Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aminatu ko miye hadin ka da ita."?

Ɗan fiddo idanun shi yayi waje yasa Handkerchief yana goge jibin kanshi muryar shi na breaking yace.

"Eh ada tsohuwar budurwata ce,amman yanzun banda wani haɗi da ita."

Kallan mamaki Barr Bashir ke mashi yace.


_Yar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Pls
❣️


_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E35&36



"Eh ada tsohuwar budurwata ce,amman yanzun banda wani haɗi da ita."

Kallan mamaki Barr Bashir ke mashi yace.

"Bangane baka da wani haɗi da itaba,indan ba abun da kakeso kacimmawa a wajen ta miyasa kake bibiyar rayuwarta."?

Wani murmushin iskanci yayi yace.
"Kawai dan bansan wani ya rabeta bayan ni."

"Wane irin wasane kakeyi Junaid kace ada take budurwarka kuma kadawo kace saboda bakason wani ya ra6eta,wane kakeso mu dauka a ciki?wannan shike nuna,ya tabbata kenan akwai wata manufa da kakeson cimmawa akanta."

"Objection My Lord yaka mata Lauyen mai ƙara ya gyara kalaman sa,akan wanda yake tuhuma yana son yayi anfani da wata damar sa wajen yima wanda ake zargi ƙage."
Cewar Barr Tukur.

"Akiyaye Barr Bashir."
Cewat Alqali.
Jinjina kai yayi yaci gaba da cewa.
"Munasan muju sahihiyar alakarka da Aminatu."

"Nifa nagaya maka na sota sanda take Jami'a yanzun kuma ba wata alaka a tsakanin mu."
"Wannan yana nufin daman can kasanta kunyi mu'ammala da ita."?

"Eh daliba tace kuma tunda muka rabu da ita bankara waiwayarta ba sai daga baya saboda ni inason ta,itace bata sona kuma banson inga wata mu'ammala ta shiga tsakanin ta da wani ɗa namiji bayan ni."

"Ko minene hujjarka.?"
"Saboda ina sonta."

"Amman kuma kace a yanzun baka da wata alaqa da ita mizaisa kadinga bibiyar al'amuranta."?

"Kamar yanda nace maka tund har taƙini ni kuma bazan bari tayi mu'ammala da waniba gwanda kowa yarasa."

"Kana nufin shiyasa kabada shaidar zir akanta dan rayuwar ta ta wulakanta."

"Aaa Barrister nifa gaskia ta kawai nafaɗa a zaman farko da akayi."
"Hmmm Junaid yanda kace kenan,amman dakake bibiyar ta,kace tunda ta shigo garin Kano kai kasan ta shigo,wannan yana nufin koda tayi jinya,a asibiti kasani kenan.?"

"Kwarai kuwa zan iya cemaka kusan dani akai jinyarta a cikin asibitin Dala ta ƙashi,dandai ban bayyana kaina ba amman ina sanya yarana na zuwa dubiya."

Kallan shi Barrister Bashir keyi yana karantar yanayin shi yace.
"Good kai ɗan dabane."?

"Objection My Lord kalaman da abokin aikina ke anfani dasu sunyi tsauri dayawa ya kamata ya daidaita kalaman shi."

"Korafi bai karbu ba Barr Jakara.
Cigaba da aikin Barr Fage."
"Godiya nike My Lord,kai Kotu ke sauraro Junaid."
Zuwa lokacin Dr JJ yafara raina gaskiar shi sosa keya yafara sai kuma yace.

"Ba abinda ya hadani da, dabanci Allah ya tsareni."
"Ameen Junaid saidai kace yaranka ko kana nufin ya'yan cikin ka."?

"Aaa ya'yana basu kai hakaba yarane amman ni ba ɗandaba bane."
"Wa'anne yaran kake nufi."?

"Barrister sai nike ganin wannan kuma sirrina ne koma wa'anne yara nike nufi ba dole saina bayyana suba."

"Junaid inda agaban Alqali kake dole ka bayyanama Court abinda aka tambayeka dan haka kai muke sauraro."
Cewar Alqali.

"Eh to daman ina nufin masu tafiyar da hidindimu na kamar harkar kasuwan cina."

"Uhmmm ashe dai Junaid ɗin ɗan kasuwane ko zamu iya sanin nau'in kayan da kake siyarwa."

"Objection My Lord bakowace tambaya yakamata abokin aikina zai dinga yimashi ba,sanin nau'in kayan da yake saidawa bai cikin case dinmu."
"Daman ana sirrinta abunda ake siyarwa a kasuwa."?
Cewar Barrister Bashir.
Yaima abokin aikin nashi tambayar ranshi a 6ace.

"Barr Bashir ka ɗaga kafa."
"Thank you My Lord."

Junaid a wancen karen daka cema Kotu kaine shaida akan Aminatu,shin wadanne irin hujjoji ka kawoma Kotu."?

"Ai hujjata a bayyane take karfa kamanta da kaina na kirawo shaidu suka ganta rike da wukar tana kukan tuggu gaban kawarta wannan kaɗai bata isa hujjaba Barrister."?
A zafafe JJ yai maganar.

"Aaa bazata isa hujjaba wama ya sani ko tana shigowa ta isketa cikin mawuyacin hali hakan yasa ta rude harta zare wukar kamar yanda kake ikirari kaganta ta daba mata wuka ta ƙara daba mata a ciki,shin a lokacin bakai basirar daukarta a cikin wayar kaba."?

Tsit Kotu tayi kamar an mutu kowa idanun shi kan JJ daya gaza magana saida raba idanu dayakeyi."
"Kayi shiru Junaid kai muke sauraro."
"Ban dauka ba."
"Ko miyasa."?

"Haba Barr miyasa kake mani tamabayoyi marassa anfani yanzun kai ace kaine ka iske an kashe mutun a gaban idonka taya bazaka razana ba."?
"Zan razana mana."

"Toh shine kuma kake mamaki dan nace maka na razana."

"Hmm Junaid kenan,ai dole inyi mamaki razanar kala kalace ya danganta zan razana idan inada kusanci da wanda aka kashe ɗin,wannan shine idan baka da alaka da ita zakaji ba dadi bawai karazana har haka ba,kuma bazaka gaza ɗaukar a cikin wayar kaba."

"Banda alaka da ita,illa ita ɗin kawar Aminatu ce."
"A lokacin yakamata ka dauki video din case din Junaid."

"Allah bai nufa zan ɗaukaba Barrister kuma ni ƙaryayyar zuciya ne dani,shiyasa razanar danayi tasa na kasa daukar case ɗin,sannan na kawo shaiduna wannan shine abinda nasani."
"Well done Junaid zaka iya tafiya kafin insake waiwayar ka."
Kowa mawa yayi ya zauna a sirace.
Kallan Alqali,Barr Bashir yayi yace.

"Ya mai girma mai shari'a zanso Kotu tabani dama ingana da mai kara."
"Kotu tabaka dama Barrister."

"Takowa nayi na ida shiga wajen tambaya kaina kasa ko hada ido da mutane banson yi musamman wa'anda nasani, tsaye nayi bance komai ba.

"Zamuso kisanarma Kotu da cikakken sunanki."?
"Sunana Amina Yusuf kuma ni haifaffiyar garin Caranci ce,ta jihar Katsina."
"Masha Allah,Kotu zataso taji minene asalin zuwanki Jihar Kano.?"

Dagowa nayi da kaina adake na maida kallona kan al'ummar dake wajen musamman Dr JJ daya gama gilla mani karya inaji inagani,shima nidin nike kallo ban fasa kallan shiba duk irin kallan tsanar da yake jefo mani nace.

"Ranar dana shigo garin kano daidai Kurna anan mota ta saukeni babban layi nazo zan tsalaka titi.....haka nagama gaya masu AtoZ.
kamar yanda nagayama Barrister lokacin daya kawo mani ziyara gidan Yari ba abinda na boye har zuwa lokacin dana iske Husna kwance jina jina cikin jini,ga wuka a cikin cake duk na gayama Barr Bashir agaban kowa,naci gaba dacewa.

"Nashiga tsananin tashin hankali mai rudarwa baki daya nasara tunanina tsabar kiɗima,bansan na fiddo wukar a cikin taba,harna yanke hannuna abin mamaki sai naji yan sanda akaina sun kamani ansaka mani unkwa agefe guda JJ ne,tsaye yana mani murmushi wanda bansan manufar shiba,daganan sukayi dani Area Commanda Kwalli."

Na ida maganar da comfidence ko kwalla babu danji nayi zuciya ta ta ƙeƙashe amman dayawa wasu kuka suke tsananin tausayina wasu kuwa ji suke imana su halakani su huta."

"Toh Aminatu zaki iya komawa kafin bukatar sake ganawa dake ta taso."
Komawa nayi gefen Karima da suke zaune bisa sit nidai tsaye nayi duk wannan zaman kuma ina gaban Kotu.

"Ya maigirma mai shari'a zan dakata anan kafin in ida faɗaɗa bincikena nagode My Lord."
"Badamuwa Barrister Bashir."
Cewar Alqali da yake rubutu yace.

"Duba da lokacin Sallah daya gabato Kotu zataje hutun takaitaccen lokaci saidai tana mai shaidama Yan sanda da'aci gaba da kula da mai laifi kafin shari'a tayi halinta."

Buga guduma yayi ya fita kowa ya mike ya fita nidai ina tareda Jami'an tsaro ko sallah wani daki suka yita, ina zaune ana tsare dani,ko magana ba ayarda kowa yai mani tsakanina da dangina saidai ido.

Haka kowa ya fita yana fadar albarkacin bakin shi aka hau sallah.
Wajen minti talatin aka fara dawowa saidai wannan karan cikar tafi ta farko.
Koda aka shigo dani saida gabana ya faɗi tsabar cikar da wajen yayi da ɗan Adam.
Alqali ya shigo kowa ya nutsu akaci gaba da zama karo na biyu.

Wannan karan Barrister Tukur Jakara ne gaban kuliya bayan Alqali ya bashi izini cewa yayi.

"Ya mai girma mai shari'a zanso Kotu tabani dama ingana da mai ƙara."
"Anbaka Barrister."
Shiga nayi inda ake tambaya na tsaya.

"Amina Yusuf Caranci shine cikakken sunan ki hakane."?
"Kwarai kuwa Barrister sunana ne."

"Kince ranar da aka kamaki kin dabawa aminiyar wuka a ciki sharri akai maki bayan keɗin da kanki kika amsa laifinki akaron farko miyasa yanzun kike jayayya da hukuncin da ake maki."

"Saboda banda abinda zan kare kaina dashi a wancan lokacin."

"Yanzun kuma ya akai kika samu kodai akwai waɗanda suke baki hujjar da zaki anfani da ita wajen kare kanki a wannan karon."?

"Ko ɗaya wancen lokacin tashin hankalin da nike ciki ya girmi in tsaya kare kaina a gaban Kotu saboda ina cikin taraddadi da tsananin tashin hankali na rasa yar uwata kuma aminyata danayi,wannan shine yasa na amsa lafin da ake tuhumata dashi a abaya."

Murmushi yayi yace.
"Saboda kin za6i mutuwa da rayuwa komi kikeson kice."?
"Kusan hakane shiyasa na aminta da hukuncin da akai mani."

"Yanzun kuma kina son rayuwarki akan mutuwar ki kenan,bayan kince mutuwa tafi maki rayuwa."

"Eh har yanzun hakan take awajena,yanzun na zabi na kare kaina dan in fidda kaina a zargi da Allah wadai da yan uwa da sauran Jama'a ke mani shiyasa nikr jayayya da hukuncin da akai mani,amman nasan rayuwata ba Asma'u a doron ƙasa tabbas akwai tawaya agareni."

"Wannan shike nuna cewa ke kika kashe kawarki da kanki kenan, kuma kike ikirarin an maki sharri."

"Objection My Lord ɗaura laifi ga mai ƙara kai tsaye batareda an tabbatar da hakan ba kamar sabawa doka ne ya kamata abokin aikina ya gyara kalaman sa dan sunyi tsauri da yawa."

"Barrister Tukur ka kiyaye gaba."
"Godiya nike My Lord."
"Inason ki sanarma Kotu dangantakar ki da mai mutuwa ataƙaice."
Sai lokacin idanuna suka kawo ruwa nace.

"Asma'u yar uwata ce ta jini kuma ta kasance kawata tun ta kuruciya mun tashi cikeda so, kauna,tausayi da aminci mai karfi atsakanin mu,duk da take yar uwata saidai kawancen mu,yasamu asali daga iyayen mu maza da mata suma aminan junane sannan mahaifiyata yayace ga Asma'u cousin dinta ce wajen iyayen su maza,tunda nike da Asma'u bata taba cin amanata ko zalincina ba,zata san komai nawa nima insanin komai nata batareda kowa yasani ba,gaskia bansan taya zan iya misalta maku kalar amincin da kauna mai karfin gaske dake tsanina da ita ba."
Hawaye suka sauko bisa kuncina.

"Kince bata ta6acin amanarki ba amman ke miyasa kika gaza rike tata amanar."?
"Allah ya tsareni dacin amanar Asma'u wannan itace kalma mafi tsana da muni a cikin kunnuwana Barrister ban fatan na zama maciya amana a kan wanima bare kuma Asma'u."

"Aminatu kince Junaid sharri yai maki bayan kowa yasan shiɗin shaidane hatta masu hotel ɗin yakirasu sungani da idon su,shin suma duk sharri suke maki."?

"Kwarai kuwa Barrister domin kaf a cikin su,hattasu babu wanda zaice gashi ya ganni alokacin da nike sokawa Asma'u wuka a cikinta kamar yanda yake ikirari,saidai nasan na taka sahun barawo,ina mamakin taya za'ayi Junaid yasan zan haɗu da Asma'u a Hotel?abin mamaki ya akai banji ihu ko kuma alamun firgicin mutunba a lokacin da nike soka mata wuka ba? Koda yake ikirarin ya firgita nidai koda nike gaban Asma'u banji alamun mutun ba saidai naji anyi arastin ɗina duk wannan inda ace naji kana zatan zan tsaya batareda na guduba."?

Na ida maganar ina kallan kwayar idon shi yace.
"Tambayata kike kenan."?
Girgiza kaina nayi nace.
"Mamaki dai nikeyi Barrister."

"Ai ba abin mamaki bane idan akayi la'akari dake d
ɗin dukiyar ta kike bukata."
"Hmmm a labarin kanzan kurengensa kenan dai ba."

Jinjina kai yayi yana mai kallona yace.
"Aminatu ki sassauta fusatar ki ga mai tambaya aikin sane ya kawo haka,kuma kada kimanta nan din Kotu ce."
"Insha Allah zan kiyaye."

"Tinda kike kintaba ganin alamu ko wata tsana da Junaid ke maki,bare harkiyi zatan zai iya yimaki sharri."?

"Tabbas kuwa tsana mafi munima Junaid yake mani,duk mutumin dazai dinga bibiyar rayuwarka akowa ne lokaci wannan kaɗai ya isa kagane tsantsar tsanar da yai maka,saboda wannan dalilin ko kuma buri nashi dayakeson ya cika."
"Wane daliline wannan Aminatu."?

"So daya ikirarin yana mani tun a school wamda a wajena bakomai bane face tsantsar kiyayya da yaje maniba,duk da ba wannan bane dalilin zaman mu nan ba,amman Dr JJ yakasance wanda ya sama rayuwata ido tunkafin inzo Kano,ya bibiyi rayuwata tun a wajen aikina yai mani barazana akan komai zanyi atafin hannun shi nike,kuma yayi ikirari yace.
sai yasani kuka da idona sai nayi kukan da bazan ta6a dainasu ba har ƙarhen rayuwarta.
ada ban dauki maganar shi da mahimmanci ba sai ranar wata alhamis yazo har cikin office ɗina ya iskeni ina sallah.



_Yar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Pls
❣️

_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E37&38



"Ina cikin sallah naji shigowar mutun office dina,har nagama sallah alamun sun nuna koma wanene zama yayi,nade sallaya nayi na aje gefe,ina juyowa nayi arba da Dr JJ yana bina da shu'umin kallo tabbas nadan tsorota sai kuma na dake ina mashi kallan ko lafiya.

Wani irin kallo yake mani mai ma'anoni yace.

Beauty kina mamakin ganina ko?kibar mamaki nazo yimaki ta'aziya sannan na jadda mamaki son da nike maki yananan ba inda yatafi."

Kallan na bishi dashi ina mamakin karfin hali irin na Junaid dahar ya iya shigowa office dina batareda neman izinina ba kai tsaye.
Tafa hannayen shi yafara yana zagaye office din nidai na zauna bisa kujera ina kallan ikon Allah.
Yada kallona kyaune nai maki har haka? ai nasan bazaki bata samun kamata ba,dole kiyi tsumayina."

Jin abinda ya fada ya fusatani dan nasan Allah ya bani wanda yafishi da komai a duniya.
Raina yafara baci hakan yasa na mike ina nuna mashi kofa da yatsana manuniya nace.
Get out of my office."
Wani kallo yake mani yana nuna kanshi da yatsa alamun shi.

"Kana mamaki ne,wannan ba abin mamaki bane,dan na kori kaskantacce irin ka,sannan inasan injaddada gaya maka karka kara zuwa inda nike sannan kada kara bibiyata kabarni insake nagaji."

Gelele yayi yana kallona har saida ya zare glass din idon shi.
"Ni kike gayama magana Caranci.?"

"Eh nafada maka miyasa kazo har office dina dan haka kafita ban bukatar ganin ka,nace mashi.
Murmushi yayi mai ma'anoni yace.

Kin burgeni fa gaskia kinada karfin hali saidai da ace kinsan kalar tarkon da nike hada maki da bakiyi ganganci maida mani martani ba,bare kuma bakar magana."

"ta Allah ba takaba Junaid na riga nace Allah kuma shi zai mani tsari da kaidin ka insha Allah ban ganin komai sai alkhairi nace mashi zuciya ta na kuna!

Shikenan nidake muzuba mugani wlh saina saki kukan dahar ki koma ga ubangijin ki bazaki taba dainawa ba sainasa kinyi danasani marar anfani saikin shiga garari da bala'in rayuwa indai na ansa sunan JJ.!"
Ni kuma nace.
"Sannu ashe tarko kake hada mani,kayi takanka JJ nariga nai maka nisa nahar abada kai kasan wannan dan haka maza kabar mani office ko insa azo ayi waje dakai."

"Nikike gayama magana son ranki Amina kinsan waye ni kuwa."?
"Waye kai baccin dan Adam kamar kowa kai ba kowa bane face Junaid Jamil Kano (Dr JJK) sai kuma me."?
da yake haka muke kiran shi tun a school
"Kwarai kuwa kin canki daidai sai kuma wannan JJ din ya shantake iliminki da duk wani tunanin ki,kijira zakiga abinda zai biyo baya indai nine.!'

"Saidai inga alkhairi Junaid."
Raina ya kuma baci sosai hakan yasa nace mashi.
"kaga malam get out of my office."

Mikewa yayi yana mani kallan tsana mai rudarwa ya gwadani da yatsa.

"Kisani komai wayon amarya sai anlashi zumar ta,kuma matsawar bansa mekiba zan jefaki cikin kuncin dahar kigama rayuwar ki,kina zirarar da hawaye kisa wannan aranki dani kike magana Amina."
"Aniyarka ta koma maka." nace dashi.
Furzar da iska yayi mai zafi ya fita yana bugo mani kofa rufe idanuna nayi sai kuma na bude ina zaro wayata wadda nasaka ta a recording dan tunda yai mani text naima kaina alqawali koda tari zaiyi sai nayi recording din shi,dagani JJ baida imani ko kadan kuma zai iya aikata komai dan cikar burin shi akaina,tunda harya iya dawowa rayuwa ta akaro na biyu tabbas ba Allah aranshi.
Hakan yasa nayi saving recording din nayi cikin wayata natashi na rufo office nashiga mota na tafi gida.
Daman na tashi daga aiki,saidai barazanar da Junaid yai mani tahanani sukuni a cikin zuciya ta,wannan kadan daga cikin abubuwan da suka hadani da Junaid."

Shiru Barrister Tukur yayi na wucin gadi kafin yace mani.
"Kikace yai maki barazana amman ai wannan ba wani abu bane kika gaya mana ba face labarin kanzon kugerege shafama labari shuni muna son ki....

"Objection My Lord yakamata abokin aikina ya daina karyata mai kara kai tsaye dan kawai tafadi iya gaskiar ta dan kare kanta wannan ya sabawa doka."
Cewar Barrister Bashir.

"Barr Tukur ka kakiyaye aikata hakan gaba zaka iya cigaba da aikin ka."
"Godiya nike My Lord."

"Aminatu zamuso duk wata hujja da kika gabatar mana da ita agaban Kotu kikawo mani ita muji da kunnuwan mu tunda kince kinsata a recording,aganina zamufi gamsuwa idan kowa ya saurara."

Sadda kaina ƙasa nayi narasa abin cewa dan nasan da biyu yaimani wannan maganar shekara ta hudu kenan taya zan iya ganin wayata bayan tunda na baro gidan mu rabona da ita kilama ansaida ta,ya zanyi.
Ahankali na dago na maida kallona wajen mahaifana nace.
"Kila za'a iya samun recording din,amman banda tabbas."

wannan ba magana bace Amina wannan shike nuni da zakiyima Junaid sharri badan komai ba dan kiga ya tagaiyara."

"Allah ya tsareni Barrister in rasa wanda zamma sharri sai wanda bai gabana mantawa nike da rayuwar shi baki dayan ta badan wannan zaman ba kwata kwata bai cikin raina akan mi zan mashi ƙage."
Na ida maganar cikin fushi naga take taken Barrister Tukur so yake ya lakaba mani wani sharrin na daban.

Murmushi yayi yace.
"Indai ba haka bane Kotu zata bukaci sauraron recording ɗin da kikace kin naɗa."
"Insha Allah iyayena zasu dubo mani wayar dama wasu hujjojin."
"Kotu na sauraron ki Allah yakaimu lafiya."
Ameen."
Juyawa yayi yace.
"Ya maigirma mai shari'a ina neman wannan Kotu mai alfarma data kara mani lokaci domin fadada bincikena game da wannan shari'ar."

Rubutu Alqali yayi yace.
"Kotu tabaka dama Barrister Tukur dakai da abokin aikinka Barr Bashir kowa yaje yai bin ciken daya kamata kafin nan da ranar alhamis domin cigaba da sauraron wannan shari'a insha Allahu."

Gam gam Alqali ya buga Court stick din dake gaban shi ya mike kowa ya mike ya fita ta private door dinshi.

Take aka sake saka mani Unkwa Yan sanda guda biyu sai Gandirobas aka tisa keyata gaba,banda kallan tsana ba abinda JJ ke aikomani dashi.

Su Ya Taufiq kuwa cikeda tausayina suke kallona idanin shi sun kada sosai,wasu na kuka wasu ko ajikin su.

Tafiya akai dani taredasu Anty Hafsat da Mami naga JJ,su dukan su kallona suke kamar idanun su zasu shido kasa tsabar harara.
Mota aka sakani Zainab da Jidda sai aikin kuka suke Mama na rikesu tareda Baba sai Ahmad yaja motar su suna kuka.

Haka aka tada motar mu,muka nufi gidan Yari har bakin kofar gidan aka shiga dani office din Adam wani littafi aka dauko naga sunyi yan rubuce rubuce kowa cikin wadan da suka kaini Court sukasa hannu sannan aka tisa keyata har gaban dakin mu,saida aka bude su Cankwai sunyi cirko cirko suna kallona,da mamaki afuskar su sai lokacin aka cire mani unkwa ina shiga aka rufomu zama nayi raina ba dadi.

Kamar jira suka hau tambayata.
"Dago daga ina kike tun safe wai lafiya mike faruwa.?"
Da ban niyar basu amsaba sai naga sun damu matuka saboda zuwa yanzun muna zaman lafiya sosai dasu cewa nayi.


"daga Kotu nike."
Salati suka dauka baki dayan su sukace.

"Ke miya hadaki da Court aini ko a mafarki ban fatan sake zuwa Court wlh,ke kuwa Dago mi kikeyi a Kotu."?
"Shari'a inasan a yanke mani hukunci ta hanyar rataya shiyasa nazabi a sake shari'a na gaji da zaman nan.

"Ikon Allah kedai rayuwarki cike take da abubuwan al'ajabi inba Qaddara ba wakeson a kasheshi aikomu da aka yanke mana hukuncin kisa da dayanda zamuyi wlh da an 6atar da case din mun fita free gaskia Aminatu kina bamu mamaki da al'ajabi."

Nidai kallan su nikeyi dan bansan yawan magana ga gajiya inaji daman nasha surutu a Court hakan yasa nabasar da tambayoyin da suke mani kuma ina bukatar wanka daman ina MP, tasa na dauka na fara bugun kofa dashi ma'aikatan snaji sunsan inada bukata sosai lafiya cewar wata ma'aikaciya.

"Inasan zanje kewaye."
Bude mani tayi na dauki kayan bukata naje dan,in gyara jikina nasha zagaye kafin nasamu mai sauki wajen kazanta saida nakara daurayewa kafin na watsa tinda aka kawoni gidan Yari ko fitsari zanyi daga tsaye nike sai in dauraye kuguna a hakan ma ba laifi ana kula,haka nagama na fito nagama kimtsawa ta,ina dawowa na kwanta sai al'ajabin karfin hali irin na JJ nike wace irin tsana ce yai mani kodai shine ya kashe Husna! Ban tunanin zai iya aikata hakan koda yake shari'a sabanin hankali Allah yasa mudace,baccin wahala mai nauyi ya daukeni.


*******
Baki daya su Baba gidan Anty Zainab suka sauka katan falorn ta kowa ya zauna sai mamaki sukeyi yanda shari'a ta wakana a Kotu.

"Wai Hussein kuna ganin akwai nasara acikin wannan shari'ar.?"
Cewar Baban Amina.

"Insha Allah kawu abinda yafi burgeni confidence na Aminatu shiya kara mana kwarin guiwa gaskia tayi kokari Allah yabamu sa'a."
Ameen suka amsa.
"Saidai inaganin wannan JJ din kamar ba shikadai bane ya aikata wannan abunba inaji araina akwai sa hannun wasu a cikin lamarin nan.

"Kwarai kuwa Taufiq aida ganin kwayar idon shi baida gaskia ina ganin shi nagane kasan shari'a sabanin hankali inda kake zaton case sai kaga ashe ba anan yake ba Allah ya kubutar da ita."
"Ameen Ya Samir"
"Wai Samir kuna gane masu laifi kai tsaye kuna ganin su."

"Eh Inna muna ganewa saidai kinsan kai tsaye baka lakama mutin laifi harsai Kotu ta yanke hakan da karin kanta sannan."
"Allah yasa mudace."
inji Anty Murja

Baba ya maganar wayar Aminatu yace.
" yakamata muganota domin da ita zamu koma Barr Bashir saida yakara yimana maganar."

"Hakane Hussein nasan tananan anjima zamu tafi Caranci nida Ahmad muduba ta insha Allah."
Cewar Baba
"Allah yakaimu lafiya."
Ameen."

"Wani hanzari ba guduba mi zai hana kai Taufiq kabisu adubota gudun risk kasan halin mutane tunda kowa yasan kai Sojane ba wanda yasan U re retired har yanzun sai nakusa dakai,inaga za'aji shakkun yimasu abinda baidace ba."
Cewar Samir.

"Eh gaskia kuje tare Hussein."
"Shikenan Mum Allah yakaimu anjiman da haka kowa yaita fadin albarkacin bakin shi,sai yamma suka tafi Caranci dan dubo wayar da recording din ke ciki.

Suna isa Caranci gidan su Husna suka anshi key din gidan suka shiga saidai yayi yar kura duk da bayan wata ɗay Dada nasawa agyara shi akai akai dakin Baba suka shiga suka hau neman waya dambu taliya bata ba alamun ta.

Nemanta suke sosai har Baban Asma'u saida yazo yataya su nema amman ba waya kowa jikin shi yai sanyi duk tsoro yakama su ainun.

Dakin Ahmad ma anduba hakama dakin Mamar su duk anduba kai hatta dosbin amman basu ganta ba,kowa ya karaya sunaji kamar wata nasara ce aka rasa a cikin shari'ar Allah kadai zaima Aminatu gata,kamar kullin shine sarki buwayi gagara misali.
Har sun fidda rai kowa yai jigum cikin falor bamai magana saidai ido da sukebin juna dashi.
aransu kuwa salati suke suna addu'a Allah ya tunkude masu musibar dake bibiyar su.

Kira Ya taufiq ya gwada switch duk da sunsan hakan zaifaru kunsan ance mai nema mahaukacin zaune komai bai raina ba.

Sun yanke shawarar su koma in an koma Court suce ba'agantaba ai akwai wasu hujjojin kuma Allah yana tare da mai gaskia a ko ina yake.

Duk da sunyi dare har ankira isha'i rashin ganin wayar shiya fusata su akan su koma Kano komin dare da sunso kwana cikin sirri.

Zasu tafi kenan sai kuma Baba yai wajen kayan kallo yajawo loka ya kara dubawa yana mikewa sai ya duba gefen TV dake jikin loka ta bango anan ya hango hasken waya fara makale,hannun shi na rawa ya dauko take ya tuna ranar da lamarin yafaru databar gida nan ya dauko wayar daga tsakar gida yana shigowa zai kashe kallon da yakeyi ya watsata bayan lokar Tv take dana sani yakama shi a zahiri yace.

"Kungan ta da hannuna nai mata wannan ajiyar danma Allah yasa masu gyaran gidan nan ba maha'in ta bane da an dauke ta,kuma da ansara abubuwa masu matukar mahimmanci gaske aciki saidai mugodewa Allah.

Kowa yaji dadi sukahau yima annabi salati suna godema Allah,daman akwai wuta Chaji suka junata,ta jima kwarai takawo suka cikata sukahau duba wayar kafin suka kwanta goma tayi na dare,sai lokacin Baban Asma'u ya tafi gida yana masu saida safe.

Koda gari ya waye daga gidan su Husna akai masu break sukaci karfe goma daidai suka fito zasu koma Kano a kofar gidan suka taddata.

Cincirindon muta....


_Yar Matane Kankia ce❣️_


Share
Pls
❣️


_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E39&40

Cincirindon mutane kowa yana fadin albarkar bakin shi.
"Insha Allah sai Allah yatoni asirin ku dayake kunga kunada sama shine an gama yanke hukunci kukeja da hukuma dan ita mariganya bata da kowa,ai tinda har Aminatu taci amanar Asma'u mu kanmu mun dinga addu'a Allah ya toni asirin duk mai kulla kulla a cikin wannan shari'ar dan kunga mahaifin ta bashi da zafi shine kuka kwaso kafafu kuna haɗa shaidar zir sai Allah ya bankaɗa

Please Login or Register in order to submit comment