Join Our WhatsApp Group

HUKUNCIN ALLAH Complete Hausa Novel Document by HUKUNCIN ALLAH


HUKUNCIN ALLAH

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 229816



HUKUNCIN ALLAH

Reading Time: 19 Hours

Added On: 29, Jul 2023

Author: Aisha Ali Garkuwa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.26 mb

File Type: txt

Views: 4377+

Download: 3860+

Last download: 3 days ago

Description/Story: ο»Ώ
πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*HUKUNCIN ALLAH*

Page 1⃣

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡sss




*"Alhamdulillah na godewa Allah daya bani rai da Lafiya da nitsuwa da konciyar hankali da damar fara wannan littafin nawa Lafiya, ya Allah ina tawassali da kyawawan sunayenka Allah ka bani ikon rubuta alkhairi da abinda zai amfanar da al'ummar musulmi Allah ka tsaremin Al'k'alami na da rubuta sherri, Allah ka kawarmin da Yatsuna da tunani na da idona akan rubuta abinda zai zamo guba ga Al'umar Annabi, ya Allah ka tsareni daga sharrin mutun da Aljani Amin Amin Ameeeeeeeeen ya rabbil izzati."*



*K'warai-K'warai na gane duniya mai sonka shikeyi maka hiddima, tabbas wannan haka yake masoya na naga zahiri ashe dai nidin ce kuke so ni Aysha Aliyu Garkuwar kuke so ba novels na ba, domin da novels nane a zaman da nayi ina hutawar nan da kun mance dani sai gashi wallahi abun mamaki kunfi nunamin kulawa a yanzu fiye da in ina typing Ana kyawun tare masoya na dan nida ku ba mugun tare akeba a,a kyawun tare muke shiyasa gani gareku da wani sabon salon tukuicin ku, sai dai fa ga shawara gareku Reeders duk mai son karanta littafin nan to ta/ya Tarawa kanta/kanshi dan in nayi koda 5 page ba wacce zan Turawa ta Prvt chartπŸ˜‰πŸ˜πŸ˜˜πŸ€πŸ»*








*Z*ahra! Zahara!, sauri ya k'arayi ganin duk kiran da yake mata bata jinshi, dan ta daddage sai rawa takeyi d'an guntun siket d'in dake k'ugunta sai bud'uwa yake, wanda yafi dacewa da a kirashi da sunan tayani tsalle sai 'yar rigarta wacce tayi cib da jikinta kanta a kitse an tubke cukun a tsakiyar kanta amman duk kitson ya tuttujare dan tsufa da yayi.

Sai sautin wak'ar nan mai taken,
Zahra-Zahra kece tauraruwa zahra-zahra kekkyawa kina da kyawu,
na sura,
dake tashi da kind'in daya cika illahirin unk'uwar,
Matasan kuma da ke zaune a bakin d'an Shagon charging sai dariya suke ganin yadda Zahra keta rawa sunata mik'a mata sweet tare dayi mata tafi.

Sauri sosai Yusuf ya keyi har kamar zaiyi tuntub'e yana isa wurin,
ita kuwa tana juyowa ganin yadda ya nufota haik'an k'adaran yasa ta faraja da baya-baya tare da rumtse idanun ta tana sauraron ta ina mari zai sauk'a a fuskarta,
shiko yana isa gareta yatsunshi biyu yasa ya kamo kunnenta ya matse da k'arfi sannan ya juya ya nufi bakin get d'in shiga gidan su da ita,
itako tuni ta saki k'ara tare da yarfa hannu tana kiran.
"Aunty na! Aunty na! Hamma Yucuf a cire min kunne na".
shiko janta yakeyi da iya k'arfin shi dan yana jin zafin yadda k'arfi da yaji ake sake Zahra take abunda ranta keso yarin k'arama amman duk wata rawa ta iya ga bibiko ita ko yaushe tana cikin maza sannan in an gayawa Aunty bata daukan abun da mahimmanci.

A haka suka shiga cikin gidan kai tsaye parlour Auntyn ya nufa da ita,
yayinda Mama kuma ke binsu a baya tana.
"Kai Yusuf sake mata kunne zaka jawo mata ciwon kunne fa."
Shiru yayi har suka shiga parlour inda Aunty take zaune tana jinsu,
suna shiga tace kai.
"wallahi kai dai Yusuf ka sawa Zahra ido,
ai yarinta ce kowa da irin tasa,
ka bar 'yarinya ta huta, in ta girma ai zata bari."

Turata yayi kan kujera sannan ya wuce bedroom yana zuwa durowa ya bud'e wurin kayan ta yasa hannu ya jawo d'an hijabinta, sannan ya fito parlour yana zuwa ya zura mata hijabin sannan ya kalleta cikin tsuke fuska da zaro ido yace.
"Maza b'acemin da gani yanzu d'auki Allonki ki tafi bappa jangird'e in kuma na fito na sameki a wurin Idi mai charge kina rawa sai na karya miki k'afa inga dame zakiyi rawan."
Simi-simi ta fice tana ruggume da Allon nata,
tana fita kamar kullum yadda ta saba in zata tsallaka titin k'ofar gidan nasu sai ta jawo rigarta ta rufe fuskarta sannan ta tsalla ka,
ita in ana duba hanya kafin a tsallaka to ita sai ta rufe fuskarta kuma hon d'in mota ko keke napep baya sata ta bud'e ido bare ta kauce musu,
a hakan cikin sa'a ta samu ta tsallaka ta wuce makarantar Allon nasu.

Tana zuwa ta shiga cikin taron yaran ta zauna sannan ta fara juye-juye tana wani kakkane ido alamar neman rigima aiko tayi tozaki da Amira yar malamin allon nasu
ido ta tsura mata tare da yamutsa fuska ta kuma kalli k'afar Amiran dake da gyambo ga k'udaje sun cika kan ciwon,
yawu ta tsirtar cikin harara da tsiwa tace.
"ke Amira ki rufe ciwonki ni bana son gani."
itama Amira a tsiwace tace.
"bazan rufeba ciwonki ko ciwona."
ganin suna surutu ne yasa bappa jangirden yayi musu tsawa tare da cewa.
"NJange-NJange, be! sini! mimarra! alifi! lallamu! hasakeri!".
sannan ya d'ago bulalan hannunshi tare da juyata kan taron d'aliban nashi,
lokaci d'aya wurin rud'e da karatun yara da 'yan mata da 'yan samarin,
rud'eqar wurin yasa Amira ta d'an matso jikin Zahra har ta d'an goga mata gyambon k'afarta a jikin Zahran,
Itako Zahra tana jin ciwon ya gogeta ta kalli Amira cikin tsiwa ta zaro takalmin robar dake k'afarta sannan ta daddage da iya k'arfinta ta zuba mata takalmin a kan gyambon har saida k'udajen dake kan gyambon suka mace tare da narkewa a cikin ciwon,
wani irin sanda rewa Amira tayi tare da mimmik'ewa ta cillara k'ara mai cike da azaba,
cikin tsoro Bappa jangirde yayi kansu dan duba me ya samu d'iyar tasa,
itako Zahra tana ganin yayi kansu ta mik'e tare da cilla allonta gefe ta cire d'aya takalmin dake k'afarta sannan ta arce a saba'in ta nufu gidan su.


A gidan kuwa tana fita Yusuf ya kalli Antyn cikin yin magana Kai tsaye yace.
"Anty sufa yara amanace ga iyayensu kuma abun kiyayewa ne,
fisabilillahi ya za'ayi ace,
komai Zahra tayi ke bata laifi a gareki,
kullum ita tana cikin maza,
sam bakya kula da suwaye take mak'alewa,
in anyi magana sai kice yarinta ce,
to wallahi in bata nitsuba bazan dena sa mata idoba".
yana fad'in haka ya fice ya haura sama inda d'akinsu yake,
sauri-sauri ya cire uniform nashi dan yaji an fara kiran sallan la'asar a masallacin k'ofar gidan nasu,
A parlour Anty kuwa yana fita,
Mama ta kalli Antyn cikin nitsuwa tace.
"Antyn yara ke kinaga zancen Yusuf shirme ne ko?
to wallahi gaskiya yake gaya miki,
domin kuwa Allah ya kawomu wani zamanin da idan kayi sakaci da lura da yaranka to tun suna k'anana wani gardin banza zai lalata miki 'ya sannan ya rabata da budurcin ta da nitsuwarta
tabbas iyaye sai an sanya lura a kan yara dole kisan shige da ficen 'yarki ko d'anki. "
murmushi tayi tare da cewa.
"Kai Mama insha Allahu ba komai Allah zai tsare mana su."
Ficewa Mama tayi ganin bazata fahimci abinda ake guje mataba.

Shiko Yusuf har ya juyo zai fito d'akin nasu ya sauk'o k'asa ya tafi masallaci sai ya hango Zahra da take gudu da iya k'arfinta ta nufo gida,
k'ara matsowa yayi jikin window nasu yana kallonta har ta tsallako koltan sannan tana shigowa cikin gidan,
ta ratsa gefen get d'in inda aka jera kan pompo
inda yaran mak'ota ke jere suna d'iban ruwa,
tana isa wurin ta tsund'uma hannunta cikin bokatin wani yaro ta fara wonke inda Amira ta manna mata gyambon,
yaro yana ganin haka ya janye bokatin yana.
"Kai Zahra wallahi kin raina min wayo."
bata kulashi ba sai kuma tayi kan sauran yaran ta rink'a tsutstsuduma musu hannu da k'afarta a cikin ruwansu,
suko sai binta suke da harara suna zare mata ido dan suna tsoron dukanta tunda a gidansu suke d'iban ruwa kullum,
gaba d'aya ta jik'a jikinta jigib da ruwa sai d'iga take tol-tol,
Kai ya girgiza cikin Al'ajabin hali irin na Zahra sannan ya sauk'o da sauri-sauri gudu-gudu
a k'asan step d'in sauk'a ya tarar da Anty,
wuceta yayi da sauri,
binshi tayi da ido tare da yin murmushi tace.
"ohoho Zahra am kinga ta kanki,
dan na sani sarai,
yanzu haka wannan saurin da yakeyi ke zai jibga."
Mama dake Bak'in k'ofar parlour tane ta tab'e baki gami da cewa.
"In anbi ta taki a kan Zahra haka zata zama saggartaciya."

Hajja Inna ce ta kallesu cikin yanayin fad'an tsofi tace.
"ai Zahra kam an bonu da ita yarinya sam batajin magana."

ita dai Anty sai Murmushi tayi dan bata fushi kan duk abin da ake cewa a halin Zahra.


Shiko Yusuf yana isa inda suke ya karyo bulala a cikin fulawin dake jere a wurin,
sannan ya rink'a caud'a matashi a sharabanta,
ihu tasa tana tsalle siket d'inta tayani tsalle shima yana tsallen a haka ya rekota har cikin gida,
da gudu ta koma bayan Antyn ta nata kuka tana.
"Hamma Yucif a kasheni
Anty a mutu fa."
hannu tasa ta d'agota ta d'aurata kan cinyarta tana dariya tare da cewa.
"Kai amman dai Yusuf baka da ta ido,
ai ko mutuwa tana kunyan idon uwa."
Hajja Inna kuwa dariya tayi cikin jin dad'i tace.
"ai da kin mutu da bakiyi magana ba,
shegen baki kamar window da bak'ar fuskarki kamar mutanen koma."
shiko Yusuf harara ya watsa mata tare da ficewa ya nufu masallacin.



Da dere bayan anyi sallan ishah,
Yusuf da Sulaiman suka shigo cikin gida yayin da Abba da Daddy ke binsu a baya
suna shiga Yusuf ya jawo kujera a tsakiyar gidan ya zauna cikin d'aga murya yace.
"Zahara! Zahra! ."
da gudu ta fito tazo ta tsaya a gaban shi
cikin tsawa yace. "zauna."
ba musu ta zauna
cikin yanayin nasiha yace.
"Zahra! ."

"Na'am."

"kina jina ko?."

"uhmm."

"Yauwa to Zahra ki nitsu ko,
ki saurareni, dan Allah ki dena fita yawo,
kibar bin maza, ki rink'a zuwa makarantar allo,
kuma in kinje ki dena dukan sauran d'alibai, ki dena neman tsokana, kibar cin zali,
kuma kar in sake ganin kinje bakin shagon Idi mai chargi karki yarda kina yin rawa in yasa wak'ok'in shi,
ki rink'a yin karatu kar kina gudowa,
in kinje ki dena dukan Amira,
kinga d'azuma da kika gudo da naje in tabbayi meyasa kika gudo,
Bappa jangirde yace min Amira kika famewa ciwon ta,
ki kiyayeni karki k'ara."
cikin jujjuya kai ta rink'a cewa.
"a k'ara, a k'ara."
ita a nufinta zatace bazan k'araba a gwarancin ta kuma ya fito kamar cewane take zata k'arane,
hakan kuma yasa Yusuf
kamo kunnenta yana matsewa tare da cewa.
"Sai na karya k'afafun kuma in tsinke kunnen."
da sauri Mama tasa hannu ta jawota tare da buge hannun Yusuf cikin fad'a tace.
"Kai Yusuf cewafa tayi bazata k'araba wallahi kana yawan cin zalin Mama nan tawa."
Mik'ewa yayi tare da cewa.
"Gobe a tsefe miki kai, kuma in naji kina kuka nida ke kuma ni da kaina zan kaiki kitson."
ita dai Zahra da haka tayi bacci.


Washe gari ya kama asabar ba makarantar Boko
dan haka ana idar da sallan asuba Yusuf da Sulaiman suka haura sama suka shige d'akinsu suka rufe sannan suka koma baccin dan hutun weekend.

a K'asa kuma Mama ce taketa koran yaran su tafi makaranta karsuyi Letti kasan cewar makarantarsu Arabic da Boko ne su Al'hamis da jumma'a suke hutunsu dan hanka yanzu gaba d'ayan su suka tafi,
ita kuwa Zahra sai tsallenta taketayi bayan Anty ta gama komai tayiwa Zahra wonka ta wonke mata kai sannan ta shirya ta cikin irin 'yan guntayen siket d'inta,
da suke k'ara mata rigima
sannan ta shimfid'a taburma a tsakiyar gidan ta kamo Zahran da nufin fara mata tsifar kan nata
aiko ta fara tirje-tirje da koke-koke tana jada baya,
sanin halinta sarai ba yarda zatayi ayi tsifan da sauk'iba,
yasa ta fizgota ta fara mata tsifan,
aiko ta daddage ta b'are baki sai kuka da ihu take,
duk ta damula fuskarta da hawaye da majina,
ganin Antyn nata bata da niyar saketa yasa ta daddage ta takafa hak'oranta a cinyar Antyn ta kafa mata cizo,
da sauri ta saketa tana shafa inda ta cijetan,
ita kuwa ana saketa tayi bakin gate a guje ta bar gidan ,
tana fita da kai rabi a tsefe rabi a kitse tayi bakin titin inda taron matasan unguwar dama na wasu unguwannin suke taruwa.


ita kuwa Anty cikin ko in kula taci gaba da harkokinta,
har zuwa k'arfe goma na safen Amman ko a jikinta batama yi cekiyar ina d'iyarta mace ta shigaba bare tasan da su waye take tare ba,
Ammi ce ta d'an lura da dad'ewar da Zahra tayi bata shigo gidan ba sannan ta kalli amaryar tata cikin ganin sakacinta tace.
"Wai yanzu bazaki binciki inda Zahra ta shigaba ba ko."

cikin ko gezau tace.
"Ya wuce tana shagon Idi ne,
ko tayi bacci a can."

"kin tabbatar tana can d'in kenan? sannan inma kin tabbatar d'in,
shi Idi kina da tabbacin halinshi ne da d'abi unshi ne? ke yanzu ranki ya gamsu da kibar 'yarki mace a tsakiyar Maza?."

ta bud'e baki da niyar zatayi magana kenan suka jiyo kukan da Zahra takeyi tare da ihu,
da sauri suka juyo gareta
Cikin tsoro Ammi ta nufi inda take ganin yadda take tafiya tana tangad'i da layi,
sannan ga pant da siket d'inta a hannu duk an tub'e matasu,
cikin zaro ido Ammi tace.
"Ke Zahra waya tub'e miki kayanki harda pant d'inki?. "
cikin wani irin sautin kuka tare da yarfa hannu tana shafa k'ugunta tace.
"Id........!!!



πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*HUKUNCIN ALLAH*

Page 2⃣

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡




*DEDICATED to Aisha Aliyu Tsamiya*






*"I*di ne a ciremin." ido Ummi ta kuma zarowa cikin wani irin yanayi ta kalli Antyn dake zaune a gefensu ta tsura musu ido da yanayin rashin karaya a tattare da ita,
tsaki ta d'an ja sannan tace.
"Zahra am komai ya faru dake da sakacin mahaifiyarki domin ita sam bata d'auki kula da tarbiyar yara da wani matsayi mai girma ba sam bata lura da zamanin da muke ciki na yawaitar *Fyad'e* akan yara k'anana ba."
sai kuma ta jawo Zahran wacce take ta layi da lumshe ido,
K'ugunta ta tsurawa ido ganin yadda take ta sosa wurin,
ganin duk ta birkice da kuka yasa Ummin ta fara haurawa saman step d'in da da zai kaita sama inda Daddy dasu Yusuf suke,
haurawa take tana kiran.
"Yusuf! Yusuf! ina kake ? maza fito kazo kaje gun Idi mai shago, ka tabbayeshi dalilin me zai cirewa yarinya suturarta?
kuma ya shirya abin da zai cewa Daddyn ku."
Shiru tayi ganin Yusuf daya fito daga...


Read / Download HUKUNCIN ALLAH

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album