Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bayan d'aurin aure aka gudanar da gagarumar walima wadda malamai suka zazzaga wa'azi akan aure da rayuwar ma'aurata, tareda jan doguwar Addu'a ga wad'annan ma'aurata.
Amarya Maimunatu tana cikin farin cikin mallakar cikar burinta, yayinda ango baka gane nasa yanayin.
Bayan kammala walima aka mik'a amarya d'akinta tareda fatan alkairin ALLAH yasa bad'i adawo suna...............
'<Øûß


https://youtu.be/eOU-ju4f6KY

_Zaku iya samun RAINA KAMA a audio ta wanann link d'in Na sama, Abban Dausayi YouTube channel tv=ØÞ>ØÝ<Øûß_


*_Bazan 6oye mukuba jiya bak'aramar dariya naci akan Comments nakuba gaskiya, lallai nalura kund'auki aurennan da zafi, Abba zakari da Alhaji garba sun zagu babu k'arya>Ø#Ý>Ø#Ý, ALLAH ya taimakeni ba a had'a daniba nima=ØÞù&
@&._*







*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=Ø-Þ=ØOÞ<Øûß
[11/30/2019, 1:17 PM] =ØžÜNoorunnisa=ØžÜ: *_Typing=ØòÜ_*



*_=Ø¡ÜHASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=اÜMUTUM DA DUNIYARSA....!!=اÜ_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>ØÝ<Øûß_*

*_[14–'15]_*


..............Sosai Jiddah ke yaba k'yawun tsarin sashen hajia deluwa, dan bak'aramin kud'i aka narkaba gaskiya, gabanta ya fad'i saboda hango Hajia deluwa dake hamshak'e cikin kujera, taci kwalliya cikin wani ubansun leshi ruwan ganye, ga wani kamshi Mai kwantar da hankali datake zabgawa.
Tunda Jiddah ta shigo itama Hajia deluwa kemata kallon k'asan ido daga k'asa har sama, sosai Jiddah taimata k'yau fiye da yanda hajia Hindu ta nuna Mata ita a hoto, dukda a yanzu cikin hijjab take kuwa.
Gabanta Jiddah taje ta zauna a k'asa, cike da girmamawa muryarta a matuk'ar sanyaye tace, “Hajia ina yini”.
Cike da yatsina hajia deluwa ta amsa da “lafiya amarya ya kwanan amarci?”.
Shiru Jiddah tayi takasa amsawa, yayinda hajia deluwa keta wani ta6e baki tana gyara zamanta, cikin dakewar murya tace, “To amarya inason muyi magana ta fahimta dake, dan banason biyo miki ta hanyar da zaki gaza 6illewa, da farko dai kisani ina matuk'ar son mijina da dukiyarsa, babukuma wata danake k'aunar tazo ta haihu dashi bayan nawa y'ay'an, kullum burina dagani sai y'ay'ana mu mallaki komansa, a girme Na girmi Mamanki ma balle ke nasani, Alhaji kam inda su Yahuza auren wuri sukayi sun Isa Haifa masa kamarki matsayin jika, inason nabaki shawarar kibar gidannan tunda arzik'inki, Zan baki ko nawa kikeso domin kibarmin mijina, dan tabbas nasan dukiyarsa tasaki aurensa, dan Ku y'an matan yanzu duk inda naira take kuna a nanik'e, abinda yasa duk nake miki wannan jawabin cikin lalama saboda nakula kamar zakiyi hankali, sannan kece mafi k'ank'anta a matan da Alhaji yata6a aura adukkan aure-aurensa. Kifita kisamu saurayi dai-daike ki aure, inma baida kud'in aurenki Zan iya masa komai, ke nama tak'aita miki zance koda cikin su Ashir kikeso ki za6a (yayanta fa=ØFÞ<Øûß).
Duk wannan maganganu da Hajia deluwa keyi kan Jiddah Na k'asa tana mamaki da al'ajabinta, gaba d'aya takasa fahimtar inda surutanta suka dosa, wannan wace irin macece?........
Kafin Jiddah tasamu zarafin amsawa sallamar matashin saurayi dazai iya kaiwa shekaru 29 ta karad'e falon.
Cikeda washe hakora Hajia Deluwa ta amsa masa tana fad'in “Wai ina kashigene haka Ashir?”.
Idonsa akan Jiddah yace, “Mami wlhy ina d'aki kwance abuna, wannanfa?”. ‘Yak'are maganar yana lasar la66a da nuna Jiddah’.
Baki hajia deluwa tad'an ta6e, ”Amaryar gidance”.
Sosai Ashir ya zaro ido waje yana kuma lek'a fuskar Jiddah, “wai mami dama wannan karon karamar kaza Dad ya d'akko mana? Kai dad yana yarfamu wlhy, inma auren zaiyi ya d'akko wadda kowa yagani zai yaba mana”.
Harara Hajia deluwa ta watsa masa, amma batace komaiba.
Jiddah kam gabanta saikuma fad'uwa yake, ga maganganun Ashir na sukar zuciyarta amma batako motsaba.........
“Kinga tashi ki tafi, kije kiyi nazari akan maganata”. Maganar Hajia deluwa ta katsema Jiddah tunani.
Dak'yar ta iya mik'ewa ta fice jikinta Na rawa, yayinda Ashir kebinta da kallo tamkar tsohon maye..


('('('('('('('('('('('

Ango Ali baisamu damar shiga gidan nasaba sai wajen sha d'aya, Malam Mustafa ne ya kaishi har gida, batare daya shigaba ya juya yana tsokanarsa wai asha angwanci lafiya.
Murmushi kawai yay bai iya bama malam mustafa amsaba, danshi ba mutumne Mai yawan maganaba inhar baisoba, idan kuma yaso zakaji yanayi sosai mussaman ma idan tashafi addini.
Cikin sanyin nan nasa tamkar mara laka a jiki ya k'arasa cikin gidan, a hankali ya furta “Masha ALLAH” akan la66ansa saboda k'yawun da falon yayi, komai yayi cikin tsari dai-dai gwargwado, bai zaunaba ya nufi bedroom d'in Maimunatu.
Cikin sassanyar muryarsa yay cikakkiyar sallama.
Maimunatu dake kwance tad'ago idanu tana kallonsa da amsa sallamarsa akan la66a, sanye yake cikin wani lallausan yadi kalar madara, sai hularsa kube ruwan makuba dad'an ratsin kalar madarar, jikinsa Na fidda wani sassanyan kamshi maisaka zuciya nutsuwa.
Shikam kallo d'aya yaymata ya janye idonsa tareda ajiye ledar hannunsa saman madubi sannan ya zauna a bakin gadon d'an nesa da ita. Tashi tayi zaune tana fad'in “Yaya Aliyu ina yini”.
A sanyaye yace, “Lafiya lau Maimunatu, ya gajiyar hidima?”.
Murmushi tayi kawai amma bata iya bashi amsaba sai wasa da gefen gyalenta da takeyi.
Kuma kallonta yad'anyi kafin yakuma d'auke idonsa, “Ga abinci nan nasan kina buk'atarsa, danku Mata idan kuna hidima nakula bakuda lokacin cikinku”.
Murmushi tayi idonta akan bakinsa dake motsawa a hankali tamkar bashi ke maganarba....
Jin tayi shiru saiya juyo ya kalleta, saurin janye idonta tayi akansa ta amsa da “to, nagode”.
Karan farko daya d'an murmusa, ya mik'e yana fad'in “Bara nad'an watsa ruwa, kafin Na dawo kici abinci kiyi alwala...”. Kafin tabashi amsa tuni ya fice.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, tajawo ledar daya ajiye ta bud'e, gasashshen namane sai kayan fruits da abinda ba'a rasaba. Bata wani kwari kantaba taci abinta tayi nak sannan taje tayo brosh tadawo ta zauna.
Kusan mintuna Arba'in saiga malam Aliyu ya dawo, sanye yake da kananun kaya wando dogo fari da riga t-shirt ruwan hanta, abinda tunda maimuna take bata ta6a gani daga gareshiba kenan, saka kananun kaya, gaba d'aya ta shagala da kallonsa saboda wani mugun k'yau dayay Mata, Yakuma komawa yaro d'anye sharaf, a ranta tana ayyana dama yana saka k'ananun kaya haka?......
Malam Aliyu da yaga ta shagala da kallonsa ne yay murmushi yana zama kusa da ita gab tareda kai yatsansa tamkar zai tsokale Mata ido.
Da sauri ta sauke ajiyar zuciya tana rufe fuskarta saboda taji kunya sosai.
Murmushi yad'anyi, yana cewa, “Na canja mikine?”.
“Sosaima”. ‘Ta fad'a har yanzu Idonta a rufe’.
“Humm dama can kallon tsoro kikemin shiyyasa kike ganin Na canja yanzu. Ina fata kinyi Alwalan?”.
Batare data bud'e fuskartaba tace, “Nifa Yaya ina up”.
Baice komaiba sai d'auke kai dayay daga dubanta yana d'an sauke numfashi, kusan mintuna biyu yana mulmula maganar dazai mata a ransa kafin ya gyara zama yakuma fuskantarta.
“Yaushe yazo?”.
Tamkar zata nutse dan kunya haka taji, gyalenta taja takuma rufe fuskarta sosai kafin ta iya bashi amsa, “Yau”.
“Babu k'yau k'arya, yau kwannansa biyu, nanda kwana hud'u zaki samu tsarki”.
Babu shiri ta bud'e fuskarta tana ware idonta a kansa, “Yaya ya akai kasani?”. ‘maganar ta su6uce Mata batare da ta saniba’.
Jikinsa kawai ya jawota batareda ya bata amsaba, cikin kunnenta ya rad'a Mata “Kinason sani?”.
Gaba d'aya kunya ta rufeta, ga jikinta sai tsuma yake saboda jinta a jikinsa, shikansa hakance ke faruwa daga gareshi, amma ya daure kamar bayajin komai.
Kusan mintuna biyu suna a haka kafin ya d'agota zaune sosai. “Tashi muyi magana”.
Gyara zamanta tayi, taja gyalenta takuma rufe fuskarta sosai.
“Maimunatu da farko dai nasan kinada ilimin addini dana zamani, kinkai shekarun da zaki iya banbance dai-dai da sa6anin haka, inaso kisaka a ranki zamuyi tsaftataccen zaman aure tamkar yanda Manzon ALLAH (s.a.w) ya koyar damu, insha ALLAH Zan sauke dukkan hak'k'ok'inki a kaina iya iyawata, kema ina fatan hakan daga gareki. Nasan tunkan ki shigo gidana kinsan inada lalura wadda itace sanadin rabuwata da matata ta farko, to kisanifa har yanzu banida tabbacin samun waraka, sai dai muna fatan dacewa, wannan kuma saikin samu tsarikine zamu tabbatar, idan babu wani canji game da lafiyata to lallai bazan cutar dakeba Zan sallameki insha ALLAH, idan kuma an dace Alhmdllh, zaki zama Aliyu, Aliyu zai zama ke, mallakar Aliyu gaba d'ayansa kuma saikin zama jaruma wajen fahimtar abinda yakeso da Wanda bayaso. Nabaki satar amsa”. ‘ya k'are maganar da yaye gyalen data lulllu6a’.
Saurin kife kanta tayi a cinyarsa saboda kunya, yayinda shikuma yay murmushi.



=ØÞta gidan Sheikh Ali ina tayaki murna>Ø-Ýù&
@&.



('('('('('('('('('('('

A gidan Umma kam bayan biki da kwanaki uku kowa ya Kama gabansa, aka barsu su kad'ai, daga ita harsu Walida babu Mai isashshiyar lafiya, kowa damuwa da tausayin Jiddah da kewarsa ta isheshi.
Washe Gari dole Uncle yahaya yanemo likita yazo har gida ya sakama Umma k'arin ruwa saboda batajin dadi sosai.
Bayan la'asar Zarah ta cire Mata saboda ya k'are, ruwa Mai d'umi suka had'a Mata tai wanka, suna tsaka da gyaran gidan saiga Abba.
Kowacce kai a k'asa ta gaidashi.
Bakinsa ya ta6e ya wuce d'akin Umma, dan ya lura yau su Zarah awani yanayin jin haushi suka gaidashi.
Umma na zaune tana cin faten waken da Maman Sadiq ta aiko Mata Abba ya shigo, kallo d'aya taimasa ta d'auke kanta.
Zama yay shima yana wani kumbura. Umma tace, “Ina yini”.
Bai amsaba, sai tambaya daya jefoma Umma.
“Yagana waike aurar da y'arne yasaki maida kanki haka? Lallai aiki ya sameki ashe”.
Wani murmushin takaici Umma tayi kafin ta d'ago ta kalleshi ido cikin ido, “Koma minene ya maidani haka wannan ba matsalarka baceba, saidai inason maka tambaya d'aya. Shin nawa Alhaji Garba yabaka kabashi Jiddah?”.
Gaban Abba ne ya fad'i, bakinsa Na rawa yace, “Yagana ban gane wannna maganar banzar takiba? Dan Zan bada auren y'ay'ana sai an biyani kud'i?”.
“Humm Alhaji kenan, bar ganin ka fini shekaru wlhy kar nake kallonka, a ina kasamu kud'in biyan banki bashin da kaci musu?”.
Harara ya watsa mata yana huci, “Shak'eni Na fad'a miki mana yagana?”.
“Aiba saina shak'eka bama, zaka fad'ane cikin kwanciyar hankali. Wlhy Alhaji ka farka daga nannauyan barcin daya d'aukeka, wato ka ciwo bashin kud'i a banki lokacin da suka baka Na kar6a yayi bakadashi ko? Saboda kakashe kud'in akan matarka da y'ay'an Sonka yanzu anema kabada kud'in ko kaddarorinka hankalinka ya tashi ko? Karasa ina zaka nufa matarka tabaka shawarar Neman bashi wajen Alhaji Garba. Shikuma dayake tsohon banzane kaje da buk'atar kud'i yabuk'aci musanyarsu da yarinyata saboda ta tsole idonsa, wlhy danasan auren manufa kayi da Jiddah ko sama da k'asa zata had'e baza'ayi aurennanba. Amma ko yan.............”
Wata razananniyar tsawa ya daka Mata yana mik'ewa a zabure, “Daga bakin wane mak'aryaci wannan zancen ya fito? Ko rantsuwa nayi babu kaffara nasan yahaya ne........”
“Kwarai kuwa nine?”. ‘Cewar Uncle yahya dayake shigowa yanzu’.
Daga Umma har Abba juyawa sukai suna kallonsa, fuskar Uncle yahya a matuk'ar d'aure yacigaba da fad'in “Wlhy ko'a mafarkina ban ta6a zaton rashin son gaskiyarka yakai hakaba Yaya, yanzu dan ALLAH har nawa Jiddah take da zakayi wannan kulla-kullar akanta? Ashe har mutane masu mutunci sukazo Neman aurenta amma ka shirya musu k'arya? Namaka magana ka gaggayamin son ranka, Anya Yaya kana tsoron gamuwarka da ubangiji kuwa?”.
“A'a bana tsoro dan Ubanka, shin komadai kaine Ubansu Jiddah ban saniba?”.
Daga Uncle yahya har Umma a tsorace suke kallon Abba.
Muryar Umma Na rawa alamar tahowar kuka tace, “Alhaji kana cikin hankalinka kuwa? Mu kake jifa da wad'annan munanan kalamin?”.
Shiru yay yakasa bata amsa saboda ya fahimci 6acin rai ya sakashi yin kato6ara.....
Uncle yahya yay murmushin takaici yana fad'in “Karki wani damu kanji da kalamansa Yagana, idan yamana sharri wannan yarage tsakaninsa da Ubangijinsa, dan shine zaimana hisabi, wannan kuma ni bazaisa naji komaiba saboda ban ta6a kwatanta aikatawaba koda a zuciya balle zahiri, ka saka a ranka kuma alhakin wad'annan bayin ALLAH kawai ya isheka ishara inhar baka rok'i gafararsu ba ka gyara mu'amularka dasu. Maman Nafisa ga magungunanki nan, ni nawuce gida”.
Uncle yahya nagama fad'a ya fice abinsa.
Umma ma tashi tai ta shige uwar d'aka abinta. Da sauri Abba ya bita.
Da sauri tace, “kaga fitarmin a d'aki zakari, idan kuma ni kake buk'atar nafita to lallai yanzu Zan barmaka gidanka tafiyarda har abada bazan dawoba koda hakan yana nufin Zan mutu da igiyar aurenka a kaina”.
Baki ya bud'e zaiyi magana tai saurin janyo hijjab d'inta “ALLAH ya baki hak'uri nizan fita”.
Bai jira amsartaba ya fice.

Duk abinda ke faruwa su walida naji, dan haka suka had'e kai a tsakar gida suna dirzar kuka.
Itama Umma yana fita tafad'a kan gado ta fashe da kuka maiban tausayi.


('('('('('('('('('('('

Tunda Jiddah ta koma sashenta taketa juya maganar hajia deluwa a zuciyarta, da mamakin kalamun saurayi da hajia ta Kira da Ashir Wanda take kyautata zaton d'ansune kenan. Lallai ita taga takanta, mutanan gidan kowanne da nashi matsalar....
Motsin dataji a bayantane ya sakata saurin juyowa, gabanta yay mummunar fad'uwa saboda ganin Ashir. Murmushi ya sakar mata yana matsowa gab da ita, “Auntyn mu gaisuwar bangirma nazo kawowa”. Yay maganar yana d'aga Mata gira d'aya.
Baya Jiddah ta matsa sosai jikinta harya Fara tsumar tsoro, Ashir ya kuma kwantar da murya tamkar yana gaban matarsa ko budurwa yace, “Wani ya ta6a fad'a miki kinada k'yau kuwa babie? Da sabon jini kika dace babie ba dad ragowar basirba, kizo nabaki dukkan farin ciki dan nine dai-daike nasan dad babu abinda zai iya miki wlhy, shegen aure-aurensane kawai da basa k'arewa......”.
Duk maganarnan da Ashir yake jikin Jiddah 6ari kawai yake, dan tsaf tagama fahim manufar Ashir a kanta, babu abinda takeyi sai Addu'ar Neman tsarin ALLAH daga shed'ancinsa, yayinda tuni hawaye sun cika Mata idanu. Ganin Ashir yamatso zai kamata yasata afkawa d'aki a guje Ashir ya take Mata baya..............
'<Øûß



=ØFÞ<Øûßturk'ashi, Uban ko d'an?.


*_Ammafa kun iya buk'ulu, irin wannan addu'a da kuke jama Maimuna kar Sheikh Ali ya angwance_*>Ø#Ý>Ø#Ý>Ø-Ý





*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*=Ø-Þ=ØOÞ<Øûß
[12/1/2019, 12:10 PM] =ØžÜNoorunnisa=ØžÜ: *_Typing=ØòÜ_*



*_=Ø¡ÜHASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=اÜMUTUM DA DUNIYARSA....!!=اÜ_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>ØÝ<Øûß_*


*_[16–'17]_*


..............Hannunsa daya kai zai rik'e k'ofar Jiddah ta had'a ta datse, take yasaki wata azababbiyar k'ara, yayinda zufa tafara keta dukkan sassan jikinsa.
Jiki Na rawa Jiddah tasaki k'ofar kafin ta lek'oshi, ganin ya zube k'asan kafet yana sakin wahalallen kuka da yarfe hannu sai hankalinta yay matuk'ar tashi, kamar zata fito saikuma taji tsoro takoma da baya da sauri ta rufo k'ofar....
Hakan yayi dai-dai da shigowar Hajia deluwa da gudu, wadda tundaga sashenta tajiyo ihun Ashir.
“Mami ta kasheni, ta tsinkemin yatsu mami..”
Abinda Ashir keta fad'a kenan yana birgima a k'asa da mik'ama hajia deluwa hannunsa.
Hannun nasa takama ta rik'e jiki Na rawa da fad'in “Ashir! Kai Ashir mitaimaka?”.
“Hannuna ta had'a da k'ofa mami! Mami kikaini Asibiti Karna mutu”.
Gaba d'aya hajiya deluwa tarud'e, da Sauri tafita tana kwala kiran direbansu, da taimakonsa suka fiddo Ashir daga sashen Jiddah zuwa harabar gidan.

Sosai hankalin Jiddah itama yake a tashe, sai faman tsiyayar da hawaye takeyi, jin fitar mota yasata bud'e k'ofarta, tasan kila suntafi asibitin, jinin daduk Ashir ya d'igar takebi da kallo wasu hawayen tausayinsa masu zafi sunabin kumatunta, data sani dabata guduba da waje ta fita, “Amma dakin tsaya ai zai tozartakine” wani gefe Na zuciyarta ya fad'a.
Zubewa tayi saman kafet d'in wajen tana kuma sakin marayan kuka da godiya ga ubangijin daya jarabceta da wannan rayuwa....
Ahaka Alhaji Garba ya shigo ya sameta, daganima sashenta yafara shigowa, dan rik'e yake da babbar rigarsa dawasu tarkace a hannu.
“Jiddah lafiya kuwa?”. Ya fad'a yana ajiye kayan hannunsa a kujerar dake kusa da ita.
A tsorace ta d'ago ta kallesa tana girgiza masa kanta, “Alhaji wlhy ba laifina baneba, bada gangan nayi masa hakaba ka yarda Dani...”
“Ban gane maganar da kike ba Jiddah? Mike faruwa? Jinin menene wanan?........
“Alhaji wlhy Ashir ne ya......”
“Yayi Ubanmi munafuka?”.
Maganar Hajia deluwa ta katse Jiddah, gaba d'aya suka maida kallonsu gareta. K'arasowa tai tana cigaba da fad'in “Wai Alhaji munafukar yarinyarnan dan kawai Ashir yazo gaisheta shine ta had'e hannunsa da k'ofa ta murje”.
“Ta murje kuma? Ke Jiddah akanmi?”.
“Akan mugunta mana da mugun hali”. ‘Hajia deluwa takatse Jiddah dake yink'urin yin bayani’.
Duk yanda Alhaji garba yaso jin ainahin zancen hajia deluwa ta hana hakan, dan Kiri da muzu tahana Jiddah yin bayani. Daga k'arshe sai fita sukayi zuwa sashensa akabar Jiddah Na hawaye. Acan hajia deluwa ta shiryama Alhaji garba karyar datakeso saida taga ya aminta sannan tabaro sashensa.

Tana dawowa sashenta malam Na marwa takira, a k'ufule tace, “Malam bazan iyaba, maza kasan yanda zakai da yarinyarnan wlhy, ni dama tuni Hindu ta tsoratani akan uwarsu datace ta nacema Ubansu dukda wulak'antatan da yakeyi, koma miye yazo kanka ka aikata Mata tabarmin gidana, yanzu haka harta gwada nakasamin yaro tunkan aje ko inama kenan”.........
“Kinga kwantar da hankalinki hajia, yinin yau gaba d'aya a aikinki nake, dama kobaki kiraniba ni Zan kiraki, gobe idan ALLAH ya kaimu ki aiko a kar6ar miki sak'o”.
Cike da d'oki Hajia deluwa tace, “Nagode sosai malam, harka saka zuciyata tayi Fari wlhy”.
Dariya yayi shima daga can.

Ashir dai ya bugu kam, dan hardasu karaya a yatsunsa biyu Na tsakkiya, farce d'aya ya fita gaba d'aya. bayan an d'orashi aka nad'e hannun da bandeji aka bashi magunguna da sallama.
Tunda suka shigo gidan yake Harar sashen Jiddah yana kunkuni, kai tsaye sashen hajia deluwa driver ya rakashi.
Sai wani sannu da tarairayarsa takeyi, “Sannu kaji Ashir, amma dai yarinyarnan muguwace wlhy, muna ganinta salaf-salaf kamar bazata iyaba”.
“Wlhy mami bazan hak'uraba saina rama, haka kawai kinsakani aikata Abu naje a banza an nakasani, to ayanzu naratse miki saina aikata Na gaske a kanta, naje da nufin Mata barazana tamin haka, to ta shirya Na gaskiyar kuwa w........”
”Kai wai bakada hankali Ashir! Ba Matar Ubanka baceba, banason halin dabbancifa”.
“To amma mami ai duk kece kikaja ko, dabaki turani mata barazanarba tayaya hakan zata faru? Ni koma kallo da zata ishenine? ALLAH kinji Na rantse saina fatattaka yatinyarnan kuma a cikin gidannan saidai dad ya koreni bayan nayi”.
Dafe kai hajia deluwa tayi, dama tasan Ashir akwai bak'ar zuciyar tsiya, duk maganar da take masa bai sauraretaba yafice fuuuu zuwa sashensu.

Jiddah kam bayan taci kukanta ta more tashitai ta koma d'aki abinta.
Bata sakejin motsin kowaba Na gidan har ta kwanta, sai a cikin barcine tad'anji motsi a d'akin, idonta ta bud'e kad'an saitaga Alhaji zaune yana latsa lap-top.
A tsorace ta tashi zaune, yad'an kalleta yana wani had'e fuska.
“Dama kin kwantar da hankalinki kin kwanta abinki, ni idanma mace Na jini a tsarina ko ta6ata banayi balle tunanin ra6arta”.
Badan Jiddah ta yardaba tazame ta kwanta, saidai dukta takura takasa barci, har kusan karfe d'aya taga yazo gefenta ya kwanta tareda juya mata baya, tun tana fargaba harta farajin saukar numfashinsa cikin gurnani.
A hankali ta sakko k'asa ta kwanta itama barci 6arawo yayta fusgarta har yay galaba a kanta.


*_Bayan kwanaki hud'u_*

Jiddah dukta kuma figewa saboda tunanin su Umma da fargabar halin datake ciki, bata sake had'uwa da Ashir ba balle hajia deluwa, Alhaji Garba kam yakan shigo mata da safe, da daddare kuma anan yake kwana, amma zai raba dare yana latse-latse a laptop, tarasa ubanda yakeyi, zamansa a d'akin yake sakata barci rabi da rabi saboda tsoro, shiyyasa dasafe saitaita zabga barci, ALLAH dai ya taimaketa yau yagama kwana bakwai ya koma wajen uwargidansa itama tasami sukuni.
Da wannan barcin hajia deluwa tasamu damar shigowa sashenta ta saka wani Abu a k'ark'ashin gadon Jiddah tun a randa tacika kwana uku a gidan.
Jiddah dai batasan mike faruwaba, yau bayan tayi sallar azahar tad'an fito falonta ta zauna, gaba d'aya batajin kwarin jikinta, saboda tunda tazo gidan bataci abinciba, kullum sai kayan kwad'ayin

1 Comments On MUTUM DA DUNIYARSA
avatar
rukayya-yahuza

1 year ago

Reply

Kai book dinnan ya hadu iya haduwa

Please Login or Register in order to submit comment