Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mafita taya zan tunkari Baba,uwa uba gashi suna san suyi mashi maganar ɗansu na sona da aure.
Daukar wayata nayi na saka number Husna kamar yanda na kiyayeta akaina,na kirata bugu ɗaya nai mata,ta ɗaga kamar maijira.

"Allah yasan kiran nan alkhairi ne kullin cikin jiran tsammani nike,assalamu alaikum."

Kuka kawai ya kufce mani,sautin kukana kawai taji tace.
"Minal kina ina dan Allah kigaya mani inzo gareki kada kitafi kibarni Aminatu dan Allah."
Kuka kawai nike amman ba kaina nikema kukaba tausayin Husna ne yakamani.

Na kasa magana saidai kukan da nikeyi marar sauti ta kuma cewa.
"Ina kika shiga Minal kinsamu cikin tashin hankali mun dauka saceki akayi dan Allah kina ina inzo insameki dakaina nayi missing dinki masoyiyata."
Da muryar kuka nima na amsa ta.
"Nima nayi kewarki Husna ina cikin Kano saidai bansan kigayama kowa sai bukatar hakan ta tashi inasan inganki zanyi magana mai mahimmanci dake."

"Shikenan kibari idan Daddyn Mina yafita kasuwa zan maki waya number kice wannan."?

"Eh."
nabata amsa munjima muna wayar mu da ita,cikeda amince na aminai kuma kawayen juna,kafin nan mukayi sallama da junan mu.
Haka na zauna cikin zullumi tunanina taya zamu samu mafita bansan inje gida in sake batama mahaifina rai,abinda zaisa ranshi ya baci yaji case din Ya Mutallib bayan nasan da zancen auren Sadiq akaina.

Washe gari naje gidan Asma'u,murna sosai kawar tawa tayi da ganina har kukan dadi saida mukayi da junan mu,nan muka nafara magana saidai yamma tayi likis.

"aikuwa Minal yanzun Ya Abdallah zai dawo kasuwa kuma kince maganar nan tana bukatar lokaci mizai hana musamu lokaci sai mu tattauna,kuma kinga Kabir yadawo gidan nan(kaninta ne) yana dubama Abdallah da shuganan cikin unguwa zai iya ganin ki."
"Hakane kawata kibari musake fidda lokaci, kuma bansan Kabir ya ganni zai iyafaɗa gida nafison idan Daddy ya dawo sai ya maidani da kanshi kafin lokacin munsan yanda zamuyi, bari in wuce kada su iskeni."
Sosai mukai kewar junan mu natafi gida.

Bayan wani lokaci nacema Ummi zanje kanti siyo Credit,to tace mani daga can nazame wajen Husna kiranta nayi waya tace ta kama mana Hotel zamuyi yini daya acan zamu tattauna maganar mu tunda sirri ce,toh shine abinda nace mata turo mani address natafi room number din na duba nahau knocking saidai bata budeba sake bugawa nayi a zatona kota shiga ban daki saboda buƙatuwa,saidai ina shiga nafara kiran sunan ta Husna amman shiru bata amsaba,Haidar nagani aje bisa gado na dauke shi sai kuka yake,ina Husna kina ina amman still shiru har toilet saida na leƙa bata,ina taho naji nayi tuntube da kafar mutun a gefen gado naganta kwance a kidime na duka ina furta.

"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un!."
Shine na furta da karfin bala'i na zube gabanta na kama wajen kaifin wukar tsabar firgita da razana har saida na yanke wajen zare wukar a cikin ta,bude idonta tayi kaɗan sai kuma ta rufe bakinta na furta kalmar J bata kara magana ba rai yai halin shi.

Ihu na saki na kifa kaina bisa cikin Husna ina kuka

"Ki tashi Husna kada kiman haka ban shirya rabuwa dake ba dan Allah karki barni kitashi bamuyi haka dake ba Habibti."
Kukan naci gaba dayi mai tsuma rai,jinayi ance.

"U are under arrest."
Dagowa nayi da idanuna masu kama da rushi na kalli yan sanda agefe daya kuma Dr JJ ne yai holding hannayen shi yana smile,daga lokacin duk wata magana ta tsaya cak a cikin bakina.

Kuka nike saidai badan an kamani bane, Aaa ina kukan rabuwa da Asma'u masoyiyata wadda banda kamar ta.

Inaji inagani aka samani unkwa akatafi dani Bomfai tareda wukar a cikin tissue.

Haka akatafi da gawar Husna akaita gwaje gwaje sannan aka nemi number Abdallah aka kaita gida.
Nashiga tashin hankalin da bantaba shiga cikin shiba kuka shine ya zamo abokin firata na zama mujiya a cikin tsuntsaye kowa bai sona bai kaunata saboda nazama azzaluma naci amanar kawata,yar uwata kuma aminiyata Asma'u haka mutane sukaita tsine mani ana tir da halina."

Kuka ya kufce mani sosai na kife kaina ina kuka mai sosa rai.

"Kiyi hakuri Aminatu inasan ki bani takaitaccen labari akan shari'ar da aka gabatar kuma miyasa kika amsa laifin daba naki ba."?
Cewar Barr Bashir.

Dagowa nayi da idanuna kamar rushi wanda nikeji kamar yanzun abun ya faru na kalle Barr Bashir nace.

Tunda labari ya karade ko ina sai ya kasance kamar Kano aka guye yan garin mu sai tir ake da halina.

Banda bakin magana hakama iyayena,kuka kuwa shine abokin firata.

Addu'a itace tsakanina da Husna akoda yaushe ban bacci bare inci abinci banda wani kwanciyar hankali bamai sona kowa ya tsaneni.

******
Washe gari aka kaini Kotu High Court aka fara shari'a da yan sanda suka kai case din.

Lauyen Gwamnati ke kare Husna ni kuma Ya Mutallib suka daukar mani lauya,aka hau shari'a a statement din cewa kai kawa ta kashe kawarta dan tana son ta mallaki dukiyar ta shine takaita hotel ta kasheta.
Nidai ina ganin ikon lillahi.
Aka fara sharia JJ ke cewa shi shaidane duk abinda yafaru ya fadi da zuwa hotel saidai inda yai karya dayace yana ganin na sokawa Husna wuka shine yaje yakira masu hotel da yan sanda saidai narasa taya JJ yasan nida Asma'u zamuyi haɗaka zuwa Hotel?taya yasan ina cikin garin Kano?Bayan kowa yasan niɗin na mutu tinda annemeni ba wani labarina.

Tambayar da nikema kaina kenan ataikaice dai haka yagama bada shidar akaina.
aka tambaye ni minene shaidata na aminta da zargin da akemani ɗaga kaina nayi sai kuma un-expected naji nace.

"Na amince nice na aikata wannan laifin na kashe kawata.
Inalillahi wa'inna ilahirraji'un aka dauka baki daya musamman wa'anda suka san wacece Husna a wajena.

Baban su ya mike yace karya nike bazan taba kashe Asma'u ba.
Alqali ya daka mashi tsawa yace tunda harni mai laifi na amince magana ta kare.

Sake kallona yayi yace.
"Aminatu kin amince kuma wanene shaidan ki."?

"Allah shine shaidana kuma na amince da duk wata hujja akaina."

Alqali yace.
"Miyasa kikai saurin amince tunda wuri."?

"Saboda Qarratace kuma Haka Allah Yaso,dan haka na amince ni nakashe kawata kuma aminiyata Asma'u,sannan bansan inba shari'a wahala shiyasa na amince da laifina."

Haka Alqali ya yanke mani hukunci saidai ya sassauta mani saboda banba shari'a wahala ba da ratayeni za'ayi sai yace akawoni gidan Yari Life Prison.

Haka kuwa akayi masujin dadi nayi wasu kuma na kuka musamman iyayena bazan iya misalta maku tashin hankalin da suka shigaba a wannan ranar wadda ko labarin ta inba doleba banso atada mani.

Inaji ina gani aka kamani zuwa Kurmawa Prison wanda nike ciki yanzun haka yanzun ina cikin shekara ta ukku kenan,wannan shine takaitaccen abinda nasani akan shari'ar da akayi last time.

Kowa yayi jigum musamman Ya Taufiq da idanun shi suka koma kamar rushi dagani kukan zuci yakeyi tausayina tab a saman fuskar shi.

Barr Bashir yace.
"Shine abinda kika gani ba wata alama da kika gani kafin wannan abun ya faru dake.?"

"Akwai Barrister saidai wani abun zanso sai anje Court zan faɗe shi gaban Alqali."

"Shikenan Aminatu aini daman hujjoji nikeson in samu hakan yayi."
Sannan ankawo maki ziyarori dayawa a cikin wayataba zuwa yai maki barazana."?

Samun kaina nayi da kallan Ya Samir nayi bansan dalilin dayasa nagaza magana ba sadda kaina nayi kasa nace.
"Shima ai mani wannan alfarmar zan bayyana komai a gaban kowa in anje can din."

"Aaa Minal kifadi mana can dinma ai zaki fadi komai agaban kowa."
Cewar Ya Taufiq ya ida maganar a raunane.

"Major batta dagani tanada nata dalilin Allah yakaimu zuwa next week insha Allah 11 ga watan nan saiki shirya Allah yabamu nasara kuma Allah ya wankeki daga zargi shine zai maki gata bamu ba,mudaine sila in Allah yaso.

"Allah yasa Barrister nagode maku Allah yasaka maku da alkhairi."
"Ameen ya rabbi."

"Ranka shidade zamu tafi i think bazan kuma zama da Aminatu ba saboda nasamu Evidance da yawa Barrister Samir inafatan daga naka bangaren ka gama komai ko."?
"Eh komai yatafi yanda ya kamata lokaci kawai muke jira insha Allah."
"Allah yasa."
Cewar Barr Bashir.

"Major muje ko?kodai zaka kara gaisawa da kanwar taka ne."?
Yai maganar a sifar zolaya murmushin karfin hali Ya Taufiq yayi yace.

Ganawa sosaima kuwa Barr Bashir, nidai firstly inga gaskia tayi halinta tabar wannan gidan shine babban burina."

"Allah ya cika mana wannan burin namu yasa mudace."
"Ameen ya rabbil alameen."

"tashi kije ciki Dago Allah ya kyauta gaba."
Ameen nace,inasan in sake ko hada ido da Ya Taufiq amman idanun su kaina dan sunji kowa nace mani Dago a gidan Yari inba haka kace ba baza'a gane niba,haka na tafi a sanyaye,har daki wanka naje nayi nai sallah na zauna ina addu'a.


_After two days_

"Ya Samir mi zakace akan wannan bin ciken da mukeyi"?

"Perfectly duk wasu hujjoji da suke a hannuna nayi handled dinsu wajen Barr Bashir hakama Barr Sagir shima ya gama komai yaba shi,kuma yana kokari saboda Barr bai yarda yai aikin shari'a bayan karyaba nasan shi,kuma insha Allah za'asamu nasara sosai."

"Allah yasa haka,har yanzun narasa sukuni akan halin da Aminatu ta afka a ciki ,banji zan iya komai musamman gudanar da harkokin Company na,baccin Qasim dake kulamani da komai anan kuma Usama gashi banbari yana zama kullin muna bisa hanya lamarin ba dadi ya Samir ina cikin mawuyacin hali."

"Kadaina fadar haka Major komai zaizo cikin sauki insha Allah."
"Haka nike fata,Aminatu na cikin garari Allah ga kubutar da ita."
"Ameen."

"Gobe zanje Kano insha Allah."
Inji Ya Taufiq
"Allah yakaimu na dauka sai ranar da za'afara zaman Shari'a zakaje."

"Aaa akwai abinda nikeson yi kuma inasan idan ana gobe za'a zauna zanje afara dani."
"Allah yakaimu lafiya."
"Ameen."

Haka suka tattauna tunda Taufiq ya dawo ba wata hamayya tsakanin su shida Samir sun hade kansu su ukkun su duk wani yan ubanci sun ajeshi gefe soyayya sukema junan su bana wasa ba.

Washe gari kuwa Taufiq yaje Kano kai tsaye Kurmawa ya isa as usual suna da guarantee na shiga tunda suka dauka kaƙara wannan karan office din Adam yaje saboda Sunday ne yana ganin shi ya karrama shi zama yayi yasa akira mashi Dago.

Ina kwance kasan floor sai muɗiɗɗika nikeyi akazo kirana nayi bako inajin haka a cikin mutun biyu raina ya bani ko Ya Taufiq wanda nafi confidence dashi, ko Ya Mutallib.

Ban iya zuwa shine abinda nafurta ina kwalla,tafiya mai kiran nawa tayi tajima sai kuma ta dawo ina kwancen dai tace.

"Ance akamaki kije ana son ganin ki."
Bazan iyaba Allah."
Na ida maganar ina kuka tsabar yanda marata ke ɗaure sai uban ciwo take mani.
karaf Cankwai tace.
"batta tashi muje ni zan kamata."
Haka akayi ta kamani mukaje har office din Adam.

Ya Taufiq ne as usual yazo mani ziyara dawowar shi bazan iya lissafaba ziyarar dayayi mani ba musamman daya samu aka amshi korafin su za'a sake sabuwar shari'a saiya samu damar ziyarata.

Baki sake Cankwai ke kallan shi,sannan taa gaidashi,amsawa yayi saidai idon shi akaina nan Adam yace tabamu waje zamu mugana,amman tajira waje,fita tayi shima fitar yayi,na zauna ina kwalla.

"Minal."
Shine abinda ya furta.
A raunanniyar murya cikin sanyin hali.
amsawa nayi nima,a sanyaye.
Matsowa yai kusa dani yace.

"Miyasameki kike kuka
baki murna da zaman da za'ayi jibi shine nazo inkara tuna maki kishirya ko bakiso."?
"Aaa inaso mana."
Nace cikeda da karfin hali dan ko magana mai karfi bansan inyi.
Sake cewa yayi.
"Miya sameki."?

Marata na nuna mashi tareda da daura tafin hannuna asama, duk da nasan MP ne zanyi amman banji kunyar shiba saboda azabar da nike ciki takai ta kawo a lokacin.
A ɗimauce ya kuma cewa.
"Ko anbaki wani abu kinci Minal."?
Girgiza mashi kaina nayi still dai cikina nike nunawa duk nai zufa.

"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un dan Allah kitaimakeni kiman magana Minal."

A hankali cikin sarkewar murya nace.
"Marata ke murɗa mani Ya Taufiq zan mutu katai mak mani."
Na ida maganar ina kuka.
A ruɗe yace.
"Ciwon ciki."
Ya maimaita a razane.
Sannan kuma cewa.
"Bari insamo maki magani."
Da sauri yafara kiran Officer.

Saidai inaji saukar......



_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️


_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E33&34



"Ciwon ciki."
Ya maimaita a razane.
Sannan kuma cewa.
"Bari insamo maki magani."
Da sauri yafara kiran Officer.

Saidai inajin saukar MP dina wani irin murɗawa marata tayi bansan na kwanta saman suminba na daura hannuna saman marata a hankali nike sakin nishi tsabar ciwon da nikeji yana ratsani,wani irin nauyi da kunya duk suka haɗe mani lokaci guda,duk da nasan ciwon da nike kenan,amman tun ana sauran kwana goma yake fara murdamani ina shan wahala sosai,a lokacin da ina aiki inashan magunguna rage pain kowa yasan ba kowane magani ake sha mashi ba asalima ba'ason ana yawan shan magani dan kana ciwon cikin Period sai takama.

Tinda nazo gidan Yari inaga sau biyu nai On duk da wannan ukku,suma biyun kwata kwata kwana ɗaya nayi yana zuwa ya dauke har mamaki nike kamar an cire mani shi kwata kwata nadaina yinshi duk da naji dadin haka saboda kwama calar dake ban ɗankin gidan akwai cutuwa,sai hakuri.
Ina ganin sun dawo tareda a rude Adam yace.
"Dago ko kinci wani abu?mi aka baki."?
Girgiza kaina kawai nay alamun bakomai.
shima yasa ko wani abu aka bani naci, tunda kwanaki anyi anafani da Nusaiba ta saman poison a abinci,yana zaton,ko anji labarin za'a sake sabuwar shari'a kada asamu dama a halakani shine duk ya ruɗe.
Banda sannu ba abinda suke jero mani.
Amman nayi mamakin Ya Taufiq daya gaza gane matsalar da nike ciki saina ɗauka dan ya ruɗene shiyasa.

Duƙowa yayi ganin na rufe idona kamar mai bacci saidai inajin zubar shi a pant ɗina amma kuma naji pain din ya rage sosai,dafani yayi dayaga idona a rufe yace.

"Aminatu buɗe idonki ya kikeji ance doka bata bari abaki kowane supliment amman su ma'aikatan zasu san yanda zasuyi sannu kinji."

"Yawwa."
Na amsa,nafara kuka kai ɗan sauti,dan bansan taya zan fara mikewa ba dagaji na baci.
"Miyafaru.?"
Yaimin maganar a sanyaye.
Zuwa lokacin yafara kuleni ni kuma nakasa gaya mashi lalura ta.

Wani irin numfashi na fesar mai zafi da kyal na iya magana nace.
"Akira mani Magajiya."

Bada jimawa ba saiga Cankwai ta shigo,zuwa tayi kusa dani ta duƙo tace.
"Amin Dago lafiya miyasame ki."

Cikin muryata mai kama da raɗa nace.
"Ina Period ne kuma nayi staining."
Mikewa tayi tace bari indawo.

Gani nayi Ya Taufiq yafita nidai ina zaune sai sannu da Adam ke rangaɗo mani.
Basu jima ba tana shigowa da wani zani Ya Taufiq na dawowa da leda baka a hannun shi kallan shi kawai nayi na kauda kaina inajin kamar in fasa kuka mai sauti tsabar azabar da nikeji.

Cankwai ta ɗagoni rigata kuwa harta fara baci na tabbata su Adam sun gani nidai nauyi da kunyar su ta cikani.
Daura mani zanin tayi a kuguna.
Gashi naji Ya Taufiq yace.
Amsar ledar hannun shi Cankwai tayi tai mashi godiya,ya bata kudi nidai ban kara furta uffan ba muka tafi a hankali nike tafiya gani nike idan na tafi da sauri ciwon kara ninkuwa yake muna isa direct kewaye na shiga duk kayan bukata Cankwai takawo mani harda ledar da Ya Taufiq ya kawo mata,ansa nayi na shiga wanka da consumer bucket na wanke jikina da kayana,ina bude ledar Part nagani kusan guda shidda dauka nayi double nasaka a wandona na saka,haka na gyara jikina sannan na saka wata riga ta yadi orange color Cankwai da kanta ta wanke mani uniform dina na dawo daki nan ta miko mani kudin da Ya Taufiq ya bata,nace ta rike hannunta duk da bansan ko nawa bane da haka nai bacci araina inajin nauyi da kunyar Ya Taufiq gashi jibi zamu fara zama Court,wannan kenan.

*ANKA*

Ku shirya gobe da wuri zamu wuce Kano saimu sauka gidan Gwoggo har muga abinda hali zaiyi akan wannan shari'ar insha Allah."
Cewar Baba.

"Allah yakaimu lafiya ni wlh duk jikina yai sanyi akan wannan lamarin sai inji duk na karaya dayawa."

"Addu'a zaki dinga yi mata Khadijatu ita take bukata awajen ki,kinga dai halin data shiga danma Hussein dan albarka dayake tai maka mata,kilan da ba wanda zai iya mata wannan gatan,Allah yasaka mashi da alkhairi."
"Ameen ya rabbi,Baba nima jiya Ya Tariq ke kirana yace gobe za'afara sauraron shari'ar."
Cewar Ahmad.
"Allah Sarki Mamana wai itace za'adinga shari'a da ita ikon Allah,wannan shine tsakiyar rayuwar Allah yasa mudace."
"Ameen."
Haka sukaita taraddadin lamarin suna mata addu'oi da fatan nasara.

_KATSINA_

Inna gobe ne fa za'a fara zama da yarki Kotu zaki iya zuwa kuwa."?
"Eh mana Hussein wancanma tashin hankalin dana shiga shiya hanani zuwa kuma naga bamuda mafita shiyasa banjeba wannan karan insha Allah mukeda nasara komai gaban mu za'ayi muga karshen munafukai insha Allahu."

"Hmm Inna ina mamakin Case din Aminatu ya akai wannan mutumin yasan sunje Hotel,kai lamarin nan akwai rainin hankali a cikin shi."

"Makircine tsantsa a cikin wannan lamarin, amman ina mamakin wa'anda zasuyima Amina wannan mugun sharrin."

Mikewa Ya Taufiq yayi yace.
"Bari in wuce Inna amman kada ki manta wlh nakusa dakai zai iya yimaka wannan abin kana rayuwrka baka damu da kowa ba sai makiyan ka sunemi hanyar ajalinka,baka damu da kowa ba ana maka bakin ciki da hassada."

"Aikuwa Hussein,ta Allah bata makirai ba,shekara ukku kenan da watanni Aminatu na garkame a Yari baiwar Allah,gashi har aikin ta duk ta rasa."

"Nifa Inna aikinta bai damuna,danni daman ba son aikin nan nike ba,kasuwanci yafi aikin nan,mudai muci gaba da yimata fatan alkhairi bari in wuce nabar Usama yana jirana."

"Saidasafe gobe,da karfe nawa zaki shiga Kano."?
"9am insha Allah."
"Allah yakaimu lafiya,
ko inzo in daukeki."?
''Aaa Hamza zai kaini tare zamuje."
"Alright good night,Allah yakaimu lafiya."
"Ameen."
Da haka suka tafi shida Usama.


_KURMAWA_
Washe gari da safe dana tashi cikin nawa ya ɗan lafa sosai har ina doguwar magana ba kamar daba,wanka nayi na saka kayana na kimtsa tsaf abuna hakanan na tashi jikina amatuƙar mace inajin faduwar gaba na shigata a hankali narasa dalilin hakan,addu'a kawai nikeyi tunda nafara shiri su Cankwai ke kallona ganin an aje Gandirobas guda biyu gefen dakin da muke ciki,hakan yasa suka kasa nutsuwa.

"Dago lafiya naga an aje mana wadannan abubuwan,sunata yimana mazurai,ke kuma kinata shiri ko lafiya."?

"Bakomai Magajiya kinga nasamu sauki sosai alhmdullh."
Nayi maganar inda shirina.
"Hakane Allah yaimana tsari da mugaye."
"Ameen."
Nace,komawa nayi na zauna gefen gado suna fira inajin su wani insaka baki wani kuma inyi shiru.

Bude kofar ɗakin mu,sukayi da karfi har saida muka maida hankalin mu kan kofar, Karima ce ranta a dagule sai mazurai take tana watsa mani harara daman can jinina bai hadu da itaba, cikin fushi tace
"tashi muje kika kafeni da mugayan idanun ki kamar mayya."
"Uhumm."
kawai nace,sannan na mike jikina sanyaye saidai ba abinda nikeyi sai addu'a.

Magajiya tace.
"Amini ina za'akaita.?"

"Oh wai kina nufin bata gaya makuba tsabar mugun hali wannan yarinya badai mugun tugguba,wai dan makirci cewa sukai basu yarda da hukuncin da akai mataba suna jayayya akam kisan da tayi,wai ba ita bace ta aikata ba,sharri akai mata,ai saita fidda uban dayai mata sharrin."

"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un,toh intana da gaskia Allah ya kwatar mata hakkin ta."
Cewar Cankwai.
Ameen nace araina.

"Wace gaskia ke gareta zata jama kanta kisane abanza ta hanyar rataya,ita har wani gaskiane da ita Allah dai ya kyauta."
"Ameen."
Suka amsa,nidai bance masu komai ba haka muka tafi,narasa wane hali nike,ciki farin ciki ko bakin ciki,office din Adam aka kaini nan na iske Yan sanda guda ukku harda mace a cikin su,saka mani Unkwa akayi,muka fito waje aka sani mota mukatafi harda Karima cikin ƴan rakiyata,zan iya ce maku kamar an daɗe mani idona nidai bakin wani gini na ganni mutane nata tururuwa ana zuwa take nagane Court ce,domin naga wa'anda nasani sosai musamman yan garin mu,harda yan unguwarmu duk nagani.

Duniya kenan karasa wake fidda labari waje kamar an hura usur kowa yaji za'a sake shari'a,saidai an hanani yima kowa magana mutane sukaita shiga ciki, nidai ina cikin mota zaune tare da Yan sanda ina kallan ikon Allah mutane sosai kala kala.

Ina ganin isowar Mama da Babana,bansan kwalla sun ziraro mani ba tausayin su ya kamani.

Suma shiga sukai ciki Ya Taufiq da Barrister Bashir da Ya Samir,sai Ya Tariq tare suka iso,suma shiga sukayi ba wanda ya nuna ya sanni awajen.

Bamu muka shigaba saida mukaga Alqali yabi ta private door dinshi zai shiga ciki, kusan a tare muka shiga da JJ yasha jajjayen kaya kallo daya nai mashi na kauda kaina shiko ya kafeni da idanu kamar maye.

Bamu jima da shigaba saiga su Anty Hafsat da aminiyar ta Mami a tare suka iso,kai kowa ya iso wajen hatta Mum saidai banda Abba amman sunzo harda Fatash.

Hakama iyayen Asma'u da mijinta sunzo.
Gaban Court na tsaya gashi sai gwadani ake wanda ma bai sanni ba ranar ya sanni tsabar nunawa dana sha,ga nasha Unkwa an hadani da Yan sanda gefe guda kuma ga gandirobas har biyu Karima da Jafar.

Gyaran murya Alqali yayi kowa ya nutsu yai shiru cewa yayi.

Yau litinin wane case ke garemu."?


*Noted:-* _Kafin muci gaba da gabatar maku abinda yafaru a Court duk inda date yazo is fiction ba zamu faɗi actual date din da akayi shari'ar ba hope zaku fahimci uzurina nagode_

Mikewa Majesty yayi yace.

A yau litinin 17/10/2021 Kotu zata saurari karar da aka kawo akan tuhumar da akema Aminatu Yusuf Caranci,na kashe kawarta Asma'u Abubakar ta hanyar makami (Wuka) a cikin Hotel duk da anyakema mai laifin hukunci saidai tana jayayya da hukuncin da Kotu ta yanke mata,za'a sake sabunta shari'ar inda take tuhumar Junaid Jamilu Abubakar saboda yace shine shaida akan duk abinda yafaru a wancan karan Kotu zataso yakare kanshi.
Saidai last time ance Aminatu ta kashe kawarta Asma'u saboda dukiyar ta,shiyasa ta kaita hotel dan ta cika burin ta wannan shine case dinmu nayau nagode ya maigirma mai shari'a."

Jinjina kai Alqali yayi yai sannan yai yan rubuce rubuce yace.

"Ina lauyan dake kare mai ƙara.
Mikewa Barrister Bashir yayi yace.
"Ya mai girma mai shari'a sunana Barr Bishir Umar Fage,nike kare wadda ke ƙara Aminatu Yusuf Caranci,godiya nike my Lord."
Komawa yayi ya zauna yace atare dani akwai abokan aikina.
Mikewa yayi yace.
"Am Barr Samir Sarki Mukhtar Munzali,tare dani kawai."
"Am Barr Sagir Adam."
shima mikewa yayi gabatar da kanshi sannan ya koma ya zauna.

Sake cewa Justice Na Allah yayi.
"Lauyen wanda ake zargi ko yana kusa.?"
"Yes My Lord Am Barrister Tukur Garba Jakara,nine wanda nike kare wanda ake zargi Junaid Jamilu Kano.
Atare dani akwai abokiyar aikina."
"Am Barr Sumaiya Kabir, thank you my lord."
Justice Na Allah ya sake cewa.
"Lauyan mai kara bissimillah."

Fitowa Barr Bashir yayi yace.

"Ya maigirma mai sharia zanso Court tabani dama ingana da wanda ake zargi Jamilu Junaid."
Anbaka dama Barr Bashir.

Fitowa Dr JJ yayi waje fuskar shi murtuke da ita ya tsaya yana facing dina cikin abin da akema mai laifi tambayoyi.
Barr Bashir yace.

"Shekara ukku da watanni da suka gabata kazo a Kotu kace kaine shaida akan kisan da akaima Asma'u kace agaban idon ka Aminatu ta kashe kawarta ko zaka iya gayama Kotu yanda lamarin yafaru."?
Shiru yayi na ƴan sakanni sannan yace.

"Tabbas nina ganta da idanuna a lokacin da take kashe aminiyar ta saidai ita bata ganni ba tinda Amina ta shigo garin Kano ar anar nasani koma ince kusan atare muka shigo saboda duk wani motsin ta idona yake.
tunda naji tana waya da kawar ta,akan su hadu Hotel na tabbata bazata kulla alkhairi ba,shiyasa na dinga binta har zuwa Hotel din data kashe kawar tata."

Numfashi ya fesar a bakin shi,yafara matsar kwalla yaci gaba da cewa.

"Ina ganin Asma'u ta rungumeta ajikinta tana cewa kawata miyasa dole sai Hotel kadai zamu hadu nayi kewarki aminiya ta,fadaman mike damun ki.
Ina kika shiga aka nemiki aka rasa."
Abin takaicin sai cewa tayi.

Asma'u inaso ki taimaka mani kibani rancen dubu dari biyar uzuri ne ya taso mani.
daga tace mata bata dasu.

Shine ta matsa gaf da ita,tace.
Yanzun duk tarin dukiyarki Asma'u shine zaki hanani kudi gaskia tarayyar mu bata da anfani kuma baki da rana a wajena.

Cikeda damuwa Asma'u ta riko hannun ta,tace.

Aa kawata kiyi hakuri idan mijina ya dawo zan baki...
Shiru ya kumayi batareda ya ida maganar bakin shi yace.
Shine bata bari ta ida maganar datai niyar yiba,ta burma mata wuka a ciki.
hakan bakaramin razanani yaiba dakewa kawai nayi a lokacin tsabar kiɗima da nayi.

Itako mariganya cikin mawuyacin hali tace.

Nikika burma wuka Amina minayi maki."?
nan fa take cewa.
saboda dukiyarki na kasheki saina kwashe komai naki,tunda baki da amfani a wajena.
Sake burma mata wukar tayi a ciki,take jikina ya linku a bari bansan na banko ƙofar ba,har saida ta waigo amman ban bari ta ganniba da gudu nayi wajen masu Hotel din a reception daganan suka kira yan sanda amman saboda makirci dataga anganta kuma taji mun taho shi ne ta rungume gawar kawar tata, tana kuka,kamar ba ita ta aikata kisan kan ba gaskia Aminatu ke butuluce duk yanda Asma'u me kaunarki saida kikaci amanar ta wannan shine abinda ya faru."
Ya ida maganar a matukar raunane idanun shi sun jajir dasu kamar yayi kuka.

Nidai ina kallan ikon Allah Kotu ta zama wajen dirama ana mani kage da raina,amman abin mamaki dayawan mutane kuka sukeyi jin labarin JJ da alama ya shigesu kwarai da gaske sun aminta dashi,nidai nawa ido.

Murmushi Barr Bashir yayi yace.

"Amman kai miyasa kake bibiyar

Please Login or Register in order to submit comment