Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

AJININSA YAKE Book 3 Complete Hausa Novel Document by AJININSA YAKE Book 3


AJININSA YAKE Book 3

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 36156



AJININSA YAKE Book 3

Reading Time: 3 Hours

Added On: 06, Feb 2025

Author: Zulaihat Sani Kagara ,

Ebook Compiler : Zaharaddeen Shomar

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 189.17 kb

File Type: txt

Views: 139+

Download: 132+

Last download: 14 hours ago

Description/Story: Ajininsa yake 3-01
Posted by ANaM Dorayi on 06:55 PM, 19-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______
.
.Duba da yawan makaranta Hausa yasanyamu
fadada hanyar sadarwar mu daga whatsapp zuwa
bude blog, daga bisani sai nafahimci kamar da
yawanmu vamufiyason shiga blog ba, Bansan
dalilin hakanba, sakamakon yawan korafe korafe
dake riskata yasanyani yin nazari wace hanyace
ke da sauki bayan wannan, karshe dai natino
face book, sakamakon haka muka yanke
shawarar bude page a facebook din duk domin
fadada hanyoyin sadarwarmu wadda ba dan
komai mukeva sai dan jin dadinku,insha Allahu
Labarinmu nagaba zai kasance ta hanyoyi Uku,
:-Whatssap. 08139787515
:-Blog Anamdorayi.mywapblog.com
Saikuma ...
:-Face book.. https://mbasic.facebook.com/
HAUSA-Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%
2CPAGE_ID10%2C7370123473
Hakan amma bazai tabbatuba sai da hadin
kanku..
Dan haka inna bukatar 20,Like a group din kafin
mu sanya littafi na gaba..
Naku har kullum
ANaM Dorayi
--------------------------------------------------------;------------------
Ya koma rigingine ya kwanta, ya rasa dalilin da
yasa Nusaiba ta tinkare shi da wadannan
maganganun banzan. So take ta hada shi da
iyayensa ko me? Idan kuma ta gaji ne, ai bai yi
mata tirke ba. Iyakar ta Alh. Basheer ya ce ya
aje masa komai na sa, sai me? Daran nan
Nusaiba bata yi barci ba, gaban Ubangiji ta
gurfana kamar yadda ta saba kai kukanta. Allah
ya za6a mata alkhairi. Haka kuma tayi kukan
bakin ciki yau ita da mijin auranta take cacar
baki. Lallai rayuwa shirin Allah ce, amma ko a
mafarki bata ta6a tunanin hakan ba a rayuwar
ta. A kodayaushe zuciyar ta na shirya mata
kyakkyawar rayuwa da jin dadi tare da
gamsashshiyar soyayya ga duk mijin da ta aura.
A kunnan ta aka yi kiran sallar farko, ciwon kai
ya ce ga shi nan irin wanda bata ta6a jin irin sa
ba. Da kyar ta sallaci asuba. Ta jawo filo ta jefa
bisa sallayar ta kwanta. Dora kan ta, ke da wuya
ta ji fitar Naseer kamar da gudu. Ta tashi zaune
tana sauraron buga kofar falon sasn su Abba.
Ta mike ta fito kofar falonsu a gwame. Tayi waje
can sasan su Umma. Naseer ta ji yana
fadin,"Zarah ba lfy, yanzu Inna tayo waya inje
maza-maza. Kafun su Abba su gama salati, ya
fice. Ta koma daki da saurin ta, ta dauko hijab
ta suro jakar hannu.don ta tabbata haka Naseer
ya fita babu ko sisi ajikinsa. Ta fito, ta iske su
Umma ma tsaye suke a waje, ya tafi ya bar su.
Makullin motar ta na cikin jakar ta bude ta
dauko,"Umma zo mu bi shi a wannan motar."
Ta ce,"Ba ni so ki na yawon nan Nusaiba, cikin
ki ya tsufa." Abba ya ce,"Gari bai k'arasa waye
ba ma, kun tafi ku 2 mata a mota? Gara ku bari
gari ya waye sosai." Ta ce,"Ba komai Abba, Allah
zai tsare. Umma zo mu je yanzun garin zai
waye." Umma ta shiga suka rankaya. Malam
Balarabe na tayi masu addu'a. Hajaran majaran!
Suka iske Naseer da Inna, domin ance jaririryar
ta mutu a ciki, sbd haka Likitar za ta yi iya
kokarinta su fito da ita, idan kuma abin ya
faskara, aiki za su yi mata. Nusaiba ta nemi
waje ta zauna jinin ta ya k'ara hawa, kan ta
kamar ya tsage, sbd tsabar ciwo. Bayan kusan
minti 40. Likitan ta fito ta ce, maza-maza su je
su biya kudin aiki. Ta mika wa Naseer takarda,
hannunsa na rawa ya rike ya duba. Dubu 35 zai
biya. Umma ta ce,"Ka fito da kudi ko ko? Ya
girgiza kai,"Sai na koma gida, kuma ina jin kudin
da ke gidan dubu 10 ne kawai, banki kuma ba
su fito ba, ya za'ayi kenan? Ya tambaya
hankalin sa tashe. Kafin Umma ta ce wani abu
Nusaiba ta miko rafar kudi, ga wasu yi maza
kaje ka biya. Ya bi tada kallo kafin yasa hannu
ya kar6i kudi ya kwasa da gudu ya nufi wajen
biya.
(Allah sarki baiwar Allah, Allah yahadamu da
mata masu tausayinmu da kaunarmu)
Duba da yawan makaranta Hausa yasanyamu
fadada hanyar sadarwar mu daga whatsapp
zuwa bude blog, daga bisani sai nafahimci
kamar da yawanmu vamufiyason shiga blog ba,
Bansan dalilin hakanba, sakamakon yawan
korafe korafe dake riskata yasanyani yin nazari
wace hanyace ke da sauki bayan wannan,
karshe dai natino face book, sakamakon haka
muka yanke shawarar bude page a facebook din
duk domin fadada hanyoyin sadarwarmu wadda
ba dan komai mukeva sai dan jin dadinku,insha
Allahu Labarinmu nagaba zai kasance ta hanyoyi
Uku,
:-Whatssap. 08139787515
:-Blog Anamdorayi.mywapblog.com
Saikuma ...
:-Face book.. https://mbasic.facebook.com/
HAUSA-Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%
2CPAGE_ID10%2C7370123473
Hakan amma bazai tabbatuba sai da hadin
kanku..
Dan haka inna bukatar 20,Like a group din kafin
mu sanya littafi na gaba..
Naku har kullum
ANaM Dorayi
Nusaiba fa duk ta rude, ta k'ara rikicewa
musamman yadda ta ga Nosis na shiga suna
fita. Likitoci 2 ke kan ta, suna ta k'ara kokarin
su, domin ba sa son ayi mata aikin. Allah da
ikonsa kuwa Likitan da aka kira, yayi nasarar
ciro matacciyar jaririyar, sai dai Zarah nan take
numfashin ta ya dauke. Ba ta ba dalilinta,
komai ya daina aiki a jikinta. Suka yi caa kanta,
latsa nan, gwada can. Amma ba alamar motsi.
Likita ya tura a dauko (Oxygen). Su Nusaiba na
tsaye. Nos din ta fito da gudu, jim kadan ta
dawo da shi da shige dakin. Zuciyar Nusaiba ta
soma bugawa, ta nufin dakin tana fadin,"Shi
kenan Antina! Su Umma suka rirriko ta, su ma
kukan suke yi. Inna ta ce,"Zo ki zauna Nusaiba,
kin ga ba ke kadai bace. Ki kwantar da
hankalinki, ki yi mata addu'a. Tana shiru.
Naseer na iso wajen, bai yarda da yanayin daya
gansu ba. Ga Nusaiba na kuka tana ta fadin,"Shi
kenan Antina." Ya ce,"Menene Umma? "Ba
komai, ji ka ka gaya ma su ka biya kudin." Ya
tsura wa Nusaiba ido, duk ta fita hayyacinta, ya
ce,"Ki yi shiru mana." Ta ja hijabi ta rufe fuska,
sannan ya wuce, ta biyo bayan sa. Yana isowa
kofar. Likitin na fitowa. Ya mika masa takarda
da siri,"Doctor an biya kudin,"Ya ce,"O.K, ka rike
risit din za'a maida ma ku da kudin ku, an riga
an ciro Bebin. Ita ma uwar sai dai ku yi
hakuri.... Nusaiba ba ta gama jin bayayin ba, ta
yanke jiki ta fadi, nan take ta hau fizga. Gaba
daya suka yi caa kanta har da Likitan. Abin
kamar bugun jinnu, duk gabobinta sun sandare,
idanuwa sun kakkafe, baki kumfa. Likita ya ce, a
kai ta ofishin sa. Naseer ya dauke cak! Ya kai ta
ofishin, ya kwantar bisa dan gadon su.
Su Umma ne biye da shi kamar za su yi hauka
saboda tashin hankali. Shi kansa Naseer hawaye
ne ke sauka bisa kuncinsa. Likita ya miko masa
takarda,"Sa min hannu nan, dole a cire abinda
ke cikin ta, don tsira da rayukansu." Bai jira
Naseer ya gama sa hannun ba, ya fice da
saurinsa. Jim kadan wasu Nosis suka shigo da
gadon daukan maras lafiya, dukkan su da kayan
dakin tiyata a jikin su. Irin kayan suka sanya wa
Nusaiba, suka maida ta gadon da suka zo dashi,
suka gara ta dakin tiyata. A tsakar wurin Naseer
ya zube ya kame kan sa hannu 2, ya rasa
duniyar da yake." Me zan gani yau? Inna-lillahi-
wa"Inna-ilaihir-raji'un! Umma ce tayi karfin hali
ta kar6i waya hannu Inna, ta kira Malam
Balarabe,"Mallam ka yi maza ka zo, abubuwa
sun rinca6e, daga Zarah har Nusaiba ba mu san
halin da suke ciki ba. A zaton da mu ke yi ma
dai Zarah babu ita. Nusaiba kuwa yanzu suka
wuce tiyata da ita." Hankalin sa yayi
mummunan tashi, salati yake yana k'arawa, har
ya rufe gida, ya kama hanya. A mota ya kira
Alh. Basheer ya labarta masa halin da suka wayi
gari da shi. Subhanalillahi! Babu 6ata lkc suka
baro Kaduna. Malam Balarabe na isa. Shi
Malama Umar ya iso. Yadda suka same su
zazzaune haka su ma suka nemi wuri suka
zauna. Naseer na nan dunkule a kasa. Malam
Umar bai ko shaida shi ba, sai da ya jima a
wajen. Ya tashi ya matsa gun sa ya tsugunna ya
dago kan sa,"Naseer! Tashi daga k'asan nan, zo
nan ka zauna." Ya kamo shi ya taso da kyar,
suka zauna bisa kujera, yana rungume da
kafadar sa. M.Balarabe shi ma ya taso, ya
tsugunna gabn su ya ce,"Sun bada gawar ne?
Ya girgiza kai, hawaye suka kara kubce masa, ya
ce,"Sun ce ba mutuwa tayi ba, doguwar suma
ce, shine suka sa mata (Oxygen)Gaba dayan su
suka sauke numfashi, suka yi hamdala ga Allah,
tare da addu'ar Ubangiji ya ba su lafiya. Kamar
wucewar minti goma da zuwan su Abba. Likita
ya fito, duk suka mike suka nufi gun sa,"Yaya
Likita? Yayi dan murmushi,"An yi nasara,"Bebi,
na nan lafiya lau, shi da uwar sa. Za'a fito da su
nan bada dadewa ba. Kowa sai hamdala. Umma
da Inna suka rungume juna. Duk da haka
hankalin Naseer bai kwanta ba, so yake ya
gansu da idon sa, ya tabbatar da lafiya lau
suke. An ba su izinin ganin Zarah na minti 5r.
Haka suka yi tsaye gaban gadon suna mata
kallon tausayi. Inna ta fara barin dakin ta dawo
wajen ta zauna, tayi shiru hawaye na tsitaya,
babu abinda za ta iya yi, komai Allah yayi, dai-
dai ne. "Yan mintoci bayan fitowar su daga
wajen Zarah, aka kawo ma su Bebin da aka ciro
wa Nusaiba. Bebi ne katon gaske jajur da shi,
sannan babu abinda ya bambata shi da Ameer.
Illa girma daya fi shi. Kowa yasa masa albarka,
suka mika wa Babansa. Ya zura masa ido kamar
ya lashe shi so da kaunar Bebin suka kama
zuciyar sa. Kwalla suka cika idanun sa,"Allah ka
raya mi shi." Ya fadi a ransa..
A lokaci guda daran jiya ya fado masa, nan da
nan ya mike ya ba Umma Bebi, ya fice da sauri
ya sami wata kwana, ya hade kai da bango.
Babu abinda ke yawo cikin ransa, sai
maganganun daya cacca6awa Nusaiba, a idonsa
yake ganin
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download AJININSA YAKE Book 3

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album