Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akwai matsala."

"Aaa Mami ni Hussein Sarki Mukhtar inada yaƙini Minal bazata iya kashe Husna ba,kuma raina fansa ne akan rayuwar Aminatu kedai kiyi fatan alkhairi."

Ya ida maganar idanun shi cikin nata.
A sanyaye tace.
"Shikenan Allah ya kyauta."
"Amin."
"Ko kefa Mufida yanzun kikai magana anasan baki ya yawaita furta alkhairi akoda yaushe Hussein tashi kaje Allah ya tsareka."
"Ameen Abbana nagode."

Bai jimaba yafito zugar Soldiers suka biyo shi,ya dakarta dasu yace Personal fitace, shiga mota yayi Usama yaja suka tafi, sai murna yake uban gidan shi ya dawo haka suka kama hanyar zuwa Caranci.

_Noted:-kada ku manta Major Taufiq ya aje aiki,amman ƙa'idar aikin Soja indai mutun yakai muƙamin Major ana bashi sojoji masu kula da lafiyar shi._

Koda ya isa Caranci kai tsaye gidan su Minal ya dosa tunda ya shigo unguwar su ya fito ake kallan shi musamman wa'anda suka sanshi,koda yaje gidansu ya iske shi a rufe knocking yayi shiru bakowa, tsaye yayi ko zaiga dawowar su,amman shiru kakeji fitowa yayi ya samu wani makwabcin su malam Musa ya tambaye shi inda masu gidan suka tafi.

"Bawan Allah ina neman masu gidan nan ne."?

"Sun tashi da jimawa watanin da suka shige."
Wani irin faduwar gaba ya riski Taufiq.
"Ina suka koma bawan Allah."?

"Sokoto akace amman bamu saniba cikin gari ko local govt Allah masani kasan ba wanda yasan sun bar gari,tsabar sun aikata kayan kunya wai yarsa ta kashe.....

"Ya isa bawan Allah ba wannan na tambayeka ba."

Rai bace Taufiq ya ida maganar,ya hau mota suka tafi sai Katsina gidan Anty Murja ya sauka tana cikin cin abinci taga Taufiq ayam batasan sanda ta rungume shiba tsabar farin ciki.
"oyoyo yaushe kadawo Hussein Allah mun gode maka."

"Ina Baba suka koma innah."?

"Wane Baban."?
tayi tambayar cike da mamaki.
"Baba Yusuf mana naje wai basu nan sun bar gari."

"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un,ka kosan sau ukku ina kai masu ziyara ban samunsu koda na kira yaya Yusuf sai sai yace mani ai sunje unguwa, ashe barin gari yayi,wlh ba wanda yasani Hussein."

"Shikenan wai wani makwabcin su yace sun koma Sokoto,dan haka ki kwantar da hankali da kaina zanje in nemo inda Baba yake insha Allahu."

"Gaskia yaya Yusuf bai kyauta mana ba,ace yabar gari kaf dangi ba wanda yasani ko number ɗin shi bata zuwa sai kayi dagaske abin takaici."

Shikenan Inna insha Allahu,Allah zai baiyana masu kuma zanje neman su, ga Minal na gidan Yari wannan wace irin Jarabawa ce amman haka Allah yaso zan tafi Inna."
"Katsaya kaci abinci mana."

"Haba Inna taya zan iyacin abinci cikin jin dadi da kwanciyar hankali koda nabar ƙasar nan banci na kirkiba inaga yanzun dana dawo na iske wannan ifitila'in kibari inje inga halin da Minal ke ciki."

"Allah yataimaka maka Hussein,Allah yaimaka albarka."
"Ameen Inna sai anjima."

Suna fita ana magrib daga masallaci Hotel suka nufa shida Usama kowa yai dakin shi.

Ranar baccin kwarai Taufiq baiba koda gari ya waye kalaci baiba ya tafi karfe tara suka dauki hanyar Kano sai Kurmawa Prison Bompai goma da rabi ya isa akaci sa'a ya iske Adam gaisawa sukayi yace.

"Barka da safiya ya aiki."?
"Alhmdulillah ko zan iya taimakon ka."?

Shiru Taufiq yayi nadan lokaci fargabar halin da zai tsinci Aminatu ya dame shi jiki mace yace.
"Eh zaka iya"
Ok inajinka."

"Inasan ganin Amina Yusuf Caranci wannan shine taimakon da nikeso kai mani."

"Amman minene hadin ka da ita.?"
"Kanwata ce."
Kallan shi yake sama da kasa yana wasu wasi yace.
"Okay bari insaka akira maka ita saidai ina bukatar ku zauna anan ku gaisa."
"Nagode."

Wayar shi Adam ya dauko ya kira Atika lokacin suna wajen aiki suna kwasar icce,Atika na kula dasu.

"Yes Sir"
Shine abinda Atika tace data ɗaga kiran Oga Adam.
"Ki kira mani Dago."
"Ok Sir"

Kallan shi kawai Taufiq yake aranshi yana maimaita kalmar Dago kamar,yana mamaki kardai ace Minal dinshi ce ta koma haka.

Ina ɗaukar wani icce a hannuna naji ance inzo ana kirana.
Atika tace inje Oga Adam na kirana.
Hakanan na tsinci kaina cikin faduwar gaba mai tsanani,daman yau tunda natashi naji banda lakka duk jikina ya mutu hakanan nike karfin hali,ina zuwa wajenta nace.

"Allah yasa ba ziyara bace dan gaskia ban bukatar ganin kowa a halin yanzun."
Na ida maganara raunane.
"Kedai Aminatu kije kilan alkhairi ke ki ranki."
Jinjina kaina kawai nayi badan nasoba natafi inda nasaba ganawa da yan uwana saidai banga kowa ba.
office din Adam na nufa,ina zuwa natura da sallama abakina,amsa mani yayi zan duka kenan domin in gaida shi,sai nafahimci bashi kaɗai bane,a hankali na ɗago da niyar ingaida bakon nashi,saidai dagowar da zanyi idanun mu suka sarke dana juna ganin Ya Taufiq ya kafeni da kallo ko keftawa baiyi, sumane kawai banba, cikin kankanin lokaci bugun zuciya ta,ya sauya da karfi yafara halbawa,a razane na mike ina gwadashi da yatsata manuniya,ganin haka yasa Adam fita.
motsowa Ya Taufiiq yayi kusa dani cikin raunanniyar fuska idanun shi sun kaɗa sunyi jajir dasu,muryar shi na rarrabewa yace.

"Minal kece a wannan halin,ina raye bansan kina cikin wannan rayuwar ba,kiyafe mani Minal, miyasa na nesanta kaina dake ban tsaya gareki ba koma menene ya samemu a tare."
A raunane ya ida maganar idanun shi sunyi jajir dasu.
Dukawa yayi gabana yana kallona niko a tsaye nike ina kallan shi,ganin kallan shi zai raunana mani zuciya bansan na juya mashi baya ba kwalla masu ɗumi suna shida bisa kuncina.

Batareda na kalle shi ba nace.
"Kaw tafi kabani waje Ya Taufiq,karka kara shigowa cikin rayuwata dan Allah naroƙeka, banda kowa banda komai dan haka bani bukatar ka arayuwa ta,kaje kayi taka rayuwar nima ka barni inji da tawa rayuwar dan Allah."

Na ida maganar ina juyowa hannayena haɗe sifar roƙo.
Ina kallan kwayar idon shi,wa'anda basu da banbanci da rushi tsabar tashin hankalin daya samu kanshi a ciki.

Rike mani hannu yayi muryar shi na rawa yace.

"Aaa Minal bazan ta6a rusa maki rayuwa ba saima gyarata da nikeson yi dan Allah kibani haɗin kai inga narabaki da wannan rayuwar bazan taba samun kwanciyar hankali ba matsawar kina a wannan halin,dan Allah Aminatu ki tallafi ɗan sauran rayuwar data rage mani rasaki tamkar datse duk wani hope dinane kece farin cikina Minal."

Fisge hannuna nayi nace.
"Ban kaunarka natsane ka Ya Taufiq,akanka ba irin iftila'i na rayuwa wanda bangani ba,na za6i nayi rayuwa dakai ashe Qaddarata na tare dakai,akan ka narasa duk wani farin ciki saboda dalilin ka mahaifina nasamu sabani dashi har Qaddara ta kawoni Kano karshe ga Yanda Allah Yaso dani sai yanzun da kowa yasan rayuwata dawamamma ce anan shine zaka sake biyoni anan din danka rushe mani yar sauran rayuwar da nikeyi cikin kunci ka kara mani wani kuncin to kasani duk wani taimakon ka,nidai banso ban kaunar shi kabarni anan ya fiman ko ina a halin yanzun."

Wasu kwalla naga sunyi nasarar ziraro mashi bisa kuncin shi ya share su,sannan ya mike yayi yazo gab dani yana kallona nima shiɗin nike kallo inajin tsanar shi acikin raina,abin kamar aikin sihiri nima har mamakin kaina nikeyi.
Karon farko dana farajin tsanar Ya Taufiq araina.

Maganar shice ta dawo dani cikin tunani na yace.

"Tabbas duk abinda ke faruwa inada nasaba dashi saboda nidin Qarrar kine Minal,saidai kinsani banta6a jin tsanarki ba,ko ƙinki arayuwata daidai da kwayar zarra,kisani kullin gubar sonki illatake mani a cikin zuciyata, nasha wahala akanki Aminatu saidai agareni ba'a wahala da ɗawainiyar masoyi.
Kisani koda Allah yasa nadawo na iskeki ɗakin auren ki tabbas zammaki fatan alkhairi saidai kisani da kaunarki zanyi numfashina na karshe,Minal."
Wani irin huci ya fesar ya juyaman baya yana goya hannayen shi bisa bayan shi yaci gaba dacewa.

"Akan sonki na zama sakarai sullutu duk tarin arziki,nasaba,kyau,kwarjini da duk wani abun da Hussein Sarki Mukhtar Munzali ya mallaka soyayyarki saida ta nuna mani suɗin bakomai bane,saboda suɗin basu ta6a bada soyayya,ashe kyautatawa, kulawa,tausayi,jinkai sune so da kauna akanki Aminatu nabar iyayena,dangina,aikina da komai nawa dan inaganin zama a cikin su alhali na rasaki tabbas zan tagayyara,na zama maraya a tsawon shekarun da nayi shin baki taba tambayar kanki ba,miyajawoma Taufiq tabka wannan babbar asarar ba?baki ta6a tunanin cewa miyasa Hussein ya zama sakarai ba?marar tunani idanuna sun rufe zuciya ta,ta makance banji ban gani banjin kwatanci ko nasiha na bijirema iyayena duk baki ta6a tambayar kanki ba miyasa Taufiq yayi hakan ba."?
Juyowa yayi ya kalleni idon sa cikin nawa yace.
"Dubi kwayar idanuna dakyau Minal na tabbata zakiga cikakkar amsarki a cikin su ba wani abu bane yajefani cikin mawuyacin hali ba duk saboda sonki ne,kece silar maida Major Taufiq haka,shine kike furta kalmar tsana agareni bayan kinsan hakan ba karamar illa bane agareni dan Allah Minal kiyi mani adalci kada ki furta kalmar ƙi agareni Aminatu."

Dafe kaina nayi inajin wata irin juwa na nane man kadani, zuciya ta na mani zafi raina na kuna nace.

"Ya isa Ya Taufiq naji duk abinda kace,saidai bukatar komai agareka na rokeka kafita rayuwata bansan komai ya dawo mani sabo,na tsani komai daya wuce arayuwata ya dawo mani dan Allah ka rabu dani Ya Taufiq! har kana tunanin akwai wata rayuwa da zanyi wadda zata kwantar mani da hankali bayan da hannuna na kashe aminiyata,inama ace hanging ɗina akayi dana huta.
Yau Alhamis shekarar Asma'u biyu da watanni rabanta da numfashin duniya,nima haka shekara kenan, rabon da in taka waje da sunan Yan tatta ahakan kake tunanin zan za6i barin gidan nan?
idan mafarki kakeyi ka farka nasan bani ba fita A gidan nan tinda kowa ya shaida nice na kashe Asma'u, kuma dan Allah Ya Taufiq kayi hakuri ka nisanta kanka daniko kasamu sassaucin rayuwa,daga karshe ina mai baka shawara a matsayin ka,na ɗan uwana na jini kaje kayi Iyalin ka dan inganta taka rayuwar,ka kama dahir kada kayi sakin na hannu kamun naguje ina maka fatan alkhairi kuma duk wata soyayya daka nuna mani nagode sosai da ita dan bazan ta6a samun madadin taba,nabarka lafiya."

Kuka ya kara kubce mani kai ta6a zuciya da sauri najuya nafara tafiya.

"tsaya Minal dan Allah ki saurari abinda zance maki,bazan barki a cikin wannan halin ba nai maki alkawali,kiyarda dani Minal dan All...

Waje nayi inajin zuciya ta kamar zata kubto ta faɗo ƙasa tsabar karaya da tayi komai ya koma mani sabo inama Ya Taufiq bai dawo gareni ba miyasa shi kadai ne Weakness ɗina,miyasa narasa sukunina miyasa zuciyata ke halbawa irin haka?inalillahi wa'inna ilahirraji'un.
ranar bacci gagarata yayi tunanin Ya Taufiq yasani gaba kuka ko nasha shi tunsu Cankwai na bani hakuri har suka samani ido dan lamarina yafara firgita su, haka na kwana zaune ba wanda nike tunawa sai Ya Taufiq musamman halin dana ga ya tsinci kanshi ga tawa matsalar da yake neman saka kanshi,wani tausayin naji ya lullubeni. a wani sashena zuciyata kuma inajin haushin shi saidai narasa dalilin jin hakan,wannan kenan.

*CARANCI*

_More Comments more posts😘_
*_Yar Mutan Kankia ke maku fatan alkhairi😍_*

Share
Pls
❣️

_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E25&26




*CARANCI*


TAUFIQ ne a gidan su Asma'u cikin sitrum din Baban ta, gaisawa yayi da mahaifin ta sannan ya mashi ta'aziyya sunjima suna gaisawa, daga bisani Ya Taufiq yace.

"Abba bansan ta ina zanfara ba,kuma bansan ya zaka ɗauki zancena ba,saidai inafatan Allah yasa kafahimce abinda zan gaya maka kuma kayi hakuri da kalamai na."

Ya ida maganar cikeda kamala yaci gaba dacewa.
''Idan nace ban girgiza ba,dajin rasuwar Asma'u tabbas nayi karya Allah kadai yasan yanda naji da labarin rashinta ya sameni, musamman yanda silar mutuwar tazo saidai muce inalillahi wa'inna ilahirraji'un!
Amman ko tantama banayi Aminatu bazata ta6a iya kisan kaiba bare kuma harta kashe Asma'u,koda ta amsa wannan laifin kisan wlh zan iya gitta raina Amina bazata taba iya kashe Asma'u ba tabbas akwai wani dalilin ko ince gadar zare aka haɗa mata dan ta afka cikin tarko kuma ta durmiya a ciki,nasan Aminatu bata da mafita dole ta amsa laifinta.
Dan Allah Abba ina rokon ka,daka bani haɗin kai dan warware wannan sarƙaƙiyawar inason inshaida ma duniya aminci har abada sunan shi aminci,zan sanya zukatan mutanen da suka dauka aminci ya ƙare a tsakanin al'umma zan nuna masu cewa akwai shi,har yanzun saidai yai karanci amman har gobe akwai na Allah,kuma masu tsoron ubangijin su,dan Allah Abba kabani haɗin kai in nuna ma mutane amana gaskia ce kuma Aminatu bazata ta6a iyacin amanar Asma'u ba rokeka Abba."
Cikeda rauni Ya Taufiq yai maganar.

Jinjina al'amarin mahaifin Asma'u yayi yace.

"Hussein duk abinda kafaɗa hakane amman taya hakan zai faruwa kuma kana ganin zan iya taimaka maka a cikin wannan lamarin?sannan wane taimako kake bukatar inyi maka."?

"Inason kasanar mani inda Baba ya koma dan Allah,ta hakane kawai zan samu insan taya zan bullowa lamarin nan."

Ɗan shiru yayi yana nazari sannan yace.
"Toh gaskia ni kaɗai nasan ainahin inda yakoma saidai nima ba tabbas,ya koma jihar Sokoto,a cikin Bakura amman yace mani zai tashi dagacan idan abokin nashi ya samar mashi gida zai siya,banda tabbas har yanzun suna Bakura ko kuwa sunbar candin shine ban sani ba."

Wata irin ajiyar zuciya Taufiq ya shiɗe yace.

"Alhmdullh naji daɗin wannan labarin,saidai Abba ya sunan mutumin inane address din gidan nashi."?
"Sunan shi Alhaji Tijjani Kabir Bakura sannan kuma ɗan asalin garin Bakura ne......
Ya ida gaya mashi address ɗinshi.

godiya yai mashi yace.
"Allah yasaka maka da alkhairi Abba nagode kwarai dagaske Allah yakai hasken makwancin Asma'u kuma Allah ya raya zuriyar data bari."
"Ameen Husseini kaima Allah yatai makeka."
"Ameen Abba."
Sawa yayi aka kira mashi ya'yan Asma'u yai masu alkairi,yanajin tausayin su aranshi tunda ta rasu nan Abdallah ya maidosu wajen maahifiyar ta,kuma har yanzun ba ƙara aure ba.

Sallama yaima Baba,sannan yai mashi rakiya kofar gida.
tafiya Taufiq yayi,komai ya gama kwance mashi a kai sake sake kawai yake ta ina zai fara,karfe biyar na yamma yabar gidan su Asma'u,bai bata lokaci ba yasa Usama suka dauki hanyar Sokoto.

Da bata lokaci da komai karfe tara na dare ya isa Sokoto,Hotel ya kama masu suka kwana.

Karfe tara na safe ya shiga cikin garin Bakura yafara neman gidan Alhaji Tijjani dayake ba boyayye bane har gidan shi aka kaisu,iso akai masu inda ake aje baki basufi minti ashirin da zama ba ya shigo falorn cikeda girmamawa suka gaida shi.

Amsawa yayi cikin da fara'a.
Kallan su yake yana nazarin su saidai bai shaidasu ba,kallan dayake masu ne yasa Taufiq yafara cewa.

"Sunana Hussein Mukhtar kuma ni ɗan Kaduna ne daman nazo ne dan.....

Bai bari ya ƙarasa bayyana mashi kanshi ba ya katse shi ta hanyar cewa.
"Taufiq ko?inada labarin ka yaushe kadawo ƙasar."?
Murmushi ɗauke a fuskar Taufiq yace.
Kwanana ukku kenan."
"Masha Allah sannun ka da hanya inafatan kowa yana lafiya."?
"Lafiya lau."
Ɗan shiru yayi yace.
"Abba daman taimako nike nema gareka idan badamuwa."

"Allah yabani ikon taimaka maka."
"Ameen dan Allah Abba inason kafada mani inda Baba yakoma."

Murmushi yayi yace. "shikenan Hussein saidai zan sanar mashi kafin in baka adress din inda ya koma."

Marairaicewa Taufiq yayi yace.
"Abba idan har kagaya mashi na tabbata bazai ta6a bari kabani ba,dan Allah kataimaka mani insamu in gyara abubuwan da suka lalace abaya,kai kaɗai ne zaka goya mani baya,domin Allah nasan mutane masu son zumunta da gyara shi dan Allah Abba."

Shiru yayi na sakanni yana kallan iyakar gaskiar Taufiq yace.

"Naji zan baka adress amman kai da kanka zaka ida neman gidan shi saboda wasu dalilai nai mashi alqawali bazan taba gayama kowa gidan shiba wannan dalilin zai hana in baka direct address din shi ka amince."?

"Nayarda Abba zan nema da kaina insha Allah.

"Kaje Anka Local Govt kanemi Gada.....
can ya koma wannan shine abinda zan iya baka."

"Nagode maka Allah yakara girma yasaka maka da alkhairi."
"Ameen Allah ya tsare hanya."
Godiya sosai yasake yi mashi suka tafi basu bata lokaci ba suka tafi ANKA har unguwar dayai masu kwatance suka isa saidai duk wanda suka tambaya gidan Alhaji Yusuf sai ace kaf uguwar babu ko akaishi inda ba nan ba haka Taufiq yaita neman inda Baba suka koma bashi ba alamun shi,har saida sukai kwana ukku har ya fidda rai ya sake komawa unguwar da suka koma yaje wajen mai unguwa ya tambaya aka haɗa shi da wani bafade suka tafi cikin mota Gada wajen ukku ce duk inda sukaje basu dace ba,sai yamma wajen la'asar suka sauka gidan mai unguwar yankin dan hutawa suyi sallah nan bafaden ke gaya mashi dalilin zuwan su,sukai mashi kwatance yai mamaki duk da yasamu labarin issue din wajen Alhaji Tijjani lokacin da zai saima Baba gida da sunki yarda saida sukaji asalin abinda ya baro da Baba garin shi sannan suka saida mashi gida shiyasa yasan Baba,bai 6ata lokaci ba yace yagane Alhaji Yusuf ɗan Katsina wanda suke cema Yusuf Baƙo dayake Yusuf din biyu ne duk dashi kuma yan Katsina ne,shiyasa suke cewa Yusuf Bako sai agane Baba ake nufi.


Dadin da Taufiq yaji bana wasa bane yaima mutanen nan alkhairi duk da sunki amsa saida kyal suka kar6a,har kofar gida aka kaisu sukai sallama da Baba wanda yake kokarin fitowa daga gidan nashi,tsaye yayi lokacin dayaga Hussein,saidai fuskar shi ba yabo ba fallasa ɗauke take da annuri tabarma ya ɗauko masu a cikin gida ya shimfiɗa masu a compound din gidan cikin wani kanofi suka gaisa da baki yakawo masu drinks nan suka gaya mashi baƙo yayi ga yanda sukabi har suka gano gidan.

godiya Baba yai masu sosai suka tafi Taufiq ya taka masu yana masu godiya sannan suka shigo ciki shida Usama,zaunawa zasuyi kan tabarmae baba yace.

"Hussein ku shigo ciki mana."

Yaji daɗi domin a ɗarare yake,bin bayan Baba yayi zuwa falorn shi,bisa kujeru suka zauna zuwa yanzun suna da abubuwa a gidan ba laifi.

Zaunawa yayi yace "Maman Zainab kizo kinyi baƙo."
Toh cewar Mama dake cikin dakin ta.
Maida kallan shi yayi wajen Taufiq yace.

"Hussein ina kashiga kabarmu cikin ƙunci da damuwa miyasa kayi mana nisa."?

Kanshi ƙasa yaɗan sosa ƙeya yace.
"Baba tunda nabar gida kasar Turkey na wuce kaji inda naje."

"Ikon Allah amman baka kyautaba Hussein daga yau duk halin daka tsinci kanka, kada ka ƙara kokarin kauracewa iyayen ka hakan haramun ne kanajina."?
"Insha Allahu Baba."

"Sannan munji dadin dawowar ka Allah yaimaka albarka ya kareka daga dukkan wani sharri."
"Ameen ya rabbi."

Ɗago kanshi yayi yana kallan Mama dake tsaye tana shifɗe ajiyar zuciya tanajin wani irin daɗi aranta.

"Allah Sarki Hussein kaine?Allah mungode maka daka maido mana ɗanmu ya dawo garemu alhamdulillahi."
Dukawa yayi yana gaisheta har ƙasa isowa tayi ta daura hannun ta bisa kanshi tace.

"Allah yaimaka albarka Hussein sannu da kokari ɗana saida kanememu kenan,da' nagari Allah yaimaka zabin alkhairi arayuwar ka Hussein yasa jinkiri da Jarabawowin da yaimaka alkhairi ne Allah ubangiji ya jibinci al'amuran ka ɗana."
"Ameen Mama nagode kwarai,saidai ina mai baku hakuri dan Allah kuyafe mani nasan abubuwa da dama sun faru a sanadiya ta nazama Qaddarar ku,sannan nasaka duk wasu masoyana cikin taraddadi kuyafe mani dan Allah."

"Allah ya yafe mana baki dayan mu Hussein bakai mana komai ba,dan haka kada ka ɗaurama kanka laifi,kasa aranka Haka Allah Yaso."

Ahmad ne ya shigo a compound din gidan su yaga bakuwar mota da number CRC kuma asanin shi tunda suka dawo Anka duk wani wanda zaizo daga Caranci Baba ya dakile hanyar hakan,ko Dada waya kawai suke da ita,ba wanda yasan actually inda suka koma daga Tijjani sai Baban Asma'u daga nan ba wanda yasani koda Taufiq yaje gun Baban Asma'u abinda yasa baiba shi direct address ba, baisan ya karya alqawali kuma hausawa nacewa ta inda aka hau tanan ake sauka,yafi ganin kwara ya hadashi da Tijjani tunda shine silar komawar shi Zamfara,amman idan ƴan gari suka ce mashi ina Yusuf ya koma sai yace masu ya koma Sokoto wannan kenan.

Cikin gida ya shigo yana ganin Taufiq da gudun shi ya qadaddabe shi sai murna suke suna yaushe gamo sunjima suna gaisawa da isha'i Taufiq zai tafi Hotel ya kwana Baba ya hanashi dan dole ya sauka ɗakin Ahmad shi kuma Usama BQ aka gyara daman akwai gado da komai ya kwana acan.

Bacci Taufiq baiba haka Ahmad ya kwana suka suna fira abubuwa da dama ya gaya mashi da dalilin su na barin Caranci,da asalin barin gida da Aminatu tayi har zuwan ta gidan Yari duk ya sanar mashi duk yanda Taufiq yaso kada yai kwalla saida suka ziraro mashi zuciyar shi cikeda tausayin Aminatu,ashe shiyasa tace ta tsane shi tabbas dole zata dinga ganin shine yajaza mata komai alhali ba haka bane abunda ya fahimta Qaddarar shi da tata iri ɗaya ce kuma haka Allah Yaso ya Gansu,kiran assalatu akai daga bisa sallaya ya tada sallah yai nafila da addu'oi kafin suka tafi masallaci sukayi sallah karfe bakwai suka dawo gida ya dan kwanta tara daidai ya tashi yai wanka ya sauya kaya farar shadda ce yasha ajikin shi,goma da rabi ya fito falor yai kalaci suna fira da Ahmad.

Sha ɗayan safe Baba ya shigo falorn fuskar shi dauke da annuri gaisawa sukayi da ɗan nashi shima Kalaci yayi,sannan yafara aiki a wani file saidai ya fahimci kamar akwai abinda Taufiq keson gaya mashi hakan yasa ya maida kallan shi kanshi yace.

"Inajinka Hussein dagani akwai abinda kakeson faɗa mani minene."?

Kamar jira yake yace.

"Kawu daman akan maganar Aminatu ne inasan in sake ɗaga ƙara zuwa gaba,dan hukuncin da aka yanke mata gaskia banyi amanna dashi ba natabbata hakan bazai faruba Aminatu bazata iya kashe Asma'u ba."

Wani ciwo zuciyar Baba ta soma duk sanda za'ai mashi maganar ƴar shi zuciyar shi na raunana a dake ya kalli Taufiq yana boye raunin shi yace.

"Bayan da bakin ta,amsa laifin ta."?

"Baba duk da haka ba'abunda zai gagara inasan kabani haɗin kai."

"Kabar wannan zancen Hussein."

Sakkowa yayi ya duka yana aza hannayen shi bisa na Baba yace.

"Kawu kayi hakuri kabari in ɗaga case din nan asake dawowa dashi inaji a jikina akwai nasara insha Allah."

Mikewa Baba yayi yace.

"Fita Hussein bani bukatar wannan maganar daga gareka,inko har kasan ita takawo kabar mani gidana ban bukatar ka."

"Baba dan Allah kafahimce ni narokeka kataimaka mani kabani goyon baya kodan zumuncin dake tsakanin mu, kada ka duba alakar dake tsakanina da Aminatu dan Allah ka daukeni ɗanka na zumunci Baba."

N"afahimce ka Hussein kabar zancen nan Aminatu canne ya dace da ita tafi samun nutsuwa."

"Abba kayi hakuri dan Allah ka saurareni."


"Ya isa Hussein, idan ka tashi zumunci kofa buɗe take amman kada ka kuskura kai mani maganar Aminatu."

Dan dole Taufiq yatafi ranshi ba dadi,Mama ko kwalla take batayi zatan haka daga mijin nataba musamman dayace da ace Amina zata dawo tabbas zai aura mata Hussein miyasa ya koma haka.

ɗaki Baba ya shiga shima ranshi ba dadi.

Washe gari har Hussein ya shirya zai koma gida har zai tafi, sai kuma ya wuce Bakura gidan Alhaji Tijjani yanda yaga Taufiq ya tabbatar mashi da cewa ya gano gidan aminin nashi amman da gani ba nasara a tafiyar alamu sun nuna mashi hakan,gaisawa sukayi ya sanar mashi damuwar shi.

"Toh kabari gobe da safe insha Allah sai muje dakai har gidan nashi kila yabamu haɗin kai abinda kai niya ka daure kayi wannan shine zumunci Allah yabaka lada."
"Ameen Abba."

Washe gari kuwa suka koma Anka har gidan Baba saidai yai makakin ganin shi da Alhaji Tijjani badan yasoba suka shiga gidan cikin falor zama sukayi Alhaji Tijjani ya kalli Baba yace.

"Alhaji Yusuf nazo neman alfarma wajenka dan Allah kabawa Hussein dama ita rayuwa ba'ai mata haka ba'asan inda ake dacewa ba."
Shiru Baba yayi na sakanni sannan yace.

_Yar Mutan Kankia ce❣️_
Share
Pls
❣️

_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E27&28


"Alhaji Yusuf nazo neman alfarma wajenka dan Allah kabawa Hussein dama,ita rayuwa ba'ai mata haka ba'asan inda ake dacewa ba."
Shiru Baba yayi na sakanni sannan yace.

"Alhaji Tijjani ba haka bane,bansan Hussein ya sake saka kanshi cikin hatsari,shida Aminatu sun zama Qaddarorin juna kwara in dakile wannan abun da yake shirin faruwa,karfa ka manta Hussein ɗana ne nida mahaifiyar shi uwa daya uba daya muke taya zanso shima ya afkama halaka,wannan dalilin yasa na hanashi yayi hakuri kada azo ayi dana sani."

Idanun Baba sun kaɗa sosai kamar zayi kuka.

"Ba haka bane Alhaji kaidai kayi hakuri kabari yaje ya ɗaga wannan ƙarar,Qaddarar data rabasu ita zata sake haɗasu,kuma bakasan abinda Allah ke nufiba shiyasa ya dawo garemu bayan kowa yagama hakura dashi,dan Allah kasa albarka kabarma Allah ikon shi shine mai kowa da komai."

Jinjina kai Baba yayi alamun gamsuwa yace.
"Naji abinda kace amman ina mamakin yanda akai harya nemoka wannan yana nuna kai kabashi address ɗina kenan."?

"Eh saidai garin daka dawo kawai nafaɗa mashi shiya nemo gida da kanshi wannan ba abinda dubawa bane Yusuf mugoya mashi baya yaje ya gwada sa'ar shi,kaga bamusan mi gobe zatayi ba."

"Shikenan Allah yatabbatar mana da alkhairi,kai kuma Hussein Allah yaimaka albarka yatsare gabanka da bayanka."

"Ameen ya rabbi
Nagode Baba Allah yakara girma."
"Ameen."
suka amsa.

Sallama yaima Baba zai wuce yace.

"Komai kenan zuwa gobe muma zamuje ganin Aminatu saimu hadu a can din insha

Please Login or Register in order to submit comment