Join Our WhatsApp Group

BAƘAR AYAH BOOK 2 Complete Hausa Novel Document by BAƘAR AYAH BOOK 2


BAƘAR AYAH BOOK 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 16809



BAƘAR AYAH BOOK 2

Reading Time: 1 Hours

Added On: 16, Sep 2023

Author: Sadi Sakhna ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09035784150

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 94.44 kb

File Type: txt

Views: 3815+

Download: 1025+

Last download: 2 days ago

Description/Story:  ____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK 2_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]




Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31


Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
Shaida tanan
+227 97 21 16 15

______________****_______________





Page 🖤1••2🖤



Tafiyah suke Jabeer yana binsu a baya bataresa saninsu ba har suka kai gida.
Kallon ƙofar ya tsaya yi yana nazarin tsarin gidan daga cikin motar.
Wai dama akwai irin waɗannan gidajen a garin abuja?? Kodaga nesa mutum zai gane yanayin rashi da ma'abota gidan suke dashi.
Katangar gidan duk ta zube ta wani wajen saboda rashin ƙarfinta,kuma ya haɗu da yawan ruwan sama dayake kwaranyah a kanta na tsawon lokaci.
Kofar gidan babu wani ishashshen makari,wani langa langane a gefe,da alama dashi ake amfani wajen kare gidan da daddare.
A taiƙacedai gidan na masu ƙaramin ƙarfine sosai.
Numfasawa Jabeer yayi bayan ya gama kallon gidan,inda ba biyota yayi ba yaga tashiga gidan,bazai taba cewa daga nan ta fito ba.
Abinda yafi bashi mamaki shine yanda taƙi karbar taimakonsa,bayan kuma tana rayuwa a gida irin haka.
Fitowa yayi daga cikin motar ya nufi gidan,waigawa yake domin samun wanda zai aikata cikin gidan,idonsa ne ya sauƙa kan wani yaro yana riƙe da kwanon a hannunsa,fuskarsa dama dama da miyar tuwo,da alama tunna jiyane,dan tuwon bayyi kamada wanda aka dafashi sannan ba.
Cikin ɗauke kai daga kallon fuskar yaron ya fara magana.
"Uhm mutumina nace zona aikeka mana,shin nanne gidan su Jaleelah koh?"
"Eh nanne gidan su ina anty hafeezah koh?"
"Eh inaga itace,shiga kace ina sallama da mahaifinta idan yana nan"
"Nawa zaka bani to idan na ƙiramaka shi?"
Mamakin maganar yaron Jabeer yayi,yanzu wannan yaron har yakai bazayyi abuba sai an biyashi?
"Karka damu shiga ka kiramin shi tukunna"
Hanyar gidan yaron ya nufah,bayan wani ɗan lokaci sai gashi sun fito tareda wani farin dattijo mai kamala da dattaku.
Gaisawa sukayi cikin mutunta juna,maganar yaronce ta katsesu da cewa wani abu bayan sun gaisa ɗin.
"Malam baka bani kuɗin ba toh"
Kafin Jabeer yayi magana Dattijon yace.
"Wanne kuɗin za'a baka,har yanzu baku bar wannan ɗabi'a ba koh,ohhh wai yaro baisan a sakashi abu ba sai an bashi kuɗi? Wuce ka tafi gida"
Da sauri yaron ya wuce yana zumbura baki,sai bayan ya tafi tukunna Dattijon ya dawo da kallonsa kan Jabeer.
"Yaro baka faɗamin mai yake tafe dakai ba har yanzu"
"Ehh dama yarinyar gidan na buge da mota a can kan titi,nayi mata magana mutafi asibiti a duba taƙi amincewa,shine nazo naji shin lafiya dai koh?"
"Jaleelah kenan kake nufi,dan itace ta dawo daga makaranta ɗazu,data shigo kuma batace komai ba,babu wanda yasan mai yafaru"
Kasa boye mamakin sa yayi jin wai batace komai ba a gida,kulada hakan da dattijon yayi ne yasashi cewa.
"Yaro karfa ka damu,haka take dama ta saba,kuma tunda har bata nuna ba inaga ba wani abin damuwa bane sosai,kayi tafiyar ka zanje na dubata inna shiga gidan,mungode sosai da kulawarka Allah ya tsare gaba"
Kuɗi Jabeer yafitar ko ƙirgawa bayyi ba ya miƙawa mutumin,tun kafin ya kaishi kusada shi ya ture hannunsa tareda cewa.
"A'ah karma ka ɗorawa kanka nauyi akan wannan,kayi tafiyar ka babu komai kaji yaro"
Daga haka ya shige gida yabar Jabeer a tsaye,dama ana samun irin waɗannan mutanen har yanzu,basuda shi amma kuma sunada wadatar zuci?
Kallon sama yayi ganin rana tayi shirin faɗuwa,gari yafara duhu,yasan zuwa yanzu wataƙila Hajiya zeenah sun dawo.
Wani idan su Hajiya zeenah sun dawo yanzu,toh fah lubna zataji labarin auren da aka ɗaura masa,kuma yasan da gangan Hajiya zeenah zatayi abinda zata san da ɗaurin auren.
Wai yazayyi kenan bai faɗamata ba saidai taji a wani wajen,yasan tashin hankalin dazai tarar ba kaɗan bane.
Saurin dafe kansa yayi,zuwa ɗazu daga haɗuwa da waccar yarinyar har ya manta da damuwar dayake ciki,ya shanye lokacinsa a nan wajen.
Hanyar inda ya ajiye motarsa ya nufah da sauri,yana bata wuta kuwa yanufi gida,a ransa yana addu'ar Allah yasa Hajiya zeenah basu dawo ba tukunna.
Tun kafin ya isa sashen Hajiya zeenah ya hango mutane a wajen,wanda hakan yabashi tabbacin ta dawo kenan.
"Tafaru ta ƙare...."
Yafaɗa cikin kasalalliyar muryah,fita yayi a motar ya nufi sashennata,yasan dole amryar da akayi masan tana sashinta yanzu,tunda baici ace an gama gyara ainihin sashennasa zuwa yanzu.To ma shi baiga wani dalilin komawa wannan sashen ba,kawai dai rigimar Hajiya ce.
Da Maleekah ya haɗu a falon ta ɗauko faranti a hannunta zata shiga ɗakin Hajiyan.
"Ke zo na tambayeki"
Cikeda tsoro da kalleshi,fuskarnan a tamm da ita babu alamar fara'ah.
"Yaushe Mommah ta dawo,tana ina kuma?"
"Uhm batafi minti talatin da isowa bama,tana daƙinta itada amaryar"
"Amarya,kowa yasan da zancen amaryar kenan?"
"Eh mommah tana shigowa ta tara dukkan ma'aikata ta shaida musu cewar kayi sabon Aure yau,kuma dama tana nemanka idan ka dawo"
Dafe kansa yayi ta gefen dama,jin ɗanyen aikin da mahaifiyar tasa ta aikata masa a karo na babu adadi,ko shakka babu yasan da gangan tayi hakan saboda lubna ta sani.
Bai sake kallon inda Maleekah take ba ya wuce ɗakin Hajiya zeenah,itama binsa tayi a baya,dan dama can zata nufah.
A can ƙasan maƙogaronsa yayi salllama kansa yana kallon ƙasa,kana ganin haka kasan yana cikin yanayi marar daɗi.
A ɗaya daga cikin kujerun ɗakin ya zauna,yaga alamar wata farar mata a zaune gefen Hajiya zeenah suna magana,amma ko kallonta bayyi ba,dan yasan itace matar da aka aura masan.
"Ahh Jabeer kaida nace ka kira su Madeenah ka shaida musu zuwana sai yanxu ka shigo"
"Nasamu wani ɗan ƙaramin hatsari ne a hanya"
"Ohh to Allah ya tsare na gaba,shin an gyara sashennaka ne ko kuwa har yanzu"
"An gyara saidai bansan ko sun gama ba,amma naga wancan ɗinma danake ciki akwai parta empty a ciki"
"Nasan da haka,akwai dalilin daya saka na zabi wancan ɗinne,kuma nasan kaima kasan dalilin. Yanzu dai ba wannan ba,mun taho da baƙi,wannan itace........"
"Please dan Allah mommah kibar wannan bayanin,inkin faɗama ba ganewa zanyi ba,inade part ne,za'a gyara taje da zauna kaman yanda kike buƙata,daga nan kuma fah saime takeda buƙata"
Cikeda bacin rai da ƙosawa yayi maganar,shuru Hajiya zeenah tayi,dan ita kanta tasan takai ɗannata bango,amma shima bazai gane bane,kullum cikin fargaba take da matarsa,gani take da dai da rana dayah idan ta zauna tayi shuru lubna zata cutar mata da ɗa.
"To naji,dare yafara nasan ka gaji,kaje ka huta sannan ka sanarwa matarka cewar yanzu ba ita kaɗai bace,karta sakankance kamar da"
Har yakai bakin ƙofa yasake juyowa ya kalli Hajiya zeenah.
"Amma mommah shin indai yanda kuke faɗan haka take,bakya ganin cewar itama wannan bazata........"
"Kaga ya isa haka kaje saida safe,sannan karka sa damuwar wannan auren cikin ranka,yanada dalilinsa daban wanda bai shafeka ba"
Akwai tambayoyi a cikin kansa kala kala,amma yasan koda yayi su bata lokacinsa kawai zayyi,dan haka yabarsu a zuciyarsa kawai ya fitah.
Jan numfashi Hajiya zeenah tayi bayan ya tafi,maida kallonta tayi kan Hilyaan wacce take zaune hankalin ta kwance akan kujera tana kallon abinda yake faruwa.
"Kiyi haƙuri fah nasan munyi tafiyah kun gaji,shi abokin tafiyar taki ankai shi masauƙin baƙi,ke kuma zaki iya kwana a ɗakin Madeenah,ko kuma a baki ɗaki daban"
"Ahah karki damu Hajiya,duk inda kika bani ma ya wadatar,na kwana ukune ai kawai kafin Anty maryam tazo,sannan ma ba zama mukazo yi ba ai,zamu fita kasuwa ne da khamis gobe"
"Medame kuke buƙata haka,babu ba abinda zaku siyah na kayan gida,gyaran daza'ayiwa part ɗin komai za'a saka shi"
"Eh dama ba wai kayan normal na gidaba,akwai abinda take buƙatar a saka na ra'ayinta ne,......
Uhm wannan shine Angon Antyn?"
Hilyaan tafaɗa,badan komai ba saidan ta kawar da zancen da ake a lokacin.
"Eh fah shine,amma bawani buƙatar ta sanshi ai ko ya santa,kafin tazo zanyimasa bayanin ainihin dalilin auren,karku damu da wannan"
Hmmm ba laifi kyakykyawane kam sosai,kaman yanda itama take mai kyau,ina gujemiki aikinki yajuye ba yanda kike so ba. A fili kuma tace
"Ahh babu wani abin damuwa sosai,naga shima bayada interesting akan auren,ko kallon inda nake bayyi ba,yayi zaton inaga nice amaryar"
Hilyaan tafaɗa ɗauke da ɗan ƙaramin murmushi akan fuskarta.
Kayan marmarin da Maleekah ta kawo ta ajiye tafara ci. Dan ita iyani mai aikace aikacen sashen a gajiye take saboda bidirin da suka sha.
"Hmmm da alama wannnan yarinyar da Hajiya ta auramin batada kunya ko kaɗan,wato tafi ƙarfin gaisheda mutane ma,oh kodayake hakan ma yafiye mata,dan wahala zata sha idan tayi ƙoƙarin shiga rayuwata"
Yana cikin zancen zuci bai sani ba yanayinsa a fili,har ya isa sashen Lubnah.
Bai sameta a falo ba,dan haka ya nufi ɗakinta,a tsaye take tana kallon window da Ƙaramin wando a jikinta,rigar ma iyah rabin cikinta,indai ba sannan tasaka kayan ba yasan dasu tayi yawon a falo babu abinda ya dameta.
Sallama yayi a bakin ƙofar,duk da a hankali yayi yasan tajishi sarai,shurun datayi kaman gunki bata amsa ba ya tabbatar masa da labari ya isa ga kunnenta kenan na auren.
Ajiyar zuciya yasake,zuciyarsa tana tsalle a cikin ƙirjinsa,shikansa yasan tsoron ta dayake bana lafiya bane,saidai babu yanda zayyi da hakan.
"Luban!!!"
Ya ƙira sunanta cikin sanyayyiyar muryah.
Bata amsa ba sannan bata juyo ta kalleshi,shikansa yasan bai isa misalta abinda yake cikin zuciyarta ba a yanzu.
Takawa ya farayi a hankali zuwa inda take tsaye a jikin windown,duk da shareshin datayi baiji daɗiba,amma yasan rabin abinda ya faru larfinsa ne dana mahaifiyar sa,ko mace mai sanyin rai ba kowace zata yarda da irin auren da akayi masa ba,miji bai sanar dakai zayyi aure ba,saidai kawai kaji a bakin masu aiki. Mai yafi haka ciwo,musamman idan aka danganta da zafin kishi irinnata?.
Hannunsa ya saƙala ta ƙasan tumbinta,duk da bawani mai yawa bane amma zaka jishi,saboda ƴar ƙibar datake da itah.
Kansa ya kwantar a kafaɗarta,sunkai kusan minti biyar amma har sannnan yagagara cewa komai .
"Dagaskene kayi aure yau"
"Kinga ba......."
"Kawai tambaya nayi,shin dagaskene yau an daura maka aure ko ahah?"
"Eh da gaskene,amma ba yanda kike tu......."
Buge hannun Jabeer tayi daga jikinta tareda fuskantarsa cikin bacin rai.
"Bana son jin komai bayan gaskiyar danaji,duk ƙoƙarina a koyaushe baka gani sai kayi ta kawomin mata cikin gidana koh,bayan kasan babu abinda na tsana kaman na buɗi ido naga wata halitta wai ita mace a gefen mijina"
"Oh gosh wai lubna yaushe zaki daina irin wannan abinne,eh aure da gaskene an ɗauramin aure yau,amma ki tsaya kiji ni nawa bayanin mana,Nifah banine naje dakaina nayi aurennan ba,Mommah ce ta yimin aurennan ki fuskanta mana"
"Wacce fuskantar zanyi,koma wanene yayi maka auren aidai kai akayi wa,mijina akayiwa ni akayiwa kishiyah,ni wannan kawai nasani ba wai wanda yayi aurenba,akan me akayi shi nasan bazai wuce ace dan ka samu ɗa ba,koba dan haka bane. Ko kace baka santa kaman yanda kayi sauran,kana ganin ta samu ciki shikenan saidai na ganka kana lailayata kaman ka samu ƙwai,koba haka bane?"
"Kaiiii lubna bafah haka bane"
"To idan ba haka bane,yanzunnan kaje ka bata takardarta basai gobeba,shine zan yarda dakai toh nasan babu hannunka a ciki"
"Mee naje na bata takardarta,yakikeso kenan na fuskanci Mommah idan na aikata hakan"
"Ni wannan bai dameni ba,kaita shafah"
"Dan kinsamu ina lallabaki shine kika faɗamin abinda kika ga dama koh,ni bazan iya aikata abinda kike so a yanzu ba,idan har abinda na faɗamiki baki yarda ba shikenan"
"Haka ma zakace aikuwa gidanmu zan tafi bazan zauna ba,inka fitarta daga cikin gidannan saikaje kayi min bayani"
"Fine ga kofa nan,dama konayimiki shamaki da ita bakya daina tsallakata,yanzu ma kuma ƙofarki a buɗe take ki tafi,sanda kika ga dama saiki dawo,dama ba yau kika fara ba ai"
"Zan tafi amma karka damu dakanka zakaxo kana rokona kafin na dawo,itakuma matarka ka faɗamata tashirya dawowa ta bazai mata daɗi ba,saita fuskanci abinda bata taba ganiba a faɗin rayuwarta"
Tana gama faɗin hakan tafara tattara kayanta cikin zuciya,tsayawa yayi yana kallonta,dan shi yanzu ta daina bashi ma mamaki.
Jin ana shirin shiga sallah ne yasashi faɗawa banɗakin dakinnata domin yin alwala.
Lokacin daya fito bata nan itada akwatinta,jan ajiyar zuciya yayi kafin yace.
"Jeki na samu na huta naji da wani abun kafin ki dawo"
A zaune take ta dafe kai tana kallon Haidar yanata yimata kuka,tun yamma take fama dashi yaƙi shan nono kuma yaƙi yin bacci,gashi ta duba jikinsa babu zazzabi.
Sakashi tayi a gaba tana kallonsa har wuntsilawa yake yana shiɗewa saboda kuka.
Ƙarar wayarta ne yasaka ta dauke kanta daga kansa ta mayar kan wayar.
Sunan Hilyaan ne ya bayyana akan screen din,hakanne yasa takai hannunta ta ɗauka a kasalance.
"Hello Hilyaan yaya kun isa koh"
"Eh mun isa anty,yanzunnan ma aka kawoni dakin dazan zauna kafin ki taho"
"Toh ya gidan tsarinsa yayi yanda nakeso,kunga inda zan zauna a gidan"
"Ehh komai yayi sosai,gobe zamuje da khamis muyi order duk abinda kike so a saka...ɗazu naga Mijinnaki gaskiya ya haɗu sosai,saidai da alama fah shima yana ji dakansa,daya shigo wajen mahaifiyar sa ko kallona bayyi ba,yayi zaton nice amaryar"
"Kinga niba damuwa ta ji da kansa ba,inyana so ma yaji da cikinsa ba kansa ba,bai dameni ba danshi zanje garinba daga shi har uwartasa,to ya matar tasa taji labarin auren ko kuwa"
"Eh kaman taji,dan muna zuwa Hajiya zeenah tasaka a shaida mata mun dawo,kaman yadda ta faɗa dagaske bata son ta kam"
"Wannan kuma tsakaninsu,nidai bazan yadda su yimin abinda banaso ba kaff gidan,ita kanta matar tasa ba yanzu zanyi maganinta ba sainazo tafiyah a ƙarshe tukunna,abinda yake raina shizan fara"
"To shikenan Allah yabaki sa'a,yadai naji Haidar sai kuka yake lafiya"
"Hmmm ai Hilyaan kina ƙoƙari sosai da yaronnan,wlh iya yau duk narasa yadda zanyi dashi,ko fita zuwa training na gagara zuwa fah yau,gashi khmis ma bayanan,waɗancan direbobin sai signarsu nake gani a cikin jeji"
"Hhhhhh gwanda ki saba ai,karki manta fah ke uwace, yakamata ki saba da ɗawainiyar danki"
Hilyaan ta karisa maganar cikin dariya.
"Zanyi wanda nayi,in yagaji ai zayyi shuru,gobe zan shiga cikin gari wajen mutanen gidan can,ki tabbatar fah ki tafiyar da komai yanda ya kamata"
"Karki damu anty zamuyi miki yanda angonki yakeso,ni ina ganin ma kina ganinsa ki faɗa soyayyar sa"
Zaro ido tayi jin maganar takaicin da Hilyaan take yi mata,tun kafin tayi magana taji ta ƙatse ƙiran ƙitt,da alama dama tsokanarta tayi.
Duba wayar tayi taga ƙiran ya katse,cije baki tayi tareda cewa.
"Lallai kinga gadon baccina dayawa,na faɗa soyayyar sa,wannan maganar kuwa zata barni nayi bacci yau?"
Bombee tafaɗa cikin cije baki tana dunƙule hannu.
Da safe data tashi har mai aiki tayiwa haidar wanka ta dafa abinci. Wanka ta shiga,bata daɗeba tafito tana tsane ruwan dayake jikinta.
Riga da wando tasaka kaman na pakistan baƙaƙe,da alama irin shigar yana burgeta,kuma yana daukar jikinta dakuma dirinta ba kaɗan ba.
Zama tayi tashi abinci sosai,dan ma yanzu tarage yawan jin yunwar datake kwanaki..
Ɗaure dogon gashinta mai walwali tayi da ribbon,kafin ta yane kanta da mayafin kayan.
Wani baƙin glass ƙato ta toshe dashi a fuskarta. Kallon madubin dake gabanta tayi na dan wasu mintuna,itada kanta tasakawa kanta dariyah ganin shigar datayi.
Belt ta ɗauka na goyon gaba ta ɗaura,kana tasaka haidar a ciki,wanda yake ta daga ƙafa akan gado,shima yasha baƙaƙen kaya masu tsada.
Baƙar motarta tashiga tayi mata key,bayan ta bata wuta yanda ya kamata...


Read / Download BAƘAR AYAH BOOK 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

3 Comments On BAƘAR AYAH BOOK 2
avatar
ummi-ummi

5 months ago

Reply

My Allah bless you

avatar
taskar

5 months ago

Reply

Replying to ummi-ummi

Ameen

avatar
ummi-ummi

5 months ago

Reply

Ayya next of chapter 4 pls

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album