Join Our WhatsApp Group

ZABINA BOOK 3 Complete Hausa Novel Document by ZABINA BOOK 3


ZABINA BOOK 3

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 40931



ZABINA BOOK 3

Reading Time: 3 Hours

Added On: 18, Oct 2023

Author: Fauziya Usman ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 261.93 kb

File Type: txt

Views: 533+

Download: 215+

Last download: 3 hours ago

Description/Story: [12/19/2017, 11:55] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 3
0⃣1⃣
By

Fauziya Usman

Safna nazaune adaki tarasa maiyakeyimata dadi sai wani irin radadi zuciyarta take tafada azuciyarta nashiga ukuna maiyake shirin faruwa dani waye kuma Nasir maiyasa yakesona bayan baisan koni wacece ba Zainab tafito daga toilet takalleta tagirgiza kai gaskiya Safna tana bata tausayi saidai bayanda zatayi saidai kawai tabata hakuri kamar yanda tasaba taje tazauna kusa da ita kafin tayi magana Safwan yaturo kofa yashigo Zainab tace yaya Safwan yadakatar da ita da hannan tafiya yake tamkar bayasan taka kasa har ya'isa inda take saidai kanta na sunkuye kasa yazauna kusa da ita idansa sunyi jajir tamkar ansamasa yaji yace haba Safna haba kanwata maiyasa zakiyimi haka maiyasa bakifadama Abba cewa inasankiba kokinasan narasakine kinsan yazan kasance idan narasaki haba Safna kiyi tinani mana maiyasa bakya tausayin zuciyatane kinasan nakasance acikin kuncine aduk kannin rayuwata ko kinasan farin ciki yayi nesa dani kinsan wane irin so nakemaki kobakisan cewa zan'iya rasa rainaba da sauri tadago kai takallesa yayinda kwalla takeyimata zuba afuskarta wallahi zan'iya komai akanki Safna domin kece wadda zuciyata tazabamin amatsayin matar Aure Safna kece ZABINA Safna wallahi dana rasaki nafidasan nakasance acikin kabarina domin idan narasaki acikin duniyarnan bansan ya rayuwata zata kasanceba saidai inada tabbacin zankasance tamkar maraya wanda yarasa Uwa da uba zuciyata zata kasance marar anfani nikaina sai yanda Allah yayi dani domin zanzautu dayawa Safna dan Allah kitaimakeni kisoni kinji yadawo da kallonsa ga Zainab yace Zainab dan Allah kice tayarda tasoni domin nasamu narayu cikin farin ciki tausayin yayanta yakamata tashare hawayenta tace kayi hakuri yayana karka damu insha Allah zaka sameta Zainab da gaske kike zansani Safna tadaga masa kai eh zaka sameta domin tana sanka yadawo gurinta nan yashiga tambayarta Safna da gaske kina sona dan Allah kifadamin naji da gaske kina sona Zainab kice tayimin magana kaga yaya Safwan karka damu yanzu abinda za'ayi katafi daki kaga dare yayi ni zanyi magana da ita kaji to shikenan zantafi amma kitambayarmin ita kiji tana sona zantambayeta Safna zantafi saida safe batayi maganaba balantana ta'iya dago fuskarta takallesa yajuya yayi tafiyarsa yashiga dakinsa yafada kangado yarasa maiyake yimasa dadi zuciyarsa cike take da kunci da bacin rai banda hawaye ba'abinda yakeyi saiji yake tamkar baitaba samun farin ciki ba a'iya rayuwarsa bayan fitarsa Zainab tace Safna kifadamin gaskiya kinasan yaya Safwan kuwa cikin muryar kuka tacehaba Aunty Zainab maiyasa kike tambayana bayan kinada amsar kamarya Safna idan nasani zan tambayekine tayi dogon numfashi tare da ajiyar zuciya Aunty Zainab kenan bantinanin akwai wani abu danake so aduniyarnan fiye da yaya safwan wallahi ina matukar sansa har inaji ajikina idan narasashi komai zai'iya samuna Aunty Zainab tinbansan soba nakesansa kaunarsa tazagaye ko ina najikina banda abinyi banda tinaninsa shi duniyata ne wadda make zaune acikinta rashin yaya Safwan shine babban kalubale arayuwata saidai kuma narasashi Aunty Zainab yazanyi ni ayanzu nafi bukatar mutuwa fiye da rayuwa domin bansan dadintaba rayuwa tamin tsauri farin ciki yagujeni nishadi yayi nesa dani jindadi yakauracemin bakomai atare dani face damuwa da bacin rai bakin tinani da fargabar maigobe zatazomin dashi Aunty Nafisa banda waya mafita banda nahakura narungumi kaddarata wannan shine kawai mafitana waiyo Allah na ya Ubangijina gani agabanka kayimin mafita kakawomin ahajinka kafiddani daga kangin rayuwa ya Allah kayiwa yaya Safwan mafita ka'aiko masa da sassauci acikin zuciyarsa kasakashi farin ciki karabashi da damuwa tafashe da wani irin kuka maitsanani Zainab sai kallonta kawai take jikinta duk yamutu tarasa maizata fada banda kwalla da takeyimata zuba ba'abinda ta'iya aikatawa lokaci daya tausayinsu yakamata yanzu miye mafita yazasuyi tarungumo Safna jikinta tana rarrashinta tare da tinanin miye mafita

Washe gari da safe bayan tayi salla taje kicin domin hada abincin break fast kamar yanda tasaba bayan takarasa tadawo tashiga bandaki tayo wanka tafito tashirya cikin riga da siket na les tafito zata fita Zainab tadakatar da ita haba Safna kibari kiyi break fast mana zatayi magana tace a'a Safna karkice bazakiciba dan Allah tayi ajiyar zuciya tajuya taje tazauna tafaracin abinci lokacin Abba yasauko tagaishesa ta'amsa tare da sakin fuska suna cikin gaisawane Safwan yasauko Abba ina kwana lafiya qlau dafatan kana lafiya ina qlau to madallah kanta nasunkuye tace ina kwana yayana lafiya qlau Safna dago fuskarki kikalleni mana tadago fuskarta sunyi ido biyu taga harzuwa wannan lokacin idansa jajir suke tayi saurin janye fuskarta domin bazata jure kallonsaba tatashi tace Abba natafi school to Allah yakiyaye Amin Abba yaya Safwan natafi adawo lafiya tafita tayi tafiyarta batajima da fitaba Safwan yafita zuwa office zaune kawai yake yabuga wani uban tagumi kallo daya zakayi masa kafahimci yana cikin damuwa Salim yashigo yasamesa yakira sunansa Safwan lafiya kuwa yayi ajiyar zuciya Salim kenan inafa lafiya maiyafaru Salim Abba yazabama Safna mijin Aure kuma ta'amince da ZABINSA Salim wallahi inacikin tashin hankali fiye da yanda kake tinani yanzu haka nima yabani sati biyu akan nafitar da matar da zan'Aura Salim kaina yakulle dan Allah kataimakeni kanemamin mafita wallahi inacikin tashin hankali sosai Salim yace innalillahi wa'inna'ilaihiraji'un Safwan awane hali Safna take wallahi Salim nasancewa Safna batasansa kawai tayardane saboda bayanda zatayi kuma nasan wannan duk tsarin Umma ne subhalillah nasan yau Abba zainemeka domin yasanar dakai gaskiya Safwan lokaci yayi da yakamata ace kasanar da Abba gaskiyar abinda yake zuciyarka domin nemawa kanku mafita

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:55] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 3
0⃣2⃣
By

Fauziya Usman

Salim bazaiyuwuba domin Umma tace batayafe nafada masaba saidai dazaka taimaka mana kaisai kafada masa domin ceton soyaytarmu dama rayuwarmu domin idan narasa Safna inada tabbacin bazantaba kasancewa acikin farin ciki ba domin itace duk kannin wani farin ciki nawa itama nasan zata kasance acikin bacin rai aduk iya rayuwarta Salim dan Allah kayi wani abu akai yayi dogon numfashi shikenan Safwan karka damu zansami Abba zamuyi magana dashi kaji suna tare Abba yakira Salim awaya bayan sungaisa yafada masa yanasan ganinsa yasamesa office ya'amsa dato ya'ajiye waya Safwan yakallesa maiyacema yanasan ganina office dinsa kajiko zancanne zaiyima dan Allah Salim kasan yanda zaka bulluwa wannan lamarin karka damu Safwan zanyi iyakokarina yanzu bara natafi karyaga najima to saikadawo yafita ya'isa office din Abba yabuga kifa Abba yace yashigo yashigo yasami guri yazauna Abba yana kallonsa yasan da akwai wani abu amma yayi kamar baiganiba Abba yakira sunansa Salim kasan dalilin da yasa nakiraka yagirgiza kai a'a Abba to nakirakane domin nafadama natsayarwa da Safna mijin da zata Aura kuma nayi magana da ita ta'amince yayi shiru yana nazari akai Abba yalura dashi sam baya fari'a baya farin ciki Salim lafiya bakomai amma Abba inasan zanfadi wani abu to bismillah inajinka Abba dama da akwai wani wanda yakesan Safna kumashi yakasance makusancinta ne yana matukar Santa nasan zamuyi farin ciki sosai idan har Auranta dashi yakasance duk da cewa bansan waye mijin daka zabamataba amma zanfi farin ciki idan har ta'Auri wannan danake fadama tinda yafara magana Abba yake kallonsa harya kai karshen maganarsa Abba yace Salim waye wannan da kaketa magana akansa yayishiru nadan lokaci Abba yakallai kaga Salim kafadamin wayeshi Abba shiba kowa bane inajinka fadamin wayeshi Abba bakowa bane face Safwan Salim Safwan fa kace eh Abba Safwan yana matukar san Safna kuma inada tabbacin itama tanasansa a'a Salim Safna batasan Safwan da Aure domin tambayarta nayi ko akwai wanda takeso kuma agaban Safwan tace batada wanda takeso sannan shikansa Safwan na tambayesa bansan iya adadin tambayar danayimasaba amma baitaba fadamin cewa yanasan Safna ba yanzu haka nabashi sati biyu yafitar da matar da zai'Aura idan kuma bahakaba toni dakaina zanzaba masa wanda nakeganin tadace dashi kuma yazamemasa dole ya Aureta koda kuwa bayasanta Salim inasan kasan wani abu wallahi da'ace yau Safna zata fadamin cewa batasan Nasir ko takawomin wanda takeso tafadamin cewa shine ZABINTA to tabbas zanbawa Nasir hakuri kuma zan'Aura mata wanda yakasance shine ZABINTA domin burina duk baifi naga Safna acikin farin ciki ba Salim yajinjina kai to Abba Allah yazaba mana mafi alkhairi yashige mana gaba Amin Salim Allah yama albarka Amin Abba nizantafi to nagode yana fitowa mamaki yakamashi Safwan dama kananan eh Salim naji komai duk abinda kukafada tabbas Salim bazantaba samun Safna ba a'a Safwan karkafadi haka zaka sameta kaji sundawo office din Safwan Salim yakallesa kaga Safwan inasan kasani yanzu abu biyune zaisa kasami Safna kasan miya a'a nafarko ko kasami Abba kafada masa ko Safna tasamesa tafada masa amma idan har bahaka kayiba to akwai matsala yanzu abinda za'ayi shine kasami Safna kuyi magana da ita Salim kana ganin Safna zatayarda tomai zaihanata zata yarda mana Salim kenan bantinanin hakan domin haryanzu Safna bata furtamin Kalmar so ba to taya zata furtawa Abba ninasan bazata iyaba karka damu Safwan zatayarda nina fadama to Allah yasa Amin bayan yatashi daga office yadawo gida yasami Umma da Zainab afalo yasami guri yazauna yaya Safwan andawo eh Zainab yagidan qlau Umma ina wuni lafiya ya'aiki Alhamdulillah yana kokarin tashi Habu yashigo tare dayin sallama yagaishesu sun'amsa yace Hajiya inayiwa Safna sallama awaje lokaci daya Safwan yaji zuciyarsa tabuga masa da karfi kansa yawani sara yajuyo da sauri yace kaje kace batanan ya'amsa dato zaitashi Umna tace Habu kace tana zuwa to Hajiya yafita yayi tafiyarsa Umma tace wallahi Safwan kakiyayeni tinkafin raina yabaci domin bazakaji dadinaba Zainab kije kifadamata tafito tayi bako ta'amsa dato tatafi tasameta akwance idanta arufe ga'alama tinani take ta isagareta tadafata tare da anbatar sunanta Safna ta'amsa tare da buda idanta Aunty Zainab kinshigo eh tinaninme kike a'a ba'abinda nake tinani Safna kinyi bako awaje tafada da sauri hartana sarkewa bako kuma Aunty Zainab eh wayeshi o banda abinki wakuma zaizo banda Nasir Aunty Zainab ina yaya Safwan yana falo tagirgiza kai gaskiya Aunty Zainab bazan iyafitaba Safna kenan hakuri zakiyi domin Umma zata'iyayin fada dake idan baki fitaba yanzuma itace tace nazo nafada maki nashiga uku Aunty Zainab yazanyi da raina kiyi hakuri Safna kitashi kitafi kinji ta'amsa dato tasanya hijabinta tafito tasamu Umma da Safwan afalo ga'alama magana suke Umma takalleta Safna maikike nufi haka zakifita daure da fuska saikace wadda akayiwa mutuwa tadaiyi shiru batace komaiba dan Allah wuce kitafi saura kuma idan kikatafi kiyi abinda zaisa yafahimci cewa bakyasansa to aisaiki tafiko tana cikin tafiya Safwan yakira sunanta Safna tatsaya batare da tajuyoba haba Safna haba kanwata yanzu fita zakiyi gurin wani da sunan zance bayan kinssn inasanki haba Safna kiyi tinani mana ko kinasan zuciyata tafashene tosaime idan zuciyarka tafashe kaibara kaji nafisan kamace daka Auri Safna wallahi safwwn zansabama kekuma zakitafi kosai ranki yabaci taci gaba datafiya yayinda idanunta suke zubar da hawaye tafito tasamesa jingine jikin mota takaraso inda yake taredayin sallama ya'amsa yana murmushi sannu da fitowa tauraruwa acikin mata barka dafitowa gimbiyata Safna zuciyata tajima tana ssnki fiye da yanda kike tsammani har inajin cewa bazan samun ingantacciyar rayuwaba idan har narasaki domin kekadai zuciyata keso inasan kiyarda dani kikuma amince da soyayyata domin nasamu narayu cikin abinci

By. Fauziya Usman
[12/19/2017, 11:55] Maman Adyan: ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤ZABINA❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Part 3
0⃣3⃣
By

Fauziya Usman

Tayi shiru takasa fadar komai banda hawaye sukeyimata zuba ba'abinda ta'iya cewa shikuwa sai kallonta yake cikin kasa-kasa da murya yace Safna lafiya maiyasameki kukanme kike dan Allah kifadamin domin zuciyata tasami sassauci Safna bakya sona ne ko kalamaina sunbata ranki Safna dan Allah kitaimaka kifadamin abinda yake damunki kinbarni aduhu kinbar zuciyata cikin kunci cikin muryar kuka tace bakomai kawai banajin dadin jikina ne shiyasa haba Safna wannan aiyawuce kawai yanzu abinda za'ayi shine kitafi gida kisamu kikwanta kihuta kinji tadaga masa kai tajuya tayi tafiyarta yakira sunanta amma batatsayaba yagirgiza kai duk tausayinta yakamashi yafada azuciyarsa lallai Safna tanajin jiki tadawo tasami Umma itakadai afalo takalleta haeyatafi eh yatafi tayi tafiyarta daki bayan tashige Nasir yakira Habu yabashi wasu manyan ledodi guda uku yace yashigar mata dasu shikuwa yayi tafiyarsa Habu yashiga tare dayin sallama Umma ta'amsa masa yace gashi yace akawoma Safna to tagode ya'ajiye yayi tafiyarsa Umma sai wani dadi takeji Safna nashiga daki tafada kangado ba'abinda take sai kuka Zainab tazo gareta haba Safna dan Allah kidena kukannan haka karwani abu yazo yasameki kinji cikin muryar kuka tace Aunty Zainab wallahi banasansa ni yaya Safwan nakeso shikawaine araina shizuciyata take kauna wallahi banasan narasashi domin shine duk kannin wani farin ciki nawa waiyo Allah na ni Safna maiyake shirin faruwa dani maiyasa mutuwa bazo tadaukeniba maiyasa haryanzu nake araye a'a Safna dan Allah kidena fadar haka domin rayuwarki tana da anfani kuma Allah shiyasan abinda yake nufi da hakan dan Allah kidena irin wannan zancan kinji Abba yadawo yasami Umma da Ammar afalo Abba sannu da zuwa yauwa sannu da zuwa Abban Safwan yauwa yana ganku kubiyu inasauran yaran suna ciki maisukeyi to wayasani yauwa Abban Safwan aiki Nasir yazo Allah sarki ashe yasami zuwa eh to yasami ganin Safna eh kagama kayanda yakawo mata kai amma yakyauta Allah yasaka masa da alkhairi Amin

Bayan kwana biyu Abba yalura da gidansa komai yakara damewa amaimakin gidan yayi haske saima duhu yakara tabbas akwai matsala sosai datake addabar 'ya'yansa kuma sunki susanar masa gashi abin yana matukar damunsa fiye da yanda basu tsammani wata rana Safwan yadawo office yasami Safna da Nasir atsaye duk dacewa yalura Safna bata cikin walwala amma ransa abace yake zuciyarsa sai wani zafi takeyimasa saiji yake kamar yafasa ihu idansa sunyi jajir yanayin datagansa yadaga hankalinta sosai domin tafahimci yana cikin bacin rai da damuwa sosai ya'isa kusa da ita yayi tsaye yana kallonta itama kallonsa take...


Read / Download ZABINA BOOK 3

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album