Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ledar na watsar.

"Ki amsa garin kwaki ne dan munsan zai maki anfani gashi ko."

Amsa nayi nadan juya laidar ko tiya bai kaiba,natsani komai daga garesu matsawa nayi kusa da step din daya rabamu nace.

"Ai daman kinyi kama da kalar garin kwakin zaki iya tafiya dashi nasan tsohuwa na buƙata."
Na ida maganar ina sakin murmushi a fuskata.
A fusace tayo kaina tace.
"Ke Aminatu zan balla......

"Haba malama dan kunga kunsamu enough time shine kuke ɗaga mata hankali daga waje nafara jiyo faɗan ku,ku fita hakan nan."
Cewar G.Atika

tafiya sukaiyi suna mani wani kallo mai nuna tsantsar tsana nida Nusaiba.
tafiya mukayi jikina a mace.
Ranar na wuni ina mamakin halayen su Anty Hafsat,araina.


_AFTER SOME MONTHS_
Wasa wasa watana Goma cif a gidan Yari amman ba alamun yan gidan mu,zasuzo ganina ada ban damuwa da rashin zuwan su saidai yanzun nafara damuwa nasan halin mahaifina matukar ya share abu to hakan na nufin ya fita shirgin shi kenan yayi fushi,sai kuma hankalina ya tashi ina ganin kodai shima yana tunanin zan iya kashe Asma'u!

Duk da yana fushi dani hakan lamarin nan yafaru, amman basu zomani ziyaraba gashi wasa wasa wankin hula na neman kaini dare sai lamarin ya dawo mani sabo ga zuwan dasu Anty Hafsat sukayi yakara jefani cikin rudani mi hakan ke nufi haduwarsu tana nuna akwai alaka mai karfi a tsakanin su,musamman yanda take gaya mani maganganu na kiyayya son ranta agaban Mami da ace zuciyar ta fes take na tabbata zataji kunyar idanun Mami kodan kada tayi mata dariya.

Duk da an dauki watanni da zuwan su wajena amman na gaza mantawa da abun araina.

Najima ina taraddadi a araina gashi ina kewar iyayena gefe guda Husna nike tunowa ga tarin tausayin ya'yan ta data bari ya addabi zuciya ta,inalillahi wa'inna ilahirraji'un wannan wace irin Jarabawar rayuwace lallai kam Haka Allah Yaso.


*******
bayan sati guda Baban Amina ne,zaune bisa kujerar falorn shi ya buga uban tagumi sannan yaima silin ƙuri da idanu ko keftawa baiyi hawaye keta zirara ta gefen kuncin shi,damuwa iya damuwa yana cikinta.

Mama tashigo hannunta dauke da farenti ta daura drinks a sama,tayi sallama baijitaba har saida ta zauna gefen shi ta bubbuga shi.
"Alhaji³.
A kiɗime ya kalleta tsabar bai masan tanayi ba.

tunanin nan yaka mata ace ka hakura dashi kodan lafiyar ka,kaga ance hawan jininka yahau over sosai ko yaushe heart attack na iya samunka ka rage damuwar nan dan Allah addu'a itace mafita."
A raunane ta ida magnar duk tagama damuwa

"Khadijatu ban tunanin zan daina kukan rasa Mamana har karshen rayuwata,ina kewar ya'ta sosai sai yanzun na tantance wane kalar so nikema ya'ta,taimin nisa nayi dana sanin juyawa ra'ayin ya'ta baya nacuci Aminatu sosai Allah kayafe mani,yanzun inasan ganinta amman kunyar hada ido nike da ya'ta bare inkai mata ziyara gashi yanzun watan ta goma ba keyata matsayina na uba agareta minene mafita Khadijatu."?

"Hikkika anyi kuskure amman inada mafita."
"Minene ita."
Cewa tayi.

"Sati mai zuwa kashirya muje muga halin da yarinyar nan take ciki duk da bazamu iya cireta a cikin Qaddarar da take ciki ba amman zatasamu sauki aranta tabbas akwai ciwo musamman idan zamu taho mubarta dole mu karfafa zuciyar mu dan tata zuciyar ta karfafa kada mu nuna mata tamu gajiyawar ta hanyar nuna mata karaya da kambaba halin da take ciki kamar ta dawwama kenan aaa addu'a itace zamu kara karfafa mata guiwa ta dingayi a matsayin mu na iyayen ta."

Karfaffar aziyar zuciya ya sauke yace.
"Hakika kinyi gaskia Khadija da tuni nabi taki shawarar kila da halin da na tsinci kaina bakai nan ba amman nayi burus dake ina ganin nafiki kaifin tunani da hangen nesa ashe ba haka abin yake ba,dayawan maza abindake cutar damu kenan rashin bin shawarwarin matan mu,sai muce ai macece karamin tunani ke gareta alhalin ba haka abin yake ba,dayawa ta hanyar mata ake samun mafita nagode naki matata Allah yabiyaki da aljanna madaukakiya."

"Ameen ya rabbi Allah yakawo mana mafita."
"Ameen."
cewar Ahmad da shigowar shi kenan duk da baisan mi iyayen nashi ke cewa ba amman yasan ta tsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi.
Baba ya kalleshi yace......
_Yar Mutan Kankia ce❣️_
Share
Pls
❣️

_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_



S4/E13&14



"Ahmad ranar lahadi zamuje ganin Antyn ku insha Allah."
"Alhmdulillah danaji dadin hakan Allah yakaimu lafiya."

"Ameen ya rabbi,zamuje dukanmu domin ta ganmu nasan zataji dadin haka."
Cewar Baba.
"Sosaima kuwa Allah yakaimu lafiya."
"Ameen."



"""""""""""""""""
Ina cikin bacci da bai jima da dauka taba zan iya cewa tunda su Anty Hafsat sukazo bacci ya ƙauracewa idona kamar abin sihiri da kyal nike samu inyi bacci saidai inyi sallolina in addu'a wani bima ibadar kasata nikeyi duk narasa gane kaina.


Baccina nike cikin jin dadi naji saukar ruwa masu masifar sanyi bisa jikina a hargitse nata shi ina zazzaro idanu dan inajin ruwan har cikin kunnena Cankwai ce tsaye akaina ta rike kugu tana yan jijjige jijjige tana ƙasƙas da chewgam bansan ina tasame shiba amman tana yawan cinshi kana ganinta kaga cikakkar karuwa.

"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un."
nafurta.
na mike bisa kwalin da nike kwance daman ta hanani kwana bisa gadona sai dai ta hade katifata da tata tayi kwance kamar gidan tsoho,inaji inagani saidai in kwana kasa matukar inasan lafiyar jikina.


Raina yagama baci zuciya ta tafasa saidai shayinta da nike yahanani in nuna mata hakan a zahiri nasan kwanan zancen.
sauran ruwan dake cikin botikin hannunta taci gaba da kyaramani shi daga saman kaina yake sauka cikin kayana,nakai karshe a kulewa har nafara ganin bishi bishi daman matukar raina ya baci nakan samu kaina cikin irin wannan situation din kuma jikina zai hau kyarma.

"Dan gyatumar ki bazaki wuce ki debo mani ruwan wankaba ko saina zaneki cikin sanyin safiyar nan."

Zuciyata, ta halba bansan na wawuro kafafaun Cankwai ba na tangrata da kasaba,ta fadi cikin ruwan dake malele a tsakiyar dakin namu ban watata watata ba,kafin ta yunkura ta mike nahau jibgarta cici karfina nike kai mata duka ta fuska hanci wuya da tsakiyar bayanta nai mata duka yafi talatin takasa yakiceni bare tasamu damar dukana.

Su Mairo sukahau salatai suna son suzo su shigar mata sunajin tsorona musamman Salame datasan haduwar bazatayi dadi ba,kallabina ya kwance dayake inada yalwar gashi kuma kaina ba kitso duk da ina tajeshi zan iya cewa ya dankare saboda rashin gyara hakan ya bata damar janyo jelar gashina taja da karfin ta har saida na saki kara kadan.

Nayi nayi in kwace kaina na gaza ganin ba yanda zanyi da Cankwai tana iya ɗabemani gashin baki dayan shi nima kama nata nayi da karfin bala'i naja iya kokarina duk da bata da gashin kuma shukku akai mata.

Sai zafin jan gashin da naimata ya gigitata tahau ihu nima zafin abinda take mani ya gigitani ta saki nawa niko naki saki gam na rike shi.


Duka tahauni dashi sosai take dukana naki saki saboda nafita hayyacina tsabar bacin rai ban ganin su Salame sosai.

Nidai naji abu a hannuna amman ban damu dakoma minene ba nasan dai bazan saki nata gashin ba tinda taki sakin nawa gwara kowa ya jigata,kwada ihun da tayi yasa nadawo hayyacina amman still biji biji nike ganinta.

"Inalillahi,Dago daman ke mayyace kika tugema Cankwai kaikainiyar gashi har guda ukku.?"
Cewar su Mairo

da ido nabi hannu naga gashin Magajiya hannuna har guda ukku a kitse a tsorace na yarda shi itako harda kashin wahala a wando duk dakin ya dume da wari ga lokacin karfe shidda ko ma'aikata basu kaida isowa ba.

"Inalillahi wa'inna ilahir raji'un Amina ni kika tugema gashi."?
The first time data kirani da sunana kenan arayuwata.

"Eh an cire akwai abinda zakiyi.?"
Nafada cikeda tsoro a cikin zuciya a zahiri kuwa a dake nike.

Ɗaga katifarta tayi tazaro zabgegiyar bulalarta ta wayar wuta a boye take ajeta ta shaudaman,sumane kawai banba saida na saki ihu,kamar mahaukaciya na haye Cankwai dake kokarin mikewa ta zaneni kokowa sosai muke tanasan zaneni naci dununta inasan in anshe bulalar nima in zaneta,tanaja ina ja har Allah maikowa mai komai ya bani sa'a na kwaceta nahau lafta mata ita ajiki gashi itama tajike tau tau haka bulalar ke sauka jikin Cankwai.

Kwarara ihu take gashi na riketa gam,sauran neighbours dinmu sai ihu suke dagaji na murnane.

Zane mana ita da kyau Da'go daman ta addabemu ba yar banza kashi, sai Dago Allah yatai makeki."
Batasu nikeba fatana in galabaitar da magajiya nasan muddin tasamu ta ingijeni zata iya kasheni nasan wacece ita saboda dukan datai mani a gidan nan yafi cikon kwando jikina da dama tabbunan dukan Magajiyane.


Ƴar6a mata wata nayi ta saki azabbbar kara da kaina na daka tsalle nakoma gefe nayi zatan wani bala'in tagani jikina yahau 6ari,haka tafadi yabar tana kwarara ihu.

Mairo da Salame suma ihun suka hauyi.
bubbuga ƙofofi Prisonors sukeyi da gudu securities suka iso a yashe suka iske magajiya gasu Mairo na ihu sunga kanwar uwar su magashiyan waje akayi damu aka dauki Cankwai daketa tsamin kashi dagani har ita under punishment aka samu basu damu da warin da take ba.

Kwalla nikeyi kawai nagaza magana dan basan bazan iyataba innace zanyi magana inaga zuciya ta zata iya fitowa waje inajimawa bance tak ba idan na rasa control dina saida kwalla wanda zirara kawai suke bazan kiraku kuka ba dan wanibi bansanin suna fita a kwayar idanuna.

Karfe takwas daidai Oga Adam ya iso dasu Atika sai uwar dakin Cankwai salati sukahau yi musamman da suka ga gashin kan ta kwal gashi an aje a gefenta sai a rafka salati ni kuma sai in kara tsorata.

"Asa masu Mari."
cewar Adam tashin hankali kuwa na tsinci kaina a ciki dan bantaba shiga cikin shiba,itako Magajiya ba wani sabon abubane agareta haka aka samu a cikin shi gani gata kallo daya idan ta dalla mani sai na girgiza amman ban yanda na sauke idona akanta sai idan itace ta sauke nata idon sannan nasan ina sauke nawa a farko ta samu weak point dina na tsorata kenan.

"Ke yar maguzawa dan uwarki zakisa azo a cire maki marin nan ki wanke kashin dake jikin ki ko saina kara cin uwarki da hujja."
Na furta hakan agadarance amman kasan zuciya ta duk burgace.

Kallan mamaki take mani dan fuskatar ta,ta shida hakan.

"Dago ni Cankwai kike zagi dan kinsamu nasara akaina na rana daya rak? anya baki taboma kanki fitina da bala'i ba."?

Hakanan naji gabana ya faɗi a raina nace,ohni Aminatu minike aikawata anya matar nan takamani basai nagane kuskure naba.

A zahiri kuwa nace.
"Ke yar matsiyata kinsa tsoronki nike?daman bakam nayi ina kallan naki salon ashe ke karamar yar iskace a harkar iskancin ma baki je ko inaba indai na cika sunana Aminatu saina hanaki shan ruwa a gidan nan kuma daga yau kika kara cemani Da'go saina datse harshenki shegiya mai idanu irin na shaiɗan ja'ira ahaka zaki ƙare."

Na ida maganar ina dungurin ta.

Kafarta tasa duk da tana daure ta halbani da ita har karfen kafarta ya daki saman tawa kafar fitsari ne kawai ban sakiba tsabar azaba.

Nima kafata nasa na halbar mata baki kusan a tare muka saki ƙara da sauri despline yazo ya kwanceni aka samani nawa Marin itama aka sauya mata wani mai guda daya bakinta nata jini ranar dai Allah ya azani kan Cankwai na gibji gayu haka muka wuni a mari duk na jigata jikina yai tsamin wahala sai shiddan yamma aka kwance mu muka koma daki tafiya nike a hankali tsbar na jigata, amman abun mamaki Cankwai kamar bata shiga Mari ba ko ajikinta tsabar ta saba,muna komawa daki salolina na jera itako kewaye ta shiga tana dawowa hayewa tayi bisa gadonta da katifa tai doube.
ina gama sallah na zazzageta na dauki katifata saidai ido batace komai ba saidai kit da tayi da harshe alamun nasan sauran.

Ko ajikina haka na haye gadona na kwanta nima baccin wahala ya daukeni sai ukkun dare na farka nayi sallar isha'i da nafilfilina tare da nemawa kawata rahama,wannan kuma yazama jinin jikina har na saba.

Washe gari kuwa haka kowa yaita hadimar shi sai gashi nima harna fara tara mutane Cankwai da tata jama'ar nima da tawa kowa na zaune saiji dakai yake,nafara yarda da cewa idan aka daku da juna kowa kama kanshi yake haka ta kasance tsakanina da Magajiya.

Muna zaune tazo tareda Jama'arta ta kallemu tace.

Ku dan maiciyin uwarku harkun fara kawo mani munafunci a cikin fadata wato kundawo bayan ta kubar ganin anyi faɗa da Magajiya anci galaba kaina ita kanta wannan sakarar lokaci nabata sai nayi maganin ku,dan kakan ninku kowa ya dawo baya na."

Kallona su Nusaiba sukayi bance dasu komai domin bance su dawo wajena ba.

Sake ɗago kai tayi ta kallesu sai gashi kowa ya koma bayan Cankwai saini kadai kamar mayya.

"Mtsw nidai nan dan gyatumin yarinya tsautsayi yasa ta sake haye mani inyi lugude bisa cikin ja'ira eheh."
Na ida maganar ina taf hannu,da kallo suka bini samun inuwa nayi na zauna ina ganin su suna kallona saidai azageni daga nesa.

Haka na samu saukuni rayuwar Yari inacin dakashin kaina ko aiki banyi sai wanda ake sakawa.

Gashi anfara mana islamiya daman na sauke nayi isa a harda nakai talatin saina daura mukai tayi har sana'oin hannu ake koyawa duk da nasan ba fita zaniyi ba na koyi takalmi da jikka.


Rayuwa taja kwanaki sunyi nisa komai yana sauyawa akwana atashi bayan wata biyu cikin ikon Allah shekarata ɗaya daidai gidan Yari yau yakama shekarar kawata Asma'u ɗaya akasa abin sona da begena ranar tunda na tashi banda wata lakka domin kwanakin mutuwar Husna abin lissafine agareni a kiyaye suke a ɗigiggide ban kwana in wunui ban lissafasu ba shiyasa abin ya zauna a raina daman ranar alhamis ne saiya kasance ina azumi duk dana saba na litinin da alhamis addu'a da tawassali kawai nike tareda neman gafara rahama zuwa ga Asma'u nasan ya'yan ta bazasu iya mata wannan gatan ba a halin yanzun kasancewar suna yara kanana saidai in Allah ya yaramani su sungirma nasan zasuyi mata,wani bangaren zasuji tsanata da haushina domin ance kunne ya girmi kaka zasuji labari marar inganci akaina amman ba yanda zanyi tunda Haka Allah yaso.

Baki daya ranar gaza komai nayi hakan yaba Cankwai damar takani ta hanyar zagina harma da dungurina take dan ta fahimci akwai ranakun da nike samun kaina weak ban iya komai wanibi inyi kuka wani lokacin inzama so silent.
Haka taita yiman bala'i saidai bance mata uffanba sai ido danike binta dashi.

danko iyalan Alhaji Abdullatib inda aka bankeni dana shigo kano suna kokarin kawo mani ziyara suna bani hakurin halin dana tsinci kaina amman Ummi bata ta6a zuwa dubani ba hakan bai zama abin damuwa agareni ba domin nima nawa iyayen sun yafeni a cikin ya'yan su basu damu daniba sun daina kaunata arayuwar su,nima mizaisa in tsaya tunasu ko insama raina son kasancewa dasu bayan nasan yaudarar kaina kawai nike suma hakan yasa sukai kokarin mantawa da rayuwata mizaisa nima inƙi mantawa dasu.
In manta da inada
kowa da komai arayuwata inci gaba dacin gashin kaina,inzama nikeda iko da kaina ba wanda zai gayamani inji ban shakkar kowa koma waye,da haka zuciya ta bushe ban tsoro bare hakkar kowa musamman a gidan Yari,dangina kuwa na fara rufe babin su,musamman iyayena da yan uwana,haka naci gaba da rayuwata alhmdulillah.



*************
A gidan su Amina kuwa Baba ne kwance magashiyan baida lafiya ko ɗaga hannun shi ya gaza banda sauka da hawaye keyi bisa fuskar shi.
bakin shi ya bushe yayi fari fat dagani kasan ya daɗe kwance kimamin wata biyu kenan tunda yai niyar zuwa gano yarsa sati mai kamawa daga yaje kasuwa wasu yan jagaliya da sukasha suka koshi sukace ai mashi atire yar shice tai kisan kai na aminiyar ta har sunfara mashi rutsida duwatsu Yan sanda sukai ram dasu,hakan yasa zuciyar shi ta buga Allah yaso bata fasheba sannan bai samu Paralise ba,saidai ciwo sosai ya kwantar dashi har dangi sunzo ana neman afuwa da gafarar juna.

Mum,Tariq ,Fatima,Auta da matar Ya Tariq Aisha duk sunzo hardasu Anty Murja kuka kowa keyi shima Baban sosai yake kuka yana cewa.
_Yar Mutan Kankia ce❣️_
Share
Pls
❣️

_*HAKA ALLAH YASO❤‍🔥*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S4/E15&16




"Umma banyima Aminatu adalici ba arayuwata ina ɗaya daga cikin waɗanda suka bada gudunmuwar saka ya'ta a cikin halaka,nakasance uba mai tsatsauran ra'ayi na dage akan abubuwa da dama dan ganin bawa ya'ta tarbiya ashe bahaka bane Allah shike dafama mutun nasan Amina nada tarbiya saidai tana tareda kalubale iri iri na rayuwa mai imani kadai zai iyacin wannan Jarabawar Allah kabani ikoncin wannan Jarabawar kabawa ya'ta mafita a duk inda take akowane hali,Allah Sarki Mamana Allah yaimaki albarka."

Ameen suka masa.

"Kayi hakuri Yusuf dole mu rike Qaddararmu da hannu bibbiyu kila musamu sassaucin laifikan da mukayi abaya abubuwa da dama sunfaru marassa dadi saidai muce Allah yayafe mana."
Ameen ya rabbi."

"Mum yaushe zamuje ganin Minal wlh ina kewarta nayi danasanin rashin fahimtar ta danayi mata azatona itace silar guduwar Ya Taufiq duk nayi blaming dinta gashi yanzun yanda rayuwa ta juya inalillahi wa'inna ilahirraji'un."

"Fatima kiyi hakuri haka Allah yaso addu'a kawai zamuyi mata Allah ya fiddota cikin wannan halin shi kuma Hussein Allah yadawo dashi lafiya indai darai da rabo."

"Insha Allah Khadija." cewar Mum.

Kowa yai jugudum musamman Tariq,dake ganin sanadiyar shine abunda yafaru da Amina ya sameta da bai kirata wayaba kila da batabar gidan suba,da haka yake blaming kanshi.

Kowa yai sukuku kamar marassa lafiya musamman Mama dake ganin ciwon mijin nata kamar bana tashi bane.

Mum tace jibi lahadi zasuje ganin Amina zasu wuce gida ranar litinin haka kuwa akayi ranar lahadi karfe goma suka tafi harda Zainab sai Jidda da Rahima kanwar Asma'u.

Koda aka kira Amina tayi mamaki domin rabon da akawo mata ziyara harta manta arayuwar ta,tayi mamaki da taji ana kiranta.

Zuwa tayi as usual tana isa tagasu Mum,kamar baki take kallan su,murmushi sukar mani kana ganin su kasan bakaramin farin cikin ganina sukayi ba saidai ni banji komi ba,isowa nayi wajen su natsaya minti biyar inji Security din dake gefenmu.

Zainab da Jidda sukahau kuka suna Antyn mu dan Allah kidawo gida muna sonki Baba yace kiyafe mashi bai lafiya shiyasa baizoba."

"Kai kuyi mana shiru waya tambayeku kada inkarajin kowa yai magana anan."
Inji Mum.
Sai lokacin naji saukar kwalla a idona
"Mum."
shi ne abinda bakina ya furta.

Rungumota nayi ina kuka tana kuka bansan yanda akai zuciya ta karyeba.

"Kiyi shiru Mamana haka Allah ya kaddara mana kidaina wannan kukan zakisa zukatan mu sukaraya."
Shiru nayi ina kallan su dan bansan mi zance masu ba,kaina ya dauki ciwo.

"Aminatu munyi kewarki Allah ya fiddoki a cikin wannan halin da kike ciki muna maki addu'a a kowane lokaci Allah ya kareki."
Cewar Anty Aisha matar Ya Tariq.

Tunda na kalli Ya Tariq sau daya ban kara kallan shiba,ina kalleshi Ya Taufiq sak nike gani,ba abinda na tsani gani a halin yanzun kamar shi gani nike,ta silar shine komai ya sameni.

"Aminatu dan Allah kiyi hakuri kiyafe mani inaji araina nine silar komai kiyafe mani."

Batare dana kalleshi ba nace.
"Ba wanda zanyi blaming nasan komai muqaddari ne haka Allah yaso,dan haka kada wanda yasama kanshi alhakin wannan abun mugodema Allah,akowane hali."

"Allah yaimaki albarka Mamata,Allah yakareki daga kowane sharri insha Allah duk mai hannu a cikin wannan abun sai asirin su ya tonu."

"Hmmm Mum nifa ba wanda yai wannan abun nice dan Allah kudaina juya wannan maganar angama yanke hukunci fatanmu dai Allah ya jikan Asma'u."
Ameen suka amsa,dukkan su idanun su sunyi jajir.
Murmushi kawai na iya yima Rahma.
Itama kukan takeyi.

"Minal kiyi hakuri akan abun da naimaki nayi blaming dinki dayawa dan Allah kiyfe....
Batareda nabari ta ida maganar taba nace.

"Kinga Fatash baki mani komai ba dan Allah kada kidaurama kanki komai ko nice ke dole inyi abinda kikayi."
"Shikenan Kawata nagode."

time off."
Cewar mai kula damu.
Hannun jidda na kama na shafi gefen fuskarta ba karamin kewar yan uwana nikejiba araina daurewa kawai nike ina nuna karfin halina da dangana.

Da kyal na kwace hannuna ajikin na Zainab tafiya nayi ina kuka kudi Mum tabani naki karba saida ta matsa mani na amsa ina kuka harna isa daki,jiki a mace na zauna sai tagumi dana rafka komai yai mani kunci.

*******Bayan wata daya na manta komi na koma kamar Da ina rayuwata kamar kowa nida Jama'a ba laifi inada yanci duk da har yanzun Cankwai bata daina yimani wulakanci ba saidai abin na damuna amman hakuri shi yafi ban iya bala'i irin nataba tunda ita bata gajiya kamar ibada ta maida abun ga zalinci kamar ibilis haka take,aiki muke wasu na kwasar shara wasu nadaukar iccen da aka faskare zuwa dining hardani acikin su aiki sosai mukayi har mungaji lokacin amsar abinci yayi mukaje muka ansa Jellof ta shinkafa wata yunwa ta yunkuro mani na dauko hadina nakara nafaraci a jikin inuwa kowa sai hannu baka hannu kwarya ake kamar mayun wata haka muka koma kaikace ba'a bamu abinci kuma ana bamu,nayi lemor farko data biyu nakai ta ukku kenan naji an warce mani abincina Magajiya ce dasu Mairo ta nuye anata tana wurgo mani robar ajikina

"Mairo kuzo muci."
cewar Cankwai,itadai Salame tagaza isowa bare taci abincin.

Bacin rai iya bacin rai nayi aganina magajiya tagama rainani a duniyar nan dole in dauki mataki maganin biri karen maguzawa.

Kallan kaskanci nai mata duk da bacin ran da nike ciki yasa ko yunwar banji baki daya tatafi,bakina yafara yimani ɗaci zuciya ta na tuƙuƙi.

Hannuna kawai na mikamata alamun tabani abincina koda bazanci ba banji zan barma Cankwai hakkina,akanta nasha kwana da yunwa a gidan nan,ta amshe mani abincina, ɗan gari kwakina ko kayan mai magi ta kwace na kwana ƙasa tasani wankin bayi,in danna mata ƙafa da jiki kamar uwata bani iya magana agaban Cankwai,duka kuwa kila dayawa a jikina da tabon dukanta zan mutu nagaji tunda har batai shakkar sake haye mani ba wannan ke nuna bata buguba da sauran rina akaba.

"Bani abincina tun muna shaidar juna Magajiya."
Na ida maganar a ƙufule.
"Karfi yacinye ko zaki ƙwata."

Baki ɗaya Prisonors sun zagayemu suga ikon Allah wasu na bayana wasu na bayan Cankwai majority kenan.
"Haka kikace.?"
Eh."
tace mani cikeda gadara.


A harzuke na cafkar mata wuya na bugata jikin bedi na shaketa kam sosai nikeson zare mata makoshi a ganina kwara in kasheta in dawwama da hujja agidan Yari.

Kowa yasan yanda life prisonors keji aransu zasu iya aikata koma minene matsawar sunsan basu taba fitaba kisama dan sun aikata agunsu ba wani abu bane.

kakari tafara naki sakin ta idanun ta sun kaɗa sosai har sun fara kafewa halbe halbe tafara tun tana yakushina harta kasa katabus.

suko yan uwan mu, masu laifi sai gara kwanukan su suke (kwas kwas) haka yake bada sauti suna ihu da haka suke kiran Gandirobas.

Banji komai akazo aka rikeni ana neman kwatar Cankwai a hannuna wadda kobata suma ba taina numfashi tabbas ta mutu ko ajikina saima dadi danaji na yadda kwallan mangwaro na huta da kuda karshe ko a sauya mani gida Yari life prison ko kuma a fiddo aje ayi hanging ɗina daman natsani rayuwa a halin da nike ciki.

Ina sakinta ta fado kasa wanwar kifamani mari Atika tayi.
"Kinsan abinda kika
aikata."?

"Karki kara dukana saimi dan na kasheta nima akasheni daman abinda nafi kauna kenan."

Koda Adam yazo yaga ta'asar dana shuka baice komai ba sai fiffita da aka hau yima Cankwai ashe sun gane suma ce tayi.
Anjima kafin tafarko,koda tafarko da ihu razananne abakin ta, muna hada ido ta tashi da zummar guduwa suka rikota gudun kada ace ta zare kada tahaukace.

"Ban kaunarta ku rabani da ita zata kasheni muguwace bata da imani yanda ta kashe aminiyar ta so take kasheni."

Haka taira surutai tana bata kaunata.
Sai lokacin Adam ya sauke ajiyar zuciya dawo ganin
magajiya ta dawo hayyacin ta yasa aka kaimu dakin Kunci,tsayawa fadar bala'in dake cikin shi 6ata lokacine, saidai baka iya motsin kirki a ciki shima Punsihment ne.

Mun jigatu sosai sai yamma aka sakemu tafiya ban iyawa a wajen na fadi ina kallan mutane bishi bishi saida asuba naganni bisa gadona.

Ko sallolina banba sai lokacin harda asubar duk nayi, zazzabi yaimani rinkim duk banjin dadi haka ita Cankwai din kuka ga ciwo duk tana fama dashi.

Najima ahaka saiga officers aka fiddomu aka bamu wankin bayi dagani sai ita haka mukaitayi baifi in wanke biyu ba duk sauran ita nike barmawa tanaji tana gani bata iya yimani magana bakaramun tsorona Cankwai keyiba har anfara rainata agidan namu,tasa aiki akiyi saidai tayi tsit kamar shaho yaci shurwa.

Daki kuwa idan ina gado bata iya zama sai nayi bacci kamar munafuka takeyin shi dukkan su banma kowa magana a dakin namu.

So take inbar dakin anki canzamu kai atakaice dai cankwai tazama ustaziya kowa yafara samun freedom akan zalincin Magajiya.

Daukaka nasamu sosai a gidan saina zama kamar nice Queen din gidan duk da bansa komai kuma

Please Login or Register in order to submit comment