Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su,harda kwalla Mum ta share tana karajin tausayin ya'yan nasu aranta.
Shidai Taufiq yanajin abunbuwan da iyayen nashi ke cewa baice komai saidai amin,tunanin shi kaf nakan Amina wanda wutar sonta ke hauhawa a cikin zuciyar shi musamman daya dawo ya isketa a cikin Jail hakan yaɗa daga mashi hankali matuka.
"Hussein kungara magana da Barrister Bashir kuwa naga yau saura kwana Ukku ai zaman karshe.
"Aaa Mum bansake mashi magana ba."
Akan mi?"

"Naga shida Ya Samir suke aikinsu kuma abinda zaku lura dashi aikin da Barrister Bashir keyi a Court da yanda yake tambayar Amina baku ganin kamar ba kareta yake ba, kamar yana Challanging din tane."

"To haka aikin Barrister yake bai goyon bayan wanda yake karewa kai tsaye musamman idan shi ke mashi Question dan shi gaskia yana bin gaskia da wahala idan zai shari'a ya goyi bayan karya."

"Kwarai kuwa ni har tsoro yafara kamani gani nike kamar baison ya kwatar mata yancin ta,amman shaidu fa gani nike kamar baida cikakkun hujjoji."
Cewar Anty Zainab

"Aa Ummi bai fara tsayawa gaban Court saida yagama tanada kowacr hujja saidai kowace hujjar shi akwai ranar daya tsara zai gabatar da ita."
"Allah ya shigemana gaba."

"Ameen saidai yana da kyau aje ayi sadaka ga mabukata ayi addu'oi Allah ya kubutar da Aminatu,ita kuma Asma'u Allah yakai haske cikin kabarin ta."

"Ameen Mum saidai kisani tunda na diro kasar nan na iske Minal gidan Yari bantaba kwanciya na tashiba banje nayi sadaka ba ako ina kuma insha Allah munyi tawassali da kyawawan ayyukan da muka gabatar Allah ya kubutar da Aminatu cikin wannan tarkon."

"Ameen Hussein Allah yaimaka albarka yanda ka jajirce wajen ganin ka kubutar da yar uwar ka Allah yasaka maka da gidan aljanna."
Ameen Baba."

Haka dai suka wuni suna taraddadin lamarin Shari'ar da akeyi wanda yau saura kwana ukku ayi zaman karshe ko suyi nasara ko kuma akasin hakan kowa ɗarɗar yake a cikin su ba wani sukuni a ransu saidai sun dage da addu'a dafatan nasara akoda yaushe wannan kenan.

_*PRISON*_

Tunda Allah yasa nasamu cikakken tsarkina na.....



_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️


_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E43&44



_*PRISON*_


Tunda Allah yasa nasamu cikakken tsarki nadage da addu'a da nafilfili musamman cikin dare.
Yauma shirin sallah nafarayi kabbara nayi kasancewar sallar nafila ce zanyi kuma akalla dare yayi haka na yini ina mikama Allah kukana akan case din da ake gudanarwa tsoro na daya kada aiyimani zalinci a murde shari'ar inaji inagani kasancewar ita shari'a sabanin hankalice bawai danna matsu na fita gidan Yarin ba kodan mutanen da sukai Sacrifice din kansu dan ganin sun ceto rayuwata,wannan dalilin yasa nike fatan nasara a cikin wannan shari'ar tawa sosai.

Addu'a nayi sannan nahau karatun alqur'ani mai girma wanda Allah yasa na haddace haka nai tayi bisa kwallin danayi sallar na kwanta bansan sadda bacci barawo yai awon gaba da niba sosai nike bacci wanda bansan aya zan bayyana maku shiba ina cikin bacci, naga Mariganya ta jawo hannuna mun fita a gidan Yari bisa wani dutsin kankara ta zaunar dani tace.
"Minal ki dage da addu'a akan wannan lamarin daya sameki tabbas akwai kulalliya a cikin shi kuma makusantan ki sune suka shirya komai kawata kowane hali kika samu kanki a ciki ki yawaita ambaton Allah shi zai maki gata,kisa hakuri aranki domin Allah da kanshi yace yana tareda mai hakuri Allah ya fiddake cikin wannan musiba da kike fama da ita alfarmar fiyayyen halitta annabi Muhammad (SAW)."

Baki dayan muka ida ambatan sunan annabi saidai ina bude baki zan mata magana na nemeta na rasa sama ko kasa a razane na mike daga bisan dutsen da nike nafara neman ta sako da lungu ina.
"Husna kina ina kifito dan Allah kada kitafi kibarni kawata ina sonki dan Allah kada kimin haka."
sai kuka nike ina bulayi ina neman ta saidai ban gantaba sai muryar ta danaji kamar cikin kunnena ake rada mani ita.
"Qaddara ta rabamu Minal kuma kisa aranki HAKA ALLAH YASO kuma komai da kike gani LOKACINE Allah ya qaddara lokacina yayi da na amsa kiran shi,badan bai sona ba kuma badan nayi azarbabi bane aaa saidai haka Allah ya QADDARA min Aminatu ba abinda zai kuma haɗamu saidai addu'arki itace so da kauna da zaki nuna mani matsayinki na kawata masoyiyata kuma aminiyata ina maki fatana nasara da alkhairi kawata sai watarana."

Kuka nasake fashewa dashi nace.

"Dan Allah Husna kifito na rokeki,kuma wannan wace ranace zanso in sake ganinki kawata."

Muryarta takara sauka cikin kunnawana.
"Ranar da ya'ya da dukiya bazasu taba anfanar rai da komai ba,ranar da ya'ya zasu dinga gudun iyayensu kawaye suna gudun kawayen su masoya na gudun masoyan su wannan itace ranar Aminatu saidai ina mana fatan alkhairi Allah yasake haɗamu da alkhairi yasa damu da rahamar shi."

Dib naji ko muryar ta banji dukewa nayi kasa ina.
"inalillahi wa'inna ilahirraji'un,Allahumma ajirni fi masibati wa'aklifni khairan minha."

Komawa nayi wajen dutsen ko zan ganta amman wayam ba Husna! Haka naita kwalla mata kira ina kwalla,jinayi an jijjigani a firgice na tashi ina rafka salati Cankwai dasu Mairo nagani gefena suna tambayata lafiya nike kuka ina surutu banda sauke ajiyar zuciya ba abinda nikeyi ga uwar zufa data gama wanke ni,najima ahaka sannan nace.
"Anyi asuba.?"

"Eh tun dazun akayita."
Mikewa nayi nayo alwalla na tada sallah najima ina addu'oi kafin natashi daga bisa kwallin na kwanta kan gado abubuwan da Husna ta gaya mani su sukai mani tsaye arai duk da nasan mafarki ba gaskia bane amman na gilgiza yanzun ya tabbata dai har abada nida Asma'u sai yaumit tanadi ranar haka na wuni sukuku.

Har mukaje wajen aiki muka kwashi duwatsu muka kai wani fili haka muka gama kwashe su tas,sannan aka bamu kalaci mukaci kowa ya koma daki rana ta take haka mukaita hidimar mu ta duniya.

********
Dada da Anty Mubaraka sukaje wajen Mama dayake tunda aka fara sauraren karar da akeyi Mama tana gidan Ummi (Zainab) duk sanda za'aje Court saidai sutafi tare haka Mama keyi.
cikin bedroom din Ummi suka zauna Dada tace.

"Hadiza kin kara zuwa wajen Aminatu kuwa"?

"Aaa ba wanda yakara zuwa kinsan an hana ganinta amman ai jibi za'akoma zama Kotu."
"Allah Sarki Aminatu,Allah ya fiddata cikin halin da take ciki."
Ameen ya rabbi."
"Kuma ance shine zaman karshe ko.?"
"Eh shine wlh anata addu'a Allah dai yabayyana gaskia."
"Ameen Anty."
Cewar Anty Mubara

"Nima duk na gama shiga damuwa jinike wani iri abubuwa sun mani yawa musamman inna tuna da wannan case din,wai Anty Hafsat tazo nan kuwa.?"

"Hmm Mubaraka kenan aitinda case din Aminatu yafara tazo gidana taimani wulakanci magana bata kuma hadani da Anty Hafsat ba koda aka sake wannan zaman bata kara cemani komai ba,bare muyima juna fatan nasara a zaman nan."

"Kai duniya dai Hafsat bata taba gudun kayan kunya narasa irin tsanar da taima Aminatu kamar ba jininta ba anyaba saka hannun Hafsatu cikin wannan lamarin."?

"Haba Dada ki mata kyakkyawan zato mana ai tsanar da Anty kema Aminatu batakai haka ba."

"Kaiya kaiya Hadiza raba kanki da ɗan Adam kuma mutun mugun icce ne ko ya mutu sai andaure Allah dai ya kyauta."
"Ni abinda ke bani mamaki Dada yanda Anty Hafsat ke hudda da Hajia Mufida(Mami),ko kunya bataji kishiyar Yayar mijin kanwar ka,amman kalan dangi irin ta Anty yanda takeson Mufida ko yar uwarta bata so haka,lamarin Anty baiba."
Cewar Anty Mubaraka.

"Allah ya kyauta muddin na samu Hafsat da mugun wannan halin ba abinda zai hana ban tsine mata albarka ba,indai za'a hada baki da ita aima Aminatu wannan sharrin batada anfani a cikin ya'yana,yanda kikasan bani na haifeta Allah ya wadaran naka ya lalace."
"Ameen amman Dada kada kiyi yunkurin yimata baki dan Allah."?

Afusace Dada tace.

"Ke Hadiza ko kece kikaima Umaima haka wlh ba abinda zai hana kema ban tsinemaki ba dukka ya'yana daya kuke a wajena duk ina sonku ina kaunar ku,saidai wanda ya nuna ni ba uwar shiba ce,wannan kuma nima zan nuna ba ɗana bane koma wanene uwa daya uba daya dan bala'i amman jin zafi da bakin ciki yayi maku katutu a cikin zuciya nidai bamma yan uwana hakaba bare ace sakayya ce nike gani akan Hafsat,can ta kwashi jin zafinta bisa titi Allah ma shaidane."

"Allah ya kyauta yasa mufi karfin zukatanmu."
Cewar Mama.
Ameen suka amsa.

Ya Taufiq ne shida Tariq sai Mum da Ummi suka shigo dakinngaisawa sukayi dasu Dada,cikin mutuntawa Dada tace.

"Hussein dan albarka Allah yasa kagama da duniya lafiya yanda ka taimaki yar uwar ka Allah ya cika maka burin ka na alkhairi."

"Ameen Dada nagode."

"Bakai zakayi mana godiya ba mune da godiya koda Allah yasa Aminatu bata fito gidan Waƙafi ba, ai kayi mana halacci ka zama kaine masoyi na gaskia wanda kowane uwa da uba zasuso ka zama suruki kuma ɗa agaresu,ni kaina inaji araina kaine alkhairin Amina,inda rai da rabo ɗana kuma kasa aranka komi ke faruwa daku Lokacine Allah zai maku gata."
"Insha Allah,Allah yaimana mai kyau."
Ameen cewar Mum."

"Wai nikam Anty Maryam ina, Mufida tunda aka fara zaman nan sau biyu na ganta."

"Tana nan kinsan kafin a tashi take tafiyar ta,ba wani haduwa take da mutane ba yanzun kuma hutun nan da akaje ta tafi Kaduna ita da Wasila bansani ba kilan ta dawo ranar da za'ayi zaman karshe amman Alhaji yace mani zaizo ranar insha Allah."
"Allah yasa yaimana Jagoranci baki dayan mu."
Ameen."

Wayar Taufiq tahau ruru hakan yasa ya fita waje Tariq na maye mashi baya falo suka zauna.
"Ina zuwa yace."
Yana kashewa bada jimawa ba saiga Usama da Barr Bashir sun shigo cikin falorn da suke zaune gaisawa sukayi bayan Barr ya zauna.
Ruwa Tariq ya aje mashi cikin gora da cup,maida kallan shi yayi kansu yace.

"Major kasan kuwa na samu hujjojin dako ada ban tanaje suba wannan shari'ar fa sabanin hankali ce za'asha kunya aranar da aka gamata."
Cikin tashin hankali Taufiq yace.
"Bangane ba Allah yasa koma minene ban danganci Minal dita ba."

"Garetane Major saidai kilan ya zamar mata alkhairi amman case din nan da kake gani munafukai ne sukaima abin ɗaurin goro bayan son kasheta da sukai niya agidan Yari dan ma Allah ya takaita lamarin gaskia abin nan yabani mamaki da tsoro matuka."
Ya Taufiq zai magana kenan su Mum suka fito daga bedroom zuwa falor nan suka tadda Barrister zaune gaida shi sukayi suma zaman sukai dan sunsan koma minene ya shafi kowa daya jibinci Aminatu.

"Yanzun kana nufin na jikinta ne suka aikata wannan abun Barrister.?"
"Kwarai kuwa domin hujjar dana gani ajiya tafi wadda najima da tanada karfin gaske."

"Su wanene fadamana dan Allah Barrister."
"Aaaa aikina bai koyar dani hakan ba,kuyi hakuri lokaci zai sanar daku komai amman jiya da kyal nai bacci na gilgiza da lamarin nan gaskiar magana."

"Ikon Allah wannan lamari saidai addu'a domin ya shantake duk tunanin mai tunani.
Kwarai kuwa,a wannan case din Suspect dinmu suna da yawa ba mutun daya bane abun am mashi hadin guiwa ne kuma da sannu zakuga komai kudai ku dage da addu'a Allah ya wargaza duk wasu azallumai yaba gaskia nasara komai rashin karfin ikon ta."
"Ameen Barrister gaskia bansan yanda!zan misalta maka farin cikin da nikeji ba saidai ince Allah yasaka maka da mafificin alkhairi."

"Ameen Major kadaina gode mani ita gaskia haka take kuma Allah shine mai gaskia mudai namu shine kamantawa Allah yabamu nasara."
Ameen."

"Barrister kaje gun Aminatu kuwa.?"

"Aaa saboda ban bukatar komai agareta a halin yanzun duk wani bayani taimani shi akaran farko kuma na gamsu dashi,saidai abinda baka sani ba kwana ne kawai banyi gidan Yari duk wani motsin Amina da wanda zaije wajen ta tunda muka fara zaman nan ana sanar dani komai."

"Allah yaimaka jagoranci a cikin al'amuranka."
Cewar Taufiq.
"Ameen,zan koma akwai abinda nike sonyi kasan ina gama wannan shari'ar akwai wadda zan daura a jihar Lagos akwai bin ciken da nikeyi."
"Kana kokari Barr Bashir Allah yakara sutura."
"Ameen sai Allah yakaimu litini mun hadu a Court."
"Allah yakaimu lafiya.
Ameen."
Godiya sukai mashi sannan suka raka shi,haka kowa ya zauna sukuku bamai wata magana suna al'ajabi aransu, wannan kenan.

★★★★★★★★
Zaune nike nidasu Mairo suna cemani.
"Dago dan Allah idan zaki dawo kitaho mana da magi bamuda ko guda ɗaya."

Murmushi nayi nace.
"Hmm Mairo kenan waya gaya maki za'abarni inje siyan magi."
"Shikenan zamu bada asiya mana."
"Allah yasa,haka yakamata kuyi gaskia."

"Wai Dago ya shari'ar da akeyi Allah yasa kuyi nasara."
Cewar Cankwai
Amin ya rabbi."
"Karfe nawa zaku tafi.?"
"Bansani ba gaskia kilan zuwa tara ko goma."
"Allah yakaimu lafiya."

Kwantawa nayi hakanan nasamu kaina dajin faɗuwar gaba ina tunanin taya shari'ar zata kasance fatana Allah yatabbatar da gaskia ya wankeni daga zargi.
Badajimawa ba akazo daukata Atika sai Adam da Jafar da yan sanda muka tafi sai Court.

Mutane sukaita zuwa bamu jima da isowaba su Abban Ya Taufiq suka iso kowa ya hallara sosai aka taru abin har mamaki yake bani.

Haka su Anty Hafsat kusan tareda Ya Taufiq suka iso kowa ya shiga nima shigar dani akai as usual ina gaban Court tsaye.

Banfi minti goma da tsayuwa ba aka shigo da JJ kallan kallo mukema juna tsakanina da Junaid,shima Yan sanda suka kawo shi,Barristers duk sun hallara da sauran ma'aikatan Court.

Justice na Allah ne ya iso da tashi tawagar kowa ya mike yana zama kowa ya zauna.
Zare glass din idon shi Alqali yayi ya kalli Majesty yace.

"Muna bukatar jin case dinmu na yau kafin mu daura daga inda muka tsaya a zama na karshe insha Allah."

```Mikewa yayi yace.```



_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️


_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E45&46



_*COURT*_


"Muna bukatar jin case dinmu na yau kafin mu daura daga inda muka tsaya azama na karshe insha Allah."

```Mikewa yayi yace.

"Yau Litinin Kotu zataci gaba da sauraran karar da ake gabatarwa ta Amina Yusuf wadda ake zargin ta kashe kawarta Asma'u Abubakar bayan yanke mata hukunci da akai shekaru hudu da suka shude,ta daga kara tace sharrine akai mata,inda aka danganta karar ga Junaid Jamilu,wannan itace shari'ar mu ta yau.```
```Nagode ya mai girma mai shari'a."```

Kallan gefen hannun shi na dama da haggu Alqali yayi yace.
"Ko Lauyen mai kara yana kusa.?"

"Yes My Lord,am Barrister Bashir Fage."
Komawa yayi ya zauna.
"Lauyen wanda ake zargi ya iso.?"
"Yes My Lord am Barrister Tukur Jakara."

"Barrister Bashir bissimillah."
Mikewa Barrister yayi ya ɗan russunar da kanshu yai ma Alqali godiya ya maida kallan shi akan JJ yace.

"Ya girma mai shari'a ina neman alfarma ga wannan Kotu mai dinbin daraja tabani damar ganawa da wanda ake zargi Junaid Jamilu."
"Go ahead Barrister Bashir."
"Nagode,Junaid bissimillah."
Shiga yayi wajen tambaya ya tsaya,a hankali Barrister ke taku harya isa gaban Dr JJ yace.

"Aikin haɗaka kukayi Junaid kaida suwaye kukai aikin nan kuma minene dalilin ku na aikata wannan laifin.?"

"Objection My Lord bai kamata abokin aikina na yima wanda ake zargi kalar wannan tambayr kai tsaye ba wannan cin fuskane."
"Korafi bai karbu ba Barr Tukur.
Cigaba da aikinka Barrister."

"Thank you My Lord,kai muke sauraro Junaid.?"

"Aaa Barrister nifa ba wani hadin guiwa da mukayi wajen wannan aikin kawai dai kana son lakaba mani ne,taya za'ai har in hadaka da wasu."
"Wannan shike nuna kai kadai kayi aikin ka kenan."?
"Eh aaa am bawai aiki naiba nidai kawai abinda nasani nabi Amina abinda nasani kenan Barrister."
"To Junaid ko zaka iya gayama Kotu wane Hotel ne kaje kuma wane room number ne dakin da akai wannan kisan.?"

Ɗan shiru yayi sai kuma yace.
"Z.....Hotel ne room 101 shine dakin da Amina ta kashe Asma'u ranar alhamis."

*Note:- Kafin aci gaba da fadin yanda aka kare wannan shari'ar zanso in gaya maku zakuga ba'afadi sunan HOTEL din da abin yafaru ba,naki fada saboda twani dalilin, kuma rashin fadar sunan Hotel bazai rage komai a cikin wannan labarin ba hakama Date din da akai shari'ar.*
*Abin bukata darasin dake cikin labarin shine abin dubawa,sorry to say bansan taya zan maku bayani ba,amman nasan zaku gane manufata nagode,muje zuwa🥰*

"Lokacin daka shigo room din kana sanye da face mark a fuskar ka,Mariganya na zaune gefen gado taji ka rufo kofar dakin tareda cire marufin fuskar ka mi kace mata,a wannan ranar."?

A firgice yafara yan kame kame yana sosa keya yahauyi dan danan jibi ya gama wanke shi sai raba ido yake yakai minti ukku yagaza furta komai sai inƙina da yake faman yi,ni abin mamaki yafara bani da tsoro.

"Junaid Jamil kai muke sauraro karfa kamanta aganban Court kake."

"Am am ai Barr am nidai batace mani komai,ohh ina nufin banje wajenta ba saida Amina ta soka mata wuka sannan muka shigo da Securities."

"Ayyah Junaid kace baka ce mata komai ba kuma kace saida Amina ta soka mata wuka sannan ka shiga to a ciki wane kake so Court ta dauka."?

"Objection My Lord binciken da abokin aikina yakeyi harda gayya a ciki so yake ya ƙure wanda ake zargi harya fara daukar laifin da bai aikataba ya kamata ya kiyaye hakan."

"Duk cikin aikine Barrister kuma wanda ake tambaya ba yaro bane yasan right dinsa,Barrister Bashir cigaba da aikin ka."
"Thank you My Lord.
Junaid wane zamu kama a ciki."?

"Eh nace sadda Amina ta kasheta sannan na shiga."

Murmushi Barr Bashir yayi yace.

"Da kyau Junaid,amman wanene Gali.?"
Ƙwalalo idanu JJ yayi woje with shock harda tari yake sosai yake tari kamar zau siƙe sannan yace.
"Bansan sunan ba sai abakin ka naji shi.?"
"Really."?
"Eh bansan shiba."

Ɗage rigar jikin shi yake yana fiffita kamar ba fankoki a cikin Hall din tsabar razana.

Barr Bashir yace.
"Junaid dakace kana bibiyar Aminatu dan bata da gaskia shin akwai abin rashin gaskia daka ta6a kamata dashi harka gano zata kashe kawarta.?"

"Eh eh Barrister shine dalilin dayasa nike bibiyarta."

"Ko zaka gabatarma Kotu da shaidarka."?
"Eh gata a wayata Barrister."

Miko mashi wayar shi Yan sanda sukayi ya buɗe aka haɗata da Projector kasancewar ta Video ne sai ga wani mutun ya bayyana yana nuna mani wayar shi,saidai ba sound a jikin Video nima na duƙo da kaina ina kallan wayar mutumin yadan kare fuskar shi kadan da himari daga nan nayi gaba nan Videon ya kare.

Kaina ya kulle take lamarin ya dawo mani sabo tabbas anyi hakan na tuna ranar a cikin kwakwalwata,maganar Barrister tadawo dani duniyar tunani yace.

"Good Evidence saidai cikas ɗaya ba magana a jikin Videon taya zamusan mi tace bare ya zama hujja agareka."?

"Barrister ainaga ga Aminatu kowa ya ganta bare ace sharri nai mata."
A zafafe JJ ya ida maganar.

"Eh kwarai bakai mata sharri ba Junaid nima nagani amman waya dauketa wannan Videon? sannan kuma wanene wannan mutumin? mi yake ce mata?sannan taya kasamu wannan Videon? Wannan su ake kira da Hujja Junaid.!"

"Objection My Lord wannan tambayar ƙoƙonto Barr Bashir keson yima Junaid hakan bai dace ba."

"Barrister Tukur,Kotu tana bukatar jin cikakken waɗannan amsoshin daga bakin Junaid,kai Kotu ke saurare Junaidu."

"Dafarko dai ni dakaina na dauketa wannan Videon"
"Ko miyasa.?"
Yai mashi magana yana murmushi a fuskar shi.

"Saboda ban aminta da itaba shiyasa,sannan kuma wannan mutumin bansan shiba gaskia,kuma bansan mi yake ce mataba."

Murmushi Barrister Bashir yasakeyi yace.

"Malan Junaid taya wannan zai zama shaida bayan bakasan mi Aminatu keyi wajen shiba sannan uwa uba bakasan alakarshi da itaba,dama ace munji mi suke cewa da yazama Hujja a garemu taya zamu anshi hakan a matsayin shaida."?

"Ai Barrister koda bakuji Sound ba ai kunga Aminatu da wani kuma naga ita din tasan mi tace mashi aiko.?"
Ya ida maganar afusace kamar zai bugi Barrister Bashir.

"Kwarai Junaid ka mantar dani abinda na shafa'a zaka iya zama kafin insake waiwayar ka."

Komawa yayi ya zauna yana sharce jibin dake gangaro mashi a fuskar shi.
Shiko Barrister Bashir cewa yayi.

"Ya maigirma mai Shari'a inason Kotu tabani dama ingana da Aminatu Yusuf."
"Ambaka dama Barrister."
shiga nayi na tsaya takowa Barrister Bashir yayi gabana yana kallona yace.

"Waye wancan mutumin da aka nuna ku atare Amina."?
Ya ida maganar yana kallona.

"Bansan shiba Barrister ranar da Junaid yai mani wannan Videon lokacin nazo zan wuce sai wani mutun yasha gabana na rabe ta gefen shi zan wuce ya kuma bina daga karshe sake shan gabana yayi yace.

"Dan Allah baiwar Allah ki tsaya tambaya ke gareni."
Jin abinda ya hadani dashi saina tsaya.
Shine ya fiddo waya ya nuna mani hoton wata yarinya yace,mani.
"Dan Allah kinsan wannan fuskar."?

Dubawa nayi na girgiza kai nace bansan taba gaskia.
Zan tafi yasake matsoni da wayar yace.

"Ance yar nan uguwar ce shiyasa na tambayeki."

Aini ba unguwarmu bace malam ka tambayi wani gaskia bansan taba.

Okay yace mani da haka natafi wannan shi ne abinda nasani Barrister."

Jinjina kai Barr Bashir yayi yace.
"Taya zaki tabbtar ma Kotu da hakan kuma ya kikeson muyarda dake Amina."?

"Barrister daga wannan bayanin basan taya zan gaya maka ba kuma Allah ne shaidana."

Jinjina kai yayi yace.
"Amman ke ina zaki a lokacin miya kawoki unguwar."?

"Ranar Ya Mutallib ya daukoni a cikin motar shi,shine nace mashi ya ajeni zan biya gidan Anty Zaliha zan bata sako shine ya ajeni dayake ta baya muka biyo kuma Mota batabi ta wajen shine na idasa shi kuma ya tafi."

"Okay ko zamu iya ganin Abdulmutallib din."?
"Eh Barr yana nan."
Juyawa yayi yace.

"Ya kai girma mai Shari'a
Kotu na bukatar gani Mutallib."

Tasowa yayi cikin shaddar shi Gray ya iso wajen Shari'a yace.

"Kaji abinda Aminatu tace Kotu na bukatar taji gaskiar lamari saidai kafin hakan minene alakar ka da Aminatu?"

"Anyi hakan ni dakaina nakwota unguwar kofar Waika na ajeta tace zataje gidan Anty Zaliha saboda ina sauri shiyasa ban shiga ba,sannan Aminatu budurwata ce wadda nike fatan aura insha Allah."

Kallan junan mu mukayi nida Ya Taufiq wanda duk wani motsin da zanyi yana kallona nima haka,jin abinda Mutallib yace dandanan naga damuwa bisa fuskar shi,fuskew akwai nayi,hatta Barrister Bashir saida yai mamaki jin kalaman Ya Mutallib saboda kusan kowa yasan alaka da Ya Taufiq.

Gyaran murya Barr Bashir yayi yace.
"Wacece Anty Zaliha kataba zuwa gidan tata.?"

"Eh kanwar Ummi ce,kuma saboda na makara a office ina sauri
shiyasa."

"Shikenan Mutallib,amman
kasan Asma'u.?"

"Eh nasan labarin ta sosai domin tana yawan kewarta kaunatar ta hanyar bamu labarin ta,inhar zaka tambayi tarihin Aminatu to zaka samu kashi biyu cikin ukku duk akwai labarin Asma'u hakan yasa nasanta."
Masha Allah Mutallib zaka iya tafiyar ka."
Godiya nike Barrister."

Maida kallan shi ga Alqali yayi yace.

"Ya maigirma mai Shari'a zan dan dakata anan kafin in sake ida gabatar da shaiduna na gaba,nagode My Lord."

Angaisheka Barrister,kafin mutai hutun takaitaccen lokaci Court zataso Barrister Tukur ya fito domin bada tashi shaidar bissimillah Barrister."

Mikewa yayi yace.

"Ya maigirma mai Shari'a zanso Kotu tabani dama zan gana da mai ƙara Aminatu Yusuf."
"Anbaka dama Barrister Tukur."

Daman ban kaida fita wajen tambayar ba cigaba dacewa yayi.

"Kince Mutallib yakaiki Kofar Waika gidan Anty Zaliha kikaje kintabbar can kikaje?"

Shiru nayi dan bansan mi zance ba amman gaskia ɗayace kuma karya fure take bata ya'ya hakan yasa nace.

"Nacema Ya Mutallib zanje unguwa yakaini saidai a zahirin gaskia bawai Kofar Waika kawai zanje ba,asalima inada dangi kuma bansan su ganni saboda....

Karab ya katseni yace. "kince bakison su ganki saboda rashin gaskiar ki komi kike nufi."?

"Objection My Lord dakatar da mai fadar gaskia agaban Court ba tareda anji yakai karshen maganar shiba wannan kamar descouraging din mai kara ne,inafatan abokin aikina zai gyara hakan gaba."
"Barrister Tukur ka kiyaye gaba,Aminatu ida maganar ki."

Nagode My Lord."

"Inada dangi a unguwar kuma bansan suganni saboda zasu iya cema mahaifina anganni ina kano kuma lokacin ina tsoron mahaifina bansan ya ganni,ko Asma'u abinda yasa nabari tasan ina gari saboda inason mu samu masalaha ta yanda zan tunkari mahaifina idan Abban Ya Mutallib zai maidani wajen mahaifina hakan yasa nace zanje kofar waika harya kawoni amman a zahiri banan nazo ba,zagayewa nayi zanje gidan Asma'u shine na kirata waya tace taimana booking mu haɗu hotel,wannan shine ainahin abinda yafaru wannan ranar."

"Amman miyasa kike boye boye bakison kowa yasan gidan Asma'u musamman wadanda suka tsinceki."?

"Gaskia kam Barrister na boye masu ne saboda nasan muddin suka haɗu da Asma'u definately zatasan yanda zatayi cikin kwana ukku ko biyu ta hadasu da Baba ni kuma ina ganin har lokacin makamar mahaifina bai yafe mani ba sannan kuma bansan Baba yace nafara soyayya bayan kuma da zancen auren Sadiq akaina shiyasa nike dojing.
hardai mukayi hadaka zuwa Hotel din da wannan lamarin yafaru."

Shiru yayi yana jinjina kai sannan yace.

"Lamarin ki kamar marar gaskia Aminatu mi zaisa kita guje guje dan karki hadu da mutane kodai so kike saikin gama kashe Asma'u sannan zaki bayyana kanki a gaban kowa."

Raina ya baci kwarai da gaske wannan kalma na tabamani zuciya cewa nayi.
"Yanda kace Barrister hakane.?"
"Amina amsa zakiba Kotu bawai gatse ba."
Nima kallan shi nayi nace.

"Duk wani abu dazan gaya maka Barrister Tukur bayan wannan wanda nagaya maka tabbas karya zan maka,ni kuma da dai in maka karya dan kare kaina kwara na dawwama a halin da nike ciki wannan shine abinda nasani."

Wani kallan tsana yake watsa mani,nima shi nike kallo ido cikin ido sauke nashi yayi ya juya mani baya ya kalli Alqali yace.

"Ya mai girma mai shari'a zan......


_Yar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Pls
❣️


_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_




Please Login or Register in order to submit comment