kafin ya fito, wayarsa daketa haske ya kalla takawa yay inda take a saman durowan gefen gado ya d'auka, mamakine ya kamashi ganin sak'one aka turo da Number Jiddah daya saya mata jiya. Bud'e sak'on yayi zuciyarsa na mamakin kona minene?, saida ya zauna a baking gado kafin yafara karantawa.
*_“Amincin ALLAH ya tabba ga adalar zuciya ma'abociyar tsoron ALLAH da addini, ina fatan ka Isa gida lafiya? Kakuma iske Y'ar uwata lafiya itama?. Fatana karayu cikin aminci da tsaftataccen farin ciki a wannan yini na litinin ya kai jarumina tauraron Al-umma a k'ark'ashin duniyar musulunci, nagode kwarai da gaske da alkairinka a gareni, ALLAH yak'ara bud'e na alkairi mai albarka kuma>ØÝ<Øûß ._*
_Taka Hauwa'u-Jiddah_.

Idanunsa ya lumshe yana sauke wani nannauyan numfashi, yayinda can k'asan ransa yake kuma gauraya dawani farin ciki na musamman, ko kad'an baiyi zaton hakan ga jiddahr ba, musamman idan yay dubi da yanda suka k'are a jiya.
Idanunsa ya bud'e akan wayar yana sake maimaita karanta sak'on, saida ya tisashi sau babu adadi kafin ya danna kiranta dan bazai iya hak'uri ba.

Jiddah suna zaune a falo gaba d'ayansu suna Karin kumallo Walida ce kawai babu taje makaranta, Zarah kuwa batajeba suna shirye-shiryen fara jarabawane ta SSCE. hankalinsu kwance sukecin Taliyar da Jiddah ta dafa musu (Y'ar Hausa) wayar Jiddah dake hannun Balu da Zarah tashiga tsuwa, kallon juna sukai sukai murmushi, Zarah taima Balu alamar Jinjina da fad'in “Aikinmu Na k'yau nida uwata”.
Hannu balu taba Zarah suka tafa kafin ta mik'ama Jiddah dake kallonsu wayar. Su Umma ma dai kallon Su Zarahn sukeyi, amma basuce komaiba, saima Yaruwaiya datacema Jiddah “Wai bazaki tashi kije ki amsaba saita tsinke”.
Tashi Jiddah tayi tafita jikinta a sanyaye, kafin ta Isa d'akinsu ta d'aga har kiran ya yanke an sake Kira. 'Dagawa tayi tana zama a bakin katifarsu.
Jin ta d'aga sai Aliyu ya d'an sauke ajiyar zuciya yana fad'in, “Assalamu alaiki warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu”.
Wani yarrr Jiddah taji tsigar jikinta ta tashi, cikin had'iye yawu da k'yar da janyo numfashi, ta amsa da “Wa'alaikassalam, ina kwana”.
Murmushi yayi daga can yana shafa gemunsa zuwa k'asumba, cikin kuma sanyaya murya yace, “Lafiya lau Amarsu, ina fatan kema kina lafiya?”.
“Lafiya lau, ya jikin Aunty”.
“To masha ALLAH, jikin auntynki kuma Alhamdulllahi .
Shiru Jiddah tayi, dan batasan kuma mi zataceba (abinka da farin shiga=ØÞ), sai dai a k'asan ranta tarasa miyasa muryarsa ke sakata a wani yanayi?.....
Katse Mata tunani yay da fad'in  Naga sak'o Na gode sosai, sakallahu khairan Juddatulkhair”.
Mamaki ya kama Jiddah, tana shirin tambayarsa wane sak'o? Dan itadai tasan bata tura masa wani sak'oba saiya katse Mata hanzari da fad'in “Lallai Na yarda anyi mafarkina daga farkon dare zuwa k'arshe da gaske, wannan sak'o ya cancanci tukuyci mai nagarta, Na bayar anan? Kosai nazo kusa?”.
Cikin shagwa6ar da Jiddah batasan tayiba tace, “Nidai Na yafe”.
“A'a madam yada saurin karaya haka kuma? Nifa ba fad'ar tukuycin dazanyiba nayi aiko, yanzu dai kin amince nazo anjima na bada?”.
Da sauri Jiddah tace, “A'a nagode, abama aunty a maimakona”.
“Kin yarda Na bata?”.
“Eh wlhy Na yarda nikam”.
“To shikenan, Zan bata rabi nazo nabaki rabi”.
“A'a kabata duka nidai”.
Murmusawa yayi yana mik'ewa tsaye, ya k'arasa gaban mirror yana fad'in “To ai shikenan tana godiya sosai, yasu Zarah?”.
“Lafiyarsu lau suna gaidaku suma”.
“Muna amsawa, suna kusa dake kenan?”.
“A'a”.
Zaiyi magana Maimuna ta shigo da sallama, yanda yake murmushi yasata tsarguwa ko yana waya da matarsane? Dan haka tai niyyar juyawa. Saurin damk'o hannunta yayi yana k'arema kwalliyarta kallo, tayi k'yau sosai tana baza k'amshi.
Jin yayi shiru gakuma d'an motsi Jiddah Na jiyowa yasakata itama tsarguwar k'ila matarsace, saitai saurin fad'in “Sai anjima”.
Matse Maimuna yayi a jikinsa shima yace, “To sai anjima a gaishe dasu Ummi”.
“to” kawai Jiddah tace ta yanke wayar. Haka kawai taji ranta ya sosu, wato da shikad'aine shiyyasa yaketa wani narke Mata, amma yanzu matarsa tazo yama kasa magana,  humm halin maza saisu tai maganar a fili tareda ta6e baki ta mik'e takoma wajensu Umma, sai dai k'asan ranta abun ya tsaya Mata sosai. (Madam Jiddah yayane=ØFÞ<Øûß=ØÞ?).
Data dawoma daina saka baki a firarsu Umman tayi, har Yaruwaiya da Balu da Zarah suka shirya suka fita kasuwa k'arasa sayayyar Jiddan data rage, aka barta itada Umma kawai.
Umma nakula da zum6ure-zum6uren da Jiddah keyi, amma sai bata kulata ba balle ta tambayeta ma.
Saima zama datayi tana tambayarta akan magungunan sanyi data bata Tasha tun kwanaki.
“Wai Jiddah magungunan Dana baki kuwa kina amfani dasune?”.
“Eh Umma inayi”.
“Idanma bak'yayi kekika sani dai, dan wannan shine gatan dazan miki, a zamaninnan da sanyi yayma Mata katutu, ba maganin mata kawai yakamata mu iyaye muyita Danna mukuba idan zakuyi aure, yakamata mufara bincikar lafiyarku ta 6angaren sanyi kafin wad'annan magungunan, dan duk macen dake tare da

1 Comments On MUTUM DA DUNIYARSA
avatar
rukayya-yahuza

1 year ago

Reply

Kai book dinnan ya hadu iya haduwa

Please Login or Register in order to submit comment