Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

KARSHEN ZALUNCI Book 2 Complete Hausa Novel Document by KARSHEN ZALUNCI Book 2


KARSHEN ZALUNCI Book 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 6704



KARSHEN ZALUNCI Book 2

Reading Time: 0 Hours

Added On: 12, Jan 2024

Author: Mansur Usman Sufi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08137237071

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 35.56 kb

File Type: txt

Views: 655+

Download: 216+

Last download: 21 hours ago

Description/Story: Karshen Zalunci book 2
Littafin yaki
Rubuta labari
Mansur Usman Sufi
08137237071
Babi na ɗaya

Sa’adda aka ci gaba da kallon-kallon tsakanin dakarun ke biye da Suhaimat matar marigayi sarki Urwat da wannan zakanya.
Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa talatin a na wannan kallo-kallo daga can sai dakarun suka zare makamansu suka zaburi dawakan su izuwa inda zakanyar take suna aihu da kururuwa mai firgitarwa.


Koda ganin hakan sai zakanyar ta sake dako wawan tsalle a karo na biyu ta dira a tsakiyar dakarun, tana gurnani mai ban tsoro.
Nan take aka ruguntsume da azababben yaƙi mai matuƙar muni da ban tsoro gami da ban al’ajabi.

Wohoho! Tabbas mai ƙarfi sai Allan ya isa ana fara wannan artabu ne wani abin al’ajabi ya fara gudana, domin halitta guda ɗaya jal ta addabi mutum dubu biyu ta zame masu alaƙaƙai sun rasa yadda za su yi da ita.
A duk sa’adda dakarun suka kaiwa zakanyar hari sai ka ga ta wurƙita haɗe da zamewa ta zillewa saran kafin badakaren ya sake ɗaga takobinshi, zakanyar ta dako tsalle sama ta sanya farantata ta tsire mashi idanu ruwan cikin ya tsiyaye take ya sulale ƙasa daga kan dokinshi yana mai kurma wawan ihu a wasu lokutan idan ta bangaji badakare a kirjinta take badakare da dokinshi za su make ‘yan uwansa dakaru fiye da goma sun zube a ƙasa matattu, kai wasu lokutan ma idan ta daki badakare a wuya sai ka ji ya karye ya yi ƙara ruƙus!! Ƙas! Ya faɗi matacce ko shurawa bai yi ba.


Haƙiƙa waɗannan dakaru suna ganin tashin hankalin da ba su taɓa ganin irin shi ba, domin kafin cikar rabin sa’a zakanyar ta kashe fiye da rabin su.
Babban abin da ya dugunzuma hankalin dakarun kuma ya fusata su shine. Gashi dai ƙiri-ƙiri suna saran zakanyar da makaman su amma sun kasa koda kwarzanar jikinta, nan fa dakarun suka fusata ainun suka zage damtse suna kaiwa zakanyar miyagun hare- hare.
Nan fa karafniyar ƙarafa da ihun mazaje, haniniyar dawakai haɗe da gurnanin zakanyar ya cika dajin baki ɗaya. Ƙura ta turnuƙe sararin samaniya saboda yadda dawakai ke yin turmutsutsu, kofatunsu na kartar kasa.

Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce idan wuya ta kai wuya sai ka ga ZARATAN MAYAƘA suna neman cika wandunansu da iska domin TSIRA DA RAYUKAnsu.


Hakanne kuwa ya faru ga sauran ‘yan tsirarun dakarun domin koda suka ga cewa a kowanne lokaci za su iya baƙuntar barzahu sai suka cika wandunansu da iska da nufin tserewa.
Amma sai zakanyar ta dinga ƙure masu gudu tana turmushe su suna faɗuwa ƙasa matattu, kafin wani lokaci ta zubar da gawarwakinsu a ƙasa.
Koda samun wannan nasara sai zakanyar ta yi girgiza sannan durfafi inda Suhaimat ke kwance tare da jaririyar ta, koda ta ga halin da Suhaimat ke ciki sai ta ruga izuwa bakin wata ƙorama ta guntso ruwa a baki sannan ta dawo inda take ta fesa mata ruwan a kan fuskarta.
Faruwar hakan ke da wuya sai Suhaimat ta ja dogon gwauron numfashi gami da ajiyar zuciya, idanuwanta suka buɗe tarwai, kuma ta miƙe zaune ya yin da ta yi arba da wannan zakanya sai ta razana ta ja da baya tana mai ɗaukar jaririyarta ta ƙanƙame ta a kirji.
Koda ganin halin da Suhaimat ta shiga sai zakanyar ta juya ta ruga izuwa cikin wannan kogon dutse da ke cikin dajin.
Cikin matuƙar farin ciki Suhaimat ta miƙe tsaye ta matsa izuwa inda wannan ƙorama take ta yiwa jaririyarta wanka itama ta tsaftace ƙazantar dake jikinta, sannan ta dawo izuwa ƙarƙashin wata bishiya, ta zauna ta shiga shayar da jaririyarta tare da shafa gashin kanta zuciyarta cike da matuƙar farin ciki.
Kuma ta shiga tambayar kanta a cikin ranta tana cewa shin wane ne ya kashe waɗancan dakaru, ko kuwa wannan zakanyar ce?.
Amsar tambayoyin da ta kasa bawa kanta kenan, a cikin wannan hali ne zakanyar ta dawo izuwa gare ta, bakinta riƙe da waɗansu ƙunshin ciyayi ta ajiye a gaban ta a wannan karon bisa mamaki sai Suhaimat ta ji ko kaɗan ba ta tsora ta da ganin zakanyar ba.
Ba tare da fargabar komai ba Suhaimat ta ɗauki ta shiga warware ƙunshin, ai kuwa sai ta ga ashe nau’ikan kayan marmari ne a ciki, dangin su ayaba da inibi kawai ta shiga ci har sai da ta ƙoshi sannan ta fasa kwakwa ta shanye ruwanta zakanyar na tsaye a gefen ta tamkar mai jiran umarni,
a sannan ne ta lura cewa a jikin zakanyar akwai alamun jini take ta fahimci cewa ita ce ta hallaka waɗannan dakaru domin ta ceci rayuwarta da jaririyarta.

Mu haɗu a babi na biyu
Ƙasaitaccen littafin yaki mai cike abubuwan al'ajabi da darasin rayuwa
Karshen Zalunci book 2
BABI NA BIYU
Rubuta labari
Mansur Usman Sufi
08137237071
Dukkanin abin da ya wakana tsakanin Suhaimat, zakanya da dakarun sarauniya Abidat.
Abidat ta gani a cikin madubin tsafin ta tun daga farko har ƙarshe. Koda ganin wannan al’amari sai takaici da baƙin ciki suka turnuƙe ta ta ji tamkar ta kurma wawan ihu.
Ba komai ne ya sanya ta wannan baƙin ciki ba, sai domin ta tabbatar da cewa a halin yanzu Suhaimat da jaririyarta sun tsira daga sharrinta.
Babban abin da ya dugunzuma hankalin ta kuma ya jefata cikin damuwa ainun shi ne wani al’amari da ta gani a cikin madubin tsafin ta.
Ta gano cewar wannan jaririya da Suhaimat ta haifa ita ce za ta kawo KARSHEN ZALUNCIn ta daga doron ƙasa. Asalin dajin da Suhaimat ta haihu a ciki ya kasance mallakin wannan zakanya mai tattare da abubuwan al’ajabi ana kiranta da suna Juraima.
Binciken bokaye da MATSAFAN DUNIYA ya tabbatar da cewa dajin Baitul-Shazwas na ɗauke da wata takobi ta musamman mallakin sarkin bokayen aljanu na duniya Sababul-Ukub, babu wani mahaluki walau mutum ko aljan da zai mallaki takobin face ya zamewa duniya ANNOBA DARI.
MANYAN SARAKAI haɗe da matsafa
da JARUMAN DUNIYA sun rasa rayukansu bisa muradin mallakar takobin, domin zakanya Juraima ba ta barin duk wanda ya raɓi dajin a raye. Bisa dole bokayen suka janye ƙudurinsu na shiga dajin Baitul Shazwas domin mallakar takobin Saiful-Imfal.
Abinda binciken ya ƙara tabbatar masu shi ne babu wani mahaluki da zai mallaki takobin Saiful Imfal da zakanya Juraima face wata jariya da za a haifa a dajin na Baitul Shazwas, sai dai ba a bayyana masu ga nahiyar da za a haifi jaririyar ba.
kuma zakanya juraima na ɗauke rabin sirrikan tsafin sarkin bokaye a jikinta, takobin Saiful-imfal na ɗauke da sauran.
Tsakanin Sarauniya Abidat da zakanya Juraima akwai gaba mai tsanani tun iyaye da kakanni, domin mahaifinta da kakanta sun rasa rayukansu ne ta hanyar mallakar
takobin Saiful Imfal, kuma lokacin da mahaifinta yana raye ya gargaɗe ta a kan kar ta kuskura ta ce za ta shiga dajin Baitul-Shazwas domin ɗaukar fansa.

Nan fa Sarauniya Abidat ta ƙara cika da matuƙar baƙin ciki tana mai tambayar kanta a cikin ranta tana cewa.
“Hakika na tafka babban kuskure da har na bari Suhaimat ta shiga dajin Baitul-Shazwas yanzu gashi ta haife abin da ke cikinta yanzu shi kenan ba ni da ikon hallaka Suhaimat da jaririyarta har sai ranar da ta fito daga dajin Baitul Shazwas.”


Daga wannan rana Sarauniya Abidat ta kasance dare da rana bata aiki face gudanar da bincike a halarar tsafinta, domin ta gano lokacin da Suhaimat za ta fito daga dajin Baitul Shazwas.
Bayan Suhaimat ta kammala kintsa cikinta da waɗannan kayan marmari sai Zakanya Juraima ta juya, ta nufi kofar wannan kogon dutse tana mai yiwa Suhaimat nuni da ta biyo bayanta.
Ba tare da gardamar komai ba Suhaimat ta miƙe tsaye ta bi bayanta tana rungume da


jaririyarta a kirji, da shigarsu cikin kogon dutsen sai ke da wuya sai Suhaimat ta ga kogon ya gauraye da wani irin haske na ban al’ajabi, sannan yana cike da dukkanin kayan more rayuwa da ɗan adam zai bukata, kai wani abin ma Suhaimat ba ta taɓa gani ko jin sunan shi ba.
Al’amarin da ya yi matuƙar ɗaure mata kai kenan kuma ya ba ta mamaki ta kama kalle-kalle da dube-dube.
Ba tare da ta jira wani umarni daga Zakanya Juraima ba sai kawai ta je ta kwantar da jaririyarta bisa wata shimfiɗa ta lulluɓe ta da mayafi sannan itama ta kwanta domin ta rintsa amma sai hakan ya gagara, ba komai ne ya haddasa hakan ba, sai domin raunukan da ke jikinta na yi mata zugi da raɗaɗi kuma inda wannan badakare ya harɓe ta da kibiya yana yi mata ciwo.


Sai da zakanya Juraima ta kawo mata wani ganyen bishiya ta murza ta sanya a raunukan, sannan ta kwanta barci ya ɗauke ta.
Wannan shi ne abin da ya faru da Suhaimat matar marigayi sarki Urwat na birnin Nurul-Kusuf a lokacin da ta tsira daga sharrin sarauniya Abidat ta birnin Sin.

Al’amarin baiwa Sunaila kuwa tun sa’adda sarauniya Abidat ta bata renon jaririn dattijon Safwan, sai ya zamana cewa dare da rana tana bawa jaririn kulawa, kuma suka...


Read / Download KARSHEN ZALUNCI Book 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album