Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk aniyar makaryaci wlh maciya amana."

Kallan mamaki kawai su Ahmad ke masu musamman duk masu maganar sunsan rabi da kwata,sun rasa gane yaushe mutane suka koma haka,sa baki a cikin abinda baka da ilimi a cikin ko Annabin rahama yace falyakul khairain auli yasmut(Kafadi alkhairi ko kuma kayi shiru).
Amman dayawan mutanen yazun harsunan mu zasu halakar damu.

Kuma ita shari'a sabanin hankalice miyasa mutane suka gaza gane komai yin Allah ne arayuwa.
Haka sukaita surutun su,sudai tak basu ce masu ba har suka shiga Mota Taufiq zai tukasu Ahmad a sit din mai zaman banza Baba a baya wani ne yazo yacema Taufiq.

"Kai dan kana takama da kudi shine kake neman jayayya da gaskia akan karya,dan kana takama kai Sojane wlh sai Allah ya kwatarma Asma'u hakkin ta muntabba da ace itace Qaddara ta faɗa mata munada yaƙini iyayen ta bazasu kokorin fiddotaba zasu rungumi Qaddarar su,amman dayake kune shafaffu damai kukeson wanke yarku a idon duniya musamman kai kana Jami'in tsaro amman baka da adalci Allah ya fiku."

Girgiza kai Taufiq yayi yana ta'ajjabi yasan dole tasa Baba barin garin su na haihuwa kodan gudun irin wadannan kananun maganganu ko barazanar rai,tuka motar shi yayi ya tafi shidaman badai miskilanci ba abinda yasa ya tsaya danjin ra'ayoyin mutane akan case din kuma sun samu abinda sukeso shine dalilin dayasa Ya Taufiq yabiyo Baban su Amina haka suka tafi yana raya abubuwa dadama aranshi tabbas koda yake ganin tashi rayuwar tana cikin kalubale Aminatu tafi shi shi ƙangin rayuwa yana karajin sonta a cikin zuciyar shi gami da tausanta da haka suka kama hanyar tafiya gida as usual gidan Anty Zainab suka sauka kowa yaji dadin ganin waya da akayi saidai basuyi wani bincike a cikinta ba sun bari sai zuwa gobe in an bukata a Kotu.

Da yamma likis Barrister Bashir yazo tareda Barr Samir sai Doctor Hassan da Arch Taufiq suka fita zuwa Hotel din akayi case din dan ida wani binciken su da yarage ma Barr Bashir sosai suka gama duk wani abun daya kamata ace sunje dashi Kotu zuwa gobe,basu suka gama abinda zasuyi ba sai magrib.

•••••••••••••••

Washe gari da safe karfe shidda na tashi wanka nayi da wuri,nagama shirina tsaf na zauna saboda ance 9am zamu koma Court saidai da mafarkin Asma'u na tashi sosai kewarta ta kuma addabata a cikin zuciya ta Allah yasani ina son Husna Allah yaimata rahama.
Karfe 8:30 wannan karan da Atika a cikin masu rakiyata sai Adam baki dayan mu muka tafi.

Sadda tara zatayi mun iso bakin Shari'a Court bamu jimaba aka hallara harda Alhaji Abdullatib Abdallah da Ya Mutallib sai Ummi da Salima (wa'anda suka kadeni a mota).

Banfi minti goma da shigowa ba Justice Na'Allah ya shigo cikin Court din kowa ya mike saida ya zauna aka koma aka zauna nidaman kamar Soja haka na koma nagire banjin gajiyar tsayuwa ba a sake gabatar da Qarar ba saidai cigaba da sauraron shari'a da aka fara bayan gabatar da rana da akayi.
Barr Bashi Fage yafara fitowa gaban kuliya bayan gabatar da kanshi agaban Alqali da yayi wannan karan cewa yayi.

"Ya mai girma mai shari'a ina neman wannan Kotu mai alfarma tabani izini ingani da mai kara Amina Yusuf Caranci."

"Anbaka Barrister Bashir."
Shigewa kawai nayi cikin abin tambaya na tsaya ina kallan Barrister.

"Kamar yanda duniya take maki kallan maci amanar tare na aminiyar ki kawarki Asma'u shin mi zaki iya cewa dangane da wannan kallo da ake maki sannan ranar da kika iske gawar kawar taki shin kin sameta da ranta ko kuwa rai yayi halinshi."?

Kaina ya amsa kuwa lokaci guda komai ya gama dawowa mani sabo fil a zuciya ta,mafarkin jiya ya yadawo mani da abinda mariganya tace mani hakanan na kara samun hope din shari'ar ba wani abu bane take cemani ba illa ki ringumi Qaddarki Aminatu kuma duk mafitar da Allah yakawo maki kada ki rainata komai kankantar ta,kimi ƙama Allah al'amuranki zai maki gata kawata komai da kika gani daga Allah ne, shi ke komai Haka Allah Yaso.
Ajiyar zuciya na sauke a sihirce nace.

"Kwarai kuwa bazan iya misalta bakin cikin da nikejiba a duk lokacin da aka gwadani ana ikirarin naci amanar Asma'u sadai komai Muqaddari ne,kuma bazan mantaba a ranar dana isketa kwance cikin jini na gama gigita na zare mata wukar a cikin ta nan na kifa kaifa bisa jikinta ina kuka mai sosa rai nace.

"Asma'u kada kitafi kibarni."
shine abinda nike furtawa saidai a cikin kunnuwa naji ta ambaci kalmar J saidai bansan mi take nufi ba a lokacin ta rayuwarta nike bani bukatar kowane zance domin bangane komai shi ne abinda nasani Barrister.

"Kina nufi bakisan mi kalmar J ke nufi kuma bakuda wani kurman zance da kuke anfani dashi wajen turama junanku wani saƙo a kaikaice."?

"Objection My Lord abinda nafahimta abokin aikina nason kirkirar wani abu dan kalabawa wanda baiji bai ganiba sharri ta hanyar furta wannan kalma alhalin da mai farin sunan muke shari'an nan mi hakan ke nufi ya kamata ya kula da aikin shi."

"Korafi bai kar6uba Barrister Tukur,cigaba da bin ciken ka Barrister Bashir."
Cewar Alqali.
"Godiya nike ya mai girma mai shari'a."
cigaba dacewa nayi.

"Bansan mi take nufi da kalmar ba saboda bamuda wata bakuwar kalma da muke amfani da ita yayin magana saboda Asma'u bata boye mani komai ba nima haka,saidai idan zamuyi magana mai mahimmanci mukan kebe kanmu muyita,batareda wani kurman zance ba,Allah shiya barma kanshi ma'anar abinda take nufi."

Jinjina kai yayi yace.
"Hakane,Aminatu akalla sau nawa Junaid ya bibiyi ratuwar ki."?

"Bazan iya kayyadewa ba,zai iya kaiwa sau biyar zuwa bakwai a wajen aikina kenan.
nan Kano bansan yana bibiyata ba saida ya bayyana hakan a gaban Kotu dayace ya ganni na kashe Husna."

"Zaki iya komawa kafin insake waiwayar ki."
Jinjina kaina nayi na koma gefen Adam natsaya.

"Ya mai girma mai shari'a zanso wannan Kotu mai alfarma tabani izinin ganawa da Junaid Jamil."
"Kotu tabaka dama Barrister."
Tasowa JJ yayi daga inda yake zaune ya iso gaban kulliya.

"Junaid ranar da Aminatu taje Hotel zaka iya gayama Kotu kaida waye kuka shiga dakin da Asma'u ta kama."?
Dan zaro idanu yayi yace.

"Ban bangane ba Barrister kamarya dawa na naje aini banje Hotel da kowaba ni kadaine naje shima dan naga Aminatu shiyasa har naje amman baccin haka mizai hadani da zuwa Hotel."?
"Saboda kana son kacika burin ka shine dalilin zuwanka."
A firgice JJ ya kalli Barrister Bashir yace.
"Wane burine wannan da akakeson danganta ni dashi."?

"Kana son ka kashe Asma'u don ka daurama Aminatu laifi domin bakada burina a duniya sai kaga Aminatu cikin gagari da tashin hankali."

"Objection My Lord Lauyen mai kara ya tsaurara dayawa yanada kyau ya gyara zancen sa."
"Cikin aikine Barrister, korafi bai karbu ba."

Ɗan murmushi Barr Bashir yayi yace.
"Kai nike sauraro Junaid."

Shiru yayi na wucin gadi sannan yaci gaba da cewa.
"Ina tunanin aduniya sau ukku na taba ganin Asma'u,taya zan kasheta bayan batai mani komai ba,kuma ita kanta Aminatu mitayi mani da zan aikata hakan akanta."

"tambayata kake kenan?to bari inbaka amsar ka.
Kana son kaga bayan Aminatu ne saboda kana sonta ita kuma bata sonka,kuma abin lura anan ban tunanin kana mata so dan Allah shiyasa ka hada mata wannan tuggun."

Hankali a tashe yace.
"Ni baruwana ban hada mata tugguba gaskia Barrister banda wata masaniya a wannan al'amarin."

"Good Junaid wannan shike nuna aikin haɗaka kukayi dan ganin bayan Aminatu ko? Kai dasu waye kukayi aika aikar nan."?
"Ni kaina ban aikata ba,bare har wasu su tayani."

"Shikenan Junaid saidai kasani katanaji kalmomin da zaka kare kanka domin zasu iya zama hujja akanka
zaka iya tafiya kafin insake waiwayar ka saidai ka tabbatar da kanemo mani waɗannan amsoshin."
Komawa yayi ya zauna.

"Ya mai girma mai shari'a zanso wannan Kotu mai albarka tayi la'akari da jawaban da Junaid yayi agaban Kotu kafin in ida gabatar da manya manya hujjojina nagode."

Shiru Court din tayi banda jibi ba abinda JJ keyi kamar kuturu nidai ina mamakin irin binciken da Barrister Bashir keyi akan shari'ar nan maganar Alqali ta dawo dani duniyar tunani.

Anan zamu dakatar da wannan shari'ar tamu Kotu ta shiga hutun takaitaccen lokaci zuwa karfe sha biyu zamuci gaba da zaman insha Allah."

Fita Alqali yayi,kowa ya fita nida JJ kallan kallo mukema juna banda kallan tsanar da yake aika mani kamar ya halakani yakeji.

Yan uwana kuwa badai abarina inje garesu saboda ina under case,amman fuskar su kadai zata nuna maka tsantsar tausan su agareni.

Kowa yaje yayi biyan bukatar shi karfe shabiyu aka dawo Kotu tacigaba da zama a karo na biyu,wannan karan kuwa Barrister Tukur Jakara shine agaban Kotu bayan izinin daya nema na ganawa dani.
As usual shiga nayi wajen amsa tambaya yace.

"Aminatu Yusuf last zama da mukayi kinfara ikirarin cewa Junaid yana bibiyarki kuma yana maki barazana da mugayen kalamai alhalin ban kyautata zaton zai maki haka,zaki iya gabatarwa Kotu da shaidun da kike ikirari kinadasu."?
"Insha Allah zan gabatar dasu yanzun nan."

Ɗan sauke ajiyar zuciya nayi na kuma cewa.
"Ina kyautata zaton wayata na hannun iyayena wanda na naɗi maganar Junaid a ciki."

"Kotu na bukatar ganin iyayen Aminatu a waje dan gabato mana da shaidar ta."
Mahaifina ya mike ya kawo wayar ya mikama Barrister Tukur shi kuma ya mikomani,saidai ina karba naji faduwar gaba mai tsanani tsorona daya kada ace angoge shi saboda anjima dayin abun,amman Allah gatan bawa.

Addu'a kawai nike a cikin zuciya na shiga cikin folder dita wadda nike ajiye abubuwa masu matukar mahimmanci agareni na bude password din danasa nafara budawa i take almost 10mint ina neman shi,amman bangan shiba.

Har mutane sunfara kuskus dayawan su nasan zagina ake ana cewa daman sharri zammasa tunda nagaza gano recording din,zufa tafara karyo mani,dago kaina nayi na kalli mahaifina wanda idanun shi suka sauya kala da duk wani masoyana hakama Ya Taufiq ya shiga damuwa saidai ta fuska yake kara Encourage dina kada in karaya,danko JJ sai killer smile yake mani wanda ni kadai nike fahimtar shu'umancin shi.

"Malama Amina ke Kotu ke sauraro idan kinsan abubuwan da kikace babu daman can aruɗe kike shiyasa kikai ikirarin kalabawa Junaid wannan sharrin kifito fili kifɗa nyaso sai.....

"Ya maigirma mai shari'a karyata mai kara kai tsaye babban laifine kuma ya taka doka dan haka yanada kyau abokin aikina ya kiyaye hakan."
Barrister Bashir yai magabar a harzuƙe.

"Ka gyara kalamanka Barr Tukur."
"Thank u My Lord."

Niko kaina yagama daukar charji ga maganr Barr Tukur tagama 6ata mani rai a dake nace.
"Bangani ba."
Shine abinda na furta kalaman da Barrister Tukur yai mani sun sosa mani rai kwarai.

Murmushi yayi mai bayyana jin dadin shi yace.
"Ashe dai maganata ta tabbata kenan,miyasa zakice akwai abu bayan kinsan baki daukaba wannan yazama kage,ko kinaso kice iyayenki su suka goge maki recording din."?

"Wannan kuma abinda bazai taba yuyuwa bane Barrister."
"Ina yake inhar kinsan gaskia kike fada."?

Shiru nayi ina tunanin miyasa naba Ya Taufiq haɗin kai a wannan shari'ar gashi wannan shaidar itace first level da Kotu zata fara gazgata gaskia ta gashi tashin farko nayi loose,anya inada sa'a a wannan shari'ar kuwa.?
Tambayar da nikema kaina kenan,inajin kwalla suna neman kubto mani nafara kokarin maidasu ɗago kaina nayi,muka hada ido da Barrister Bashir kana ganin shi ya shiga tashin hankali ba damar yai magana tunda ba hurumin shiba ne,saidai kallo yake mani mai ma'anoni,yana ƙara nuna mani wayar hannuna.

"Zaki iya kawo wayar aba Majesty ya bincika saidai middin kikaima Junaid ƙage zaki gamu da hukunci daidai laifin ki."

Harya anshi wayar nace. "tsaya Barrister bani in kara dubawa."

"Aminatu Kotu tabaki 5mint kiduba for the last time karki manta Kotu ba wajen wasa bane."
Cewar Alqali.

Text na fara shiga jikina na 6ari,saboda neman recording din yasa na manta da text din dayai mani,ina ganin Text din nakara samun hope duk da yawan text dana iske musamman na wajen aikina amman Allah yasa naga na Junaid din.

Sake bin cika files dina nike har zan fito naga recording kunnawa nayi saiga sunan shi ya fito JJ a jiki aiko maganar shi ta karade Kotun,mikama Barr nayi ya mikama Majestry aka kunna kowa yanaji Court tayi tsit,ina ganin Baba na godema Allah,Ya Taufiq harda kwallan dadi yayi,nima kukan zuci nikeyi inankara godema Allah,haka aka ji komai sannan aka ba Barr waya yace.

"Munji wannan saidai kamar ba muryar Junaid ba dan...."

"Objection My Lord karyata mai hujja alhalin ya gabatar da itaba gaban kuliya kai tsaye babban laifine yakamata Barr Tukur ya kiyaye hakan nan gaba."
"Akiyaye Barr Tukur."

Shiru yayi can kuma yace.
"Kince akwai text shima munason mugan shi."
Ansa nayi ban bata lokacin naba na bude na mika mashi aka fara karanta shi kamar haka.

*Assalamu-alaikum*

_Beautyna ya karin hakuri Allah yai mashi rahama yasa ya huta ameen._

*Ayyah kwara daya tafi domin koda kin aure shi nidin bazan bari ku zauna lafiya ba kin dauka alqawalina na banza ne,zan yadda makamaina akanki bayan kedin desire dina ce,kisa aranki zan dawo rayuwar ki,kuma komai kikeyi a tafin hannuna yake,kuma duk inda kikaje ni JJ ina taredake matukar baki aureni ba saina kinyi kukan dahar ki mutu bazaki taba daina suba dani kike zance Dr JJ*

Zufa Barr Tukur ya goge yana zame hulae kanshi.
bandaJJ daketa raba ido,ya amshi wayar ya miko mani akaba yan sanda sukaba mahaifina,ya maido kallan shi wajen Alqali yace.

"My Lord zanso Court tabani......


_Comment dinku na musamman ne inaganin sakonnin ku da fatan alkhairin ku agareni Allah yabar kauna,nima ina maku fatan alkhairi akoda yaushe🤍_



_Yar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Pls
❣️

_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E41&42




"My Lord zanso Court tabani dama,kafin ta sake waiwayata in gabatar da wani ɗan bin cike."
"Anbaka dama Barrister."
"Thank you My Lord."

Komawa Barrister Tukur yayi ya zauna.

Alqali ne yaɗa zare glass din idon shi yace.
"Ko lauyen Maikara yanada abin cewa."?

"Yes My Lord,inasan Court tabani dama ingana da mahaifin mariganyiya Asma'u."
"Kotu taimaka izini Barr Bashir."
Fitowa Baban Husna yayi gaban Kotu ya tsaya dayan wajen tambayar dake facing dina.

B"aba zamuso ka sanarma Kotu nasabarka da dangantakar dake tsakanin ka da marigayiya.?"
"Da farko dai ni sunana Abubakar Hamza ni hafaffen dan jihar Katsina ne a garin Caranci,Asma'u ya'ta ce ta cikina kuma ta kasance babba a wajena da ita Allah yafara azurtani,sannan inada kyakkyawar alaka da ɗiyata,wannan shine dangantaka ta da Asma'u Abubakar Hamza."

"Masha Allah,Baba zamuso kaima Kotu bayani akan dangantakar dake tsakanin Asma'u da Aminatu."?

"Kamar yanda kowa yasani Asma'u da Aminatu yan uwane na jini ta bangarena suka hadu,tunda nike duniya bantaba ganin Aminatu da Asma'u sun samu sabani ba wai ace faɗa saidai ajizanci na ɗan Adam suna son junan su sosai basa boyema juna sirrikan su,bacci kadai ke rabasu zan iya cemaka baccin ma wani lokacin atare sukeyin shi,Barrister bansan ya zan kwatanta maka alakar dake tsakanin Asma'u da Aminatu ba wannan sai Allah shi kadai yabarma kanshi sanin irin kaunar da sukema junan su saifa su da sukejin hakan a cikin zukatan su."
"Hakane kam Allah yajikan Asma'u."
"Ameen ya rabbi."

"Shin kai kuma minene alakar ka da mahaifin Aminatu.?"

"Anawa bangaren da mahaifin Aminatu dani abokina ne tun na yarinta tare muka tashi,shine yai mani abota da zanyi aure haka nima,zan iya ce maka aminina ne yardaddena bai taba cin amanata ba idan ina cikin damuwa yakan shiga idan abin dadi ya sameni shine gaba wajen farin ciki zan iya ce maka banda kamar Yusuf har gobe,tsananin tarayyar mu tasa kaf ya'yan mu suka haɗe kansu kuma kusan kowa nada warin abokinsa shiyasa shakuwar Asma'u da Aminatu tayi karfin gaske abun ya samo asali daga iyayen su,sannan kuma shi makwabcina ne,na amana koda ba abota zan iya cewa koba raina zai iya kulawa da zuriyata nidai bantaba kokawa ba akan makotaka ba,gaskia nayi dacen makwabci nagari,abokina,dan uwana kuma aminina wannan itace dangantaka da Alhaji Yusuf."

Jinjina kai Barrister yayi yace.

"Allah yakara donkon zumunta."
"Ameen Barrister."
Nidai share kwalla nike kaf shari'ar da ake ba abinda ke daga mani hankali kamar atuna maganar Husna nakan rasa sukunina inshiga damuwa da dimauta.

"Shin Alhaji Abubakar lokacin da akaci Aminatu ta kashe Asma'u ya kaji lamarin kuma kaima ka gasgata hakan aranka."?

"Subhanalillahi ko a mafarki bazan ta6a yarda Aminatu zata iya kashe Asma'u ba,bare kuma a zahiri kuma har gobe kai har in mutu ni Abubakar bazan gaji da karyata duk wanda yai wannan furucin agabana ba,wlhil azim Aminatu bazata taba kashe Asma'u ni inada wannan tabbacin na kokonto banyi."
"Wannan shike nuna ka aminta da Aminatu dari bisa dari bazata iya kashe Asma'u ba."?

"Raina fansane Barr Bashir,Aminatu bazata iya mintsili mai cutarwa ga Asma'u ba bare akaiga kisa,inaga dai bakasan kyakkyawar alakar dake tsakanin suba ne,shiyasa kake kara jaddamani wannan tambayar."

"Gaskia ne nima kaina ban yarda Amina zata iya kashe Asma'u ba,saidai kasan ance shari'a sabanin hankali ce dole muyi bin cike shiyasa kaji nace maka haka."

"Toh gaskia Aminatu bazata iya aikata abinda ake zarginta akaiba kada ka manta Asma'u fa ya'ta ce ta cikina, duk yanda nakai ga son Aminatu bazan sotaba naki Asma'u kodan alaka ta so da kauna dake tsakanin ɗa da mahaifi,ai yasa ku gasgata maganata har abada Amina bazata iya kashe Asma'u ba wannan shine gaskiar zancen Barrister."
"Masha Allah Alhaji zaka iya komawa mungode da wannan shaidar taka."
"Nima nagode Barrister."
Komawa yayi ya zauna ya sake kallan Alqali yace.

"Ya mai girma mai shari'a ina neman wannan Kotun mai alfarma tabani izinin ganawa da mijin mariganya Asma'u."
"Anbaka dama Barrister."
Fitowa Abdallah yayi gaban Kotu ya tsaya.

" Bawan Allah zamuso ga sanarma Kotu wanene kai kuma minene alakar ka da mariganya Asma'u."

"Sunana Abdallah Abdulkadir ni hafaffan dan Kano ne dangina duk yan nan,alakata da Asma'u mata tace,uwar ya'yana wannan shine alakata da Asma'u Allah yaimata rahama."
"Ameen kace uwar ya'yan ka kana nufin kunada zuri'a da ita?"

"Eh kwarai kuwa ya'yan mu biyu akwai Aminatu sai kuma Aliyu Haidar shike karami."

"Masha Allah,duk da bansani ba kace kanada Aminatu amman sai nike ganin kamar amintaka dake tsakanin ta da Aminatu yasa akai mata takwara hakane."?
"Eh saboda amintar su tafi hakan sannan Mina nada nasaba da Aminatu saboda uwace agaresu."

"Alhaji Abdallah kace uwa ce agaresu taya uwa zata nakasa ya'yan ta ta hanyar kashe mahaifiyar su indai itadin uwace ta gari kamar yanda kake ikirari."
Kallan Barrister Bashir nayi naganin kamar ma ba kareni yake ba,yanda yakema Abdallah tambaya kace shine ke againsing dina saidai ina zatan kilan haka salon aikin nashi yake,cewa yayi.

"Aminatu bazata iya kashe Asma'u ba,nifa inaga wannan shirine kawai tuggu aka hada mata."
"Wakake zargi.?"
"Bana zargin kowa Barr nasan dai gaskia zatayi halinta insha Allah."
"Allah yasa idan nafahimce ka Abdallah kana da yakinin Aminatu bazata iya takashe Asma'u ba hakane."?
"Kwarai kuwa abinda nike nufi kenan inada tabbacin hakan Aminatu bazata iya kashe Asma'u ba."

"Masha Allahu,zaka iya komawa ka zauna idan Kotu na bukatar wani abu a gareka zata sake waiwayar ka nagode."
Komawa Abdallah yayi ya zauna,shiru ta sake kaurewa a Kotun kowa yana maida kallan shi wajen Alqali da ke magana.

"Barrister Bashir akwai wata hujja da zaka gabatar wa Kotu a halin yanzun."?
"Eh ranka shidade saidai akwai abinda nike shirin ida tabbatarwa kafin a ida gabatar da shari'an nan insha Allah."

"Allah yasa duba da shaidun da aka gabatar a halin yanzun da wanda za'a gabatar nan gaba Kotu tabawa lauyoyinta damar gabatar da shaidun karshe nan da ranar litinin mai zuwa daga shi Kotu zatai duba da shaidun data tabbatar domin yanke hukunci dan haka Kotu ta dakatar da zaman nan sai rana ita yau litini.
Sannan Kotu tabada dama hukuma ta rike Junaid Jamilu gidan wakafi kafinta,tabbatar da duk wani hukunci ko akan shi ko akan Aminatu duba da wasu dalilai wanda hakkin Kotu ne harsai anyake hukunci insha Allahu."

A firgicie JJ ya mike tsaye yana zare idanu ga uwar zufa sai keto mashi take kana ganin shi kasan yagama shiga tashin hankali.

Shiko Alqali daukar guduma yayi ya buga kowa ya mike yafita kowa ya kama gaban shi,nidai saijin dadi nike ganin shaidun da aka gabatar musamman dana samu recording din JJ bada wani bata lokaci ba aka sani mota mukayi gidan Yari aka maidani har daki.


Bayan kwana ukku,Anty Hafsat ce tazo gidan Yari saidai da alama tabi hanyar sirri aka barta taganni domin zuwa yanzun tunda akafara shari'a dani,ko Ya Taufiq
ba'abari ya sake ganina ba in mun hadu sai Kotu shima din magana bata hadani da kowa a cikin su,Barrister Bashir da Samir kadai keda damar ganina dan binciken aikin su amman sai ga Anty Hafsat tazo har cikin office naje ita da Karima na iskesu wani matsiyacin kallo na aika mata mai cikeda tsanar ta.
Itama kallan take watsa mani tace.

"Allah ya tsine ma hali irin naki Amina yanzun tsabar gantalewa Junaid zakima sharri kega watsastsa ko?toh bari kiji wlh saikin dawwama gidan yari har abada kina takama wancan tsinannan yadawo zai kwatar maki yanci ko?kisani kina nan kuma bake ba auren shi,Junaid yafi karfin ki."

"Uhmmm Hafsat kenan damuwarki,amman inasan kisani ta Allah ba takiba kuma komi ya sameni kisani Haka Allah Yaso kuba ku isakuyi mani komai ba."

"Haka kikace?Kijini da kyau da izinin Allah yanda waccan shari'ar aka garkame ki,wannan ma zakici sarka har lahira natsane ki Aminatu."

Murmushi nayi mai ban takaici nace.
"Nasani ai basai kin maimaita mani ba,kije da anniyar ki ta Allah bataki ba."
"Ke bakida hankali ba yayar mahaifiyar ki bace kikema haka."

"Allah ya tsareni uwata bata hada komai da wannan ban kaurar ba,ke kuma kisani yanda kikazo har inda nike kika baƙanta mani kika cimani mutunci nabarki da Allah,kinci amanar zumunci dan kanki."
"Da kice badan kaina ba anan zaki dawwa har abada Aminatu."

Juyawa nayi nafita ganin idan na tsaya jinta tabbas zuciya ta zata iya bugawa, komawa dakina nayi na zauna na buga uban tagumi araina sai sake sake nike.
Ina ganin idan nabar gidan Yarinma jidalin Anty Hafsat ya isheni ko anan dinma ban tsiraba Allah kaimani tsari da mugun kudurin ta.

Haka na zauna tunda Anty Hafsat ta tafi ba'a kara kawo mani ziyara ba amman kalamanta na bani mamaki minene hadin ta da JJ ina tasan shi kodan taga makiyi nane shiyasa take goyon bayan shi,da haka na watsar da lamarin ta.

Haka rayuwa ta kasance a gidan Yari banda wata matsala saita tunani shima ba sosai ba.
Su Cankwai kuwa mun shaku sosai mun daina fada komai tare mukeyi kamar bamu ba.


******
Rt Major Taufiq ne zaune gaban Umma Zainab shi dasu Tariq sai Mum da Baba,ba abinda suke sai tunanin yanda shari'ar Aminatu zata kasance.

"Nifa gaskia sai inga kama da wata a kasa cikin lamarin shari'ar nan ina zargin akwai makusntan mu da suke da sa hannu a case din nan ba JJ kadai keda laifin nan ba."
Cewar Ya Taufiq

"Kwarai kuwa Hussein nima abinda nike tunani kenan domin case din nan ya daure mani kai kwarai da gaske."
Inji Ya Tariq
"Abinda baku sani ba har gidan Yarin fa bibiyar Aminatu akeyi da mugayen jafa'i iri iri nidai tsoro na daya kada suyi galaba akanta hakan yasa nakara rokon Adam akashe ansar Visitors da sunan zuwa ganin ta gudun kada a cutar da ita sai gashima Court da kanta ta hana kowa zuwa ganin ta."
YaTaufiq ya ida maganar araunane.

"Ya dace gaskia Hussein nima tunanina kenan kai Allah yai mana magani amman rayuwar Aminatu cike take da kalubale iri iri na rayuwa Qaddararta daban take lamarinta na zuwa a bazata Allah dai yasa taci wannan Jarabawar amman an wahaltu dayawa Allah Sarki Mamana."
Baba ya ida maganar a raunane duk zuciyar shi ta karaya yana karajin tausayin yar tashi.

"Yusuf kadaina karaya dayawa kowa da tashi jarabawar saidai kusani kuma iyaye kuna da naku gudunmuwar dakuka dage wajen haramta abunda Allah ya halasta kun nace sai kun raba tsakanin Hussein da Aminatu harda hakan komai ya lalace mana."
Cewar Anty Zainab.

"Haba Ummi kidaina tuno baya mafi munin zance intuna bayana sai inkasa yafema kaina bacin rai da fushin zuciya yasa na yanke hukunci mai zafi akan Aminatu,ni kaina ina kunyar hakan,bansan ya zan misalta maku yanda nikeji ba."

Y"a isa Allah ya yafe mana baki dayan mu,amman daga yau duk abinda kukaja kukaga yaki jawuwa to kusama Sarautar Allah ido,musamman harkar aure rabo na iya tafiya da wani ita rayuwa ba'ai mata haka,Allah ake fallawama al'amura baki daya."
"Hakane kam Allah yasa mudace."
Ameen suka amsa.

"Aini Zainab tension din dana shiga a kan case din Aminatu da Hussein bansan ya zan misalta shiba musamman wajen mahaifin yaron nan ya birkice kamar wanda akaima sammu,Allah dai yasa ba rabon Alhaji ya sakeni da tuni komai ya lalace,sai gashi daga baya kuma Allah ya warware masa komai ai ban fatan Allah ya maimaita mana irin wannan lamarin gaskia yaran nan sunga rayuwa,musamman Aminatu dake gidan Yari Allah ya kubutar mana da ita."
Cewar Mum.
"Ameen."
sukace baki dayan

Please Login or Register in order to submit comment