Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gamsar dani saidai kisani gangunan jikin mu zasuyi nisa dake amman ruhinmu yana tare dake."
Cewar Mama dake kuka sosai tanajin tausaina da tausan kansu.
"Nagode Mama Allah yakiyaye hanya yasa zaman can yafi nan alkhairi."
"Ameen."

Shiru ya biyo baya saidai sheshekar kukan da ya gauraye wajen karfin hali nayi nace.

"Baba wane gari zaku zauna a Sokoto."?

"Bakura zanje wajen aminina Alhaji Tijjani zan kwana biyu wajen shi daga baya zai nema mani gida ko a inane sai insaya,kinga bance maki ga taƙamaiman inda zan zauna ba."

"Toh Babana Allah ya tabbatar da alkhari zanyi kewar ku da yawa."

Na ida maganar ina murza tafin hannun shi,cikeda kewar su araina.
"Muma muna kewarki duk da haka zan dinga kawo maki ziyara duk bayan wata biyu Aminatu."
"Nagode Babana."
Rungumeni yasakeyi saidai munajin kewar junan mu sakina yayi yana aza mani kudi a tafin hannuna,juyawa nayi saka makon lokaci daya kure mana,ina ɗaga masu hannu natafi ina fita,naba Atika ita ke aje mani kuɗina saboda tsaron lalura,dubu ukku na zara a ciki na tafi ɗaki naba Cankwai da su Salame kowa dubu sai murna suke haka na zauna jikina yai sanyi ina tuna halin dana jefa iyyena shikenan ni kuma yan gidan mu duk sun watse a Caranci za'abar gidan mu ba kowa duk munzama tarihi, bakomai komai yanada lokaci kuma Haka Allah Yaso.


************
Koda Baban Amina ya koma gida da kanshi yaje gidan su Asma'u wajen mahaifin ta,suka gaisa cikeda mutunci gami karamci maida hankalin shi yayi wajen aminin nashi yace.

"Alhaji Yusuf nauyi da kunyar abinda da dangina suka aikatama Ahmad su suka hanani zuwa inbaka hakuri koda ka shigo falorn nan ba karamin nauyin ka najiba ina mai baka hakuri bansan hakan ta faruba."

Murmushin karfin hali Baba yayi yace.
"Bakomai Alhaji ni ban kullace kaba kuma nasan Komai ke faruwa damu Qaddararren al'amarine,Allah ya yafe mana baki daya saidai nazo maka da wata maganace ta daban nasan watakil zamu samu masalahaa cikin wannan matsalar da muke fuskanta."

"Inajinka da naji dadin hakan kwarai da gaske."

"Daman ba wata magana ce mai tsayiba inasan zan bar garin nan da zama ma'ana zan koma garin Sokoto."

Daidai Maman Asma'u ta shigo kawo masu ruwa taji zancen Baba,bata santa saki tiren ruwan ba, jikinta mace ta iso wajen ta zauna tafara kuka.

Baban Husna mikewa yayi yace.
"Bazai yuyuba Alhaji Yusuf wannan shike nuna bakaji daɗin abinda yan uwana sukai maka ba, tabbas da ciwo lamarin,saidai kada kamanta aminci ƙauna da yarda dake tsakanin mu,tun muna yara banda aminin dayafika a duk duniya,karfa ka manta kaine abokina wanda ya rokoni wajen iyalina haka kaima,har Allah yasa amintar dake tsakaninmu takoma wajen ya'yan mu,akan mi zaka rabu damu bayan mun saba koba abota kaifa makwabcina ne,sannan karka manta matar 'ya' take awajena kana so karaba zumuntar
dake tsaninmu ko mi kake nufi."?

Ajiyar zuciya Baba ya sauke yace.

"Alhaji kenan wlh tunda nike banta6a ganin mutane masu karamci dasanin yakamataba kamar kuba, zanso inrayu har karshen rayuwata taredaku,aganina hukuncin dana yanke hakan shine masalaha saboda kar kawunan mutane su rabu muzo muita zubda jinananmu a banza a wofi wannan shine dalilina."

"Aaa ban lamunta ba saidai inka kullace nine shiyasa."
"Ko kadan....
Da haka Baba yai mashi gamsashshen bayani kamar yanda yaima Amina har saida ya gamsu yace.

"Na fahimci manufarka kuma nima nagoyi bayanka dari bisa dari fatan Allah yasa komi ya wuce ya zama tarihi har abada,ita kuma Aminatu Allah ya wanketa a idon mutane kuma ya kubutar da ita daga halin data tsinci kanta a ciki,ita kuma Asma'u Allah ya jaddada rahamar shi agareta ya hadamu baki dayan mu agidan aljanna sannan yabamu ladar hakuri da juriya da mukayi yabamu ikon cin wannan Jarabawar."

Ameen suka amsa.

Sai lokacin Mama tasamu damar yin magana tace.

"tabbas zanyi rashin aminiya ta, inama bamu saba ba."
"Hakuri zakiyi Habiba addu'a zamitayi,kuma Haka Allah Yaso,sannan komai Lokacine."

Da haka Baban Aminatu ya koma gida yasa kowa ya fara haɗa kayan shi cikin sirri,daga Aminatu sai yan gidan su,ba wanda yasan zasubar gari sai Baban Husna da mahaifiyarta sai kuma Dada,daga su ba wanda yasani.
sai hada hada suke cikin mutane ana jifar su da maganganu son rai sudai basuce komai ba sun wallafama Allah komai sunsan shi zai masu gata.

Cikin dare wajen karfe biyu Baba yai sallama da aminin nashi,haka yai masu rakiya har iyakar gari a cikin mota suka dauki hanyar Sokoto shi kuma ya dawo gida zuciyar shi cikeda kewar su yasan yai rashin aboki nagari amini kuma makobcin arziki haka yadawo gida ba dadi aranshi,wannan kenan.
A hautsine ya mike tsaye ya kaiama table din dake gaban shi duka da hannun shi,idanun shi sun ƙaɗa sunyi jajir zagaye yafara cikin......
_Yar Mutan Kankia ce❣️_
Share
Pls
❣️


_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E21&22



A hautsine ya mike tsaye ya kaima table din dake gaban shi duka da hannun shi,idanun shi sun kaɗa sunyi jajir zagaye yafara a cikin Office zarya yafara,yaje ya dawo yana dukan hannun shi guda cikin ɗayan hannun shi,cikin kankanin lokaci wata irin zufa ta keto mashi.
"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un."
tareda kiran sunan.
"Minal."
Shine abinda labbansa suka furta,can kuma yace Mum da kidime yai bakin kofar zaibar office din sai kuma ya dawo ya dauki wayar shi da key din mota yai waje,Sectary dinshi nai mashi magana bai kula shiba yaja Mota sai gida cikakken parking bai tsaya yiba yai cikin gidan.
bedroom dinshi ya wuce kai tsaye ya janyo wata jikka duk tayi ƙura a jikin ta ya fiddo wayoyi guda biyu sai Tab ɗinshi kunna wayar yayi saidai dukkansu basu da chaji a jikin su, junawa yayi yace.

"Shikenan Minal nasan kinyi auren ki, kin manta dani a rayuwar ki miyasa zan gaza mantawa dake bayan ke,kin jima da shafe babin rayuwata,inalillahi wa'inna ilahir raji'un!
kadawo hayyacin ka Hussein mike damunka taya zaka nacema mace ɗaya kamar ansa maka hannu,Allahumma ajirni fi musubati wa'aklifni khairan minha."

Sake mikewa yayi yana kaima iska bugu da karfi jinshi yake kamar bisa ƙaya.

Wayar shi ya dauka wadda yake using da ita duk da layin na kasar TURKEY ne saboda can yatafi lokacin daya bar gida.

Number Minal yai dailing Switch off shine abinda akace mashi.
Wurgi da wayar yayi ta fadi gefen Cafet kwance yai kamar matacce,can kuma ya dauko wayar ya kira wani abokin shi Qasim kira biyu ya ɗaga.

"Qasim ka sai mani ticket gobe zan koma gida,nagaji ina bukatar kasancewa da dangina i lose more inportant things to me pls."

Koda ya gama wayar kunna wayar shi yayi ya kira Tariq not reachable ranar ya jima yana kiran numbers amman basu zuwa dan dole ya hakura ya kosa yaji Qasim yagama mashi shirin komawa Nigeria ya dawo gida,ba wadda yake son gani sama da Minal duk da kuwa yasan tai aure,amman ya gaza hakura da ita a rayuwar shi.

Shekarar shi ukku da watanni a Kasar Turkey ba abinda yakeyi sai zanen gidaje na alfarma yana saidawa daman abinda ya karanta kenan Arthector cikin kankanin lokaci Companyn shi yai shura,a cikin kasar Allah ya yarda.

da yamma misalin Qarfe hudu Qasim yagama hada mashi komai tafiya kawai zaiyi karfe goman dare ya isa Airport yayi Boading, jirgin shi karfe sha ɗaya ya tashi hakan kuwa akayi.

Washe gari da safe da misalin karfe goman safe Major Taufiq ya fito sanye cikin farar Jallabiya kana mashi kallo ɗaya kasan ya rame domin yai duhu,sai kuma yakara kyau.

Fitowa yayi daga side ɗin shi zuwa na Mum,a main entrance din shiga Apartment din nata yaci karo da Aisha,mutuwar tsaye tayi tana mashi kallon mamaki a iya saninta tasan Ya Tariq bai zuwa gida da sassafe.

"Auta come and give me a hug."
Da gudu ta koma falorn Mum tace.

"Mum kifito Ya Taufiq ya dawo wlh shine."

Da sauri Mum tayo ƙasa tana dafe kirji tana kallan Taufiq wanda yaketa smile afuskar shi,shidai mamaki ga yama kasheta.

Jefa kafarta tayi jikin ta yai masifar sanyi sosai tace.
"Kaine Hussein kodai mafarki nike."?
Yana isowa gabanta ya rungumeta,wasu kwalla masu zafi yaji sun shiɗo mashi.
"Forgive me Mum pls,I miss u."
Itadai ta gaza komai sai ajiyar zuciya da take shiɗewa tace.

"Alhmdullh Allah nagode maka daka maido mani da da'na."
Daga Mum har Aisha kallan shi kawai suke sun rasa mi sukeji murna tagama addabar su.

"Ina Abba yake."?
Yai maganar yana raba jikin shi dana Mum.

"Hussein dagske ba mafarki nike ba daman zan kuma ganin ka kafin inbar duniya?oh Allah nagode maka daka maido mani da ɗana cikin aminci."

Cikeda kewar mahaifiyar tashi yace.
"Haba Mum Calm down nine Hussein dinki nadawo gareku,kidaina kukan nan pls."

Riko hannun shi tayi tasa Aisha ta dauko mata hijab ta zira daman kayan bacci ke jikinta haka suka nufi side din Major Sarki,suna zuwa sukayi Private Falor din shi nan ta zaunar da Taufiq kamar wani jinjiri ta shiga bedroom din mijin nata,ta iske shi yagama shiryawa cikin Kakin shi (Uniform) zaije office.

Da mamaki aranshi ganinta da sassafe yasan ba lafiya.
Kallan da yake mata yasata yin magana.

"Alhaji nazo maka da babban al'amari muje kagani Suprise zan nuna maka."
baice mata komai ba ta riko hannun shi zuwa falorn shi,suna fitowa yai ido hudu da Taufiq yana zaune gefen Aisha.

jin tsayuwar iyayen nashi ya dago kai yana kallan su,da sauri ya sauka ƙasa bisa guiwar shi kanshi duke ƙasa yace.

"Ka yafemani Abba natuba."

Kwalla masu dumi sukai nasarar ziraro ma Major Sarki a fuskar shi,hannun shi yasa ya ɗagoshi ya rungume shi tsam a jikin shi yana karajin so da kaunar da ɗan nashi har a cikin zuciya yace.

"Bakaimin komai ba Husseini nine zan nemi afuwarka ɗana,Allah nagode maka daka dawo mani da ɗana mafi soyuwa agreni ina kaunarka Hussein."

Shima yanajin so da kaunar mahaifin nashi har cikin zuciya sunjima a haka sannan suka zazzauna.

"Inaka shiga Hussein kuma yaushe kadawo."?

Murmushi yayi mai yalwa a bisa fuskar shi yace.

"Kafin in gaya maku inda naje zankara baku hakuri kuyafe mani,nasan nayi maku rashin ɗa'a,daban girmama umurnin kuba dan Allah kuyafe mani."

"Munyafe maka Hussein nidai inasan insan halin daka tsinci kanka."
Abba yai maganar cikeda rauni.
"Toh Abba zanso ace kowa yana nan zan gaya maku komai."

Jikin Abba na rawa yakira Tariq bai dagaba sai yakira Aisha,bugu na biyu ta daga Abban yace taba mijin nata waya.

Kai mashi tayi.
Ko gaisawa bai bari sunyi ba Abba yace.
"Inasan ganinka yanzun nan."
"Toh Abba."
Haka yakira kowa ya sanar mashi.

Zai kira Mami kenan sukaji shigowar ta,tana waya,a firgice ta saki wayar hannunta,ƙasa tana dafe kirji ba kadan tagama tsorata ba ganin Taufiq.

Shiko Taufiq a sheƙe yake kallan Mami murmushin yaƙe kawai yai mata,shiko Abba yai tsammanin al'ajabi da farin ciki sukasa ta,gaza ko motsin kwarai banda Mum datasan wacece Mami.

Cikeda da farin ciki Abba yace.
"Kina mamaki ko Mufida lokaci guda Allah ya maido mana ɗan mu,ki karaso ciki kiji ɗumin danki."

Jikinta yai masifar sanyi da kyal ta ƙaƙaro murmushin tuggu da makirci ta iso wajen Taufiq,badan taso ba ta dafa kafadar shi.

"Sannu da dawowa Son Allah abin godiya kasakamu cikin tashin hankali daka tafi ina kaje."?

"Oyoyo Mami na,am happy to see u."
Yai maganar yana Murmushi.
Samir ne ya shigo yana ganin Taufiq ya saki wani yalwataccen murmushi ya rungume shi saijin dadi yake,bakin shi yakasa rufuwa yace.
"U re well come Bro, inajin kiran Abba raina saida yabani kilan kaine kadawo Allah ya karbi addu'an mu alhmdullh nice to see u again Hussein."

Murmushi yaima Samir ya sake rungume shi kowa fuskar shi fes da annuri banda Mami dakeji kamar ta kurma uban ihu tsabar bakin ciki.

Salamar Tariq suka tsinkaya ya shigo yana gama waya,idon shi na bisa screen din phone din shi,sautin muryar da yajine, ta maido da hankalin shi kan mutanen dake zaune cikin falorn tozali yayi da ɗan uwan nashi,wanda ya mike a zabure sai murmushi yake aikawa Tariq.

Kamar kananun yara haka suka rungume junan su cikin azama tare suka furta. "alhmdullh."
Suka saki kukan dadi da farin ciki.
daidai Fatash ta shigo gidan,itama tana ganin Taufiq ta fasa uwar kara a guje taje ta rungume su baki dayan su, ta saki marayan kuka tace.
"Ya Taufiq kadawo Allah mungode maka."
Shima kwallan yake fitarwa tsabar farin cikin ganin family din shi yace.

"Nadawo Fatima miss u all."
Kuka taci gaba dayi daman gwanace a harkar kuka.

Sake rungume shi Tariq yayi shima kwallan yake tsabar farin cikin daya samu kanshi a ciki.

"Hussein u re back,kodai ina mafarki ne kaine."?
Kukan farin ciki yaci gaba dayi.

"Hassan nine nadawo gareku kuyafe mani,nasan na saku cikin mawuyacin hali."

Harda sujuda saida Tariq yayi tsabar murnar ganin Taufiq dan yajima da fidda rai da sake ganin dan uwan nashi,ranar dai farin cikin da suka tsinci kansu bai misaltuwa musamman Abba Mum da Tariq,kowa sai nan da nan yakeyi da Taufiq sunjima suna yaushe gamo da junan su,sallah ta tadasu suna dawowa kowa ya zauna Abba yace.

"Kai muke sauraro Hussein ina kashiga dakabar gida."?
Gyara zaman shi yayi yai facing mahaifin nashi yace.

"Tun lokacin dana bar gida ba inda natafi sai kasar Turkey inda na tabbatar da wahala inga dan gida ba kamar sauran kasashen ba,najima ina jinyar kaina musamman halin dana jefaku a ciki.
Na daɗe ban yafema kaina ba,nayi danasi iya danasi dana bujirema iyayena.
Wahala na shata bawai dan bukatar kudi ba ko wani abu ba,aaa zullumi da fargabar rasa abubuwa masu mahimmanci danayi a rayuwata.
Ban iya fara komai ba,sai zaman gida kullin ina tunani,daman tun anan gida nakashe phones dina.
Ba wanda yasan zanyi tafiya hatta Usama dayake PA dina yawanci yasan abunda nikeyi.

Nazama maraya ta kowane fanni farin cikina,rashin iyayena da yan uwa,kukan zuci da yawan tunani shiya zama abokin firata.
Mutun daya yasan inda naje shine Qasim,komai zanyi shike daurani ahanya yana kwantar mani hankali.

Nasha jinya sosai harna fidda dai da rayuwa na ɗauka mutuwa zanyi saida nashare watanni masu tsayi ina ciwo,ga ciwon zuciya dandai banda hawan jini.
Qasim shi ne yai jinyata har Allah yasa na warke bayan ruwa dana sha leda leda haka nasha jinya marar daɗi.

Koda na warke dakyal nike zama tsabar ciwon dana kusan shekara a kwance ban iya komai.

Koda na warke kasayin komai nayi saidai in zauna gida dakyal Qasim yasa nafara harkar zanen gidaje da flowers su nike zanawa ina saidawa har kwangila munayi na tazanen taswirar Estate,mu saida saidai kuma nasamu ɗaukaka sosai yanzun haka Qasim shine MD na Company na,Allah yasa albarka na mallaki gidan kaina da abubuwa da dama,zan iya cemaku nasamu ɗaukaka a cikin ISTANBUL har zuwa yanzun da nike gaya maku,komai nawa yana can Qasim shike kulawa da komai shi Estimate Enginearing ya karanta idan aka bamu kwangilar gini shike Estimate din bulo nawa ginin zaici har a gama,haka nike zaune a kasar Turkey saidai zuciya ta baki ɗayan ta,tana gida nasan narasa abu mai mahimmamci agareni saidai inasan indawo gida amman kamar an rikeni muddin nace zan dawo gida ina rasa sukuni a rayuwata,har dai jiya Allah ya nufa zan dawo gida,dan Allah ina kara neman afuwar ku,kuyafe mani."
Numfashi yaja mai nauyi ya kuma cewa.
"Kunji labarina ban wani fuskanci kalubale ba,dayawa saina lalurar danaita fama da ita watanni da dama.
Amma tunda naga duk abinda nasa agaba inasamu hakan ya tabbatar mani da cewa iyayena sun yafe mani a duk inda nike albarkar su natare dani,dan Allah Mum,Abba da yan uwana ina mai kara baku hakuri kuyafe mani."

Hawaye iyayen nashi suka goge suna maijin tausayi na dan nasu.

"Hussein wlh tunda nafahimci rayuwar da muka saka aciki,nafara dana sanin kin janyoka a jikina na share maka hawayen ka amatsayina na mahaifin ka, ina ganin sam bakai dacen uba ba,ban cancanci a nunani a matsayin ubaba,saboda ban kasance mahaifin dake sharema ya'yan shi hawaye ba, inhar zan gaza bawa ɗana duk wani farin cikin daya dace dan haka nidai bakai mani komai ba kuma nayafe maka duniya da lahira Allah yai maka albarka."

"Ameen Abba nagode kuma ni nasan nayi dacen iyaye saboda duk duniya a lokacin ba wanda yaso yai mani gata kamar ka nidai ne nagaza fahimta, idona ya rufe zuciyata,ta makance kunne baiji idanuba basu gani Qaddarata tana tare dani komai ke faruwa dani Haka Allah Yaso saidai nasan komai daren dadewa zai zama tarihi tunda komai lokacine da wannan na tsaya Abba ina alfahari daku amtsayin ku na iyayena."
Jijina kai Major Sarki yayi yana alfahari da ɗan nashi a cikin zuciyar shi,Mum tace.

"Allah ubangiji ina rokon ka,wannan yaro daka maido mana shi cikin aminci Allah kai mashi zabi arayuwar shi kasa mashi albarka,Hussein kaimana biyayya kowa ya shaida,yau da gobe batar ba komai ba dan haka mun yafe maka bamu rike dakai Allah yai maku albarka baki dayan ku."
"Ameen Mum."

"Gaskia ne ni kaina narasa abinda zance saidai muyima Allah godiya."
Cewar Mami.

"Hussein tunda katafi idan natunaka,nakan shiga kunci sai in ɗaura ma kaina laifi duk wani baraka da sabani daya shiga tsakanin ka da Abba nine sila da ban shiga tsakanin ka da Aminatu ba da hakan bai faruba,dan Allah kayafe mani."

Murmushi yayi yana jinjina girma da ƙimar da Samir keda shi a ranshi yace.

"Nayafe maka Ya Samir ban rikeka da komai ba Haka Allah Yaso."

Shidai Hassan banda Murmushi ba abinda yake baice komi ba daman shi gwanine a smile saidai Hussein dake maida mashi martani suna karajin so da shakuwar a tsakanin su.

Shiru ya kaure wajen kowa da abunda yake sakawa aranshi can ya dauki wayar shi yai dailing number Switch off shine abinda aka ce mashi kwantar da kanshi yai bisa kushin yana nazarin rayuwa tare da rufe idanun shi masu yima shi gizon abubuwa da dama daurewa kawai yake saidai tunda ya diro da kafar shi a cikin kasar shi yakejin akwai babban al'amari daya samu Minal amman kwarjin da iyayen nashi sukai mashi ya hanshi yai tambaye su,yana tsoron kada suga har yanzun bai girmama umurnin suba.

''Yaya kasan wani abu."?
Hakanan yaji gaban shi yafaɗi.
''Aaa minene Fatima.''?

Kallan kowa tayi ba wanda ya hanata magana tace.

"Tafiyar ka abubuwa da dama sun faru marassa dadin ji da sauraro a ciki kuwa harda kai Minal gidan Ya.....
Wani uban tari ya sarƙi Taufiq har saida aka bashi ruwa sannan ya lafa cikin kankanin lokaci idanun shi sun gama canza launi.
Karfin hali yayi yace.

"Inajinki gidan mi.?"
"Gidan Yari aka kai Minal."
ta ida maganar a raunane.

Zumbur ya mike tareda furta inalillahi wa'inna ilahirraji'un!zufa na tsatsifo mashi kanshi yai bala'in sara mashi.

"Mitake a gidan Yari Abba ina auren nata."?
Cikeda damuwa yai tambayar.

"Aurenta babu saboda mijin da zata aura a ranar
da za'a daura masu aure yai accident da abokan shi suntaho daurin aure baki dayan su suka rasu wannan dalilin yasa Aminatu batai aure ba,ananan Qaddara takaita kano dan gujewa fushin da mahaifin ta keyi da ita,ta hadu da iftila'i akace ta kashe kawarta Asma'u kaji dalilinta na zuwa gidan Yari kuma an yanke mata life Prison."
Komawa yayi dabas ya zauna bisa kushin wasu kwalla yaji sun ziraro mashi masu bala'in zafi yace.
"Nayi imani da Allah Minal baza.......
_Yar Mutan Kankia ce❣️_
Share
Pls
❣️

_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E23&24




"Nayi imani da Allah Minal bazata ta6a kashe Husna ba,wannan kuma ƙagene dole akwai masu sa hannu a cikin wannan lamarin haba aidagajin abinda kai zai dauka ansan shi."
Ya ida maganar cikeda rauni.
Sakkowa yai kasa ya rike hannun mahaifin shi cikin raunananiyar murya yace.

"Abba kasa mani albarka kai mani izini inje in ku6utar da yar uwata a cikin wannan mawuyacin halin da take ciki nakan rasa sukuni jin dadi da farin ciki a rayuwata,ashe dai Aminatu tana cikin mawuyacin hali dan Allah Abba ka taimaka mani kai mani izini."

Kallan tsaf yakema ɗan nashi ya kara gasgata so da kauna da Taufiq kema Aminatu,ada ya ɗauka so shirmene ba gaskia bane ya ɗauka nishadi ne kawai irin na ya'yan zamani ashe ba haka bane.
dan ada ba'adamu da auren soyayya ba mace takan auri namiji dan Jarumtar shi,shi kuma namiji yakan auri mace dan nasabarta da addinin ta,kalilan ke auren matan su,saboda kyawun su kodan soyayya mafi yawa akan masu aure basu san junan suba kuma su zauna cikin aminci da abokan rayuwar su.
ya ɗauka har yanzun ana tafiya a wannan al'adar hakan yasa yake ganin Taufiq zai iya rabuwa da Aminatu ya rayu batareda itaba shiyasa ya aura mashi Khairat ashe ya tafka babban kuskure,ashe soyayya gaskia ce ya gasgata hakan akan ɗanshi Hussein.

Sihirtacciyar aziyar zuciya ya sauke yace.
"Naimaka izini Husseini Allah yaimaka albarka inasan kaje ka kwatar ma yar uwarka hakkinta,ka wanke ta a idon duniya saboda kalilan ne kaɗai suka amince Aminatu bazata iya kisaba amman mafi akasari sun tafi akan itace ta kashe Asma'u duk da itadin ta amsa hakan agaban kowa cikin Kotu."

"Kwarai kuwa Abba,ba komai yasa ta amsa laifin daba nataba sai tarin fargaba da rashin mafita, ta za6i mutuwa akan rayuwa badan komai ba,dan tahuta da bala'in dake cikin rayuwa saidai komai yana da lokaci Abba nagode maka da goya mani baya ɗari bisa ɗari."

"Allah yatayaka cika wannan burin naka Hussein"
"Ameen Mum."

Da haka kowa yaita sake sake a cikin ransu.
ana kiran la'asar kowa ya tafi masallaci,suna dawowa Tariq da Taufiq sai Fatash suka shiga mota sai Malili gidan Tariq.

"Oyoyo."
Daddy shine abinda Major da Aira ke cewa,ba karamin sani kukaima Taufiq ba kullin sai Tariq yabasu labarin shi banda pic da kusan kowa yana da nashi.

Mamaki yake yana ganin ya'ya har biyu agaban ta baisan dasu ba saidai ba yan biyu bane duk mazane tsakanin su two years ne babban keda 4yrs baijima da barin kasar ba ta haihu sai karamin keda 2yrs bata jima da yaye shiba.
Abubakar da Umar shine sunan su yai mamaki ganin har Tariq yai ya'ya huɗu,haihuwa ukku gwanin shi'awa da burgewa sai wasa yake da ya'yan nashi sun jima suna gaisawa,wannan kenan.


***********
Babane a cikin Sokoton Shehu duk abinda Alhaji Tijjani zaiyi yagama komai yaima Baba hanya ya sayi gida.
Saidai ba a Sokoto ya sayi gidan ba,a Zamfara ne ya sayi gida cikin ANKA Local Govt.
Yan kwanaki suka ƙara a Sokoto daga Bakura suka koma gidan nasu makimanci yanada gate sannan akwai Compound wanda zai iya daukar mota biyu zuwa ukku,kana shiga cikin harabar gidan falor ne babba kasancewar gidan safe contet ne mai dauke da 4 bedrooms sai kitchen and store.
A bayan gidan kuma akwai BQ sai ɗakin mai gadi abakin gate,ba komai ke cikin giban sai gadaje da suka saka,ba kujeru zan iya cewa kusan kudin shi Baba ya kwashe ya sai gidan shiyasa suka sai kayan bukata na yau da gobe da kayan ma'ai kaci kayan aiki na (kitchen) danma Alhaji Tijnani ya taimaki Baba sosai haka suka koma saidai bamai wani lakka a cikin su danma sun ɗan saba akalla zasuyi yan watanni da komawa,Zainab da Jidda aka newa makaranta a cikin Anka ita Zainab tana SS3 sai Jidda auta tana JS1 haka suka fara zuwa makaranta shi kuma Baba ya nemi Transfer ya koma aiki a asibiti general hospital Anka daman likitane ko ince malamin asibiti bai jimaba ya soma zuwa aiki,Ahmad kuma ya jona Masters dinshi a University of Gusau.

Haka rayuwa ta kasance masu saidai ransu na tareda Aminatu akoda yaushe suna tunata.

*********
Washe gari safe Rt Major Taufiq ne cikin shadda Milk mai aikin Coffee yai side din mahaifin nashi duk inda zai wuce Soldiers ke sara mashi saidai yai murmushi koda yake Reteriate ne,haka Soji suka rako shi yana zuwa bakin Main Entrance suka kame nciki yayi akai sa'a ya iske Mum da Mami suna ganin shi cikin tsananin son da sukema ɗan nasu suka rungume shi suna gaisawa bai jima ba yace.

"Abba daman nazo in maku sallama zan tafi shiyasa nazo kusamani albarka."

"Major ina zaka kuma tunda safe."?
"Wajen Aminatu zani,saidai zan fara biya gidan Kawu kafin in wuce Kano."

"Okay amman baka bari ka huta sannan."

"Abba banji zan iya kara awa ɗaya a garin nan batareda natafi wajen Minal ba kwara inje musan halin da muke ciki kamar zaifi."
"Shikenan Hussein kai dawa zaka tafi."?
"Usama."
"Amman Hassan fa."?
"Yanada aikin operation kuma shine on duty because He's Incharge of Theater abubuwa sunyi mashi yawa."

Jinjina kai Major Sarki yayi alamun gamsuwa yace.

"Allah ya tsare hanya yasa kadawo lafiya kuma Allah yabada nasara akan abinda kasa agaba damu baki daya."
"Ameen Abba."

"Allah ya kiyaye Hussein ka kula kaji Allah yai maka albarka."
"Ameen Mum."

Itako Mami da kyal ta ƙaƙaro murmushin da baikai zuciba tace.
"Anya Hussein ba zakaba kanka wahalaba anya kana ganin zaka iya ja da wannan shari'ar kisafa akace tayi karka manta fa."

Wani shekakken kallo Taufiq ke aika mata a gadarance yace.
"Kema kin aminta Minal zata iya kashe Husna."?
"Am am nidai tsoro ɗaya aje a ɗaga kara kuma tazo ta afka

Please Login or Register in order to submit comment