Join Our WhatsApp Group

IDAN RANA TA FITO 1,2 and 3 Complete Hausa Novel Document by IDAN RANA TA FITO 1,2 and 3


IDAN RANA TA FITO 1,2 and 3

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 67744



IDAN RANA TA FITO 1,2 and 3

Reading Time: 5 Hours

Added On: 30, Sep 2023

Author: Halima K Mashi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 404.87 kb

File Type: txt

Views: 2091+

Download: 1115+

Last download: 2 days ago

Description/Story: VISIT www.aihausanovels.com.ng For More Novel.

AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers.



We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors



We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission.



AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ?auke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.



Mun samar da littattafan hausa na nau'uka daban-daban, kama daga littafin, soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa.

IDAN RANA TA FITO

NA
Halima m/mashi
PAGE 1.....! Na karama motar idanu kai bani ba ma duk mutanan da ke kauyan kallon motar suke domin ni dai a sanina wannan shi ne karo na uku daga na mota kuma duk gidan hakimi take zuwa wato gidan maigari dai su ne suke da yan uwa a birni,na bi motar don in ga gidan da zata na ma manta da batun aike na a kayi kaikuwa kofar gidan maigari ta tsaya,na kuma ci gaba don ina matukar so in ga cikin motar ina son sanin ko kamar daki take? Zare idanu na yi lokacin da naga wanda ya fito daga cikin motar wani saurayi ne dan birni me kyau yana sanye da wasu irin kaya,ga kuma wani kamshi yana tashi.Sam ban san na saki baki ina kallonshi ba,ya nufi cikin gidan maigari ashe nima na bishi ban sani ba sai kurum na ji ni cikin kwata,lokacinne fa hankalina ya dawo na gane me nake yi,na kuma tuna zan je siyan kanwar miye ne.Lallai yau zan ci duka gurin Baba Gaje,babu rana ta banza da ba za a dake ni sau uku ko sau hudu ba na sani wani lokacin da laifina domin bana ganin abin kallo na wuce kuma abin mamaki ba ya wuya a gurina.Lokacin da na....! Lokacin da na dawo siyan kanwa sai da na kuma yin zagaye ta gidan maigari ko zan sake katarin ganin motar tare da wannan dan gayun dan birnin.Abinda na gani yanzu shine ya fi bani mamaki tare da daure min kai.Wata yar karamar a ba ce na gani a hannunshi ya kara ta a kunnanshi yana ta magana shi kadai ba ni ba har samarin kauyan kalloshi suke ringa yi.Ya shiga motar ya tashe ta,na so in matsa kusa da motar in taba ta ko dan in karasa amma in tsoro,haka ya tasheta ya tafi ban nufi gida ba sai da motar ta kule.Ina isa na hau rabe-rabe saboda hangowar da nayi Baba Gaje tana kwashe tuwonta,miyar kuma tana aje gefen murhu,da alama an sauke ta tuni.Ta banko min harara "sai yanzu ki ka ga damar dawowa? Yar iska shegiya matsiyaciya babu,abinda zai hana ni kirbarki yau yar asara". Na soma kuka ina cewa "Don Allah Baba kiyi hakuri". Lanto ta dube ni ke ina ki ka tsaya ne?cikin kuka na ce um....um kofar gidan maigari ne a ke kallon mota shi ne fa na dan tsaya..." Ta katse ni kallo koh? Na yi shiru,ta ci gaba da shararta.Jummala da ke can gefe ta ce "ai kallon Haka matan gidanmu suka yi ta surutu.Baba Gaje tana ci gaba da sine min, dama haka fadan gidanmu yake musamman a kaina babu wanda ke bada hakuri domin kowa yasan masifar Baba Gaje kuma tsoronta suke yi, domin ta fi su samun kudi sana'o'i babu wanda Baba Gaje bata yi, kuli, goro, man gyada, shinkafa da wake ga kuma koko, sannan duk kauyen mu ita ce uwar adashe. Ina labe bayan rumbu ina ji Babana na nemana, na fito in shashsheka,

2...Ina la6e bayan rumbu ina ji
Babana na nemana, na fito ina
shashsheka, ya ce "Jidda wai me
yasa kullum sai kin nemi laifin da za
a ta6a lafiyarki ne?" Cikin
shashshekar kuka na ce,"Baba siyan kanwa aka aike ni." Ya kama
hannuna shine ki ja samu kallanki
na tsiya ki ka dade ko? Na ce mota
ce kofar gidan Maigari shi ne na dan
tsaya ya ce, na ce ki daina tsayawa
kalle-kalle kin. Gaje dai dukanki zata yi, eh dakunta zan yi Muka ji muryar Baba Gaje dama kun saba
ku dunga la6ewa kuna zagina duk
wahalar da nake da ita ba a ganoma
ba zan yarda ba, ehe." Baba ya ce,
Saurara Gaje ni ba na hana ki dake ta ba ne ina dai yimata nasiha ne ta daina tsayawa kalle-kalle, amma
yanzun ki mata hakuri in yaso nan
gaba in ta kara sai ki dake ta. "Ai
wlh sai na dake ta, kuma ba za ta ci
tuwon gidannan ba. In aike ta don ita 'yar tsinanniya ce sai ta je ta yi zamanta, tasan zata fita da goro ta
dan zaga don mugunta ta ki
dawowa. "Na ce kiyi hkr
don......"Kafin na karasa na ji saukar mari. Baba yasa kai ya fita
don na sani ba zaya iya ganin halin
da zan shiga ba ne dama nata tsarin
in tana dukana duk wanda ya ce
tayi hkr to zata ce yana goyon
bayana ne. Daga nan sun kulla gaba ita dashi, in kuma tana gaba da ke to doke ne duk matan gidan su
daina shiga harkarki, in kuwa wata
ta kula ki to itama ta shiga. Bisa ga
wannan dalilin sai dai su sa idanu, in
ma za su yi magana sai dai su ce maganina kenan duka, haka ta jibge
ni son ranta ta sake ni tare da
shurina da kafa tayi tafiyarta, na ci
kukana na gaji na koma gefe na
ra6e. Su Indo da Shafa suka biyo
mana gada Hinde ta fiti 'yar gabn gishin Baba Gaje kenan, ta kira Salame da Laminde suka fita, na
tashi zan bi su duk da na san Hinde
zata iya koro ni sai Baba Gaje ta ce,
"Ke Kuluwa zo nan yau in ake ba
zuwa dandali sai dai kai goron nan na dawo nta nuna min tiren gashi can kin san kudinshi saura kallon ki
na tsiya ya ja ki bar goron yau ki
sha wuya, ni dai na fita." Muryar
Baba na ji ya ce,"Jidda ya ki nan." Na
je na tsugunna "Gani Baba. "Ya ce,"Ungo, nasan ba ki ci abnci ba
ko?" Na ce, "Eh." Bakar leda ya bani
ban san ko me ciki ba, ya ce," kici
kin ji? Tashi ki tafi. Ina za ki ne da
tire?" Na ce "Dandali zan kai goro."
Ya jinjina kai "kada ki damu ki zama mai hkr, Allah yaba tare da masu hakuei, tashi kije ki kula da kanku
da kuma sana'arki kin ji ko?" Na ce
"To Baba....
[18/09 9:00 am] Inna👬👫: Idan rana tafito

3... Sai da na tafi na duba naga rogo
ne da kuli, a fiki na ce Allah Sarki
Baba, Ina tafe ina ci sam ban ankara
ba sai ji na yi na ci karo da mu2m,
tuni tiren goron ya yi baya ya fadu
na fara kallon da wa na ci karo gabana ya fadi ganin Ado. Yana
tsaye yana kallona. na duka na
soma tsince goron ina fadin nashiga
3 na yau zan sha jibga in ban gansu
duka ba... Ado ya tsugunna tare da
hasko cocila 'yar karama duk da cewa akwai hasken farin wata
musamman yau watan yana 14 ya
ce duba a hankali na kalli cocilar 'yar
mai kyau ba kalar ta Babana ba da
ya ta6a sautu birni a ka siyo mishi,
sai na ji muryarshi yaba cewa ki duba mana me ki ke kallo haka? Ban
ce komai ba na ci gaba da
duddubawa banga wani ba ya ce
kirga ki gani ki ya cika, na ce ban
san ko na nawa ta zuba ba, ita ce ta
kirga da kanta, ya ciro naira 10 nawa nawa ne goron? Na ce"Da na ficika ne da na kwandala." Ya mika
min 10n "To rike wannan ki cika." Ya
yi tafiyarshi na bishi da kallo, ko
cikin mafarki bn ta6a zaton Ado
zaya iya yi min magana ba, saboda Ado Saurayi ne mai girman kai
game da jan aji, in ji 'yanmatan
kauyenmu sannan shi kadai ne ya yi
boki duk wata wasika in za a rubuta
ko za a karanta sai annemi Ado, duk
cikin kauyan shi ne babban yaron Maigari kuma duk kauyan babu
wanda ya kai Magari dukiya,
dabbobi da gonaki sannan su kadai
ne ke zuwa birni. Jin an dauke tiren
goron daga kaina sai na dawo cikin
hayyacina yare da yin firgigit don ganin ko waye.......Bint o ce kanwar Ado, ta ce Kuluwa garin kallo wata rana sai an sace ki, nayi
'yar dariya na ce "Binto ina za ki?"
Ta ce, "Dandali can za ki kai goron?
Na ce, "Eh." Ta ce "hu'um, ke dai
gaskiya ba kya hutawa gashi kin daina zuwa Mkrnt, na ce kema Binto
kin sani in ban ke ba duka zan ci
Mkrnt kuwa saboda kudin Laraba, ta
ce in daina zuwa da Baba ya bani
kuma ta kwace ta ce bani ba Mkrnta.
Binto ta ce, shi yasa na daina zuwa gidanku ce min take yi in daina kula ki kai ke kula Maza ne da ke su
Hinde sune dai-dai ni ni ko kin san
ko a dandali rana daidai ce ba ma
kwasar ta da su akanki....ko kin zo
ko ba ki ba, a haka muka isa dandali na zauna kusa da mai gyada don ta kunna aci balbal, wato fitlar
gwangwani
Mar 6, 2015
Aisha Ummu Shureim Sa'eed
4..Binto ma gurina ta zauna muna ta
hira ina bata labarin karon damu ka
yi da Yayanta, lokacin da muka
dawo gida ba wanda ya sai
goron,don haka sai na mika mata
naira goman a zuwan cinikin da nayi, ta zauna ta kirga goronta
sannan ta dube ni "Siyan goron aka
yi?" Na ce "Wani ne ya zubar min
bai sani ba shi ne ya bani."Ta daga
zaninta ta saka cikin lalitar ta tare
da cewa "Irinsu ake so, shi ko wannan wanene? Na ce "Ado ne na
gidan Maigaro."Hinde ta mike tab
karya ki ke yi, Adi ne zai saurare ki?
Sai dai in Mazan ki ki ka kula kalmar
na bakanta min rai suna nufin ni
'yar isla ce. Cikin Muryar kuka na ce kai Hinde da yaushe na kula Maza? Baba Gaje ta ce to sarkin ruwan ido
ke da ba kya raina abn kuka, in ma
Mazan ki ke kulawa ina ruwana ni
dai kudi na sani. Mikewa na hi naje
nayo alwala don yin sallah dama kullum ba a barina yin sallah sai dai in na zo kwanciya in hada gashi an
ce hada sallah babu kyau, su Baba
Gaje ma sallar ba damun su ta yi ba,
koda zata yin ma sai dai ta yi ta
dokota ba tare da tasan hukunce- hukunce nta ba. Na dawo a gajiye ga yunwa, murnata daya shinkafa da waken sun kare, na shigo da
kwarin gwiwata. Baba Gaje tana
suyar kuli ba mika mata kudin ta
kirga sannan ta kalmashe ta zuba
cikin lalita ga sauran tuwi can dauki kici ki zo ki fita da wancan kunun, na dube ta Baba bana Hinde ba ne? Cike
da masifa ta hayyako min, eh nata
ne ta gaji don haka maza ki fita da
shi kuma kada ki dawo min da ko
kwano daya ne hakan na fita da kunun tsamiyar, ina Hawaye
tsautsayi na fito ta lungun gidan
Liman zan bi layin gidan Maigari
domin in kai ma wasu masu faskare
icen gidan Maigari kawai sai ga wani
yaro ya shigo da gudu ya bangaje ni kafin na yi wani kokari tuni tiren ya fado, kunun ya zube........... Jikina yana rawa na shiga kuka ina cewa sai naje gidanku an biya ni n
[18/09 9:00 am] Inna👬👫: IDAN RANA TA FITO
( 7)..! Na ce ta rasu, nan na soma kuka domin tunowa da na yi da mahaifiyata, ya ce daina kuka kada wani ya zo wucewa ya ji ya zargi wani abu daban, Allah ya jikanta. Cikin kuka na ce Ameen. Na dube shi. Mahaifiyata yar kauyen Rimi ce a can sumaila, shi ko Babana dan asalin nan kauyanne, wato farau ta nan Garko. An ce ya auro ta ne sanadin wani abokinshi, wanda ya kasance dan Rimin mahaifanta sun rasu sai wanta gurin shi take zaune kuma shi ne ya aurar da ita ga mahaifinmu, kamar yanda ka sani gidanmu gida ne da ya tara yan uwa wato gidan gado. Babanmu shi ne babba yana da kanne hudu kowanne da matarshi sai ko autarsu Baba Dije tana aure a sekahu, mahaifiyata ladidi ta samu Gaje uwargida da ya yanta shida. Sani da Awwalu da Musa, isa da kuma Hamisu sai cikin Hinde masifaffiya ce sosai, kaf gidan kowa tsoronta yake ji haka nan shima Babanmu yana shakkarta yanda Babana yake bani labari tun da aka kawo mahaifiyata gidan sam bata huta ba duk ayyuka da na gidan da na saidawa mahaifiyata ce ke yinsu, ko lokacin da take da cikina ba sauki rai da take mata,ya ce min ....! Wasu ma suna zargin cewa ita ce ajalin mahaifiyata domin ita ce a kanta lokacin da zata haihu, ta hana kowa shiga har ta haihu sannan ta fito ta sanar da haihuwar tare da rasuwa, a nan ne kowa ya zarge ta sai dai babu mai hujjar fadin hakan. Da wuya tana kisa kila da na mutu tun ina jaririya, madarar shanu nasha na girma ko yaushe ina gurin babana saboda Baba Gaje bata da lokacina kuma ta hana wasu su dauke ni in nayi kashi kuwa zagi da tsinawa haka take min uma sai dai mahaifinah ya wanke min, lokacin da na soma zama zuwa rarrafe idan nayi mata yarban nata yara dukana take yi iyaka karfinta hakanata so, babanah ya ce ba zai manta lokacin da na yi kyanda ba ya cire rai da ni danta yi min mugun ka mu gashi babu kulawa shi ne ya ke jinyata, ya ce a duk sanda ya fita neman dan na cefane ko yaje masallaci ko a ka kira shi yin aski baya sa ran cewa zai dawo ya same ni da rai in ma kashi nayi ko amai ko dai wani abu haka sai sanda ya dawn zaya gyara ni shi ne ya koya min sallah da kuma karatu, kai duk wata tarbiya da ya dace uwata ko ya ma yarta shi ne ya koya min sai da na soma zuwa makarantar allo sannan Baba Gaje ta maido dani dakinta ashe da! Ashe da manufa tayi hakan, nan ta kara sana'o'i talla kuwa tun daga lokacin na duka yinta ina siyar na tsira in ban saida ba duka, sannan Hinde in ta dawo da nata ni ce zan hada duka. Ado ya yi ajiyar zuciya cikin tausayi ya ce toh sauran mazan gidan dukh babu wanda zaya iya daukan wani mataki kanta??? Na ce babu saboda gurinta suke rancan kudi randa basu samu ba ka gako ba za su so su bata da ita bai ni fa gidan bani da wani gata sai mahaifina haka kuma ya yansu su hadu ne kanmu daya dasu amma ban isa ko magana in suna yi in saka baki ba, sai su shiga zagina ya ce yau fa wane laifin ki ka yi??...


Read / Download IDAN RANA TA FITO 1,2 and 3

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album