Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar kullin mafarkin daine na afka.

Aminatu yaushe kika susuce har haka kika bari kowa ke wulakantaki son ranshi tashi kigayama Allah kukanki sannan duk wanda yai maki kirama tashi kiyi sallah kawata bacci ba naki bane.

Zufa tagama wankeni na tashi miyasa nike yawan mafarki da Husna anya badan nasama raina ita bane badan nasa itace gatana ba,mai kaunata a koda yaushe itake bani shawarwarin da suka dace dani, mai sona.
Inaga wadan nan abubuwan su suka taka rawa wajen yawan mafarkai na Husna da nikeyi a kullin idan a farke nike tunaninta shine abincina alwalla na tashi nayi sallah ina addu'a ina kuka.

Saidai wani ikon Allah tinda nazo gidan Yari hatta Period dina kamar anmani mugun abu kaf ya dauke banayin shi sam,nikam hakan yai mani dadi dan bansan ya zanyi da lalurar shiba a halin da nike ciki.

Bayan kwana biyu Atika tazo kirana wajen da ake ganawa da yan gida,kwata kwata natsani ace anzo ganina bansan inga yan gida badan nayi blaming kowa a halin dana tsinci kaina ba saidai nasan haka Allah ya hukunta akaina,ganin su na maidani baya tsohon tabon zuciyata yakan dawo danye sai nayi jinya sosai kafin na dawo daidai wannan shine babban dalilin dayasa bansan ganawa dakowa amman banda wani zabi.

Ina zuwa Shugaban wajen yace arakani cikin minti goma shima dan wadanda sukazo sunnemi wannan alfarma gabana nadan bugawa kadan na isa inda katanga tadan rabamu amman muna ganin juna har yar uwarki macece zaku iya rungume junanku.

Tsaye nayi cak nakasa daga kafata bare in isa wajen su,Atika ce ta rikoni har wajen su, hawaye sukafara sintiri a kuncina

"Ya'ta."
shine abinda Baban Husna yakirani dashi.

Take wani irin kunya da nauyin su suka dabaibayeni musamman Mama itama hawayen takeyi.

Riko hannuna tayi cikin nata tace.
"Ɗago ki kallemu Aminatu,karkiji nauyin mu kinji."
Ɗagowar nayi na kalleta nakasa control din hawayen idanuna,idonta cikin nawa saidai kallo daya zakai mata kagane tsantsar so da kaunar da take mani irin na ɗa da mahaifi.

Mamar Asma'u macece mai kawaici kara gabata da hakuri Allah yaimata sanin yakamata shiyasa da dama nakan iya gaya mata matsalata ko shawarata batareda mahaifiyata tasani ba,domin itadin uwace agareni.

"Aminatu kukanki zai ƙara karya mana guiwa munzo dan ganin lafiyar ki,amman kuka bai kamace kiba ya'ta addu'a ita zaki yawaita yi Allah yai gaggawar tona asirin wanda ya kashe Asma'u,amman wlh ni nayi imani da Allah bazaki iya aikata wannan abunba koda amafarki ne,saidai miyasa kika amsa laifin da bakisan kin aikata shiba?"
Cewar Baba.

Kaina na sauke ƙasa nace.
"Kuyi hakuri kuyafe mani koma mi yafaru laifinane nasan najefaku cikin tashin hankali da kunci saidai haka Allah yaso ni kaina Baba bansan mi zance game da wannan abun ba kudai kuyawaita ma Asma'u addu'ar rahama ni kuwa nasan nan zan dauwama dan Allah duk lokacin da aka kawo gawata gareku, ku sanarma duniya bani na kashe Husna ba, wataƙila kona samu masu sallatar gawata,inada yaƙini matukar zan mutu a wannan yanayin mutane da yawa bazasuzo kan gawata ba,saboda a idon su nazama maci amana,azzaluma wadda ta kashe kawarta yar uwar ta kuma aminiyar ta da hannun ta,kaicona dana kasance cikin azzalumai."

Sosai nike kuka mai sauti hakuri suke bani.

"Aaaa Aminatu keba azzaluma bace,ko za'a kwana ana gayamana kece kikai wannan laifin mu iyayen Asma'u zamu shekara muna karyatawa kedai kada ki fiddarai da rahamar Allah danshi gafururrahim ne."

Jinjina kaina nayi inajin haushin kaina da kaina dana amsa laifin da banawa ba gashi kowa ya tsaneni bamai kaunata inama daga Kotu ratayeni kawai akai dana huta da challanges na rayuwa.

"Baba kayafe mani dan Allah nasan dole kuji haushina idan ana dangantani da kisan Husna."

Rike hannayena yayi yace.
"Kidaina kuka ya'ta mu iyayen kine da Asma'u ba ita kedin tamuce bamu taba sauyaki saima kara kaunarki da mukayi domin kin maye mana gurbin Asma'u,kuma bazamu gusheba muna nema mata rahamar ubangiji ba,ke kuma muna addu'a Allah ya wankeki daga wannan mugun tabon da aka yaba maki wai wuyar wankuwa."

Kuka nike narasa mi zance tausayin su ke kara ratsanani tako ina inajinsu har cikin zuciya ta amatsayin su na iyayena.

Mun danjima dasu har abinci suka kawo mani saidai ka'idar gidan ba'aba prisonors abinci har sai wanda yakawo yaci na mintoci sannan kuma ba kowane kalar abinci ake karba ba,Atika tace mana lokaci yayi sai lokacin Mama tafara kuka hannunta cikin nawa Atika ta janyeni inaji inagani suka tafi sunajin tausaina so da kaunata haka nakoma cikin gidan kurkuku gida marar dadi wanda ke dauke da tashin hankali da kalubale na rayuwa ba wanda zai iya baka labarin shi sai wanda yataba dandana abinda ya kunsa.

Washe gari dana tashi baki daya jikina ke mani ciwo katabus ban iyawa karfin hali kawai nikeyi amman ni kadai nasan yanda nikeji.

Mairo da Salame sai wani cika suke suna batsewa sukai su dawo haka suketayi suna nunaman isa da gadara kallo daya nai masu na watsar gyara kwanciyata nayi,na rufe idanuna kamar mai bacci naji sun,tabka mani bugu a firgice na mike zaune,saketabka mani bugu Salame tayi abaya.
A sauko nan ba dakin gyatuma bane aje ayi mana dibar ruwa zamuyi wanka.

Wani irin bakin ciki ya tokare mani makoshi duk irin wulakancin da sukai mani wannan yafi tabamani rai.

Fara jawoni tayi bisa Up na gado,rike karfen nayi gam ganin tana iya jiman ciwo,itaki tanata fizgoni nasa kafata na halbata sannan na diro bisa gadon,na tsaya bisa kafafuna na kama kasa.

Ina jifanta da wani mugun kallo.
"Kaikai dan ubanki ni zaki halba dan kina yar isaka."?

"Eh an mareki ko kinada abinda zakiyi.?"
Un-expected na furta hakan.

"Kam bala'i da yan ukku bala'i kike sa'insa."
Cewar Mairo.
"Ni kuma da Yar ɗaya kata'i ba."

"Ci kutumar uwarta Salame kafin in sauko bisa gadon nan."

Gada gadan Salame tayo kaina ta kawo mani wani irin naushi na rike hannun ta na wanketa da maruka biyu lafiyayyu.

Taga taga ta tafi zata kife ƙasa ta sake yowa kaina,nima kanta nayi muka fara faɗa. sungumarta nayi na gwadama Allah na azata kasa nahaye ruwan cikin ta naita ɗuma ina marinta sosai nike dirkar Salame,shako wuyana ta baya Mairo tayi tana dukana,guiwar hannuna nasa na daki.....

_Yar Mutan Kankia ce❣️_
Share
Pls
❣️

_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E9&10



guiwar hannuna,nasa na daki cikinta da karfin tsiya har saida ta fadi kasa tahau ihu.
"Wayyo Allah na ta kasheni kutaimakeni."
Shine abinda take cewa.
niko bugun Salame nike sosai ga dakin mu garkame da kwado sai ihu sauran yan Yari keyi hakan ya jawo attension din masu kula damu.

Da sauri suka iso Atika keta kokarin bude kofar kamar batason budewa dan dagayya ta tsaya nawar budewa.

Ingijeni Salame tayi ta rarumi hannuna ta gartsa mani cizo kwala kara nayi mai razanarwa nasa hannuna naita bugun mata baki harsai da ta sakarmani hannu yayi jajir duk jini ya kwanta nasha wahala fitsarine kawai banba,ganin yanda taiman da hannu a harzuke na sake cakumar ta fuska kawai nike noshi,Atika ta janyeni gefe sai haki nike kamar nayi dambe da katti ukku.

Kuka Salame kawai take hatta fuskar ta kumbure suntum musamman bakinta.

Itako Mairo tana kasa magashiyan ta rike ciki sai raki take tana nakasheta ta shiga ukkunta.

Fiddomu akayi waje cikin rana Despline yazo ya tambayi ba'asi anaganin su Mairo aka kori karar akace suma suji inda dadi yau Allah ya aramani rana.

Harara kuwa nashata kamar idonsu zai fado,bude kowa akayi akafito aiki sai yaba mani ake.
"Kin kyauta da kika ragargaji shaggun nan daman sun matsamana da ukuba kullin sai sun hanamu sakat a gidan nan inama Cankwai kika buga aida munfi jin dadi amman ajuri zuwa rafi angaishe ki Dago."

Jinjina kaina nayi inajin wani sukuni na musamman,da Allah yasa na bugi Salame.

Saidai Dagon da suke cemani banjin dadinta sam amman da bala'i saidai Cankwai ta samani Dago.



********
"Yusuf naga shirun nan yayi yawa akan Aminatu ace ba wani labari kaf zuriyar mu zamu zira ido laifin daba nataba ya tabbata akanta kenan kana ganin hakan ya kamata?"

"Haba Umma inba saka idoba mi zamuyi ita da kanta tace ta amince ita takashe Asma'u ni mike gareni baki ganin idan natashi nace zanja wannan karar akan rayuwar ya'ta mi iyayen Asma'u zasu gani su da suka rasa yarsu fa mi sukace."?

"Aaa karkai masu muguwar fahimta mana ninasan iyayen Asma'u basu taba cewa haka,
kowa ya tabbata Amina bazata taba aikata wannan abunda ake zarginta dashi ba."
Cewar Mum.

"Umma ki kula da case din nan bafa zarginta akeba ita ta amsa da bakinta."

Kallan shi Hajia Maryam take,ganin da gaske yake bazaibi kaidin hakkin Amina ba,aganin shi kar ace bai damu da mutuwar Asma'u ba ta yarsa yake,wannan alkunyar itace zata cuci kanin nata.

"Naji ninasan abinyi bazan saka idoba inaji inagani rayuwar Aminatu ta salwanta koda Asma'u ce ake zargi da kisan Amina wlh sai inda karfinmu yakare yanzunfa wajen wata nawa da daure Aminatu sai kace bata da kowa a duniya."

"Yanzun mi zakiyi karkije kiyi aikin dana sani Umma."
Ba ruwanka tunda kai kace bazaka iya komai ba aini zan iya."

"Hakane Umma gaskia nima dan ba yanda zanyi shiyasa na hakura,ba abinda banyiba amman yahana zuwa ganin ta wai zamu tada mata hankali."
"Wannan ba hujja bace ki shirya jibi insha Allah Tariq zaikaimu."

"Aaa ai ba kowane lokacine ake ganin suba mubari sai Next Week lahadi sai muje ganin ta."

"Allah yakaimu lafiya."
Ameen."
Ba yanda Baba ya iya yasa ido.



Yau aka saki Magajiya Cankwai kana ganinta kasan ta wahalu duk inda zata gitta kai kasa kowa ya noke nashi, gudun kada ku hada ido kashiga wani bala'in.
Daki ta tafi tareda su Mairo suna take nata baya.
Ina hangen su sun hade kai da alumu mugun kuduri suke dauka akaina kallan bazan da suke watso mani kadai yasa jikina yin sanyi,kasa shiga dakin nayi ga yamma tayi gandirobobi sun fara rufe dakuna har akazo dakin mu shiga nayi aka rufemu sai kuma safe.

Jiki a mace na isa zan hau bisa gado Cankwai ta cafko kafata na diro ƙasa tace.
"Ubanwa ya baki ikon hawa bisa gado."

Kallan Up and Down nai mata,bance komai ba.
Sai Mairo dake magana kasa kasa itada Salame tana fama da bakinta kamar shantu.

"Ke bakisan kikawo gaisuwa wajen Cankwai ba."
Wani mugun kallo na watsama Mairo,duk tasha jinin jikinta.

Rabu da ita Mairo yanzun bazan yi lokacin taba kuma ƙasa zaki kwana duk iskancin da kika shuka yadawo kunnuwana kinsa bansan abinda kikaima su Salame ba,zakici ubanki."

"Allah ko bissimillah."
Nace muryata na rawa,jiki sage nakoma bisa kwalli na zauna ina tsoron Allah ina shakkar zalunci irin na Cankwai.

Nasan ko giyar wake nasha bazan iya dukanta ba,shiyasa nakoma kasa bakina alaikum na kwanta kada in kwana da kumburarren jiki musamman danaga dare yayi kuma ni kadai ce,a cikin su.

Bayan wani lokaci Baban su Amina ne yadawo daga wajen aiki zai shigo gida ya iske tasasar mutane a bakin gidan shi.
Isowa yayi yana tambayar su ko lafiya.

"Itace ta kawo haka,munzo muyi maku warning mun samu labari kuna son kubi ta barauniyar hanya dan ku gudu da Amina a gidan yari,wlh muddin hakan ta tabbata muna kasheta bazamubar jinin Asma'u ya tafi abanza ba,tunda ita taci amana mayaudara daku."

"Kwarai kuwa gwara kajimu da kyau inhar haka tafaru hatta gidan ka saimun ƙona shi wlh kun zamar mana annoba a gari."

Shidai Baba kallan su kawai yake,yana mamakin wanda ya kirkiri wannan labarin shidai yasan zasu daga ƙara dan bimata kadinta amma badan guduwa da itaba.

"Allah yabaku hakuri nidai nasan ba yanda za'ayi a fiddo mutun mai laifi inhar antabbatar da bashi ya akaita laifin da'ake tuhumar shiba,ni taya zan iya fidda Aminatu Allah shine zai mata gata bani ba."

"Karya ne tunda asirin ku ya tonu ai dole kace haka mundai gaya maku azzalumai maciya amana,kamar Amina ta iya kashe Asma'u abin kunya asararru."

"Naji duk abinda zakuce kuce amman ba'a kofar gidana ba,kuje can kuyi tsiya takunku."

"Wai kai har kanada bakin yin wata magana awajen nan kuyi laifin bari mu bankama gidan naka wuta sai muga ta tsiya."
Mutane suka fara taruwa aka hau raba rigimar.
Shi kuma yace insun isa su kona gidan bai hanasu ba.

Nanfa makota akahau jan matasan shi kuma aka shiga dashi gida ranshi duk yagama baci lamarin mutane yafara kaishi karshe iyayen yarinya basu damuba sai yan gari wannan wace irin masiface inalillahi wa'inna ilahirraji'un shine abinda yake maimaitawa.

Mama da Ahmad suka hau tambayar shi abinda yafaru saidai baiba kowa amsaba,ganin hakan baida anfani inda sabo sunsa ba.

Haka rayuwa ta kasance inyau ba'ai masu habaici ba ko maganganu marassa dadi ba gobe sai anmasu tun Baba bai damuwa haryafara shiga hali sosai akan lamarin.


*************
Yau tunda natashi Cankwai tafara yimani bala'i da masifa ta inda take shiga batanan take fita ba.

Dan na bugi Salame koda muka fita aiki wankin bandaki aka sata da wasu daga cikin Prisonors mu kuma daukar shara zamuyi mukai inda ake juyewa tace,inzo zuwa nayi nata aikin gaban ta na tsaya.

"Ke amshi tsintsiyar nan ke zaki wanke ban dakin nan yanzun nan."
Wani irin karni da wari ke tashi ga uban ɗoyi zuciyata take tafara tashi,na duba ko zanga Officers a wajen ba ko daya,amsa nayi dan tsira da lafiyar jikina.

Kwalla masu zafin gaske suke shido mani nidai Cankwai ta zamar mani annoba ta hanani sukuni a cikin yar sauran rayuwar data rage mani a duniya.

Ba wani detergent da mutum zai zuba dan yaji sauki sai omo blue din nan shina bada shima kadan nafara sharewa,wani zarni daya daki hancina bansan nafara kakarin amai ba,haka naita yunkurin amai ga cikina ba komai saidai yellow din kumallo da nike fitarwa dan azaba danike sha.
Haka naita wankewa harna gama sannan nacema Cankwai nagama aikin.
Toh tace sannan naci gaba da danna mata kafafunta tana kishingide.

"Angaishe da Sarauniya, dole a jinjina maki duk wanda yazo nan ke ya tadda kadan kika iske suma duk sunyi biyayya duk wanda baibi umurnin kiba baya kwana lafiya ba,mi kikeso aimaki."?

Cewar wata kilaki dan bansan sunan taba.
"Kwance mani wannan dankararren kan nawa, ya isheni da kaikayi Allah yasa wannan munafukar bata goga mani kwalkwata ba,kinsan ba abin mamaki bane."


Kwance kan tayi dake dankare da datti har wani tsami ke tashi tsantsagwaron kazanta zuba suka fara mata ni kuma ina danna mata kafafunta dake dankare da faso tsabar dadewa da tarin kazanta.

Ana kwanta datti na zuba kamar kasa haka aka gama kwance mata kanta aka maida mata wani kitson ba wankewa ba komai ana gama kitson,Officer Mariya tazo da wata sabuwar mai laifi wadda Qaddara ta kawota gidan Dan kande kana ganinta kasan tana cikin tashin hankali da firgici a ranta sai kuka takeyi kamar ranta zai fita,wajen mu ta tsaya da ita.

"Sarauniya Magajiya Cankwai keda Jama'arki."
"Aikuwa ranki shidade bakuwa mukayi.?"

"Kinganta nan yau din nan tazo shiyasa nakawota wajen Sarauniya dan ku gaisa."
"Aikuwa an kyauta wane room aka kaita."?
Gaya mata tayi

"Ana aiki idan aka gama sai ahadata da yan dakin su."

"Eh har dakin nakaita naga ba kowane shiyasa na kawota nan kafin agama tasan nata aikin."

"Ba damuwa Uwar dakina ai inkuna da irin mu a wannan gidan ba wani gagararre muma da bazarku muke taka rawa jayayya da Cankwai ba dadi Allah yasa ki zama shugabar gidan nan baki daya"

"Kai rufaman asiri kar ajiki."
"Addu'a fa nayi,koda yake ga wannan yar tsirkun tafe da kanta kamar na jimina."

Atika kenan data taho inda muke zaune kallan mu tayi tace.
"ke Dago ba aiki kuke ba,Cankwai kema tashi kije kiyi abinda aka saki."

"Idan naƙifa mi zakiyi? yar tsirku,ko yauma zaki kai karata akara kamani ne.?"
"Dan ansaki aiki aibune waike miyasa bakida kirki.?
"In ana saidawa siyo kisamani yar tsirku aiki kuma banyi."
"Aaa Cankwai kitashi kije kiyi abinda akasaki."

"Uwar dakina rabu da ita miruwanta dani,da bangama aikin ba na zauna."
"Kinji tagama ashe."

"Ita bata iya cewa tagama sai bala'i,dan kinga ana daure maki daga sama,akwai ranar da alkadarinki zai lalace marar arziki."

tafiya Atika tayi tana maganganu.

"Gulmamma kisha kuruminki Cankwai indai damu agidan nan ba wanda zai maye gurbin ki,kin tabbata Sarauniyar gidan nan."
Godiya nike uwar dakina Allah yasa kifi haka."
Ameen"
bari inje office.
tana tafiya Cankwai ta watsama bakuwar da aka kawo mana harara tace.
"Ke ni tsarar uwarki ce zaki mani tsaye akai baki russunama Shugaba."
Dukawa tayi tace.
"Barka da hutawa."
hawaye na tsere a fuskarta

"Baki shirya zama gidan Dan kande ba kike kukan munafunci,kwanta ki amshi kasonki barka da zuwa gidan Dan kande kabarin duniya."

Matseta tayi da cinyoyinra taita zabgarta da bulala sai wulle wulle take saida tai mata radau sannan ta saketa.
Sai kuka take.

"Yiman shiru ko insa ki cika wannan botikin fentin da hawaye munafuka."

Shiru tayi jikinta nata bari da kwallan sun taho da sauri zata maidasu.
Bar kallona banda kirki nan kikazo kisamini,kuma nan zaki barni mutu ka raba.
akalla shekarata Ashirin ana fafatawa dani a wannan gidan faɗi can kwanta can harna iso nan cif banda wanda nayi abaya,banyi kukaba saike shigowar yanzun zan zauneki yanzun nan."

"dan Allah kiyi hakuri na rokeki nadaina."
tana goge kwallan idanun ta.

"Nafiki sanin shi tsabar sanin ilimin addini alqur'ani na haddace shi tas kuma duk a gidan Dan kande na koyi shi banda hadisai suma anan na iyasu aiki dasune banyi kina mani ba daidai ba zan take sani in wanke ki tas,kamar Allah ya aikoni."

Nidai ina kallan Cankwai ashe tanada sanin ilimin addini take zalinci koni banda hadda banfi rabiba abinda na haddace, amman ita duka yana kanta,ikon Allah ga sani ka barna yan bariki kenan.

Maganarta tadawo dani tunanin dana lula.

"Miya shigo dake wannan gidan kuma minene sunanki.?

"Hauwa'u."
tabata amsa jikinta nata faman rawa.

"Shine kadai na tambayeki."?
Muryarta na rarrabewa tace.
*Jinjinar ban girma agareku Commenters and Posters Allah yabar zumunci so dan lillahi nike maku😍*

_Yar Mutan Kankia ce❣️_
Share
Pls
❣️

_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E11&12




"Hauwa'u."
tabata amsa jikinta nata faman rawa.


Shine kadai na tambayeki."?
Muryarta na rarrabewa tace.
"Sharrin sata aka laƙa bamani abinda yakawoni kenan"
Ubanmi kika sata."?
"wlh Allah bani na sataba laqa mani sharri akayi."

Tastas Cankwai ta wanketa da kyawawan maruka har biyu,tsabar zalinci tace.

"Dan ubanki duk wanda kika gani gidan ɗankade rabi da kwatarmu duk sharri akai masu ba yanda zasuyi suka gurfana anan saboda shari'a sabanin hankali ce."

"Ubanmi kika sata."?
"Diamond ne nasata."

banda 6ari da rawar gabbai ba abinda takeyi dagani taji zafin marin da Cankwai tai mata.

"Idan kika kara bani amsa a gajarce saina zauneki kinyi kashi a wondo."

"Sakar gold ta uwar dakina."
ta ida maganar a tsorace.
"Kam ubancen Sabira kinji wata shegiyar duk layin yancin amana ne kenan,ai wannan ta'aci mata uwace,ku ɗage mani ita,ke Dago tashi kuyi mata shalga shalga."
Fuskar Magajiya ba alamun tausayi ko imani gashi kowa ya mike,nima banda zabi na mike muka riketa taita zabgama Hauwa'u duka a mazaune sai kuka take tana zille zille.
gashi ba wani ma'aikaci a gidan ko daya bare ya kawo mata ɗauki,nidai tausayin ta ya kamani nasan zafi da radadin dukan Cankwai ga bata da imani sam,saida ta gaji muka ajeta.

"Wellcome to gidan Dan Kande ko mai uwa saida ya shirya bare maraya biyayya tilas a wajen Magajiya ta mai mujiya sai dubu ta taru anbuga dani anbarni munga jiya munga yau gobe kuma saida izininlillahi munci zamaninmu munci nawasu tsufuwa kuwa gaba muka bashi,ko muna rankwafawa sai muntaka,duniya rawar yan mata angaisheki Cankwai har gobe a sabon jini kike jinki wazai ja dake yasan yayi ganganci sai damu gidan Dan kande ke cika."

Haka taita kirara kanta gaskia lamarin Magajiya yafi karfin ilimina batada imani ko tausayi batasan tsoro ba,hausawa nacewa nagaba yai gaba....

"Ke Nusai zonan."
Matsowa tayi tana goge idanunta.
"Inafatan damu zaki kare rayuwarki.?"
"Eh aaaa."
tabata amsa a tsorace.
"Amsa daya zaki bani yan mata."?
"Shekaru biyu zanyi ko tarar dubu dari biyar ni kuwa banda maganin ko naira dubu hamsin bare makudan kudade irin waɗannan hakama dangina basuda halin su, dole nahakura nazo nan din."

Wani irin tausayin ta yakamani ganin irin tata Jarabawar wasu dadama abu kalilan ke kaisu gidan Yari rashin gata ko galihu kesa suyi shekaru a daure da za'a samu masu arziki suna gidan yari suna bin cikar cases na Yan Yari da antaimaki mutane da yawa wajen kubutar dasu,a ciki akwai wadda nasani dubu hamsin tajama ta daurin shekara a gidan Yari saboda batada maganinta inama yan uwan mu,masu arziki zasuna yawan kai ziyara a gidan Prisons dan taimakon mabuƙata wa'anda basu da yanda zasuyi da yawan masu laifi wlh wasu sharri ne akai masu sai aturosu wani daga amaidashi kafin zuwa wani lokaci a yanke mashi hukunci sai a manta dashi abubuwa da dama na Qaddara yana cikin gidan Yari Allah katsare mu baki daya.

Koda muka koma daki jikina ya gama sanyi abubuwa da dama suka tsaya mani arai musamman case din Hauwa'u duk da ba aikina kenan ba tabbas dagani sharri akai mata kuma harda rashin galihu yasa aka kawota gidan Yari.

Koda banda agogo nasan karfe sha biyu tayi su Cankwai sai sharar bacci ake angama zalinci wanda ya zama ibada gareta sai munshari take tana sakin bama baman tusa kamar bodara.

Hancina na doɗe kamar inyi amai bansan sanda baccin wahala ya daukeni ba sai karfe shidda na farka ko sallah ba wanda ya tadani daman bawai dan suna tsare sallar bane,ina sallah karfe takwas daidai muka fita,daman nayi wanka ,ba wani aiki da zamuyi shara kawai mukayi sannan muka anshi kalaci.
Haka rayuwa ta kasance ga kowa yana harkokin gaban shi.

Bayan sati ukku, muna zaune a fadar Sarauniya Magajiya kowa na fadin albarkacin bakin shi,musamman su Salame da Mairo wata Prisoner tazo ta gaida Cankwai,amsawa tayi agadaren ce.

"Da'go ana kiranki a office din Oga Adam."
Toh nace mikewa nayi zantafi.
"Sauran aje ayima mutane tsirƙu."
"Toh."
nace mata natafi.
Ina zuwa nagaidashi.
"lafiya lau Aminatu ya hakurin zama."?
"Alhamdulillahi."
"Kinyi baƙi,Jafar rakata minti goma zatayi."
"Okay Sir."
Badan nasoba natafi ina zuwa naga Anty Hafsat da Mami tsaye wani kallo suke mani mai kama da kin bamu tausayi.

nima kallan tsana nike masu amman na danne tawa kiyayyar agaresu domin bansan dame sukazo ba duk da nayi mamakin ganin Anty Hafsat da Mami atare duk yanda take nuna mana kiyayya amman Anty Hafsat take huɗɗa da ita koda yake aidaman ance ɗan uwanka shike badakai arayuwa.....

Maganar suce tasa na kuma kai kallona garesu tareda gaidasu.

"Aminatu Yusuf Caranci tunkan rayuwa tai nisa harkin fara tagayyara?jibarki yanda kika lalace karshen watsewa kece garkame a gidan Yari kinyi kisan kai wa'iyazubillah gaskia kinyi asara bayyananna maci amana."
Cewar Mami.
Bance mata komai ba baccin kallan tsanar da nike binta dashi.

"Haba Anty Mufida taya kike bata bakinki akan wannan kidahumar yarinya ai daman nagaya maki Amina sai kin wulakanta kin tagayyara sai rayuwarki ta tsaya kin zama abar tausayi yau gashi kin rasa auren Sadiq kin rasa Taufiq kowa ya huta da mugun halinki,kuma kisa aranki bake ba fita mutu karaba takalmin kaza har abada."

Anty Hafsat ta ida maganar a zafafe tsabar tsanar da take mani.
Wannan karon murmushi nayi ina jinjina kaina dan na tabbata Anty Hafsat da Mami basu sona ashe zargin da nikeyi da gaske ne!

"Uhmm Mami kenan ina abun yake maye yaci jariri kin dauka zamana anan na har abadane koda yake baki kuskure ba,dan rayuwata ba Asma'u batada anfani rashinta yafimin komai ƙuna.
Sannan kusha kurumin ku kobani nabar baya inada yan uwa da masoya dole kuka gansu sai kun raza domin kamar inanan ne!

Ke kuma Hafsat baki bani mamaki ba daman tuni nasan baki kaunata wlh yanda baki sona bantaba sonki ba daidai da kwayar zarra asali natsaneki natsani mai kaunar ki,ko alahira bani fatan inhaɗu dake, Sadiq da kike magana shike gabanki,kuma Ya Taufiq nidashi Kainuwa ne dashen lillahi koda gangar jikin mu bata tareda ta junanmu kusani ruhinmu da zukatanmu suna tare da juna.
mi kikeci naƙasa na zuba kohar kin ƙosane,kisa aranki komai yana da lokaci."

Shekeke tayi tana kallo kamar wata bakuwa.

"Oho dai borin kunya dai kike kinci amanar aminan taka, a haka zaki ƙare a garkame har igiya tairara azo ai mutuwar kasko."

"Ko?dan Allah shikenan Allah yabamu sa'a nidaku aga wazasuyi mutuwar kasko,kuma inasan kusa aranku wlh tunran gini tunran zane komai hukuntaccen al'amarine Bakin Alqalami ya bushe sannan kuma Qaddarata ce, kusa aranku *Haka Allah Yaso* a lokacin da yaga dama nariga da nai maku nisa Mami ina zaune a gidan Yari amman kullin zukatanku sun gaza nutsuwa akaina dani kuke kwana kuke tashi tsabar ratar danai maku bakomai kusa ranku a cikin inuwa domin kuwa Komai Lokacine."

Kamar andasasu suke kallona dan takaici daya gama addabar su,Anty Hafsat ce karfin hali tace.

"Toh haka kikece ko mudake muzuba mugani shege kasafasa ɗan halak sai yanka."
Jijina kaina nayi alamun eh, nace.
"ko kina tantama ne."?

Karamin tsoki naja hango wucewar Nusaiba nayi nakira sunanta, tahiwa tayi ta tsayani juyawa nayi zan tafi Mami tace.

"Amina."
Cak natsaya sannan na juyo.
Wata bakar ledace ta miko mani kallan kaskanci nike masu dagasu har

Please Login or Register in order to submit comment