Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

GWARZON SADAUKI Book 2 Complete Hausa Novel Document by GWARZON SADAUKI Book 2


GWARZON SADAUKI Book 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 16240



GWARZON SADAUKI Book 2

Reading Time: 1 Hours

Added On: 27, May 2024

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07064681880

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 84.33 kb

File Type: txt

Views: 1510+

Download: 907+

Last download: 25 minutes ago

Description/Story: GWARZON SADAUKI
Littafi Na Biyu (2)
Part A
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey
AI'amarin jaruma Ilaila kuwa ko da ta ga an harbo kibiyoyi an kashe abokan tafiyarta guda shida nan take sai ta yi wuf ta suri garkuwarta da takobinta ta shammaci mai hular karfe ta gabza mata naushi a ka da garkuwar dake hannunta.
Saboda karfin naushin sai da mai hular karfen ta hantsila baya ta rinka mirginawa a kasa izuwa can inda koramar nan take. A lokacin ne aka ci gaba da harbowa Ilaila kibiyoyi amma sai ta dunkule jikinta waje daya ta kare jikinta da garkuwarta. Sai da ta ji kibiyoyin sun daina dira akan garkuwar tata sannan ta mike tsaye zumbur ta falfala da masifaffen gudu i zuwa cikin dajin Hairil Salas sakamakon ta fita daga cikinsa ta bi hanyar da Nazima ta bi!
Haka dai ta cigaba da gudu ba waige amma saita ci gaba da ganin ruwan kibiyoyin wasu suna wucewa ta samana wasu ta gefenta. Kawai dai tsananin sa'a ne da nisan kwana suka sa ko kibiya daya ba ta soke ta ba. Ba ta daina ganin ruwan kibiyoyi ba masu kawo mata hari har sai da ta shafe sama da rabin sa'a tana gudu. A wannan lokacin ne ta yi tuntube ta fadi kasa, ta dinga mirginawa a kasan da gudu ba ta ankara ba sai ji ta yi a fado kasa cikin wani rami mai tsananin zurfin gaske don haka sai ta kurma uban ihu lokacin da ta saddakar da cewar ajalinta ya zo.
Ba zato ba tsammani sai ta ji fanjam ashe cikin ruwa ta fado. Ko da tai nutse izuwa karkashin ruwan sai kanta ya bugu a jikin wani dutse nan take ta suma.
Hakika mai rabon ganin badi ko ana daka shi a turmi sai ya gani, maimakon Ilaila ta cigaba da nutsewa i zuwa kasan kogon da ta fada sai gashin kanta ya nannade a jikin jelar wani katon kifi da ya zo giftawa da gudu. Ai kuwa sai ya janyeta ya tafi da ita yana ta gudu har sai da ya iso gabar kogin sannan gashin kan nata ya warware daga jikin jelar kifin kuma sai ambaliyar ruwan ta hankadota wajen cikin rairayi.
A wannan lokaci alfijir ya keto an fara wata irin iska mai karfi da sanyi, wannan iska ce ta sa Ilaila ta fartado daga dogon suman da ta yi ta mike zaune a matukar firgice sannan ta dubi gabas da yamma kudu da arewa. Ko da ta liga inda take ta tund lokacin da tuntube ta fado kasan rami ta kalli kogin dake gabanta kuma ta hango hisan dake tsakanin gabarnkogin da can saman ramin da ta fado sai ta cika da tsananin mamaki
Ya ya aka yi har na iya ketare wannan kogin na iso nan? Amsar da Ilaila ta kasa bai wa kanta kenan amma sai wani abu ya fado mata a rai ta ce duk yadda aka yi suma na yi sa'adda na fada cikin kogin nan kuma akwai yiwuwar cewa wani ne ya kawo ni nan ko kuma wata dabbar ruwan ce ta janyo ni nan.
Gama ayyana hakan ke da wuya Sai ta hango kyallen wuta a can nesa sosai a bayan wani kogon dutse, da yake har a sannan gari bai|yi gaske ba sai Ilaila ta mike tsaye ta kama sanda ta nufi inda wannar hasken
wuta yake.
Sannu a hankali ta kusance wajen sai ta fara jiyo sautin muryar mutane da yawa suna a hira.
Sai da ta matso daf da su sannan ta labe a bayan kogon dutsen ta kasa kunne tana sauraron hirar da suke yi. Kawai Sai ta gane cewa ai wadannan mutane ba wasu ba ne face rukunin dakarun $umame na চiyu, kuma Shugabansu ne yake cewa "Ya zama wajibi mu yi shiri, mu bi bayan mayakan nan mata wadanda suka rage ba su mutu ba. Kun sani dai labarl ya riskenmu cewa a cikin su akwai wata shaidaniyat da ta fi shugaban yan rukunin farko iya yaki har ma ya ajiye mukaminsa ya bar
dajin nan. A halin yanzu yaransa sun kashe mutum $hida daga cikin mayakan matan, an harbi daya da kibIya a kafadarta amma tsere an nemeta an rasa. Ita ma Wannan hatsabibiyar cikin nasu ta gudu ba a ganta ba. Barita ce ta kawo mana wannan labarin kuma tanal cikin dajin nan tare da wasu daga cikin dakarun rukuni na uku suna farautar ta hatsabibiyar jarumar.
"Lallai duk inda take sai sun cimmata. Yanzu tun da mun yi kalaci sai ku tashi mu hau dawakanrnu mu ruga 1 zuwa can wajen dajin nan domin mu cimma mayakiyar da aka harba a kafada kafin ta isa birmin Misira saboda Sarki Marhat ya ce lallail kada a bar a ta fita a raye. Za mu bar mutum daya jal ya yi gadin komai namu da ke cikin wannan kogon dutse."
Gama fadin hakan ke da wuya sai shugaban dakarun sumame na biyu ya mike tsaye suma sauran yaran nasa sa Suka mike gabadayansu.
Nan take Suka debi makaman yakinsu suka hau dawakal suka bi hanyar da za ta fitar da su daga cikin dajin gabadaya Suka bar badakare guda daya jal zaune a kofar kogon dutsen yana gadi.
Sai da Ilaila ta tabbatar da cewa wadannan dakaru sun yi nsia da tafiya sannan ta cigaba da tafiyar sanda har ta iso bayan wannan badakaren da aka bari gadi bai ji motsınta ba, kawai sai ta hannayenta biyu tal kama kansa ta murde masa wuya, ta yar da gawarsa kasa.
Ckin anzari] ta cire tufafin Badakaren ta sauya da nata, kawai sai ta dauki gawar ta jefa bayan wasu duwatsu yadda babu mai gani ta.
Nan take Ilaila ta dauki makaman yakin badakaren da ta kasheh ta kwance dokinsa ta hayenkuma tajuya da baya, ta nufi hanyar da yan'uwansa suka bi!
Maimakorn laila ta bi sawun dawakan dakarun sai a bi wata hanyar daban wacce za ta iya shan kansu ta ci gaba da yi wa dokinta Kaimi. Ashe wannan hanyar da ta bi anan ne ragowar rukuni na hudu na dakarun Sumame suke kuma kowane rukun sansaninsu daban.
Tabbas zakaran da Allah ya nuta da cara ko ana muzuru ana shaho sai
ya yi. Da gudu bisa doki Ilaila rinka wuce sansanin dakarun sumamen har guda hudun sa dai kawai ta daga musu hannu su daga mata amman babu inda aka tsayar da ita. Dalili kuwa shi ne tana sanye da kakin dakarun sumame na biyu da kuma irin kayan yakinsu ajikinta.
Da yake gabadaya tukuni su shidan sun san junansu kuma sun san kalar tufafinsu da makamansu wannan yasa ta tsallake bincike.
Haka dai Ilaila ta ci gaba da gudu bisa dokinta ba sassauci har sai da rana ta kwalle. A daidaı lokacin ne ta iso iyakar daji da birnin Misira, kawai sai ta hango Nazima a guje bisa kafafunta ga dakarun sumame
bayanta bisa dawakai su ma a guje suna kokarin cimmata amma saboda karfin gudun nata sun kasa cimma ta.
Har i zuwa wannan lokaci akwai kibiya soke a kafadar Nazima ba a cire ta ba, amma saboda juri ya da jarumtaka ta kk yarda dakarun Sumamen su ¢immata.
Saura bai taku biyar ba wani Badakare ya cimma Nazima har ma ya kai mata sara da takobinsa ta sunkuya ya sari iska sai ta daka tsalle ta tsallake iyaka ta fada cikin yankin birnin Misira ta fadi Kasa da ruf da ciki.
Ko da ganin haka sai Dakarun Sumamen Suka kada linzamin dawakansu suka juya da baya suka koma inda suka fito.
Duk wannan abu da yake faruwa Ilaila ta buya cikin duhuwar ciyayi tare da dokinta tana kallo. Har dakarun sumamen suka zo suka wuce ta kusa da ita amma ba su ganta ba.
Ita kuwa Nazinma ko da ta ga dakarun sumamne sun hakura sun koma da baya ízuwa cikin daji sai ta yunkura da nufin ta mike sayc ta nufi cikin birnin Misira.
Kawai sai ji tayi an maketa ta baya. Nan take ta sulale kasa sumammiya. Ba wani ba ne ya maketa ba face jaruma mai hular karfe. Kawai sai ta sunkuya ta dauketa ta dora ta a kan wani doki da ta zoda shi sannan ta hau dokin ta kada shi ta nufi hanyar da za ta kai ta inda kurkukun mata yake na birnin Misira
Lokacin da Ilaiia ta ga abin da ya faru ga Nazima sai ta kada dokinta ta
nausa wani bangaren dabaru na dajin. A can cikin daji ne ta rabu da dokin kuma ta cire tufafin da ke jikinta na dakarun sumame ta sanya nata kuma ta rufe fuskarta, sannan ta sake dawowa kofar birnin Misira ta shiga cikin gari.
Sai da Ilaila ta shafe kwanaki goma sha úku tana boye cikin birnin Misira sannan ta yi shiri rana daya ta yi kundumbala ta haura gidan Sarkin Misira da tsakar dare domin
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download GWARZON SADAUKI Book 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album