Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

JAMI'IN DAN SANDA Complete Hausa Novel Document by JAMI'IN DAN SANDA


JAMI'IN DAN SANDA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 85981



JAMI'IN DAN SANDA

Reading Time: 7 Hours

Added On: 10, Nov 2023

Author: Maman Yusuf ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : ????AINUWA ????RITER'S

Author Phone : 07069711327

Book License : Paid

Category: Action Novels

File Size: 506.14 kb

File Type: txt

Views: 1618+

Download: 2079+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: ο»Ώ[6/12, 8:18 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§




*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍




πŸ…ΏοΈ 1




Kuka take sosai har tana shid'ewa ,Yarinya ce 'yar wata ukku kyakykyawar gaske Fara sol Kamar 'yar turawa , kallo Daya zaka Mata kasan cewa ta galabaita tun tana kukan da hawaye har sun daina fitowa ,
Abun mamaki duk wannan kukan da take tana rik'i ne a hannun wani matashin saurayi Wanda bazai wuce shekara 30 zuwa 32 ba , tunda yarinyar ta Fara kuka kanshi yak'e k'asa , fiye da minti talatin ko motsin kirki yakasa Yi duk kuwa da irin yadda kukan yarinyar ke soya mashi zuciya , yanajin kukanta har cikin ruhinshi Amma tsabar tashin hankalin da yake ciki ya Sanya ko motsin kirki yakasa Yi,

A hankali ya d'ago manyan idanunsa Wanda suka rine sukayi jajir yayinda jijiyoyin kansa suka firfito ,kallo Daya namasa Saida na firgita , isashen namiji ne ajin farko Kuma k'ak'k'arfa gaba Daya jikinshi a murd'e yake duk wasu alamun k'arfi sun bayyana a jikinshi ,

Akan yarinyar ya sauke idanunshi kamun a hankali yafara jijjigata , jakar dake kusa dashi ya bud'e wata 'yar gora ya d'auko ya bude ya kafawa yarinyar a baki , ruwa ne ,takuwa Sha sosai sannan a hankali tayi shiru tana ajiyar zuciya,
Kamar wata Mai wayo Haka ta kafe shi da ido suna kallon junansu , a hankali wasu hawaye masu zafi suka Fara sauka akan fuskarsa ,

_Bazan yafe ba , bazan ta'bawa yafewa Wanda duk ya jefa rayuwata a wannan had'arin ba ,tabbas sai na dauki fansa Koda Zan rasa Raina sai na dauki fansa wannan alkawari ne_

_Bazan baka *Muneeba* ba har sai kayimun alk'awari biyu, na farko inason kayimun alk'awarin bazaka ta'ba zuwa Neman fansa ba na biyu Kuma inason ka *Ajiye aikinka na d'an sanda* idan ba Haka ba to bazan ta'ba baka 'yata ba *Hisham* gara ta mutu a nana Hisham ta k'arasa maganar cikin tsananin azabar da takeji ga jini na fita ko ta ina a jikinta,_

Magan ganunta suka shiga dawo Masa cikin kunne Kamar yanzu take fad'a Masa ,
Rik'e kansa yayi dayaji Yana juyamasa Kamar zai cire yayinda zuciyarshi ke mashi wani irin zafi Kamar zata fashe, tsabar bakin ciki yasa ya fasa wata irin k'ara wadda Saida dajin ya amsa kuwa , hakan kuwa ba k'aramun razana *Muneeba* yayi ba nan ta fashe da wani irin kuka a gigice,

Tashi yayi da ita a hannunsa ya duk'a ya dauki Yar k'aramar Jakarshi ya juya yaci gaba da nausawa a cikin jejin,

Dajine Mai matukar girma da had'arin gaske Haka yarinka ratsawa ta cikinshi Babu alamar tsoro a tare dashi, yayinda Muneeba take goye a bayanshi tana baccin wahala, ................✍🏼




*Pls ku taimaka ku tayani share in ya karbu zanci gaba, yan bati siddan asha karatu lfy wannan free ne daga taku 'yar mutan sokoto mmn Yusuf Mai kayan mata*πŸ€—


MARYAM UMAR ABDULLAHI CE........✍🏼
[6/12, 8:18 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§

*Mallakar*

*Maryam Umar Abdullahi*
(Mmn Yusuf)

*Marubuciyar*
*Minene Asalina*
*Mutum ce kuwa*
*Husna ko Huzna*
*And now*πŸ‘‡πŸ»
*Jami'in d'an sanda*


*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍




πŸ…ΏοΈ_2


..............Yayi tafiya Mai nisan gaske kamun yasamu gidin wata babbar bishiyar mangoro ya zauna Yana maida numfashi , zuwa wannan lokacin ita kanta Muneeba ta gaji da baccin hawalar da ya sureta ta tashi , saboda yanayin yadda ya goyata din ma ya Isa ya wahalar da ita,
Wannan karon batayi kuka ba sai sauke numfashi da takeyi a hankalai hannunta Yana cikin bakinta tana tsotsa yayinda take kallonshi tana wutsil-wutsil da kafafu irin na yara,
Shima idon ya tsuramata cikin matuk'ar damuwa da tausayin tilon 'yarshi hawaye ne suka Fara fita daga idonshi suna sauka akan fuskarta , hawayen da bayajin akwai Ranar da zasu daina zuba,
Jin saukar danshi akan fuskarta yasa ta bingile da dariya a hankali ya sakar Mata murmushi ganin yadda take dariyar ,sun shagala sosai Kamar daga sama yafarajin wata irin suwa kadan kadan , juyawa yayi yafara dube_dube , aikuwa sai ganin k'aton maciji yayi ya laulaye waje Daya ya fasa kanshi Yana fitar da harshenshi irin yadda maciji keyi in yaso mugunta ,

A firgice ya mik'e tsaye Yana maimata innalillahi wa Inna ilaihin raji'un Sam ba kanshi yakeji ba Muneeba yake ji da don ta shine da baik'i macijin Nan yayi ajalinshi ko ya huta da wannan bak'incikin,

Take wata zuciyar tace mashi _kana nufin zaka iya mutuwa ba tare da ka dauki fansa akan mak'iyanka ba ? Yana da matukar muhimmanci ka rayu yazama doli karama abunda aka maka_ duk acikin Yan second yayi wannan tunanin ,
Macijin kuwa ya tare hanya ba inda zai ra'ba ya wuce , gashi kiris yake jira ya motsa ya kawo mashi Sara , ganin Babu yadda zaiyi Haka yafara motsa kafarshi a hankali , aikuwa Kamar jira macijin keyi yayi kanshi gadan-gadan da sauri Hisham ya d'aga k'afa da niyar guduwa Amma kamun kyaftawar ido macijin ya kawo mashi Sara a k'afa , wata k'ara ya saki saboda azabar da yaji taga-taga yayi zai fad'i Amma Yak'i yarda ya Kai k'asa hannunsa na rik'e da Muneeba k'am kamar zai maidata ciki,
Yink'urawa maciji yayi yak'a Kai mashi wani Sara a k'afa take yak'ara sakin wata azababbiyar k'ara Wanda baisan sanda ya saki Muneeba ba ya fad'i k'asa , take duniyar tafara juyamashi idanunshi suka Fara gani dishi-dishi hannunshi ya d'aga yanata son yakai ga Muneeba Amma yakasa a hankali idunshi suka Fara rufewa ,yayinda yakejin wani irin zafi a k'asan zuciyarshi , tausayin Muneeba dakuma rashin daukar fansarsa , inaaaa yakamata na rayu, yakamata na rayu wannan itace kalmar da yayi ta nanatawa har idonshi suka rufe ruf,

Muneeba kuwa tana gefe tana rusa kuka kamar zata tashi wajan don taji ciyo a kanta sanadin fadowar da tayi daga hannunsa , a hankali macijin Nan yafara kusantar ta har yaje inda itake , kuka takeyi sosai yayinda macijin ya fasa Kai da nufin saranta,

Kai *Hajar* kamar kukan yaro nakeji ko, ?
" Eh Nima naji saratu na dauka ko kunne na ne yaji ,
"to amma mi zai kawo yaro cikin wannan k'asurgumin dajin Mai had'arin gaske ,? Wanda mu kanmu da muke da tsarin jikinmu ba k'aramun fama mukeyi da miyagun abubuwan dake cikin dajin Nan ba,

"Kinga saratu ba wannan ba zo muje muga Mike faruwa Haka suka mik'e da azama suka nufi inda sukejin kukan yaron,
Kamar daga sama suka hango yaro kwance Yana tsala kuka ga Kuma maciji yana Shirin saranshi, cikin matuk'ar zafin nama da k'warewa Hajar ta fito da bakar ta ta saita macijin , cikin matuk'ar k'warewa ta sake mashi kibiyar suttt sai a tsakkiyar kanshi , take yayi wata irin gumza.yafara birgina a k'asa ,kamun kace mi ya mutu a wajan , da sauri Hajar ta k'arasa ta dauki Muneeba tafara jijjigata cikin harshen fillanci take cewa da Muneeba tayi shiru,

Itama saratun cikin fillancin take cewa ke Hajar Taya Zaki dauki yaro daga ganinshi bazaki tsaya har ki tantance ko mutum ne ba , inba hakaba Taya za'ace an samu yaro anan shi kad'ai" ?..............maganarta ta katse ne lokacin da sukayi ido hudu da Hisham kwance ba alamar Yana numfashi ,
Aguje sukayi kanshi suna dubashi , ganin saran maciji a k'afanshi yasa suka zaro ido waje cike da tashin hankali , Nan Hajar ta dubi saratu tace "Saratu Yi sauri kije ki kiramana Baffah yazo ya dubashi ,
Hajar inaga fa ya mutu kawai kizo mu koma gida inyaso sai mu tafi da wannan yaron daga baya su Baffah suzo su tafi da gawar,

"Aa Sarah Bata tunanin ya mutu kawai kije ki Kira Baffah Ni Zan tsaya anan ................... *daga alkalamin Yar mutan sokoto maman Yusuf*


Karki wuce baki karantaba kila ki amfanaπŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»


πŸƒπŸ’

πŸƒπŸ’
*MAGUNGUNAN CIWON SANYI (TOILET INFECTION)*πŸ‘‡πŸ»
πŸƒπŸ’

*KARIN NI'IMA DA GAMSAR DA MAIGIDA*πŸ‘‡πŸ»


*CUTA DA MAGANI*πŸ’Š πŸ’Š

πŸƒπŸ’
*_Mu na rokon da Allah...


Read / Download JAMI'IN DAN SANDA

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album