Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah."
"Toh Baba Allah yakaimu lafiya."
"Ameen."

tareda Alhaji Tijjani suka tafi ya mai dashi har gida,sannan ya kama hanyar tafiya Katsina gidan Anty Murja ya sauka,ya gaya mata duk yanda sukayi da Kawun nashi fatan alkhairi tai mashi washe gari da safe Tariq ya kirashi yace su haɗu a gidan Yarin dan susan abinyi.


_ANKA_
"Baban Zainab sai inga abinda kaima Hussein baka kyauta ba,ya nunama yar mu so na haƙiƙa tana cikin hali hakan baisa ya gujetaba mizaisa kai masa haka."?

Murmushin manya Baba yayi sannan yace.
"Khadijatu bari kiji abinda baki saniba ita rayuwa da kike gani ba'ai mata haka koda Hussein ke ɗana bashi ke nuna inmika mashi wuya hakanan ba batareda na tirjeba dalilina kuwa shine kinga Aminatu da Hussein akwai soyayya mai ƙarfi a tsakanin su kowa ya sani,kodan son da yake mata zai iya yin komai akanta nayi anfani da wannan damar na nuna bansan taimakon shi a zahiri, badan komai ba dan in nuna mashi indai dan son da yake matane zai taimaketa banso dalilina kuwa inasan ingane wane rin so yake mata,kuma nagani so na gaskia yake mata,sannan zai so Amina akowane hali take ciki, koda bai aureta ba a matsayin matar shiba zai sota dan zumuncin dake tsakanin su.
Kuma abinda nikeson ki fahimta da'ace a cikin ya'yan zuriyar mu wannan abin ya faru da wata Hussein bazai ruɗe har hakaba,saidai zai taimaka dan zumunta dake tsakanin su,itako Amina har yanzun sonta bai sauyaba a cikin zuciyar shiba,tunda gashi naxe ban buƙatar taimakon shi amman hakan baisa yai fushiba,saima ya sake dawowa tareda Alhaji Tijjani,hakan kaɗai ya tabbatar mani da cewa Hussein masoyine na gaskia.
kada ki manta inda rabon Aminatu zata fito gidan Yari ba abinda zai hana ban aura mata Hussein ba insha Allah,wannan shi ne burina.
domin a wannan zamanin bazaka samu wanda zai nunama naka so kamar yanda Hussein ke kaunar Aminatu ba,kuma na tabbata itama tana son shi bazata taba gudun shiba."

Wata sanyayyar ajiyar zuciya Mama ta shiɗe tace.
"Hakane kam, naji dadi daka fahimci abinda nike nufi ba abinda zamuyi ma Hussein duk duniya kamar mu aura mashi Aminatu,inda rai da rabo komai yanada lokacin shi."

"Wannan haka yake,Allah ya tabbatar mana da alkhairi."
"Ameen."

_KURMAWA JAIL KANO_
Kwance nike bisa katifata zazza6i yai mani kamu sosai ko aiki ban iyawa kyakkyarwa kawai nike na kudundune kamar mage,duk sanda zan rufe idona Ya Taufiq ke mani gizo da maganganun shi sai inga kamar amafarki duk na shiga damuwa bansan ina tuna komai daya danganci Ya Taufiq,tambayoyi naima kaina miyasa nike tunashi miyasa nagaza cireshi araina? Mi hakan yake nufi?Saida rayuwa taimani kunci sannan zai dawo cikin rayuwata,bayan a silar shi komai yafaru inama lokacin daya kirani a waya ban daga ba duk da Ya Tariq yace shine,miyasa soyayyar Ya Taufiq kullin ruruwa take a cikin zuciya ta bayan Qaddara ta rabamu,rayuwa taimani kunci nasan har abada bazanga jinina ba,inalillahi wa'inna ilahirraji'un.

Zirarar da hawaye kawai nike gashi tunda nace yafita rayuwa ta,ba wani labari hakan yana nuna daman bai wani damu daniba a wajen shi dani da babu duk ɗaya kenan?tunda har zai dawo ƙasa amman ya manta dani tsawon 10 days kenan daman ance duk wanda ya maida namiji uba zai mutu maraya nidai gashi yazo ya tado mani da tsohon ciwon dake cikin zuciya ta,ya tafi yabarni ga kuncin rayuwa ina fama dashi miyasa Ya Taufiq yafara zama mutun marar tausayi alhali shidin ba haka yake ba.

Da wannan tunanin bacci ya daukeni mai nauyin gaske mafarkai nike tayi iri iri harda na Husna nayi saidai rayuwace mai dadin gaske magana tafara yimani naji muryar Mairo akaina tana bubbugani wani irin haushi ya kamani bude idanuna nayi da sukai mani nauyi sosai na kalleta.

"Kije ana kiranki a office din Oga Adam."
Juyawa nasake yi araina na kudiri ban zuwa nasan koma waye ba alkhairi bane ya kawo su kilama Mami da Anty Hafsat ne sukazo, ina fama da kaina zasu sake aza mani wata lalurar baccina na koma.
Muryar Karima naji tana kirana.
"Ke Dago kizo ke zamu tsaya jira."
ta ida maganara fusace.

Badan nasoba na sauko nabita zuwa wajen Adam anan naji yana cewa gaskia kune last visitors da zaku kara ganin Aminatu wannan month ɗin,kunzo ganin ta dayawa doka batace haka ba duk da ranar visting kuke zuwa.

Insha Allah,muryar Ya Taufiq naji da har nayi niya zan koma sai kuma nashigo saboda Karima na bayana kuma bazata bari in koma ba.
tsuke fuska nayi tamau nace gani.

"Minti goma kije ku gaisa."
Fita yayi yabarmu,kallo daya nai masu na kauda kai ko gaidasu ban ba.

"Minal"
Kallan shi kawai nayi bansan mi nikeji akan Ya Taufiq ba.
"Dan Allah inasan ki mani bayani dalilinki na zuwa wannan gidan domin inasan ya zama shaida agareki in munje Kotu."

Wani irin kallo nai mashi nace.
"Nace maka ina bukatar taimakon ka? Dan Allah Ya Taufiq karabu dani ana dole kowa ya shaida ni Amina Yusuf ni na kashe Asma'u Abubakar mi zaisa kaima bazaka yardaba pls i beg of you dan Allah kabarni inji da abinda ke damuna Ya Taufiq karka maida rayuwarka cikin garari kusantar ka agareni ba karamin barazana hakan zai jefaka ba,kanaso kafaɗa cikin halaka dan kawai kanaso kataimakeni?dan Allah karabu dani hakan na hadda samani karewar zuciya nagode da kaunarka agareni."

Juyawa nayi zan tafi Allah yasani in ina tareda Ya Taufiq zuciya kamar zata faso kirjina ta faɗo ƙasa, sai kace wadda aka saka mani hannu ina rasa sukunina amman idan yaimani nisa kuma kewar shi ta dameni haka zanta jinyar zuciya ta ina shiga uƙuba sosai.

"Aminatu.?"
Cak na tsaya jin maganar Ya Tariq.
"Kima Hussein kyakkyawan zato kiyi hakuri kibamu haɗin kai nasan kin amsa laifin daba nakiba dan kawai ba yanda zakiyi dan Allah ki mana wannan alfarmar."

Ban juyoba kuma ban tafiba narasa mi zance ina tunanin idan na fita wace rayuwa zanyi da mutanen gari ya za'a dauki maganar.
Dukanmu shiru mukayi Adam ne dasu Baba suka shigo gefe na koma na basu wuri suka wuce, sai Anty Murja da wani baƙo,duk da nagane
shine abokin Baba,na Bakura munsan shi awaya insuna gaisawa da Baba,tare sukayi karatun su a UDUS lokacin da suna Masters dinsu.

"Kin ƙara wasu baƙin Amin Dago,kekam kin zama yar dangi."
Cewar Adam ya ida
maganar yana murmushi ya fita.

Gaidasu nayi suka amsa.

"Aminatu nasan su Hussein sun maki bayanin komai haɗin kanki muke nema kuma mumiƙama Allah komai shi zai zama gatanki."
Cewar Anty Murja.

"Gaskia ne Amina kiba ɗan uwanki haɗin kai bamusan yanda ta Allah zata kasance ba."
Inji Baba Tijjani.
Jinjina kaina kawai nike ban magana.

"Yawwa Mamana ki daure kuma ki cire karsashi na rashin Asma'u ki faɗi gaskiar ki,kinga kin tabka babban kuskure da kika amsa laifin daba nakiba, yanzun maido wannan shari'ar sabuwa za'ayi kuma sai anbi long process amman a haka Hussein yace zai taimaka maki sai ki gode mashi,muna fatan Allah yaimana jagoranci."
"Ameen Baba."
Na amsa da raunanniyar murya zuciyata na karyewa.

Nasihohi suka sake yimani sannan suka tafi Baba yabani kudi,shidai Ya Taufiq bai kuma cewa komai ba ya tafi,wani irin tausayin shine ya kamani nasan bazan ta6a maida masoyi na gaskia ba irin Ya Taufiq Allah yasani nasoshi kuma na kaunace amman Qaddara ta rabamu duk da su,suna son suga anwake ni daga zargi sai inga da wahala idan zamu sake haɗuwa a matsayin masoya,saidai Haka Allah Yaso ya ganmu kuma saimu barma Allah ikon shi.

***********
Bayan sati biyu shiru ba alamun Ya Taufiq nima harna fara shiga damuwa domin ba wanda nikeson gani kamar shi.
muna aiki saiga Jafar yazo kirana wannan karan office din shugaban wajen baki daya aka kirani bai cika zamaba saita kama,a sanyaye na isa Ya Taufiq ne da wani mutun cikin Suite din kaya,har saida gabana ya faɗi.

Lokacin dana iso suna maida ID Cards dinsu ne cikin aljihu koda bansani ba nasan shaida ce suka nuna mashi.

Gaidasu nayi na tsugunna ƙasa suna bisa kushin.

"Aminatu kinyi baki Rt Major Taufiq da Barrister Bashir Fage,sune sukazo akan case dinki,Court ta anshi korafin da aka shigar za'a sabunta shari'ar ki da mamaciya Asma'u Abubakar,dan haka ki nutsu da kyau ki faɗi iyakar gaskiar abinda kika sani,idan kikaima shari'a wasa da hankali idan anyake maki Life Prison aka gane kece kikai kisan dagaske kuma kika musa da hukuncin da akai maki,to kinsan hukuncin da za'asake yimaki yafi wannan dan haka ki kiyaye idan kinsan dagaske kice kikai wannan laifin kada afara zaman nan ki ɗauki hakuri ki zauna anan,in kinsan harga Allah bakida laifi akan case din nan baki da matsala Allah zai tsaya maki,dan haka Barrister Bashir gareka."

Jinjina kai nayi nace.
"Insha Allah."
Suma cewa sukayi.
"Mungode da wannan damar."

"Aaa bakomai ai kofa bude take kuna zuwa kuna binciken ku kafin afara zaman Court wannan ai damace a hukunce lauyoyi zakuna iya zuwa ko ina kuyi investigation ai shine aikin naku."
"Hakane Allah ya taimaka mana."
Cewar wanda aka kira da Barrister Bashir
"Ameen."

Kallona Barrister yayi yace.
"Aminatu duk tambayar da zanyi maki anan ki tabbatar idan mukaje gaban Alqali itace zaki maimaita kada ki yarda ki sauya kalamanki hakan hujjane akanki,kuma kiji tsoron Allah ki fadi gaskiar abinda kika sani karki cuci kanki."

"Insha Allah zan faɗi iyakar gaskia ta."
nace cikin raunin murya narasa yanda akai jikina yai sanyi dayawa.

"Miyasa kikabaro gidan ku har kikazo wannan garin Kano."?
Sadda kaina ƙasa nayi nace.
"Da safe kiran Ya Taufiq ya shigo awayata ban tsaya na dauki muryaba naci gaba da wayata ina nuna tsantsar kaunata agareshi datarin kewar shi a lokacin mahaifin yajini ranshi ya baci aganin shi taya zansa afara maganar aurena da Sadiq sannan kuma zandawo da Ya Taufiq a cikin rayuwata,hakan kamar zubda mashi ƙimane za'adinga yi mashi kallan karamin mutun mai magana biyu.

A gaskia mahaifina ya fusata sosai ranar saida ya dukeni.
Ni kuma ganin zai mani illa hakan yasa na gudu zuwa gidan su mariganya Asma'u mahaifiyar ta,taita lallashina kuma tana mani nasihohi,har yamma tayi tace in koma gida zata shigo tabawa Baba hakuri.

Ni kuma nagama tsorota da fushin mahaifina dan nasan bai iya fushiba hakan yasa na yanke shawara zuwa wajen Yayar shi Umma Zainab dan in gaya mata halin da nikr ciki, kila idan tazo ta bashi hakuri zai hakura saboda duk zafin Babana yana girmama maganar yayyan shi.
Saidai ance Qaddara ta riga fata koda mota ta ajeni ƙurna babban layi nazo zan tsallaka titi mota ta bankeni ban kuma sanin inda kaina yakeba sai asibitin Murtala,haka akaita saka mani ƙarin ruwa bishi bishi haka nike kallan mutane saidai likitoci sun tabbatar masu nasamu karayar kashin kafa sannan na goce a ƙuguna dole akaini asibitin kashi,daga nan akai mana transfer zuwa asibitin Dala na ƙashi aka sakani Under treatment aka fara yimani aiki tabbas nasha wahala matukar gaske akai mani dauri akai hanging kafata haka nasha jinya na tsawon lokaci najima bansan inda kaina yake ba watanni na kwashe gocewar ta lafa mani saidai karayar ita nike fama da ita kusan shekara da watanni na kwashe, duk da an maidani gida inda suka kaɗeni gidan Alhaji Abdullatib Abdullahi,acan Doctor Salihu ke zuwa yana dubani har kafata tafara sakin kwari alamun warkewa tazo kasan karaya mugun abune atakaice nakai shekara biyu ina jinya da sun mani maganar iyayena sai inhau kuka dan kada su tambayeni asalina saina koma kamar kurma ban magana saidai ido.

Kowa yana bani kulawa ta musamman Ya Mutallib wanda ya kasance da' ɗaya tilo namiji wajen Alhaji Latib so na gaske yake mashi jinyata kuwa Salima da Ya Mutallib kamar su ke jinyata domin shakuwa ta shiga tsakanin mu sosai kamar yan uwa aganin shi ta silar shi na samu karaya da dagocewa,tinda shine ya kadeni."

"Kince shakuwa ta shiga tsakanin ku har zuwa lokacin basu sake yi maki maganar gidaba."?
Cewar Barrister Bashir.

Ɗago kaina nayi na kalle shi saidai azahiri Ya Taufiq nike kallo wanda shima nidin yake kallo kamar ya samu tv nima ban ɗauke idona akan shi ba,naci gaba da cewa.
"Eh a lokacin sun fahimci ina cikin matsananciyar damuwa saboda a ganin su duk sanda zasu tado mani.....

_Yar Mutan Kankia ce❣️_
Share
Pls
❣️



_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E29&30




"Eh a lokacin sun fahimci ina cikin matsananciyar damuwa saboda aganin su duk sanda zasu tado mani da bayana (past) banda aiki saina kuka hakan yasa suka daga mani kafa saima shakuwa dake kara shiga tsakanina dasu koda naga hakan saina fara magana suma sunyi mamaki ashe da bakina,saidai sun fahimci tambaya ke banso.

Ya Mutallib shike maidani treatment duk bayan wata ukku saida ya kasance har tafiya shike koya mani da sandina nike tokarawa ina tafiya a ɗingi she.
tausayin shi agareni ƙaruwa yake a kullum haka yake bani kulawa kamar cikin mu daya baida buri daya wuce ya ganni cikin fari cikina.

Nakai shekaru biyu da rabi agidan su ina jinya har Allahu gafurur rahim yabani lafiya nafara tafiya da kaina,amman ban sauri a hankali nike tafiya saboda first stage dina ne a training da ake mani.

Mahaifiyar shi Hajia Saudatu tabani kulawa hakama mahaifin shi sun maidani 'ya.

Akwai wata rana akalla nasamu wata ukku zuwa hudu da warkewa ina zaune a garden din gidan ina tuna rayuwa abubuwa da dama sunƙi fita a zuciya ta kwalla kawai nike fitarwa naji an zauna kusa dani ana sharen kwallana na tsorata saidai Ya Mutallib ne.
Murmushi na kirkiro a fuskata,shima shi yayi mani yace.

"Haba Amna kukan mi kikeyi miyasa kike yawan warewa ke daya kina kuka ko har yanzun baki dauke mu a matsayin yan uwanki ba."?
Araunane yai mani maganar.

"Aaa bakomai kayi hakuri insha Allah bazan kumaba,kuma na dauke ku dangina yan uwana saidai ince Allah yasaka maku da alkhairi."

"Bakomai indai inaso kibani tarihin kin kwashe tsayin lokuta muna tare dake bamu sanki ba,kinki bamu hadin kai duk da dabaki fi wata ukku da warkewa ba amman ya dace ki sanar mana wacece Aminatu."

Samun kaina nayi da shiga damuwa saidai ranar wanka ba'a boyon cibi,nima ya dace in koma wajen iyayena ina kewar su kwarai da gaske.

Insha Allah zan baka labarina saidai kabari sai washe gari in Daddy da Ummi nanan agaban kowa zan fada maka wacece Aminatu."

Haka akayi kuwa washe gari muna gama break fast Daddy yace.

"toh Son kace kanwar taka yau zata gaya mana wacece ita muna sauraran ta."

Murmushi mukayi baki dayan mu yace.
"Eh Daddy insha Allah yanzun kuwa zata sanar mana labarinta."

"Hakane ya'ta."?
"Eh Daddy insha Allah."
"Munajin ki Allah yasa."
"ameen."
nace dasu,cigaba da cewa nayi.

"Sunana Amina Yusuf Caranci na kasance babba a wajen mahaifina tun ranar dana......
Haka naci gaba da gaya masu asalina da abubuwan daya kamata su sani musamman dalilin barina gidan mu har tsautsayi ya gifta suka bankeni da mota.
Tabbas naga tausayin su akaina sauke ajiyar zuciya Daddy yace.

"Nasan duk inda zuciyar mahaifin ki,take tana cike da zullumi dan haka zanbi duk hanyoyin daya dace inga na sansanta ku,sannan inda rabo saiki auri Sadiq din tunda shi Taufiq din ba'asan inda yake ba Qaddararku ta rabaku kiyi hakuri Aminatu Haka Allah Yaso inada yakinin mahaifin ki zai yafe maki tinda bada gangan kikabar gidaba,kuma jinki shiru da sukayi lalura ce ta hanaki, komawa agaresu bawai dan kin guje suba ne."
Lallai sun kwantar mani da hankali ainun har saida naji dadi araina dana gaya masu damuwata.

Haka rayuwa ta kasance kaf dangin su sun zama nawa saidai ko waje ban lekawa ina gida.

Ranar datasa nafara ganin kwanda in koma gidanmu da zaman da zanyi a gidansu saboda Ya Mutallib,lokacin daya bujiro mani da soyayyar shi agareni saidai banyi amanna da hakan ba dalilina kuwa na tsani duk wani abu waishi so arayuwa a tunanina banda sa'a a soyayya,
Ya Mutallib yabi duk hanyoyin da yasan zaibi dan inso shi amman naƙi saboda na zama bebiya a kalmar so ban fahimtar yaran domin na ɗanɗane ta,saidai nidai tawa soyayyar ruwan maɗaci ce,saboda tana tafe da Kalubale iri iri na rayuwa,kuma bazan so in saka shi cikin matsalolina ba.
Tun yana nuna mani so a boye har yafara nunawa afili Salima itace tafara ganowa.
Munacin abinci yace.

Amna innason in gaya maki wata magana bansan yanda zaki dauki zance ba, Allah yasani kamar yanda nace ina sonki,wlh ba wasa nikeba aurenki nike sonyi dan Allah ki aminta dani."

Mikewa nayi nace.
"Kayi hakuri Ya Mutallib ban cancanci ka soni ba dan Allah kada kasaka rayuwarka cikin sarkakiyar rayuwa irin tawa amman kayi hakuri dan Allah ba so a cikin zuciya ta."

Banjira cewar shiba nayi dakin mu cikeda damuwa araina,inaganin kamar banyma Ya Mutallib kara ba.

Ganin nafara jan baya dashi sai ya daina nuna mani so yaja baya dani saidai kyautatawa bai fasa yimani itaba.
Baida buri sai yaga na saki jiki dashi sosai muna haka har yayi tafiya zuwa Dubai yafi wata sannan yadawo,ni mutun ce da bata iya saboba ɗan zaman da nayi dasu sai suka zamar mani yan uwana na jiki nakan maida matsalar su tawa naba mahimmaci sosai.

Baifi sati biyu da dawowar shiba ya kuma yimani maganar son da yake mani har Salima ya turo mani sai kuma na tuna alkhirin su agareni Allah yasani badan inason Ya Mutallib ba na aminta dashi saidai a abota na na amsa mashi, ya amince ahaka mukaci gaba da friendship dinmu.

Har waya saida ya siyo mani da sim card ya bani naji dadin ta domin inasan kiran mutane da dama amman banda ita domin tawa gida nabar ta.

Waya muke da Ya Mutallib muna soyayya amman ba maganar aure a ciki koya yafara yimani zancen zan dakatar dashi.

Haka rayuwata ta kasance da friendship dinmu da komai cikin yan lokuta mun saba sosai da junan mu.

Har Ummi ta,ta6a kama mu,yana sharing words a tsakanina dashi saidai lamarin ya ɗaga mata hankali.
Kiranmu Daddy yayi yace.
Mike tsanin mu dajunan mu.
Ba wani boyeboye Ya Mutallib yace ni yake so kuma aurena yakeson yayi.
Saidai Daddy yaji dadi amman Ummi ce taki amanna da hakan taya zai aureni bayan basu gama tantance asalina ba, bayan kowa yasan tsintarciyar mage bata mage dan haka da sake.

Hankali Ya Mutallib yai matukar tashi Daddy ya kwantar mashi da hankali kasancewar ɗanshi tal a duniya bazai so ya rasa komai ba,saidai idan nace da' ɗaya ina nufin namiji akwai Salima itama ita dayace shiyasa yake masu so na daban.

Bayan wata daya soyayyar da Ya Mutallib yake mani ƙaruwa take agareshi hakan yasa Ummi tace matsa agano asalina,Daddy bai damuwa harya fara shima magana ni kuma na hanasu zuwa gidan mune kada Babana yace dana gudu soyayya na kulla da wani, bata su nikeba bayan nasan da maganar auren Sadiq shine na kara kawo mashi wani, inasan in zubar mashi da ƙima a idon duniya.
Wannan dalilin shike Descourage dina nakin bada number mahaifina duk da kuwa tana haddace akaina.

Kullin Ya Mutallib dai da magana sai guda ɗaya
"Amna ina kaunar ki da gaske nike maki ki bani dama in maye maki gurbi da dama arayuwar ki."

Nasan har abada Ya Mutallib bazai taba maye gurbun dana rasaba amman yana kamantawa iya geargwado.

"Abdulmutallib bafa zan zuba ido ka fadama halaka ba idan kanasan ka auri Aminatu muna son musan asalinta."

Inji Ummi,saidai bantaba jin haushinta aganina hakan da tayi shine solution ni kuma nasamu dama da zan yakice ɗansu ya daina sona sannan indai sai Ya Mutallib yasan asalina zasusa ya aureni ni kuma zan masu wasa da hankali, kila daga haka zasu koreni sai innemo gidan Anty Zainab nasan insha Allah Baba zai yafe mani sannan zan auri zabin mahaifina.

Bayan sati biyu Daddy ya kirani yace.
"Zuwa nan da sati ukku, idan na dawo daga tafiya zani kaishi wajen mahaifina ya maidani gida, yasan insha Allah zai yafe mani sannan daga baya zai nemawa Ya Mutallib aurena.
Ban musaba nace to Allah yakaimu.

Murna gun Ya Mutallib bai misaltuwa danni tausayi yake bani tunda har yanzun bantaba bari son shi a raina ba daidai da kwayar zarra banjin komai kuma bangane kowa indai a fagen soyayya ne nai mata jan fenti natsane ta.
Wannan dalilin yasa nike tausayin shi saidai ina mashi so na yan uwantaka.

"Aminatu kince mahaifin Abdulmutallib yace zaki kaishi wajen mahaifin ki miyasa baki kaishi,kai tsayeba kamar yanda ya bukata."?

Cewar Barrister Bashir.
Numfasawa nayi zan fara magana sai kuma Ya Taufiq yace.
"Barrister lokacin sallah yayi yakamata mudakata anan muyo sallah tukunna."

"Hakane kam ya dace gaskia bari kagani yanda za'ayi.....
Wayar Barrister tahau ruri dagawa yayi yace.
"Barrister Samir kun same shi kuwa."?

Bansan abinda akace mashi ba ya kuma cewa.
"Okay yanzun zamu fito nasa Sagir da Hassan suna mani wani binciken na daban sunce insha Allah komai zai tafi normal."
Sake cewa yayi.
"Aaa kajiramu gamunan tafitowa ma."
Kashe wayar yayi yace.

"Officer aikin namu ya sake kaɗawa wani waje,akwai suspect din da muke target ne insha Allah zuwa jibi zan nasamu enough time,zan dawo inyi zaman karshe da Aminatu inason in haɗa hujjoji akan wannan zaman da fatan zaka bamu hadin kai kuma kowace magana zamuyi ta a gaban ka."

"To Barrister Bashir,Allah yakaimu lafiya yasa agama bin cike,cikin narasa."
"Ameen."
Cewar Ya Taufiq.

Ɗan cije lebena nayi kadan saboda take naji cikina ya katsa mani sosai.

"Minal bakijin dadi ne."?

Naji yaimani tambayar bazata,saboda bani zatan kaf dinsu akwai wanda zai gane inajin wani ciwo amman Ya Taufiq ya gane hakan.

"Aaa."
nace atakaice,nasan bai yardaba ya kyaleni nine kawai,sallamata akayi godiya nai masu nakoma dakina fatana daya Allah yasa dai ba MP dina zai dawoba dan tunda na shigo gidan Yari ban zatan na kuma yinshi yawanci indai zan samu kaina a tension yakan zo mani kuma inafin sati ina fama da ciwon mara wahala nikesha sosai har sai yazo mani sannan zai daina yi mani.

Ina komawa dakin na zauna ina rike mara idanuna rufe na jinjina kaina a jikin bango.

"""""""""
Koda suTaufiq suka fita bincike suke sosai akan Case ɗin,Barr Bashir da Barr Sagir sai Barr Samir (Ya Samir) suka taramma case ɗin Aminatu,sai kumaTariq shima yana bada gudunmuwa sosai amman tafiyar baki daya ta Taufiq ce.

Bincike suke sosai akan issue din Amina tsohuwar shari'ar suke bibiya da statement da aka kawo masu haka sukaje Hotel din da aka kashe Asma'u suka hau bincike sosai a cikin shi hatta dakin da aka bata suka sa aka rufeshi zuwa na wani lokaci,aka daina kama shi mabudin akaba Barr Bashir.
Sosai sukaba case din mahimmancin gaske, cikin file case din suka duba da statement na wukar da akai kisan da ita,har asibitin da akai gwajin sukaje aka hau bincike aka gano files da copy din statement,karshe sukaje wajen Barrister din dayaja case din sun samu hadin kanshi sosai aka dubo wukar dake aje inda ake aje makamai na cases iri iri cikin leda an adanata an haɗata da statement case dinta da number ajikin ta,haka aka ɗaukota.
Bin kicen dasu Taufiq sukai bana wasa bane,cigaba da dubo wadanda suka bada shaida sukayi anan sukaga sunan Junaid Jamilu Kano(Dr JJ) sukaga duk shi kaɗai yabada shaida anan suka sa mashi alamar tambaya,Kotu ta tura mashi sammaci aka aika mashi Letter din Sammaci.
Saidai yasha mamaki domin ya jima da rufe babin rayuwar Amina a duniya haka ya ansa ya duba harda date din da za'afara zama Court duk ya gani yasha mamaki da al'ajabi.

Wasa wasa shari'ar Amina ba karamin bin cike suke mata ba sosai a haka har akai kwana huɗu suka sake komawa gidan Yari zasuyi zaman karshe da ita daga shi sai afara zaman Court.
Koda aka kira Aminatu ta tafi office din da aka ware masu suna yimata tambayoyi.

Ina shiga cikin office ɗin naga harda Ya Samir nasha mamakin ganin shhi,a hankali na zauna domin har yanzun ciwon cikin da nike fama dashi bai daina damuna ba,gaida su nayi suka amsa a hankali na saci kallan Ya Taufiq sai yanzun naga ya rame mani saidai yai kyau,saboda tunda yafara kawo mani ziyara banda kwanciyar hankali sam sai yau naji nadan samu nutsuwa sai yanzun nike karajin tausan shi yanda naga ya ɗaga hankalin shi akaina,maganar Barr Bashir ta yanke mani tunanina,zan sadda kaina kasa kenan daga kallan Ya Taufiq ya kamani ina aikin kallan shi kunya naji ta kamani na sauke kaina kasa.

"Munajin ki Aminatu,sannan ki tabbatar duk abinda zaki fada anan zaki iya kare kanki a Court dan bansan asamu matsala shari'a ta adalci muke son ayi."
Cewar Barrister Bashir.

Sake sauke kaina nayi ƙasa naci gaba da cewa.
"Insha Allahu duk abinda zan gaya maku baza asamu canjin komai ba zan sake faɗar shi a gaban Kotu."
"Allah yasa Aminatu."
Ameen nace nacigaba da cewa.

"Tunda Daddy ya bukaci ganin Baba......



_Yar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Pls
❣️


_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E31&32




Tunda Daddy ya bukaci ganin Baba,na gaza samun nutsuwa araina saina fara nemawa kaina

Please Login or Register in order to submit comment