Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

HAKA ALLAH YASO S4 Yar Mutan Kankia

_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_



*Godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai daya bamu aron lokaci mai matukar tsada da muka sake haduwa daku a karo na hudu cikin littafin nan mai farin jini mai taken HAKA ALLAH YASO labarin Amina Caranci,inafatan Allah yasadamu da alkhairan dake cikin wannan labari ya karemu da duk wani sharri,yakarama annabi Muhammad SAW daraja da ahlilbaiti da dukkan sahabansa baki daya har zuwa tabi'ai da wa'anda suka bada gaskia har zuwa ranar saka mako,ameen*


S4/E1&2


Bankasance mai rakiba ko yawan butulci akan abinda Allah ya tabbatar da sai ya wanzu a gareni kuma nasan ita Jarabawar Allah ga mai imani kawai take tabbatuwa saidai cin Jarabawar abune mai matukar wahala sai ga wanda Allah yaso kuma ya saukakama hanyoyin da zaici Jarabawar da yaima bawan shi,nasan duk abinda ke faruwa dani *Haka Allah Yaso* kuma shi kadai zai kawo mani ɗauki a duk halin dana tsinci kaina yana sane dani,na dadi ko akasin haka,wannan dalilin kesawa ko ina cikin ƙunci nakanyi dariya duk da halin da nike ciki ya girmi jindadi ko nishadi amma na mikama Allah wahidilkahhar Sarki buwayi gagara misali kukana nasan shi zai kawo mani ɗauki a duk inda na tsinci kaina,bani da wata dubara sai abinda Allah ya tsara mani domin shikeyin komai yanda so ga ɗan Adam a lokacin dayaga dama nasan,a yanzun ma bai manta dani ba saboda *HAKA ALLAH YASO!*


_Rayuwa kenan ba yanda Allah bai Jarabtar bawa dan yaga girman imanin shi Ya Allah idan katashi Jarabamu kaimana wadda zamu iya dauka ka tsare mana imanin mu a duk inda muke,ameen_


*_AMINA CHARANCI kenan da rayuwa taima ƙunci a ciki Prison,Ya Allah ga baiwar ka nan ka kawo mata dauki👏🏻_*


************

Tunda aka shigo dani Kurmawa Prison hankalina yai matukar tashi musamman dana ga anbani uniform wani karamin ɗaki aka nuna mani na shiga na sauya kayana zuwa dark blue mai number ajikin su, saidai 22 shine last digit number kayan da aka bani.

Ina gama sawa Gandiroba ta tisani gaba zuwa wani ɗaki dake dauke da mutun ukku,nice cikon ta hudun su,ana budewa akasa na duka nakurɗa cikin shi gabana na duka fat fat fat,ban taba tunani rayuwata zata sauya zuwa irin wannan rayuwar ba da nike kallo yawanci a film din kasashen waje yau gani ni Amina Yusuf Caranci a cikin Prison na ƙwaryalwaryar birnin Kano babban Prison din su.

Fadin tashin hankalin da nike ciki bai misaltuwa saidai tashin hankalin rasa HUSNA danayi ya girmi musibar da nike ciki.

"Ke."
Wata matashiyar mace ta kwada mani kara bisa kaina ta kirani da Ke

Kallo ɗaya nai mata na sauke kaina kasa dan alokacin zuciya ta ke ƙuna hoton Asma'u ke mani yawo cikin zuciya ta,musamman dana isketa kwance cikin jini lallai wannan abune mai matukar tashin hankali a gareni inama hukunci da aka yanke mani ta hanyar ratayane dana huta da ƙuncin rayuwa irin wannan.

"Ke dan gyatumar ki,baki zuwa kikawo gaisuwa wajen shugaba shine zakizo ki samu waje ki zauna sai kace ta Allah."

Jin kalaman matar da naji sun kira da Mairo su sukasa hawayen da suka ƙafe a idanuna suka ziraro mani masu ɗumi.

"Ku kamo mani ita nan,muyi mata wellcome to gidan Yari gidan Ɗan Kande duk wanda yazo nan saida ya shirya."
Cewar wadda suke kira da Sarauniya,kafin in ankara sun kinkimoni hannuna da kafata sukai mani sharga sharga zuwa gabanta niko sai wullewulle nike suna ajeni gaban ta na kifama Mairo mari raina a bace.

"Kai dan gyatumin Yarinyar nan dole yau mukoya mata hankali tasan tarabu da duk wasu masoyanta dole taima *Cankwai* biyayya ko adauki buzunta Mairo kama mani kafarta,ke kuma Salame rike hannun ta ku ɗage mani ita."
aiko haka akahau kiciniya dani aka ɗagani sama,a kalkashi gadon su,na karfe ta zaro bulalar geza ta dinga shauɗa mani ita bisa gadon bayana zuwa mazaunai na,sai wullina nike tabbas inajin zafin saidai tension din da nike ciki ya girmi kagane bala'in dukan da Cankwai ke mani aikin wulle wulle nike kwalla na zirara bisa kuncina hakan yasa tace a barni nafara kuka suka sakeni da kyal na zauna duk mazaunaina sai zugi suke mani.

"Maza kiba shugaba hakuri ko asake maki na jaki kuma sai mun tubeki zamu zaneki."

Dago idanuna nayi kamar garwashi nace yi hakuri.

Abinda ya isheni ya isheni kuma na fahimci ita rayuwar nan daga inda akace ga mutun gidan Yari tabbas kwanan Alkiyamar shice ta tsaya domin kamar rayuwar kace,aka datse ka rabu da iyayen ka Yan uwanka dangin ka da duk wani masoyan ka na gaskia dole rayuwa taima Yan gidan Yari kunci.

"Ke miye sunanki.?"
"Aminatu."
nace muryata na rarrabewa.

"DA'GO zakice Malama daga yau sunan ki kenan kinajina.?"
"Eh naji."

"Laifin uban mi kikayi kikazo gidan Kaso."?

"Aminiyata na kashe."
Nasamu kaina da furtawa duk da saida na faɗa naji abinda nafada din.

"Kai amman anyi matsiyaciya marar imani duk kin fimu rashin imani tunda har kika iya kashe masoyiyar ki,gaskia Dago kinci amana,kusa ke ɗaga mani ita inci Ubanta."

Ban musa masuba haka takara zaneni sannan suka sakeni daman ance Sarkin yawa yafi Sarkin karfi dole na mika wuya inaji ina gani.

"Azzaluma to koni da nike shugabar mata ban wannan rashin imanin irin nakiba,domin zuwana gidan yari na farko kishiyata na datsema harshe saboda na gindaya mata sharaɗi kada ta kwanta da mijina amman na iske tana mashi kiss shine na yanke harshen ja'ira.

Zuwana na biyu kuwa Uwar mijina naima dukan mutuwa saboda katsalandan a cikin al'amuran mijina aurena na biyu kenan.

Zuwana na ukku kuwa Kanwar Baba na zane dan ta zageni danni ba mahalukin da zai zageni in kyale shi koda kuwa gyatumi ne.

Zuwa na hudu mijina na kusa kashewa zuba mashi guba nayi danma Allah yasa bai mutuba saboda nace yabani kudi yahanani,aurena na ukku kenan saida nayi shekara bakwi gidan Yari

sai wannan karan kuma wanda ba fita domin mijina na hudu yakawo mani budurwa abokin dandina har cikin gidana duk da kar tasan karce, ni kuma nagaza hakura duk na kashe su,kinga ko ai nafiki imani tunda ni kisan danayi amanata akaci amman ke kika kashe aminiyar ki da hannunki kin zama cikakkar butulu kinci amanar aminci."
Cewar Cankwai ta ida maganar tana dungurina,tace.

"Ke kuma Mairo gaya mata dalilin zuwanki gidan Dan Kande."
"Ba wani abu bane ya kawoni gidan nan ba, kishiyata na bankama wuta ta mutu dan kawai ta daukar mani magin miya alhali ba ranar girkin tabane,kuma bata nemi izinina ba minene laifina dan na rage mugun iri a cikin duniya aiko a lahira ban fatan sake zama da kishiya."

Nidai da idanu nike binsu naga tsantagoran yan bariki ni kuma haka rayuwa ta juyamani wannan shine tsakiyar rayuwar mai wahalar gaske.

"Kema Salame gaya mata naki labarin."

"Sanadin faɗa da kanwar kishiya har na tsige mata kunne jini yaita shatata daganan ta margaya barzahu shine fa nazo nan shekara ta goma kenan cif,dan haka kema ki shirya tsaf kinzo kenan ba fita mune uwarki mune ubanki mune dangin ki,ko biyayya kikai mana sai kinci na jaki. gidan nan ba wanda baisan Cankwai ba,da 'yan ukku bala'i gwarama ki daina kukan munafuncin da kikeyi tunda har kika iya kashe aminiyar ki wannan zaki iya komai su balama anyi asarar kunnuwa ga kyau kamar tsada saidai ba kyawun hali tir dake mugun halin ki Dago."
ta sake ran kwashina akai sai tsinata sukeyi,nidai kuka nike kamar raina zai fita ina ayyana girman aminci har waɗannan marassa imanin sunsan girman dake tattare da aminci ina gani,inalillahi wa'inna ilahirraji'un Allahma da kanshi daya halicci amana mala'iku da sauran halittu gaza daukar ta sukayi hatta kasa,sai mu yan adam muka dauka ina zankai girman amana,kauna da soyayya mai karfin gaske dake tsakanina da Husna ya mutanen garin mu dana duniya zasu kalleni in akaji da bakina na aminta ni na kashe Asma'u,taya zanyi da bakin mutane akaina gashi wadannan basu sanni ba basu san amincin dake tsakanina da Husna ba,amman sun tsinema halina inaga wadan da sukasan wacece Asma'u a wajena ya muke da junanmu lallai kam rayuwa inba Jarabawa bata cika cikakkkar rayuwa,Ya Allah kadauwamar dani nan Ya Allah kajikan Asma'u kayi gaggawar bi mata hakkin ta ka jibin rayuwar marayun data bari inalillahi ni Aminatu ya zanyi da rayuwata.

"Babu yanda zakiyi da ita ja'ira zoki danna mani kafafuna maciya amana kinbani dani ban kara ɗaga maki kafa tunda harkika iya kashe aminiyar ki,waima dan ubanki akan mi kika kasheta."?

Akan dukiya."
Nace atakaice kamar yanda aka rubuta a statement dina banda niyar canzawa nasan ta Allah itace daidai namu shine bi.

"Kutumar Uba akan dukiya kika kashe kawarki aminiyar ki gaskia Dago kedin kin cika mai busassar zuciya."

Kafa tasa ta halbani tace.
"Kikaimani wuƙi wuƙi da idanu kamar na mujiya dan uwarki cigaba da danna mani kafata kafin dare in sake daurayeki tas da bulalai tunda baki da imani kin samu daidai ke duk da naki yafi namu amman munsan hanyoyin cuzguna maki yar banza munafuka."

Cigaba da danna mata kafar nayi ina hawaye kamar ruwa ba abinda suke mani bane,ke bani haushi ba,aaa ina hango girman rashin danayi na aminyata Asma'u,nasan na cancanci azaba agaresu tunda har zan iya aikata abinda suke mani kallan na aikata duk da nina fadi hakan da bakina,wannan kenan.


*Caranci*

"Ina bakin cikin ganin wannan ranar inama mutuwa nayi na huta da ganin wannan bakin ciki ni Yusuf yau nine ya'ta mafi soyuwa a wajena itace garkame a gidan Yari ni gani a gida inama ban kai wannan lokacin ba,wai Aminatu ita aka yankema hukuncin kisa,arasa wanda za'ace ta kashe sai Asma'u inalillahi wa'inna ilahirraji'un.
Tabbas bazan taba yarda Mamana zata iya kashe dabba ba bare kuma Asma'u wanda kowa yasan alakar su.!
Lallai Aminatu bakiyi dacen Uba ba,nagaza baki farin cikin ki nakafe na rabaki da duk wani farin cikin ki aganina ina maki gata ashe ba haka bane,miyasa na biye ta Alhaji Mukhtar muka dage sai munraba tsakanin ku da Taufiq miyasa na biyema zuciya ta,na rabaki da jinina Hussein dan kawai wani dalili namu marar tushe gashi munfarraƙaƙu,yanzun haka ba wanda yake da tabbacin Hussein yana raye ko ya mutu Allah masani."

Kuka Baba yasake saki mai tsuma rai sannan yaci gaba da cewa.
"Ga ya'ta a gidan Yari daurin rai da rai shikenan narasa ya'ta bani bata ban kara ganin ta,na cuceki Aminatu da nagaza yi maki uzuri a rayuwata kinmani biyayya matukar biyayyya amman ni Yusuf na gaza cika maki burin ki inalillahi wa'inna ilahirraji'un Allah ka kawo mani mafita Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan minha."

Kuka suke baki dayan su dakyal Ahmad yace.

"Baba tabbas ba aima Anty adalci ba katabbata batazaƙi zabinkaba, koda ace da Ya Taufiq take waya, yaka mata ace kaji nata uzurin amman Qaddarace ba yanda zamuyi kuma haka Allah yaso."

"Ahmad kudaina ɗaura laifin nan kan kowa Allah yagama tsara komai dole sai Aminatu tayi gidan Yari,ni ba wannan yafi damuna ba rashin Asma'u yanzun zamu gaza sukuni a cikin jama'a da mun fita za'ace Yarmu ta kashe aminiyar ta,wane abune yafi wannan ciwo gashi abin takaicin da bakin ta,ta amsa laifi tace itace ta kasheta,yanzun mike garemu,Allah Sarki ƴata kiyi hakuri Aminatu mun gaza taimakonki *Haka Allah Yaso*"
Cewar Mama dake kuka kamar ranta zai fita.

Haka mutane akaita zuwa yi masu jaje wasu kam badan Allah suke zuwa ba.

Agidan su Husna kuwa zaman makoki akeyi gobe ake sadakar ukku gwanin tausayi lamarin ga ya'yan ta saibin kakar tasu, suke suna ina Momi musamman Minah dake kuka dayake tafi Haidar wayau sosai.

"Mama kikaini gun Momi na,tabani Sweet."
Irin wadannan maganganun suke dagama Mamar su Husna hankali hakama Mamanar su Minal intazo zaman makoki suke tada mata hankali duk da tazama bora abin hantara ga jama'a ana zaman makoki amman bai hana ai mata habaici ba saidai tayi kuka ta gode Allah saidai cikin ikon Allah iyayen Husna sun dauki Qaddara sun tabbata Amina baza taba kashe Asma'u ba saukin kenan ko ana maganar sune na farkon karyata lamarin saidai kunsan yawan maganar baida dadi,kuma haka mutane suke basu da gadonka sunada gadon maganar ka.

Haka rayuwa ta kasance hatta Abba da Mum su Tariq,Fatash duk sunzo dasu akai zaman makoki sosai suka tausayawa iyayen Husna halin da suka shiga dan Abba yai masu ihisani dan kusan abinda akaci na gaisuwa shi ya dauki nauyin shi daman halayyar mutane kenan, kana mutuwa sai afara ta ciki wani addu'ar ma bazai makaba saidai azo aci abinci Allah yasa mudace.

Rayuwa ba dadi ta kowane bangaren guda biyu gidan su Husna da Minal wanda suka zama yan uwa dangin juna masoya kuma aminai na hakika wanda suke sadaukar da farin cikin su dan cikar burin dan uwan su,sai ga yanda Allah ya hukunta wanda yake zartar da komai a lokacin dayaso yagama dama ga yanda yaso da Minal,Allah yabata ikon cin jarabawar da yai mata,wannan kenan.

*Prison*

Tunda gari ya waye babu abinda mukeyi sai.......

*Yar Mutan Kankia dan girman Allah kitaimaka ki cigaba da yimana posting din Haka Allah Yaso dan darajar Sayyidina Rasulillahi kitaimaka mana,wlh da labarin nan muke kwana muketashi dashi a ranmu munajin labarin nan na ratsamu musamman darussan dake cikin shi, pls Anty Jameey.....*


_Ire iren waɗannan maganganun da masu kirana waya duk akan cigaban book din nan, har masu magana ta Dm to kusani Yar Mutan Kankia taga sakonku saidai kamar yanda nace maku tabbas banda lokacin posting ina busy dayawa shiyasa amman duba da yanda akeson cigaban labarin nan insha Allah zakuna samun posting koda bani nayi post din kai tsayeba sannan ku dinga share dan saura su_ _samu,Comment dinku shi zaisa ku dinga ganin posting akan lokaci._

*Nagode da addu'oinku agareni na fatan alkhairi duk nagani kuma nagode Allah yabar so da kauna,ameen kardai ku manta.

_Yar Mutan Kankia ce❣️_
Share
Pls
❣️

_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E3&4




Tunda gari ya waye ba abinda muke sai jidar kattin duwatsu muna kaiwa cikin wani katon fili mai girman gaske ga rana ana kwalawa dan danan jikina ya saki zafi da kuncin da nike ciki suka bigeni ina cikin tafiya na rafka uban tuntube na fadi,ina tare da Shugaba Cakwai daka mani tsawa tayi har saida yan cikina suka koma gama gefe daya dan tsorota da nayi.

"tashi munafuka kinsan kina gudun wahala kika yarda kikazo gidan Ɗankade kadan kikagani indai rayuwar yari ce.
ba abinda kikagani da kanki saikin tsani kanki da kanki,yar banza maci amana."

Jini ke zuba a kafata amman gudun kada tasa a dagani ta bigeni dolena na mike ba wani dressing da zan samu duk da nasan girma da darajar treatment saidai yanda rayuwa tazo haka ake binta,nima tawa rayuwar kenan.

Haka muka wuni ana abu daya har nagaji saida aka kira salla mukaje mukayi salla sannan mukaje inda ake raba abinci muka ansa.

Yunwa nikeji sosai kamar zata halakani saka hannuna nayi cikin kwanon tasar dake gabana na dibo lemor shinkafa jellof wadda bata da banbanci da farar shinkafa naci saidai ina sawa bakina kamar zanyi amai haka naji,lallai kam gidan Yari azabar duniya ce, take rayuwa ta dawo mani sabowa ina tuna sanda nike gaban iyayena kaci abinda kakeso amman nan abincin kamar mutun ya roko gashi ba dadin gaba ba na baya,hawaye suka tubomani sai ji nayi an fusge kwanon hannuna.

Mairo ta juye cikin abincin Cakwai tana hararata dan dole na sauke kaina ƙasa nakasa magana.
banda yunwa ba abinda nikeji gashi loma daya nayi an nuna mani fin karfi an kwace.

Miko mani kwanon tayi tana cewa kilbibi kowa ya cinye nashi cikin sakanni sai ita zata tsaya yaguna mabukata sun karbe ke kuma cikinki ya gaya maki ai yunwa ba kanwar uwarki bace bare ta Ubanki munafuka."

Araina kuwa ina mamakin halayen mutanen da Allah ya haɗani dasu iyayena kuwa suna shan zagi ya zanyi tunda Haka Allah Yaso ya ganni saidai in gode mashi.

*Minal ina fatan Allah ya nuna mani ranar bikin ki sai nafi kowa farin ciki musamman idan kika auri Ya Taufiq shikenan rabin burina gayama cika na duniya kawata*

Na afka cikin tunani musamman maganganun Husna naji ance

"Ke tunanin uban mi kikeyi tashi dibo mani ruwa inyi wanka."
mikewa nayi wanda nagama lulawa a cikin tunanin maganganun da Husna take yawan yimani gab da ajalinta ashe tafiya zatayi tabarni ashe dagani har ita ba rabon kowa yaga wannan ranar da take da burin gani wanda nima agareni hakan take,daman rayuwa mutun yana tashi Allah na nashi ta Allah itace daidai.

Haka nagama dibo ruwa duk sukayi wanka sannan nasamu nima nayi wanka kayan jikina sudai na maida.

Ana la'asar nahau sallah najima ina rokawa kawata gafara da rahamar ubangijin talikai inaji inama awayi gari nima nabita inda ta tafi kona huta da azabar da nike ciki.

"""""""Yau ake sadakar Ukku kofar gidan su Amina da Husna cike yake da dan Adam anata addu'ar rahama ga mamaciyar,katuwar kula Ahmad ya fito da fanke a ciki daddaure a leda yafara rabama masu addu'a saidai duk wanda ya mikamawa sai suƙi amsa masu kar6a kadan ne tsabar tsana da kiyayyar da ake masu tunda lamarin ya faru sun zama mujiyoyi a cikin tsuntsaye.

Wani Saurayi ya mikawa saida ya amsa shida abokan shi suka hau jifar shi da ledar fanke suna cewa.

"Bamuci akai bola abincin annoba yarku ta kwaso abin kunya ta kashe kawarta aminiyar ta,shine harda biyomu da wani munafukin fanke wato ga mayu dagani wannan fanke na murnar mutuwar Asma'u ne kukayo bana sadaka ba."

"Haba bawan Allah waya gaya maka Aminatu zata iya kashe Asma'u."
Cewar mahaifin Husna

"Ita da bakinta ta faɗi hakan ai shari'ar a gaban idanun mu akayi ta,inama taba shari'a wahala anyi hanging dinta cin amana baida dadi."

"Ka iya bakin ka bakasan shari'a sabanin hankali bace insha Allah sai Aminatu ta dawo garemu ita kuma yar uwarta mun dauka kwanan tane suka kare muna mata fatan alkhairi Allah ya karbi shahadar ta."
Ameen Baba cewar saurayin.

"Rabu dashi gaskia ya fada ai duk wanda yaje Kotu kowa yaji Aminatu da kanta ta amsa laifin ta dole ace itace ta kashe Asma'u."

"Haba Alhaji Yusuf kaima baka yarda da yarka ba kenan kana zargin ta ne.?"

"Ko daya bamu da za6i sai muyi riko da Jarabawar da Allah yaimana kuma kadafa ku manta duk abinda dake faruwa haka Allah Yaso akanmi bazamu dauki dangana ba."

"Mun dauki dangana saidai ni bazan gaji da karyata duk wanda zai furta wannan kalmar agaban idona,tayama kai zai dauka ace Amina zata kashe Asma'u.?"
Inji mahaifin Husna

"Shikenan Allah ya bamu ikon cin wannan jarabawar."
"ameen ya Allah."


*******Dare ya tsala wajen karfe ɗaya amman ina rakube jikin bango su Cankwai,Mairo da Salame duk sun kwanciyar su bisa gadon su na karfe irin dai na boarding amman nawa gadon an hanani in kwanta ga katifa an jefa sama amman ba damar in kwanta dokace daga Cankwai bazan fara kwanciya akai ba sai nayi wata ukku su basu hada makwanci da maci amana.

Kuka nahauyi kamar raina zaibar gangar jikina wani irin sanyine ya shido mani lokaci daya dan dole na kwanta kasa bisa wani kwali da muke sallah akai sai kyakkyarwa nike banda wani abu da zan rufe kaina dashi dagajin yanayin sanyin da nikeji take nagane zazzabine ya rufeni ga yawan tunani dana jefa kaina da ace za'a gwadani tabbas na kamu da hawan jini mai karfin gaske.

Tunani kawai nikeyi rabi da kwata na Asma'u ne kadan ne nike tunanin kalar rayuwar da zanyi a Prison taya zaman nawa zai kasance shin dagske nan zan dawwama saidai amaida ma iyayena gawata?duk wahala dana sha abaya daman banda raban cika burina Oh! Allah kasa wannan Jarabawar da kai mani tayi sanadiyar shigata aljanna rabbi na tuba kayafe mani.

Ban bacci sai karfe ukku na dare sannan baccin wahala ya daukeni.

Ina cikin bacci naji an tafka mani uban bugu a baya a razane na tashi sai raba ido nikeyi zuwa lokacin ko jikina ringis yake da zazzabi mai wahalarwa.

"Kika kafeni da idanu na munafukai zaki tashi kokuwa saina sa anmaki wanka da ruwan sanyi yanzun nan."

"Mikewa nayi da salati dauke a bakina mukayi sallah ina zaune inda nike ina lazumi."

Cankwai ta koma ta kwanta tasani danna mata kafa har tayi bacci,daga zaune na kife kaina gefen gado bacci ya kwasheni takwas daidai Gandirobas suka buɗemu muka hau aikin mu,wannan karan shara nayi wasu kuma suna wanke toilet.

Muna gama aiki na samu gefen inuwa na zauna na buga uban tagumi,wata matashiyar mace ta zauna gefena duk da ta girmeni itama kana ganin ta tana cikin damuwa kallo daya nai mata na kauda kaina gefe.
"Baiwar Allah sannun ki."
"Yawwa sannu."
Shiru ta kumayi sai kuma tace.
"Dan Allah minene sunan ki.?"
"Aminatu."
"Ni kuma Nusaiba"
"Dan Allah inasan muzama kawaye inba damuwa."

Kallanta kawai nike taya za'ayi wata abota agidan Yari aini tuni narasa kawa kuma ban tunanin ni Aminatu zan iya sake wata Qawa a rayuwata ta duniya.

"Kiyi hakuri ban bukatar wata kawa nagode da kulawar ki agareni."

Duk da fuskarta ta nuna rashin jin dadin hakan saidai ban damuba tunda iyakar gaskia ta na fada mata.

Wasa wasa yau kimamin watana guda gidan Yari ba wanda yazo mani Visting,duk da nima bani bukatar sake ganin kowa a tare dani nasan hakan zai kara tado mani tabon dake cikin zuciyata wanda nasan warkewar shi agareni abune mai wahala.

Yauma abinci muka anso saidai ban bari Cakwai ta anshe mani ba ninaci abuna zuwa yanzun tun banjin dadin cin abincin gidan harya bimani baki wasu na mashi hadi saidai ni banda shi bare in mashi daga shi sai halin shi nike cinshi ko Nusaiba ta bani ban yarda in karba saidai ince nagode.

Haka rayuwa taita wanzuwa da kalubale iri iri na rayuwa kowa

Please Login or Register in order to submit comment