Join Our WhatsApp Group

MUSAYAR RUHI Book 1 Complete Hausa Novel Document by MUSAYAR RUHI Book 1


MUSAYAR RUHI Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 43309



MUSAYAR RUHI Book 1

Reading Time: 3 Hours

Added On: 25, Jan 2024

Author: Npeedy A Aji ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : KAINUWA WRITER'S

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 289.88 kb

File Type: txt

Views: 469+

Download: 220+

Last download: 10 hours ago

Description/Story: *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*


*NA*


*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_



```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*


AND NOW
```MUSAYAR RUHI```



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*



*Page 1 & 2*



*W* ata kyakkaywar matashiyar budurwa yar kimanin 23 yrs zaune cikin makeken Parlour gefanta kuwa qawayentane kowacce tazubamata ido cike da shi'awa sabida yadda tayi masifar yin kyau kasancewar yau saura kwanaki 2 kacal d'aurin auranta suna cikin hidimar biki event suketayi kala kala amma batare da ango ba sabida shikam bayama qasar se ranar d'aurin auran zaidawo waya takeyi cikin shagwa'ba

" _Haba my D wai ace yau saura 2 days bikin mu amma har yanzu kaqi kadawo gaskiya nafarayin tantamar Soyayya ta gareka kai bakanan amma ko katuromin bro d'in naka tunda babu wanda zaigane bakai bane gashi kasa sefaman jin kunya nikeyi cikin qawayena gaskiya banji dad'i ba "

Ajiyar zuciya yasauke daga wancan 'bangaran yace " am sorry my B kinsan yanayin aykin nawane haka amma ay kinga inadawowa Nigeria 🇳🇬 zancigaba dayin ayki anan dole nagama dakomi kafin nadawo sabida inaso muyi rayuwa irin wadda se'anyi kwatancenta rayuwarmu zatazama abin shi'awa gakowa sannan kidenayin tunanin wai Hammat zezo wajan shi'aninku kinsan halin shi indama zanbiye tatashi dabanyi wannan auran yanzuba ki kwantar da hankalin ki kafin lokacin d'aura auran mu nashigo cikin Nigeria in sha Allah nide inaso kiriqe amana my B kinsan ina matuqar son ki please don't forget me "

Murmushi tayi tace " haba my D tayaya kake tunanin zan barka please kabar wannan maganar duk wuya duk rintsi inatare da kai " ajiyar zuciya yasauke daga 'bangaran shi yace " idan hakan takasance zanyi farinciki sosai "

Sunjima suna waya cikin tsananin Soyayya gaskiya wannan Soyayyar tasu tamusamman ce bayan tagama wata daga cikin qawayen tana tayi murmushi tace " gaskiya Hamidat wannan Soyayyar taku tana matuqar burgeni sosai Allah yasa nasamu mai sona kamar yadda Hamut yake sonki " murmushi Hamidat tayi tace " Amin shiyasa nike mugun alfahari da Hamut sabida yagamayimin komi a rayuwa tunda yabani zuciyar shi "

Murmushi kowa yasaki cikin tayata murna dede lokacin wata matashiyar budurwa taqaraso wajan sannu tayi musu sannan tadubi Hamidat tace " Aunty Momcy nakiranki " miqewa Fadila tayi tabi bayanta wani madedecin Parlour suka shiga sannan suka shiga cikin bedroom d'in Momcy zaune take itada qawayenta da wasu daga cikin qannanta fita qanwar tata tayi gaidasu Hamidat tayi suka amsa cikin sakin fuska zama tayi tace " Momcy gani " murmushi Momcy tayi tace " ay iyayen naki sunada yawa Hajiya Shahuda kekiranki " duban Hajiya Shahuda tayi Hajiya Shahuda aminiyar Hajiya Salima ce wato Momcy su Fadila tare sukeyin shawara akan komi dazasuyi duban Fadila tayi tace

" Hamidat mahaifiyar ki tasanar dani cewa bakison shan magungunan da'aka had'a miki ko maiyasa kinsan halin maza kuwa? sunason mace tamusamman daga ranar farko samun darajar mace ko rashin samunta zaikasance agun mijin nafiso Hamut yarikice akanki fiye da tunani Hamidat kinsan waye Hamut samun namiji irinshi akwai wahala dan gaskiya baqaramin sa'a kikayiba kina shiga kinzama gimbiya zuwa wani lokacin kad'an zakizama Sarauniya tunda shine maijiran gado " cikin sanyin murya tace " su 2 de Momy kokin manta twins ne su Hamut dakuma Hammat kuma kowanne yacancanta yayi sarauta dan duk sunhad'a komi sannan nifa kunsan yanayina keda Momcy inacikin mata masu qarfin shi'awa dan Allah karkusa nayi abin kunya yazama nice nanemeshi bashine yanemeniba kunga idan hakan takasance darajar tawa tazube kenan sabida Hamut zaiga kamar nasaba da yin lamarin dan Allah kubarni haka wanda nashama nikad'e nasan cikin halin dayasakani " murmushi Hajiya Shahuda tayi tace " yaro yarone tabbas nasan Hamut da Hammat Twins ne amma ay Hamut shine Hassan ko kinga kenan shine babba shine mai hawan wannan kujerar sarautar sannan wannan yanayin naki cetonshi zamuyi idan baiji kin rikitashiba tayaya zai nace miki har kisamu irin biyan buqatar dakikeso kinsanfa yanadajin kai sosai irinsu koda sunason abu tofa basanunawa dan haka yazama dole kishanye duk wani magani dayake gurinnan kafin jibi maza d'auka kisha kowanne agabana " babu yadda Hamidat ta'iya dole tasha badan ranta yasoba

Wata katafariyar masarautace wadda tahad'a abubuwa dayawa akwai karamci da mutunci ga tausayi da sanin yakamata ammafa akwai izza wajan hukunta duk Wanda yayi badede koda kuwa d'an gidanne Sarki Jabir shine kekan kujerar mulkin garin akwai masarautu dayawa a qasanshi sarki Jabir matan shi 4 amma abin mamaki bashida yawan yara yaran shi biyar 5 hassan da Hussein sune banya kuma sune yaran uwar gidan shi wato Hamut da hammat se Ansar qanin su me shekaru 20 kafin haihuwar Ansar sarki Jabir yayi aure aure har 3 bayan Hajiya Kilishi wato mahaifiyar su Hamut amma duk su biyun babu wadda tayi koda bari se amaryar shi mai yara 2 mace da namiji Fadila da Fadil duk sa'oin Ansar ne hakan yasa sarki Jabir yakejin tsunanin son yaran shi duka hajiya mariya da hajiya hajara sunyi masifar tsanar yaran duk itako hajiya Fulani wato mahaifiyar su Fadil da Fadila rayuwarta tana cikin tsananin kunci sabida rabantada sarki Jabir wajan biyan buqatarta ta aure tun bayan haihuwar Fadila sekaru 18 kenan sabida tsakanin Fadil da ita tazarar 2 yrs ne tarasa wane matsayi sarki ya ajeta

Itako hajiya Kilishi matada wata matsala agun sarki Jabir se gun hajiya hajara da hajiya Mariya musamman agun yaran dasuke riqo hajiya Mariya tana riqon yara har 3 Kumsat da Amir da Jamil itako hajiya hajara yara 2 Haisam da Amina hajiya Kilishi natason 'ya mace sosai hakan yasa taroqi sarki akan tanason riqe marainiya bayan tahaifi Ansar da 3 yrs babu wani tantama ya amince inda taje gidan marayu ta amso Hanan tana cikin tsumman goyo wato tana jaririya kasancewar tagama shayer da Ansar da 1 year yasa batasamu damar shayer da Hanan ba sede akabata madara sosai hajiya Kilishi takejin tsananin son Hanan har yanzu Hanan batasan ba hajiya Kilishi bace ta haifeta sabida taroqi sarki Jabir akan bataso Hanan tasan haka yakuma jama sauran matan nashi kunne Ansar da Fadil da Fadila har cikin zuciyar su sund'auka Hanan jininsu ce sabida lokacin da'aka kawota basuda wayo Hanan yarinyace kyakkyawa sosai tanada haquri sosai tanada mugun zurfin ciki tanafama da Asma tayimata kamu sosai da'alama da'ita akahaifeta sabida tun da hajiya Kilishi tad'akkota sukefaman yin magani amma ina gashi har ta girma amma Asman tananan sunyi masifar shaquwa da Ansar da Hamut amma Hammat ina yatsani Hanan sosai tunda Hajiya Kilishi tad'akko Hanan yaji tsanarta cikin zuciyar shi hakan yasa Hanan takejin tsoran Hammat sosai

Hamut yanada sanyi sosai da haquri da kauda kai akan abu yanada kunya sosai amma kas yanada rauni akan duk wani abunda yakeso dan kuwa bai'iya miqa zuciyar shi akan abinda yakesoba miqata yakeyi duka yanada masifar biyayya agun iyayenshi duk abinda sukeso koda bayaso haka zehaqura koda zai cutu shid'in pilot ne shiyasa baya samun zama yanason Hamidat sosai kamar ranshi duk irin kunyar shi amma baya iya 'boye soyayyar Hamidat cikin zuciyar shi tun tana 'yar 12 yrs yake tsananin sonta tun daga lokacin duk wata hidimarta shine yakeyimata duk da kuwa gidansu akwai mazan kud'i hatta hidimar skul d'inta shine mahaifin su Hamut da mahaifin su Hamidat wah da qanine dangantakace tajini sosai Sarki Jabir shine babba akwai fahimta tsakaninsu sosai mahaifiyar su tanada rai sunayimata biyayya sosai mahaifin su yajima darasuwa mahaifiyar su tanacikin masautar tanada masifar sosai batada wasa ko kad'an hakan yasa kaf matan sarki Jabir suke jin shakkarta sabida idan tace hakatakeso ayi tofa babu makawa se'anyi tanaji da Hamut sosai samada Hammat sabida sauqin kanshi batashiri da Hammat sabida halin shi

Shiko Hammat yanada Zafin zuciya sosai ga kafiya akan duk wani ra'ayi nashi bairagama kowaba cikin masarautar kaf se mahaifiyar shi da mahaifin shi yatsani soyayya koda bata tsakanin mace da namiji bace duk wani abu wanda zaiso bayasonshi sabida bai yarda da wata soyayya ba seta tsakanin iyayen shi amma yagasgata yanason abu 1 tsananin so makuwa wato D'an uwan shi Hamut yanajidashi sosai kamar ranshi shine kad'e yakesashi yayi abu koda baiyi niyyaba yasashi yabari koda kuwa yakafe akan abun kowa acikin masarautar yana jin tsoran Hammat hatta su hajiya Mariya dan take zeyima rashin kunya idan Sarki Jabir yayi magana yabar cikin masarautar natsawon lokaci har se Sarki Jabir yaje yadawo dashi sabida baya iya jure rashin shi a cikin masarautar idan kuwa yadawo tofa kowa yashiga uku cikin gidan yadinga jamusu masifa kenan wajan sarki shidin Soldier ne me babban matsayi baya had'a hanya damace komi kyanta ko matsayinta sabida yatsani mata sede mahaifiyar shi kawai Sarki Jabir yaso suyi aure lokaci d'aya amma ina sabida shi Hammat yace bashida ra'ayin hakan cikin ranshi dole akabarshi

Da Hamut d Hammat suna tsananin kama idan suka jero tare baka'iya ganesu sabida komi nasu iri d'ayane tsayinsu farinsu komi se abu 2 wanda yabanbantasu halinsu tawani 'bangaran se yanayin idanun su Hamut yanada manyan idanu masu d'aukar hankali farare ne tas shima Hammat idanunshi manyane masu saka sakka da fargaba acikin duk wani sassan wanda yayi tozali dasu amma shi blue eye gareshi sewani ratsin fari Wanda yazagaye black din cikin idon nashi wannan kenan

Sosai akeyin hidima cikin wannan katafariyar masarautar dagani kasan bikin d'an gatane jiniyar isowar motocin Hammat yasa kowa yashiga cikin hankalin shi daga hadimai har dogarawa masu tsara wajan walima kuwa kowa tsayawa yayi sabida wasu sunyi zaton Angon ne kimanin motoci 7 ne suka danno kai cikin katafariyar harabar cikin masarautar kowacce akwai tambarin sunan Yarima Hammat jikin number motocin itako wadda yake ciki akwai tambarin STARS guda 2 a jikin motar se 'yar qaramar tutar Nigeria ajikin gaban motar

Cikin sauri sauran soldier suka fito suka bud'e mishi murfin motar kowannensu yana riqe da bindiga kamar zasu yaqi idon shi sanye da baqin glass fuskar nan tashi amatuqar tamke wani irin tsaki yaja yakwantar dakanshi jikin kujerar babu alamar zaima fito

Tsayin lokaci sannan yafito yadubi inda ake shirya kayan walimar yaja tsaki yanufi cikin masarautar part d'in mahaifiyar shi yashiga yana shiga Hanan tayi saurin miqewa tace " barka dashigowa yaya Hammat " wani irin mugun kallo yawatsa mata hakan yasata saurin barin Parlour nufar bedroom d'in hajiya kilishi yayi yana shiga yahangi Hamidat da wasu daga cikin qawayenta zaune saman wata lallausar darduma gabansu da fruit kalakala sosai yaji ranshi yayi mugun 'baci yaja tsaki yafita boko amsa gaisuwarsuba yana fitowa yacikaro da Hajiya kilishi duban ta yayi fuska babu walwala yace

" Haba Ammi mekuma wannan yarinyar takeyi cikin masarautar nan ayau inace segobene za'a d'aura auran shine tawani zo tun yau " murmushi Hajiya kilishi tayi takama hannunshi tazaunar dashi tace " Huseen kenan to ay haka al'adar masarautar taku take kafin d'aura aure ake d'akko amarya balle wannan datake yar gida kagama tunda kadawo shikenan sekahalarci wajan walimar kaida amaryar bro d'in naka tunda kaga shi bayanan " jin haka yasa Hammat sake tamke fuska sosai had'ida maida tabaran shi yamiqe yace " Ammi tofa inde danine sede afasayin wannan walimar subari segobe idan bro na yadawo " daga haka yasakai yafita mirmushi Hajiya kilishi tayi tace " Huseen kenan uban rigima "

Haka kuwa akayi walimar batare da Hammat yako leqa wajanba washe gari har misalin 02:20 amma Hamut bai'iso ba kuma yakira tun dare yace jirginsu yataso gashi d'aura auran 02:30 ne dole akad'aura aure batareda Ango ya'iso ba a'bangaran su Hamut kuwa hazone yahana jirgin nasu sauka sefaman shawagi sukeyi ganin haka yasa Hamut saka rigar iska maisaukar lema d'aurawani yayi saman kujerarshi yamusu sallama yadiro daga sama yakusa isowa babu zato yayi ido hud'u dawata qatuwar bishiya kafin yayi wani yunquri yadaki wannan bishiyar saurin yin baya yayi dakanshi dakuma girjinshi hakan yasa qugunshi da cikinshi suka bugu sosai wani irin mugun ciwon ciki dana mara yaji alokaci d'aya qarasa fad'uwa qasa yayi cikin tsananin azaba yashigayin salati ciro wayar shi yayi cikin qarfin hali yakira Hammat yasanar dashi abinda yafaru dakuma Inda yake kafin wani lokaci sukazo babu jira akasureshi zuwa asibiti kowa hankalinshi amatuqar tashe Sarki Jabir Hajiya kilishi hajiya Fulani da mahaifiyar Hamidat wato Momcy se mahaifin Hamidat su hajiya Mariya kuwa suna gida suna addu'ar Allah yasa Hamut yamutu tsayin lokaci sannan doctor yafito duban su yayi cikin damuwa yace

" Maimartaba muje office muyi magana " cikin tashin hankali Sarki jabir yace " nan duk iyayenshine kafadi meye matsalar " ajiyar zuciya doctor yayi yace " gaskiya Maimartaba Hamut yagamuda muguwar jarabawar ubangiji yasamu babbar matsala wadda tsakaninshi da mace sede kallo sabida bazai iya sauke haqqin aure wajan saduwaba sakamakon buguwar dayayi aguqunshi dakuma cibiyarshi yajawo mutuqar wasu jijiyoyi bance bazai warkeba har abada sabida komi yanagun Allah to amma dakamar wuya mude anan bazamu iyaba kuma bana tunanin akwai wani doctor dazai iya sede nace kuyimai addu'a " saga haka doctor yabar gurin cikin damuwa ta'be baki Momcy tayi tace " tab lalle ayko yazamadole yasakarmin 'ya bazai yiwu tazauna da mace ba " kallon mamaki kowa yabita dashi


_Marmyn Zarah CE_ 👌🏻🤝🏻
*⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*


*NA*


*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_



```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*


AND NOW
```MUSAYAR RUHI```



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*




*Page 3 & 4*




*S* osai zuciyar Hammat tayunquro duban momcy yayi cikin 'bacin rai yace " toseme dan ansakar miki yarki to ammafa kisani duk sanadintane wannan abun yafaru na tabbata idan badan wannan auran ba bazaiyi gaggawaba wajan sakkowa daga jirgi ba sannan fad'ar doctor bafad'ar uban giji bace in sha Allah bro na zaiwarke nankusa kisani komameye yasameshi shi yafi qarfin akwatantashi da mace namiji ne tsayayye "

Daga haka yanufi room din da Hamut yake afusace dubanta mahaifin Hamidat yayi cikin 'bacin rai yace

" Salma kece kike fad'in haka dabakinki tabbas kinzama butulu to amma kisani idan har nine mahaifin Hamidat to batadawani miji wanda yawuce Hamut koda kuwa bazai warkeba har abada idan nasakejin wannan banzan furucin senayi mugun 'bata miki rai " shima barin gurin yayi cikin 'bacin rai Sosai hankalin Sarki jafar yatashi itako hajiya kilishi wasu hawaye...


Read / Download MUSAYAR RUHI Book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album