Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na ganin gidan Yari nan ne Final Destination na Prisonors saidai shima din akwai kalubale na rayuwa musamman wajen abokan zaman ka dole kaima shugaban gida biyayya wahalar yau daban ta gobe daban.

***********

"Alhaji Yusuf nifa aganina bai kamata azubama wannan case dinnan idonu ba itadai Asma'u ga ta yanda Allah ta kasance ta rigamu gidan gaskia sannan kowa yanada yakini ba Aminatu bace ta kashe taba bai kamata munaji muna gani ba ta dawwa Prison ba."

"Bayan duniya ta shaida Mamana itace ta kashe Asma'u taya kake tunani a matsayina na mahaifin ta zan fito ingayama duniya hukuncin da akaima ya'ta ban lamunta dashi ba tayaya hakan zai faru.?"

"Saboda ta amsa laifin ta saboda bata da wata mafita da yawuce ta amshi Qaddarar ta,a lokacin ɗimuwa tashin hankali da tarin fargaba su suka taka rawa wajen karbar laifin daba nataba,a ganinta data tarayu ko ta mutu duk daya suke a wajen ta su suka taka rawa a zuciyar Aminatu harta amsa laifin daba nata ba,bataki ba tabi Asma'u a inda tatafiba a ganinta shine kwanciyar hankali awajenta."

"Hassan kana ganin akwai ranar da Mamana zata sake rayuwa a cikin mu.?"

"Indai zamuƙi aminta da shari'ar da aka zartar mata ba,zata dawo ba abinda za'afasa."
"tayaya kuma ta ina hukumafa ba abin wasa bace."

"A daukaka kara gaba kotun koli shikenan."

"Ita wake shaidar ta bayan wadda aka kashe bata raye balle ta fadi gaskia ita kuma wannan ba wanda zata kawo matsayin shaida dan Allah kawai mu dauki hakuri akan lamarin nan Haka Allah Yaso."

Yayana nifa inaganin....

"Yanda yace haka za'ayi Baban Bilkisu mu dauki wannan Jarabtar in mukacita zamuci riba ni aganina."
Cewar Mamar Amina.

"Shikenan hakan za'ayi Allah yabamu dangana akan wannan Jarabawar Allah yasa mucita kuma Allah ya toni asirin duk masu saka hannu akisan Asma'u."
Ameen Hassan addu'ar kenan."


_*JAIL/PRISON/GIDAN YARI*_


Amai niketa kwararawa kamar yan cikina zasu fito waje haka nike sheka uban amai ga ciwon ciki ina fama dashi marar dadi zan iya cewa bantaba ciwon ciki irin shiba nasan dai ba priod dina bane bare ince a iya ilimin da Allah yabani na likita sai nasa shi a gurbataccen ruwa ne ke kawo hakan.

Da kyal Allah ya taimakeni aman ya tsaya Nusaiba wadda ta koma mani kamar tip da taya itace ta kamoni zuwa inuwa sannun banda arzikin shi musamman wajen su Cankwai su aganin su, tsabagen tuggune kesa inlafe ince ban lafiya.


Kwantawa nayi kasa sanyin wajen na buguna ina dan rufe idona bansan sanda bacci yai awan gaba dani ba.

Tun biyu nike bacci wajen sai hudu Nysaiba ta tadani tana bani wani magani wai insha ansa nayi naga Saftrinne nidai nasan bashi bane maganin ciwon dake damuna ba tunda ba mura nike ba,amman saina ansa kamar nasha na watsa shi a rigata nasha ruwa ina dan ya mutsa fuska kadan,sannu tai mani na amsa da yawwa.

Bayan kwana biyu,ina zaune bisa gadona wanda shine karon farko dana zauna kanshi su Cankwai sun hanani har wani dadi nikeji duk da kasancewar shi gadon karfe amman sai naji kamar ina bisa royal kodan kasan da nike yawan kwana shiyasa nasamu kaina dajin hakan

Dan gishindi dawa nayi ina timing lokaci kafin su dawo gun aiki na runtsa bacci ya fisgeni sosai nike bacci tareda mafarkar iri iri marassa kan gado a ciki kuwa harda mafarkin Ya Taufiq nayi wai gashi nan ana daura mana aure Asma'u nata murna tanajin dadi tana cewa kin cika mani burina kawata shiko saijin dadi yake yana smile afuskar shi saidai niko Murmushi babu a fuskata kana ganina kasan ina cikin matsananciyar damuwa.

```Kisaki ranki Minal kiyi rayuwarki kamar kowa kidaina damuwa komai zai faru Allah ya hukunta namu shine mubi abinda yake wajibi agaremu kisa aranki Haka Allah Yaso,ina maki fatan alkhairi```


Hannu nike mikama Husna ina tataho gareni tana kara yimani nisa sosai harta bacema ganina,kuka nasaki mai karfin gaske wanda hakan ta kasance a zahiri ina kwalla kara naji an watsa mani ruwa a jikina a kidime na duro bisa gadon jikina na rawa sosai zuciya na halbawa da karfi,hakurin da zanfara ba su Salame naji sun rufeni da duka tako ina bansan na fara ihuba daman ga mafarkin da nayi ya dameni ainun.

Da sauri gandirobar data maidosu ta kulle dakin kasancewar yamma tayi bamu kara fita sai kuma gobe,ta dawo da sauri ta bude kofar tafara yi masu fada.

"Ke Cankwai daganin wannan fitsarancin ba uban da zaisa a aikata shi sai ke waike miyasa kin addabi kowa agidan nan.?"

"Oh ashe na dameku ku sallameni mana sai kuyi yanda kukeso dagaku har Prisonors dinku matsawar Cankwai na rayuwa a cikin gidan Yarin Kurmawa bazata fasa ba mata kashi ba dole ai mata biyayya inba hakaba jiki magayi."

"Ke Cankwai wai miyasa baki da kunya ni kikema fitsara nayi kama da tsararki.?"

"Ai kikai kama da tsarar Cankwai ki gode Allah,ke Atika bari kiji ingaya maki kema kikace zaki zafafa zansa suyi maki dan karan dukan tsiya ko in illataki tunda nasan bawai fita zanba a cikin gidan nan ba,kingako koda na kasheki,na kashe banza karshen ta dai asake yankeman life prison ko ace aje akasheni daman ai karshena kenan kingako kwara kima Cankwai Magajiyar Karuwan Mai Mujiya biyayya inba hakanan ba....kinsan sauran."
ta ida maganar tana jan yatsa a wuyanta alamun zata yankata.

Dan dole Gandirobar ta tafi badan taso ba tabarni dasu sukace in tsane ruwan katifar ko susa na lasheta.

Haka na kama gogeta da suturar jikina na tabbata Allah kadai yasan yawan mutanen da suka kwanta akanta gashi dasu nike sallah ba yanda na iya haka nagama naci gaba dayima Cankwai dannar jiki daketa faman tsamin dauɗa tsabar datti ga kyankyami ya isheni.

_Yar Mutan Kankia ce❣_

Share
Pls
❣️

_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E5&6




Ina zaune cikin ma'aikatan gidan tazo kirana binta nayi zuwa wani makimancin office.
"Ranka shidade gani."
Amina Yusuf Caranci ko.?"
Eh nice."

"Daman visitor ne yazo,ganin ki Atika kaita wajen ganawa da baki."

Hakanan naji gabana ya faɗi dan fatana Allah yasa kada wanda yazo inda nike amanta dani baki daya.
Bin bayan ta nayi har zuwa wajen da aka tanada dan ganawa da baki.

Sunkuye kanshi yake kasa kana ganin shi zakasan yana cikin damuwa har yar rama yayi sai kuma yadanyi duhu kadan jikina a mace na isa wajen shi,a tsaye nike daga ciki wani wall karama data rabamu mutun zai iya daura hannun shi bisan karamar katangar jiki na saka hannuwana shima haka kallan juna mukahauyi dukkan mu ba wanda yai kokarin yima dan uwan shi Murmushi saboda kowa da abinda yakeji a cikin zuciyar shi,nice na nemo duk wata Jarumtata nai karfin yin magana

"Ya Mutallib barka da yamma."
Shiru yayi sai aikin kallona yake yace.
"Yawwa Amnah."
Da haka yake kirana.
"Ya kadaici ina missing dinki Amnata Allah ya kubutar mani dake cikin wannan ifila'in da kika tsinci kanki insha Allah sai kinbar wannan gidan bazamu jure ganin ki hakaba Allah ya fiddake cikin gaggawa.

Samun kaina nayi da kallan kasa dan banaji zan iya cewa ameen a halin da nike ciki.

"Ya Ummi da Salima.?"
"Lafiya lau suna gaidaki.
Daman yan kayane nace bari inkawo maki kala ukku ne sai,yan provision wa'anda kuke using sannan mi kike bukata.?"

Girgiza kaina nayi,alamaun bakomai nace.
"nagode Allah yasaka da alkhairi yakara budi."
"Hmmm Amna kidaina yimin godiya da ace zan iya yimiki gata tabbas dana rabaki da wannan wajen saidai bawa bai gujewa duk wata Jarabawa da Allah zaiyi mashi kici gaba da hakuri insha Allah sai Allah yakawo silar da zaisa ki kubuta a cikin gidan nan kodan kyakkyawar zuciyar ki,kidaina damuwa kuma insha Allah nima zan iya kokarina Amna kisa aranki Haka Allah Yaso."

"Insha Allah Ya Mutallib duk yanda Allah yatsara shine daidai naji dadin wannan ziyarar daka kawo mani."

Jinjina kai yayi Officer Atika dake gefen mu tace lokaci yayi,badan yasoba yaiman salama yatafi ni kuma nakoma cikin Office din aka duba kayan daya kawo mani,kayane kala ukku sai mai magi bani akayi na koma ciki.

Saidai tunkan in isa dakin mu nafarajin tsoro ya kamani tsorona daya kada Magajiya ta kwace mani sakona dan naga haka taima wata Nabila.

Aiko ina isa na iskesu zaune bakin wata bishiya suna firar su marar kan gado sai shewa sukeyi duniya tai masu dadi sosai baka taba cewa a Prisons suke tsabar sun maida shi gida sun saba.

"Dago zonan shugaba na kiranki."
Tafiya nayi jiki a mace ina zuwa na duka ledar hannuna suka warce agabana suka zazzageta suna wullo mani kayana ajiki suna kwance dayar ledar suka saki shewa.

"Ahaiye ashe dai zamuja kaya Mairo rike mana wannan munyi wata munacin abinci mai dadi."

A"ngam Oga Cankwai da girman kujerar ki babu wata Sarauniya a gidan nan saike inda mai Ja da wannan batu kowaye ta fito muganta,wlh sai Magajiya shugbar mai Mujiya zama dake dole biyayya tazama tilas."

"Wannan haka yake."
Inje Salame.
"Ke zaki iya tafiya aje ayi wanki daman kinfara bashi."
Toh nace har zan tafi suka kara cewa.
"zo nan."
Dukawa na sakayi a gaban Cankwai.
"Salame gaya mata dokar Magajiya."
"Bakiyima Oga Cankwai godiya ba."
"Nagode Allah ya kara girma."
Ameen munafuka."

Tafiya nayi raina na kuna sosai na rasa taya zan fara kwatarma kaina Yanci wajen abokan zamana sun matsa mani gashi zaman bamai karewa bane ya zama dole innemawa kaina mafita tunkan dare yai mani.

Yanzun inaji ina gani sun anshe mani kayana dan cinzalin da mugunta irin nasu dare yayi su hanani kwana gadona saidai kasa nice dibar ruwan su,nice komai nasu aikinma indasu akasa sani subar mani shi ni kadai zanyi anya zan iya jurar wannan wahalar kuwa?haka naita sake sake nikadai narasa mike mani dadi a duniya.


Mama Pov.

"Alhaji yaushe za'akaima Aminatu ziyara.?"
Kallan Baba yayi kamar bazai maganaba sai kuma yace.
"Hmm ba rana Khadija dan banjin zan iya zuwa wajen ta."

"Amman kasan dai hausawa nacewa barin kashi a ciki bai maganin yunwa daurewa kawai zakayi muje muganta kilan ta samu sassaucin abinda takeji a ranta."

"Ba wani sassaucin da zata samu saidai mukara jefata cikin taraddadin abinda yafaru da ita na rayuwa,kawai muci gaba da yimata addu'a inda rabo sai kiga Allah ya wanke Aminatu a idon duniya wannan shine kawai."

"Baban Ahmad katsaya kasaurareni ita rayuwa ba aimata haka kaga dai irin wadan nan kurakuren sune mukaita aikatawa tsakanin ya'yan mu muka dage sai mun raba Taufiq da Aminatu mun manta Allah shikadai yabarma kanshi ikon sanin abinda gobe zatayi gashi shi Hussein an rasa shi, ita kuma garin ta gujewa bacin ranka ta gudu wanda har yanzun bamusan dalilinta na zuwa kano ba taje ta fadawa tsautsayi har wannan abun ya faru yanzun kanason kace zamuyi burus da lamuranta mi kakeson yar sauran rayuwar data rage mata zataji tace tanada iyaye a raye bayan mun gaza bata duk wata kulawa data dace da ita a matsayin mu na iyayen ta."

"Khadijatu kiyi hakuri bazan iya zuwa ganin Aminatu ba gaskia."
Sabodame.?"

"Dolen dole sai kinji dalilina bazan jeba shine dalilina ko ana dolene?"
Yai maganar a zafafe.
"Shikenan ni zanje in gano ya'ta ina bukatar sakata a idona."

"Wannan kuma badai da yawuna ba idan kuma zakije ga fili ga maidoki."

Tashi yai yabar wajen,itako Mama tsabar takaici batasan tafara kwallan bakin ciki ba,ganin baudewar Mijinta sai Allah.
*********
Bayan sati biyu,tunda aka kai Aminatu Prison kowa yazo yaima Mama jaje banda Anty Hafsat,itama yaudin bukatar tace ta kawota wajen kanwar tata,gaisawa sukayi ɗan shiru ne ya biyo baya kowa da abunda yake sakawa aran shi.

"wai ina yarinyar nan ko tatafi aikin ne,likita bokar turai."
Sakake Mama tayi tana kallan ta gwanin ban mamaki kamar andasata

"Ke matsalata dake kenan Khadija sai kima mutun ƙuri gaki dana gani masha Allah haba."

"Hmmm Anty Hafsat kenan ai abun kallon kikayi agareni da naji kina tambayar Aminatu bayan duniya tagama shaidawa Aminatu na gidan Yari."


Af haka fane wlh mantawa nike da zancen nan Allah kyauta ai anrage iri saidai muce sai mun iso tinda ance saidai gawarta kinga ai batada mararraba da gawa."
ta ida maganar ko ajikinta.

"Wa'iyazubillah yanzun Aminatu gudan jinina itace mugun iri? Lallai kiyayyarki ga Aminatu bata wasa bace ikon Allah.!
Dan kin manta da ita a rayuwar ki bai damuna domin daman kedin ba dolenta bace,sannan da kike maganar gawa sai kiga wanda yake zaune gida tubus mai gata mutuwa ta dauke shi tabar wanda ke cikin kunci wlh ko yau aka maido mani gawar Aminatu ban taba bakin ciki dan nasan Allahn daya bani ita yafini kaunar ta,kuma shikeyin yanda yaso a lokacin dayaga dama wannan kuma sai wahidir qahhar."

"Danayi magana saikice bansan Amina na tsaneta naji banson ta ɗin sai me? Kuma ki gayamani a wannan marrar da muke ciki waye zai sota bayan abinda ta aikata ta kashe kawarta aminiya haba kufa mutane ba'a iya maku.

"Eh naji kada kowa yaso Aminatu inda Allahn daya halicceta na sonta,iyayenta na mata addu'a da mutanen kirki saimi dan kowa yakita."

"Kedai akeji Khadija duniya tayi tir da irin halayen Aminatu tadaici amana Allah yakyauta,ni tashi zakiyi ki dauko mani kudi akwai abinda zanyi dasu."

Wani kallan tsana Mama ta bankama ta sosai jitake kamar tai mata dukan tsiya dan takara jin tsanar Yayar tata.

Mikewa Mama tayi taje daki ta dauko kudi zasukai dubu Hamsin ta nunama Anty Hafsat tace.

"Gasu amman sai inkina da karfi zaki kwata taso ki amsa."
Zaune tayi tana kallan ta,cikeda mamaki tace.

"Bangane in kwataba rance nace ba kyautaba malama."
"Na karfine ban badawa Hafsat in uwatace ke ki tsine mani ban badawa angaya maki ke nike tarawa dukiyar?"

"Nafahimci yau rashin arziki kikeji Khadija mudai bamu fasa yadawa muce Amina ita ta kashe Asma'u ai da bakin tama tafadi haka baremu yan tayawa."

"Nidai kike gayama haka ko Anty Hafsat kiri kiri kin nuna tsanarki ga Aminatu ko? Ni kullin burina in rufa maki asiri ke kuwa burin ki,kitona nawa asirin bakomai kiyi yanda kikeso komai lokacine watarana sai labari."

"Aikam gashi munatayi tunda muna bada labarin irin butulci na dan adam yarki tayi abun kunya gantalalla ai kadan tagani indai mune."

"Ku suwa banganeba.?"
"Hmm da sannu zaki gane,mtsw andaiji kunya in ansanta Allah kyauta."

Tafiya tayi tabar Mama cikeda al'ajabi.
Ahmad ne ya fito falorn ya zauna kallo daya yaima mahaifiyar tashi yaga tsantsar damuwar ta.
"Akan abubuwan da Anty Hafsat tafada maki kike damuwa kibar komai hannun Allah shi zai mana magani Mama saidai ina zargin sa hannun Anty Hafsat a cikin wannan lamarin Mama gaskia......

"Yiman shiru Ahmad ko in sabamaka.!"
Tayi maganar tana mikewa jikinta har rawa yake tsabar bacin rai.
"Kiyi hakuri Mama bazan kuma."

"Karka kuskura kajefi Yayata da kalmar zargi duk kiyayyar da takema Aminatu batakai nan ba nayi imani da Allah bazata taba jefa Aminatu cikin wannan ukubar ba,jini ɗayafa ba abin wasa bane haba Ahmad."

"Hakane nayi kusukure kiyi hakuri bazan kara makamanciyar wannan maganar ba."
Itadai gaba tayi abunta tana jujjuya maganar ɗan nata aranta duk saita siga damuwa.


*Two Days Later*

Babane ya shigo cikin gidan ko sallama babu idanun shi sunyi jajir kamar rushi ya buga uban tagumi, yai zurfi a tunani.

Mama da Hauwa'u suka fito daga bedroom suka ganshi yai shiru ga kwalla nata sauka bisa kuncin shi,dan danan Mama takara shiga matsananciyar damuwa.

Hauwa'u da yanzun zatakai shekara goma ta rugo wajen mahaifin nata ta fada mashi itama kukan take tana tambayar abinda akai mashi.
"Babanmu kadaina kuka mi akai maka kake kwalla dan Allah kadaina."

Itama kukan take tana share mashi hawayen idanun ta.
Kamar karamin Yaro haka Baba ya hade kanshi dana Jidda yana kuka sosai mai sauti.

Ahmad da shigowar shi kenan daga shi har Mama sun gaza motsin komai,suma zubar kwallan suke saida suka bari ya lafa sannan suka karaso inda yake suka zauna.

"Alhaji dan Allah kadauki Qaddarar nan kadaina wannan damuwar da kake ciki Allah na taredamu."
Baba kayi hakuri dan Allah."
"Kayya Khadija nagaza sukuni a cikin al'umma banda yadamani maganganu a garin nan ba abinda akeyi yanzun abin haushi ina masallaci daga nayi tambaya akan hukunci dake cikin yin sharri da zamba cikin aminci.

Budar bakin Alhaji Isuhu sai ceman yayi ai mai tambayar yafi kowa sanin amsar domin ba wanda yakaimu zamba cikin aminci an bamu amana munci ai kadan nagani!
Wannan maganar tafi kowace bata mani rai kuma bazan taba mantawa da itaba har in mutu abainar nasi,ya wulakantani,shiyasa kika na dawo gida ko amsar Malam ban tsaya jiba nashiga ukkuna Khadija wannan wace irin Jarabawa ce ko ina yada mani kananun maganganu akeyi."

"Kayi hakuri dole saimun daure da surutun mutane,Aminatu shiga ƙunci kawai tafimu da fargaba amman mu mun fita kwasar bakin ciki."

"Hakane Mama Allah ya kyauta gaba ya saka mana akan duk wani sharri da ake bimmu dashi."
"Ameen ya rabbi."

"Ahmad kada kamanta Mamana da kanta ta amsa laifin nan a gaban Court mu mike garemu saidai mudauki dangana."
Ranar haka kowa ya wuni jigum ba dadi aran su,wannan kenan.

_Yar Mutan Kankia ce❣️_
Share
Pls
❣️

_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E7&8



One Month Later


Ina zaune bisa wani dutse dake kusa da wata bishiya nida Nusaiba zuwa yanzun kam tashigo jikina sosai dan kaf gidan Yarin da ita kadai nasaki jikina da ita muna gaisawa.

Muna zaune kowa yayi shiru bamai magana a cikin mu.
Na dauki yar karamar tsakuwa agabana ina dan jefawa nesa damu kaɗan nayima waje daya ƙuri irin na zurfafa a tunani sosai,naji Nusaiba na tabani a firgice nadawo duniyar tunanin dana wulla kallanta nayi nace.

"Mikikace.?"
Cikeda mamaki take kallona tace.
"Wato duk abinda nace baki jina kenan ina baki labarin ya'yana da mijinane."

"Ayyah banjiba wlh shiyasa inajinki."

"Kinganni nan yau kimamin shekarata biyar agidan nan saura shekara biyu infita,kullin sai.nayi kuka idan na tuna ya'yana tsorona ɗaya kadai kishiya ta illata mani yarana."

ta ida maganar araunane.
"Haba keko Hauwa'u taya zata illatasu ina Baban su,bai nan?"

"Yana nan matsalar yana zuwa aiki,ita kumqla matar shi lalata take da mata nataba ganinta da ya'ta shiyasa nai mata bugun mutuwa shinefa danginta sukace bazasu yarda ba kuma sunada kudi sosai asalin zuwana kenan Prison lakaba mani sharru sukayi, cewa sukayi bugun danai mata na taba mata mahaifa bazata iya haihuwa ba kinji dalilin zuwana gidan Yari."

"Ikon Allah sai kallo kowa dai duniya da Qaddarar dake kawo shi wannan gidan ke kuma taki Qaddarar kenan Allah yasa kici wannan Jarabawar kuma Allah ya tsare maki ya'yan ki daga kaidin ta,amman miyasa bakikai su wajen iyayen kiba.?"
Nai mata maganar ina mai jin tausayinta araina.

"Amina kenan mijina bazai bariba akan ya'yana har Kotu munje anyi shari'a dayake yafini sama dole aka mai dasu hannun matar shi kedai lamarin nan ba'acewa komai sai godiyar Allah."

"Gaskia ne karki damu kanki duk inda kike addu'arki zata iskesu Allah ya raya makisu kuma ya karesu."
"Ameen nagode."

Shiru wajen ya sake dauka nima nashiga yan tunane tunanena wannan karan akan su Cankwai ne taya zan samarma kaina yanci tinda dai zaman nan bamai karewa bane kwara in samarma kaina mafita tunkan lokaci ya kure mani.
Ihun da Nusaiba ta rafkane shiya dawo dani duniyar tunanin dana wulla jikina yahau bari Cankwai ce keta zura mata bulala a tsakiyar baya itako sai zillo take tana gantsarewa.

"Bana hanaki zama wajen Dago ba? so kike ki koya mata munafunci ko?jiki magayi da magajiya kike zancen."

Duka take mata bana wasaba,har jikinta yafara jini da gudu su Atika suka iso wajen suka fisge bulalar hannun Cankwai baiwar Allah Nusaiba duk ta kidime dan azaba niko cikina ya duri ruwa na tabbata nawa rabon sai dare zan karbe shi,tunda makwancin mu daya dasu.

"Waike Magajiya dame kike gadara dashi a gidan nan da zaki matsama Prisonors da duka da azabarki zasuji ko kuwa da bala'in daya kawosu wannan gidan wanda kowa ke neman tsari dashi."
Atika ta ida maganar afusace.
"Ke Atika ki iya bakinki bar ganin komai zan saba maki,bar ganin kina gadara da wannan uniform din naki to ni nawa Uniform din yafi naki daraja dan akaina zaki iya rasa naki aikin kizo nan muzama daya kema inta dirkarki kamar ganga gwara ki rufawa kanki asiri kibi Cankwai Magajiya ki zauna lafiya nice Sarauniyar wannan gida dole abini azauna lafiya in ankiya jiki magayi."

"Kwarai kuwa da girman kujerar Magajiya
Cankwai yarinya tai taurin kai yanzun Yan ukku bala'i su tubemaki ita ki zane abarki son ranki."
Cewar Mairo.

"Haka kukace ko?wlh bari shugaban gidan nan zaizo dashi zan hadaku zaku gane kuren ku."

Fuuu Atika ta tafi nidai kamar munafuka nakasa ko motsi hakama Nusaiba dake soshe soshen azaba harda fitsari saida tayi.

"Ke kuma Dago kikazo nan kina gulma so ake akoya maki yanda zaki bijirewa umurnin Cankwai ko?ai tare zamu kwana yau saina zaunaki da wadannan duwaiwan nawa sai kinsan kinzo gidan Prison."

jikina na rawa na rike Cankwai ina kuka ina neman afuwa.

"Dan Allah Shugaba kiyi hakuri wlh ba maganarki take mani ba bamu isa muyi gulmarki ba, kece shugabata banda kowa saike a gidan nan dan Allah kada ki dukeni na tuba bazan karaba."

"Af ai kinji inda aka baro biɗa baya Cankwai bata yafiya matsalar kenan indai ta furta saita zartar amman zan sauya maki da wani abun na daban kinajina.?"

Eh naji minene."
Nai tambayar a shakkance.
"Keda wannan munafukar kullin kune zakuna wanke kewaye harna tsawon sati daya kin amince."?

"Eh na amince,saboda ina ganin da dai katuwa tsohuwar kilaki ta kamani ta zaune taita dirka kwara na wanke shi wanda tunkarar kewayen kanshi bala'i ne damma ahakan ana wanke shi amman zarni wari daci hamami gamida wari duk ya kunsa,musamman idan aka samu maha'inta suka bata shi da MP ai bamagana.
Amman na aminta haka na zauna kamar marainiya kusan bamu da banbanci danni nafara yarda nidin marainiya ce narasa kowa da komai nawa.

Ana inda nike zaune nan baccin wahala da fargaba ya daukeni,saidai idan zan bacci sau goma sainayi mafarkin Asma'u sau goma ba abinda take mani sai bani hakuri akan kalubale na rayuwa.

Kiyi hakuri Minal komai na duniya mai wucewa ne,insha Allah duk halin da zaki tsinci kanki Allah natare dake kiyawaita addu'a azumin nafila da azkar su kadai zasu fiddaki cikin masibar da kike ciki sannan ki yawaita istigfar kawata.

Idan na farka nakanyi kuka mai tarin yawa nakanji inama ban farkaba nakanga kamar mafarki nike Asma'u bata mutu tana taredani akowane lokaci,Allah Sarki duniya ba mutuwa akema kuka ba sabo akema kuka, daman ance Sabo turken wawa wannan haka yake,nasan bazan taba maida kwatankwacin Asma'u ba a rayuwata Childhood friend dita, kwana arba'in tabani a duniya ranar da aka gama wankan Asma'u a ranar aka haifeni gashi ta rigani zuwa duniya kuma tarigani barin ta,haka Allah yaso.

Kwalla keta zirara bisa fuskata bansan suna saukaba saidai dumin su da suka diga bisa tafin hannuna nadagasu sama ina newa kawata rahamar Allah da gafarar shi najima ina rokon Sarki buwayi gagara misali.

Tunda na shigo gidan Yari bantaba daga hannu nace Ya Allah kafitar dani Wannan gidan ba,aganina fargaba da tashin hankalin dake jirana a waje musamman garin mu,zaman gidan Dan kande inji Cankwai yafi mani sauki da sukuni shiyasa ban fatan infita.

Wannan dalilin yasa addu'a kaf ta Asma'u ce ba dare ba rana.

Haka rayuwa ta kasance idan yau da dadi gobe kam saidai agodewa Allah ga abinci inna kar6o wanibi dana faraci su Mairo su amshe mani inaji ina gani nasama raina tsoron su mai tarin yawa a cikin zuciya ta.

Akwai wata rana nagama tsara mizancema su Magajiya akan zalina da sukeci na gaji saida nataho gadan gadan rai bace nafara magana kenan cak kalamaina suka tsaya sakamakon wawan kallo data auna mani,jikina yahau bari ranar jikina yagaya mani tace saina maimaita abinda nafada amman nakasa ina shakka in fada ta illatani dan bugun datai mani kamar inyi zawo tsabar rikidewa.

Tana cikin dukana naji an hankadeta aka wanketa da mari Shugaban Gandirobas din ne wai shi Adam yasa aka saka mata mari aka sakata cikin wani kuntataccen daki wanda mutin bai iya walwala a ciki aka rufe,sai lokacin masu son taimakona suka iso aka dagani kayana sunyi budu budu tsabar birgima.

Dakina aka maidani akace basai nayi aiki ba karan farko dana hau gadona na gidan Yari tunda nazo ban haushi ba,uwata Cankwai ta hanani kullin kasa nike kwana har sanyi yafara jifar mani kashi ina fama da mura ga cikina kullin kululu(sauti) shine aikin shi tsabar yunwar dake dawainiya dani kwance nike ina mamakin miyasa indai zan hada ido da Cankwai nike gaza komai akanta ina tsoronta fiye da kima hakan ke nufi!?

Bacci yai awan gaba dani mai nauyin gaske harda nashari nikeyi duk da jikina yai mani tsami zan iya cewa the first time danai bacci mai dadi a gidan Kaso.


Tsabar dadin baccin da nikeyi sai naji dukan da Cankwai tai mani ya zamar mani alkhairi.

Saidai

Please Login or Register in order to submit comment