You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
mata na kashe kawarta da akace tayi, ASMA'U ABUBAKAR daga yau Litinin shekara ta.... Akalashin wannan Kotu ta wanke Amina sannan ta kwanceta daga ɗaurin rai da akai mata a gidan Yari bisa sakin layin na 578 sashi na 330,sannan Kotu ta ɗaure Junaid Jamilu da Hafsat Adam sai Mufida Shehu daurin rai da rai agidan Yari sai kuma Khalid Lawal ɗaurin shekaru huɗu,sai Karima Tasi'u da Saminu Idris su kuma kisa ta hanyar rataya."
Gam gam Alqali ya buga gudumar Court duk aka mike nan na zu6e ƙasa ina kuka.
Mama sukazo suka rungume ni da Mum, maman Husna,Anty Murja.
Yaya Taufiq kuwa sujudar shukur yayi.
Dada kuwa ba abunda take cewa sai.
"Allah ya tsine maki albarka Hafsat."
abinda take cewa kenan tana kuka su Umaima harda suma, saida tayi.
Dr JJ kuwa kuka yake yana kiran.
"inason ki Caranci,Beauty ina kaunarki."
haka aka kamasu cikin Unkwa aka fita dasu,nima Atika ta kamani da Yan sanda suka fita dani mutane suka bimu riii cikin motoci sai gidan Yarin Kurmawa bakin shiga aka dakatar da kowa aka shiga dani ina kuka office aka shiga dani,aka ɗauko files akai cike cike a cikin shi sannan aka bani nasa hannu.
Atika ta rungume ni tana kwalla.
Ogam Adam yace kalleni cikin farin ciki yace.
"Congratulation Aminatu Yusuf Caranci yau dai Allah yasa.....
_Yar Mutan Kankia ce❣️_
Share
Pls
❣️
_*HAKA ALLAH YASO❤🔥*_
*NA*
_YAR MUTAN KANKIA❣️_
_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_
_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_
S4/E49&50
End❤🔥
_*RELEASED FROM JAIL*_
Congratulation Aminatu Yusuf yau dai Allah ya wanke ki daga wannan ƙangin rayuwar Allah yaima rayuwarki albarka yasa kifita cikin nasara."
Murmushi nayi nace "thank you Oga Adam,ameen ya Allah."
"Bakomai Dago Allah yatsare hanya sai wata rana."
yana cewa Dago na tuna dasu Cankwai nace.
"Dan Allah inasan zan gana dasu Cankwai."
"Bakomai Atika rakata."
aka aka rakani ina zuwa suka rungume ni,muka hau kuka sainaji inama bazamu rabu ba haka mukaita kuka inajin kewar su araina.
"Dago dagaske an wankeki daga zargi."?
Gaza basu amsa nayi tsabar kukan da nikeyi saida nudding kaina dana dingayi.
"Muna tayaki murna Amin Dago Allah yaima rayuwar ki albarka ya haɗaki da duk wani alkhairin ki duniya da ƙiyama."
"Ameen Magajiya."
nace ina kuka.
Sake riungumeni sukayi kuka dai nayi shi harna gode Allah.
"Dago kiyafe mani zalincin danai maki dan Allah."
Nayafe maki Magajiya nima kuyafeni dan Allah duk na yafe maku."
"Mun yafe Dago Allah ya tsare yakaiki cikin ahalinki lafiya muna maki fatan alkhairi."
"Ameen nagode kwarai."
Kuɗina na amsa wajen Atika na basu nace su raba haka muka tafi sunata daga mani hannu suna kiɗi da silbobi suna murna Dago released from jail.
haka na isa office din Adam aka bani kayana anmasu number haka na shiga wani daki na saka Personal dina Allah Sarki shekaru kusan huɗu da ciresu kamar yanzun aka bani kayan Yari yau gashi na maida nawa na cire kayan Yari kayan da kowa ke neman tsari dasu bare ya shiga gidan,saboda bala'i kunci dake cikin gidan,rashin yanci ya tabbata a gidan Yari Allah kai mana tsari da rayuwar Yari da dukkan musulmai baki daya ameen.
Ina mikoma Adam kayan dana cire ana shigowa da Anty Hafsat taci kuka ta koshi gabana aka mika mata kayan dana cire akace ta shiga ciki ta sasu,hakan ya nuna ɗakin su Cankwai za'a wullata nasan kashin ta ya bushe tana son ta bani hakuri naki sakin fuskata fita mukayi har waje sai naji wani irin iska na musamman na ratsani.
da sauri Ya Taufiq ya taromu ya bude mani motar shi na shiga baya Usama yajamu muka tafi nidai bansan ina aka nufa dani ba.
banda Murmushi ba abinda Ya Taufiq ke zabga mani nima haka munyi tafiya mai nisan gaske ashe Caranci muka wuto da motoci bayan mu kai akace amarya aka dauko gidan mu aka tsaya duk muka fito iska ke ratsani ina kallan garin mu na haihuwa ina tuna kalubale dana fuskanta a agarin mu,take Husna ta fado mani arai ganin kannen ta sun rugo sun rungumeni harda Mina ya'ta daukar ta nayi duk da,ta girma zatai shekara bakwai a duniya na dauketa mukai gidan mu sai kuka nikeyi su Mama,Mum,Ummi,Dada,Maman Husna,Anty Mubaraka,Ummin Ya Mutallib,Baba,Abban Ya Taufiq, Baban Husna,Ya Taufiq,Ya Tariq,Ya Samir kai da sauran mutane duk anzauna falorn Baba wanda shi kanshi raban shi da zama haka tunda suka koma Anka,daman ansa angyara gidan kafin mu iso,nima zama nayi ƙasa Zainab ta nanike mani ita da Hauwa'u sai Haidar saman cinyata Mina na gefena ina kwalla musamman innaga Mina dake kama da Husna sak hakama Haidar dan dai shi ya dauki hasken ta sak amman yafi kama da Ya Abdallah,Baba yace.
★★★★★★★
"Alhmdullh ala kulli halin godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai daya nuna mana wannan lokacin mai dinbi tarihi yau gashi Allah yasake hadamu cikin aminci ba abinda zamuce saidai mukara godema Allah (SWT) dayima annabin rahama salati,Allah yakara tsaremu daga kowane sharri duniya da kiyama."
"Ameen ya rabbil alameen."
Muka masa baki ɗayan mu.
"Gaskia kam lamarin nan saidai Allah,shi kaɗai yasan dalilin faruwar wannan al'amari tabbas munga mu'ujiza kuma shi Allah ba yanda baiyin lamarin shi komai ke faruwa haka ya hukunta Allah yasa Jarrabawar da ya qaddara mana muncita Aminatu barka da arziki Allah yaimaki albarka yakara tsareki daga kowa ne sharri Allah yai maki zabin alkhairi a cikin rayuwar ki."
"Ameen Mum nagode."
Na amsa ina goge kwallar data cika mani idona.
Kama hannuna Maman Husna tayi tace.
"Ya'ta barka da arziki nagodema Allah daya hukunta kika dawo cikin mu,wannan bakaramin arziki bane kisani komai ya faru dake Haka Allah Yaso sai kikara gode mashi kuma kisaki ranki ki daukar kamar komai ba faru ba,mudai ya' kike a wajen mu muna sonki kuma muna kaunarki ya'ta."
"Insha Allah Mama kisa aranki Husna ta tafi kuma tadawo domin ku iyaye haka na dauke ku,kuma insha Allah duk abinda ya' zataima iyayen ta zanmaku shi a rayuwata insha Allah bazaku taba kukan rashin ya' ba wannan Alqawali ne,nagode maku da kuka daukeni ya' kuka shaidawa duniya Allah yasaka maku mafificin alkhairi."
"Ameen Amin Dagona." cewar Abba yace.
"Bansan ta ina zanfara neman afuwarki ba Aminatu,tabbas nayi abubuwa da dama marassa dadi na cutar da rayuwar ku nabiyema son zuciya naƙiki Amina dan kawai son zuciya da zigi na mace dan Allah ya'ta kiyi hakuri akan kiyayyar dana dinga yi maki,bada gayya naƙikiba Amina,dan Allah......
hade hannayena nayi sigar ban hakuri nace.
"Abba dan Allah kadaina wlh bantaba kullatar ka da komai ba Abba,nasan duk abinda yafaru damu harda rashin yi maku biyayya da mukayi mu zamu nemi afuwar ku dan Allah kayafe mana mun tuba."
"Ya'ta ba abinda kukai mana Allah ya yafe mana baki dayan mu."
"Ameen ,gaskia yau din nan bansan taya zan misalta farin cikin da nike jiba,Allah yai mana albarka baki dayan mu yakare mu daga sharrin mutun da aljan da dukkan sharruka kuma Allah yabamu ikon yin hakuri da iyalan mu baki daya."
cewar Dada.
Ameen muka amsa,ranar dai haka kowa yaita nuna farin cikin shi duk da haka saidai Mama tai Smile tanajin dadi maganar kirkima ta gazayi.
"Aminatu nayi nadama dayawa a rayuwata sai nikejin nine ummul aba'isin faruwar komai,inama ace ban fara furta kalmar so agareki ba! inama ace lokacin da dan uwana yace yana sonki na kwatantama mahaifina gaskia ya aminta,akan furucina yau gashi mahaifiyata ta halaka! akan furucina Mami ta jefamu cikin kunci kunya gami da tashin hankali bantaba zatan zafi da kiyayyar da Mami ke maki zaikai su ga aikata wannan bala'in ba,ashe adawar da mahaifiyata keyiwa Hussein akan auren ki ashe yakai haka har gashi takaiga kisan baiwar Allah bataci bata shaba! Miye laifin Asma'u dasu Mami zasu aikata hakan agareta dan kawai itadin tafi kusanci dake? Dan atozartaki duniya ta tsine maki kawa ta kashe kawar ta kuma aminiya? Kaicona komai yafaru nine sanadi dan Allah Aminatu da Hussein kuyafe mani nayi danasin shiga tsakanin ku,yau gashi akan tarayyar ku mutane da dama sun halaka Allah kadai yasan tsakanin ku anyi jayayya da ikon Allah gashi ya nuna mana kudurar shi...
Kuka ne ya kufcema Ya Samir ba wanda yahana shi,fatar da cikin shi domin yana cikin tashin hankali bayyananne.
Cigaba dacewa yayi dan Allah kuyafe mana nida yan uwana."
Sauke hannun shi Ya Taufiq yayi shima idanun shi sun sauya kala yace.
"Ya Samir kadaina kuka tabbas mu,kanmu muna bakin cikin lamarin nan,ka dauki Qaddara tabbas Mami ta jefa kanta a halaka saidai muce Allah ya yafe mata damu kanmu baki daya kuma kada blaming kanka danka ce kana son Minal,kuma komai kaga ya faru kasa aranka Haka Allah Yaso dan Allah kada kadamu kanka Ya Samir."
Ya ida maganar cikeda da damuwa.
"Kayyah Hussein ni kadai nasan yanda nikeji nidai kuyafe mani dan in samu sassaucin rayuwa."
"Munyafe maka Ya Samir,kuma ina godiya da gudummuwar ka akaina Allah yasaka maka da alkhairi yabar zumunci."
Ameen suka amsa.
Barrister Bashir ya tashi zai tafi godiya sosai akai mashi musamman ni haka sukai mashi rakiya ya tafi.
Nima dakina na shiga wanda ya zamar mani bako a wajena zan iya cewa rabona dashi shekara kusan shidda kenan kallan shi kawai nike ina tunano abubuwa da,dama da suka faru dani musamman idan Baba yai mani tsakani da Ya Taufiq saidai in fada bisa gadona insha kukana Allah Sarki rayuwa.
Aje Haidar nayi bisa gado na bude wardrope ga kayana jere abun su,rufewa nayi nadawo gefen Haidar na zauna sai wasa yake wanda yake shekaru na biyar kenan sai ɗumi yake mani.
Momi zaki sai mani Choculate ko? uncle Kabir yace zai siya mani."
Yana wasa yake maganar shi hankalin shi kwance abun shi.
Shafa gefen fuskar shi nayi inajin saukar kwalla a idona ina karajin so da kaunar jinin Husna araina.
"Eh ɗana zan siyamaka ina bakin shan Choculate din yake.?"
"Haaah."
ya bude mani bakin shi yana nuna mani rungume shi kawai nayi ina kuka mai tsuma rai najima a haka sannan na sake shi Mina ce ta shigo dakin tace.
"Haidar kazo inji Uncle Kabir."
"Aaa Choculate Momi zata bani."
Nidai kallan su kawai nike musamman yanda suka saki jiki dani sosai kamar sun sanni.
"Ita zai baka ka taso Haidar."
Tafara jan shi,yaki yarda saida na duka gaban shi nace.
"Kaje gun Uncle inka dawo zan siya maka Choculate kaji."
Toh yace yabita suka tafi sai murna suke.
Tausayin su yakara kamani ganin tsantsar kuruciyar su,basu damu da rashin mahaifiyar suba,sun dauki kowa matsayin uwa ba ruwan su,sai hidimar su sukeyi Allah Sarki rayuwa!
Kukane ya kubce mani na fada bathroom danyin wanka inajin kunci araina,wannan kenan.
**********
Washe gari da safe su Mum,Ummi da Anty Murja suka shirya zasu tafi gidajen su gwanin dadi kowa saijin farin ciki yakeyi daman Already Abba da Ya Tariq sai Ya Samir sun tafi tun jiya su Mum ne suka kwana haka driver dinsu yazo ya tafi dasu,Ahmad ya dauki Ummi zuwa Kano shi kuma Ya Taufiq ya tafi da Anty Murja katsina,ranar yini akayi ana shigowa yima Mama jaje da murna.
Anataya ta murnar dawowata wasu na mata jajen yanda lamari ya kasance harda Yayar ta a ciki kowa da abun da yake faɗi.
dayawa daga cikin yan unguwar mu sun gaza shigowa gidan mu tsabar kunya da,dana sanin abinda suka aikata mani,musamman wa'anda sukace sai sun kashe Ahmad ko haɗuwa da Baba sukayi sai su gudu sunajin nauyi da kunyar shi matuka.
akwai wani malan Lawal yafi kowa tsinata a unguwar mu saboda shi har Baba saida ya daina fita sai in tazamar mashi dole(Sallah) sannan zai fita tsabar yanda aka sako shi gaba da habaici da kananun maganganu.
Yanzun tunda akai Komai gaban su Kotu sai ya kasance Baba ya zama surikin shi,daya ganshi saiya gudu gashi ya bada shaidar zirr ko masallaci da sun hadu da Baba saiya boye tsabar nauyin Baba dayake ji.
Duk abin nan Baba na lura da M.lawal saida yabari zai fita ya riko shi,duk yasha jinin jikin shi.
"M.lawal akan mi zaka maidani sirrikin ka dan Allah kadaina wannan gudun nawa banjin dadi sam,ba kai kadai ba duk wanda yaji abinda yafaru dole yaji ba dadi,indai abinda kayi manine wlh nayafe maka duniya da lahira,ai rashin sani yasa kai mani haka dan Allah kadaina wannan abun banjin dadi ko kadan."
Duk sai yakara jin badadi.
Cikeda farin ciki yace
"Nagode maka Alhaji Yusuf yanda kayafe mani Allah yasaka maka da mafificin alkhairi ya yafe mana baki daya nagode maka."
"Bakomai nima nagode Allah yabar zumunci,,
Ameen."
Tunda akai haka sai ya kasance tsakanin M.lawal da Baba zumunci ake mai karfin gaske.
_Ya Allah yakasa mu kasance masu yawan yafiya kuma Allah karabamu da zargi arayuwar mu._
*Shiyasa ba'ason mutun ya yanke hukunci ko bada shaidar zir danka wulakanta dan uwanka musulmi Allah yasa mudace,ameen.*
★★★★....★★★★
Bayan kwana biyu ina zaune cikin ɗakina muna haɗa kaya zamu koma Anka hankalina yadan yafara kwanciya ina cikin zuge troly dina naji Jidda tafasa ihu,da gudu nayi waje dan ganin abinda ke faruwa Ya Taufiq ne ya cillata sama shine ta saki kara duk ta razana,ice cream ya mika mata tanata murna,fuskata dauke da murmushi,shima smile din yai mani yana mani wani irin kallo mai ma'anoni iri iri sunkuyar dakaina nayi zan koma daki,abinda naji yace shiyasa na tsaya.
"Ki sameni Sitrum din Baba."
Toh nace mashi ina zuwa ɗaki na sako gyalena sannan nasaka turare mai sanyin kamshi na fita zuwa falor.
Iske shi nayi sungama gaisawa da Mama,gwanin ban shi'awa,Zainab ta aje mashi ruwa da lemo.
Ida shiga nayi da sallama a bakina Mama ta fito zuwa tsakar gida,inajin idanun shi akaina,saidai inajin dan faruwar gaba kadan kadan.
Zama nayi bisa kushin dake facing dinshi,sai nasamu kaina da kasa hada ido dashi yai mani kwarjini da yawa.
"My Happiness ko bakiji dadin zuwana bane."?
Girgiza kaina nayi ina wasa da yatsun hannuna nace.
"Aaa naji ina wuni.?"
"Lafiya lau Baby na,ya gajiyar Shari'a i hope kin maida komai ba komai ba ko.?"
Dagowa nayi na kalle shi,shima ni yake kallo ko keftawa baiyi samun kaina nayi da murmusawa na maida kaina ƙasa nace.
"Yayana kayi kyau sosai saidai ka rame miyasameka."?
Sakkowa yayi bisa kushin din daya zauna yadawo gabana ya duka yana facing dina.
Wani irin kunyar shi naji takamani sadda kaina nayi kasa ganin irin kallan da yake mani idanun shi sun sauya launi.
"Princeses."
"Na'am."
na amsa mashi.
"Daga kanki ki kalleni dan Allah."
Kallan shi nayi ido cikin ido ban musa mashi ba.
"Yau kikafara jin kunyata har haka.?"
Sadda kaina nayi narasa dalilin dayasa nikejin nauyin Ya Taufiq,sai nagane dalili blaming dinshi danayi da maganganun dana fada mashi agidan Yari su suka dawo mani akai ga nauyin shi duk ya addabeni.
Cikin sanyin murya nace.
"Dan Allah Ya Taufiq kayi hakuri nasan naga laifin ka nagaya maka maganganu marassa dadi bansan miyasa nayi.....
Daura yatsan shi yayi bisa lips dinshi yace.
"Sheet
Aminatu?"
"Na'am."
"Kidaina bani hakuri nasan halin da kika tsinci kanki kuma duk ta sanadiyata komai ya sameki duk dan arabamu komai yafaru akan mi bazakiji kin tsaneni ba?dan Allah Babyna ki manta kowa da komai nidai kece farin cikina Minal soyayyar ki ba abinda yaragu a cikin zuciya ta,Minal kullin kaunar ki kara ruruwa take a cikin zuciya inama mukasance ma'aurata ki zama uwar Ya'yana dana gama more rayuwata ina kaunar ki Minal."
Idanuna na rufe nasake budesu,kwalla na ziraro mani a fuskata inajin kalaman Ya Taufiq har cikin kasan zuciya ta,kalaman da sukafi komai yiman dadin sauraro kalaman da suka kasance mafarkina muradina abin cikar burina,kalaman dana daɗe da fidda rai da sake sauraron su,ashe akwai ranar dazan kuma jin zazzakar muryar shi mai tafiya da duk wani kuncin zuciyata inama iyayen mu,su aurar damu ga junan mu inama su yafe mana wannan karan taya zasu karbi soyayyar mu,nidai Allah yasani banji zan iya rayuwa batareda Ya Taufiq ba domin shine cikar burina....
"Minal."naji amon sautin shi cikin kunnuwana,hakan yasa nadawo duniyar tunani.
"Inama Qaddara tasake hadamu a wannan lokacin Ya Taufiq kasani kaine cikar burina na soka zanci gaba sonka har karshen rayuwata saidai ina tsoron abu daya."
"Minene Aminatu.?"
Yai mani tambayar a raunane.
"Kada Abba ya hanamu kasancewa amatsayin ma'aurata inajin tsoron wannan ranar bansan ya zanyi ba."
"Hakama bazata faruba kisa aranki mun gama samun cikar burin mu insha Allahu."
"Hmm Allah yasa hakan amman....
"Ya isa Minal kada kisa zuciyata, ta raunana mana ki mana fatan alkhairi dan Allah."
"Shikenan Allah yaimana Jagoranci."
"Ameen my Life."
Shiru ya biyo baya shi yana aikin kallona ni kuma ina wasa da hannuna kuma ina satar kallan shi.
"My Angel Close ur eyes."
Kallan shi kawai nike ina smile tareda kallan tuhuma.
Pls yace yana hade hannayen shi.
Rufe idanun nawa nayi.
"Give me ur hands."
Mika mashi nayi nidai ina mamakin mi Ya Taufiq keson yimani.
Ji nayi ta aje mani abu bisa hannayena.
"My Queen open it."
A hankali na budesu na sauke su bisa hannuna tareda waro idanuna waje ganin Suprise din da yai mani.
Waya ce sabuwa dal cikin kwali ya dora mani kirar iphone rasami zancema Ya Taufiq nayi saidai kallan shi da nikeyi.
Waving face dina yace.
"Yadai.?"
Sauke ajiyar zuciya nayi nace.
"Amman wayar nan gaskia bazan ansaba,abubuwan dakai mani kadai sun isa nagode maka Allah yasaka maka da mafificin alkhairi kataimaki Ya Taufiq ka sadaukar da farin cikin ka akan nawa dawainiyar zatayi yawadan Allah kafahimce ni."
Ɗan hafe rai yayi yace.
"Aminatu kinfi haka agareni dan nabaki waya minene zakice bazaki karba ba,hakan yana nufin baki sona kenan."?
"Rashin ansar waya bashi ke nuna bansan kaba,bansan abubuwa....
"Ya isa indai kikace bazaki karbi wayar nan ba tabbas baki sona,kinsan anfanin ta gareni taya kika zatan zan nisa dake kuma ace ko waya bamuyi saidai in baki sona dama kuma bakiyi missing dina ba."
rasa mi zance mashi nayi, zanyi magana naji muryar Baba yace.
"Ba'a maida hannun kyauta baya Aminatu ki kar6a,Hussein zai maki abinda yafi waya,tunda harya sadakaur da rayuwar shi dan inganta taki rayuwar minene dan yabaki waya."
"Nagode Allah yasaka da alkhairi."
Nace inajin dadi araina.
"Ameen ya rabbi."
"Hussein yaushe kazo Ya Umma.?"
"Lafiya lau Kawu najima da zuwa."
"Hussein kanata dawainiya da Aminatu,bansan taya zanfara godemaka ba,saidai ince Allah yasaka maka da mafificin alkhairi kuma Allah ya kareku da dukkan wani sharri ya kauda idanun maƙiya akan ku yai maku albarka."
"Ameen Babana mungode."
Cikeda farin ciki Ya Taufiq ya amsa addu'ar Baba.
Dan jim kadan mukai,Baba ya mike ya fita waje.
Taba fira mukayi sannan ya mike yace.
"Babyna zantafi sai munyi waya dan Allah kisa layin ki,yau pls."
Insha Allah, My hope Allah ya tsare mani kai yasa kaje gida lafiya ina gaida Mum."
"Ameen my life."
Fita yayi ina mashi bye bye a falorn Mama ya iske Baba yai masu sallama ya tafi.
Wani irin missing dinshi naji ya mamayeni,haka rayuwa ta kasance alhmdullh.
Washe gari mun shirya zamu tafi Anka saiga sallama koda Baba ya fita iso yaima su Ya Mutallib ne da Dadyn su,har falor Baba ya shigar dasu sai nan nan yake dasu.
Yana masu sannu da zuwa.
Ruwa na kawo masu muka gaisa cikin girmamawa.
Nafita zuwa falorn Mama.
Dambun nama tace inkai masu dauka nayi zuwa falorn da suke zaune har zan shiga naji Alhaji Abdullatib yana cema Baba.
"Shiyasa nace bari inzo da wuri muyi magana dakai,sai muji yanda zamu bullowa lamarin nan,insan samune kar adauki lokaci mai tsayi asamasu ranar auren."
Kunnuwana ya amsa kuiwa ina tambayar kaina suwa za'asama rana wace magana Daddy keyi mike shirin faruwa?
Gyaran murya Baba naji yace........
```HAKA ALLAH YASO kenan wanda yake dauke da darussan rayuwa iri iri mai ban mamaki al'ajabi ban takaici da tabuwar zuciya gami da``` ```ilimantarwa, fadakarwa harma da tunatarwa Allah yasa mu anfana da darussan dake cikin shi ameen.
Sai mun hadu a cikin littafin LOKACINE last season five,wane lokacine wannan dame yake tafe da kuma wane salon zai zo maku andaice Lokacine nima Yar Mutan Kankia nace LOKACINE.```
*Shin wace magana Alh Latib yakema Baba?*
*Wace amsa Baba zai bashi?*
*Ya soyayyar Minal da Ya Taufiq zata kasance,da wane salon zatazo?*
_Wohoho Allah gwani na Annabi Muhammad (SAW)._
_Hausawa nacewa Wasa Farin Girki_
*Kudai ku kasance da ALQALAMIN👇🏻*
_Yar Mutan Kankia❣️_
_Godiya ta musamman ga dukkanin masoyana hakika kudin na dabanne akowane lokaci kune abin alfaharina kusani yanda kuke nuna mani kauna nima ina kaunarku a kullin inaganin_ _sakonnin ku ta kowane fanni banda_ _bakin da zan gode maku saidai ince rabbi yabar kauna,musamman Commenters and_ _Posters Allah yabiyaku da alkhairinsa._
```Ina godiya da fatan alkhairin ku agareni Allah yabar kauna ameen.```
*Ina rokon Allah ya sadamu da mafificin alkhairi ya shirya mana zuriyar mu,wa'anda basu da aure Allah yabamu mazajen aure na kwarai mutanen kirki Allah ya wadacemu da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan kasar tamu baki ɗaya da makotan mu ameen ya hayyu ya qayyum🤲🏻*
Share
Pls
❣️
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels