Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E47&48


"Ya mai girma mai Shari'a zan dakata anan kafin nazama na biyu nagode."
"Angaisheka Barrister Tukur."

Maida glass din fuskar shi Justice yayi yace.
"Duba da shaidun da aka gabatar Kotu zataje hutun takaitaccen lokaci kafin mu daura daga inda muka tsaya duba da lokaci."

Tashi yayi yafita kowa yafita nida da JJ muna tare da Jami'an tsaro su Atika suka tafi dani wani ɗaki inda suke sallah nan muka shiga.
Shiko JJ fita akai dashi da alama har sai anyi sallah sannan za'adawo a cigaba da shari'a.

Abinci Atika tabani nace na koshi dan banjin zan iya cin komai a halin da nike ciki.

Kiran salla aka fara karfe ɗaya alwalla nayi na dauki abaya dake aje bisa sallaya nayi sallar azahur tunda na aza goshina kasa nafara jero addu'oi ina kwalla masu ɗumin gaske wanda bansan suna shiɗa bisa kuncina ba.

```Ya Allah kaine Sarki buwayi gagara misali gareka ake neman taimako da buƙatu kai kace mu rokeka zaka kar6a mana addu'armu ya hayyu ya qayyum nice baiwar ka mai yawan zunubi mai yawan rauni ya ubangiji natuba kayafe mani ya Allah ka kawo mani ɗauki a cikin wannan Shari'ar ka wankeni a idon duniya ka fiddani da iyayena da duk wasu makusantana daga kunyar duniya da lahira,Ya Allah kafini sanin halin da nike ciki Allah ka kawo mani ɗauki kabani ikon cin wannan Jarabawar dana afka a ciki kasa tazama ka6aki agareni ranar gobe,Ya ubangijina ka yafema kawata Asma'u kaimata rahama Allah ka sanyaya mata kabarin ta,ya ubangijina duk wanda keda hannu a cikin wannan lamarin Allah kotuni asirin shi kowaye shi ya hayyu ya qayyum nayi tawassali da sunayen ka tsarkaka ka gafarta mani dan darajar fiyayyen halitta annabi Muhammada (SAW), natuba astagfirillah Allahumma inni as'aluka bi'annaka antallahu la'ilaha illa anta al'ahadussamadullazi lamyalid walam yuladi walam yakullahu kufuwan ahadi!```

Ina addu'a ina kuka nayima annabi salati,inaji ana cewa ke Dago lokaci yayi kita shi hakanan haba mi kikeyi haka.

Nidai cigaba da gayama Allah kukana nayi naci gaba dacewa.
_Lahaula wala quwata illa billah_
_La'ilaha illa anta subuhanaka inni kuntu minazzalumin._

*Rabbana atuna fidduniya hassanatan wafil akirati hasssanatan wakinna azabar nar."*
Haka nayi tawassali da Allah SWT Allah, na ɗago daga sujuda nagama sallah ina shafawa sannan na mike nabasu hijab na koma gefe sukayi sallah.

Saida muka kara minti goma sannan muka koma Court danci gaba da zaman karshe.

wannan shine ake kira da ƙila waƙala ko in haye ko in burma cikin tarkon dake bibiyata saboda shari'a sabanin hankali ce.

As usual da addu'a nike shiga Kotu,ina shiga idanu kaina kamar wata barauniya har bansan kallan mutane saboda kukan danayi haka na isa gaban Court na tsaya bamu jimaba Alqali ya shigo ya zauna kowa yagama natsuwa yace.

"Ko lauyan Mai ƙara na kusa."?
Mikewa Barrister Bashir yayi yace.

"Junaid Jamilu bissimillah."
Fitowa yayi ya shiga cikin abin tambaya yace.

"Junaid wanene Gali?"
Idanuwa waje JJ ke kallan Barrister yace.
"Bansan shiba Barrister."

Wani irin murmushi Barr Bashir yayi wanda shi kadai yasan ma'anar shi yace.
"Kada kamanta Court ba wajen wasa bane kuma bawa Shari'a wahala yana cikin laifi zaifi kyau ka fadi iyakar gaskiar ka Junaid."

"Ya maigirma mai Shari'a,bai kamata abokin aikina na zargin wanda ake zargi yana nuna karya yake faɗa ba, bayan shiɗin iyakar gaskiar shi yake faɗa."
"Ka kiyaye Barrister Bashir."
"godiya nike My Lord."

"Junaid ranar alhamis da lamarin yafaru kaje reception ka nemi abaka address ɗin dakin da Asma'u takama acewarka kaiɗin mijinta ne, hakan yasa aka kirata dataji ance Abdallah ne tabada izini aka baka number din dakinta miyasa ka yaudari mutane ta wannan hanyar musamman kayar da kayi akan mijinta."?

"Aaa Barrister bansan sharri akanmi zakace wai naje Reception nifa bin bayan Aminatu nayi naji tana waya da kawar ta nan naji room number din naje."

"Kwarai kuwa hakan tafaru bakai karyaba amman saboda kasan bazaka samu damar zuwa dakin ta kai tsaye ba shiyasa kabi ta wajen reception danka cika naka burin miyasa kayi hakan."?

"Nidai so kake ka tursasani kawai Barrister amman maganar danayi itace ainahin gaskia ta."

Jinjina kai Barr Bashir yayi yace.
"Okay ba komai naji abinda kace Junaid da kyau."

Juyawa yayi yana kallan Alqali tare da gyara tsayuwar shi yace.
"Ya mai girma mai Shari'a zanso Court tabani damar inafara gabatar da hujjata ta farko a gaban kuliya."

"Anbaka dama Barrister."
"Thank you my lord.
Kotu zataso a gabatar mata da Gali Hashim agaban kuliya."

Badajimawa wani ɗan sanda ya shigo dashi,ni kaina nagane shi ranar da naje Hotel shiya bani wani ticket natafi ɗakin da Asma'u ta kama mana.

Yana isowa ya tsaya gefen JJ Kallan kallo akema juna a tsakanin su,har Junaid ya fara raina gaskiar shi.

"Gali minene hadinka da Junaid kuma wane aiki kakeyi a Z Hotel.?"

"Nidai sunana Gali Hashim kuma a reception nike aiki nike kula da duk wani ɗaki,banda wani haɗi da Junaid saida yazo ya sameni yace yana neman room number din Asma'u,saboda shi mijinta ne sai yace mani baison inkirata yana son yayi Suprise dinta,kuma yace mani sunan shi Abdallah.
Hakanan naji ban yarda da shiba saidai na bashi yana tafiya nakira telephone din room dinta tana ɗagawa nace mata naba mijinta room mumber dinta yace zai suprise dinki.

Cikin shock tace mani aaa mijina bai nan yana kasuwa minene sunan shi.
Abdallah yace mata.

Magana tafara tace.
Gaskia ban......
shiru naji dan nima na tsinkayi muryar shi yana magana.
"kinyi mamakina Asma'u?maimakon kiga kawarki tazo sai kikaga Dr JJ ko? Ba abin mamaki bane....
Ban jirana ida jin mi yace mata ba,na tafi da gudu na haye sama dayake ɗakin a upstairs yake dan naji kamar ba alkhairi yakai shiba.

Zan shiga kenan na dakata a bakin kofar inaji yana cemata.
"Kinyi haɗaka da kawarki dan kuyi sirri ko? gashi na rigata isowa dan ayi sirrin dani saidai kafin ta iso zan baki mamaki."

Muryarta na tsinkaya tana cewa.
"JJ miya kawoka dakina mi zaka aikata."?

Inajin haka na ɗan leka ta kofa bansan dauko wayata ba nasaka Videoting jikina yahau 6ari nasara duk wata dubara domin idan nace zan shiga cikin ɗakin zai iya kasheni ,dan dagani ba imani atare dashi,ina ganin yazaro wuka dalleliya ya luma mata a ciki ya zare ya kara caka mata ita.
Ina ganin haka bansan na saki karaba a haukace yayo bakin kofa dan ganin wake wajen na tabbata yana ganina bako shakka zai kasheni tsabar ruɗu da firgici har fitsari saida yafara kubce mani da gudu nayi ƙasa nasamu waje na lafe nagama rudewa.
daganan bansan abinda ya kuma faruwaba koda na koma gida ciwo ya rufeni kamar anmani aikin sihiri nafi wata ukku ina fama da lalura bansan yanda case din ya kare ba saidai da bincike ya sake tashi na tuna da case din shine nazo dan wanke wannan baiwar Allah daga zargi."

Sauke ajiyar zuciya mutane sukayi haka aka kunna komai dayafaru ga Husna tsaye JJ ya luma mata wuƙa sannan yasa hannu ya bankadata tafaɗi gefen gado cikin jini.
nidai kuka kawai nikeyi,inajin tausan kawata.

Gali gaci gaba da cewa sannan akwai CCTV Camera wadda ake sakawa a Corridor.
Haka aka kunnata saiga JJ yabi Gali saidai bai ganshiba.

"Wannan shine abinda yafaru tunda abin yafaru na di6e cctv camera na'aje da wannan vedion din na adanasu nasan dole watan wata rana hakan zaifaru saboda shi rai fansa gare shi."
ya ida maganar kwalla na sauka bisa kuncin shi.

"Sannu da kokari Gali zaka iya tafiya."
"Nagode Barrister." yakoma ya zauna.


banda fita ba abinda JJ yakeyi,danko Barrister Tukur harda cire hula kowa yafara mamaki.

"Junaid ko wannan karya ake maka."?

Inƙina yafara yace.
"Eh aini ba'aduba mani tawa shaidar ba dan kawai anaso aci mani mutunci."

Murmushi Barr Bashir yayi yace.
"Gabatar mana da taka shaidar Junaid."

"Gata a wayata aikowa yaga Amina tana tare da wannan mutumin suna magana ko."
ya ida maganar kamar zaiyi kuka.

"Kai Junaid kowa yaga wannan Videon kuma Kotu zatayi duba da kowace hujja da aka gabatar mata da ita."
Cewar Alqali.

"A sake kawo sabuwar shaida,banda tsohuwa saboda anriga angama gabatar da ita."
Justice Na Allah ya ɗan ida maganar da sifar fushi.

"Insha Allah My Lord.
Junaid kace Aminatu itace ta kashe Asma'u ta hanyar kaca mata wuka,yanzun idan aka gabatar maka da result din shaidar hannun ka a jiki n wukar zaka yarda."?

"Intaba tabbata zan yarda mana."

"Okay Doctor Sadiq bissimillah."
Shigowa yayi da result a hannun shi yazo gaban kuliya ya tsaya
Kallan shi Barr yayi yace.
"Dr Sadiq Kotu zatso ka gabatar mata da saka mako.
Jinjina kai yayi yace.

"Am Doctor Sadiq Sani Sule.
Shekaru huɗu da suka shude ankawo mana case din nan, sanda akalkashin Jagoranci ASP Garba Musa akace a bincika tumprint dake jikin wannan wukar da kuke gani saidai ina cikin aikin case din aka kira waya ta hanyar Asp Garba Musa akace case din yakare saboda yarinyar da ake zargi bataba Shari'a wahala ba ta amsa laifin ta hakan yasa na adana result din cikin files akai sa date da statement case din ajiki, itama wukar naba Asp Garba,sai yanzun kwatam case din ya taso har transfer anmani dawowa nayi ko shekara ban hada dawowa ba,shine naima Barr Bashir hanya mukaje gun Asp Garba.
Duk da cewa yabar Area of Commender ya koma Yobe aiki shine yazo akai hadin guiwa da DPO din Station din aka nemo wannan wuka gata cikin leda da issue case dinta."

Mikama Alqali akayi yasa tissue aka fiddo wukar.
kwalla ke ziraro mani danaga wukar da aka kashe Husna da ita komai sabo ya dawo mani.

"Doctor Sadiq wannan saban gwajine ko kuwa tsohon result ne.?"
Cewar Alqali.
"Eh tsohone ranka shidade."
"Kotu ta umurci aje da wannan wuka kafin atashi asake sabon gwaji sannan a tafi da jami'an tsaro kuma a haɗo da Jami'an Inec."
"Angama ranka shidade."
Haka suka tafi.

"Barrister Bashir akwai wasu shaidun ne."?

"Eh ranka shidade,akwai idan anbani dama zan ida kawo su."
"Eh anbaka amman kabari sai andawo da result din,sannan."
Maida kallan shi yayi wajen Barrister Tukur yace.
"Barr Jakara ko kana da hujjar da zaka gabatar a halin yanzun"?

"Aaa ranka shidade saidai ko zuwa nan gaba kafin agama nagode."
"Masha Allah Barrister."
Komawa yayi ya zauna.

Daura kanshi JJ yayi bisa katakon abin tambaya yayi uban tagumi Barr Bashir ne yace.

"Junaid zamuso kagayama Court kaida suwaye kukayi wannan aika aikar.?"

Dagowa yayi ya aza idanun shi akaina har saida gabana ya faɗi tsabar yanda idanun shi suka gama rinewa yace.

"Caranci bansan yanda akai duniya tai mani atishawar kareba bansan yanda akai duniya ta juya mani bayaba.
nasoki beauty naso na keta maki haddi Allah ya kareki daga kaidina hakan yasa na kudiri kota wace hanya sainabi dan ganin na kuntata maki na hanaki sukunin rayuwa dake da Taufiq saboda shine yai silar kwatar ki daga kaidina a Jami'a wannan dalilin yasa nabi hanyoyi daban daban dan ganin na jefaki cikin ƙangin rayuwa yau gashi ranar dana sani ta tsayama Dr JJ ina girma da matsayina yatafi yau ina popular ta da izza gami dacin zarrafin yara danai tayi yake? tabbas Amina na zalince ki zalinci mafi muni kaicona."
Ya ida maganar kwalal na ziraro mashi sai kuma ya kalli Barr yace.

"Barrister Bashir na jinjina maka samun tsayayyun lauyoyi Jajirtattau irin ku da ansamu cigaba a kasar nan tamu tabbas ance gaske dokin karfe ce kuma karya fure take bata ya'ya!
Ni Dr JJ na aminta wannan laifin aikin haɗakane mukeyi da mutane masu daraja makusanta Amina."

Nidai jikina yai sanyi saidai naji tashin hankali danaji yace akwai makusan tana to su waye.?"

Sai naji Barrister shima yace mashi su waye Junaid"?

"Akwai Hafsat yayar mahaifiyar ta sai Hajia Mufida Shehu kishiyar mamar Major Taufiq sai babban yaron Abdallah, Khalid Lawal."

Da sauri su Ya Taufiq suka mike musamman Barrister Samir dake zaune gaban Court cikin shigar lauyoyi Anty Hafsat kuwa sai fita take da gelenta harda cire kallabi tana zare idanu,Dada Anty Mubara su Umaima harsun fara kuka,banda mijinta dako a jikin shi.

"Kotu na bukatar ganin ganin Hafsat da Mufida sai Khalid yanzun nan."
Cewar Alqali.

Haka Anty Hafsat ta fito waje kanta kasa ko kallan mutane tagazayi tsabar kunya hattani kunya ta isheni hakama Mama dake hawaye.
Shima Khalid ɗin fitowa yayi yanata soke kai ƙasa,abin takaici kusan wajen zaman su ɗaya da Abdallah.

Saidai an nemi Hajia Mufida (Mami) anrasata a cikin Court danko Major Sarki ya shiga tashin hankali makura.

Barr Bashir yace.

"Taya akai har suka kasance cikin wannan case din Junaid"?
Ajiyar zuciya mai karfi JJ ya sauke yace.

"Tunda case ya hadani da Amina a school har akai mani demotion ta sanadin ta saina kuduri daukar fansa akanta ko in dauke kanwarta Zainab in rape dinta ko in kashe mahaifin ta kusan kullin ina garin su har kofar gidan su a sirrince.

Ina zaune gefen mota ta kofar gidan su saiga Hafsat zata shiga cikin gidan su,zuwa tayi taimani magana tace.

"Yaro lafiya naganka anan.?"

Kallo daya nai mata nagane bata da imani ko kadan kuma yawan zuwan da take gidan su bana Allah bane daman nasa an bincika mani wacece ita,take nagama gaya mata manufa akan Amina inason keta mata haddi,cikeda farin ciki tace muje gidanta mu zanta.

Hakan yasa nabita mukaje gidanta nan take gaya mani rayuwar Amina take nema nan na goyi bayanta dari bisa dari.

Muna cikin magana saiga sai wayarta tahau ringing Hajia Mufida nagani ya bayyana,sai naji tace ki shigo ciki anyi babban kamu bata jimaba ta shigo har dakin ta.
Nan fa muka hau magana saina fahimci kamar ma sunfini rashin imani saboda su rayuwar ta suke nema ni kuma kawai pride dinta nikeso sai naki yarda da qudirin su,hakan yasa Hajia Mufida tabani kudi na gugar kudi million ukku akan wannan plains din na kashe Asma'u dan ace Amina ce, saina yarda saboda ba wanda yasan inda Amina take saini shiyasa suka dage saida na shiga cikin wannan plains din."

Jan numfashi yayi mai zafi ya fesar yaci gaba da cewa.

"Tunda Amina tabar gida nike bibiyar ta har mota ta kade aka kaita asibitin Murtala dagacan aka mai data asibitin Dala ta ƙashi.
karshe kano na koma da zama har aka sallameta ta koma gidan Alhaji Latib har sukai magana da Asma'u ina binta naji plains dinsu daman a lokacin dama kawai muke.

tareda tai makon Khalid mukasan zasu haɗu Hotel kasancewar baida shamaki da gidan Abdallah mijin Asma'u.

Shima mun haɗu dashi da nike bibiyar Amina ina ganin ta shiga gidan kawarta,nan na shiga shagon dake jikin gidan kamar zan siyayya nan nike tambayar shi,akai sa'a yanada labarin ta bakin uwar ɗakin shi,take na bashi dubu dari cash nace zan mashi transfer dubu ɗari biyar duk motsin Asma'u ya gaya mani,nan mukai exchanging contact,saidai ban gaya mashi so muke mukashe taba.
Haka ya sanar mani ta fita zasuyi haɗaka Hotel yaji tayi booking.
Ni kuma na tsaya inda nasan dole tanan Amina zatabi shine nabita naji sunyi waya,sai nayu saurin rigata isa.
shine naje Hotel har dakin da ta kama na cakawa Asma'u wuka a ciki wadda Hafsat tabani bisa umurinin Hajia Mufida.
wannan shine ainahin abinda yafaru ni nakashe Asma'u tareda umurnin Hajia Mufida da yayar mahaifiyar ta Hafsat."

Inalillahi wa'inna ilahirraji'un duka Court aka hau salati nidai kuka kawai nikeyi zuciya ta na ƙuna komai ya kwance lamarin kamar film haka nike ganin labarin rayuwata.

Faduwa kasa Anty Hafsat tayi tana birgima taba cewa ammata sharri wai dan antsaneta ita batasan JJ ba."
Murmushi JJ yai mai ciwo yace.

"Mijinta shaidane ya iskemu har yai mana wa'azi da munyi yunƙurin kashe shi yace ba wanda zaiji gashi can atambaye shi in karya nike mata."
Ya ida maganar yana gwada Baban Umaima.

Murmushi Barrister Bashir yayi yace.

"Ya mai girma mai Shari'a daman wannan itace hujjata ta karshe dazan gabatar wadda Junaid ya fada yanzun,muna son Court tabamu dama mugana da M.Usman."
"Amabaka izini Barrister."

Fitowa yayi ya tsaya akace.

"Miyasa kana makusancin su kasan gaskia labari akai wannan aika aikar har aka kulle Amina shekara huɗu tana gidan Yari."?

"Ranka shidade na shiga tashin hankali ranar danai masu nasiha saura kadan su kasheni koda dare yai kasa kwanciya hankalina yayi shiyasa na gudu natafi Lagos saida komai ya lafa nadawo na maida komai ya wuce kamar bansan abinda yafaru ba.
saidai na naɗi komai amman Mamory din ke gareni gashi."

USB aka saka shi aka nemo recording din sai gashi duk abinda JJ ya fada shine ba ragi ba kari akahau salati da sallalami wasu na kuka.
Ana gama ji yaci gaba dacewa.

D"a ace natsaya da sai Hafsat tayi yanda tayi ta kasheni kota hanyar gubane amman da suka cika burin su aka kama Amina shine nadawo na nuna komai ya wuce amman ba karamin tanadi nikema M card din nan ba,da kaina naje na samu Barrister Bashir na gaya mashi komai amin afuwa.
Naki faɗa ne saboda hatsabibanci irin na Hafsat duk da take matata amman makirace kuma batada imani kaji dalilina aimin aikin gafara."

"Zaka iya tafiya Alhaji Usman bakomai.
Cewar Alqali.

"Junaid,Hafsat da Khalid kun aminta da abinda ake zargin ku."?
Eh sukace itama kukan takeyi tana gefena tace.

"Eh amman wlh Mufida ce shugabar mu ko Guba daka saka Aminatu a gidan Yari mune sanda mukaje mata ziyara muka ce,ita da fita har abada nan mukaga kawarta Nusaiba nan muka samu Karima muka bata million ɗaya mukace taba Nusaiba guba ta samata a abinci saidai anyi rashin sa'a aka kamata ganin asirin mu zai tonu shine cikin dare mukasa Karima tasa pillow ta shaketa har saida ta mutu."

Inalillahi wa'inna ilahirraji'un kawai ake cewa.

Kuka take hardasu majina tana cewa.

"Munso mukashe Amina tun a gidan Yari saboda muna tsoron kada watan wata rana gaskia tayi halinta tafito saboda banda abinda nikema bakin ciki a duniya irin cigaban Aminatu,ita kuma Hajia Mufida tayi hakan ne dan kada Hussein da Aminatu suyi aure batason taga sunyi aure saboda tace ai danta aka hana shima bazai aureta ta,shi kuma Junaid ya gwammaci ta mutu dan kada ta auri Taufiq bashi ba,tunda keta mata haddi yake sonyi wannan shine makircin da muka jima muna shukawa dan Allah Amina kiyafe mani."

Tayi maganar tana neman dafani da sauri naja baya dan tsoron ta nikeyi sosai gani nike zata iya shakeni har saiji na mutu.

Shigowar Dr Sadiq ya katsema Barrister Bashir maganar dayai niyaryi.
saka mako aka akawo akaba Alqali saiga shi komai na JJ ne har tumprint akasa yayi komi nashine saboda yan inec akasa sukai mashi take suka amsa laifin su.

Alqali yace.
"nan da minti goma aje akamo mani Gandiroba Karima yanzun yanzun nan."

Haka aka tafi,saidai Kotu sheshekar kuka kawai ke tashi banda Ya Samir kanshi duƙe bisa banci yanajin tuggun da Mami ta aikata akaina,saidai nayi mamaki da banji ance hadda Anty Wasila ba duk da kuwa tana Court din sai kuka takeyi.

Buga guduma Alqali yayi kowa ya nutsu yace.

"Barr Bashir kagama tambayoyin ka."?

''Aa My Lord zanso inji tabakin Khalid."
"Anbaka dama Barr Fage."
Maida kallan shi yayi kan Khalid yace.
"Miyasa an yarda dakai kaci amana?miyasa ka iya fallasa sirrin gidan uban gidanka."
Kuka yakeyi yace.
"Wlh Barr cemani yayi intai maka mashi da shige da ficen su acewar shi wai Aminatu yakeso kuma yansan idan Asma'u ta fito waje ya sani saboda akwai maganar da zai mata mai mahimmancin gaske ni kuma ban kawoma kaina komai shune nabashi numberta kuma nagaya mashi lokacin data fita."

"Lokacin da akai shari'ar farko kana ina.?"
"Wlh ban nan ogana ya turani Lagos kasuwancin bansan komai ba sadda nadawo har angama komai Barrister."

Jinjina kai yayi yace.
"Alhaji Abdallah dagske anyi haka."?
Mikewa yayi yace.
"Tabbas anyi haka Barr."
"Okay,Khalid ka aminta da laifinka na faɗin sirrin gidan uban gidan ka."?

"Eh na aminta amman aimani sassauci."
Jinjina kanshi Barr yayi ya kalli Alqali yace.

"My Lord anan zan tsaya da shaiduna inafatan Court zata dubi da hujjar dana gabatar nagode."

"Angaisheka Barr Bashir."
Rissinawa yayi ya koma ya zauna gefen Ya Samir.
Alqali yace.
"Barr Tukur kanada sauran wata shaida."?
Mikewa yayi yace.
"Banda wata shaida my Lord."
Jinjina kai Alqali yayi yana goge fuskar shi da handkerchief yace.

"Kowa yaga yanda wannan Shari'a ta kama masu laifi sun amsa laifin su duk da sunba Shari'a wahala gami da sharri ga wadda bataci bata shaba na kisan kawa,yar uwa,masoyiya kuma aminiyar ta dan haka Court ta yankema wadannan mutanen hukunci kamar haka.

Nafarko kowa anasaka mashi tarar kudi na dubu dari biyar biyar akan wadda sukaima sharri dan samun magunguna da kula harta maida jikinta.

Na biyu Court ta yan kema Junaid Jamilu Kano Life Prison har abada zaman Jail,da hukuncin ratayane amman saboda amsa laifi dayayi zai dawwama a gidan Yari har mutuwar shi.
Hawaye masu zafi suka zuboma JJ tunawa nayi ranar da aka yanke mani hukunci har dariya suke mani gaskia duniya abar tsoro ce.

Sannan wannan Kotu mai adalci ta yankema Hafsat Adam life Prison a Kurmawa Jail,akan saki layi na dubu ukku da tamanin...

Kurma ihu su Umaima sukayi itako Dada tarasa abinyi,dan takaici.

"Sai Hajia Mufida ina iyalanta suke.?"
Fiddausi ta mike tsaye a sirrace dan Ya Samir yagazan ko ɗago kanshi.

Alqali yace.
"Kowa ya shaida za'asa anemo Mufida kuma za'aje Jami'an tsaro na sirri duk ranar data dawo zatayi Life Prison,idan kuma kamota akai taba Shari'a wahala za'a kasheta ta hanyar hanging,ku kiyaye wannan kuma za'abaza neman ta har abada."

Zama tayi suna kuka nikaina naji ba dadiba.

Sannan Kotu ta yan kema Khalid Lawal zaman gidan Yari na shekara huɗu bisa laifin fidda sirrin gidan ubann gidan shi da yayi ga azzalumai."

Kokowa ake da Karima haka aka gurfarnar da ita a gaban Kotu sai kuka take ko kallan mutane batayi da kyau.

Daka mata tsawa Alqali yayi nan aka tuhumeta,yace.

"taya akai har kika shiga ɗakin da aka rufe mariganya Nusaiba bayan anshaidama Court ɗakin arufe yake da kwaɗo kuma akwai mai tsaron ɗakin alokacin."?
Alqali yai mata tambayar kai tsaye.

Sheshshekar kuka take tace.

"Lokacin da lamarin ya faru na kira iyayen ɗakina na shaida masu halin da ake ciki shine Hafsat tace zasu turo mani naira dubu dari biyar inba mai gadin dakin cin hanci saiya bude mani haka kuwa akayi.

Ina zuwa na sami Saminu lokacin karfe takwas da rabi nayi badda kama nazo wajen shi daman ina cikin masu night duty.
Ina zuwa na shaida mashi kudurina da alfarmata ada yace bazai yardaba sai nace.
"Saminu a wannan iskar dake kaɗawa wane sakarai zaiga daula ya tsaya yana yanga bayan kowa abinda yake nema kenan aduniya."

Murmushi yayi yace.
"Ban fahimcekiba Karima."
Ina nufin zan baka naira dubu ɗari biyu cash."
"Uhmm ban bukata sun mani kaɗan."
Nakara maka dubu hamsin in zaka iya bude mani."

Albarka yace,har na fidda ran amincewar shi sai kuma yace.
"Kibani naira dubu dari ukku inkinga zaki iya."
Jinjina kaina nayi nace.
"Mi za'afasa kudi ba matsala bane anshi nan dubu dari biyune gobe zan cika maka dubu ɗari."
Yana amsa ya bude mani ɗakin tareda bani pillown shi agaban shi na shake Nusaiba tana bacci shiya tayani ta hanyar danne mata kafafu tana wullewulle tana koma muka kasheta har saida muka tabbatar bata numfashi sannan muka kyaleta nan ya rufe dakin kamar ba abinda yafaru har gari ya waye labari ya bazu saidai binciken da likitoci sukayi ya nuna toshe mata hanci akayi,kaji abinda yafaru ranka shidade nida Saminu idris ne tareda Hafsat bisa umurnin Hajia Mufida Shehu."

ta ida maganar tana kuka Alqali yace.
"ane mani Saminu Idiris."
Take Oga Adam ya nuna shi zai ji6i yake yana zare idanu fitowa yayi sai raba idanu yake.
Alqali yace.

"Kaji abinda akace ka aikata hakane."?
"Um um wlh ita tazo ta sameni ba yanda zanyi ne aiman afuwa."

"Ka yarda da abinda ake tuhumarka"?
Alqali yai maganar ba wasa afuskar shi."

"Eh nayarda kwaɗayine ya kwasheni natuba."

Jinjina kai Alqali yayi yace.
"Kuna ma'aikata aka haɗa baki daku aka kashe mutuniyar kirki dan kawai bata da galihu ko? barin irinku a cikin al'umma shi zai gurbatata dan hakazaku ɗanɗani kuɗarku.

Sannan duba da amsa laifin da kukayi Kotu ta yankema Karima Ɗahir da Saminu Idris hanging ta hayar rataya."

Zubewa tayi kasa tana kuka kamar mahaukaciya.
nidai salati nikema annabi akaina ni kaɗai dan suga bayana gashi mutane da yawa sun halaka!

Inalillahi wa'inna ilahirraji'un nike maimatawa ina kuka.

Nina jamaki Asma'u da ace bakida alaqaka dani da ba'a kasheki ba saidai Allah yasa haka *ALQALAMI* ya bushe tuni sai hakan tafaru,gashi *BAKIN JININA YAJAMAKI* kawata saidai *QADDARATA* ta shafi taki Qaddarar Husna,Allah yaimaki rahama masoyiyata *HAKA ALLAH YASO* Saidai komai *LOKACINE* naki lokacin ne yayi shiyasa kika tafi kikabarni nima komai daren daɗewa zan iskeki masoyiyata ina kewarki kawata yau gashi Allah ya kawo lokacin azzalumai.!"
Kuka na sake fashewa dashi.

Jinayi Anty Hafsat ta dafani tana kuka bansan sadda na ka6e hannun taba,ashe maganar da nikeyi tafita waje dayawa kuka mutane keyi,idanuna suka sauka kan Ya Taufiq shima kwallan ya goge maganar Alqali ya maido mana hankalin mu kallan shi mukayi yace.

"Duba da hujjojin da Lauyoyin mu suka gabatar da yanda masu laifi suka amsa laifukan su Court mai alfarma ta duba da dukkan waɗannan hujjoji ta wanke AMINATU YUSUF CARANCI daga zargin da ake

Please Login or Register in order to submit comment