Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bani magana da kowa nakama kaina kwarai da ainun.

Munfi wata biyu a haka da Cankwai ba wani wulakanci bankomai a dakin sai su keyi.

Haka rayuwa takasance dani a gidan Yari duk wadda ta gwadani da yatsa saina sauke shi cikin kankanin lokaci kaf clif din Cankwai na sai tasu saidai banta6a doka indoka da kowaba saida Cankwai shima sau ɗaya akaro nabiyu na zabi in kasheta da dai in cacar baki da ita ko dambe wannan kenan.


*******Bayan wani lokaci daya shuɗe abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda abinda ya girgizani fiye da tunanin mai tunani,mun anso abinci nadawo daki na'aje shi zanje inyo fitsari saboda matsuwa data kamani,fita nayi zuwa bayi nabar Nusaiba adakin tanacin nata abincin saboda tana iya kawo mani ziyara batareda fargaba ko tsoroba tinda nasamu yancina.

Inadawowa fitsari naga kofar dakinmu cike da prisonors harda Atika da Karima duk ma'aikatane Cankwai keta bala'i tana cewa.

"Bani kadai nagani ba,nakira wadannan bayin Allahn zasu wuce sunga tana zubama abincin Dago shinkafar 6era kuma gasu atambayesu idan ba'ayarda dasu Mairo ba.


Mutuwar tsaye nayi jikina yai bala'in sanyi ina maimaita wace Dagon kuma waya zuba guba a abinci na?anya nidai kodai banji da kyauba.

"Saikin cinye shi."
cewar Magajiya.

Fito da abincin akai waje da Nusaiba tana ta kuka ance saita cinyeshi,su Atika sun hana Oga Lawal da Adam duk sunzo taki taci abincin sai aikin kuka da takeyi taki yarda ta hada ido dani.

"Ina Aminar take."
Gani nace jiki a mace
"Kinada yar tsama da Nusaiba ne."?

"Aaa asalima bantaba ko gardama da itaba zan iya cemaka itace kawata a wannan gidan."

"Ke Nusaiba kin zuba shinkafar 6eran nan kodai anmaki sharri ne,in kinsan baki zuba ba kici abincin."
Cewar Adam
Girgiza kanta tayi tana kuka sosai tace.
"nazuba ba karya akai mani ba."

Kowa ya tsorata ana mamakin ina tasamu shinkafar 6era tana Prison.

"Shikenan Lawal samu leda kasaka kwanon abincin nan za'akai case din nan a gaba dole ajiwanda taba yarinyar nan wannan aikin dagani sata akaita dan ba inda zata iya samun gubar nan."
Inji Oga Adam.

Nidai salati nikeyi ina al'ajabi mi nayima Nusaiba takeson kasheni ko shiyasa ta nace muyi kanwace,kuma in ra'ayin kantane ai batajin komai gashi tana kuka kamar ranta zai fita gaskia na maganar Adam sakata akayi waya sata in hakane?

Ni kadai nikema kaina Question daban da amsar su,saidai ina yawan ganin ta da Karima (Gandiroba) amman bansan mi sukeba.
Never Karima bazata aikata hakan ba,kodai Cankwai kesan kasheni tai amfani da damarta tasa Nusaiba dan tasan tana tsoronta,sai kuma wata zuciyar tace Aaa aidata fadi wanda yasata tunda itadin tasan ba life Prison zatayi ba,kodan takoma gun ya'yan ta data keson takoma gida nan da shekara mai zuwa wa'andin ta ke cika ta rayu dasu, bata iya aikata kisa ba.
gaskia akwai wata a kasa banza batakai zomo kasuwa dole akwai abinda ake boyewa akwai lauje cikin nadi.

"Shikenan Sir insha Allah za'a tsareta zuwa gobe asan halin da aka ciki.
Kuma ba wanda yaci poisons din har ita ,aaa sai an duba ansa ainahin gaskiar lamarin zuwa safiya."
"Okay Sir."
Oga Adam yagama magana da shugaban su ta waya.

"Karima aɗauketa akaita wancan dakin a killaceta kar abar kowa ya rabeta kima mai kula da dakin magana,kuje."

Bansan yanda akai naji tausayin Nusaiba araina ba duk da itadin tai niyar kasheni saidai ban tunanin dan karin kanta akwai abinda mu bamu sani ba,nasan idan aka bin ciketa tabbas za'a gane gaskiar lamarin har aka tafi da Nusaiba bata bari idanun mu sun haduba.
lamarin Nusaiba ya dameni har kuka saida nayi mata.


Washe gari da safe kuwa aka tashi da mugun tashin hankali misalin karfe goma na safe,lokacin Adam yasa a fiddota zasu kaita wajen bin cike saidai ana bude dakin da aka sata aka iske gawar Nusaiba.

Tashin hankali kowa ya shiga musamman Adam,kiran wanda ke kula da wajen akayi saidai a binciken su anduba kaf makullan dake hannun mutumin ko ɗaya ba'arasa ba.

Ansake kiɗimewa gashi kwadon dakin agarkame ba yankewa akaiba dole dai da mabudi aka bude shi.
Kuma kwadon bai sharing hakan na nuna masu karfin iko suka aikata laifin dan dagani wannan ba aikin Prisonors bane,daga sama ne.

Ba 6ata lokacin yan Sanda sukazo da shugaban gidan aka dauki gawar Nusaiba sai asibiti sukahau bin ciken su.

Labarin da mukaji ance shaketa akaita ta hanyar tsada mata numfashi da abin dode hanci kamar pillow har rai yai halin shi,da haka akai hotunan gawar aka nemi iyayen ta akayi Jana'izarta.

Sosai shuwagabanni suka fara binciken ainahin kisan Nusaiba sosai suke bincike daga sama har kasa,wannan kenan.

```Kadan daga cikin rayuwar gidan Yari kenan mai dauke da kalubale kala kala narayuwa Allah yatsaremu daga halaka ameen```

tsaye nike agaban su nakasa ko kefta idanuna akansu.....
_Yar Matan Kankia ce❣️_
Share
Pls
❣️

_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E17&18



tsaye nike agaban su nakasa ko kefta idanuna akansu,tsabar mamaki idanuna sun gama bushewa ko ɗigon kwalla babu a idanuna,su kuwa idanun su sunyi jajir kana ganin kasan sunfi kowa shiga tashin hankalin halin dana shiga a duniya.

"Ya'ta kece kika koma haka."?
Cewar Mama araunane tayi maganar.

Baya na juya masu zuciya ta,tagama karyewa kallan kwayar idanun su,shi zaisa so da kauna dake tsakanin Ɗa da Mahaifa yadawo a cikin zuciya ta bayan gogeshi da nike tunanin najima dayi.

"Anty Aminatu dan Allah ki waigo ki kallemu kece farin cikin mu."
Cewar Ahmad.

Batareda na waigo na kallesu ba nace.

"Da bakuzo gareni ba,miyasa bakuci gaba da shafe babin rayuwata ba har abada kamar yanda kukayi niya,kunzo dan kugaya mani cewa kuma kun tsaneni akan abinda na aikata, kuma kun aminta zan iya kashe Asma'u shiyasa kuka goge babin rayuwata!
Dan Allah Baba nagode da ziyarar ku,kubarni in rayu ni kadai zanfi samun sukuni arayuwata nagode maku Allah yasaka maku da alkhairi."

Na juyo ina kallan kwayar idanun su sannan na
Juya,inajin kwalla na neman kufto mani a kwayar idanuna, na danne su.

"Mamana tabbas kina iya fadar komai akanmu,mune iyayen ki,saidai mun gaza kula dake kamar kowane ɗa mun gaza baki duk wani farin cikin da kike nema agaremu matsayin ki na Ya' musamman ni Aminatu nahanaki right dinki da dama,ya'ta ra'ayina shi kaɗaine abin girmamawa banta6a duba matsayin naki ra'ayin ba,baki taba zuwa da bukatarki ba,nabi naki ra'ayin saidai nawa kaɗai kikebi baki taba yiman musuba ya'ta kinman biyayya Mamana kina zaton Allah zai barki ki dauwama anan,bayan kin mashi biyayya kuma kin kautatawa iyayen ki."?

Sai lokacin naji saukar kwalla bisa kuncina still ban juyoba dan bansan haɗa idanuna dana iyayena,hakan yana ƙara karya duk wani kudurina na shafe kowa da komai arayuwata inzama ni kaɗaice banda kowa.

"Baba tabbas da'ace zan dauwama anan zanfi kowa farin cikin hakan zanfi kowa jin dadi tuni na fiddarai dajin dadin rayuwa daman ni bansan shiba kalilan nasani,wacce ke sauraron matsalolina tabani shawara akowane lokaci tana tare dani,sannan ta tare mani kowane bangare yau gashi an wayi gari narasata duk wani farin cikina ya datse,akan mi kuke ganin inada ra'ayin rayuwa a cikin mutanen da suke barazana da tawa rayuwar, na rokeku dan Allah kuje kuyi rayuwar ku kada ku damu da duk wani nawa farin cikin inayi daidai gwalgwado
koda nike a wannan halin,hakan bai hana mani sukuni ba, kuma ina yawan gode Allah akowane lokaci saboda haka Allah yaso ya ganni."

Zuwa wannan lokacin Mama tafara kuka mai sauti,tareda Atika dake gefenmu anbamu minti talatin ne, itama goge kwalla take niko firi firi da karfin tsiya na tsaida kwallan idanuna.

"Aminatu."
Muryar mahaifiya ta daki kahon zuciya ta,bansan na waiga ba ina kallan fuskar ta kwalla na zirara idanun ta sun kaɗa jajir tausayin ta game da kaunarta ya rufeni nasan duk abinda Mama zatayi da izinin mijinta takeyin shi domin itadin mai yawan biyayya ce ga tarin hakuri.

"Kalamanki na nuni da irin tsanar da kikai mana dagaske kin tsani mahaifan ki."?
Samun kaina nayi da girgiza mata kai.

"Karki manta ya'ta ba wata uwa ko uba dazaiso yaga ɗanshi ko ƴar shi a cikin mawuyacin hali iyaye sukanso ya'yan su fiye da yanda sukeson kawunan su,tausayin su da kaunar su yakan mamaye zukatan su,lokuta da daman nakanji inama in fansheki saidai ba dama,a kanki ya'ta mahaifin ki ya kwanta lalura ta watanni,
Bai zuwa ko ina duk kaunar dayake maki itace ta jefa shi cikin halin da yake ciki a halin yanzun,duk da haka kina zatan iyayen ki basu kaunarki."?
Sake girgiza mata kai nayi.

"Kada ki manta Aminatu, tun lokacin da Allah ya azurta iyayen ki da samun cikin ki,kowane burin su yana kanki,har aka haifeki sai soyayar su takoma akanki baki dayanta ba abinda yai saura tsakanin iyayen ki sai tausayi amman kaf son su sun mai dashi kanki.
sukan kula dake ci sha sutura,lafiya,ilimi,makwanci da duk sauran dawainiya tun kina ciki har zuwa girman ki wannan kulawar ta ubace,anya akwai wanda yafi wannan kaunarki akaf duniya Aminatu."?

"Aaa." nace awannan karon ina danne zuciya ta domin ta gama karewa.

"tarbiya datafi komai wahala zuwa kula da duk wani lalurarki musamman ta ya'mace wannan fadi tashin na mahaifiya ne,tundaga daukar ciki rainon shi haihuwa har zuwa shayarwa mahaifiyar ki itace taci kashin ki,fitsarinki, ki mata kuka ta lallasheki,in baki lafiya bata iya bacci,murmushin ki shine dariyar ta,bacin ranki shine kukanta bata da buri kullin sai taganki cikin aminci addu'arta Allah yakareki daga sharrin zamani ya haɗaki da miji na kwarai yaima rayuwarki albarka duk wata fitina ko masifa ta duniya Allah ya kareki da ita aduk inda kike samu kanki sannan ya kareki daga sharrin makiyanki ya dauraki bisasu a kowane hali,wadda ta fifita rayuwarki akanta tata harkina da madadin ta a duniya."

"Aaa Mama."
wannan karan zuciya ta gama tsinkewa kukan dana danne gam bansan ina kwallaba.

"Idan hakane Aminatu kiyima iyayenki uzuri sunfi kowa son ganin ki,mungaza zuwa ganin ki cikin lokaci tsabar tsoro da fargabar irin halin da zamu sameki zukatan mu sun raunana bamuda sukuni arayuwa duk lokacin da zamukai lomar abinci abakin mu sai kin fado mana arai wane hali kike kinci baki cikiba Allah masani karshe haramiyar mune cin abincin kiyimana afuwa Aminatu muna sonki har yau har gobe har abada ke tamuce dan kin shiga cikin hali bazamu guje maki ba kullin muna maki addu'a wlh Aminatu Allah ke sonki da rahama kisa aranki bazaki ta6a ta6ewa ba,kedai ki daure kici wannan jarabawar Haka Allah Yaso kuma Komai Lokacine ya'ta."

"tabbas Mama nasan banda waɗanda sukafiku akaf duniya kune komai nawa ana ziyara danjin daɗi amman ni nawa yana kaurace mani nakan shiga matsanan ciyar damuwa ina rasa duk wani farin cikina nakan tuna da Asma'u wannan shi ne abin tashin hankalina yau kimamin shekara ta ɗaya da wata shidda ina wannan gidan taya kuke tunanin zanso infita bayan kalubalen dazan fuskanta idan nafita yafi na nan,Allah kadai yasan mutane nawa ke tsine mani waje akan wannan laifin dana aikata!
Dan Allah Mama,Baba kubarni in rayu nika ɗai kamar yanda nasama raina banida komai da kowa."

"Aaa Anty Aminatu bazamu iyaba kece farin cikin mu."
Cewar Ahmad dake kuka sosai.

"Saura mintina biyar ganawar ku ta kare Alhaji."
Cewar Atika.

Jinjina kai Baba yayi sai naji fargaba ta dirar mani a cikin zuciya ta,nasan tafiya zasuyi subarni,ashe dagaske nida kowa nawan ɗin har abada shikenan banda raban ganin jinina a duniya,nan ne zan ida rayuwata inalillahi wa'inna ilahirraji'un.

Karfin hali Baba yayi yace.
"Mamana yanda kikace hakan za'ayi,saidai kisani nafi kowa bukatar son ganin ki,har nan kwanta ciwo koda nasamu lafiya banji zan jure tsawan lokaci batareda nazo ganin kiba ya'ta ina maki fatan alkhairi,Mamana mai kyakkyawar zuciya Ya Allah kazama gatan Aminatu akowane hali ta tsinci kanta Allah kada kaba duk wani makiyinta ikon nasara akanta,Ya Allah idan an ƙulla mata ka warware mata."

Ya ida maganar yana kuka mai sauti,wani irin tausayin iyayena ya rufeni.
Ameen suka amsa baki dayan su.

"Muje Dago lokaci yacika."
"toh."
najuya zantafi
"Ga sako Mamana sai kin jini."
Girgiza kaina nayi.
Kuɗi yabani banjin zan karba dan muddin nace zan amfani dasu zan dingajin ji6in iyayena so da kewar su kadai zai iya hanani sukuni arayuwata.
Banjira cewar shiba na shige ciki nan nabar Atika.

Tafiya nike lakwas kamar marar lakka,mahaifina kawai nike gani a cikin zuciya ta.
Kyakkyawan Buzu fari mai kyawun gaske duk yayi duhu ya rame sosai saidai hancin shi dake tsaye bisa fuskar shi,kallan danike ma mahaifina duk da bansa na'ura na auna shiba take nagano yana fama da hawan jini mai bala'in zafi Chronic, un expected ana iya rasa shi,hakan yasa na sassauta kalamai na agaresu gudun kada zuciyar mahaifina tasamu matsala saidai harga Allah naji zafin kin kawo mani ziyara da sukaƙiyi kodai mahaifan Husna sunzo guna yakai sau biyu hatta makiyana su Anty Hafsat sunzo sai iyayena dole inji ba dadi araina.

Ina zuwa daki na iske su Cankwai kwance a gadona da sauri ta tashi zaune zata shidar mani gado.

"Ki zauna ba kwanciya zanba."
Nace mata ina zama ƙasa na buga uban tagumi abubuwa da dama namani yawo akai tunani ya addabeni jinayi an dafa kafadata Cankwai ce sai su Mairo sun sakani tsakiya.

"Mike yawan sakaki damuwa har haka Aminatu.?"
Cewar Cankwai takirani da cikakken sunana,kuma cikin sanyin murya ashe daman Magajiya tanada daɗin murya harhaka,cikeda mamaki nike kallanta nace.
"Bakomai."

"Aminatu ada na daukeki makiyiyata natsaneki akan laifin da kika aikata alhalin tsakanin kine da wadda kika kashe da ubangijin mu,bantaba cewa ni miyasa banganin girman nawa lafin ba, saina wasu,dan Allah inason ki yafe mani abubuwan da nai maki abaya,wannan gabar na janyeta Sarauta kuma zan maki mubaya'a."

Duk da ina cikin damuwa saida na maida attension dina wajen Cankwai nidai nasan ban gaba da ita kawai dai mulkinta ne ya isheni ga zalinci amman bata gabana daman itace mai neman fitina kullin.

"Nayafe maki sannan kisani bantaba kullatarki ba,nidai ina kare kaina daga gubarki na cutar dani da kikeson yi wannan shine,sannan maganar Sarauta kuma nibani buƙata kuma daga sama aka naɗaki sannan kisani indai tanice bazaki ta6a faɗa dani ba,saidai inke kikaso hakan,sannan ina godemaki da Allah yasa ta hanyarki na ku6uta daga halaka duk da naso hakan kodan inhuta da ƙuncin rayuwa,amman haka Allah yaso shi kaɗai yasan dalilin nuna mani rayuwa iri iri har zuwa yanzun inakara gode mashi.

"Bakomai nima insha Allah bazan kuma faɗa da kowa ba,nagode maki,itama Nusaiba Allah yajikanta tabbas akwai lauje cikin naɗi."
Cewar Cankwai.

"Allah yaƙara tsaremu baki dayan mu."
Nace.
Ameen duk suka amsa

Aminci sosai nike da Cankwai mulki ba abinda tafasa tsabar yabi mata jini amman bata zalinci ansamu freedom amman akwai gadara.
Haka rayuwa taja komai saidai muce alhmdulillah.

********Hafsat ce tsakar gidan su Aminatu sai bala'i take tana turawa Amina Jafa'i iri iri.
tana cewa.
"Da kikaji ance munje gano Aminatu gidan Ɗan kande,ance maki dan muga lafiyarta mukaje?
Waike Khadija kin dauka har yanzun inason Amina bana gaya maki ba,wlh natsane ta aidaman nagaya maku tayi auren mugani yanzun gata,ta karata gidan Yarin sai taje tayi soyayyar acan mugani."

Banda kallan mamaki ba abinda Mama kema Anty Hafsat.
"Hmmm Hafsat kenan daman angaya maki ni Khadija banda tunani dahar zance kinason Amina,tuni nasani baki sonta kuma na tabbata banda wulakanci mizai kaiki gunta,wlh ki guji rayuwa kema kin haifa dai."

"Alkhairi zan gani kuma Amina saidai gawarta badai tafito da kafarta ba."

"Aikin banza aikin wofi ashe dai zata fito kuma mu zamuyi mata sutura Sannan mukaita makwancin ta ai da sauki tunda bacan za'a binneta ba."
Mama ta ida maganar a fusace.

"Kudai kuka sani kuma nida Hajia Mufida (Mami) mutu karaba na lura kina hassada dan kinga tana sona."

"Hhhh Hafsat kenan tabaya ta raggo ai dalilina kikasan Mufida, komai zaki samu arzikina kikeci ba komai ko alahira wani nacin arzikin wani bare nan gidan duniya kedai ki guji rayuwa Allah ya kyauta."

"Kada inci arzkin naki saimi haka za'a maga gantalewa dai,nagaba yai gaba wlh bakin ciki saidai ya kasheki kuma.......
Baba ne ya datse mata maganar ta,ta hanyar cewa.

"Ashe daman duk abinda ake faɗa akanki gaskia har haka kika tsan.....

_Yar Mutan Kankia ce❣️_
Share
Pls
❣️

_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E19&20



"Ashe daman duk abinda ake faɗa akanki gaskia ne,har haka kika tsani Aminatu lallai kam Hafsat banda makiya kamarki a duniyar nan, wlh nakuma ganinki kinzo mani gida sai nasa hukuma sun kaman ke,alakar dake tsakanin kida matata nayanke har abada."

Baba ya ida maganar a fusace.

"Saime danka yanke alakar dake tsakanina da Khadija,daman ba damuwa tabace da ita da babu duk ɗaya kuma kuna kadan kagani,kuma gashi kun fara gani 'ya' na gidan Yari garkame."

"Fitar mani gida tunkan in illataki marar mutucin kedai ba yar uwar rufin asiri bace,azatona koba rayuwae Khadija ke mai iya zamarwa su Aminatu uwace ashe ba haka abin yake ba,ke baki da burin daya wuce kiga bayan su bakida wani buri sai kiga sun halaka ta Allah ba takiba Hafsat kuma mu bazamu nufi naki ya'yan da sharri ba domin shi sharri dan aikene kuma alhaki kuikuiyone komai daren dadewa zaibi mai shi Allah ya shiryeki in kedin mai shiryuwa ce."

"Kaima kanka addu'a kafin kai mani ,nima na datse duk wata alaka bani baku, kowa yaci tuwon gidan shi,ayican da kayan kunya maciya amana."

"Munji fitar mani gida kuma nima bani bake ina mai bakin ciki ace ke Yayata ce inama ban haɗa jini dake ba,Allah ya mantar dani duk wani so da kaunar danike maki Hafsat,ban alfahari dake a rayuwata kin zamar mani Qaddara Allah yafiki aniyarki ta koma maki."

Mama ta ida maganar ranta a 6ace.

"Oho dai Khadija naimaki nisa wlh saikin taho."
Fita tayi tana murmushi abindata Mama taita kuka,shiko Baba yabar gidan baki dayan shi ranshi a bace.

——————————————
Bayan wata biyu da zuwan ziyarar su Baba wajen Amina,da gudu Zainab ta fado gida ayam kamar anjefota,tana haki Mama da Baba na zaune tsakar gida suka mike ganin Zainab na kuka tana haki kamar zata mutu.

"Miyafaru."
Suka tambayeta baki dayan su.
"Ya Ahmad na waje suna faɗa da wasu sun mashi taro."

Da gudu sukayi waje anata dambe da Ahmad ya buga su buga ganin sun gaza cimashi sukai mashi taron dangi kuma anki rabasu amman sukaƙi hakura sai dukan shi sukeyi suna cewa.
"Sai mun kashe shi."


Yan sanda suka iso da mota duk aka sakasu harda Ahmad ɗin,Baban Husna ya dauko su,domin rigimar tafi karfin tunanin shi kuma in yabari suna iya halaka Ahmad.

Ana zuwa station akasasu bayan Kanta(Cell).
DPO yasa aka dauki Statement akasa kowa yai jawabi Sajen na rubutawa.

"Nadawo siyen madara kenan naji sunyi Jacking dina sun hauni da zagi da duka wai Yayata ta kashe masu yar uwar su nima sai sun kasheni tunda anki kasheta ana son a saketa, kaji abinda ya hadamu."
Kuka Ahmad ya saki mai sosa rai.

Kallan su DPO yayi yace.
"Hakane."?
"Eh hakane Yar uwarmu ta kashe duk amanar dake tsakanin su taci amanar ta agaban kowa cikin Kotu tace,itace ta kasheta."

"tana ina wadda tai kisan kan.?
"tana Gidan Yari."
"Waya kaita.?"
"Alkali yace akaita anmata ɗaurin rai da rai.


A kufule DPO yace.
Shima wannan ɗin ba hukunci bane?shine zakuzo ku dauki doka a hannuku, shi Ahmad mi yaimaku kukeson kashe shi,kuma ita wadda tai kisan ai kwara a kasheta akan rayuwar da ta tsinci kanta,dan haka dole ku ɗanɗani kudar ku."

Hakuri suka hau ba DPO yace.

"Maida mani su Cell,kai kuma Ahmad kayi hakuri komai lokacine insha Allah komai zai zama tarihi."
"Allah yasa."

Can suka barosu suka dawo gida rai ba dadi,haka Baba yai jigum yana mamakin yanda rayuwa ta sauya masu daga jin dadi zuwa ƙunci,Baban Asma'u yaita basu hakuri akan hukuncin da ya'yan yan uwan shi sukaima Ahmad har sun fasa mashi hannu dressing akai mashi.

"Bakomai Alhaji."
cewar Baba,saida yamma sannan mahaifin Asma'u ya koma gida yanajin tausayin aminin nashi.


"Toh Bakura insha Allah sai kajini bada jimawaba akwai abinda zan ida sannan kasa a gyara komai yanda yakamata, Allah yabamu alkhairi nagode kwarai da gaske."

Kashe wayar Baba,yayi baice komai ba yai ɗakin shi.


"Bayan kwana biyu ya shirya shida Dada sai Mama suka tafi Kano wajen yar su, watan su Ukku kenan da zuwar mata ziyara.

Suna zuwa shugaban wajen suka gani yai masu izini aka kira Aminatu, ina zuwa naga iyayena harda kakata bansan sanda nasaki murmushi ba saboda farin cikin dana shiga itace ziyarar dana fara jin dadin ta har cikin raina suma sunji dadin ganina cikin farin ciki fira mukayi harda dariya mukeyi baki dayan mu kamar ba a gidan Yari nike ba,munjima muna fira baifi minti goma su tafiba Babana ya rike hannuna yace.

"Aminatu.?"
Yanda naji mahaifin nawa yakirani da cikakken sunana hakan yasa na maido hankalina baki daya akan shi nasan magana mai mahimmanci zai mani.
Na'am Baba."
"Aminatu inasan zan sanar dake wani mai matukar mahimmanci duk da nasan hakan ba lallai zai maki daɗin jiba saidai ya zama dole in sanar dake hakan ya'ta."

Cikeda girmamawa nace.
"Minene Baba inajinka."
Sauke ajiyar zuciya yayi yace.
"na yanke shawara gobe goben nan da izinin Allah zanbar garina na haihuwa zanyi Hijira zuwa wani gari ma'ana zanbar Caranci da zama zan koma garin Sokoto."

Wani irin faɗuwar gaba naji ta ziyarci banda.
"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un ."
ba abinda bakina yafara furtawa na kuma cewa.

"Baba miyayi zafi har haka miyasa zakuyi mani nisa bayan sake dawowa acikin rayuwata kun ɗanɗana mani dadin kasancewa daku duk da nakasance a wannan halin,hakan baisa naji narasa iyayenaba kuna kara mani kwarin guiwa yanzun zan tabbata banda kowa da komai kamar yanda najima ina mafarki."?
Kuka na 6arke dashi mai sosai rai.

Mama da Dada suma kukan suke ga tarin mamaki da fargaba a fuskokin su da alama suma basusan da wannan al'amarin ba.

"Mamana duk duniya kece ta farko dana fara sanarma wannan maganar domin kece abokiyar shawarata,ada na karaya na dauka cewa na rasaki ashe ba haka bane,a nan dinma zan iya zuwa inyi shawara dake ya'ta,kuma in samu masalaha akwai dalilan da sukasa na yanke wannan hukunci Aminatu badan in gujeki ba kodan in saka rayuwar ki cikin gagarari ba."
Ya ida maganar kwalla na sauka bisa kwayar idanun shi,nima kukan nike nace.
"Miye dalilin Baba."?

"Mun shiga cikin tsangawama,tashin hankali da kyara duk awajen jama'ar gari aimana gori a zagemu aimana ature a cikin bainar Jama'a duk akan lamarin nan Mamana nayi kuka da bakin cikin rabuwa dake haka mahaifiyar ki yan uwanki dangin ki makobtan mu kowa yaji ba dadi saidai yau da gobe ta wuce wasa.
Ankai matakin da dangin Asma'u sunfara daukar fansa da kansu acewar su kin kashe masu yar uwa kuma anbarki da ranki bari su kashe kanin ki Ahmad,ina tsoron kada shaiɗan yai galaba akansu su illata rayuwar Ahmad,daga baya zumuncin mu dasu ya lalace nima nawa dangin suce sai sun ɗauki fansa kinga,duk wata alaka da kuka jima kuna ginawa keda Asma'u ta tashi abanza kenan,tunda dangin ku sun 6uge da daukar fansa akan yan uwan su bayan jini guda ke yawo a jikkunan ku,wannan dalilin yasa na yanke wannan shawarar da azo ana aikin danasani marar anfani kwara mu nisanta da garin baki daya in yaso daga baya komai daren daɗewa in komai ya lafa muna iya dawowa asalin mu, ya kikace Mamana."?
A raunane mahaifina yaimani tambayar.

Kukan zuci nike nasan koma minene nina jefa iyayena halin da suke ciki miyasa na amsa laifin da banawa ba?saboda narasa hankali tunani,ilimi ji da ganina shiyasa na ɗaurama kaina laifin kisa,kisan ma na aminiyata Husna dole wa'anda sukasan tarayyata da ita zasu kasa yafemani har abada dan ban cancanci yafiya ba,na zama azzaluma maciya amana,tattaro kuzarina nayi na goge kwallan idona nace.

"Tabbas Baba nasan na jefa duk wani ahalina cikin gagari da bakin cikin rayuwa wannan dalilin yasa na gwammaci inkare rayuwata anan har abada da infita nasan bakin cikin da zan fuskanta shi kadai ya isa yai ajalina!
Baba nima nagoyi bayanka ɗari bisa ɗari kubar garin baki daya ku nisanta da duk wani labarina da zai hana maku farin ciki da jindadin rayuwa,hakan shine masalaha tabbas iyayen Asma'u sun cika akirasu da iyaye sunma zumunta kara sun kauda kai akan duk wani surutun mutane,sun nuna nidin ƴarsu ce,saidai yau da gobe batabar bakomai ba,ina tsoron kada ƴan zuga su ingizasu har sufara jin zafin lamarin amman idan kuka tafi yau da gobe za'adaina maganar baki dayanta sai labari yakawo labari,tabbas watan wata rana za'a iya yinta ance kunne ya girmi kaka."

"Allah yai maki albarka Mamana kin cika 'ya' da kowane uba zaiso tazamo yarsa wlh nasan wannan Jarabta ce Aminatu, badan kina sa6amana ba, daidai gwargwado kina bin dokokin ubanginjinki, ki ɗauka aranki Haka Allah Yaso Aminatu kuma Komai Lokacine wata rana sai labari."

Jinjina kaina nayi in sharema Mama hawaye da Dada sun gaza magana saidai kukan da sukeyi.

"Ina maki fatan alkhairi Aminatu Allah ya ji6inci al'muranki."
Cewar Dada
"Ameen ya rabbi nagode Dada."

"Ya'ta duk da bansan da zancen nan ba amman bayanin da mahaifin ki yai ya

Please Login or Register in order to submit comment