Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Ajininsa yake 3-01
Posted by ANaM Dorayi on 06:55 PM, 19-Nov-15
Under: Ajininsa yake
_______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______
.
.Duba da yawan makaranta Hausa yasanyamu
fadada hanyar sadarwar mu daga whatsapp zuwa
bude blog, daga bisani sai nafahimci kamar da
yawanmu vamufiyason shiga blog ba, Bansan
dalilin hakanba, sakamakon yawan korafe korafe
dake riskata yasanyani yin nazari wace hanyace
ke da sauki bayan wannan, karshe dai natino
face book, sakamakon haka muka yanke
shawarar bude page a facebook din duk domin
fadada hanyoyin sadarwarmu wadda ba dan
komai mukeva sai dan jin dadinku,insha Allahu
Labarinmu nagaba zai kasance ta hanyoyi Uku,
:-Whatssap. 08139787515
:-Blog Anamdorayi.mywapblog.com
Saikuma ...
:-Face book.. https://mbasic.facebook.com/
HAUSA-Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%
2CPAGE_ID10%2C7370123473
Hakan amma bazai tabbatuba sai da hadin
kanku..
Dan haka inna bukatar 20,Like a group din kafin
mu sanya littafi na gaba..
Naku har kullum
ANaM Dorayi
--------------------------------------------------------;------------------
Ya koma rigingine ya kwanta, ya rasa dalilin da
yasa Nusaiba ta tinkare shi da wadannan
maganganun banzan. So take ta hada shi da
iyayensa ko me? Idan kuma ta gaji ne, ai bai yi
mata tirke ba. Iyakar ta Alh. Basheer ya ce ya
aje masa komai na sa, sai me? Daran nan
Nusaiba bata yi barci ba, gaban Ubangiji ta
gurfana kamar yadda ta saba kai kukanta. Allah
ya za6a mata alkhairi. Haka kuma tayi kukan
bakin ciki yau ita da mijin auranta take cacar
baki. Lallai rayuwa shirin Allah ce, amma ko a
mafarki bata ta6a tunanin hakan ba a rayuwar
ta. A kodayaushe zuciyar ta na shirya mata
kyakkyawar rayuwa da jin dadi tare da
gamsashshiyar soyayya ga duk mijin da ta aura.
A kunnan ta aka yi kiran sallar farko, ciwon kai
ya ce ga shi nan irin wanda bata ta6a jin irin sa
ba. Da kyar ta sallaci asuba. Ta jawo filo ta jefa
bisa sallayar ta kwanta. Dora kan ta, ke da wuya
ta ji fitar Naseer kamar da gudu. Ta tashi zaune
tana sauraron buga kofar falon sasn su Abba.
Ta mike ta fito kofar falonsu a gwame. Tayi waje
can sasan su Umma. Naseer ta ji yana
fadin,"Zarah ba lfy, yanzu Inna tayo waya inje
maza-maza. Kafun su Abba su gama salati, ya
fice. Ta koma daki da saurin ta, ta dauko hijab
ta suro jakar hannu.don ta tabbata haka Naseer
ya fita babu ko sisi ajikinsa. Ta fito, ta iske su
Umma ma tsaye suke a waje, ya tafi ya bar su.
Makullin motar ta na cikin jakar ta bude ta
dauko,"Umma zo mu bi shi a wannan motar."
Ta ce,"Ba ni so ki na yawon nan Nusaiba, cikin
ki ya tsufa." Abba ya ce,"Gari bai k'arasa waye
ba ma, kun tafi ku 2 mata a mota? Gara ku bari
gari ya waye sosai." Ta ce,"Ba komai Abba, Allah
zai tsare. Umma zo mu je yanzun garin zai
waye." Umma ta shiga suka rankaya. Malam
Balarabe na tayi masu addu'a. Hajaran majaran!
Suka iske Naseer da Inna, domin ance jaririryar
ta mutu a ciki, sbd haka Likitar za ta yi iya
kokarinta su fito da ita, idan kuma abin ya
faskara, aiki za su yi mata. Nusaiba ta nemi
waje ta zauna jinin ta ya k'ara hawa, kan ta
kamar ya tsage, sbd tsabar ciwo. Bayan kusan
minti 40. Likitan ta fito ta ce, maza-maza su je
su biya kudin aiki. Ta mika wa Naseer takarda,
hannunsa na rawa ya rike ya duba. Dubu 35 zai
biya. Umma ta ce,"Ka fito da kudi ko ko? Ya
girgiza kai,"Sai na koma gida, kuma ina jin kudin
da ke gidan dubu 10 ne kawai, banki kuma ba
su fito ba, ya za'ayi kenan? Ya tambaya
hankalin sa tashe. Kafin Umma ta ce wani abu
Nusaiba ta miko rafar kudi, ga wasu yi maza
kaje ka biya. Ya bi tada kallo kafin yasa hannu
ya kar6i kudi ya kwasa da gudu ya nufi wajen
biya.
(Allah sarki baiwar Allah, Allah yahadamu da
mata masu tausayinmu da kaunarmu)
Duba da yawan makaranta Hausa yasanyamu
fadada hanyar sadarwar mu daga whatsapp
zuwa bude blog, daga bisani sai nafahimci
kamar da yawanmu vamufiyason shiga blog ba,
Bansan dalilin hakanba, sakamakon yawan
korafe korafe dake riskata yasanyani yin nazari
wace hanyace ke da sauki bayan wannan,
karshe dai natino face book, sakamakon haka
muka yanke shawarar bude page a facebook din
duk domin fadada hanyoyin sadarwarmu wadda
ba dan komai mukeva sai dan jin dadinku,insha
Allahu Labarinmu nagaba zai kasance ta hanyoyi
Uku,
:-Whatssap. 08139787515
:-Blog Anamdorayi.mywapblog.com
Saikuma ...
:-Face book.. https://mbasic.facebook.com/
HAUSA-Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%
2CPAGE_ID10%2C7370123473
Hakan amma bazai tabbatuba sai da hadin
kanku..
Dan haka inna bukatar 20,Like a group din kafin
mu sanya littafi na gaba..
Naku har kullum
ANaM Dorayi
Nusaiba fa duk ta rude, ta k'ara rikicewa
musamman yadda ta ga Nosis na shiga suna
fita. Likitoci 2 ke kan ta, suna ta k'ara kokarin
su, domin ba sa son ayi mata aikin. Allah da
ikonsa kuwa Likitan da aka kira, yayi nasarar
ciro matacciyar jaririyar, sai dai Zarah nan take
numfashin ta ya dauke. Ba ta ba dalilinta,
komai ya daina aiki a jikinta. Suka yi caa kanta,
latsa nan, gwada can. Amma ba alamar motsi.
Likita ya tura a dauko (Oxygen). Su Nusaiba na
tsaye. Nos din ta fito da gudu, jim kadan ta
dawo da shi da shige dakin. Zuciyar Nusaiba ta
soma bugawa, ta nufin dakin tana fadin,"Shi
kenan Antina! Su Umma suka rirriko ta, su ma
kukan suke yi. Inna ta ce,"Zo ki zauna Nusaiba,
kin ga ba ke kadai bace. Ki kwantar da
hankalinki, ki yi mata addu'a. Tana shiru.
Naseer na iso wajen, bai yarda da yanayin daya
gansu ba. Ga Nusaiba na kuka tana ta fadin,"Shi
kenan Antina." Ya ce,"Menene Umma? "Ba
komai, ji ka ka gaya ma su ka biya kudin." Ya
tsura wa Nusaiba ido, duk ta fita hayyacinta, ya
ce,"Ki yi shiru mana." Ta ja hijabi ta rufe fuska,
sannan ya wuce, ta biyo bayan sa. Yana isowa
kofar. Likitin na fitowa. Ya mika masa takarda
da siri,"Doctor an biya kudin,"Ya ce,"O.K, ka rike
risit din za'a maida ma ku da kudin ku, an riga
an ciro Bebin. Ita ma uwar sai dai ku yi
hakuri.... Nusaiba ba ta gama jin bayayin ba, ta
yanke jiki ta fadi, nan take ta hau fizga. Gaba
daya suka yi caa kanta har da Likitan. Abin
kamar bugun jinnu, duk gabobinta sun sandare,
idanuwa sun kakkafe, baki kumfa. Likita ya ce, a
kai ta ofishin sa. Naseer ya dauke cak! Ya kai ta
ofishin, ya kwantar bisa dan gadon su.
Su Umma ne biye da shi kamar za su yi hauka
saboda tashin hankali. Shi kansa Naseer hawaye
ne ke sauka bisa kuncinsa. Likita ya miko masa
takarda,"Sa min hannu nan, dole a cire abinda
ke cikin ta, don tsira da rayukansu." Bai jira
Naseer ya gama sa hannun ba, ya fice da
saurinsa. Jim kadan wasu Nosis suka shigo da
gadon daukan maras lafiya, dukkan su da kayan
dakin tiyata a jikin su. Irin kayan suka sanya wa
Nusaiba, suka maida ta gadon da suka zo dashi,
suka gara ta dakin tiyata. A tsakar wurin Naseer
ya zube ya kame kan sa hannu 2, ya rasa
duniyar da yake." Me zan gani yau? Inna-lillahi-
wa"Inna-ilaihir-raji'un! Umma ce tayi karfin hali
ta kar6i waya hannu Inna, ta kira Malam
Balarabe,"Mallam ka yi maza ka zo, abubuwa
sun rinca6e, daga Zarah har Nusaiba ba mu san
halin da suke ciki ba. A zaton da mu ke yi ma
dai Zarah babu ita. Nusaiba kuwa yanzu suka
wuce tiyata da ita." Hankalin sa yayi
mummunan tashi, salati yake yana k'arawa, har
ya rufe gida, ya kama hanya. A mota ya kira
Alh. Basheer ya labarta masa halin da suka wayi
gari da shi. Subhanalillahi! Babu 6ata lkc suka
baro Kaduna. Malam Balarabe na isa. Shi
Malama Umar ya iso. Yadda suka same su
zazzaune haka su ma suka nemi wuri suka
zauna. Naseer na nan dunkule a kasa. Malam
Umar bai ko shaida shi ba, sai da ya jima a
wajen. Ya tashi ya matsa gun sa ya tsugunna ya
dago kan sa,"Naseer! Tashi daga k'asan nan, zo
nan ka zauna." Ya kamo shi ya taso da kyar,
suka zauna bisa kujera, yana rungume da
kafadar sa. M.Balarabe shi ma ya taso, ya
tsugunna gabn su ya ce,"Sun bada gawar ne?
Ya girgiza kai, hawaye suka kara kubce masa, ya
ce,"Sun ce ba mutuwa tayi ba, doguwar suma
ce, shine suka sa mata (Oxygen)Gaba dayan su
suka sauke numfashi, suka yi hamdala ga Allah,
tare da addu'ar Ubangiji ya ba su lafiya. Kamar
wucewar minti goma da zuwan su Abba. Likita
ya fito, duk suka mike suka nufi gun sa,"Yaya
Likita? Yayi dan murmushi,"An yi nasara,"Bebi,
na nan lafiya lau, shi da uwar sa. Za'a fito da su
nan bada dadewa ba. Kowa sai hamdala. Umma
da Inna suka rungume juna. Duk da haka
hankalin Naseer bai kwanta ba, so yake ya
gansu da idon sa, ya tabbatar da lafiya lau
suke. An ba su izinin ganin Zarah na minti 5r.
Haka suka yi tsaye gaban gadon suna mata
kallon tausayi. Inna ta fara barin dakin ta dawo
wajen ta zauna, tayi shiru hawaye na tsitaya,
babu abinda za ta iya yi, komai Allah yayi, dai-
dai ne. "Yan mintoci bayan fitowar su daga
wajen Zarah, aka kawo ma su Bebin da aka ciro
wa Nusaiba. Bebi ne katon gaske jajur da shi,
sannan babu abinda ya bambata shi da Ameer.
Illa girma daya fi shi. Kowa yasa masa albarka,
suka mika wa Babansa. Ya zura masa ido kamar
ya lashe shi so da kaunar Bebin suka kama
zuciyar sa. Kwalla suka cika idanun sa,"Allah ka
raya mi shi." Ya fadi a ransa..
A lokaci guda daran jiya ya fado masa, nan da
nan ya mike ya ba Umma Bebi, ya fice da sauri
ya sami wata kwana, ya hade kai da bango.
Babu abinda ke yawo cikin ransa, sai
maganganun daya cacca6awa Nusaiba, a idonsa
yake ganin lokacin da ta miko masa rafar kudi,
duk a tunanin take ganin halin da ta shiga.
Wanda komai zai iya faruwa da ita. "Da mutuwa
tayi da shi kenan, ta tafi ta bar ni da hakkinta a
wuya na?" Ya fashe da kuka sosai, irin wanda
bai ta6a yinsa a rayuwar sa ba. Ji yayi an kamo
shi,"Malam Umar ne,"Haba Naseer, ka yi hkr
mana, ka roki Allah ya ba su lafiya. Wannan
koke-koken ai ba su da amfani. An san ka na
cikin tashin hankali, amma jurewa za ka yi, ka
zama namiji. Zo mu je, yanzu za mu tafi, don a
samu a bizne jaririyar wajen Zarah. Yi hkr d'an
gidan Inna." Ya goge masa fuska, ya riko
hannun sa suka dawo. Yarinyar na lullube cikin
zani, ya nuna wa Naseer ita, yayi jim, yana
kallon ta, sannan ta dauke kai. Ya matsa kusa
da Abba ya ce,"Ka zo da waya?" Ya ce,"Ga ta, ai
na riga na gaya wa su Alhj, suna tafe." Ya
ce,"To shi kenan, bari in kira Sageer." Ya kar6i
waya, ya matsa gefe,ya kira duk wanda yake
son kira, sannan ya maida wa Abba wayarsa,
suka dauki shatan tasi ta maida su gida. Suna
bada baya. Su Alh. Basheer na isowa. Abinka da
asibitin Shika, sai suka rasa ina za su dosa, don
haka ya kira wayar Naseer. Tana ta bugawa,
amma da yake tana gida, babu mai dauka. Ya
kira ta Abba, su kuma sun riga sun kusa gida,
saboda haka Malam Umar yabasu lambar Inna,
suka kira. Naseer ya fita ya nemo inda motar su
tayi fakin. Yana isa wajen. Ummi ta fara kwalla.
Yana neman tsugunnawa. Alhjn yayi sauri ya
kamo shi,"Sannu Naseer ya fargaba? Ya ce,"Mun
gode Allah." Ya ce,"Malam Balarabe ya ce ashe
doguwar suma Zara tayi ko? Ya amsa da kai? Ya
dan rungumo kafadar sa,"Ka yi hakuri kaji? Allah
zai ba su lafiya." Ya gyada kai, ya dubi Ummi
suka gaisa, sannan yayi masu jagora zuwa inda
suke, suna tafe yana maida masu yadda abin ya
faru. Bayan sun gaisa da su Umma. An jajanta
wa juna, sai Alh.Basheer ya nemi ganin Likita.
Abn ka ga mai kudi, nan da nan ya sami duk
abubuwan daya bukata watau daki na
musamman da likita shi ma na musamman. Kan
ka ce kwabo, an hada Zarah da Nusaiba waje
daya, an zuba masu komai na bukuta. Ummi na
rike da Bebi, yana to son a zuba masa abinci a
bakin sa. Da yake akwai kayayyakin Zarah,
ruwan zafi kuma tana da zuma da dabino sbd
tana yawan cin dabino, sai Inna ta kawo, duk
Ummi ta ba shi, sannan ta dan kada zuma a
ruwan dumi, ta cika masa ciki, nan da nan ya
koma barci. Ganin hankali ya dan kwanta. Inna
ta ce Naseer ya koma gida yayi wanka, daga nan
ya kwaso wa Bevi kaya da ita Nusaiban. Yana
fitowa su Sageer na shigowa shi da Fa'iza, dole
ya sake komawa, suka gaida su Umma. Ya kawo
masu Bebi suka gan shi. Wucewar 'yan mintoci
15 ya karbi mukullin motar Nusaiba, tunda ga
Sageer zai tuka a maida ta gida. Sun yi fakin
kofar gida, suka yi sallama suka tafi, ba tare da
sun tsaya wani surutu ba, domin Naseer baya
ma son yin magana.
Yana shiga gida, ya tu6e kayan jikin sa, ya zaro
sauran kudin da suka rage cikin rafar da
Nusaiba ta ba shi. Ya zauna bakin gado ya zura
masu ido, jim kadan ya sauke numfashi, ya aje
su bisa filo. Ya wuce bayi ya sakarwa kan sa
ruwa. Bayan yayi wanka, ya kimtsa ya kawo
wayoyinsa da kudade ya zuba aljihu. Ya fito ya
nufi dakin Nusaiba.
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
Gaban hoton ta ya tsaya ya k'are mata kalo ba
tare da ya san me zuciyar sa ke sakawa ba.
Wadirof ya bude, ya d'ebo riga da Zani kala 5r.
Yayi tsaye yana tunanin a ina zai ga kayan Bebi,
tunda bai ta6a siyowa ya ce mata ga shi ba?
Abinda ya yanke shawara shine ya shiga kanti,
ya siyo. Wata zuciya kuma ta ce masa "Kai dai
dudduba." Yana gama tunanin sa, ya nufi
akwatuna ya fara budewa, abn ya ba shi
mamaki, domin setin nan kaf kayan Bebi ne ciki
a mak'are. Yayi shiru duk al'ajabi ya ishe shi, ya
nemo jaka ya debi kaya iya dibar sa, kayan
shafe-shafe, su pampas da setin bahon wanka,
wanda komai na bukatar wankan Bebi. Akwai
shi a ciki. Ya loda kaya a but, ya sallami Abba
ya koma asibiti. Yana shigowa da kaya niki-niki,
ya iske Zarah ta farfado, sai faman kuka take yi,
sbd jin abin daya faru da Nusaiba. Su Umma na
ta bata hkr. Ganin Naseer ya shigo, dukkan su
suka fita waje.Ya matsa wajen ta ya zauna gefen
gadon, da sauri ta fado masa ta sake 6arkewa
da kuka. Idanuwan sa suka cike da kwalla, ya
kasa cewa uffan tsawon lokaci. Sannan ya
dagota, ya share mata hawaye ya ce,"Ya isa
haka. Ya jikin? "Yayi sauki. Ashe abinda ya faru
kenan? Ya ce,"To yaya za'ayi? Allah ya ba ku
lafiya." Kwalla suka sake zubo mata ta
ce,"Amin.", Na ga Bebin mu kamar Ameer ne
aka dawo mana da shi." Yayi dan murmushi,"Shi
ne ma, domin shi ma sunan za'a maida masa."
Ta ce,"Yayi dai-dai." Suka k'ura wa Nusaiba ido,
a lkc guda kuma suka kalli juna ya ce,"Allah
yasaa ita ma ta farfado. Lafiya, kamar yadda ki
ka tashi." Ta ce,"Amin yayana." Ta wuce da
kanta kirjin sa, tayi ajiyar zuciya, ya sumbaci
tsakar kanta, sannan ya gaya mata su Sageer
sun zo shi da Fa'iza. Suna gaishe su." Ta dago a
hankali ya taimaka mata ta kwanta tana
fadin,"Muna amsawa." Ta bi shi d kallo, ta ci
gaba da cewa,"Na san ba ka ci komai ba
yayana, ka hada Tea mana ka sha." Ya kada
kai,"Ban jin yunwa Zarah." Ta ce,"Ai kai ba za ka
ji ya ba, amma tana nan tana cin ka." Yayi dan
murmushi ya ja ha6arta, ya ce,"Hankalina bai
gama kwanciya bane Zarah, sai na ga
farfadowar yarinyar nan." Ta dan lumshe ido, ta
bude wani dadi ta ji ya ratsa, ta miko yatsun ta,
ya rike ta.. Ta ce,"Insha Allahu lafiya lau za ta
farfado. Kar ka ka zauna da yunwa yayanmu, za
ta iya yi ma illa." Ya sumbaci, yatsun ya ce,"Shi
kenan, zan sha yanzu." Umma tayi sallama, ya
mike da sauri yana amsawa, ita ma maganar
abincin tayi masa, sannan ta bude jakar kayan
daya kawo, ta debo wa Yaro kaya, ta dauke shi
suka fice. Anan ya hada Tea ya dawo bisa kujera
gaban Zarah yana sha, suna hirar Nusaiba.
Bayan sallar la'asar. Alh. Basheer ya ce shi zai
koma. Ummi ma ta ce me za ta tsaya yi, tunda
ga su Umma ga Inna? Haka suka wuce, duk ba
su ga farfadowar Nusaiba ba, idan Allah ya kai
rai gobe, za su dawo. Bebi kuwa na lkie da
Zarah. Naseer ya tasa su yana ta fama kallon
abin sa, son sa na k'ara kwarara jikin jinin sa da
bargonsa suna kashe jijiyo har bisa fatar sa.
Karfe 9n dare ya baro Shika. Zarah tare da Bebi
ta kwana, ko ya motsa, ita ake mika wa ruwan
dimi ta ba shi, duk da jikin ta babu kwari sosai.
Shi kuwa Naseer kasa runtsawa yayi, saboda
tsabar tunanin abubuwan daya aikata wa
Nusaiba, wadanda a yau yake ganin suna so su
zame masa da na sani. Lokacin sallar asubahi ya
yi, ya tashi ya je yayi alwala, ya bada farali. Da
kansa ya shiga kicin, ya shirya duk abubuwan
da yake son tafiya da su asibiti. Yayi wanka, ya
kimtsa. Karfe 7 saura kwata, ya dauki hanyar
Shika. Karfe 8:30 Nusaiba ta farfado da surutai
tare da sambatun da babu wanda yake fahintar
me take fadi.Likita ya ce ba damuwa, za ta
wartsake nan bada dadewa ba. Suna fa jin dadi,
musamman Naseer da zuciyar sa ke cike da
zullumi. Ko su Alh.Basheer da suka zo, sun yi
farin ciki kwarai, anan suka iske su Malam
Balarabe da Malam Umar. Shi yake gaya masu
cewa Bebi sunan marigayi watau Iliyas ya ci.
Wasa-wasa Nusaiba ta kai har dare bata gane
kowa, sai sambatu. Likita dai sai kara basu
hakuri yake yi, yana jadadda ma su za ta
warware. Amma haka suka kwana da ita, ba
barci. Surutai babu ma'ana. Abinda yafi basu
tsoro, shine yadda harshen ta ya karye, tana
magana kamar wacce ta sami matsalar
shanyewar gefen jiki. Da safe kowa ya zo da
kuzarin sa, turus! Yake yi, saboda abin akwai
ban tausayi, ballatanta da idanuwan ta suka
bud'e waras! Tana kallon kowa, amma bata
sanin ko waye. Murna fa ta koma wa kowa ciki,
domin al'amarin Nusaiba k'ara gaba yake yi,
abin tamkar tabin hankali. Kwana 3 kenan. Da
sassafe ta tashi da wani kuka mai tsuma zuciya
da ban tausayi, babu abinda take kira, sai
"Antina! Alhali ga Antin ta tana tallafe da ita. Ita
ma kukan take yi, tana fadin,"Ga ni fa nan
amarya, ba mutuwa na yi ba."Ta tsura mata ido
zuru! Shi kan sa kallon mai ban tsoro ne, sbd
idanuwan a juye suke, duk sun firfito waje.
Zarah ta sake fadin,"Kin ganni? Ni ce amarya,
ban mutu ba. Ki daina cewa za ki mike da gudu,
kin ga (Operation) aka yi miki. Duba ki gani, kin
ga Bebin mu? Ga Umma ga Inna. Yanzu yayan
mu ma suna tafe. Ki na son ganin su ko? Ta
girgiza kai, ta ce da karfi,"Antina ta mutu na ce!
Wayyo Abba na, sun kashe Antina! Da gudu
Zarah ta bar dakin, ta zube barandar waje, ta
fasa kuka. Kwatsam! Sai ga su Ummi, tun daga
nan suna jin ihun ta, tana kwala wa Abbanta
kira. Ummi bata son lkcn da ta watsar da
kayayyakin hannun ta ba, suka fada dakin. Su
Umma na rirrike da ita. Alh.Basheer yayi azama
ya rungumota,"Ga ni Nusaiba, ga ni, ki yi shiru."
Amma kara fadi take,"Abba na ka zo sun kashe
min Antina! Hankalin sa yayi mummunan tashi,
ya dubi su Umma."Ina Doctor ne wai? Ta
ce,"Sun zo har su 4. Nosis sun zuba magunguna
cikin karin ruwar nan, sun mata allurai, har
yanzu barci ya ki zuwa." Alh.Basheer yayi waje,
ya nufi ofishin likitan daya dauka na
musamman, cikin zafinsa ya shiga, a tsaye ya
fara fadin. "Wai me ke faruwa ne Doctor? Ban
gane condition din yarinya ta ba! Shi ma ya
mike cikin sanyin murya ya ce,"Cool down Alhj,
zauna." "No I can't sit Doctor! Kullum yarinya sai
k'ara rikicewa take! Why? Wai ba anan ku ka yi
mata tiyata ba ne? Ya ce,"Alhj babu wata
maganar an ta6o mata wata jijiya. Infact, aikin
ta bai shafi ko'ina a jikinta ba, sai inda Bebi
yake. Ka zauna mu yi magana, Please! Da kyar
ya zauna, shi ma Lkita ya zauna." Dama kai na
ke jiran zuwan ka mu yi magana. Nusaiba ta
fada cikin matsananciyar damuwa, wacce har ta
sanya ta fizge-fizge, alhalin tana da ciki. Babbar
matsalar ce ga mai ciki idan ta sami kan ta a irin
wannan yanayin, domin ya kan kai a rasa su
duka. Shine za ka ga mutan kauye da suka
jahilci abin sai su ce bugun jinin ne, maimakon a
hanzarta kawo ta asibiti, don daukan matakin
gaggawa, sai a shiga hayaki da shafe-shafen
turaren aljanu. Daga karshe ka ga an rasa uwa
da Da. Abinda na ke so ka gane anan, damuwa
babu abinda bata haifarwa, amma ina son ku
natsu, za mu bicike da kyau, mu gano aininhin
abinda ke damunta. A halin yanzun muna
Expecting comma ta shiga, abinda muke magana
kenan da sauran Doctor." Alhj fa bai
yarda."Wannan ba comma bace, ta6in hankali
ne, sbd haka idan ku yi bincike a kwakwalwarta,
ko nawa ne zan kashe! Ya ce,"Wannan duk ba
matsala, yanzu zan rubutu gwaje-gwaje da
hotunan da za'ayi. Idan an rubuta kudaden, sai
aje a biya." Rubuta min, in je a biya kudin."
Yana zaune Likita ya rubuta duk binciken da
za'ayo. Tare suka fito, ya hada shida Yaron da
zai raka shi ofisoshin da za su rubuta kudaden.
Al'amarin Nusaiba kuwa ta rikita kowa, kuka
kawai suke yi. Shi kan sa Bebin kukan yake
tsalawa, yana jin yunwa, amma ta hana su yi
'yan dabara a lika shi, ya sha nono. Naseer ya
doso wajen, tun daga Nesa ya tsinkari muryar
ta. Da gudun sa ya karaso, yana tambayar
Zarah! "Me ya faru?, Murya na rawa ta
ce,"Nusaiba ta rikice Kai tsaye ya shiga dakin, ya
zube jakar da ke hannunsa, ya nufi gunta yana
fadin,"Ya haka Umma? Duk suka dare, suka ba
shi wuri, tana kyallo ido ta gan shi, ta zaburo
tana mika masa hannu, "Abba na! Abba na, ina
ta nemanka za su kashe ni? Bai san lkcn daya
rungumota ba,"Menene? Iye? Ba ki san akwai
ciwo a jikin ki ba? Allah da ikon sa, shiru tayi,
tana ajiyar zuciya,"Kai na ke ta kira Abba na, ka
ki zuwa, kai ma ba ka so na ne? Idanuwansa
suka cika da kwalla. Kowa yayi waje yana share
hawaye. Ya jima kafin ya ce,"Ai gani na zo, me
aka yi? Wa ya sanya min ke kuka? Ta zura masa
ido ta ce,"Antina suka kashe min, shine suka zo
ni ma suka danne ni, za su kashe." An ce miki
Antinki bata mutu ba, tsaya ki gan ta. Zarah! Ya
kira ta. Ta shigo, ya jawo hannayensu ya
hada,"Kin gan ta? Antinki ce. Ta fizge hannunta,
ta saka ihu,"Ba ita bace! Allah ba ita
bace,"Antina ta mutu
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga
labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin
habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara
gudanar dashi
Ya rufe bakinta ya ce,"Shi kenan na ce, shi
kenan ba ita bace." Zarah ta yi sauri ta fice.
Sannan tayi shiru. Ya dube ta ya ce,"Abinda ki
ke yi, ba shi da kyau, ki na jin Bebin mu na
kuka, kin ki bashi nono, me ki ke nufi? Ta
ce,"Abba na ina naga Bebi kuma? Ga shi

Please Login or Register in order to submit comment